Blogroll

BANNER 728X90

Friday, 12 January 2018

ANTIN YARA Page 61-70

koda suka isa gida maryam kuka kawai takeyi,su abdallah kuwa suna gidansu mum dan ba'ama zo dasuba.
Iyayen maryam sun tausaya mata sosai,musamman yah ibrahim,ahankali aka fara shirye shiryen tfyansu kano domin aduba lfyar maryam kamar yadda shukrah tagaya musu,mama da yah ibrahim da kuma muh'd ne suka tafi kano inda dad d'in manosh yabiya musu kud'in jirgi se aminu kano.
  Kamar da wasa doctor ahmad babban dr ne wanda kowa yasani, ya iya aikinsa sosai batare da b'ata lokaciba cikin 2days akayiwa maryam duk wani gwajegwaje daya dace,maganan shukrah dai ya tabbata domin k'odan maryam kusan dukma sun samu matsala wanda dolene se'an mata sabon dashe,ma'ana se'an sa mata wani k'odan.
Hankalin mama ya tashi sosai,tanata hawaye,yah ibrahim da muh'd ne suke rarrashinta tare da kwantar mata da hankali,kwanansu biyar suka koma yola.
   Mamaki sosai akayi dajin matsalar maryam,mahaifinta yace zai fitar da ita zuwa *india* domin ayi mata aiki,amma sam maryam tak'i tace ita babu inda zataje se manosh ya dawo.
Su marwan sunyi iyakan k'ok'arinsu zuwa masallatai da kuma malaman sunna akan abinda ya sami amininsu manosh,sun raba kud'ad'e sosai kota ina zuwaga marasa k'arfi domin atayasu da addu'a Allah ya baiyana manosh.
Addu'oi sosai aketayi ba dare ba rana, kusan kullum ake kiran number manosh amma sam baya shiga yau kusan sati kenan.
Abdallah da alfiya kuwa tunda akace musu daddynsu yayi tafiyane shikenan suka yadda tunda dama yanayin tfya yayi 2to3month ma baidawoba,dan haka sam basu damuba.
Ahankali mahaifin manosh yake shirye shiryen tfyansu maryam india batare da sanin mahaifin maryam ba.
   Idan kaga maryam da miher dole ka tausaya musu sun rame sunyi wani iri,barema maryam da damuwan yayi mata yawa kuma dama kunsan batada auki.
Miher tana son bro nata wanda kowa yasan da hakan,shiyasa majid yake iya k'ok'arinsa domin kwantar mata da hankali,hakama maryam kullum nasiha iyayenta suke mata da kuma yah ibrahim dasam baya son ganinta cikin damuwa,hakan yasa zaibada k'odanshi guda d'aya asawa maryam,amma sam koda aka gwada baiyi daidaiba.
K'awayen maryam gabad'aya sun zama abin tausayi domin ganin irin halin da maryam take ciki,rashida tace da marwan ita aje a gwadata idan har a'a iya sawa maryam k'odanta to wlh ta bayar da guda d'aya tunda zasu iya rayuwa da d'ad'd'aya, marwan yace karki dau luv zamu samo mafita amma ina tausayin aunty sosai wlh,friend na manoh dukkansu basa iya kocin abinci saboda rashin abokinsu,kowa yasan irin shak'uwar da take tsakaninsu.
Mahaifiyar manosh kuwa ta zama Allah sarki domin sun d'auki son duniya sun d'aurawa manosh dayake shine d'ansu na fari.
Kuma duk wanda yasan manosh ko kuma wata alak'a dake tsak'aninsu tofa dole ya shiga damuwa. Cikin sati biyu lbrn manosh ya baza ko ina dayake sojane mai kwazo ga kuma taimakon marasa k'arfi,sam bayida kyama kamar dai matarsa wato *auntyn yara*.
  Lubna ce kwance a gidansu tana cewa mum nata gaskya mum lokaci yayi daya kamata in taimakawa maryam akan taimako da rufin asirin data min,mum zanje inba maryam k'odata guda d'aya,bazan iya bari anemo k'odan wani dabamu saninshiba asawa maryam.
Hajiya khadija tace lubna lfyarki kuwa bana so ki sake sa bakinki cikin maganannan,kuma wace irin taimako maryam tayi miki haka? Lubna cikin muryan kuka tace mum kinsan me,ada bani da wata mak'iya irin maryam saboda yadda nake k'aunar bro manosh araina,babu wanda yasan hakan dagani se miher naso in sanar dashi amma dayake shiba mijina bane senaji cewa ya samu mata a girei,nayi bak'in cikin hakan sosai tunma bansan wacece yake nemaba,ranan muka had'u da maryam da kuma friends nata a yakubu shopping plaza na yarda keyn motata batare dana saniba ta biyoni ta bani anan ne muka san juna da maryam harna karb'i numbernta. Mum daga bayane na san cewa maryam itace yarinyar da bro manosh yake so,tun daga lokacin tsanarta ya shiga zuciyata nayi niyan d'aukan mataki sosai dan in raba maryam da bro manosh. Lubna tayi shuru tana kuka sosai cikin tausayawa tace mum kinsan me? Nice nasa akayi kidnaping maryam lokacin da aka kusayin aurensu,nasa akayi nesa da ita yayinda nake samun duk wata lbr agun miher wanda ita kanta basan inada hannuba,tun daga numan nasan aka sakeyin nesa da ita mum zuwa jejin yankari dake jihar bauchi,amma dayake Allah ba azzalumin bawansa bane dukda cewa ita maryam tasan cewa nine nasa ayi mata hakan amma sam tak'i gayawa ko iyayenta da suka haifeta ta b'oye zancen cikin ranta domin bataso asamu matsala tsakanin familynmu da kuma familyn su bro manosh saboda tasan irin shak'uwa da soyayya dake tsakanin bro marwan da kuma bro manosh hakan yasa tayi shuru tabar komai aranta mum.
  Marwan yana tsaye abakin k'ofa ya kasa shigowa yana sauraron lbrn da lubna take baiwa mum nasu,wanda mamakine sosai abaiyane a fiskarsa.
Lubna taci gaba da cewa mum bayan maryam ta dawo gidane,shi wanda na basu aikin yace inje muyi magana domin maryam tasan komai kuma k'ila zata tauna musu asiri,tsoron kar sunana ya fito dan yadda nake tsoro bro marwan yasa ranan na fita naje can inda saddam yake ya bayan GG..kuka lubna ta fashe dashi tace mum koda naje juice ya siyaya mana nidashi,ban kawo komai a rainaba saboda k'ishin danakeji a wannan lokacin kawai sena canye wannan juice d'in,shikenan ban sake sanin inda nakeba kodana farka senaji jikina wani iri mum saddam ya cuceni yamin fyad'e....
   Mum ta kama salati tare da kwalla a idanunta itama lubna haka tace naso na kira miher amma senayi tunanin bazata rufamin asiriba dole za'a sani,shine na kira maryam ban b'oye mata komaiba na gaya mata komai,kinsan me mum hankalin maryam ya tashi sosai take tazo inda nake mum ta taimakamin ta kimtsa kaina hawayene cike a idanunta tare da tausayawa,muna tare da ita su bro manosh sukazo gun nida maryam muna ciki d'akin ab'oye a toilet munata addu'a saboda maryam tayiwa bro manosh k'aryan cewa tana cikin kasuwa suna sayayya se kuma gashi yazo inda muke a d'akin saddam,hankalin maryam ya tashi sosai badan komaiba sedan jinin dake kan katifar saddam kuma gashi ni babu yadda nake alokacin jikina rawa kawai yakeyi. Cikin ikon Allah mukaji suna cewa saddam ya gudu kenan tunda gashi harda kwad'o ajikin kofan,kuma wlh mum babu wanda ya kullemu ta waje,seda suka tafi muma muka fito da sauri shine maryam ta kawoni har gida tayi miki k'aryan cewa bigeni akayi da mota naji ciwo a k'afa,kuma mum maryam itace ta had'ani da ibrahim wanda yake matsayin yayanta,bata b'oye mishi komai akan batun fyad'en da aka minba ta gaya mishi komai,tare da neman amincewarsa akan ya aureni,k'aunar da ibrahim yakeyiwa maryam ne yasa ya aureni badon yana sonaba,kuma wlh mum koda na rana d'aya ibrahim bai tab'a nuna kyamarsa akainaba se kauna da kulawa na musamman kuma har gobe babu wanda yasan da wannan zance fyad'e dagani se maryam da ibrahim duk maryam tayi hakanne don ta rufamin asiri mum da kuma k'aunar da take min,gaskya mum maryam macece wanda ba'a samun irinsu a zamanin yanzu,ina ganin k'aunarta aduk lokacin da muka had'a ido da ita.
Dan haka zan iya yiwa maryam komai koda hakan zaisa in rasa rayuwatane to lallai zanbawa maryam k'odata guda d'aya watak'il zan iya biyanta da alkhairan datamin arayuwa......
Ba mum kad'aiba harta marwan dake tsaye a waje ya shigo rai a b'ace,take lubna ta gudu bayan mum dan yadda ta ganshi tasan sarai yaji komai dan haka ta fara kuka sosai tana cewa waiyo mum dan Allah karki bari ya dakeni wlh ina da ciki mum,bro marwan dan Allah kayi hakuri.
Mum tace karka tab'ata marwan nace ka kyaleta! Cak marwan ya tsaya yana kaima lubna sakon harara yace baga irintananba mum,daga taimako gashi ta b'ata mana suna tayi abin kunya,ke bari kiji ingaya miki dabadan cikin dake jikinkiba wlh yau dase na kusan karyaki wawiya mara hankali dole kibar mana gidanmu dan dama ke 'yar tsuntuwace ni kad'ai iyayena suka haifeni tsintattiyar mage kawai ya fita rai a b'ace ya fisgi mota.
Daga lubna har mum kuka sukeyi lubna tana bin mum da kallo mai d'auke da tambaya tace mum menaji bro marwan yake cewa? Wainiba 'yarku bace? Tsuntoni kukayi hakane mum? Mum da kuka yaci karfinta tace hakane lubna keba 'yarmu bace.
Lubna ta tsaya da kukanta tace tosu waye iyayena mum,a ina kuka samoni mum,meyasa kuka b'oyemin mum? Mum cikin kuka ta rik'o hannun lubna tace shi kanshi dad naku baisan iyayenkiba lubna domin ce mishi nayi na tsuntokine,lubna keba 'yar kowa bace se 'yar Alhaji muh'd atta. Zaro ido lubna tayi tace wanne kenan mum? Mum ta rungumeta tace wanda dai kika sani mahaifin maryam *auntyn yara* ku 'yan biyune lubna maryam itace babba sannan ke uwarku d'aya ubanku d'aya da ita lubna ki gafarceni dan Allah,cikin mamaki lubna ta janye jikinta tace taya hakan ya faru kenan mum? Kina nufin kowa yasan hakan kenan? Mum tace babu wanda ya sani dagani se hajiya iya kakarki lubna. Kuka sosai lubna takeyi tare da barin palon da gudu......
Da sauri auntyn yara ta waigo donjin me lubna take cewa,kai se sukayi gwaru akansu atare sukakai hannu goshinsu don sunji zafi dukkansu.
Maryam ta karb'i wayan hannunta tare da cewa sannu lubna ita lubna sannu take mata suna masu kallon junansu cike da murmushi,maryam tabar d'akin da sauri ta koma d'akinta tare dasa wayan a kunnenta tace cikin zumud'i tace *hello peach*, muryan manosh yace apple ya kike yasu abdallah,lfyanmu lau peach nah ina ka shiga ka barmu da tashin hankali da kewa,yace kiyi hakuri apple yanzuma na kirakine dan in gaya miki cewa ki mance dani a rayuwarki kwatakwata kamar baki tab'a had'uwa daniba domin bazan sake dawowa garekuba apple ki cireni a zuciyarki su abdallah kuwa ki gaya musu cewa na mutu kuma mamaci baya dawowa ta yadda zasu manceni daga k'arshe kuma ki samu miji wanda kike ganin zai rik'e min su alfiya ki aura koda d'aya daga cikin abokainane wannan shine dalilin dayasa na kiraki kinji apple,ya k'arashe maganan cikin murya maiban tausayi.
   Ita kuwa maryam tunda taji abinda ya fara fad'a taketa zubda hawaye harya k'arasa. Jin tayi shurune ya sake kiran sunanta apple pls am sorry,na zab'i hakanne dan in cetoki daga sharrin shukrah bawai don wani abuba...bai k'arasa maganaba naryam ta katseshi da cewa ya isheni haka peach bana son sakejin komai daga gareka indai akan wannan magananne mubarta kawai,yanzu ka gayamin ya yake a ina kake me kuma shukrah tayi maka haka peach? Yadda manosh yaji muryan apple bashi yasan tana cikin tashin hankali,yace karki damu da sanin halin da nake ciki apple dama abinda na kira in gaya miki kenan ina miki bankwana ta karshe.
  Da sauri da kuma ihu tace pls peach karka katse wayannan ka saurari abinda zance maka,ina cikin wani hali sosai peach na rashin lfy,k'odata gabad'aya sun b'aci dole se an min dashe,yanzu haka ana shirye shiryen fita dani india ne dan haka ka saurareni wata k'ila maganata dakai na k'arshe kenan zaiyu idan najema bazan dawoba dan haka inaso ka yafemin dukkan wasu abubuwa dana maka na rashin sani,sannan ina so ka sani har inbar duniya babu wani d'a na miji dazan iya zama dashi bayan kai kuma har inbar duniya bazan dena yin addu'a Allah ya d'auraka akan shukrah daduk wani abu mai cutarwa ameen,inaji ajikina cewa zaka dawo garemu peach,sedai bana tunanin zaka sameni sedai iyayenka da kuma yaranmu peach dan Allah ka kula min dasu domin kune farin cikina daga k'arshe ina k'aunarka k'auna ta hak'ik'a wanda baya k'arewa _i love you so much peach_, alfarma d'aya zan nema agunka shine inji kalmar soyayyata abakinka pls...?
  Kwalla sosai manosh yakeyi idanunshi kamar attarugu,amma ina bazai iya gaya mata kalmar so ko d'ayaba,dan haka yace ina miki fatan alkhairi apple se anjuma......
Kuka sosai maryam ta fashe dashi tana cewa peach dan Allah karka barni ka tsaya ka gayamin cewa kana sona dan Allah my captain,kuka sosai takeyi tana kallon wayan. Mama da lubna da suke tsaye akanta tun ihunta na farko sune suka rik'eta sunta rarrashi dan sunji dukkan hiran maryam da manosh d'in.
Yah ibrahim da babane suka shigo dajin muryan kukan maryam suna tambaya ko lfya? Nan lubna ta gaya musu komai,inda mamaki ya kamasu sosai. Yah ibrahim yayita kiran numbern amma sam baya shiga,maryam dai se kuka takeyi tana ta surutai kamar wanda ta zare tana cewa baba manosh yace in samu miji inyi aure yana nufin ya sakeni kenan baba,menayi mishi dazai min haka baba,nagaya mishi halin da nake ciki amma koya kula baba,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Lubna tana rungume da yarta itama kuka takeyi sosai,sam bata son ganin naryam cikin damuwa musamman ma datasan cewa yartace uwarsu d'aya. Hakadai ranan lubna bata koma gidantaba shi ibrahim d'inne ya koma saboda mahaifiyarsa ita kad'aice se mai musu girki. Daga baba har mama abin ya basu mamaki ganin yadda lubna takeyida maryam,bayan iyayenta sun rarrashetane se suka barsu a d'aki ita da lubna.
Yah ibrahim kuwa tunani iri iri yakeyi a zuciyarshi,ga kuma damuwan halin dayaga maryam aciki yau ya tausaya mata sosai harma yake tunanin inama dashine ya aureta da shikenan maryam bata da damuwa sam,amma ina haka Allah yake tsarawa kowa rayauwarsa. Wayarsa ce tayi k'ara number manish ne,mamaki yayi sosai tare da d'auka da sauri yace slm,wslm yaji muryan manosh,basu gaisaba manosh yace na kirane don inji cewa dagaskene za'a fitar da aunt india? Ibrahim yace eh hakane,manosh yace to shikenan idan kun dawo ka sama mata miji ka aurar da ita dan nikam bazan dawo garekuba na zab'i in zauna anan domin ceton apple zan iya jure komai ibrahim shiyasa nafiso ace kaika auri aunt ba waniba pls ka auri aunt nasan zaka kula da ita kamarni. Ibrahim yace mekake fad'ane captain insha Allah zaka dawo kuma kadena sa ran cewa wani abu zai same aunty babu abinda zai sameta da yardan Allah zaka dawo kushi gaba da zamanku munata addu'a kuma shukrah setasha wahala wlh muguwa...tsawa maikyau ibrahim yaji akunnensa ana cewa wlh k'arya kake ibrahim wahala kam sedai auntyn yara amma badai niba,kuma zanga yadda zaku karb'o my manosh daga hannuna dama kai kad'aine mai taka min birki kuma ina so kasan cewa my manosh yabarku kenan har abada bazaku sake ganinshiba,sannan ka gayawa mahaifin maryam ya kiyayeni wlh su dena b'ata lokacinsu waisu suna so suga bayana to wlh idan bai dena shiga gonataba sena tozarta maryam d'in da kuke ji da ita. Hhhhh ibrahim yayi dariya yace dama ashe kece shukrah,kece kika ari muryan captain kike so ki b'ata tsakaninsu da aunty,to Allah ya tona asirinki muguwa,ina so kisan cewa aunty tafi k'arfinki shiyasa har yanzu kika kasa mata komai shine kika b'ullo mata tasan muryan mijinta koh,tota Allah ba takiba wannan kad'ai bai isheki shukrah,komai kikayi seya warware hakan yana nufin bazaki tab'a samun nasara akanmu bane kuma mahaifintama yafi k'arfinki hatta shi captain yafi karfinki wlh kawai dai jarabawace Allah ya sauko mishi dashi kuma insha Allah zamuci wannana jarabawan muzuba dake shukrah *QUR'AN* yana sama da komai acikin duniyan kuma dashi zamu karb'o captain agurinki idan kuma kin isa toki hanamu d'aukoshi daga gareki kawai lokaci muke jira kekanki kisan duk duniya babu wanda captain zai bud'ewa zuciyarshi ta shiga ta zauna se *aunty* . Haushi da takaici yasa shukrah katse wayar
  Yah ibrahim ya tsinci kanshi dayin murmushin tare dajin dad'in sanin cewa ba manosh bane yayi magana da aunty shukrah ce. Take ya kira baba a waya ya gaya mashi komai,baba baiyi mamakiba dan yasan babu abinda aljanu basayi, take yaje ya sanar dasu maryam dan hankalinta ya kwanta.
Ai kuwa dad'i sosai taji tare dayin add'ua Allah ya kare mata mijinta ya kuma dawo dashi garesu.
Marwan kuwa yana kwance ne kawai amma yakasa bacci dan irin abubuwan dayaji yau da kuma gani. Tun bayan barin su lubna gidan yaketa tambayar hajiya iya kakarsa meke faruwane danshi kansa yasan akwai wani abu dayasa lubna tayi mata hakan amma sam hajiya iya tak'i cemishi komai se kukan nadama da taketayi babu sassaushi. Haka marwan ya gaji ya tafi gida gun mum nasu,koda ya gayawa mum nasu abinda lubna tayiwa hajiya iya sam mum batayi mamakiba,shima marwan d'in ya lura da yanayin mum d'in nashi wanda yasashi tambayar mum nasu yace wai meke faruwane mum nakasa fahimtar komai tabbas akwai wani abu dayake faruwa mum dan Allah ki gayamin.
  Marwan ya kamota suka zauna yana share mata kwalla.
Mum ta dubi marwan tace zan gaya maka marwan amma sekamin alk'awarin bazaka bari mahaifinka ya d'auki mummunan mataki akainaba, cikin rashin fahimta marwan yace banganeba mum?
Mum tace marwan dad naka yana k'aunarka fiye da komai a duniya,idan yasan abinda na'aikata tonasan zamana dashi yazo k'arshe, kaine zaka iya hanashi rabuwa dani d'ana saboda k'aunarka da yakeyi.
   Marwan ya sauke ajiyar zuciya yace namiki alk'awari mum har abada bazan bari ku rabu da dad ba. Mum tace nagode marwan, sannan ta fara bawa marwan lbr kamar haka...
.
marwan ya rasa mema zaicewa mum nashi,dan tsabar yadda jijinshi yayi sanyi kamar k'ank'ara. Cikin sanyi murya yace mum danasan abinda kika aikata kenan daban miki alk'awarin dana d'auka mikiba,amma koba komai ke mahaifiyata babu abinda zan iyayi ko kuma ince miki,sedai kiyi hakuri amma sam abinda kukayi baidaceba sam wlh mum abin babu dad'i ji. Matsowa yayi kusa da ita yana kwalla kamar yadda takeyi yace mum kidena kuka inaso kimance da cewa kin bani wannan lbrn,ki d'auka cewa har yanzu sirrine kamar yadda kuka rufeshi keda hajiya iya,dan gaskya mum nibansan ne nake cikiba a yanzu haka. Komin dad'ewa gaskya zai fito wanda bansan yazan tsinci kainaba a wannan lokacin da kowa zaisan me mahaifiyata da kakata suka aikata.
  Jiki babu kwari ya mik'i zai fita tayi saurin kamoshi tace dan Allah kaban mafita ya d'ana. Mum wlh babu wata mafita danasan zan baki akan wannan lamarin domin baki bani wani ilimi akan hakanba lokacin da kuka bani tarbiya keda dad. Mum tace nasan ban kyautaba shiyasa nake neman nafita marwan? Marwan yace mafita shine kisami dad ki gaya mishi komai tun kafin lubna tatona muku asiri mum.
Bayan fitan marwan ne mum taketa kukan dana sanin akan abinda suka aikata. Shikuwa marwan gida ya koma da zazzab'i mai k'arfi daya rufeshi,seda rashida ta kira dr muh'd a waya yazo gida yayi masa allura da kuma magunguna inda suke mishi sannu. Sam marwan ya kasa had'a ido da abokan nashi saboda tun a yanzu kunyansu yakeji bare kuma ace gaskya ta bayya kowa yaji.
  "Lubna ce kwance tana bacci ad'akin maryam hankalinta kwance,ita kuwa maryam se mamakin kulawar da lubna tayi da ita takeyi acikin zuciyarta tare dajin sonta a ranta. Wayan lubna ce yake k'ara koda maryam ta duba setaga yah ibrahim ne,daidai nan lubna ta farka tare dasa wayan a kunne tace hello,yace kin tashi lfy yasu aunty,tace lfyansu lau ya mama,yace tana lfy ina hanyan zuwa d'aukanki da fatan kin shirya? Ta murza ido tare da kallon maryam tace wlh yanzu na tashi ko wanka banyiba kabari se anjuma kad'an pls...? Yace ok naji amma ki tabbata kin shirya dan zamubi gidan marwan mu gaisheshi bayida lfy tun jiya zazzab'i mai k'arfine ta rufeshi wlh. Subhanallah!tobari kawai na shirya nan da 1hr sekazo.
  Maryam ta kalli lubna tace lfy? Lubna tace bro marwan ne ba lfy zazzb'i sosai,maryam tunda nake ban tab'aganin rashin lfyanshiba bro marwan yana sona sosai har cikin ranshi dukda zafinshi amma akan gaskya yake komai nashi i respect him so much aunty,maryam tace eyyah nima barina shirya muje tare inyaso zanbi gunsu miher zuwa yamma sena dawo.
Maryam ta gama shiri tsaf,ita kuwa lubna tana zaune tana k'are mata kallo,maryam tace naga kina zaune,lubna tace eh bazan maida kayan jikinabane shiyasa dan sunyi datti. Maryam ta gane me take nufi hakan yasa ta d'auko mata zanin da manosh ya saya mata tunda ta d'inka bata tab'a sawaba ta batashi tace ga wannan kisa,godiya sosai tayi ai kuwa nan danan ta mik'e tasa sun mata kyau sosai ajikinta ta juyo tace aunty nagode kayan sun amshi jikinki sosai wlh harda rungume maryam,azuciyarta tace nagode sosai 'yar'uwata jinin jikina.
  Mama ta shigo tace todai sekunci abinci kafin ku tafi,bamusu sukaci amma maryam kad'an taci dan dama tunda aka nemi manosh aka rasa tadena cin abinci. Ita kanta mama lubna tana burgeta kome dalili oho,ita kuwa lubna sakewa sosai tayi dasu ko'ajikinta dukda ta lura da cewa suna mamakin yadda ta sake dasu tazama kamar 'yargida.
  Gun motan yah ibrahim suka nufa bayan sun gaisa suka shige maryam ce a baya suna tfy ta hango manosh daga nesa. Peach ta kira sunanshi cikin mamaki wanda yasa yah ibrahim tsaida mota da sauri suka had'a baki tare da cewa ina yake? Tayi musu nuni da hannu zuwa inda yake tsaye ajikin wata black car. Mamaki sosai sukayi dan tabbas shine tsaye sanye da kakin sojojinsa ya hard'e hannaye yana duba agogon hannunsa bisaga dukkan alamu wani yake jira...
.
Marwan auren so da k'auna mukayi da dad naka kuma shi shi d'an wan mahaifinane auren dangi aka mana nida dad naka.
  Tun ina 'yan'mata Allah ya d'oramin son yara musamman mata,kowa yasan da haka a dangi. Bayan munyi aure da mahaifinka ne kusan 2yrs kafin na samu cikinka,bazan iya gaya maka burin da muka d'auka akan wannan cikinba,dan muna ta fatan Allah yasa mace zan haifa,amma se yazama kaine marwan na haifa,hakan baisa na fidda ran haifan maceba.
  "Marawan har kakai 12yrs ban sake sake samun cikiba,babu irin damuwa da tashin hankali da bamu shigaba harta dangi,dayake ansan yadda nake son mace,gashi dangi kam kowa namiji yake haifa ba mace ko d'aya. Hajiya iya mahaifiyar dad naka tana sona sona tamkar 'yar cikinta sam bata son ta ganni cikin damuwa,har zamuje gidan marayu d'aukan yarinya,amma se mahaifin dad naka wato wan mahaifina yace a'a bai aminceba,hakan yasa muka hakura har wata rana naje girei gun hajiya iya yini...
  "Muna zaune se aka zo da sallama wai wata mata tana nak'uda kuma ta galabaita sosai gashi duk mak'otan sunce bazasu iyaba sedai a nemo tsofi,sakamakon mijinta baya kusa,kuma yana fama da kansa ana tunanin idan an kaita asibitima kud'i za'a nema lokacin kuwa kowama yana fama da abinda zaicine. Hakan yasa nida hajiya iya mukaje gun wannan mata mai nak'udan wanda batama san inda takeba ta zama abin tausayi bata cikin haiyacinta sam.
  Munfi awa muna kanta cikin ikon Allah ta haifi bby girl kyakkyawa,kwalla ne ya zubo a idona dan ji nayi kamar in gudu da jaririyar,muna cikin murnan kenan sega wani kai ya fito ashe dai 'yan biyune dukkansu mata,murna sosai mukayi nida hajiya iya muna cewa ashe 'yan biyune shiyasa ta wahala haka.
    Tofa shine hajiya iya tace dama mijin natan baida hali kuma gashi har yara biyu,dan haka tace in tafi da d'aya tunda babu kowa a waje,duk wanda suke jiran haihuwan harsun gaji sun tafi saboda sunga bata haihuba. Ni kuwa banyi tunanin komaiba saboda yadda nake son mace,a d'ankwalina na nad'e jaririyan nasata cikin himar na koma gidan hajiya iya,acan na mata wanka da komai na koma gun hajiya na d'auki kayan jaririya d'aya dayake sund'an sayi kayan kad'an,na koma na sama mata.
Ita kuwa hajiya iya tayiwa jariya da uwar wanka ta kimtsasu saf,amma har'a lokacin uwar jaririyan bata farfad'owa harse bayan awa biyu,koda taga abinda ta haifa murna sosai tayitayi tare dayiwa hajiya iya godiya.
   "Bayan hajiya iya ta dawo gidane,tace maza in tafi da jaririyar gida kar asirinmu ya tonu,tsoro ya kamani nace tome zan gayawa dad naka? Tace zata mishi bayanin cewa an sami jaririyar ne a hanya aka ajiyeta kuma kowa na tsoron d'auka saboda yadda duniya ta canja,shine ita ta d'auka mana tunda tasan muna son 'ya mace. Dayake lokacinma dad naka yana umrah shine komai yazo da sauk'i kuma haka muka gayawa kowa na dangi da kuma abokan arziki harda kuma....
  Hajiya khadija ta tsaya anan da lbrnta tana kuka,marwan kuwa jikinsa yayi sanyi yama rasa me zaice mata saboda shidai asaninsa wannan abunda mum nashi da kakarsa sukayi sata kenan satan jaririya. Mum ta lura da yanayin marwa tayi saurin rik'o hannunsa cikin muryan kuka tace marwan karka manta kamin alk'awarin zaka taimakeni amma tun yanzu naga rashin jin dad'i afiskanka,marwan karkace komai ka saurari ci gaban lbrn..
  Haka na rik'e jaririyannan na samata sunan hajiya iya muna kiranta da *LUBNA* gata sosai ta samu agun mahaifinka,kuma dukkanmu muna sonta tsakani da Allah..marwan ya katse mum nashi da cewa naji mum kuma na fahimta,yanzu lubna 'yar gidan wayene,su wanene iyayenta a ina suke? Mum tana kuka sosai tace marwan iyayen lubna sunan a raye kuma acikin girei sannan 'yartama tana raye dan lubnan itace k'arama. Marwan ya mik'e tsaye yace mum baku kyauta ko kad'an wlh,wannan abinda kuka aikata bansan me zance akaiba kun kyauce sosai wlh kun raba yarinya da iyayenta da 'yar'uwanta yanzu idan maganannan ya fito waje duniya sukaji mum ya kike so inyi da raina,sunanefa zai b'aci mum ace mahaifiyata ta aikata hakan mum,da wani ido zan dubi jama'a musamman abokaina mum? Kwallane yake zuba daga idanun marwan yace a ina suke? Mum ta mik'e ta kasa dena kuka tace marwan se yanzu nake nadaman abunda na aika busa son zuciyata.
Marwan yace no mum,dukda tarbiyan da kuba lubna kiga dai abinda ta aikatawa *aunty* yanzu da asirinta ya tonu a lokacin da dawani ido zan kalli princ mum,kinsan yadda nake son manosh kinfi kowa sanin shak'uwarmu dashi da kauna dake tsakaninnu ashe ankama lubna ce tayiwa aubty haka daya zanyi,kumafa kiga ita *auanty* ne ta had'a lubna da miji nagari irin ibrahim,mum kinsan yadda ibrahim yake son aunty,wlh daya san lubna ce tayiwa aunty haka wlh bazai tab'a bariba,amma kuma duk wannan bai isaba kika yaudaremu dukkanmu dangi akan tsintota kukayi alhali bahaka maganan takeba haba mum... yanzu waye mahaifin lubna ki gayamin mum?
Cikin nuryan kuka sosai tace bakowa bane *illa mahaifin maryam aunty'n yara* marwan aunty itace twin sister'n lubna ita ta fara zuwa duniya kafin lubna,ta k'are maganan tana zama a k'asa kamar kayan wanki. What! Marwan ya tambaya da k'arfi da fiskan mamaki tare da juyawa yana kallon mum nashi kamar yaga dodo yana fad'in *innalillahi wa'inna ilaihir raji'un*,ita kuwa mum kuka kawai takeyi tana rik'e da hannun d'an nata...
.
Da sauri yah ibrahim ya tsaida motarsa suka fito dukkansu suka nufi gun da *manosh* yake tsaye,cikin mama maryam ta rik'o hannushi tace peach? Ahankali ya juyo yana kallonta kamar wawa,yah ibrahim yace aunty sakeshi...ai bai k'arasa maganaba seka wata kyakkyawar budurwa ta fito daga wani shago kawai ta d'auke maryam da mari tana cewa ke wace irin shashashace dazaki rik'emin miji?
  Ai kafin yah ibrahim yayi magana lubna ma tayi saurin d'auke budurwan da mari tace ai shashashun suna dewa wawiya jaka ke har kinkai a tab'a mijinki,yah ibrahim ne ya shiga tsakaninsu yanayiwa lubna fad'a,ita kuwa maryam sam bataji marinba tamaida hankalinta gun manosh da yake tsaye yanata kallonta baya ko kyafta idonsa. Ahankali ta sake dawowa gefensa tana mai zubda kwalla tace *peach* jikina yana bani cewa kaine dan Allah kacemin wani abu. Kawai setaji yace baiwar Allah banine wanda kike tunaniba,sunana *muawiya* sannan wannan matatace. Kuka mai k'arfi maryam ta fashe dashi tare dabarin gurin aguje zata koma mota nan sukayi kicimus da majid,kallon juna sukeyi har cikin ido tanata hawaye tace majid dan Allah ka k'are mishi kallo wancan ba captain bane duba kakinsafa dan Allah kazo muje nasan zaka iya ganeshi tunda tare kuka taso.
Da sauri majid ya karasa lokacin fad'a sosai akeyi tsakanin lubna da wannan budurwan tace cewa kisa maganata a ranki cewa senayi maganinki,lubna tace ta Allah ba takiba banza mara hankali da kyar yah ibrahim ya janyo lubna ya kaita mota gun maryam se faman kuka takeyi lubna ta zauna a gefenta tana rarrashinta. Majid yaje dabda manosh ya tsaya yana k'are masa kallo tun daga k'asa har sama,shima manosh d'in kallonsa yakeyi kamar dai yadda yayiwa maryam,majid yace *dude kaine*? Budurwan tace yau naga ikon Allah waiku wasu irin mutanene haka,kawai kunzo kun damemu kunat....tsawa mai kyau majid ya daka mata kimin shuru badake nakeyiba! Take ran budurwan ya b'aci idanunta sukayi jah jazur kamar attarugu tayi saurin rik'e hannun manosh tace kadaiga yadda akacimin mutunci amma ka kasa sewa komaiko,shikenan mutafi dan idan nacigaba da zama anan to lallai mutanen dake yankinnan kam zasu shiga cikin matsala. Yah ibrahim da majid suka kalli juna sukace matsala kuma? Daidai nan maryam ta fito daga mota da gudu tana cewa yah ibrahim wlh peach d'inane shine gashi yana min bye bye. Koda yah ibrahim da majid suka maida kallonsu ga manosh da budurwan se sukaga wayam,babu su kuma babu motarsu.
Mutanen dake gurin kowa kafa menaci ban bakaba kusan rabi duk sun gudu,su kansu yah ibrahim sun tsorata sosai,majid yace ina suka shiga? Maryam cikin muryan kuka tace wlh manosh ne yah ibrahim wannan duk aikin shukrah ce wlh sune lokacin da take magana kaida majid kuna kallon junanku se manosh ya juyo yana kallon inda seting motarmu take shine ya d'aga min hannu yanamin bye daga nan kuma suka b'ace yah ibrahim dan Allah kace tadawo min da mijina inda manosh ya tsaya nan maryam taje ta zauna agun daya ajiye kafafunsa tanata kuka,lubna da yah ibrahim ne suka d'agota dakyar suka kaita mota shima majid ya shiga nashi suka koma girei gidansu maryam.
Koda baban maryam ya samu lbrn abin shuru kawai yayi danya rasa mezaice,mama kuwa tanata rarrashin maryam tare da cewa lubna kekuwa meyasa kika rama mata marin?yanzu gashi kin mari aljana idan kuma ta d'auki matakifa gaskya bana son wani ya cutu ata dalilin maryam. Lubna tace mama zan iya bada rayuwa indai akan maryam ne kuma matuk'ar ina raye tofa sedai ad'auki raina bazan tab'a bari a cutar da itaba wlh har abada anyina farko kuma anyi na k'arshe wlh Allah ya isa bazan tab'a yafewa Allah ya isa mama....tanata kuka wanda hankalin kowa yadawo gun lubna se zagi da fad'e-fad'e takeyi wanda babu wanda yafahimci abinda take nufi se ita kad'ai.
  Maryam ce ta kamota tace lubna ki nutsu mana meyakawo zagi kuma nan lfyanki kuwa? Tace lfyata kalau aunty wlh an zalinceni kuma bazan yafeba Allah ya isa! Da k'arfi ta k'arasa maganan,nan dai hankalin kowa ya tashi akace gaskya akwai matsala,yah ibrahim ya kamota,takisam ta mannu ajikin maryam tanata kuka. Majid yace gaskya akwai matsala kodai shukrah ce ta maidata hakan? Hankalin kowa ya tashi domin kowama abinda yake tunani kenan.
Maryam ta rungumeta tace a'a majid shukrah bata isa ta mata komaiba lubna dan Allah ki bari kicemin lfyarki kalau kinji,lubna ta d'ago da kanta tana kallon maryam tace lfyta kalau aunty babu abinda yake damuna se abu d'aya,maryam tace menene wannan abun? Lubna kamar zatayi magana se kuma ta fasa domin yadda take k'aunar hajiya kadija aranta bataso ta tona mata asiri,nan ta sake fashewa da kuka tace kigafarce aunty bazan iya fad'aba sannan ta mik'e da sauri ta koma d'akinsu tanata kuka mai k'arfi,su kuwa aka barsu da kallon labule,kowa hankalinsa atashe kuma tunaninsu shine kodai shukrah ce tayimata wani abu akan marin data mata?
Bayan sun gama magananne yah ibrahim yace aunty kiramin lubna tazo mutafi,bamusu maryam ta mike jiki sanyaye tanata tunanin had'uwansu da manosh yanzu,tace dama rungumesa nayi lokacin dana ganshi,wayyo Allah peach Allah ya dawomin dakai ya mijina uban yarana i luv u so much peach dan Allah ka dawo garemu. Maryam bata sammata shigo d'akinba kuma ita ta d'auka cewa acikin zuciyarta take wannan maganan bata cewa lubna tajiba. Lubna ta dakata da kukanta tace kiyi hakuri aunty insha Allah bro manosh zai dawo gareki shukrah bata isatayi komaiba wlh,itama kuma lokaci da zaidawone baiyiba kidena kuka pls aunty dukda dai nasan yadda kikeji amma bana so inganki cikin damuwa pls kiyi hakuri mucigaba da addu'a kinji aunty? Rungume juna sukayi sunata kuka sannan maryam tace yah ibrahim yana kiranki wai kije ku tafi kuma dan Allah kugaida marwan kice nima zanzo ko zuwa gobe insha Allah. Lubna dai bata soba amma babu yadda ta iya seta mike ta shiga palon baba rai ab'ace tace baba mama se'anjuma sannan ta fita waje tanata kuka,mamakinta ya sake kamasu dukkansu haka dai suka fito suka tafi tanata kuka.
    Tun a hanya ibrahim yake tambayarta dalilin kukanta amma sam tamak'i kulashi har suka iso gidan marwan. Nanma da kukan ta shiga gidan amma tad'an tsagaita sukadai gaisa da rashida sannan tagaida bro marwan yanata k'are mata kallo ita kuwa sam tak'i kallonsa. Rashida tace lubna yanaga idanunki sunyi jah haka? Lubna tace bakomai,yah ibrahim ne yabasu lbrn abinda ya faru,ahankali marwan ya mik'e zaune yace kunga manosh? Ibrahim ya tabbatar mishi da zance,mamaki sosai sukayi dukkansu,rashida tace Allah sarki maryam Allah ne kad'ai yasan yadda takeji acikin ranta yanzu haka,dabadan rashin lfyarkaba danaje na d'ebemata kewa dan nasan tana cikin damuwa da tunani musamman ma yau data ganshi dan tana matuk'ar k'aunar captain sosai,hawayene yakebin idanun rashida,ita kuwa lubna fita tayi da gudu tana kuka bata tsaya ko inaba se cikin mota. Da sauri rashida tabi bayanta tana tambayarta ko lfya? Shi kuwa yah ibrahim lamarin ya fara damunsa sosai. Marwan yace ibrahim ina neman wata alfarma agurinka akan lubna,dan Allah duk wani abu da zata maka kayi hakuri kamata uzuri ninasan irin k'aunar da lubna takeyiwa aunty. Ibrahim yace bakomai wlh zamu tafi,haka dai sukayi sallama suka tafi rashida dai bataji komai daga gun lubna ba.
Yah ibrahim ne da lubna kwance akan gado yana cewa haba y luv yau kwana nawa kenan rabonda wani abu ya shiga tsakanina dake? Tace to ai period nakeyi shiyasa,yace amma fa kwananki uku kenan da gama period d'in nabarki ranan jiya kuma agidansu aunty kika kwana sannan kuma yau kicemin bakya mode? Cikin sanyin murya tace dan Allah kayi hakuri wlh damuwace tamin yawa bazaka tab'a gane kainaba shiyasa nake baka hakuri idan kuma ka yarda zaka gamsu kai kad'ai shikenan bisimillah nidai bazaka samu tallafinaba yau. Ibrahim baiji dad'in kalamantaba gashi yanada bukatarta hakan yasa ya daure ya juya yayi kwanciyarsa.
  Shurun dataji yayine yasa tasan cewa fushi yayi,ahankali take kiran sunanshi my luv dan Allah kayi hakuri karkayi fushi kamin uzuri tunda ban tab'a maka hakanba se yanzu banaso kayi fushi domin bana son tsinuwan Allah ya tabbata akaina kaji my luv tana rungume da bayansa ajikinta. Yace naji amma ki sakeni dan kina kara tayarmun da hankaline,bamusu ta sakeshi tare dayin godiya se wayansa ta fara ringing. Da sauri ya da'uka dan ganin mahaifin manosh ne mai kiranshi,bayan sun gaisane yake sanar dashi cewa tafiyansu india ran monday ne shida baba mama da maryam da kuma lubna,yah ibrahim yayi godiya sosai sanan ya ajiye wayar ya juyo yana kallon lubna yace tfyarmu ran monday amma banda ke,ta marairaice tace habamana my luv najifa lokacin dayacemaka da lubna saboda yasan kila zaku wuce 4month kuma dama ka'ida ba'ason miji yabar matarsa har tsawon watanni hud'u,yace to aike babu amfani zuwanki tunda kina hanani hakkina, dasauri ta rungumoshi tana dariya tace wlh nadena amma pls karka barni my luv kaga ai zan taya mama kula da aunty ko? Shima murmushi yayi sannan ya matseta ajikinshi suka fara sarrafa junansu kamar zasu had'iye junansu....
.
Bayan yah ibrahim da lubna sun samu cikakkiyar gamsuwa da junansune suka wuce toilet bayan sun tsabtace jikinsu ne se suka sake shirin kwanciya amma duk sun kasa bacci babu abinda yake musu yawo a kwakwalwa se b'acewar manosh da shukrah da sukagani d'azu agaban idanunsu kamar a fimlm.
  Wannan abu ya dami mutane dewa sosai harta wanda abin ya faru aaban idanunsu sun kasa yadda da hakan ya faru dan gani sukeyi kamar amafarki. Hakan yasa akakai lbrn gidan *radio gotel* wanda basusan da faruwan abun bama tofa gashi yanzu sunji agidan radio magadai ya baza ko ina agarin *Adamawa*. Hakan yasa majid yaje gidan *TV GOTEL* akayi hira dashi inda yake cewa aabansa akayi komai ba kuma tatsuniya bace gaskyane domin abokinsune wanda kusan kowa ya sanshi tunda sojane mai kwazo sosai. Hakan yasa akayita rok'on jama'a cewa sutaimaka a addu'a akan b'acewan captain manosh,kokuwa d'aukeshi da aljana tayi tsawon wata uku kenan harda kwanakima. Wanda matarsa itace maryam muh'd attah wanda akafi sani da AUNTY'N YARA mahaddaciyar qur'ani, cikin kwanaki biyu ko ina se faman rok'on ALLAH aeyi akan manosh da kuma duk 'yan'uwa musumai da irin hakan ya shafa,domin idan idan ka shiga damuwa tofa karkayiwa kanka addu'a batare dakasa 'yan'uwankaba.
    Maryam kuwa tun wannan lokacin ta sake shiga matsanancin damuwa fiye danada. ita kuwu lubna yah ibrahim yayi iyakan k'ok'arinsa dan yaji ta bakinta saboda canji dayagani tattare da ita musamman akan aunty, amma sam ta'i gaya mishi komai dan batamasan ta ina zata faraba.
Ana saura kwana uku tafiyansu aunty india,sega hajiya khadija agidan hajiya iya. Koda hajiya iya ta ganta seta fashe da kuka itama ma hajiya khadijan kukan takeyi,bayan sun gama koke kokensune hajiya khadija tace da hajiya iya dan Allah hajiya muyi k'ok'arin fad'an gaskya tunkafin su auntyn yara subar k'asar watak'ilama tfyarsu kenan bazamu sake had'uwa kuma gaskya bazan so hakanba yazama dole mufasa wannan dad'ad'd'an kwan kowama yaji warinta ban damu da abinda zai biyo bayaba nidai mu sauke wannan zunubin da muka d'aukawa kanmu. Hajiya iya tace shikenan khadija karki damu nina haddasa komai kuma zan wankeki da yardan Allah....garakam! Gara kugayawa duniya abinda kuka aikata kaka,konima zan samu lfy,juyowa sukayi sukaga marwan tsaye akansu ranshi a b'ace yake magana yanacewa wlh baki kyautaba kaka kinso kanki dewa awannan lamarin natabbata koda daddy zai zauna bashi da d'a aduniya bazai tab'a yarda da wannan abinba wannan aiba sonshi kikeba hajiya danba haa ake son mutumba,hajiya iya cikin muryan kuka tace jikana marwan bason mahaifinkane yasa nayi hakanba sedan son da nakeyiwa mahaifiyarka da kuma toshewar kwakwawa irin nawa. Marwan yace babu toshewar kwakwalwa anan kaka,domin wannan abun da kikayi se mutum mai wankakken kwakwalwane zai iya aikatashi kawaidai son zuciyane irin naki da kuma rashin tausayi,kaka matar dabasan yanda akayi ta haihubama dan tsabar azabar datasha kiduba yadda ake kwatanta rad'ad'in haihuwa wanda kema kinsan hakan tunda kin haifa amma shine kika sace mata yarinya haba kaka! Wani irin shaid'anune suka shiga kanki awannan loacin!? Mum ce ta mik'e tace marwan kayi ahankali kakarkacefa duk lalacewa. Afusace yace tabbas kakatace shiyasa nake gyara mata kuskurenta mum ba lubna da iyayenta kad'ai kuka cutaba hardani da dad! Gabad'aya kun gama b'ata mana suna mum,kuna tunanin zaku gayamusu gaskya suyi hakuri abar maganan to mum sauran jama'an garifa?? Shikenanfa sunanmu yab'aci kun cucemu kuma wannan sunan bazai tab'a gyaruwaba domin yariga dayazama tabo! Kuka sosai marwan yakeyi tare da juyawa hanyan waje yace nizanyi tfy yau nida rashida se bayan wata d'aya zamu dawo kigafarceni mum...
Hawaye yakasa tsayawa daga idanunsu dukkansu sunabinsa da kallo harya fita.
Mum tasan halin d'anta marwan sarai,sam bayason zalinci,gashi dama rashin amininsa manosh yafi komai d'aga mishi hankali,yanzu kuma gashi tasake k'ara mishi damuwa wanda har yasashi rashin lfy kuma gashi yatafi ya barta.
  Rashida ce zaune ita da aunty tana gayamata irin sauyi sosai da take gani agun marwan,ko hakkin aurenta ya denabata kwata-kwata,sannan bayason duk wani magana dazata gayamishi seyace dan Allah kirabu dani. Aunty tace kiyi hakuri rash,watakila yanada damuwane kuma kinsan maza idan har sunada damuwa tofa basa buk'atar *sex* domin shi sex jindad'i da kwanciyar hankali shine ke kawosa wanda ba mijinki ne kad'aiba duk mazan duniya haka suke. Dan haka kiyi hakuri *kimishi uzuri pls?* Sannan kikai kukanki gun Allah,Allah ya daidaita al'amurorin mijikin su koma yadda suke insha Allah komai zai daidaita,kuma banaso ki sake gayamin duk wani hali dakike ciki keda mijinki domin babu wanda zai miki maganin damuwanki se ALLAH.
   Rash taji dad'in kalaman maryam har cikin ranta kuma taji sanyi azuciyarta,sannan tabbas itama se yanzu take danasanin gayawa maryam sirrinta da mijinta tunda wannanma shine karo na farko dasuka fara samun matsala itadashi. Sallamar marwanne ya tsaidasu suka fito zuwa palon baba.
  Marwan yace aunty zamu tafi,dan Allah ki k'ara hakuri mucigaba da addu'a insha Allah captain zai dawo garemu musammanma gun apple d'inshi da kuma abdallah alfiya. Murmushi sosai tayi dan tasan yanaso yasata farincikine,tace insha Allah kuma nagode sosai Allah ya kiyaye hanya akulamin da k'awata sosai pls,murmushi yayi na k'arfin hali yace baki da matsala indai wannanne aunty. Rash tana murmushi ta mik'e tare dacewa barinaje na d'auko jakata.
      Bayan fitar tane marwan ya sunkuyar da kanshi k'asa  yace aunty dan Allah kiyi hakuri da abinda zakiji bayan tfyarmu,aunty banaso ki tambayeni komai zakiji komai bayan mun tafi,kuma dan Allah kiyafi wanda suke da hannu cikin abin badanniba sedan ALLAH,shiyasa zanyi wannan tfyn saboda inaga yin hakan zaimin d'an sauk'i araina,sannan banaso kigayawa kowa abinda na gayamiki ayanzu,ki rik'eshi amatsayin irin sirrin da kika rikewa *lubna* abaya. Yana kaiwa nan ya mik'e yafita waje ita kuwa jikinta gabad'aya yayi sanyi dai-dai nan rashida ta shigo tace to aunty semunyi waya kenan,ta daure tace to Allah ya tsare Allah ya dawo daku lfy,rash tace ameen sannan suka fito waje rash ta shiga mota marwan yaja dasauri suka tafi inda akabar aunty atsaye jiki babu kwari maganganun marwan ne suketa mata yawo a kwawalwar ta...
.
Jiki sanyaye aunty ta koma cikin gida dama mama bata nan,dan haka ta wuce d'akinta ta kwanta tana tuno kalaman marwan. Tace me yake nufi da wad'annan kalaman nashi? Kuma me yake nufi da sirrin dana b'oyewa lubna? Kardai na fyad'en da saddam yayi mata? Towaya gaya mishi indai hakane? Duk wannan tambayoyin ita kad'ai takeyiwa kanta bayan tasan bata da amsoshinsu.
  Hakan yasa tayi shuru tanata tunani,daga bisani aka kira sallah ta mik'e taje tayi alwala tayi sallah tare da addu'oi sosai kamar yadda ta saba musamman akan *peach* d'inta,sannan tayi akan maganganun marwan cewa Allah yasa taji alkhairi.
Yau asabar mum d'in manosh tazi duba aunty tare dasu abdallah da alfiya. Sunyi murna sosai da ganin juna dan sund'an juma basu had'uba,sakamakon mum d'in manos datace subar aunty ta huta sedai akan kawosu suyi kwana biyu. Sunyi kyau sosai se k'ara girma sukeyi. Abdallah yace mum wai yaushe daddy zaidawone gaskya ya dad'e sosai ni ina son ganinshi ya d'aukeni muje yawo inga sauran abokansa sojoji da wannan ogan nashi yana da kirki sosai domin yana sona,rananma yazo gidan su mum din dad yayi mana sayayya sosai kaya masu kyau yace dad namu yakusa dawowa amma gashi har yanzu shuru. Aunty ta rungume d'anta ko ince sanyi idaniyanta domin jinshi take kamar abdallah marigayi,tace kad'an k'ara hakuri kad'an kaji aiyukane suka mishi yawa amma ya kusa dawowa kaji? Alfiya kuwa fushi takeyi waisam se an kira mata dad nata sun gaisa tunda ya tafi basuyi wayaba kulum rikicinta kenan,hakan yasa aunty ta kira muhsin sakamakon yakan kwaikwayi muryan manosh wani lokaci,bayan ya d'auka da hello aunty,kawai setaji hawaye yana bin idanunta amma seta daure tace hello daddyn abdallah da alfiya,jikinshi yayi sanyi kuma yasan cewa su abdallahne suka sata kiran babansu domin sun tab'ayin hakan agaban jama'a bayan sunbar gurinne dad din manosh yace se'a dinga had'asu da muhsin ta waya tunda muryansu kusan d'ayane.
  Muhsin bai iya cewa komai se tausayinta daya kamashi,tace dama ashe bakayin waya dasu abdallah ko,gaskya yanzu dai ga alfiya se fushi takeyi barina bata. Da murna ta karb'a tace daddy,kwallane ya zubo daga idanun muhsin amma seya daure yace sweetynah yakike,tace lfy lau daddy inaka shiga haka kaki dawowa nidai gasky muna so kadawo domin mu koma gidanmu da mummy kuma kaga gidansu mummyn daddy basu da swiming pool kuma inaso inyi wanka,dariya sosai muhsin yayi yace karki damu nanda wata d'aya zan dawo kinji,kidai inaso idan kikayi sallah kice Allah ya dawomin da daddyna lfy kinji,tace idan nayi zaka dawo? Yace da wurima kuwa,ai kuwa setayi murmushi tace da kana kusa dani dase mun tafa daddy,yace yanzuma zamu tafa mutafaaa,ahankali ta ajiye hannunta akan screen shima haka kamar suna kallon juna setayi dariya tace *i luv u daddy* yace *i luv u too my swthrt* sannan yace ina abdallah,tace gashi can yayi fushi wai bazaiyi magana dakaiba sedai ka dawo kuje yawo a mota,yace kie mishi yayi hakuri ya karb'i wayan,tace daddy yaqi ga mummy,yace to kicewa abdallah ina gaisheshi kuma shima yayimin addu'a zan sayo mishi mota karami wanda zaku shiga ku biyu kuma ina sonshi kinji? Tace to daddy mungode byee. Bayan alfiya ta mik'awa mummyntane setace to daddy kafa dawo dawuri dan kaga abdallah yana fushi dakai ka dinga kira ta wayan mum seku gaisa,yace insha Allah aunty,tace nagode se anjuma.
   Muhsin ya sauke ajiyar zuciya tare da tausayamusu dukkansu,se kuma ya shiga tunanin lokacin da suke hira dukkansu suna cewa captain kam ai dole ya k'ara aure,seyace musu wlh apple na ita kadai ta isheshi,kuma ko wani irin rayuwa ko hali zata tsinci kanta nan gaba koda kuwa zata zama batada matancin kwata-kwata to wallahi ita kawai nakeso ba wani abuba,guys ina k'aunar apple yadda bakwa tsammani fatana mukasance tare da ita har a lahira, basan wani irin k'auna nake mataba bansan taya zan fahimtar daku akan k'aunar da nake mataba, ama dai nasan cewa bazan iya rayuwa babu *aunty ba wlh* shiyasa fatana idan mutuwa zata d'auki d'aya daga cikinmu tota d'aukemu atare da apple d'ina.
  Bayan muhsin ya gama wannan tunaninne se hawaye yazo masa ido,yace Allah sarki abokina Allah yabayyana mana kai ameen.
   Su alfiya yini sukayi dan sunzo yiwa aunry bye ne akan tfyarta india,sun kuma mata addu'a kamar dai yadda mum d'in manosh tagaya musu. Dakyar abdallah ya yarda yabi mum,saboda yace shisam zaibi mum nashi india yanata kuka dakyar suka tafi. Bayan tfyansu ne aunty taketa faman nata kukan inada mamanta taketa rarrashinta tare a mata nasiha kamr yadda ta saba,aunty tace mama ina iyakan k'ok'arin ganin cewa na dena,amma sam bana iyawa mama taya za'axe aljani ya d'auke d'an adam ne tayaaaa seta fashe da kuka,inda maman nata take cewa haba maryam,karki fad'i haka mana,maryam d'ina nasanta da ilimi da d'aukan kaddara maikyau ko mara kyau,dan haka kicigaba da addu'a Allah yana tare damu maryam koai zai daidaita insha Allah kiyi k'ok'ari kici wannan jarabawan maryam kinji? Tace to mama nagode da kika tunatardani amma nina kewar captain mama wlh inaso inganshi mama koda so d'ayane,itama mama seta tsinci kanta cikin hawaye sakamakon tausayin 'yarta. Amma ahakan tayita gayamata kalamai masu sanyaya zuciya harta dena kukan.
  Yaune lahadi su maryam sun gaa shiri tsaf hakama su yah ibrahim da lubna.
  Dama baba ya sanar dasu yah ibrahim da kuma umma mamansa cewa suzo akwai magana kamar yadda hajiya iya ta sanar dashi.
Hakama d'an nata wato mahaifin marwan harma da dad d'in manosh dayake aminaine duk aka taru agidansu *auntyn' yara* inda lubna take zaune kusada aunty tana kallon hajiya khadija da kuma hajiya iya dan taga ta ina zasu fara.
   Mum d'in marwan dai kanta a sunkuye ta kasa sakewa sam dan batasan mezai biyo bayaba,duk dai ana zaune a palon baban maryam kowa kuma ya damu yasan dalilin wannan taron. Sallaman muhsin da majid da kuma muhammad ne ya katse su,bayan sun samu guri sun zauna ne aka fara gaishe gaishe,koda muhsin yace aunty ina wuni,seta amsa cikin muryan kuka saboda ta tuno da mijinta,kowa kuma yasan dalilin hakan,lubna ce tayita rarrashinta sannan hajiya iya ta d'ago kanta idonta jajur,kowa ya d'auka akan b'atan manosh ne zatayi magana,inbanda lubna datasan dalilin taron. Hajiya  ta fara magana kamar hakaaaaaa...
.
"Bakomai yasa na had'a wannan taroba sedan wata magana mai girma ko kuma ince na taramu ananne saboda in tonawa kaina asiri akan abinda na aika".
  Hawayene yasa hajiya iya tsayawa tana mai goge kwalla,inda d'an nata wato mahaifin narwan ya shiga damuwa. Hajiya iya tacigaba da magana cikin muryan kuka ta kwashe lbr tun daga farko har k'arshe kamar yadda mahaifiyar arwan ta bashi lbr dalla-dalla. Tun bata k'arasaba kowa ya kama fad'in innalillahi wa'inna ilaihirraji'un",hajiya iya tace dan Allah kuyi hakuri karkuce komai harsenaga.
Taci gaba da cewa nasan zakuji wani iri kilama bazaku yaddaba sakamakon yadda na muku bayanin amma wannan shine gaskyan lamari. Dan Allah kugafarceni kuyafemin wannan laifi mai girma dana aikatashi cikin jahilci da kuma sonkai irin nawa.....
  Tunda hajiya iya ta fara magana idon aunry yake zubar da kwalla kamar pampo har kuma yanzu,nanne take tunanin kodai mafarki takeyine,amma sam ba mafarkibane wannan gaskyane,amma kuma anya abinda hajiya iya ta fad'a gaskyane? Lubna ce ta katse maryam da maganan zuci da takeyi,tace aunty kida shakku akan abinda ta fad'a domin babu k'arya ko kad'an aciki fase gaskya zallah. Shine dalilin dayasa naje gidanta nake gaya mata maganganu ranan,sakamakon bazan iya gayawa kowa abinda mahaifiyata da kuma kakata suka aikataba shiyasa na rik'e abun a raina dan banaso sunansu ya b'aci dukda dai nagane gaskyan amma hajiya khadija ta rik'e tamkar 'yar cikinta hakan yasa nayi shuru ban gayawa kowaba,sannan wannan shine dalilin dayasa bro marwan ya k'irk'iro da tfyarsa wanda ko aminansa basu san dalilin wannan tfyanba saboda kunyan abinda familynsa suka aikata baisan ta yadda zai fiskanci mutaneba.......Aunty ce tasa hannunta akan bakin lubna tana kwallah sosai idanunta sunyi jah,ta kalli hajiya khadija da hajiya iya sannan tace hajiya shin dagaskene...? Atare suka d'aga kai ma'ana ehh gaskyace" hajiya khadija ta k'ara da cewa maryam nasan bamu cancanci yafiyaba amma dan Allah kuyi hakuri wannan shine dalilin dayasa muke k'aunarki sosai aranmu nida hajiya iya,shine dalilin dayasa bamaso ace yau munganki cikin kinci dan musan bamu kyauta mikiba dan Allah alhaji kuyi hakuri mun yadda da duk wani hukunci da zaku yanke mana amma fatanmu shine kusan gaskya akan cewa lubna 'yar cikunkuce k'anwa ga maryam.....
  Su baba dai kasa cewa komai sukayi hakama su dad d'in manosh. Shi kuwa dad d'in marwan jiyake kamar ya tsaga k'asa ya shiga dan kunyan abinda mahaifiyarsa da kuma matarsa suka aikata,ga kuma 'ya'yan cikinsa su majid,"oooh" wannan abin kunya dame yayi kama?
  "Maryam tanakuka ta kalli iyayenta inda kansu yake sunkuye dan basusan me zasuceba,musamman baba,yana ganin girman hajiya iya sosai,bazai iya yin komai akaiba illa yafiya. Maryam tagane komai akan halin da iyayenta suka shiga,hakan yasa ta matso kusa da iyayenta inda kowa yake binta da kallo,tace baba mama,nidai har abada馃槹hawaye sosai takeyi,inda hajiya iya taji zuciyarta na bugawa sosai,maryam tace nayafe musu har abada baba,kuma ina sake baku hakuri akan kuyafe musu,lallai marwan yayimin wani magana kafin ya tafi ya kuma nemi yafiyanmu tun kafin inji wannan lbrn,seyanzune nagane meyakenufin da wannan kalaman nashi,sannan yanzu haka bamu san wani hali suke cikiba baba,dan lokacin da marwan yabar k'ofar gidannan gabad'aya baya cikin hayyacinsa,dan Allah baba kayafesu kaida mama domin ceto rayuwar marwan da rashida danko numbernsu baya shiga,seyanzu na gano dalilin ciwon marwan baba dan Allah baba ka yafe musu..... tana kaiwa nan ta mik'e zuwa d'akinsu tana kuka ita kuwa lubna kallonsu takeyi cikin tausayawa,tace baba kayi hakuri a yafe musu kodon rik'eni dasuka babu kyama babu wulakantawa se d'inbin soyayya da suka nuna min fiye da d'ansu bro marwan,ta sake juyawa ta kalli dad d'in marwan tace daddy har gobe bazan dena kiranka da sunan daddyba,haka kuma kema mummy ina k'aunarku har gobe,nagodewa Allah daya had'ani da 'yar'uwata dukda kun rabamu,kuma cikin k'ankain lokaci nayi koyi da halayenta nagari,daddy samun 'yar'uwa kamar aunty abin alfaharine agareni. Yau zan gayawa kowa abinda baku saniba,daddy nayiwa aunty mugunta har halakata naso nayi sakamakon son zuciya irin na hajiya iya,lokacin da aka nei aunty aka rasa nice nasa akayi kidnaping nata har zuwa jejin yankari,amma cikin ikon Allah aunty ta dawo gida lfy,kuma ita tasan cewa nice nasa a saceta saboda kar ayi aurensu da bro manosh dan k'aunarshi danakeyi acikin raina. Amma hakan baiyuba kuma tak'ita gayawa kowa abinda ya faru harda iyayenta ta b'oye musu saboda bata so ta b'ata tsakanin iyayenu da kuma aminantakar dake tsakanin bro manosh da bro marwan,haka kuma wanda nasa aikin ya yaudareni ya b'ata min rayuwata ta hanyar yimin fyd'e wanda duk alhakin auntyne ya kamani,shiyasa ban gayawa kowaba se ita auntyn,saboda ina tsoron fad'a muku agida daddy,sannan aunty itace kawai wanda ta fad'o min araina wannan lokacin,bayan na kirata nagaya mata komaine,sam batasa komai a rantaba tazo har inda na mata kwatance itata staftaceni ta rufamin asiri ta hanyar had'i aure da yah ibrahim dan tasan zai rufamin asiri zai kuma zauna dani zuciya d'aya.....
    Lubna ta tsaya anan tana shehshek'an kuka inda hajiya khadima taketana kai har kusan duk wanda yake palon seda yayi kwalla dajin lbrn da lubna take bayarwa.
" lubna tace wannan sirri dana gaya muku yau babu wanda yasan dashi dagani se aunty,koshi yah ibrahim d'in baisan komai akan sace auntyba,amma dai yasan abinda saddam yamin ya kuma amince ya aureni. Nabaku lbrn nanne badan komaiba sedan innuwa hajiya iya da mummy cewa Allah yasa mana k'aunar junanmu tunba yauba nida aunty,sedai shaid'an yayi tasiri akaina har nake neman halakata dan soyayya,amma duk kukuka janyo hakan,dabaku rabamuba da tare zamu tashi inji jina kusa dani...kin cuceni hajiya kun tarwatsa min rayutawa nidai bazan tab'a yafewaba wlh.. mama ce ta kamota tana rufe mata baki tareda goge kwallan idanunta tace lubna ya isa haka tashi kije gun 'yar'uwanki kinji? Bamusu ta mik'e ta fita nata kuka,su yah ibrahim ma fita waje sukayi dukkansu 4 sukayi zugum a waje babu wanda ya iya cewa komai acikinsu....
  "Jirginsu marwan ya sauka a abuja, inda suka sauka a hilton. Tun da marwan ya fita bai dawoba rashida ta shiga damuwa gashi wayarsu duk ya karb'e ya cire sim.
Saukowa tayi dama da kud'i a hannunta sosai,taje ta sayo k'aramin waya da sabon sim mma tama rasa waye zata kira,hakan yasa tafara kuka ko abinci bataciba.
  Marwan kuwa tunda ya fita da motan wani abokinsa da yake aiki acan din yaketa tfy,baima san ina yake zuwa. Gabad'aya hanklinsa atashe yake,halinda ake ciki yanzu agida yola,sannan ko wani hukunci dad nashi zai yanke akan mum oho,yanzu abokansa sunsan komai,gashi babu lbrn aminsa dazai iya gayawa damuwarsa wato manosh. Kuka yakeyi sosai kamar k'aramin yaro,baya ko kallon gabanshi hakan yasa wata mota k'ok'arin kaucewa marwan amma sam yagagara saboda yadda marwan yake sake dososhi,se alokacin hankalin marwan ya dawo jikinsa ya fara fad'in innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ya kauce da sauri tare da tsyawa a gefe shima wancan din ya tsaya yana zagin marwan,shi kuwa se hakuri yakebashi amma sam se faman masifa yakeyiwa marwan,dak'ar dai ya hakura ya tafi. Shi kuwa marwan zama yayi acikin mota yana zubda kwalla.....
"dad d'in marwan yakasa cewa komai sabida bayida abin fad'a akan mahaifiyarsa". Mahaifin manosh ne yacewa mahaifin maryam dan Allah alhaji kuyi hakuri da abunda muka aikata muku,dukda dai mahaifiyarmuce dukkanmu tunda ta haifemu" amma tabbas sunyi kuskure mafi girma arayuwa,babu da wani abu da zamu iyace cewa sedai muyita baku hakuri daku yafemana sannan 'yarku dama tadawo hannunku tunda tana auren d'anka ibrahim. Za'a iya sanar da dangi amma ataimaka ab'oyewa mutanen waje. Mahaifin maryam yace bakomai alhaji wannan yawuce,sedai fatan Allah yasa mukiyaye gaba,Allah yasa wannan ya,zama darasi akan wasu,saboda munbarwa Allah komai wlh nafe duniya da lahira,amma fa idan da wanine aka mishi haka tofa bazai yafeba,sannan dole se hukima ta shiga shicin zance wanda hakan zai iya janyo wata babban rigima tsakanin familys harma yakai gidan yari.
  Amma alhamdulillah yazo gidan sauki tunda duk gashi Allah ya had'a zuri'a a tsakaninmu" bazamu iya cewa komaiba se Allah ya kare nagaba,sannan nagode da kulamin da yarinyata da kukayi,nagane manufar hajiya iya da kuma dalilinta.
Sedai ba haka ya kama a bullowa lamarinba,ita a tunaninta lokacin ina fama da talauci ta yadda bazan iya rik'e koda yarinya d'ayaba,se kuma gashi Allah yabani kyauta biyu a lokaci guda,tofa musani Allah baya d'aurawa bawa abinda bazai iyaba,tunda shiyabani su toshizai bani hanyar da zan renosu,alokacin bani dashi,yanzu kuma ina iya rike mutanen daba jininabama,kamar yadda kuka rikemin lubna. Bakomai hajiya Allah ya yafemu gabad'aya. Har k'asa hajiya iya ta sauko tana kuka tare dayin godiya,hakama mahaifiyar maryam tace tayafe bakomai. Nanne dad d'in manosh yayi magana kansan a sunkuye dan kunya,yace mungode sosai alhaji Allah yabar zumunci,wani lokacin mata basu da tunani,duk abinda zuciyarsu ta rayamusu shi kawai sukebi tabare dasunyi shawara da kwakwalwarsuba,aduk lokacin da zuciya ya raya maka abu maikyau ko mara kyau tofa ana so mutum yayi shawara da kwakwalwarsa domin zuciya zata kaika ta baroka,yanzu kai dakayi hakuri wlh inda wanine bazai hakura,kuma kaduba abinda lubna tayiwa maryam,da maryam ta fad'a awannan lokacin toda abu ya lalace tun daga wannan lokacin se daga baya kuma za'aji kunya,kuma dukkune sanadin faruwar hakan. Hajiya da girmanki amma ki aikata irin wannan abu haka babu dad'inji,sannan kuka b'oyemin akan tsintota akayi wannan wani irin tunanine haka? da wani akayiwa hakan da sunanmu ya gama b'aci,yanzu haka kunyan had'a ido dasu nakeyi wlh mungode sosai Alhaji zamu tafi,yana kaiwa nan ya fito suka biyoshi a baya,bai k'arasa gun motaba ya yanke jiki zai fad'i da sauri su majid suka tallafoshi aka sashi cikin mota ida muhammad yaketa faman dubashi yace ai jininsane yahau sosai. Subhanallah ake ambato agun,da sauri suka shige se jimeta inda akayi hospital dashi.
Dad d'in marwan baida hawan jini sam,amma yau gashi dr yace hawan jinine ya kamashi sosai.
  'Ya'yan nashi sunyi iyakan k'ok'arinsu agun dan kula da mahaifin abokinsu.
"Shi kuwa mahaifin manosh,yana cikin damuwa wanda har yake jin ciwon kai mai zafi,amma haka ya daure yana nan akan abokinsa.
"Su maryam kuwa fitowa sukayi daga d'aki sukazo gun hajiya iya kamar yadda babansu ya umarcesu.
Dan tun lokacin dataji abinda ya sami d'an nata shikenan aka rasa gane kanta. Hakuri aketa bata,itama hajiya khadijan sam ta kasa sakewa,hakan yasa tace zata komar da hajiya iya gidansu can na jimeta tunda akwai masu girki,ita zata tafi asibiti gun mijinta.
Haka aka rakosu har waje suka tafi. Maryam sebin motar nasu da kallo takeyi har sukayi nisa sannan lubna ta kamo hannunta tace aunty kidenasa damuwa aranki pls komai ya wuce kamata yayi ace kina murnan samun k'anwa.
Jiki sanyaye ta juyo suna kallon junansu tace lubna,bakya jin komai gameda abunda ya sami daddynkine? Lubna tace daddyn bro marwan dai. Maryam ta dafa kafad'arta tace lubna har gobe har jibi shima daddynkine sannan inaso ki nuna damuwarki sosai akanshi kamar yadda kike nunawa akaina inhar kinasona da gaske. Jikin lubna yayi sanyi ta wuce gida tasa himar nata har k'asa tace mama baba zanje duba daddy,babu wanda ya hanata,seda tazo dabda maryam tace zanjene saboda ke saboda kuma shi daddy bayi da laifi sansan zanjene dan bro marwan bayanan,nasan koba komai zan d'ebemasa kewa.
"Maryam tanata bin lubna da kallo harta dena kallonta zata shiga gida kenan setaji ana kiran sallan la'asar,koda ta juyo dan ganin mai kiran sallan seta wannan tsohonne dai wanda ta taimakawa a farkon littafin...
  "Marwan ahankali yake tfy harya isa gun abokinshi yace kaini masaukina.
Bamusu ya kaishi batare dayace mishi komaiba,saboda yadda yaga marwan yasan bazai samu kowace amsa daga bakinshiba.
"Bayan ya saukeshine marwan ya fita yace nagode,abokinsa yace yaushe zanzo to?" Dan numberka kona kira bana samu. Marwan yace zan kiraka sannan ya shige.
Rashida tanata safa da marwa setaji nocking,da sauri taje ta bud'e kofa taga marwan atsaye kansa a sunkuye dukya galabaita yayi wani iri kamar maiyin azumi. Hakan ya tabbatar mata da cewa baici komaima,kallonta yakeyi cikin tausayi ga kwalla dasuke yawo a idanunsa. Tausayinshi ya kamata,ta rungumeshi sam ajikinta tana kuka tana cewa waime yake faruwane luv,dan Allah ka sanar dani bana son yadda nake ganinka ahakannan pls luv, baice da ita komaiba se kwallan da yake zubarwa,ahankali ta cire masa kayan jikinsa itama haa ta jashi zuwa toilet inda ya zama kamar jariri haka ta wankeshi tas sanan itama ta wanke jikinta ya d'auki towel itama haka suka fito a tare,yasa kaya tasake janshi wuza gun cin abinci amma sam yakici da k'yar tasashi yaci kadan sannan ya koma gado ya kwanta.
Bayan ta gama komaine tazo inda yake tana tsunbatan sassan jijinsa a hankali tana kallonshi har cikin ido. Shi kuwa sam hankalinsa baya jikinsa,lips nashi ta far kissing ahankali cikin nutsuwa,shi kuwa idanunsa arufe yana jin yadda take mishi,kamar a mafarki yaji muryan manosh yana cewa marwannnnn
  Azabure,ya mik'e rash tace lfy luv,yace my luv manosh naji yakirani wlh ahine. Rash ta mik'e tace manosh fa kace,to a ina yake? Allah yasa dagaskene luv dabanda zaikai aunty farinciki maza muje muduba,bamusu yanufi k'ofa ita kuwa tasa himar ta fito,se juye juye sukeyi suna duba kofofin d'akinan ko zasuga fitowarsa koma suji muryanshi.
Can yasakejin marwannn,ai kuwa yana juyawa seyaga manosh yana k'ok'arin fitowa daga wani d'aki amma sam j'afarshi baya motsi kaman an manda da superglue. Da gudu suka k'arasa gun,amma ina take kofan ta kulle kanta. Bugawa marwan yakeyi kamar zai b'alla kofan amma ina,sunan manosh yaketa kira yanacewa prince gani ka bud'e kofan pls kaida waye? Shuru babu amsa,seyaga k'ofa ta bud'u da kanta,dasuka shiga shiga amma babu alaman mutane acikin d'akin.
Marwan yace ina bazai yuba wannan duk sharrin shukrah ce,duk yadda akayi suna nan,lallai bazan bar nanba senagano captain,nan suka zauna sunata addu'oi,ita kuwa rash tsone ya kamata sosai dan tabbas itama taga manosh da idanunta...
  " aunty kuwa koda tsohonnan ya idar da kiran sallah,gunshi ta k'arasa tace baba,murmushi yayi mata yace inatayaki murnan samun 'yar'uwarki. Murmushi tayi mai had'e da tsoro tace nagode,nakuma tuna da abinda ka gayamin a yanzunnan. Yace masha Allah maryam zan tafi,tace baba dan Allah mijinafa,kokasan inda shukrah takai min shi? Dan Allah baba kataima. Baba yace wacece shukrah? Jikin maryam yayi sanyi tace baba aljanace ita,ta rabani da mijina tsawon kusan wata hud'u kenan ba'asan inda yakeba.
Baba yace ta ita maryam bansan komaiba akan wannan kimana tausayamiki sosai,Allah ya bayyana miki shi,kuci gaba da addu'a maryam babu wani abu dazai gagara,sannan kisa a ranki cewa Allah zai dawo miki da mijinki,karki dogara da wani kinji? Jikinta sanyaye tace to baba nagode tare da kwalla a idanunta. Ahankali tabar gun masallacin tayi hanyar komawa gida saboda mutane sun fara zuwa sallah,kan ta karasa kofar gida ta juya amsam bataga baba ba,kuma babu alamarsa tagurin. Mamaki,sosai tayi tayi da gudu ta shiga gida tana kuka ,hankalin iyayenta a tashe suke tambayanta ko lfy,tace gamo tayi da aljani. Iyayen suka tsaya kallon junansu,mahaifinta yace maryam wani irin gamo? Nan maryam ta basu lbr tun daga farkon had'uwansu da baba stohonnan har kuma taimakon daya mata a jejin yankari lokacin da saddam ya harbeta da bindiga a hannu da kuma abinda tsohon ya gaya mata akan lubna.
Mamaki sosai iyayen sukayi,babanta yace maryam anya kuwa lfyanki lau? Tace wlh baba lfyta lau yanzuma shinagani shine wanda kukaji muryanshi ya kira sallah. Baba yace ajani ya kira sallah kuma maryam? Tace eh wlh baba nasan bazaku yaddaba amma wlh shida kanshi yagayamin shiba mutum bane aljanine. Baba yace to Allah ya karemu dadukkan 'yan'uwa musulmai,suka amsa da ameen sannan ya fita zuwa masallaci yanata kalle kalle tare da tambayan jama'a ina wanda ya kira sallah yanzu? Wanine yace tun d'azu yabi tacan,baba yace shibazai tsaya yayi sallan bane? Yaro yace oho mishi tsohone kodai zaije ya dawone oho mishi. Haka dai su baba suka idar da sallah amma wannan wannan tsohon bai dawoba,baba kuwa ya jinkirta yanata karatun qur'an a masallaci harya isar amma baiga kowaba haka ya wuce gida. Lokacin suna cin abincine se maryam tace baba har yanzu lubna shuru kodai sun wuce gidane itada yah ibrahim,mama tace kirasu kiji,bamusu ta d'auki wayarta ta kira lubna,cikin nuryan kuka lubna ta d'auka tace aunty zan dawo anjuma kad'an,maryam tace ya jikinnashi? Lubna tace da sauki yana bacci,maryam tace yanaji muryanki kina kuka lubna? Lubna ta share kwalla tace aunty daddy ya saki mummy. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.......
.
Sakifa kikace lubna,tace eh sannan ta katse wayar.
"Maryam ta kalli iyayenta tace baba wai daddyn marwan ya saki hajiya khadija" duk basuji dad'in lamarinba,amma babu abinda zasu iyayi akai haka suka gama cin abinci suka wuce dan k'arasa shirye shiryensu.
Kusan 10:00pm yah ibrahim ya kawo lubna gida,idan suka dad'e suna magana da baba kafin ya tafi.
Ranan dai basuyi wani baccin kirkiba dan gobe zasuyi tfy.
Maryam kuwa tama rasa meke mata d'ad'i.
  "Washe gari da safe mahaifin maryam ya sanar da tfyan da zasuyi a masallaci don yiwa maryam aiki,sannan kuma yasake rokon jama'a ayita addu'a wa surukinsa wato manosh Allah ya bayyanashi. Addu'a sosai aka musu awannan lokacinma.
Da misalin 9:10am yah ibrahim yazo ya kwashesu a mota inda suka wuce hospital suka gaida mahaifin marwan sannan suka wuce airpot. 10:20am jirginsu ya tashi abuja,suna sauka dama komai ya zama ready yah ibrahim ya gama komai suka wuce suna zaune zaman jiran tfya india.
Marwan kuwa suyita addu'a har rashida ta fara bacci,shine ya d'agata yakaita d'aki ya kwantar da ita sannan ya koma yayita zama harya gaji sannan ya dawo shima hakadai suka wayi gari.
  "Bayan sunyi breafast ne marwan ya sake komawa d'akin amma bakoai aciki" mamaki sosai yakeyi abu kamar a drama?" Rash ce ta biyoshi hakadai suka sake dawowa d'akinsu inda take ce mishi itata sayi waya kuma tayita kiran numbern 'yan gida baya shiga dan haka ya bata numbern su majid,sam marwan yak'i yama karb'e wayan. Nan rash tayi fushi tace waime kake nufine kakawoni nan ka ajiyeni babu wani bayani jiya haka ka fita ka barni bakaika dawoba seda lokaci ya kure waima ina kajene marwan?
Cikin mamaki yake kallonta yau sunanshi ta kira kai tsaye. Yace luv yau nine kuma marwan? Sannan zargina kike kome dakike min wannan tambayoyin? Tace eh zarginka nakeyi saboda abirkice ka dawo jiya kamar wani bugagge idan ka gaji da zama danine nikam kamaidani gidanmu gabad'aya kacanja kadena bani hakkina idan ka sau matan banza awaje toka sallameni intafi gidanmu nan ta fashe da kuka. Shi kuwa marwan maganganun nata sun mishi zafi sosai gashi dama yana da damuwa,baice da ita komai yafita yabar mata d'akin tanata kuka.
Shukrah waike wani irin muguwace haka? Hahahha lallai kam manosh ka samu baki,wlh indai bazan samekaba tofa sedai in hallakaka itama maryam d'in ta rasaka tunda kai taurinkai kakeji dashi,danka samu na sake maka bakinka ko,tokamin bankwana manosh semun had'u a kiyama..............
  Ihu mai k'arfi manosh yasa,awannan lokacin kuwa su yah ibrahim zasu tafi dama wayoyinsu akashe yake. Juyowa yayi yana kallon aunty se faman kuka takeyi tana tsaye,gunta yazo shida lubna sukace lfy aunty muje mana? Kuka ta fashe dashi tace sam bazatajeba ta fasa,mutanen gun suka tsaya suna kallonsu,da k'yar mahaifinta yashawo kanta ta yarda se waige waige takeyi har suka wuce tana kwalla.
Yah ibrahim ma kwallan yakeyi dan yana mugun tausayawa aunty sosai. Haka suka wuce cikin jirgi tana tsakiyan mamanta da kuma lubna jirgi ya tashi..
  Rash kuwa tayi kuka harta gode Allah can sekashi ya dawo tanata had'a kayanta ciki kit. Kallonta yakeyi tare da tambayar ina zakije? Ko kulashi batayiba ta gama komai tazo wucewa seya kamo hannunta ya matseta a jikinshi yana cewa haba luv meyake damunkine,meyasa bazakin uzuribane yanzu har zaki iya tfya kibarni? Tace shiyafi komai sauk'i wlh. Yace luv bakigane bane ina cikin damuwa dan Allah kimin uzuri pls my luv,rungumeta yayi tsam yace inada bukatarki atare dani kece zaki kwantar min da hankali amma kuma shine kike gayamin maganganu kike k'ok'arin tfya kibarni? Pls luv kiyi hakuri i luv you so much.      Hawayene kebin idanunta inda tace i luv you too bazan tab'a barinkaba kaine kab'ata min rai ai. Yace kiyi hakuri pls kinji,tace yawuce tana murmushi inda suke kallon junansu daga nan ta fara kissing nashi shima haka har suka sulale akan gado hmmmm.
Manosh ne kwance a k'asa baya cikin hayyacinsa se muryan wani mutum da yakeji yana cewa manosh bud'e idanunka ka kalli jirginsu matarka ya tashi,amma ina manosh bazai iyayin komaiba a wannan lokacin. Mutumin yace manosh gacan aunty cikin jirgi daure ka mata fatan Allah ya kiyaye hanya. Shuru kakeji kamar gawa, ni kuwa *sad-naa* kallonsu nake kamar a tv babu halinna in gane inda suke,haka dai nayita cija baki ina zubda kwalla tare da kallon jirginsu aunty harna dena hangoshi. Ganin hakan yasa mutumin ya d'auki manosh kamar an d'auke wuta haka na dena kallonsu,sena koma hilton gunsu marwan inda suke manne da junansu a cikin bargo,gadukkan alamu dai marwan yana biyan bashin kwanakin da suka wuce ne hahahaha!
"Mutuminnan bai tsaya ko inaba se gidan manosh,dahar zai shige sekuma ya tuna da cewa ai babu kowa a cikin gidan inbada mai gadi. Hakan yasa ya baina a daidai bakin gate rik'e da manosh a hannusa kamar dai yadda ake rik'e jarirai. Mai gadi yaji ana buga gate,kuma sam mutumin baikaima hannunsa kusa da gate ba. Da sauri yazo yana cewa wayene gidan babu kowa seni kadai mekuma kuke sone...? Mai gidansa yagani wato captain manosh a hannu wani tsohon mutum,Alhamdulillah maigadi ya furta yana kwallan farinciki tare da cewa Allah majirok'o bayinsa alhamdulillah....
.
maigadi yakasa rufe baki,ya kuma rasa mezaiyi a wannan lokacin.
"Tsohon yace bamu taburma mana, bamusu maigadi yaje ya d'auko carpet nashi mai kyau wanda aka kawo mishi tsaranban makka ya shinfid'a cikin rawan jiki yace bisimillah.
  Tsoho ya zauna tare da kwantar da manosh yace ahanya na sameshi kwance babu yadda yake,bayan na d'aukosane nake tambayarsa inda yake waye mahaifinsa shine dai ban samu amsaba,kawai senaga hotonsa a gurare da dama an manna,shine na tambayi jama'a suka kwatantamin gidansa tare da nuna farin cikinsu.
  "Mai gadi Allahu Akbar"
"Tsohon yace nidai zan tafi dan akan hanya nake nabar iyalita tana jirana can"
Maigadi yace dan Allah kad'an jira barina sanar da iyayensa,amma sam tsohon yaqi yace shidan Allah yayi badan asan yayiba dan haka ya tafi amma inaso ka gayawa matarsa ina tayata murna,kace mata inji baba.
  Koda tsoho ya fito lokacin maigadi yana kiran numbern aunty amma sam baya shiga.
Hakan yasa ya kira numbern dad d'in manosh bugu d'aya kuwa ya d'auka tare da cewa kana lfy,maigadi yace lfy lau alhaji se alkahiri yauga oga yanzunnan wani mutum ya kawoshi a stintarshi yayi kwance a k'asa,gashinan...dad d'in manosh ya katseshi da cewa kana nufin d'an manosh? Maigadi yace shidai alhaji gashinan amma baya halin lfy. Subhanallah ganinan.....
Dad yana ajiye waya yayita Hamdala yana godiya wa ALLAH tare da d'aga hannayensa sama da sauri ya kira malam da kuma aminansa da duk dai nakusa dashi. Kowa yaji lbr se godiyawa Allah.
   "Mahaifin majid ne ya kira majid suna hospital akan dad d'in marwan" koda suka sami lbrn murna da farin ciki baya misaltuwa. Shikansa dad d'in marwan dukda dai jikin nashi yayi tsanani amma sedayayi murmushi tare dayi godiya wa Allah ya kalli abokan d'an nasa dukyaga suna burin ganin aminunsa daga idanunsu ya gane hakan.
Anitse ya tashi ya zauna yace karku damu muhsin kuje kuga abokinku aina samu lfy ku isarmin da gaisuwata agareshi kafin nazo. Bamusu suka fati cikin d'oki inda yake ta binsu da kallo
Manosh kwance maigadi yayita yayyafa mishi ruwa amma sam ko motsawa baiyiba daidai nan motoci suketa hon abakin gates yayi saurin bud'ewa suka shihshigo.
"Daga dad d'in manosh har abokansa bansan suwaye suke mararin ganinsaba harda gudunsu suka k'arasa gun. Majid ne ya karb'i key yabud'e gidan muhsin da muhammad kuwa suka d'auki manosh se cikin palo inda duk gurin yayi k'ura.
Akan kujera suka kwantar dashi kamar gawa baya ko motsi.
  Kowa ya tsaya kallo manosh inda kowa yake zance zuci akan yadda suka ganshi.
Muhammad ya gwadashi ya tabbatar da cewa yana da rai,hakan yasa akayita masa addu'oi ana tofawa a ruwa ana yayyafa mishi,shi kuwa malamin man habbatus sauda dadai sauran had'in su man juda yaketa shafa mishi ajiki.
"Aikuwa segashi ya fara motsawa ahankali amma idanunsa a rufe yake motsawa da dukkan jikinsa"
Murmushi abokansa suka farayi tare dacigaba da addu'an"
Mahaifinsama addu'a yaketa mishi, shi kuwa malami mai ruk'yya se karatu yakeyi.
"Ahankali manosh ya fara bud'e idanunsa yana rufesu hardai ya bud'e garau inda yakebin kowa dake palon da kallo d'aya bayan d'ayan harya gama sannan yace ruwa zansa. Malam ya bashi ruwan addu'an muhammad ya tallafosa aka bashi ruwan ya shanye tas yace ak'ara mishi,hakan yasa aka gane lallai ya dawo hayyacinsa saboda manosh yana son shan ruwa sosai kobayajin k'ishi. Bayan an k'ara mishine yace zaisha fruit,hakan yasa akan yana jin yunwa.
Cikin mintuna goma mahjid yafita nemo fruit ya dawo ya wuce kichine ya d'auki plate da wuk'a yadai yanka yadda zai iya sannan ya dawo ajiye agaban manosh inda yaketa binsu da kallo kamar bai sansuba.
"Majid yace ga fruit d'in"
"Ido manosh yasa akan fruit d'in" bayan wasu dak'ik'ai seya girgiza kai alamun bazai shaba.
    Muhsin yace kasha mana abokina nasanka da son fruit fa.
Manosh ya girgiza kai yace ba irin wannan nake shaba. Majid yace kamar yah? Wanne kake sha to?
Kafin manosh yayi magana muh'd ya tuna da irin fruit da aunty take mishi seyace kana nufin irin wanda aunty take maka?
   Da sauri ya d'aga kai yana kallon muh'd cikin alamun tambaya? Muh'd yace eh na aunty kake so koh mai irin fiskarka??
Ihu mai karfi manosh yasa wanda dukkansu seda suka tsorata harda malamin. Manosh yacigaba da ihu yana cewa nooooh! Dad shukrah ce wlh tacuceni tagama dani dad ya rik'o dad nashi da k'arfi yana kuka.
  Dad yace son saurara mune anan babu shukrah ka saurareni kaji? Ahankali ya nutsu yace "dudes?"
Nanne abokansa suja san cewa yana cikin hayyacinsa sunda ya kirasu da wannan sunan *dude*" murmushi sukayi tare da rungumeshi sukace Alhamdulillah Allah mun gode maka _we are so happy to see "dude_"
"Murmushin k'arfin hali yayi yace _thankyou_, sannan ya kalli dad nashi yace dad mum fa? Yace suna hanya itada driver dasu abdallah,murmushi manosh yayi yace ina dad d'in marwan? Tare da juyowa da sauri ya sake kallon su majid yace ina marwan? Shuru sukayi dan suma tunda ya tafi suketa nemansa basusan inda yajeba tunda numbernshi baya shiga kuma bai kira kowaba har yanzu.
Manosh ya sake maimaita tambayarsa ina marwan? Muhsin yace kaima kasan da yana gari da tare zakaganmu yayi tfya ne.
Manosh yace ok dad nashi fa? Dad yace yana asibiti bayida lfy,subhanallah harda asibi dad,meyake damunsa to? Dad yace my son kana da buk'atan hutu dan haka muje gida idanka huta zakaji komai. To yace da dad d'in nashi yana kallon su muhsin da alamun tambayan *ina aunt?*馃槵 sukuwa dake sun gane abinda yake tambaya,bayaso dad nashi yajine saboda yana kunyan dad nashi. Se suka ce yawwa gasu mum sun iso,ai abdallah da alfiya suna ganin dad nasu suka ruga aguje suka haye jikinsa ya rungumesu yana sauke ajiyan zuciya kad'an-kad'an.
Mum kuwa da umma mahaifiyar yah ibrahim hawayen farin cikine ya lullub'esu sunkasa cewa komai se murmushin farinciki.
  "Manosh yace mum umma ina yininku,sukace lfy manosh barka Alhamdulillah Allah ya dawo mana dakai,kunyansu yakeji sosai bai iya sake cewa komaiba sesu alfiya dasuketa damunsa da surutu. Mum tace kuzo nan bayida lfy kubarshi idan ya huta sekuyi hiran,abdalla yace yaudai da ddynmu zamu kwana,mum tace tabbas kuwa amma sekun barshi ya huta,da kyar majid ya lallab'esu suka koma gun mum inda malam yace to Alhamdulillah inaga shikenan ai nizan tafi.
  "Dad da malam ne waje suna tattaunawa inda malam ya bashi magani yace manosh ya dinga shafawa a jikinsa,sannan ya samu hutu kuma a dinga mishi karatu koyayi da kansa. Godiya sosai dad yamishi yabashi abun sadaka amma sam malam yak'i karb'a yayi tafiyarsa.
Maigadine yazo da wuri yace alhaji ogan ya tashi? Dad yace eh Alhamdulillah yana halin lfy,maigaji yaji dad'i sosai yace to masha Allah zan iya shigowa? Dad yace eh bisimillah.
Tare suka shigo yagaida ogansa,cikin fara'a manosh ya amsa sannan yatafi yana farinciki sosai.
Iyayensu majid sukayi addu'oi sosai sannan suka tafi inda dad ya rakasu. Alfiya da abdallah kuwa gurin wasan lilonsu suka wuce se wasa sukeyi.
   Bayan fitan su dad ne manosh yacewa majid ina miher ne? Majid yace taje suna k'awarta ta haihu,tun d'azu nake neman numbernta dan in sanar da ita amma baya shiga"
  Manosh zaiyi magana kenan seka dad ya shigo yace toku tashi mutafi gida,ba musu suka tashi tare da tallafawa manosh ya tashi tare da k'arewa gidan kallo ko ina yayi kura sosai.
Haka suka tafi inda muhsin ya d'augo abdallah a sama yana cewa wlh nikam agidanmu zan kwana,muhsin yace bakaga gidan yayi k'ura bane aidole se anzo anyi share share.
  Manosh suna tfya atare hargun mota inda ya shiga motarsu majid yana rik'e da alfiya a ciyarsa yana gyara mata gashi seyace rad'a mata cewa _ina mummynkine dasu babanta_? Alfiya kuwa tabashi amsa da k'arfi ta yadda kowa zaiji tace tayi tfy ai bata gayamaka bane?
"Kunya sosai yaji dansu dad sunjisu"
"Hakan yasa yayi shuru har seda motansu dad dasu mum yayi gaba sannan nasu manosh d'in inda shida abokansane kawai se kuma su abdalla dansuki binsu mum sunce gurin daddynsu zasuje"
Se yanzune manosh ya juya da sauri yacewa muhsin kai wai ina *aunt* ne babu wanda yacemin komai,kunyansu dad ne yahanani tambayarta wlh _where is my wife_ muhammad dake driving yace ba alfiya ta baka amsaba,tayi tfy wlh,majid yace tfya mai nisama kuwa,muhsin yace akallah zatakai 3month kan ta dawo ba. Kallonsu manosh ya tsayayi d'aya bayan d'ayan yace wai meyasa kukemin hakane bawasa nakeyibafa kunsani ina apple d'ina? Abdallah yace daddy apple ta tafi *india* batada lfyne shine suka tafi ita da mama da baba da kuma uncle ibrahim da aunty lubna duk suka tafi....

0 comments:

Post a Comment