Blogroll

BANNER 728X90

Friday, 4 January 2019

CANJIN RAYUWA Kashi Na 1 (Shafi 36-40) - ISMAIL SANI


CANJIN RAYUWA
 [Kashi na 1]
(Shafi 36-40) Tare da - _Halima K. Mashi_
Post By ISMAIL SANI

Ya’u ya ce, ba za ka gane ba,ai ubanta zata sa ya tozarta ka.ga zagin wulakanci,lsmail ya ce, ALLAH ta zage ni sai na mare ta.ya’u don dariya sai da motar tayi kamar zata sullube masa.ya ce gaskiya kar kayi wannan kuskuren, lsmail ya ce,nanne kaduna? ya’u ya ce,eh amma ba garin kaduna ba ce zariya ce,nan dama baka taba zuwa ba?kai ni ina zaton sokoto kawai muka taba zuwa yin gasar karatu lokacin ina SS1. ya’u ya ce gaskiya ni ban zata ba,in na kalle ka sai ka ce ka taba fita kasashen duniya. lsmail ya ce,ni kifin rijiya ne ban san ko in ba.in mun zo kaduna ka nuna min ina jin labarin garin ina son zuwa.    ya’u ya ce,shike nan za nuna maka,tun daga na yake nuna masa garuruwa har suka isa kaduna.ya ce, bari in bi da kai ta cikin garin maimakon by pass tunda kana son ganin garin. shikenan lsmail sai kalle-kalle ya ke yi.ya ce,garin ya birge ni.amma duk a zato na ya fi haka,yadda sunan kaduna ya cika ko ina.ya’u ya ce,zaman garin yana da dadi saboda ba su shiga harkan abinda bai shafe su ba.lsmail ya ce,wani ya taba bani labarin garin ‘yan karya ne ko?ya’u ya ce eh, to ni ma dai haka na ji ana cewa,to muna da ‘yan’uwa.

Suna zuwa katsina gurin innarmu,mu ma mukan zo,ba wasu masu karfi ba ne,amma komai za su yi sai inga suna son yin wanda yafi karfinsu,ni ma sai na amince ‘yan karya ne.amma daga baya lokacin ina yin tuki a nan kaduna a wata unguwa wai ita unguwa rimi sai na gane ba wai karyace da su ba,yin hakan a jinin ‘yan kaduna ne yake.ka gane malam lsmail? Su mutane ne masu son yin komai me kyau,kuma basu da kyashin sayan duk abinda ransu ke so,ko da kudinsu kenan idan za a aje maka dan kaduna mai dubu dari biyar,da dan wani gari mai milyan biyar,za ka ce dan kadunan ne mai milyan biyar,wancan mai dubu dari biyar.lsmail ya ce na gane,in ko haka ne sun burgeni.saboda ni mai irin raayi na kenan,arziki na ALLAH ne,in na samu zanyi abinda nake so da halas di na.haka suka yi ta labarin ‘yan kaduna har suka kai abuja garin manya.

Shi kam a ranshi ‘yan kaduna sun yi mashi, yana son mutane masu test,wadanda ba komai ne ya yi masu ba.

Tafkeken gida ne na gani na fada,tunda suka doshi gidan lsmail ke mamaki sai ka ce fadar shugaban kasa,duk yadda yake kisima gidan a rashi ya wuce nan,tun kafin su shiga ma kenan.su na shiga sai ya ga ma kamar wata sabuwar duniya ce,wannan mutumin wane irin kudi ya mallaka?lsmail ke tambayar kanshi.  dama tun kafin su kara so ya kira hajiya ya fada mata cewa sun iso unguwar,ita kuma ta kira momi nafisa ta sanar da ita.lsmail ya na jingine jikin mota,wani matashi ya iso wurinsa ya ce,wai wanene malam lsmail?ya ce,ni ne. ya ce,to zo mu je,ya kalli ya’u direba zo muje, ya ce,a’a,ni dama aiki na shine na kawo ka,kuma na kawo ka,yanzu zan juya.lsmail ya bashi hannu suka yi sallama bayan gidan suka nufa inda suka nufa gefen yara, suka je ya bude wani daki, an ce ka shiga nan.lsmail ya kalle shi,ba mu gaisa ba?ya mika masa hannu suka gaisa.ya ce,suna na lsmail,kai fa?ya ce hamisu, kuma nine direban yaran gidan nan.ga daki na nan kusa da na ka,mu biyu ne a cikin dakin,ni da me share-share,game da kula da fulawoyi.lsmail ya ce, ALLAH ya sa mu amfani juna,hamisu ya ce,amin.

lsmail ya shiga yana kallon dakin tamkar ba dakin masu aiki ba,hamisu ya ce,ai kurar dakin ba ta yi yawa ba,don kanin momi bai yi sati da tafiya ba,da cikin dakin yake.lsmail ya ce,kurar ba tada yawa ma kenan,amma duk da haka bari in dan kakkabe,ya shiga ciki sosai,hamisu ya ce,in zaka yi sallah ga bandaki nan.lsmail ya ce,tunda muka taso,duk inda sallah ta same mu,sai mu tsaya muyi ta.ya ce, shikenan baka da wani nauyi a kan ka.lsmail ya gyara daki mai dauke da katifa katuwa,sai duruwar ajiye kaya,sai kuma dan teburi a gefan katifar. hamisu ya ce,bari in sa a sanar da momi cewa ka iso,kuma naba ka masauki, yanzu saura abinci. kusan minti ta latin da fitar hamisu,sai ga wani kuma dauke da plate a rufe da cokali da kuma ruwa.suka gaisa,

Kusan minti ta latin da fatar hamisu,sai ga wani kuma dauke da plate a rufe da cokali da kuma ruwa.suka gaisa,sannan ya ce,ga abincin ka.shi ma nan haka lsmail din ya sake gabatar masa da kansa, suna na lsmail kai fa?ya ce, suna na jabiru,kuma nine mai dafa abincin rana da dare,lsmail ya bashi hannu suka gaisa.bayan fitan sa ne ya bude plate din abincin, dafa dukan shinkafa ne,ta ji kifi da alayyahu,ya ci ya koshi,ya sha ruwa ya koshi.daga nan barci ya sace shi, saboda gajiya bai taba yin doguwar tafiya kamar haka ba daga katsina zuwa abuja.                          can da ya farka ya kalli agogo,sai ya ga lokacin sallah ya karato,nan da nan ya tashi yayi alwala,ya fito waje bakin gate don ya ga karamin masallaci a gurin. hamisu yana zaune kusa da maigadi suna hira,yayi masu sallama,suka amsa. ya ce,hamisu ina ladani ya kira mana sallah lokaci yayi, hamisu ya ce,ba a fa kiran sallah a masallacin nan,sai dai kawai kowa yayi alwalarsa ya shiga yayi sallah.lsmail ya ce,saboda me?hamisu ya ce,ni dai haka na tarar suna yi,to ai duka-duka mu uku ne ke yin sallar,ni da maigadi da mai shara.ko maigidan ba kullun yake sallah a cikin masallacin ba,ya fi yi a cikin gida.yaron sa namiji daya. ya kai shekara shabiyu, amma ko shi ba a turo shi. lsmail ya ce,ko ku uku za ku iya jam’i,don haka ni kam zan kira sallah.               lsmail ya shiga ya ga da abin magana da komai,yana kwada kiran sallah daidai lokacin motar alhaji bashir tana kunno kai ko da direban ya tsaya bai fito ba,sai da ya ji karshen kiran sallah,muryar tamkar balaraben saudiyya. maimakon ya shiga gida sai ya samu kansa da nufar masallaci,gurin da aka tanada don alwalla,nan ya je ya tattara hannu rigarsa ya soma alwalla.su hamisu suka tsaya suna kallonsa, nan dai lsmail yaja su sallah,hamisu yayi masu ladanci,sai dai alhaji shi kadai ya tsaya a sahunsa.      suna idarwa suka fito, lsmail ya gaida alhaji,ya nuna masa jin dadinsa da sallar da ya kira har suka yi jam’i.lsmail ya ce.

Ismail ya ce,alhaji zan yi wata magana,amma in na bata maka rai ka yi hakuri,amma hakki ne a kaina in sanar da kai.bai kamata ka tsaya ba a sahu ba,duk da cewa mu din masu nema a karkashin ka ne,amma gurin allah ba bu bambamci,musamman gurin sallah.sahu dole ne,na san alhaji ya sani.tuni kawai na yi masa,alhaji ya ce.na gode ba komai,sannan ya nufi cikin gida.

sai karfe tara na dare, kuku ya sake kawo masu abinci,da ya karba sai ya fito,ya samu hamisu shi ma yana cin nasa,ya aje ya ce, me zai hana mu rinka ci tare?hamisu ya ce,ba damuwa bisimillah.suna ci hamisu ya ce,na ji mamaki da na ga kana magana da maigidan nan,wai me ka ce masa ne?lsmail ya ce,wata magana wanda bai dace in fito na fada ba,a takaice kuskure ne nayi masa tuni, hamisu ya ce tabdi,gaskiya ka yi saa,ai maigidan na mu mafadaci ne na gaske. wanda bai son a shiga huruminsa,kuma yana da wata yarinya mara mutunci,wanda kowa ke tsoron ta,hatta matan gida. sai dai gaskiya yana biyan kudi da tsoka,shi ya saka ga na jure,ni ne direban yaran gidan,don haka na fi kowa wulakanta. lsmail ya ce,na san ta,kuma ni malaminta ne,na zo in koya mata karatun addini. hamisu ya dago ya kalle shi,yayi dan murmushi, lallai ina mai baka shawara,ka nemo duk wani hakuri da kau da kai,ka kara a kan wanda kake da shi. lsmail ya yi ‘yar dariya,ya ce,ta taba yi maka?ya ce,to da wanda ta raina ma iri na?       ban san iya sau nawa ta zuba min miyau a fuska ba.banda kalaman cin mutunci.lsmail ya ce,kai kuma sai ka tsaya kana kallonta? hamisu ya ce,ya ya zan yi,tunda ina so,dubu talatin yake biya na a wata,ba ko’ina zan samu haka ba.lsmail ya ce,sannu da kokari,amma ni kam ba zan dauki wulakancin nan ba.sun jima yana ba shi labara,kafin suka yi sallama.   haka da asubahi ya kwada kiran sallar farko, MIMI wacce lokacin ta yi sallama da kalil dinta wanda suke chatin tun misalin taran dare,ta bude idanunta tana jin sabon lamari a gidansu.ta tashi ta sauko daga kan gado,ta kunna wutar dakin na ta,

Sannan ta nufi windo,ta yaye labule tana kallon masallacin,wanda dama saitin windon nata yake.tabbas masallacin nan ne,to wane ne wannan da karfi hali?lta tunda ta ta so bata taba jin an kira sallah a masallacin nan ba.ta koma ta kwanta ta saki tsaki.za ta ga mai wannan kokarin na hana mutane barci.ta fara barci ta ji an sake kiran sallar,aka shiga masallaci aka yi sallah,ba ita ta samu barci ba sai da aka idar da sallah.  don haka bata farka ba sai shabiyu,ta yi mika tare da hamma,ta silalo kafarta kasa kan lallausar kafet. tamkar sarauniya ta ke jan taku har zuwa bandakinta, wanda aka tsara shi da kalar pink,kalar da take bala’in so,bandakin da yafi na kowa tsaruwa a gidan, hatta mahaifinta.ta shiga bahonta,bayan ta cika shi da ruwan dumi,sama da awa daya ta dauka a wanka,ta fito.gurin shafarta daya ne da kayan sawanta, bata cika yin kyale-kyale a fuska ba, hoda kadai sai jambaki bayan mai,amma tsadarsu ta ishi talaka jari.

Ta saka wando baki irin mai kama jikin nan,da riga ja,ta ja dogon gashinta ta kama shi da bakin ribbon. ta soma wanka da turaruka.ta nufi gadonta ta dauki wayarta tana dubawa,miss call kusan goma dadin ta,da na dear khalil,dana hajiya guda biyu.    bakin gadonta zaune tana kiran layin dadinta,ya daga tare da cewa uwata ya ya aka yi?cikin shagwaba da muryarta din nan wanda ke fid da sauti a hankali cikin salo ta ce, dad na ga miss call din ka ne fa?ya ce,uwata har na fita baki tashi ba,lafiyarki kalau ko?ta ce,eh dad,emm yawwa dad wane ne jiya cikin dare ya hana ni barci da kiran sallah?ya ce, malaminki ne,gabanta ya yi bala’in faduwa ta ce,dad shine da zuwansa zai canza mana tsarin gidanmu?mene ne nufinsa da haka?

Ya ce,babu komai MIMI,kin san malamai da son masallaci,yau ni mana samu yin sallar asuba a kan lokaci,sannan makwabtanmu sun shigo mun yi sallar tare da su.ta ce kash dad,yanzu gidanmu gurin tara mutane kenan? ya ce,kar ki damu musuluncin kenan,ina fata za ki sauko domin daukar karatu.

Gurin malamin na ki.kuyi amfani da falon baki, ko falo na ki ke so?ta ce,aa dad ya tsaya can falon baki,ba falon ka ba,da wannan bakauyiyar kafar tashi.ya ce,shikenan tunda naima tana gida ita mata soma karatun,in su ahmad sun dawo da yamma sai yayi masu,ta ce,shikenan dad,bari in kira hajiya naga ta kirani.ya ce,ok nima yanzu muka gama waya,ki ce ina gaida ta.cikin fargaba ta kira mahaifiyarta,hajiya ta daga cikin lallausar murya ta yi sallama,MIMI ta amsa tare da cewa,ina ki ka bar waya?ta ce,ina barci yanzu nayi wanka sai naga miss cal dinki.hajiya ta ce,na zaci kin fita gurin karatu ne?ta ce,hajiya ban san ma ya zo ba sai yanzu dad ke fada. ln na yi break zan yi yanzu,hajiya ta ce,ki maida hankali saboda ki san abinda zaki bauta ma ALLAH mahaliccin ki.suna yin sallama kiran kalil ya shigo sai da yayi daf da tsinkewa ta daga,wannan wani raayinta ne.ta ce, hello dear ya aka yi?ya ce,ba komai ina son in ji muryar ki ne?yanzu ki ka tashi?ta ce, fh,yaya hutu?ya ce,ga shi muna yi,don ALLAH ina son in zo gidanku wannan karon,ina jin tsoro kamar zan rasa ki,kar ka damu dear na fada maka don juna aka yi mu,ina jin haka a jiki na.      ya ce, lovely har yanzu ban yi mafarkin haka ba ina ganin sai zancen ya je gurin manyanmu.ta yi ‘yar dariya, ka san fa dad naka ba zai yarda ka yi aure yanzu ba, ni kuma in dad dina ya ganka guri na kila ya ce,zai min aure,ka ga sai matsala ta samu.

ya ce,na fahimce ki,ba na son na sha wahala a aurenki kamar yadda na sha kafin na samu amincewar soyayarki na garu.ta yi ‘yar dariya cikin salon maganarta ta ce,dear ka manta da haka,bari na karya,ya ce,to shikenan sai in mun hadu online ta ce,tam.cikin tafiyarta tamkar mai tausayin kasa take saukowa daga benenta,wanda ita kadai ce a sama ta ke mallakin kato falo da dakuna uku. daya dakin barcinta daya kayan karatun ta,tun daga computer zuwa kasa, dayan kuwa rufe yake duk da cewa shima da komai a cikinsa.

(Zan ci gaba)..

#IP


0 comments:

Post a Comment