HUJJATA PART 1 (ONE)
.
Zaune
take tamike kafa tana kadasu daya kan daya, hankalinta akwance kana ganinta
kaga wacce bata damuwa kuma duniyan yazomata cikin dadi dasauki alokacin,
tadauki remote.
.
Tadanna
takai tashan mbc bollywood wanda suke film din ashqui 2, a nutse take kallon
tana kuma fahimtan metake kalla, kallon yadau dadi sosai, taji sallama tuni
tadaure fuska don tasan mai muryan, yashigo hankalinsa nagunta tare dacewa
walida nadawo, tadaga kai tajefa mishi hararar sannan tajuya tacigaba da
kallonta, baice komaiba yasa kai yashiga dakinsa saboda inda akwai sabo yasaba,
yasan hakanne sannu da dawowarsa, zuwa yayi yayi wanka yacanja kaya yayi
sallan. Azahar sannan yafito sanye da kananun kaya, yanufi dinning table sannan
yazauna walida abincin fa? Shiru ba amsa ! Saida ta kwashi minti shida sannan
tace akan bakasan wacce take maka girkin bane zaka min magana? Kakirata mana!
Baice komi ba yanufi kitchen din gydan nan yatarar dA mai aikinsa mrym tana kan
hada abinicin cikin bacin rai anma sanyin murya yace mrym ya abincin nawa?
.
Tadurkusa
cikin ladabi tare dacewa yanzu nake shirin hadawa nagama kayi hkr, baice
komaiba yajuya cikin mintuna tazo tajera tsaf tafita yabude yahau ci, ba
aladansa cin abincin mai aiki ba anma kasancewar tun aurensa da matarsa wanda
yakai wata hudu yanxu kenan ta. Kaurace damasa girki tace sai mai aiki, bahali
kullum yaje gidansu cin abinci anma bayanda ya iya dole yakoyi cin na maryam
yarinya yar kimanin shekara 17 wacce take girki, kuma yalura yarinyan akwai
tsafta sosai , duk da yana tausaya mata. Kasancewarta karama anma bautan.
Datakeyiwa matarsa Allah ne kawai yasani, itace wanke wanke shara, goge goge,
wanke bandaki hatta dakinsa da ita take shiga tagyra tuni yadakatar da ita
acewarsa indai walida bazatayiba to shi yahakura zaiyi dakansa, aikuwa hakanne
dakansa yake wanke bandakinsa. Yagra dakinsa, matarsa kuwa daga ci sai sha sai
wanka taci kwalliya tazauna kallo, kokuma aje biki ko suna ko kasuwa, gun
kwanciya ma sai ranshi yabaci yake samun kanta, ko kuma ita tanada bukatansa,
duk bakin cikinta yana shanyewa ne saboda sunyi sOyayya da walida tsawon
shekara bakwai tarike masa amana tana sonsa anma yarasa meyasa daga aurenta
komi yacanja all their plans are gone, yanzu yadawo mata hoto acikin ygda, yaci
abincin yamike tsaf yafita baya gurun dayake shan iska yana karanta jarida
ahaka har lokacin sallah yayi yayi alwala yanufi masallaci, anan yazauna harsai
da akayi ishai yadawo, yashiga daki yasamu mutumiyartasa agaban tv yawuce daki
yakwanta bacci. .. Walida kuwa tamike tsum tayi wanka tashiga daki takwanta
cike da farin ciki ko rashin damuwa aranta, washegari tafito ta tarar mrym
tagama duk wani hidiman gydan. Donhaka kawai tayi wanka taje gaban dinning
sannan tace mrym ina yahaya?
.
Mrym
tagaysheta sannan tace yafita aiki bayan karyawa tadaga kai, nan takarya tayi
wanka tsaf tashirya tadauki mukullin motanta. Tashiga kasuwa tasiyo atamfofi 5
super da holland, sannan takoma gyda tadauki ferfesun kazan datasa maryam
tamata tun dasafe tawuce gydan surukanta wato gydansu yahaya, sallamanta gydan
bakowa sai maigadi don haka saitasa kai tashiga cikin gyda hajiyansa tagani a
falo ta tsuguna harkasa tagaysheta haj. Fatima kuwa ta amsa cike da murna da
farin cikin samun suruka mai hankali, nan kanwarsa tafito hafsat itama dagudu
tafada jikin walida , hajiya tace ke zaki karyata, hafsat taringa dariya nan
suka gaysa da walida, walida tabawa hajiyan ferfesun kazan, da atamfofin sannan
tace hafsat tashirya takaita shopping tunda sunday zatakoma skul, kasancewar
tana boarding skul, hafsat na tsalle tamike suka fice, yahaya kuwa yakoma gida
yaji shiru tabbas tafita ne, yazauana yakira mrym tare da tamabayanta ina
walida tace batasaniba itama, anma tafita tun safe, ranshi abace yayi dialing
numban walida tana gani alokacin tana driving tuni tabAwa hafsat tadauka hafsat
tadauka kafin tayi magana tajishi yana fada! Walida kikiyayeni.
.
Kifita
idona, dasauri tace yaya wai tana tukine, saiyayi shiru yakashe wayan, uhm
gydansu taje kenan, wannan wacce irin makirar yarinya ne? Saita siye zuciyan
iyayensa ko yaje musu complain suyita karyatashi mtsww, yaja tsaki yajefar
dawayan, bayan tagama wa hafsat shopping tayi sallama dasu tadawo hankalinta
akwance, hafsat kuwa tana shiga tace hajiya kiga duk kokarin da anty walida
takeyi yaya matsifa yake mata, nan tabata labari, ran hajiya yabaci, tuni
takirashi alokacin walida tashigo yana son mata magana yaga kiran mahaifiyarsa
yadauka yadan rutsuna nan tahaushi da fada, yanzu dannan duk gwaninta da maatar
nan. Takeyi kai baka gani? Kasamu mace tagari anma kana wani irin rayuwa matan
yanzu dai sai ahanakali karungumi matarka kuzauna lafiya banson tashin hankali
karka kuskura. Kabatawa yarinyannan rai, yayi gum takashe wayanta, nan. Ya
ajiye wayan ko kallon walida.
.
Baiyba
itakuwa dma tasan zaa rina, tanemi gu tazauna tajawo remote abunta. baccinta
tanufi dakin maigidan nata, yana sanye da jallabiya dauke da quran ahannunsa
bayan idarwa yarufe, abinda yake burgeta kenan azamanin yanzu amasu shekarun
shi bakowa zaka samu mai rikon addini irinshi ba kasancewarshi matashi mai ji
dakanshi, yhy saurayine dan shekara 27 wanda yayi aure a kuruciyarsa, dogone
chocolate, yanada dara daran ido, wanda shiyafi jan hankalin duk macen data
kalleshi, gakuma saje agefen fuskanshi, gashinshi yadan taru luf luf mai laushi,
shikadai ya isa ya tsuma zuciyar mace, balle ki gangaro kan hallayansa, veri
jovial mutum yanason raha, yanada hazaka sosai, mutum ne mai sin mutane da
talaaka, anma kasancewar zaman gydansa yasa yanzu kullum kaganshi kamar marar
lafiya. , tabbas bahaushe baiyi karyaba dayace mace itace gyda, yarufe qur'anin
sannan yazo kan gado yaja bargo zai kwanta, ta matso tajanye bargon, swthrt
magana nakeso muyi, baice komai ba , tace so nake infara zuwa aiki, ya kalleta,
sannan yajuya ban amince ba, nan tayi narai narai da ido tafara kuka abinda ya
tsani ji kenan, wit ol his hrt yanasonta dell make a beta lyf, anma meyasa take
masa wasa da rayuwar aure? Yace saikin gayamin HUJJAN ki na abubuwan dakikemin
tun bayan sati daya da aurenmu! Ta kalleshi duk jikinta yayi sanyi anma tuni ta
danne ranta sannan tace inada HUJJATA , kuma mai karfi ne, anma saninsa baida
faida agareka, yayi murmushi wanda yafi kuka ciwo yaja bargonsa yakwanta tuni
ta bi jikinsa dole yanutsu yasaitu kafin yace Allah sa hakan shiyafi alheri,
dasauri takara shige masa tana murna, thn u bea I. Love uu, yace I love u more,
duk da akwai wasu damuwan aranshi, toh meye hujjanta? Ahaka sukayi baccinsu,
ita cike da kwanciyan hankali shikuwa cike da tunani da fargaba, washegari
dasafe mrym hartaa gama hada musu komai, akalla tayi sati uku tana zuwa aikinta
inda yanemata a federal secretariat.
.
Dasafe
karfe 9 take fita shikuma sai karfe. Goma yake fita tabarsa da mrym yana zaune
mrym zataxo ta yi aikinta tafice afalon, kullum da hijabi harkasa, wataran
yakirata yatambayeta yanayin karatunta tace masa a jss3 tafita, yace tanaso
tacigaba? Tace masa ae! Aikuwa tuni yafara nema mata wani makaranta mai kyau,
yanema mata admsn a dolphin maria colledge duk batare da walida tasaniba
saidaya gama yakira walida tana kallo saidata gama kallonta kafin ta isa
gareshi yace nayi deciding mrym zata koma makaranta, walida tace wat?
impossible!bazai yiwuba aikin. Fa? Yace duk zatayi. Karki damu, nan tace ita
bata yaddaba, aikuwa yace zai gayawa hajiyansa tafi HUJJANTA na rashin son mrym
taje makaranta ahaka babu yadda ta iya don arayuwanta abunda zaace ankai gun
haj.
.
Wanda
badaidai bane ace tayi bataso, acikin satin mrym tafara zuwa makaranta, da
asuba take tashi tayi aikinta karfe bakwai yhy yabata kudin break da kudin abun
hawa tatafi makaranta inta dawo radaura musu abinci , nan harna dare kafin tayi
magriba da isha tayi baccinta, tuni tasaba kuma daga gani tanajin dadin
makarantan, ahankali kanta yake budewa tahadu da wayayyun mutane, gakuma maryam
din ba tayan baya ba wajan kyau, fara ce , doguwa ko ina ajikinta zamzam coca
cola nake nufi kenan, tana da gashi sosai, kirar fulani, gashi Allah yabata
kwalkwalwa tuni tafara jansu a ajinsu ss1 data shiga duk ta bata cika kula ko
shiga hidiman mutaneba kasancewar tasan asalinta anma Allah yabata farin. Jini
maza da mata har malamai kowa sonta yake, tayi kawaye sosai,anma mostly akwai
kawayenta biyu dasuka shaku sosai, akwai zahrau aminu yakubu, da kuma zainab
ibrahim kawule, sunshaku sosai hartake gayamusu halin datake ciki nacewa ita
mai aiki ne! Basu kyankyameta ba don duk mai hulda mrym dole yaso taraiya da
ita, macece mai gudun bacin rai watarana walida baztaaje aiki ba dinhaka da
mrym tagama shiryawa zata tafi tace bazatajeba itama ko incase tana needing abu
fa? Nan ta tube uniform tazauna, aikuwa yhy yana fitowa yaganta yace lfy mrym
ba uniform? Kafin tayi magana tuni walida tace ae ininace bazatajeba saboda
nima bazan fitaba incase zanyi needing wani abu, yaja tsaki keeeh . - ISMAIL SANI







0 comments:
Post a Comment