Blogroll

BANNER 728X90

Friday, 12 January 2018

ANTIN YARA Pge 31-40

miher tayi shiga na alfarma,daidai nan lubna ta kirata a waya tana tambayanta ya maganan zuwa tambayane nasu bro manosh,nan miher take gaya mata cewa ai maryam bata da lfy tana hospital d'in su bro muh'd yanzu hakama ina jiran prince ya fitone mu tafi.
Lubna tace eyyah Allah ya bata lfy,a ranta kuwa tace Allah yasama ta mutu.
Koda wasa lubna bata gayawa miher cewa tasan maryam ba,kuma bata yiwa miher tambayoyi akan maryam d'in sam,dan gudun zargi.
Manosh ya fito cikin shigar indians da blue sari na maza yayi kyau sosai,ya mik'awa mihaer key d'in *benz* nashi yace taje zai bita a baya. Mirna sosai tayi yau bro manosh yabarta tayi driving da kanta. Tana gaba yana binta a baya da *307*din apple nashi.
*Atiku abubakar mall* suka nufa inda manosh ya kashe kud'i sosai harta flaks seda suka saya mata da cups su plate dukdai wani abu da zasu buk'ata a hospital haka mihar tayi ta d'auka, se kallonsu akeyi don yadda sukayi kyau shi kuwa captain ko dariya bayayi se amsa waya da yakeyi. Mihar tana biye dashi bayan sun biya kud'ine suka tafi tana gaba yana binta a baya har,suka isa hospital d'in.
Lokacin yah ibrahim da abdallah sun koma girei domin suyiwa maman rashida bayani kuma tayi abinci dasu. Manosh yacewa miher ta shiga idan maman maryam bata d'akin tozai shigo,ai kuwa seta shiga da sallama da kuma kayayyaki sosai a hannunta har rashida ta tayata da wasu,sannan ta sake komawa ta kwaso sauran nanma seda rash ta tayata sannan suka gaisa maryam tana bacci har yanzu,mihar tace yamai jiki,rash tace da sauki wlh,tace Allah ya sauwaka mama fa? Tace mama sun fita da baba amma inaga sun kusa dawowa.
Da sauri mihar ta fita taje ta sanar da bro manosh,kafin su shigo maryam ta farka tana cewa mama zansha ruwa,dama yah ibrahim yad'an sayo abin tab'awa kad'an dan haka rash ta mik'a mata ruwan tasha sosai sannan ta koma ta kwanta rash tana mata sannu da jiki,tace yawwa.
Manosh da mihar suka shigo da sallama,kunya sosai maryam taji tace rash mik'amin himar d'ina,da sauri tad'an rataye matashi a k'irjinta sannan suka k'araso.
Rash suka gaisa da manosh yace ya mai jikin,tace da sauki yace to Allah ya bata lfy tace ameen sannan rash tace mihar mud'an basu guri ko,tare suka tashi suka fita sannan yazo ya zauna akan kujeran da yake kusa da gadonta yana kallonta. Kunya sosai taji ta dai daure ta tashi ta zauna tare da gyara rufe jikinta tace ina wuni,kallonta kakeyi tare dajin k'aunarta yana ratsashi yace lfy apple ya jiki,tace da sauk'i.
Yace wato dama kina jin jiki shine kika cemin kaine yake miki ciwo ko,mirmushi tayi tace amma ai da sauki yanzu. Yace drip d'in harya k'are ne? Tace eh yace se bayan isha za'a samin wani,yace ok Allah ya baki lfy apple,tace ameen tare dajin kunyanshi sosai danba himar a jikinta dukda dai ta rufe jikinta amma yana iya hango kananan kitson dake kanta gata da bak'in gashi.
Ya maida kallonsa kan wayanshi yace ina wayanki,nan ta mik'a mishi ya karb'a ba tare daya kalletaba ya shiga galary, pic d'in da rashida tayi mata da kayan daya saya matane ya gani pic d'in sun mishi kyau sosai atake ya turasu zuwa wayanshi sannan yasa mata credit na 3k seya mik'a mata yace kimin kyau a hotonnan ya nuna mata wayanshi.
Murmushi tayi tace nagode meyasa ka tura baka sanar daniba,yace tokiyi hakuri bazan sakeba. Batace komaiba se kuma tace nagodefa da d'awainiya Allah ya saka da alkhairi,shuru yayi kamar baiji metaceba yana ta dannan wayanshi.
   Ita kuwa se kallonshi takeyi dan yadda yayi kyau sosai. Batate daya kalletaba yace apple nifa bana so ayita kallona,kinya sosai taji dan tasan bai kalletaba,tace nifa ban kallekaba,yace kin kalleni mana aina ganki,tace ta ina kenan yace ta idona mana, dariya tayi tana ci gaba da kallonshi se wayanshi yayi k'ara ya d'auka yadai miher,tace bro mum da dad nata sun dawo dayake sunsan kana ciki se basu shigoba,yace ok tnx sannan ya katse wayar tate da mik'ewa tsaye yana kallonta. Itama shi take kallo tace ina zakaje,yace zan tafi in barki ki huta mana,kawai jin bakinta tayi tace mishi pls karka tafi yanzu,yace meyasa bakya so in tafi,tace haka kawai,ka zauna kamin hira.
Ba musu ya koma ya zauna yaci gaba da danna wayanshi yana magana batare daya kalleta yace su mama sun dawone kuma suna waje shiyasa nake so in tafi dama ina son inga baba. Tace to ai bakomai suma bazasu shigoba inhar sunsan kana ciki,yace eh hakanne yasa zan tafi ai. Yanayin manosh yana burgeta sosai da wasu irin abubuwansa,sam seyaso kallonta kafin ya kalletan,sannan kamar bakoda yaushe yake son magana ba. Shuru tayi tanata kallonshi sosai tana yaba kyansa a ranta,seyace tunanin me kikeyi apple,shuru tayi,yace pls ki dinga cin abinci sosai sannan ki dena cin yaji dan abdallah yacemin kina cin yaji sosai. Mamaki tayi sosai,tace yaushe kukayi hira dashi haka,yace ina ruwanki,tayi murmushi tace to zan dena insha Allah tunda yana nemar yimin illa. Manosh ya mik'e yace apple am goying amma zanyi missing naki wlh yau bazamuyi hiraba kenan tunda mama tananan bazan iya kiran wayankiba amma zan dawo safe kinji, tace to nagode sosai. Yace Allah ya baki lfy tace ameen sannan ya nufi kofar fita,harzai bud'e kofa tace eeem....tsayawa yayi cak tare da juyowa yace yes akwai wani abu ne,mirmushi ta mishi tace bakomai seda safe,shima murmushin ya mata tare da cewa idan akwai ki gayamin,tace akwai abinda nake so amma zanyi maka texsn,yace ok ina jira sannan ya fita.
Manosh ya gaida mama cikin girmamawa sannan ya gaida da baba tare da cewa dama yana son magana dashi,daidai nan yah ibrahim yazo da abinci sosai a kwando suka gaisa sannan ya wuce.
Miher da rash suka shiga da mama sega yah ibrahim,miher ta gaishesa sannan ya ajiye abincin tare da cewa aunty ya jikin dai,tace da sauki sosai,yace to Allah ya baki lfy tace ameen sannan ya fita gunsu baba inda suke magana da manosh. Godiya sosai baba ya dingayi tare da cewa ibrahim kagafa mota ya kawowa maryam wannan kyauta yayi girma dewa wlh dukda dai kace mahaifinkane yayi mana mun gode sosai,nanma ibrahim yayi godiya sosai,sannan yaje ya kira mama itama baba ya gaya mata godiya,sosai sukayi wanda baizai misaltuba,manosh yaji dad'i sosai a ranshi sannan ibrahim ya rakashi hargun motarshi sukayi sallama,sannan ya kira miher a waya,nan ta musu sallama tace zasu da mum nata da safe,rash ce ta rakata har wajen mota sannan suka tafi.
Koda baba ya gayawa maryam kyautar da manosh yayi mata da taimakon babanshi mamaki sosai tayi,babanta ya nuna mata takardun motan dukda sunanta a jiki,dan kunya bata iya cewa komaiba anata tayata murna sannan baba yace zasu tafi shida ibrahim seya tuk'a motar maryam d'in shi kuwa baba yahau nashi suka tafi ibrahim yanata mamaki.
Manosh yayiwa maryam texs kamar haka
_am still waiting my apple_
_akan abunda kike so_
Koda maryam ta karanta setaji a yanzu kam bazata iya cewa komai se tace
_Allah ya saka da alkhairi_
_wannan kyauta yayi girma dewa my peach banajin zan iya sake tambayar wani abu_
Bayan manosh ya karantane seya ce
_pls apple kigayamin indai kina so inyi farin ciki dan ina k'aunarki sosai apple nd i can do anything just for you sweetheart_
dad'i sosai maryam taji sannan ta sake tura mishi
_ba wani abu bane illa flower_ _i love you nd i love flowers so verry much peach_
Koda ya gama karantawa murmushi yayi yace indai wannan ne sekin gaji dashi dan lambunsa guda zanyi a gidanmu my apple,da haka yayi bacci.
Washe gari da safe ya shirya seda ya tambayi maryam tace su baba sunzo sun koma,ita da mama da rash ne,yace ok ganinan zuwa tace to sekazo.
Koda manosh yazo cikin kakin sojojinshi yake se kallonshi yakeyi,office muh'd ya wuce yace yadai abokina ya wifey nane da jiki,muh'd uace tofa tu ba'a baka ba,kar dai harka shirya kenan se tafya,manosh yace wlh kuwa driver yana waje daga nan airport zamu wuce,muh'd yace ok jeka ka fito se in rakaka,manosh ya wuce d'akin da sallama dama mama ta fita tunda maryam tace manosh yazo taje can d'aya d'akin gun wasu matan da y'arsu ba lfy suma.
Manosh ya shigo kenan rash ta mik'e tare da gaisheshi sannan ta fita,ita kuwa maryam flowers d'in kawai take bi da kallo da kuma yadda yayi kyau a kakin sojojin. Akan kujeran ya zauna suka gaisa seya ajiye mata flowern a gefenta,da sauri ta d'auka tana murmushi tare da shinshinawa taji wani k'amshi mai dad'i wanda yasa ta limshe idanunta tace _thankyou so much captain_,murmishi yayi yana kallonta yadda take ta murna da ganin flowers d'in,itama shi take kallo yare da d'auko *ring*mai kyau na maza ta mik'a mishi batare datace komaiba. Hannun yasa ya karb'a tare da cewa thankyou apple naji dad'i sosai,yasa a yatsan hannunshi tare da pecking d'in yatsan nashi yana mata murmushi tare da cewa ya jikin,tace naji sauk'i sosai wlh,manosh yace alhamdulillah zuwa gobe za'a sallameku insha Allah nizanyi tfy kuma zankai 1week kafin in dawo su dad zasuje gun baba dan asa mana rana kinji?
Sam maryam bataso tfyan manosh ba haka kurun tad'an canja fiska,shi kanshi ya lura da hakan seya sauya muryanshi yace "apple r u aokey?" Tace yes am fine ina zakaje? Yace zanje kaduna ne,karki damu kinji zan dawo insha Allah addu'arki nake buk'ata apple,kallonshi takeyi tare da tausayin kanta tace Allah ya kare min kai,yace ameen suna kallon junansu ciki so sannan tayi saurin kawar da kanta gefe tana kallon flower daya kawo mata,manosh bazai iya jurewaba dan haka ya mik'e tare da cewa nizan tafi apple ga wannan,ya ajiye mata kud'i a gefen gadonta sannan ya nufi kofar fita. Har yakai gun k'ofan kanta na kallon flowern,seya juyo yana kallonta sam taqi kallonsa har ya gama kallonta sannan yaja k'ofa ya fita harzai kulle kenan seta d'aga kanta suka had'a ido cikin tausayin junansu yace _i love you so much apple_
_tace i love you too manosh_
Harda d'an kwalla a idonta sannan yaja kofar da sauri ya rufe,ita kuwa hawayene suka zubo mata kona menen oho....
.
Hankalin maman maryam ya kasa kwanciya,seta kira baban maryam a waya tana tambayanshi ko maryam ta iso? Baba yace a'a bata isoba,hankalinta ya sake tashi tace malam yaci ace ta iso ai,shi kanshi hankalinsa ba'a kwance yakeba,amma seyayita kwantar mata da hankali da daddad'an kalamai yana cewa kinsan fa maryam da taimako da kuma tausayi,zaiyu wani abinne ya tsaida ita a hanya amma bari nabi sawunta.
Mahaifin maryam ya rufe shop nashi yabi hanya ai ko seyaga almajirai sunata d'iban abinci a k'asa kuma ya tabbatar da cewa wannan kulan abincinshine. Wayansa ya d'auka ya kira matarshi ya tambayeta cewa me kika dafa minne yau,tace shinkafa da miyace mai had'e da wake,katse wayan yayi ya kama fad'in *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* tare da duduba guraren kozai hango maryam amma sam se *rivom* nata daya hango wanda shida kanshi ya sayo matashi.
Hankalinshi ya tashi sosai,ya kira number'n maryam yanata ringing amma ba'a d'aukaba har kusan sau biyar. Haka ya wuce gida a rud'e inda ya had'u da yah ibrahim da abokanshi suka gaisheshi ya amsa amma suna ganinshi sunan akwai abinda ke faruwa,ibrahim yace baba lfy kuwa,yace lfy lau ka biyoni gida.
Haka suka juya abokanshi suna tsaye daga waje su kuwa suka wuce gida. Mama tana jin sallama ta fito tare da cewa malam lfy,nan ibrahim ya gaisheta sannan baba ya gaya musu duk abinda ya gani a hanya sannan yayita kiran number'n maryam shuru. Addu'a suketayi dukkansu tare da tunanin to ina maryam take?
Ibrahim ya kira rashida da sameera a waya suka ce mishi sam maryam bata zoba,ya sake kiran zahida da amina suma sukace bata zoba,nan ya wuce gidan hajiya iya nanma batanan,koda hajiya iya taji lbrn hankalinta a tashe harda kukanta dan yadda take son maryam a ranta.
Nan tayi lullub'i ta wuce gidansu maryam inda mahaifiyarta taketa addu'a tare da kwalla a idonta. Duk wanda yaji yasan ba lfy bane domin maryam bata tab'a yin hakaba,ga kuma rivom da mahaifinta ya gani agun yasan lallai akwai matsala sosai.
Bayan anyi sallan azahar ne mahaifin maryam yayi bayani a masallahi akan a tayasu da addu'a. Duk wanda yaji seyayi addu'a dan base na gaya muku daliliba.
     Cikin k'ank'anin lokaci magana ya baza ko ina a garin girei. Ibrahim ya kira manosh a waya amma yanata ringing bai d'agaba,hakan yasa ya kira number'n marwan bugu d'aya ya d'auka bayan sun gaisane yake ce mishi manosh fa,domin yayita kiranshi amma bai d'aukaba,marwan yace wlh ni ina office ne maybe baya kusane. Ibrahim yace ok dama wlh maryam ce aketa nema tun d'azu taje kaiwa mahaifinta abinci har yanzu shuru babu ita babu lbr,ahanya akaga kulan abincin a zubar a k'asa sannan an tsinci rivom d'inta har haryanzu babu wani lbr.
  *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* marwan yaketa nanatawa tare da mik'ewa yayi gun manajer'nsu bayan sunyi magana marwan ya d'auki motarsa se gida.
Miher ya gani a tsakar gida zata fita,nan dai suka gaisa yace ina prince,tace yana bacci bayajin dad'i kanshi yana ciwo. Marwan yace ok sannan ya wuce d'akin miher tanata binshi da kallo dayya taganshi tasan ba lfy,haka kawai taji ta fasa tfyan dan tana so taji menene da sauri tabi bayan marwan ta lab'e daga bakin kofa inda taji marwan yana cewa "dude" "dude" ahankali manosh ya bud'e ido yana mamakin ganin marwan a wannan lokacin. Marwan yace sorry na tashe ya jikin,yace alhamdulillah lfy? Marwan yace ka kashe wayar kane,manosh yace no a silent nasa dan ind'anyi bacci wlh ya akayi,marwan yace "dude" akwai matsala baga'a apple ba tun 11:40am yanzu gashi har 3:20pm,kuma duk inda ake tunanin tana zuwa anje bata nan sannan........da sauri manosh ya mik'e tare da d'aukan wayanshi yaga miss call din baban maryam dana ibrahim dadai wasu daban,number'n apple ya kira yanata ringing amma sam bata d'agawa. Kamar zaiyi kuka ya sake kiran wayan yanata cewa "pls apple pick d call okey" where are you apple,wurgi yayi da wayan seda screen d'inshi ya pashe ya shige toilet da wuri,shi kuwa marwan ya d'auko wayan amma ina ba'a ganin komai taci screen.
Manosh ya fito ya shirya suka fita ko mum nashi bai sallamaba,daya ga miher yace miher maryam ta kiraki?miher da jikinta yayi,sanyi tace a'a,yace kiyita kiran numbern ta sannan ki gayawa mum cewa ba'aga maryamba nina fita.
Hawaye miher ta fara dan yadda taga bro nata ya hargitse a lokaci d'aya.
Basu wuce ko inaba se girei,inda suka isa har parlon mahaifinta yana zaune da mutanen unguwa,sukayi sallama tare da gaisuwa sannan manosh ya farayiwa baba tambayoyi kamar ba surukinsaba,shi kanshi baba yasan manosh a rikice yake,manosh yana gama jin komai ya musu sallama suka wuce gurin yayita dube dube amma baiga komaima. Abokinsa *faruq* ya kira wanda yake aiki a *mtn office* yace faruq matar da zaura an d'auketa wayanta a kunne yake inaso kabin min line nata pls insan a ina take da sauri dan Allah. Da sauri faruq ya fara neman line na maryam amma baiga komaiba da tana inda babu netwrk,nan ya sake duba kira na k'arshe daya shiga wayarta ba'a d'aukaba yaga lokacin tana *gurore* sannan yanzu baya iya ganin inda suke. Faruq ya kira manosh yace captain d'azu kaine ka kirata last kuma ya shiga lokacin tana gurore. "Whats! Gurore fa kace faruq? Faruq yace tabbas captain karka damu zanci gaba dabin line d'in inga suna inda ba netwrk ne.
Katse wayan manosh yayi yace ina tausaya musu wlh tunban kamasu kowaye yayi miki wannan aikin "he will pay for it wlh" dan bazan barshiba. Marwan yace muje gida mu shirya manosh,manosh yace no karka damu ka koma kawai yanzu motarmu zaizo zamu bi bayansu,marwan yace ok "dude but pls becarefull,daidai nan motan sojojin ya iso wani ya fito daga gaba manosh ya shiga sannan shi ya shiga baya suka tafi,sega majid yazo suka wuce girei gun iyayen maryam,koda marwan ya gaya musu inda maryam take mamaki sosai sukayi,mahaifiyarta kuwa kuka sosai takeyi,makota sunata bata hakuri.
Abdallah yana zaune a masallaci tare da samari da sauran yara anata karatun qur'an amma abdallah hawayene kawai yakebin fiskanshi.
K'awayentama duk sunzo sunata kuka
Manosh ya kira muhsin yace pls zan tura maka pic na apple kai gidan TV da radio dake adamawa dukka duk wanda yaba da wani bayani akwai babban kyauta ageshi,mihsin yace ok "dude" pls ka kwantar da hankalinka insha Allah za'a sameta cikin k'oshin lfy,manosh yace Allah ya amshi addu'anmu tnx "dude" sannan ya katse wayan.
Maryam ta fara bud'e idanunta tare dayin addu'a harta gama bud'esu dukka tana k'arewa d'akin da take kallo. Katiface kawai a d'akin da wani zanin gado se tsami yakeyi ga akwati da tarin taba wiwi dasu totolin sune kawai a wannan d'akin. Nan danan taji gabanta ya fad'i tanata addu'a tare da mik'ewa ta murd'a kofan amma setaji a kulle yake,nan ta tuna da wayanta datasashi cikin pants nata tun lokacin da suka bige mata abincin babanta. Da sauri tasa hannunta akan pants d'in cikin ikon Allah taji har yanzu wayan yana jikinta,hamdala tayiwa Allah sannan ta ciroshi da wuri dama a silent yake,kodata duba missed calls babu adadi a cikin,da sauri ta kashe wayan gabad'aya dan ganin 7:00pm ne ko sallan azahar batayiba. Kofan data gani ta bud'e taga toilet ne amma babu kyan gani sam a cike yake da k'azanta,hancinta ta d'aure da d'ankwalinta ta shiga da yake akwai ruwa ga kuma morning fresh da izal nan da nan ta wanke shi tas sannan tayi alwala wayanta yana cikin pants nata ta shinfid'a d'ankwalinta tayita biyan sallolinta.
Tana cikin yin sallanne se taji ana bud'e kofan tare da shigowa. Daga jin muryanshi kasan d'an giyane,yana cewa daga zuwanki har kin fara mana kashi ko kashi kin bud'emu da wari kota ina,koda yake shinkafa da wake kuka dafa a gidanku yau shiyasa,ga abinci nan idan kin gama sallan sekici,bayan ya ajiyene ya d'auki kwalin sigari sannan ya tafi.
Bayan maryam ta idar da sallolintane tare,dayin addu'in neman tsari sannan ta dubi abincin daga gani a resturant aka sayo,amma sam bata ciba seta tashi tasa sakatan d'adkin ta ciki sannan tashiga toilet ta kunna wayanta tare da kiran number'n mahaifinta bai d'aukaba dan yana tlband'aki,dan haka ta sake kiran mahaifiyarta bugu d'aya ta d'auka tare da cewa maryam,maryam tana magana a hankali tace na'am mama sannan,ta fara kuka tana cewa mama ya kuke ku kwantar da hankalinku ina halin lfy amma bansan a ina nakeba...bata k'arasaba taga call d'in manosh,tace mama zan sake kiranki bari inyi magana da manosh,to maryam Allah ya kareki zan sake kiranki bayan kunyi wayan kiyi k'ok'ari kozaki gane inda kike dan azo a taimaka miki su waye suka d'aukeki? Maryam tace wlh mama har yanzu bansan komaiba ina kullene a wani d'aki banga kowaba har yanzu. *innalillahi wa'inna ilaihir raji'un*suketa nanatawa ita da mamanta suna hawaye amma ita maryam daurewa takeyi kar ajita tana waya azo a karb'e.
Banyan maryam sun gama hira da mamane se call d'in manosh ya shigo. Da sauri ta d'auka tare da cewa hello peach,wani sanyi yaji har cikin ranshi yace apple ina fata basu miki komaiba,cikin muryan kuka tace eh bakomai amma ina jin tsoro sosai dan ga dukkan alamu mutanen bana garibane domin kayan shaye shaye ne cike a d'akin kota ina peach,hankalin manosh ya sake tashi sosai yace ki b'oye wayan apple zan kiraki anjuma i love you aunt ki kula da kanki pls zanyi k'ok'arin gano inda kike kinji? Ok Allah ya taimaka peach bansan inda nakeba bare in gaya maka,pls aunt ki dena kuka "i will soon come to you" nasan inda kike already,ina nake pls ka gayamin,calm down apple kina *numan* ne nima yanzu haka muna numan d'in zanzo inda kike yanzu ki b'oye wayanki zan kiraki anjuma okey? Ok thankyou,i luv apple,i luv u too byeee...
.
33-34 da sauri maryam ta share kwallanta dan kar azo a ganta. Manosh kuwa wani iri yaji a ranshi sam baiso ya bartaba amma babu yadda zaiyi,awaje ya samu muh'd sukayi sallama ya sake jaddada mishi cewa ya kula mishi da apple shidasu majid.
Manosh ya isa kd lfy,yana isa maryam ya fara kira,taji dad'i sosai suka d'an tab'a hira sannan sukayi sallama.
  Hajiya iya dake zaune a gefen maryam tace surukin nawa kenan shine ba'a tab'a kawo minshiba,dariya maryam tayi tace saurin me kikeyi hajiya ai dole zaizo ya gaisheki dan kece babbar k'awa.
Dariya sukayi dukkansu maman rashida tace to maryam mudai zamu wuce Allah ya baki lfy,tace ameen mama nagode. Hajiya tace ni wannan mota naki semun rabata gaskya,ya zaiyi ya kawo miki bai kawomin,rash da maman maryam sunata dariya,maryam tace karki damu wai yasan ke baki da k'afane bazaki iya tuk'iba kinga ni se inyi ta kaiki duk inda zakije ko? Nanma dai dariyan akayi daidai lokacin samira zahida da ameena suka shigo da sallama.
Bayan an gaisane su maman rash suka fita inda yah ibrahim ya mayar dasu a motar maryam.
Maryam da k'awayenta se hira sukeyi tare da tayata murnan samun mota. Sosai maryam take samun jama'a harda malaman islamiyyansu se zuwa gaisheta akeyi dayake ita mai jama'a ne sosai. Daga masu kawo mata fruits se masu bata kud'i,su kansu doctors da nurses d'in sunata mamaki har tambaya sukeyi wai maryam d'innan 'yar wayece a garinnan dan yadda jama'a suke sintiri agunta. Shi kanshi dr muh'd yaji mamaki sosai,dan haka ya kira manosh yace gaskyaka samu mata wlh ka rik'eta da kyau sannan mu dami su dad akan ayi maganan aurennan da wurifa. Dad'i sosai manosh yaji yace insha Allah.
Maryam ta samu sauk'i sosai koma ince ta warke. Da yamma miher da mum nata sukazo inda miher ce tayi driving nasu gwanin sha'awa.
Lokacin maryam ta idar da sallan la'asar kenan tana addu'oi setaji bud'e kofa tare da sallama,mamantane ta amsa musu dan rash ta koma gida.
  Koda maryam ta idar,kunya sosai taji da ganin mum d'in manosh. Kanta a sunkuye tace sannu da zuwa,mum tace yawwa maryam sannu ya jiki,maryam tace da sauki ina wuni,tace lfy lau ya kika k'ara ji da jikinki,tace da sauki,mum tace to Allah ya k'ara lfy Allah kuma ya yaye miki,maryam tace ameen gabad'ayansu sannan mum ta zauna kusa da maman maryam akan carpet dake shinfid'e a k'asa,ita kuwa miher ta zauna a gefen maryam tana zolayarta matar bro kin samu lfy se kuma magan aurenku da bro,ahankili tayi maganar cikin zolaya tana dariya.
Maryam data kasa sakewa dan kunyan mum murmushi kawai takeyi,miher tace wlh ki dena jin kunyan mum dan bata da matsala sam wlh garama ki saki jikinki bro yace in kawo miki wannan,flower ne d'an k'arami maiban sha'awa,amma maryam taqi karb'a dan kunya,miher se dariya takeyi tace idan bakya so shikenan se in gaya mishi yanzunnan,muntsinin miher tayi ta cinyarta batare dasu mum sun ganiba. Daroya sosai miher takeyi tace shikenan nifa wasa nakeyi kar anjuma inji kin cijeni,mirmushi sosai maryam tayi tajin kalmar miher amma sam taqi tayi magana,mum ma ta lura da cewa maryam a takure take dan haka tace miher mu tafi ko donmu barta ta huta. Murmushi maryam tayi miher ta mik'e,maryam tace mun gode Allah ya kare,mum tace ameen sannan tayi gaba itada maman maryam. Ai suna fita maryam ta karb'e flowern tace wlh sena had'aki da captain kinata sani magana bayan kinsan bazan iyaba ko,miher tayi dariya tace nima ai zan gayamishi harda muntsinin da kika min,dariya sukasa dukkansu sannan tace miher mungode sosai ku bakwa gajiya da d'awaiyinane pls bana buk'atar wani abu kuma dan Allah ya isa haka mana,miher tace dani kikeyine,kallonta maryam ta tsayayi tace ni kike mannawa hauka ko,miher tace "am sorry our wifey" ban isa in manna miki haukaba wlh amma wlh mum bazata tab'a yarda inzo dubaki empty hand bane nizan tafi nabar mum tana jirana zamuzo gobe nida *my majid* kafin a sallameki *apple* tate dajan lallausar kumatun maryam. Dariya sosai maryam takeyi yayinda miher ta fita da sauri tana mata byee,ita kuwa murmushi takeyi tare da cewa tonagode Allah ya kiyaye hanya.
Maman maryam ta bud'e ledojin kayan tea ne manyan gwangwanaye da kuma fruits. Mama ta kalli maryam tace sude basa gajiya wlh,mamansu tana da kirki wlh gata da sauk'in kai kamar ba matar mai kud'iba kuma naga soyayyarta akanki sosai wlh. Maryam tayi murmushi tace wlh mama hakama miher tana sona sosai wlh gaskya ba laifi Allah yasa su d'aure a haka,mama tace ameen sannan sukaci gaba da hiransu irinna *uwa da 'ya*.
Yau aka sallami maryam,babantane ya d'aukesu a motarshi inda sukaitawa dr muh'd godiya, cikin girmamawa yace wlh bakomai baba Allah ya bata lfy,suka amsa da ameen sannan maryam tace nagode fa sosai da k'ok'arinku Allah yabar zumunci,murmishi yamata tare da cewa ameen aunty bakomai semunzo girei,tace wlh na hutar daku hakama yayi wlh sannan ta tafi yana musu Allah ya kiyaye.
A girei ma tinda maryam ta dawo zuwa ake ana gaisheya.
Bayan kwana biyu ne miher tazo da drivernsu da kula sabuwa babba a hannunta peppe chikeen ne a shike. Murna sosai maryam tayi da daginta suna d'an tab'a hira sannan ta mik'e tace zan tafi dan akwai inda zanje wlh sannan ta bud'e zip na jakanta ta ciro flower tace inji camtain. Murmishi maryam tayi tace nagode bari in wanke kulan ki tafi dashi,mihe tace no wlh danke kawai na sayi kulan dan haka shima nakine. Gidiya sosai maryam tayi tare da rakota har waje sukayi sallama.
Bayan tfyantane samira da rsha sukazo sukaita hira,maryam ta d'ibo musu kazan sunaci suna hira inda maryam take sanar dasu cewa gobe za'azo tambayarsu.
Washe gari da misalin 10:00am na safe iyayen manosh dasu marwan sukazo girei domin tambayan auren 'ya'yansu. Dama baban maryam yasan da zuwansu dan haka shima ya nemo mahaifin samira da kuma 'yan unguwa dan shine uban maryam da rashida dukka.
Koda sukaga mahaifin manosh masu ji mamakiba dan yah ibrahim ya musu bayanin komai kuma yace ya yafe harma da maman rash,amma baban maryam yace dole za'a sanar dashi kodon yasan yayi kissa kuma *azumi sitti* yahau kansa.
Zuwan manya sukayi da iyaue su majid,dan seda sukayi tambayan zahida da amina sannan sukazo girei.
  Karb'a na musamman aka musu inda aka gaggaisa kuma aka fahimci juna ansa aure nanda 3month.
Bayan an gamane sukayi godiya sannan suka tafi.
Bayan sun koma gidane mahaifin maryam ya kira mahaifin manosh yace dama inaso muyi wata magana mai muhimmancine akan wani bawan Allah daka tab'a bugewa akan hanya girei shekaru biyu da suka shige,idan baka mantaba akwai wata yarinya dataketa bin motarka a wannan lokacin tana kuka. Jikin mahaifin manosh yayi sanyi dan baizai tab'ance wannan rananba.
Baban maryam yace to wannan mutumin bakowabane illa mahaifin rashida wanda marwan yake neman aurenta,tun daga wannan lokacin daga bugeshi ko minti goma bai k'araba Allah yayi mishi rasuwa. A wannan lokacin akwai wanda ya ganka shine da kukazo girei yace lallai kaine wannan mutum, yanzuma na gaya maka hakanne dan kasan cewa azumi yahau kanka,sannan yana da kyau ka nemi gafarar iyalansa,wanda ya gankan bakowa bane illa d'an cikinsa wanda yazo ya gaisheku mai suna ibrahim wato yayan rashidan kenan,amma sunce sun yafe har abada sun d'auki kadda.
Mahaifin manosh ya sauke ajiyar zuciya yace nagode sosai alhaji Allah yabar zumunci,kuma wlh naji dad'i sosai da yadda kamin magana a sirrance Allah ya saka da alkhai kuma insha Allah gobe zanzo gun iyalan marigayin,wlh tun wannan lokacin nima bani da sukuni kuma na koma girein na tambayi wani matashi akan wani da aka buge da mota nan ya tabbatar min da cewa Allah yayi mishi rasuwa,wlh tun daga wannan lokacin na kamu da hawan jini kuma nayi azumina sittin,sannan nayi aike zuwa ga iyalan wannan mutumin a wannan lokacinma sedai na hana abayyana sunan,kuma nasan nayi kuskure sosai wanda hakan shiyasa na gyara halayyata da dama alhaji nagode sosai kuma insha Allah gobe inanan zuwa girei da safe.
Mahaifin maryam ya tuna da randa akazo da abinci da kaya da kuma kud'i har *dubu d'ari uku* wai a baiwa iyalan marigayi,kuma sunyita tambaya daga gun waye aiken yazo amma sam basu samu amsaba.
Kamar yadda mahaifin manosh ya fad'a da safe yaje shida mahaifin marwan da kuma drivernsu,inda suka samu mahaifin maryam a gida dan baije ko inaba tunda yasan da zuwansu. Shiya musu jagora har cikingidansu yah ibharim suka gaida da iyalinsa sannan suka bada hakuri tare da musu gaisuwan rashin. Suka amsa tare da cewa cewa ai kwananshine ya k'are dan haka bakomai sun yafe wlh,godiya sosai mahaifin manosh yayi tare da musu alkhairai sosai sannan kuka fito tare da yah ibrahim yana rakasau da baban maryam.
Bayan fitowansune mahaifin manosh yake tambayan ibrahim akan aikin da yakeyi,nan ibrahim ya gaya masa cewa bai dad'e da gaba NYSC nashiba yana jirane tukunna,nan mahaifin manosh ya bashi *card*nashi yace ya same ran monday.godiya sosai ibrahim yayi dan yasan kawai aiki za'a bashi.
Lokaci yanata tafiya angwaye se himma suke bayarwa wajen aikin ginin  gidajensu da zasu tare da amarensu. Manosh kusan kullum seyaje girei tun bayan dawowarshi,ranan suna hira yake tambayar apple wani irin gida take so,dadai tak'i gaya mishi,amma da taga zai b'ata rai tace ita dai ranta nason gidan sama,sannan ya kasance *milk da d'an army green*. Murmushi manosh yayi yace shikenan nagode. Itama murmushin tayi tace amma pls karka takura kanka danni kai nake so ba gidaba dan haka kakyi komai d'an daidai pls,dad'i sosai yaji yace shikenan apple zanyi d'an daidai *mata 4* dariya sosai tayi tace bakomai tunda dai nice *uwar gida*
Soyayyarsu abun burgewa wlh domin mai tsafta ce.
Maryam ce zata kaiwa babanta abincin a shop nashi tana cikin tfy se wata bak'ar mota ta tsaya,da sauri suka fito maryam bata zata gurinta zasu nufoba kaiwai suka big'e abincin hannunta ya zube a k'asa,kan tace wani abu sunsa mata hanki a hanshi mai d'auke da magani take ta mance inda take sukayi saurin jefata cikin mota suka fizgi motar a guje. Adaidai wannan lokacin iyayen maryam sukaji gabansu ya fad'i atare suka hau fad'i *Hasbunallahu wani'imal wakim* suketa nanatawa...
Hankalin manosh a taahe ya kalli d'aya daga cikin sojojin yace ina tausayawa duk wanda yayiwa maryam haka wlh.
  Miher ce zaune ita da mum nata a palo suna jimamin abinda ya fari da maryam se wayanta ya fara k'ara da sauri ta d'aga tare da cewa hello lubna,lubna tace miher ya gida naji bro marwan yana cewa anyi kidnaping maryam d'in da bro manosh zai aura? Miher tace wlh kuwa lubna,lubna tace subbahanalillah yanzu su waye sukayi wannan aikin,miher tace wlh har yanzu dai shuru tukunna amma ansan inda maryam d'in take yanzu haka,lubna tace haba alhamdulillah a ina aka sameta,miher tace bawai an sametabane fa,andai gano inda take a *numan ne*. Lubna tace har numan aka kaita kai Allah ya tona asirinsu zanzo gobe insh Allah,to sekinzo nagode.
  Koda lubna ta ajiye wayan miher se ta kira wani tace hello *saddam* ya akayi har su bro suka gane cewa maryam tana numan,aikinka baiyiba saddam domin yanzu haka su captain suna numan dan haka kuyi gaggawan d'agata daga numan ku k'ara gaba da ita zan tiro maka da kud'i yanzu a account naka saddam idan asirinmu ya toni zansha wuya agun bro marwan wlh seya kusan kasheni pls indai da gaske kana sona tokayi wani abu plss saddam. Murmushi yace karki b'ata bakinki bbynah, yanzu zamubar adamawan ma kwatakwata karki damu sweetheart zan nuna miki cewa da gaske nake k'aunarki bari na nemo wani abokina,lubna taji sanyi a ranta tace nagode sena jika.
Maryam kuwa dama ta kashe wayan gabad'aya tasa a cikin pant nata. Yadda aka ajiye mata abincin haka sukazo suka samu,yace wato bakici abincin bako,bai jira jin abinda zata ceba ya toshe mata baki da hanci da wani hankachif fari take ta mance inda take seya d'auketa cak se mota suka kama hanya,cikin ikon Allah kuwa ba'a tsaidasuba har suka bar numan.
Tfy sukeyi hankalinsu a kwance suna dariyan mugunta yana cewa *captain manosh* zanga iya kwarewarka kafin in shiga hannunka kuwa sena gama lalata budurwan naka tukunna dan nasan idan na shiga hannunka tofa tawa ta k'are shiyasa nima zanyi abinda nakeso tunda dama banida iyaye se kawai in bisu bayan na shana hhhhhhh...
Manosh se kiran line na maryam yakeyi amma shuru, seyayi tunanin kodai tana tare da mutanenne shiyasa bata bud'e wayanba. Nan dai yace bari yad'an k'ara jira. Anan ne muhsin ya kirashi yace "dude" na raba hotunanta kota ina yanzu haka ma ana haskawa a gidan *TV GOTEL* , *NTA* da kuma *ATV* duk anta haska hotunanta,manosh yace nagode abokina pls kuyita tayamu da addu'a sannan kuyita bada sadaka Allah ya bamu sa'an gano inda take,muhsin yace ka kwantar da hankalinka abokina insha Allah zamuga maryam cikin k'oshin lfy dan maryam tana da halayya masu kyau.
Iyaye maryam kuwa hankalinsu yad'an dawo jikinsu da sukaji lfyarta k'adau amma dai har'a yanzu suna cikin tashin hankali sosai. Duk girei seda akaji zance sace maryam auntyn yara,dan haka aketa addu'oi babba da yaro kai harta almajirai idan sukaji lbrn tofa suna komawa gun malaminsu suka gaya mishi,yace musu kwarai yaji a radio dan haka kota ina addu'oi maryam take samu.
Hajiya iya kuwa tafi kowa tashin hankali ana zaton,ko menene dalili oho? Kuka takeyi safe da dare tare da addu'an Allah ya baiyana maryam.
K'awayen maryam sun zama abin tausayi musamman rashida data tina kalmomin data dinga gayawa maryam ranan,dan haka ta dinga kuka tare da kewar aminiyarta. Hakama abdallah ya shiga wani hali sosai dan ganin maryam yakeyi kamar yarsa da cike ciki d'aya,yah ibrahim nema yake lallashinsa dan kowa yasan irin k'aunar da take tsakaninsu hakama ita maryam d'in tana ji da abdallah fiye da,sauran yaran.
Manosh baiga kiran maryam ba har 12:00pm dan haka yasan cewa akwai matsala,kuma shi yasan babu wadda ya gayawa cewa maryam tana numan daga iyayenshi se iyayen maryam se kuma friends nashi,dan haka abin ya dameshi sosai gashi faruq yace mishi wayan maryam a kashe yake bazai iya gane inda takeba dole se wayanta yana kunne.
Da misalin 2 na dare suka isa wani jeji tare dabi cikin jejin daba kowa se wani d'an k'aramin gini daba'a k'arasashiba nan suka tsaya suka fitar da 'yan kayayyakin da suka taho dashi suka dai kimtsa gurin se suka kwantar da ita akan bargo sannan suka zauna a gefe.
  Saddam ya kira lubna yace hello bbynah mun iso lfy,tace sannu da hanya a inakuke yanzu? Yace muna jihar bauchi cikin gefe da *jejin yankari* ido lubna ta zaro tace har bauchi,yace yes bazasu tab'a tunanin zamuzo bauchiba,dad'i taji har cikin ranta tace nagode bbynah aikinka ya gyaru,murmushi yayimata yana busa sigarinshi yace bbynah gaskya bazan kyale yarinyarnanba dolene sena tab'ata fa,hankalin lubna ya tashi tace no bbynah kafa cemin ni kad'ai ce yarinyar da kake so taya za'ayi kashe min haka kuma,wato dama kana cin amanata kenan ko? Saddam yace wlh ba haka bane bby shikenan wlh bazan mata komaiba amma kinsan ked'in kince dole semunyi aure kafin muyi wani harka kuma gaskya ni a matse nake wlh,lubna ta murgud'a baki tace karka damu idan mun gama wannan aikin zakasha mamaki da irin gift d'in dazan baka wlh bbynah,nan saddam yaji dad'i yace okey my luv shikenan sekin jini,tace ok but pls karka mata komai indai har kana sona,yace wlh bazan mata komaiba karki damu bbynah.
Maryam bata farkaba har asuba,ta jita ak'asa nan ta tashi da sauri tana addu'oi tare da k'arewa gurin kallo setaji hawaye a fiskan,kukan tane ya tashi mutum guda d'aya da yake kwance daga gefe dan sauran kam duk sun shiga gari neman abinci.
  A gigin baccin yazo inda take yace ke 'yanmata yane? Kallonshi takeyi tare da cewa bawan Allah inane nan kuma? Yace nan jihar bauchine ta gefen jejin yankari. *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* maryam taketa fad'i sannan tace karfe nawane yanzu? Ya duba wayanshi yace 5:30am,tace ina zan samu ruwa nayi sallah,nan ya d'auko pure water ya mik'a mata tare da ciro bindiga a aljihunsa yace kinga wannan,wlh idan kikayi wani kuskure sena pasa kanki dashi,jikinta na rawa tace to alwala kawai zanyi inyi sallah.
Komawa yayi ya kwanta ita kuwa jiki na rawa ta koma gefe tana alwala. Bayan nan ta koma cikin ginin tare da lekashi taga dai bacci na damunshi sosai,dan haka ta ciro wayanta ta kunna tare da da turawa manosh texs sannan ta kashe wayar tahau yin sallah.
Manosh daya kasayin bacci yana zaune a mota a numan seyaji texs ya shigo wayanshi,da sauri ya duba
  _hello peach,sun d'aukeni daga numan zuwa jejin gefen yankari dake jihar bauchi gurin babu kyan gani a tsakiyar jeji muke cikin wani kango da babu ko rufi asaman pls peach do something ka kulamin da iyayena plss da kuma abdallah nah byeee_.....
Manosh ji yayi kamar zaiyi hauka dan yadda yakejin k'irjinji yana tafasa. Kwana d'aya kawai amma dukya fita hayyacinsa haka ya juya ya koma girei ya dad'a baiwa iyayen maryam hak'uri tare da kwantar musu da hankali,sannan yasa aka kira mishi abdallah yace kayi hakuri abdallah maryam tana cikin jarabawane amma komai zai wuce ina tabbatar maka da cewa auntynka zata  dawo insha Allah kuma dukda halin da take ciki sam bata mance da kaiba tace ingaisheka abdallah. Rungume manosh abdallah yayi yana zubda kwalla shima manosh daurewa kawai yayi sannan ya kalli yah ibrahim yace ka kula dashi dan sak'on maryam kenan akanshi.
Manosh ya shige mota ya wucegida a galabaice,toilet ya shige ya watsa ruwa sannan ya fito yasa jaket maroon da black yana k'ok'arin fitowa sega mum nashi da miher,nan ya koma lallausar gadonshi *milk colour* yad'an jingina yana kallonsu.
Kuka miher ta farayi tare da ciro wayanta ta d'aukeshi hoto taje har kusa dashi tace kalli yadda ka zama fa bro, kwallan idonshi ya share tare da kamo hannun miher yace karki damu zan koma normal ne bayan na samo apple d'ina. Mum tanata kallonsu tare da tausayawa d'an nata tace Allah ya baka sa'a *son*, yace ameen mom nina tafi sena dawo,har waje miher ta bishi tanata kuka harya tafi....
.
Bayan maryam ta idar da sallah ne taketa hamman yunwa,dan tunda ta baro gida bata sake cin abinciba se ruwa data sha,gata da *ulcer*.
Lek'owa tayi taga har yanzu bacci yakeyi,dan haka taje inda yake tanata crwa 'bawan Allah脳2' ahankali ya bud'e ido tare da tasowa ya zauna! Kallon juna suka tsayayi domin sun tabbata akwai inda suka tab'a had'u dukkansu d'in. Can maryam ta tuna shine mutumin da mota ta tab'a bigeshi a hanya harta taimaka mishi yahau mashine aka kaishi hospital tabbas shine wannan. Wani sanyi taji a ranta tare dayin mirmushi tace bawan Allah dama kaine ka rabani da iyayena? Shuru yayi yana kallonta cikin mamaki yace dama kece yarinyar da aka d'auke? Kallonshi ta tsaya yi tana mamaki tare da cewa aka d'auke ko kuka d'auke bawan Allah.
Bayansa yaketa waigawa sannan ya mik'e tsaye cikin hanzari yace banina d'aukekiba abokin aikinane,maganar gaskya nidai ba mutumin kirki bane wannan ranan da muka had'u dakema sata naje nayi aketa bina tare da fasamin jiki,dak'ar nasamu na gudu shine na b'ullo ta girei har muka had'u dake kuma na miki k'arya kika tausaya min tare da taimakona.
Maryam tayi shuru tana sauraranshi tace to bawan Allah dan Allah ka gayamin abu guda d'aya wanene yasa a kamoni? Shiru yayi yace bazan gaya mikiba sedai in taimakeki in baki wayana ki kira duk wanda kike buk'ata indar har kinaga za'a iya taimaka miki,shuru maryam tayi tace to ai nabar wayata a gida ban kuma san numbern kowaba sena iyayena da k'awayena.
  Shuru yayi nad'an lokaci sannan yace toki gayamin numbern iyayenki,nan ta gaya mishi numbern babanta yasa ya kirashi,bugu d'aya ya d'auka lokacin suna tare da dad d'in manosh yaje yi musu jaje. Maryam tace baba nice yanzu haka ina jihar bauchi cikin jejin dake gefen yankari,baba yace to wannan numberfa? Tace baba karka damu lfyata lau babu abinda ya sameni sedai ina jin yunwa sosai har k'irjina ya fara min ciwo,subhanallah maryam haka suka barki da yunwa dan basu da imani tun jiya? Baba sunban abinci amma bazan iya cibane ka gaida mama kuma dan Allah karka kira numbern nan domin na d'aya daga cikinsune ya taimakamin idan ka kira suka gane zasu kasheshi. Hankalin mahaifinta a tashe yace shikenan maryam na fahimceki amma dan Allah ki daure kici abinda suka baki kodan lfyarki,to baba ya mama take,lfy lau karki damu damu maryam ki kula da kanki,insha Allah zaki dawo garemu da izinin Allah,Allah ya amshi addu'ar mahaifina na gode....bata k'arasa maganarba ta katse saboda kuka daya ci karfinta.
Mahaifin maryam hankalinsa a tashe ya kira manosh ya gaya mishi komai,manosh yace karka damu baba insha Allah zata dawo kudai tayamu da addu'a.
Shi kuwa bawan Allah kallon maryam yakeyi tare dajin tausayinta ya bud'e ledanshi ya d'auko *maltina da biskits*  d'aya ya bata ta karb'a tare dayin godiya,yace bakomai ki koma inda kike dan nasan sun kusa dawowa zanyi iya k'okarina dan in taimakeki ki dena damuwa kinji? To nagode sannan ta koma taje ta zauna tare da bud'e malt d'in da biskits tana sha.
Wayarta ta bud'e sega texs d'in manosh dana miher,na miher ta fara bud'ewa inda taga hoton manosh sanye da maroon jaket,ita kanta maryam tasan manosh ya shiga wani hali daga ganin hoton nashi,sannan ta karanta texs nata kamar haka
         _slm 2u my aunt_
_bansan mezance mikiba aunt,amma ina cikin damuwa sosai musamman yadda naga bro manosh ya zama kamar bashiba dan rashinki_. _Aunt munanan munata addu'a Allah ya d'auraki akansu,kinga dai yadda bro nah ya zama wlh tun jiya baici komaiba har yabar gida yanzu_. _ina sonki wifeynmu,pls koda empty rexs ne ki aiko min dan inji sanyi a raina_. Yours miher....
Koda maryam ta karanta setaji kwalla ya zuba mata,nan ta tura mata da
  _thankyou so much sis,nagode sosai da kulawarki,kuma nayi farin cikin ganin pic d'in peach,dan yasani farinciki sosai wlh_. *nagode*
Koda taga texs d'in manosh batayi reply ba se kawai ta kirashi. Katsewa yayi ya kirata ta d'auka tare da cewa *captain*, sanyi yaji har cikin ranshi yace yes apple a wani hali kike yanzu? Karka damu ina halin lfy,sedai nayi fushi dakai,meyasa mena miki apple? Saboda kabar cikinka da yunwa rabonka da abinci tun breakfast d'in safe meyasa hakan peach? Am sorry apple amma kema ai bakici komaiba,eh amma yanzu haka ina shan malt da biskits,naga pic naka yanzu miher ta turo min peach a jiya kawai amma ka canja. Yadda yaji muryanta kamar zatayi kuka yacewa sojan da yake driving tsaya anan ka karb'o min malt da biskits,sannan yace "apple am goying to eat now okey" pls banaso kisa damuwa aranki muna hanyan bauchi kinji? Murmushi tayi tace "thankyou peach" cikin sanyin murya. Sunanta ya kira a hankali *aunt*, cikin muryan kuka tace uhmm,yace pls stop it apple i will soon come to u okey? Har yanzu kukan takeyi "tace okey i have to peach byee...
Bayan ta katse wayanne ya had'iye tausayinta a wuyanshi daidai lokacin aka kawo malt da biskit d'in ya bud'e ya fara sha,bayan ya gamane ya karb'i driving d'in gudu yakeyi kamar zai tashi sama..
Can kuwa koda maryam ta ajiye wayan da sairi ta kashe ta mayar pant d'inta dan taji zuwan mota.
Saddam ne tare da sauran abokanshi 3 suka dawo,wannan d'ayan da suka bari yana kwance ya mik'e yare da cewa ya kuka dad'e ne haka? Saddam yace wlh bari kawai,ta tashi kuwa,eh ta tashi tayi sallah,saddam yace gaskyafa ni a matse nake wlh dan haka kawai zan sauke gajiyata akanta wlh,d'ayan yace haba saddam karkayi haka pls da safiyannan idanma hakane ai gara ka bari se dare kai kanka zakafi jin nishani idan duhu yayi. Saddam yace hakanefa,to gaskya dole na koma cikin gari in nemo wata dan wlh a matse sosai nake kasan abunka da sabo,yana kaiwa nan yaje ya duba maryam tana rakub'e a gefe tana kuka. Dariya sosai saddam yayi yace garama ki dena wannan kukan domin anjuma zakiyi wanda ya fishi sauti hhhhhhhh
Hankalin maryam ya sake tashi domin taji hiransu. Abinci wani ya kawo mata ya e gashi kici ko fine girl,ko kallonshi batayiba ya ajiue ya k'ara gaba.
Tana jin motarsu ya tashi ya tafi ta lek'o taga duk sun tafi seshi wannan bawan Allah. Wayarta ta kunna ta nemi layin manosh amma sam baya shiga,ta tabbatar da suna hanyane dan haka taje tayi alwala tare dayin sallan walaha tayi addu'oi sosai sannan ta sake gwada numbern manosh har yanzu dai shuru yak'i shiga,haka ta koma gefe tana zaune tanata karatun qur'an a cikin zuciyanta har azahar tayi.

Maryam tanayin alwala yazo yace amma ki gayamin sunan k'awayenki mana,tace lfy? Yace lfy lau,nan dai ta dinga kiransu harta gama yace babu wasu da kike tunanin sun tsaneki? Tace gaskya babu,yace to shikenan jeki kiyi sallah.
Bayan ta idarne seta bud'e wayanta cikin ikon Allah call d'in manosh ya shigo,da sauri ta d'auka tace hello,yace peach kina dai lfy ko? Tace lfy lau manosh kuna ina,pls kazo da sauri domin suna da niyan aikata wani abu a kaina pls..karki damu apple inanan a inda kike yanzu zanzo gareki,mik'ewa tayi da sauri tare da jujjuyawa tana kallon jejin tace ina kake peach?...
Wayan hannunta ya karb'a tare da kashe wayar gabad'aya yana binta tana komawa da baya tana cewa dan Allah kayi hakuri. Ran saddam a b'ace yace wato dama da waya a hannunki ko,to wlh bazaki b'ata min aikiba sedai in kasheki in kashe banza. Bindiga ya d'au zai harb'eta d'aya mutumin yace haba saddam kar kayi haka mana mace zaka kashe kuma k'aramar yarinya,kawai muyi gaggawan barin nan d'in shine mafita,domin yarinyar data saka aikin itace take baiwa masu binciken address d'in inda muke dan a kamaka ka fita daga rayuwarta for good. Kan saddam ya d'aure sosai yace kana nufin *LUBNA AHMAD* tana min wasa da hankali ,yace kwarai kuwa.
Mamaki ya cika maryam ta nanata sunan a cikin ranta *lubna ahmad*? Kawai seta d'iba da gudu ta barsu atunaninta ai su manosh sun iso inda take. Bindiga saddam ya d'aga tare da harbinta ai kuwa seya sameta a saman hannunta kusa da kafad'arta,ihu sosai maryam ta saka tareda fad'uwa k'asa tana kuka. Saddam zai kara mata se d'ayan ya bige bindigan yace meyasa hakane saddam wai kasheta zakayine? Sauran ukun ne sukazo da mota sukace kuzo mu sampe sojoji sunji k'aran bindiga zasuzo kuma,d'ayan yace bari in d'auko yarinyar dan bazamu barta a hakaba ai. Da gudu saddam yahau mottafi suka tafi suka barshi,gashi sam baiga maryam a inda ta fad'iba kamar wanda ta b'ace. Yanata tsaidasu saddam amma sam sunk'i tsayawa sema harbinsa dasukayi a k'afa ta yadda bazai iya guduba. Ai kuwa segasu manosh da gudu ya k'araso yana cewa apple, apple na iso ina kike? Kan mutumin ya nufa tare da d'agoshi yace ina maryam! Take mutumin ya fara b'ari dan yasan shikenan kashinsa ya bushe tunda ya shiga hannun *sojoji*, yace *sir* wlh ban saniba acan ta fad'i nima ita nake nema...

0 comments:

Post a Comment