Blogroll

BANNER 728X90

Friday, 19 January 2018

DAN ALHAJI Part 3

*** DAN ALHAJI  3 ***
.
A cikin yan mata ya rinnga yaba wa da hankalin yaudarace kawai wannan yarinyar idonta a bude yake kana ganin kalaman ta kamar wata tsohuwar yar bariki yac e ba haka bne kawai mata masu tattausan lafazi soyya ce mai karfi take shiga tsakanin su a kullum sulainman na zuga shi mai zaiyi da yar talaka,dayaga abin bana wasa bane sai da yasan yadda yayi Alhaji muaz yasan zancen zai auri yar talaka sanin halin alhaji muaz na kin hurda da talakawa ko kadan baya son ya rabe shi ya dinga fada ya zubawa idonsa toka tun da yake bai taba yiwa safuwan fada ba sai karonnan ran safuwan ya baci yace shi ita yake so ya ko haukansa ta inda ya shiga batanan yake fita ba yace kaje ka dubo ko yar wa kake so ka aura zan aura ma,
.
safuwan yayi buris da maganar yaci gaba da zuwa gurin rufaida yasa a gaba yana ta wallafo masa illolin zama da talaka kuma ya dauki alkawarin in dai ya rabu da yarinyar nan zai kara masa wasu kanfanoni annan ne HAJIYA BILKI yar katsina wan asali kenan ga kunya ga kara haba yallabai kabar yaro ya auri wacce yake so talaka da mai kudi duk Allah ne ya haliccesu kuma ba wanda yasan wada yafi mu lokacin da mukayi aure kana dashine? da na sha yasar da kayan dakina ina mana abinci na kuma sha kwana da yini anan fa yace ina wuta ya sakata?
.
ya ringa fada wai tayi masa gori a gaban yaro itama ta daka ta tashi ba wanda ya saurara a ranar dai rai ya baci sosai dan sai da hajiya tayi masa fushi sosai wato yajin aiki ya rasa yadda zai sha kanta gashi baya son bacin ran ta kona miskala zarratin amma yana ganinin indai akan ya hakura safuwan ya auri yar talaka ne sai dai ko wacce wacce.haka sabani ya ringa shiga tsakanin su har sai da aminiyar ta hajiya jamila ta ringa tausar ta akan ta rabu dashi dan zamanine hajiya bilki tace baki san halin yallaban ba yana da bala'in taurin kai nima dakika ga muna zaune lafiya dan ni dince ta makaryaci kinsan dai komai yanzu ma wani lokacin birkicewa yake yi wai shi aure zai kara yana son karawa safuwan yar uwa tunda naki haifuwa kinji fa kamar ni nake bawa kaina ni yanzu na zubawa sarautar Allah ido kowa dai ya hau kujerar naki,a majalisa su sai zuga shi suke wai kar ya aure ta tunda abbansa baya so kawai yasan hanyar da zai yi ya yaudareta ya nuna musu sam shi auranta zaiyi nina daina hurda da ko wacce yarinya najashi cikin zolaya nace har tima yace koma wace ce suka hau dariya gaba dayansu yanzu kam kusan ace tunda ya hadu da rufaida ya daina kula ko wacce yarinya sai dai abin da ba'a rasawa dan abin ko rawa shima din ya yi bala'in ragewa yana kuma ganin da zarar ya aureta zai de na gaba daya su kuma sun kudirin niyar ko ta halin kaka bazai aure taba jarabawa ta fito gaba daya rufaida tayi passing malam nasiru yayi murna sosai ya ringa sa mata albarka habiba ko baki yaki rufuwa saboda murna bayan tayi wanka ta huta ta dauki waya ta sana da safuwan shima yayi farin cikin yace aina dauka baZa ki sanar dani ba ai labari ya iso min tun dazun a hanya naci karo da lubabatu suke bani labari
.
duk makarantar keda bahijja kun zarce kowa.ina mika sakon murna kafin nazo har gida sai dai ina ganin ya kamata mu shirya wani dan kwarya kwaryan party na taya ki murna tace a'a na gode abba bazai yadda ba su bahijja basun gaya maka munyi daxun a makaranta ba? ai ya isa wani haddan mota ya shiga ya wuce yayi mata siyyaya ya hada kaya kamar hauka dan sai daya cika motar da kaya atamfofi da dai sauran kaya basai na tsaya ina ir gosu ba da dai duk masu azabar tsada sai kuma bangaren takalma da gyalluluka da yan kunnaye fashion dasarkoki har dana gold yayi parking motar a kofar gidansu yara suka ringa shigar dasu daga habiba har rufaida ba wanda bai tsorata ba suka ce kai ku tsaya ba nan gidan aka ceku kawo ba wanan ai kayan masu kudine suka ce a'a nan aka ce mu kawo da yake sun san shi mutum ne mai kyauta kusan duk yaran layin suka ce safuwan ne fa yace mukawo umminta tace maza ku mayar ke kuma dauki gyalenki kije kice kin gode ya ajiye yi azama kafin abbanki ya dawo bake ba har ni sai ta shafa ganin yara yayi sunyi kaya niki niki suna dawowa dasu ya dubeta yace meye haka?
.
tace kabari ba yanzu ba yace wannan wacce irin magana ce? a fusace yake maganar duk abinda na baki sai kice kin gode kiki karba to wallahi ina tantama akan so da kika ce kina min itama ta fusata tace ai dama ba abinka nake so ba kai....bata karasa ba ya kwallawa yaran kira yace kowa ya dauki abinda yake so ya kai gida" suka tsaya tsororo suna mamaki.
.
yadaka musu tsawa yace ba da kunake ba nan da nan suka sawa kayan warwaso kowa yayi gida da abinda ya samu yana murna yakai wa uwarsa ita ko kafin yaran su karasa ta shige gida ya shiga matarsa ya hada wata yar karamar guguwa yayi ficewarsa daga layin,tana shiga gida ta fada kan cinyan umminta tana kuka habiba tace lafiya ? tace yayi fushi ransa ya bace sosai tace gwara hakan dan wallahi abbanki yaga wannan kayan raina in ya kai dubu sai ya baci.
.
Zamu ci gaba anjima, inshaallahu, amma kuna tare dani kuwa?

0 comments:

Post a Comment