Blogroll

BANNER 728X90

Wednesday, 17 January 2018

NI A.Y.S NAKE SO Page 1-5

NI A.Y.S NAKE SO Page 1-5
.
NA
Princess Eshat Aysm
.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA (A.Y.S)
.

Wani irin tsawa aka buga dayasa hanjin cikin ta mur?ewa, ta ?aga ido taga sama tayi bak'ik'irin, tsoro ya kamata gashi tayi nisa akusa da mutane, nan take ta fara kuka tana danasanin fitowa, wani tsawan aka sake bugowa, ta runtse ido tana tunanin a ina zata samu abun hawa, sai da Ammi ta hanata fita amma tayi taurin kunne, wani kukanne ya kufce mata ta fara shek'a shi da iya k'arfin ta.
kamar daga sama taji hoon ?in mota abayan ta, da sauri ta juya, ganin glass ?in motar me duhu ne bata ganin naciki yasa ta runtuma da wani mahaukacin gudu.
Jan motar akayi akaci gaba da binta, sai gudu takeyi tana kuka, "yau naha?u da 'yan yankan kai Allah ka tsareni, gashi ba kowa yau nashiga uku".
gwaruwa tayi da wani garu yasa dolenta ta tsaya, Motar ne ta nufota, ya bu?e murfin motar yafito, sai yanzu ta da?a razana, ta tabbatar wannan kam ba mutum bane saboda kyawun shi ya wuce na mutane, ta waro ido da hanci tana kallon inda yake nufo ta, dogone fari k'al dashi, hancinsa kamar pencil, ga wani rami a gefen kumatunsa (Dimples).
tsugunawa tayi a wajen tana kwararo addua, har gaban ta ya k'arasa ya tsaya, "Ni ban gudu miki ba sai ke zaki gudumun, kalli sama, wannan ruwan ya sauk'o zai iya tafiya dake shikenan kin mutu, shi yasa na tsaya zan temake ki".
Tunda ya fara magana take kallon ?an mitsitsin bakin shi, maganar ma dagani a dole yake, cikin tsoro ta ce "kana nufin kai ba Aljani ba ne"?
Dariya ta bashi har dimples ?inshi suka lotsa, ya ce "kin ta?a ganin aljani ne? Su ai dukkanin su munana ne, ni kuma ya kika ganni".
ya kashe mata ido "kafin tayi magana ruwa ya sauk'o da k'arfi sosai, ko ganin gabansu basuyi saboda inda hadirin ya rufe wajen.
Lalume ya fara yi har yaji ya rik'o hannun ta, wani k'ara ta saki duk a razane take, ya janyo ta da k'arfi ta fa?a k'irjinsa, dai2 lokacin akayi wani walk'iya me hasken gaske, motarsa ya hango yayi saurin janta suka shiga ciki, sai a lokacin ya sauk'e ajiyan zuciya, ya juya ya dubeta sai ?ari takeyi, wani k'aton rigar sanyi ya janyo a sit ?in baya, ya  mik'a mata yace  " sanya wannan, amma ki cire jik'akken tukunna".
Kallon shi tayi daga sama har k'asa "Basshi kawai na gode". Ganin haka yasa yafuta a motar ya rufo, ruwa yaci gaba da dukansa, "to shi wannan mutumin bayajin sanyi ne, oho mishi shi yaso".
Ta fa?a tana karka?a rigar, najikin nata ta cire ta saka na sanyin, harda k'aton hula a jiki, lokaci guda ta nemi sanyin ta rasa, har wani ?umi takeji yana shigar ta.
?u?ewa yayi ya shiga, fuskanshi yana kanta, lokaci guda kuma ya kauda kai ya tada motar "Ina zan kaiki".
ya tambaya hankalin shi nakan tuk'i, ta?an zaro ido "basai ka kaini ba nagode, idan ruwan ya ?an tsaya zan tafi babu nisa".
Bai kalle ta ba ya ce "baki bani amsaba fa". Aranta tace "yanzu me nabaka idan ba amsa ba".
Kallon shi tayi tace "kayi hak'uri". da sauri ya kalle ta "amsar kenan"?
Ta ce "eh". tada motar yayi ya ?au hanya "idan nakai ki gidanmu ai zakiyi magana me kyau".
ware ido ta sake yi "a'a tsaya zan fa?a maka, amma idan anganni a motar nan zansha duka".
yace "karki damu, namiki alk'awarin bawanda zai bugeki".
kwatance ta masa gidanmu yana bayan NITEL a nesa zaka ajiyeni".
Bai ce mata kome ba, sun ?anyi nisa ta ce "kai bakajin sanyi ne"?
.
"inaji lokacin da naga kina ?ari, amma da kika saka rigarnan sai naji nadaina ji, inaga jininmu iri ?ayane".
"uhm". kawai tace.
Ba wanda ya sake magana har suka iso anguwar, da hanu tayi ta masa alama har suka isa k'ofar gidan, da hanzari ta bu?e motar zata fita ya dakatar da ita "ke agarin ku haka akeyi".
Tayi dariya ta ce "kayi hak'uri mantawa nayi, nagode, sunana AISHA".
murmushi yayi ya ce "bance kimun godiya ba, Sunan ki na tambaya, naga kina farinciki kin shiga motar kyakkyawa ko"?
Dariya ya bata aranta tace "shima yasan yanada kyau".
Ta kalleshi ta ce "ina wani kyau mutum yana kama da aljanu".
Dariya yayi sosai ya ce "sunana UMAR MUHAMMAD, zaki iya k'irana faruq".
"suna me da?i na gode da taimako".
Bu?e motar tayi da fara'arta ta nufi gida, gaban tane yafa?i ganin mahaifin ta a tsaye, dayake lokacin ruwan ya tsaya, juyawa tayi ta kalli motar Faruq tunawa da tayi yamata alk'awarin baza'a daketa ba, yananan a wajen amma bata ganinshi, dak'yar ta k'arasa, tun kafin yamata magana tafara rantse2, "Abbahna ruwane yamun duka wlh taimaka mun yayi....
cikeda ?acin rai yace "na tambaye ki, shiga motar wani shine kin kare kanki, kada ruwa ya dakeki, kinsan hatsarin da shigar yake nufi"?
Bakinta na rawa tace "Nasani Abbah".
Duk tagama ji?imewa, tasanshi sarai ya tsani yaganta tana hira balle ace ta shiga motar wani, kullum sai yayi mata garga?i, bata jira me zai sake fa?aba tayi cikin gidan da gudu.
Faruq yana kallonsu, mezaiyi inba dariya ba, yarinyar nan gaba ?aya matsoraciya ce, ahankali ya fito a motar har ya iso gaban Abbah ya tsuguna ya gaishe shi.
A dak'ile Abbah ya amsa, Faruk ya sunkuyar dakai ya ce "ruwane naga zai mata illah, ban ?auko ta da wani manufa ba, kayi hak'uri dak'yar ta yadda ta shiga ma".
Tun tsugunawar sa Abbah ya lura yaron kamili ne, ya masa k'warjini sosai, hanu ya ?aga masa ya ce "na gode".
Juyawa yayi ya nufi cikin gidan Faruk ya bishi da kallo yana tunanin tsaurin ra'ayi irinna Abbah.

.
Da gudu ta shige ?aki tana neman Ammi, ganin bata nan tayi ?akin su Hajara da gudu, suna ganin ta suka tintsire da dariya, Sadiya ta ce "waye ya koro ki, ruwa ya miki duka ko"?
B'ata rai tayi "kunsan bana son tambayoyi, mik'omun wayata".
"Aunty a ina kika samo wannan rigar"?
Hajara ta fa?a tana k'unshe dariya, harara ta sakar mata ta ce "Nidai nashiga uku, ku kenan ba dama kuga abu sai kuyi ta damun mutane, to na Faruq ne".
Me zasuyi inba dariya ba, sun santa sarai idan batada gaskiya tayi ta ?ata rai kenan tana tsare gida, tunanin su ya tafi akan Abbah ya bugeta ne, wayar ta fizge a hanun Sadiya, "Bani nahau Facebook, nasan masu sunan 'yan gayun nan sun turo kalamai masu da?i".
dukan su suka matso kusa da ita, Sadiya ta ce "kullum ke group ?aya kike shiga, yau kam kishiga mana wani".
Dariya Aisha tayi ta ce "sai dai kuyi zuciya a fara barinku kuna rik'e waya, wannan tsaurin Boss ?in namu bazai bari mutum ya?an me rayuwa take cikiba".
Hajara tayi tsaki "ni kiyi kishiga mana".
Login facebook tayi, an cika mata inbox da sak'o amma ko dubawa batayi ba, Grup ?in 'yan gayu ta shiga, *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIA*
Kullum sunan da take gani yana shawagi kenan a group ?in, mssg yake turowa masu zafi na love, yau kam bataga post ?inshi ba, ta dudduba duk babu na yau, sai tsirarrun post ?in da akayi shima duk tambaya ake yau bamuga AYS ba.
Hajara ta ce "to waye kuma AYS"?
"oho musu, inaga ita macece, ni Abdullahin nan yana masifar burgeni, ni duk inda nashiga sunanshi ake ambata, da alama yaron yanada farinjini, kuma yanada baiwa, yanada tarin masoya amma bashida girman kai, ko inane zarian oho".
Sadiya ta ce "ke zarian ma baki sani ba, anbarki a baya".
Tashi tayi tana cewa "zan lek'a ammi ko ta fito daga wanka, Hajara kije ki zubo mana abinci yanzu zan dawo".
Duk sukayi waje, Aisha kam wayar tata ta zubawa ido, sosai takejin kewar Abdullahi, yau me yahana shi hawa, Allah yasa lafiya, rigar jikin ta ta kalla tayi dariya "wannan kuma ?an rigimar nabar rigata a motar sa, yanzu hakama ya yar mun, hmmm amma gaskiya kyakkyawa ne, Allah kada kabani mijin da yafini kyau, 'yanmata suna bibiyan shi hawanjini ya kamani, shi dakanshi ma gori zaimun tab?i Allah ya tsareni".
Mik'ewa tayi tashiga wanka, tana fitowa tasaka kayan Sadiya riga da zani, ko iya ?aura zanin batayi ba balle ?ankwalin, haka dai ta mur?a ta ?oye wayar ta tayi ?akin Ammi itama.
AMMI macece hamshak'iya, sam batada k'awayen da suka wuce 'ya'yanta, suma yaran kansu a ha?e yake, komai a tsakanin su sukeyi ba ruwansu da k'awaye, idan ?aya yana cikin matsala to tamkar dukansu ne, MUHAMMAD MESAJE shine mahaifinsu, irin mazannan ne masu tatssauran ra'ayi, bayaso yabada doka a tsallake, magana ?aya yakeyi baya canzawa, yaran su 5 ne, AISHA, SADIYA, HAJARA, AL'AMIN, ABDU, JAFAR.
Babu abunda suka nema suka rasa kullum cikin Farinciki suke rayuwa.
.

Faruq tunda ya?au hanyar gida yaketa dariya shi ka?ai, "wannan yarinyar tayi mun sosai, zankai wa Momcy labari".
Yana isa kamfacecen gidan su yayi hon, da sauri me gadi yazo ya bu?e, saida yazo futa ya hango rigar ta da hijabin ta, nurmushi yayi ya ?auko, k'amshin ta ya bugi hancinsa, ya lumshe ido yana murmushi, ?akin shi ya nufa yajefa kayan a mchn na wanki, sannan yayi wanka ya nufi ?akin mahaifiyar shi, jikin ta yaje ya kwanta yana zun?ura baki, ta shafo kanshi ta ce "Babana ina kashiga".
"yau ko sau ?aya baki k'irani ba".
"sorry my son, netwk ne babu kyau, ina fata babu abunda ya ta?a mun kai".
Cikin zumu?i ya ce "Akwai Momcy, wata yarinya ta ta?amun zuciya, na kamu da sonta Mom".
Mamaki gami da farinciki ya kama Mom, kullum adduan ta Allah yakawo ranarda zaiga yarinyar dayake so, babu irin matan da ba'a kawo mishi ba yace baiga wacce tamishi ba, yau Allah yayi, rungume shi tayi tana sa mishi albarka, "Nayi murna Babana, ka gayya to abokanka zan shirya muku Fati na murnar ganin yarinyar da kake so".
"woooo lov u Momcy Allah yabarmun ke a raye".
dariya tayi. Tace "maza tashi kaje kaci abinci, idan nabarka haka zaka kwana".
Cikin farinciki yake don haka babu gardama ya tashi. UMAR FARUQ mahaifin shi ya rasu yanada shekaru 15, shi ka?ai suka haifa, don haka Momy ta?au son duniya ta ?aurawa Faruq, sauda yawa sai tayi tunanin tayi aure sai taga duk ku?in ta suke so, don haka ta hak'ura ta rik'e ?anta tilo.
???
Tana shiga wajen Ammi suka tuntsire da dariya, Ammi ta ce "oh ni Amina Allah yabani 'ya, yanzu ?aurin zanin ma sai kin tikuikuye shi, wannan ai abun kunyane ma".
Zun?ura baki tayi saura k'iris tafara kuka, Sadiya tana dariya ta ce "Ammi wannan ?aurin zanin ai yayi".
Duk ha?iye dariyan su sukayi, yanzu sai ta cika musu gidan da kuka babu gairi babu dalili.
.
Sun gama cin abinci sunyi Sallah Abbah yashigo, da nutsuwa ya dube ta ya ce "Nafara wasa dake ko, duk ranar da kika k'ara shiga motar wani zakiga yanda zanyi dake, sai kin gwammaci ruwan yayi miki duka".
Ammi ta ce "me Maman taka tayi, yau dai anji kanku".
Murmushi yayi baice komai ba ya nufi ?akin shi.
"Ke kuma motar wa kika shiga"?
Ammi ta tambaya,
"Ruwane zaimun duka....
Tsawa ta daka mata, "ki rasa wajen fakewa sai motar wani, kedai kin ?ata wayonki, natabbata Hajara bazata iya haka, tsaya ma kiji, idan bakiji tsoron Allah ba zakiji tsoron abunda zai miki, aduk lokacin da mace dana miji suka ke?e to dole akwai she?an a tsakanin su, kin tabbata babu abun da yayi miki".
idon ta narai2 ta ce "Wlh Ammi baimun komai ba".
"to kada kisake, kuma azamanin nan idan da kin ha?u da ?an yankan kaifa, Allah ya kiyaye".
Tsoro duk yakamata, tayi alk'awarin bazata sake wannan kuskuren ba, har magriba suna zaune Ammi tana musu wa'azi. koda dare tayi ?akinta ta wuce tanaso ta kwanta, tunda ta ?au wayar ta a?akin su Hajara taje tayi kwanciyar ta.
Harta fara bacci ta tuna da Abdullahi, tashi tayi ta zauna ta ?au wayar ta.
Still bataga post ?inshi ko ?aya ba, tsaki taja "to wai ina ruwana dashine".
Latse2n ta tagama taja bargo ta kwanta, dak'yar ta samu tayi bacci, da asuba tana sallah ta sake hawa, wani ajiyan zuciya tayi me k'arfi, sunan nashi tagani yayi post masu yawa, duk saida tabi ta karanta su, da?ine ya kamata, ganin sunan ka?ai yana sata farinciki, bata ankara ba taji ana buga mata k'ofa, da hanzari ta ?oye wayar, ko ba'a fa?aba tasan Abbah ne, "yauma nayi laifi ban futa da wuri ba kenan".
Ta fa?a a ranta tana k'ok'arin bu?e k'ofar, shi?inne kuwa, kallon ta yayi na?an sakwanni ya ce "Mamana yau bakiyi karatu ba".
Ta langa?ar da kai ta ce "Abbah na kaina ne yake ciwo".
da tausayawa ya ce "muje kisha magani".
A falon Abbah duk k'annan nata suna ciki kowa da Qur'ani a hannun shi, duk suka gaishe ta, ta amsa tana ta kalan tausayi kada Abbah ya gane lafiyan ta k'alau, zama tayi a kusa da Sadiya Abbah kuma yaje ?auko mata magani, ?an dungurin ta Sadiya ta yi tace "kedai Abba yana biye miki, da wanine da yanzu yasha duka".
ta ce "ke nifa kaina ke ciwo, magani yaje ?auko mun".
"yaushe kan naki yafara ciwo, to idan kikasha magani ciwon gaskiya zakiyi".
Ta zaro ido "da gaske kikeyi, to lafiya ta k'alau nikam".
duk suna jinsu suka kwashe da dariya.
.
.
Saida suka gama aikin gidan tas suka nufi wajen Ammi, gaishe ta kawai sukayi suka nufi kitchn.
Aisha ta ce "Abdullahi yahau fa".
Dukkan su suka washe baki, "me yahana shi hawa jiya"?
Hajara ta tambaya.
"ina zansani, ni banta?a magana dashi bafa, ko grup ?inma basu san da wata Aisha ba".
Ta fa?a tana dariya, suma dariya sukayi, Sadiya ta ce "Amma ke ?innan.... Ki misi magana kawai".
Hajara tayi caraf ta ce "me zatace mishi, kawai munsan yana burgemu basai anmishi magana ba, yaje ma ya
raina mana ke, shareshi kawai".

Tace "wallahi kuwa".
?ata rai Sadiya tayi ta ce "kuma idan baki ganshi ba kada kisake mun maganar shi, wannan ma girman kai ne".
"ke ni nake girman kan".
"kiyi hak'uri".
Bawanda yasake magana suka ?aura girkin rana, *HAD'IN SALAD* Suka farayi, suka yankashi da albasa, tumatir, gurji, karas ?in kuma suka kankareshi suka ha?a waje ?aya, mai suka ?an yarya?a masa sai magi, suka juye suka kai wa Ammi.
Kafin taci abincin rana shi take ci, yana k'ara lafiya, yana saita ciki, me hawanjini ta yawaita ci zata nemeshi ta rasa, kuma gashi bawani ku?i zaki kashe ba.
Zaki iya yin na zogale kuma zaki iya coslow duk yana k'ara lafiya da ciko da mace.

Jalof ?in shinkafa da kwakwa sukayi suka juye a flask suka shiga wanka, komai tare sukeyi babu abunda Ammi bata koya musu ba, idan ana hutun makaranta ba ruwanta da aiki.
.
Iskane yake ka?awa ga wani k'amshin k'ada dayake tashi, dayake garin damuna ne, Abbah yana kishin gi?e yaji ana k'wank'wasa musu k'ifa, Jaridar hanunshi ya ajiye ya futa.
Faruq yagani tsaye a wajen, yasha manyan kaya harda hula, fuskarnan sayau ga fara'a a tattare dashi, kallo ?aya Abbah ya mishi ya gane shi, hanu ya mik'a mishi su gaisa amma sai yaga ya tsuguna har k'asa yana gaishe shi, Abbah yayi murmushi ya amsa cikin sakewa.
Faruq ya susa kai yace "nazo wucewa ne nace bari na tsaya mugaisa".
Abbah ya fa?a?a fara'ar sa ya ce "ka kyau ta, Allah yayi albarka, nagode sosai, a garinnan kakene"?
sunkuyar dakai yayi yana murmushi "muna ?an bayanku ka?an, gidan Alhaji Muhammad Buzawa".
"au wanda yarasu ko, kaine UMAR FARUQ kenan, nasanshi sosai abokina ne".
shidai Faruq murmushi kawai yakeyi, burinsa yaga Aisha don ko bacci be iyayi ba yana alla2 gari ya waye yazo ya ganta, wannan dattijon kuwa bai isa yace wajen ta yazo ba, gara ya lalla?a shi su saba a hankali...
tunanin shi ne ya katse jin Abbah yana cewa kashigo daga ciki nanma ai gidanku ne".
ya ce "idan nadawo zan shiga yamzu ana jirana".
daganan sukayi sallama ya tafi. Kwana 4 amma har lokacin Abbah baya kulata, kota gaishe shi baya amsawa, idan taje karatu ma korata yake yi, kanta kuwa kullum acikin ciwo yake yi, saboda tsaban kukan datakeyi, awajen k'annan ta da Ammi ne take ?an samun sauki.
.
.
*Dare mahutar bawa*
Ammi ta zuba tagumi baccin ma yak'i zuwa mata, wannan shariyar da Abbah yake nunawa Aisha abun yana ta?a ta, tunda ya k'wace wayar sai ya hak'ura, dubanshi tayi taga baccin shi yake yi, mik'ewa tayi da niyyar barin ?akin taji ya rik'ota,
"Haba Amina, meyasa kike damun kanki, kinsan duk duniya nafi kowa son Aisha, idan nabarta zata lalace, baki ganin tafi k'annan nata sakarci".
Ammi ta ta?e baki ta ce "tun farko kajata a jiki yanzu ka ?ullo da wannan hukuncin
Kullum da kuka take wuni".
harcikin ranshi yaji kukan nata, ya ce "Daga yau nadaina fushin shikenan nima adaina fushi dani ko".
murmushi tayi ta ce "ko kaifa".
Saida suka kwanta yace "yaron daya ?auko ta a mota rannan ashe ?an gidan BUZAWA".
Da mamaki tace "ayyah rashin sani".
"jiya yazo mun da wani magana, wai Aisha yakeso da aure".
Ammi tayi dariya tace "Haba2, Aishar nawa take, ai yabari ta girma tukun".
"nima abunda na fa?a mishi kenan ya nuna mun nataimaka Mishi yanda zan rik'e Aisha haka zai rik'eta, ganin ya takuramun na amince mishi, nima zan huta da ?acin ran da take saka mini".
Tashi Ammi tayi rik'e da baki ta ce "?an wannan laifin har kana k'iranshi laifi, gaskiya kabarmun 'yata tayi karatu kafin".
"Amina har kin manta halin Aisha, duk ranar da zata fita sai ansamu wani ya biyo ta, yanzune da suke hutu samun kwanciyar hankalina, Auren nata shine gatan ta, kinga yaronnan bashida wani aibu donme zaki ?aga hankalin ki".
"To amma Alhaji masu biyotannan fa ba ita take k'iransu ba, su suke biyota".

Ya nisa yace "yanzu dai nagama magana aure zanmata, gobe zai kawo mahaifiyar sa su gaisa".
Ganin bata sake fuskaba yasa ya shiga rarrashin ta har ta sauko, "Allah yasa hakan yazamo alkairi".
Washegari da sassafe Ammi tace musu zasuyi bak'uwa, gaba ?aya suka hau murna don akwaisu da son bak'i saboda basu zuwa ko ina, daga gidan kakansu sai  makaranta, Aisha binsu kawai take da kallo inda suka zak'e, ita bataga abun murnaba, dama anguwa zasu tayi farknciki, ita sam batason mutane, idan ba tasan mutum ba bazakaji ta masa magana ba, saninma irin na sosai ?innan, danginsu gaba ?aya bata saba dasuba sai Maman Ammi.
"Aunty mungama girkin".
taji Hajara tana fa?a.
Ta ce "Yaran Ammi 'yan albarka me kuka dafa mata".
gabanta suka kawo suka dire, k'amshi kuwa ya cika wajen,
Jalop ?in Kuskus sukayi sai Chip na potatoes, sai drink kala biyu, da Sweet Runs.
"karfa kuce banyi aikin ba, wannan rawan kan naku kunji jiki, bakusan bak'uwar ba kun zak'e dayawa".
Sukayi dariya Sadiya ta ce "tunda kika ga Ammi tasan da zuwanta ta musammance".
Hajara ta ce "Ni damuwata musamu muyi mata rakiya idan tazo tafiya, kinga zamuga gari".
Duk suka tuntsire da dariya, Aisha ta ce "nikam bana fatan nasake zuwa ko ina ruwa ya tareni....
Hango Abbah sukayi ya nufo gunsu fuskarnan cike da fara'a, duk suka zuba ido suna tunanin meya kawoshi.
Hanun Aisha yazo ya rik'e, da dariyarshi yace "Mamana har yanzu ba'a huce ba ne? Ko ?an sake rannan yanzu bakiyi".
Ta sunkuyar dakai tana dariya, "komai ya wuce ai, na yafe miki".
Su Hajara suka hau tsallen murna, "Abbah mungode, dama ?azu tagama kuka wai yanzu baka kulata".
Tausayin ta ya kamashi ya kalle ta, idonta har sun ciko zata sake ?are baki yace "kukan me kuma, nadaina fushin kada kisake tsallake dokata kinji".
?aga mishi kai tayi, ya ce "muje Amminki tanason ganinki".
yana rik'e da hanunta suka nufi wajen Ammi.
Ammi tana hakimce suka shiga, ya ce "ga uwata ki mata fa?a, amma bance a ?ata mata raiba".
Ammi tayi dariya tace "nima uwatace nafika sonta".
Duk sukayi dariya kafin yace "Zanshiga ciki, bazan koma office ba nafiso yaronnan yasameni akwai maganarda zamuyi".
ta ce "To Abbahn yarana".
Yace "Abun naki harda son kaine, yaranmu zakice".
"to yaranmu". "ko kefa". Sukayi dariya ya fita.

.
Aisha tana kishinge?e ajikin Ammi, irin wannan wasan nasu yana bata mamaki don ita gani take sun girma amma sai suyi ta wasa.
"Aisha kinajina ko, nasanki da rashin hankali, wannan bak'uwar tanada matuk'ar muhimman ci a rayuwar ki, idan tazo kika share ta kamar yadda kika saba yi wa mutane zakiga yanda zanyi dake, ki sake jikin ki sosai kada tagane bakison mutane kinji ko".
Zun?ura baki tayi ta ce "Ammi wai ni me nakeyi na rashin hankali, kullum sai anmun fa?a".

dariya Ammi tayi ta ce "ke?inne ai, kije kiyi wanka yanzu ki shirya, kada kisa riga da zani kinsan baki iya ?aurawa ba".
kuka tasakarwa Ammi harda bubbuga k'afa "ga su Sadiya amma ba'a k'irasu ba saini.... Buge bakin Ammi tayi tace "zaki tashine ko saina sa?a miki".
da gudu ta tashi tana kuka.
su Hajara suna jiyota sukasa dariya, Sadiya ta ce "Aunty ya kamata kibarmun girmannan tunda dama nafiki tsayi da k'iba".
Hajara tace "da hankali".
ganin zasu ?ata mata rai yasa ta wuce tabarsu a wajen.
Ruwan wankan ta ha?a me ?an zafi tasaka turaren wanka aciki ta shiga, da?in ruwanne ya kashe mata jiki tayi zamanta har tana lumshe ido, AYS ne ya fa?o mata arai tasake lumshe ido tana tunanin yaushe zata sake ganin sunanshi, da zata samu taji muryan shi da taji da?i, da k'yar tayi wankan tafito ?aure da towel, hand drya ta ?auka ta tsane ruwan kanta dashi sannan tashafa mai da hoda ta ?an murza lips stik abakinta, "bak'uwar tanada muhimmanci agareni kuma, me Ammi take nufine, to hala wata 'yar uwa take mata, ba wani kwalliyar da zanyi gayyan sa ciwon kai".
sumbatun ta tagama ta ciro wani less riga da siket purple, sai zagayen fari ajiki tasha aiki, ?inkin yayi mata ?as daidai jikin ta, ganin ba iya ?aura ?ankwali tayi ba yasa ta ?auko k'aramin farin gyale ta yafa me goldin ajiki, tana cikin fesa turare taji hayaniyan su Hajara, "wa innan mahaukatan yanzu haka bak'uwar ne ta iso suke wannan ihun".
?an tsaki taja tayi waje itama. Kusan shiga babban falon nasu taji taci karo da mutum, saura ka?an ta fa?i ta ?ago cike da masifa tayi tsammanin k'annen tane, mutumin data ganine yasata sandarewa awajen, UMAR FARUQ ne, yana sanye da shaddarsa rigar ?inkin half, tayi bala'in yimasa kyau, murmushi kawai yake zubawa dimples ?innan nasa suna lotsawa, hanu yasa ya rufe fuskan shi, "wannan kallon zakisa nazama mummuna".
Lek'ek'e ta farayi ganin babu kowa ta ce "me ya shigo dakai gidanmu, karufamun asiri ka tafi".
Nok'e kafa?a yayi ya ce "nima gidanmu ne, babu ruwanki dani".
Ka?a baki tayi  zatabar wajen yajawo mayafin ta, "kinyi kyau sosai, kamar nasace ki na gudu haka nakeji".
Murmusawa tayi ta ce "kaima kayi kyau".
Murmushi yayi yace "nagode".
.
D'akin Ammi ta nufa anan take jiwo hayaniya, Farar matace kyakkyawa kana ganinta kaga Faruq, tsayuwa tayi turus, ko ba'a fa?aba tasan mahaifiyar Faruk ne, ganin Ammi tanata watsa mata harara ne yasa ta k'arasa kusa da matar ta gaisheta, da fara'ar ta ta amsa, Ammi tace "yarana sun ha?u duka, saiki za?i naki aciki muga ko zaki gane ?iyar taki".
Momy tayi dariya ta ce "tun shigowar ta nagane ta, wannan tayi lukuta".
ta nuna Hajara ta nuna Sadiya ta ce "wannan tayi tsayi da yawa, amma ?iyata 'yar daidai ce, daban take".
Ta jawo Aysha ta ce "ko ba itace wannan ba".

gaba ?aya sukayi dariya, Ammi tace "kin canka".
Sadiya ne ta zun?ura baki tana mita wai su bata sonsu, Momy tayi dariya ta ce "kunga wannan ?auketa zanyi takoma wajena, dole na za?e ta".
Sai kuma suka fara mata gwalo.
Abincin da sukayi suka kawo mata, babu wani fulako tanaci tana santi, itadai Aisha duk ta takura kanta, matar nan ta jani da yawa.
"Tareda ?ana nake, ban muku bayani ba, Aysha taimaka kije kada yaga na da?e".
Ammi ta ce "ah ah kitafi mishi da abinci".
.
Su Sadiya ma duk mik'ewa sukayi suka bi bayan Aisha, suna daf da shiga falon Aisha ta ce "A'ina Ammi ta samo mutanennan, ?an natafa wanda ya?auko ni a motane ranarda ruwa yamun duka".
kama baki sukayi Sadiya tace "dama yasan gidannan kenan".
Hajara ta ce "koma yane idan sun tafi Ammi zata mana bayani".
Da sallama suka shiga, ?an ?agowa yayi ya amsa amma k'asa2, duk hankalin shi yana kan Aisha yabita da kallo ko kyafta ido bayayi, yayi missing ?in fuskarta sosai,  su Hajara kuwa hankalin su yana kan shi ganin yanda yabi Auntyn su da kallo kamar zai ha?iye ta, ita ?inma duk kunya ta kamata aranta tace "me mutuminnan yake nufi ne".
.
Gaishe shi sukayi suka bar wajen, lokaci ka?an Hajara ta dawo mishi da kayan abinci, Aysha ta mik'e zata bita yayi saurin taka k'afarta, 'yar k'ara ta saki yayi yayi saurin ?agawa, lokacin har Hajara ta fita, ya tsuguna wai yana hura mata k'afar, dariya ya bata don ita ba zafin da taji rakine kawai, amma ta k'unshe dariyar, zama yayi a kujerar da yake fuskan tarta, yak'ira sunanta a hankali, ?agowa tayi ta zuba masa ido, ya ce "kinga mahaifiya ta ko"?
Ta ?aga masa kai kawai, ya ce "tana sonki sosai, don ke tazo gidannan".
Zaro ido tayi, yace "eh, tun ranar da ruwa ya miki duka kika tafi da imani na, nasan idan narantse miki ko baccin kirki banayi ba tare da tunanin ki ba bazanyi kaffara ba, ban ta?a so ba, kada ki watsamun k'asa a ido, nayiwa Mahaifin ki magana kuma ya bami ke".
Binshi kawai takeyi da kallo har yagama, jin maganan shi na k'arshe ne ya jefata a damuwa, tunanin ta ?aya idan tayi aure shikenan bazataga Ays ba, fashewa tayi da kuka da iya k'arfin ta, hankalin shi in yayi dubu ya tashi, "don Allah kiyi shiru baki sona ko?
.
Bazan miki dole ba kiyi tunani, amma wallahi idan baki amince ba akwai matsala, ki tausayamun Aisha".
har k'asa ya suguna mata, sai a lokacin ta rage kukan, yace "Baki sona ko".
Ta girgiza kanta, "to meyasa kike kuka".
Nanma girgiza kanta tayi, ya ka?a kai yace "bani wayarki nasa miki numbata, idan kinyi tunani duk hukuncin da kika yanke ki fa?amun".
A hankali ta ce "banida waya".
Shiru yayi can ya ciro ?ayar wayarshi ya mik'a mata "
.
Ki rik'e wannan zan k'iraki nanda kwana biyu".
har tasa hanu zata kar?a ta tuna Abbahn ta, ta ce "kabarshi kawai, Abbah na yahanani rik'e waya".
Da?i yaji aranshi wannan ma wani tsaro ne, ya ce "ki kar?a, zanyi wa Abbah bayani, bazai hanaki ba".
Hanu biyu tasa hanu ta kar?a, da zolaya ta ce "bafa aro ba, kyauta".
Yayi dariya ya ce "zan iya baki kyautar kaina balle waya".
Murmushi tayi tace "nagode".
Zuciyarta fal farinciki tayi ?akinsu Hajara da gudu, tun kafin su san me takeyiwa dariya suka hau tayata ('yan abi yarima asha ki?a).
wayar ta mik'a musu, me tsadan gaskene sosai, Hajara ne ta ?ata rai ta ce "kinsan Abbah ya hana ko".
"to 'yar bak'inciki sai kitsaya kiji bayani, nasan wannan kallon da biyu, nafi matsuwa naji me yakawo su gidannan".
Sadiya ta fa?a tana gyara zama, dungurin ta Aysha tayi ta ce "ke tsaya nahau Fcbk sai nabaku labari".
Sake baki sukayi suna kallon ta suka kasa magana, tsawon lokaci Hajara ta ce "Aunty anya ba asiri aka miki acikin fcbk ?innan ba kuwa, daga baki waya...
Sadiya ta katseta, "tayani wannan tunanin, kuma babu abunda takeyi aciki dazai amfaneta sai kallon sunan wannan ?an Aljanin".
Itadai batace musu komai ba tahaura abunta, sak'onnin nasa ta duba duk sallama ne yafi goma, ?ata rai tayi aranta ta ce "baimayi kewata ba yaronnan".
amsa mai sallamar tayi kafin ta sauk'a.
tajuya duban ta ga k'annenta da suka zuba mata ido, ta ce "menene haka kamar zaku cinyeni, to ai banma hauba, bari nabaku labari, Faruq wai sona yakeyi".
nan tayi musu bayanin inda sukayi, hhh tsalle suka fara suna murna sunga kyakkyawan saurayi, "Aunty kada kitsaya jan aji don Allah yaha?u, kuma kinga Mahaifiyar shi tana sonki, me yarage miki, zakiyi ta haifan nyawawan yara".
murmushi tayi ta ce "shikenan tunda kuna so nima inaso na amince, amma sai ya k'ira nanda kwana biyu zan fa?a mishi, rungumeta sukayi su duka suna murna.
.
Kwana 4 amma har lokacin Abbah baya kulata, kota gaishe shi baya amsawa, idan taje karatu ma korata yake yi, kanta kuwa kullum acikin ciwo yake yi, saboda tsaban kukan datakeyi, awajen k'annan ta da Ammi ne take ?an samun sauki.
.
.
*Dare mahutar bawa*
Ammi ta zuba tagumi baccin ma yak'i zuwa mata, wannan shariyar da Abbah yake nunawa Aisha abun yana ta?a ta, tunda ya k'wace wayar sai ya hak'ura, dubanshi tayi taga baccin shi yake yi, mik'ewa tayi da niyyar barin ?akin taji ya rik'ota,
"Haba Amina, meyasa kike damun kanki, kinsan duk duniya nafi kowa son Aisha, idan nabarta zata lalace, baki ganin tafi k'annan nata sakarci".
Ammi ta ta?e baki ta ce "tun farko kajata a jiki yanzu ka ?ullo da wannan hukuncin
Kullum da kuka take wuni".
harcikin ranshi yaji kukan nata, ya ce "Daga yau nadaina fushin shikenan nima adaina fushi dani ko".
murmushi tayi ta ce "ko kaifa".
Saida suka kwanta yace "yaron daya ?auko ta a mota rannan ashe ?an gidan BUZAWA".
Da mamaki tace "ayyah rashin sani".
"jiya yazo mun da wani magana, wai Aisha yakeso da aure".
Ammi tayi dariya tace "Haba2, Aishar nawa take, ai yabari ta girma tukun".
"nima abunda na fa?a mishi kenan ya nuna mun nataimaka Mishi yanda zan rik'e Aisha haka zai rik'eta, ganin ya takuramun na amince mishi, nima zan huta da ?acin ran da take saka mini".
Tashi Ammi tayi rik'e da baki ta ce "?an wannan laifin har kana k'iranshi laifi, gaskiya kabarmun 'yata tayi karatu kafin".
"Amina har kin manta halin Aisha, duk ranar da zata fita sai ansamu wani ya biyo ta, yanzune da suke hutu samun kwanciyar hankalina, Auren nata shine gatan ta, kinga yaronnan bashida wani aibu donme zaki ?aga hankalin ki".
"To amma Alhaji masu biyotannan fa ba ita take k'iransu ba, su suke biyota".

Ya nisa yace "yanzu dai nagama magana aure zanmata, gobe zai kawo mahaifiyar sa su gaisa".
Ganin bata sake fuskaba yasa ya shiga rarrashin ta har ta sauko, "Allah yasa hakan yazamo alkairi".
Washegari da sassafe Ammi tace musu zasuyi bak'uwa, gaba ?aya suka hau murna don akwaisu da son bak'i saboda basu zuwa ko ina, daga gidan kakansu sai  makaranta, Aisha binsu kawai take da kallo inda suka zak'e, ita bataga abun murnaba, dama anguwa zasu tayi farknciki, ita sam batason mutane, idan ba tasan mutum ba bazakaji ta masa magana ba, saninma irin na sosai ?innan, danginsu gaba ?aya bata saba dasuba sai Maman Ammi.
"Aunty mungama girkin".
taji Hajara tana fa?a.
Ta ce "Yaran Ammi 'yan albarka me kuka dafa mata".
gabanta suka kawo suka dire, k'amshi kuwa ya cika wajen,
Jalop ?in Kuskus sukayi sai Chip na potatoes, sai drink kala biyu, da Sweet Runs.

"karfa kuce banyi aikin ba, wannan rawan kan naku kunji jiki, bakusan bak'uwar ba kun zak'e dayawa".
Sukayi dariya Sadiya ta ce "tunda kika ga Ammi tasan da zuwanta ta musammance".
Hajara ta ce "Ni damuwata musamu muyi mata rakiya idan tazo tafiya, kinga zamuga gari".
Duk suka tuntsire da dariya, Aisha ta ce "nikam bana fatan nasake zuwa ko ina ruwa ya tareni....
Hango Abbah sukayi ya nufo gunsu fuskarnan cike da fara'a, duk suka zuba ido suna tunanin meya kawoshi.
Hanun Aisha yazo ya rik'e, da dariyarshi yace "Mamana har yanzu ba'a huce ba ne? Ko ?an sake rannan yanzu bakiyi".
Ta sunkuyar dakai tana dariya, "komai ya wuce ai, na yafe miki".
Su Hajara suka hau tsallen murna, "Abbah mungode, dama ?azu tagama kuka wai yanzu baka kulata".
Tausayin ta ya kamashi ya kalle ta, idonta har sun ciko zata sake ?are baki yace "kukan me kuma, nadaina fushin kada kisake tsallake dokata kinji".
?aga mishi kai tayi, ya ce "muje Amminki tanason ganinki".
yana rik'e da hanunta suka nufi wajen Ammi.
Ammi tana hakimce suka shiga, ya ce "ga uwata ki mata fa?a, amma bance a ?ata mata raiba".
Ammi tayi dariya tace "nima uwatace nafika sonta".
Duk sukayi dariya kafin yace "Zanshiga ciki, bazan koma office ba nafiso yaronnan yasameni akwai maganarda zamuyi".
ta ce "To Abbahn yarana".
Yace "Abun naki harda son kaine, yaranmu zakice".
"to yaranmu".
"ko kefa".
Sukayi dariya ya fita.
.
Aisha tana kishinge?e ajikin Ammi, irin wannan wasan nasu yana bata mamaki don ita gani take sun girma amma sai suyi ta wasa.
"Aisha kinajina ko, nasanki da rashin hankali, wannan bak'uwar tanada matuk'ar muhimman ci a rayuwar ki, idan tazo kika share ta kamar yadda kika saba yi wa mutane zakiga yanda zanyi dake, ki sake jikin ki sosai kada tagane bakison mutane kinji ko".
Zun?ura baki tayi ta ce "Ammi wai ni me nakeyi na rashin hankali, kullum sai anmun fa?a".
dariya Ammi tayi ta ce "ke?inne ai, kije kiyi wanka yanzu ki shirya, kada kisa riga da zani kinsan baki iya ?aurawa ba".
kuka tasakarwa Ammi harda bubbuga k'afa "ga su Sadiya amma ba'a k'irasu ba saini.... Buge bakin Ammi tayi tace "zaki tashine ko saina sa?a miki".
da gudu ta tashi tana kuka.
su Hajara suna jiyota sukasa dariya, Sadiya ta ce "Aunty ya kamata kibarmun girmannan tunda dama nafiki tsayi da k'iba".
Hajara tace "da hankali".
ganin zasu ?ata mata rai yasa ta wuce tabarsu a wajen.
Ruwan wankan ta ha?a me ?an zafi tasaka turaren wanka aciki ta shiga, da?in ruwanne ya kashe mata jiki tayi zamanta har tana lumshe ido, AYS ne ya fa?o mata arai tasake lumshe ido tana tunanin yaushe zata sake ganin sunanshi, da zata samu taji muryan shi da taji da?i, da k'yar tayi wankan tafito ?aure da towel, hand drya ta ?auka ta tsane ruwan kanta dashi sannan tashafa mai da hoda ta ?an murza lips stik abakinta, "bak'uwar tanada muhimmanci agareni kuma, me Ammi take nufine, to hala wata 'yar uwa take mata, ba wani kwalliyar da zanyi gayyan sa ciwon kai".
sumbatun ta tagama ta ciro wani less riga da siket purple, sai zagayen fari ajiki tasha aiki, ?inkin yayi mata ?as daidai jikin ta, ganin ba iya ?aura ?ankwali tayi ba yasa ta ?auko k'aramin farin gyale ta yafa me goldin ajiki, tana cikin fesa turare taji hayaniyan su Hajara, "wa innan mahaukatan yanzu haka bak'uwar ne ta iso suke wannan ihun".
?an tsaki taja tayi waje itama.
Kusan shiga babban falon nasu taji taci karo da mutum, saura ka?an ta fa?i ta ?ago cike da masifa tayi tsammanin k'annen tane, mutumin data ganine yasata sandarewa awajen, UMAR FARUQ ne, yana sanye da shaddarsa rigar ?inkin half, tayi bala'in yimasa kyau, murmushi kawai yake zubawa dimples ?innan nasa suna lotsawa, hanu yasa ya rufe fuskan shi, "wannan kallon zakisa nazama mummuna".

Lek'ek'e ta farayi ganin babu kowa ta ce "me ya shigo dakai gidanmu, karufamun asiri ka tafi".
Nok'e kafa?a yayi ya ce "nima gidanmu ne, babu ruwanki dani".
Ka?a baki tayi
zatabar wajen yajawo mayafin ta, "kinyi kyau sosai, kamar nasace ki na gudu haka nakeji".
Murmusawa tayi ta ce "kaima kayi kyau".
Murmushi yayi yace "nagode".
D'akin Ammi ta nufa anan take jiwo hayaniya, Farar matace kyakkyawa kana ganinta kaga Faruq, tsayuwa tayi turus, ko ba'a fa?aba tasan mahaifiyar Faruk ne, ganin Ammi tanata watsa mata harara ne yasa ta k'arasa kusa da matar ta gaisheta, da fara'ar ta ta amsa, Ammi tace "yarana sun ha?u duka, saiki za?i naki aciki muga ko zaki gane ?iyar taki".
Momy tayi dariya ta ce "tun shigowar ta nagane ta, wannan tayi lukuta".
ta nuna Hajara ta nuna Sadiya ta ce "wannan tayi tsayi da yawa, amma ?iyata 'yar daidai ce, daban take".
Ta jawo Aysha ta ce "ko ba itace wannan ba".
gaba ?aya sukayi dariya, Ammi tace "kin canka".
Sadiya ne ta zun?ura baki tana mita wai su bata sonsu, Momy tayi dariya ta ce "kunga wannan ?auketa zanyi takoma wajena, dole na za?e ta".
Sai kuma suka fara mata gwalo.
Abincin da sukayi suka kawo mata, babu wani fulako tanaci tana santi, itadai Aisha duk ta takura kanta, matar nan ta jani da yawa.
"Tareda ?ana nake, ban muku bayani ba, Aysha taimaka kije kada yaga na da?e".
Ammi ta ce "ah ah kitafi mishi da abinci".
.
Su Sadiya ma duk mik'ewa sukayi suka bi bayan Aisha, suna daf da shiga falon Aisha ta ce "A'ina Ammi ta samo mutanennan, ?an natafa wanda ya?auko ni a motane ranarda ruwa yamun duka".
kama baki sukayi Sadiya tace "dama yasan gidannan kenan".
Hajara ta ce "koma yane idan sun tafi Ammi zata mana bayani".
Da sallama suka shiga, ?an ?agowa yayi ya amsa amma k'asa2, duk hankalin shi yana kan Aisha yabita da kallo ko kyafta ido bayayi, yayi missing ?in fuskarta sosai,  su Hajara kuwa hankalin su yana kan shi ganin yanda yabi Auntyn su da kallo kamar zai ha?iye ta, ita ?inma duk kunya ta kamata aranta tace "me mutuminnan yake nufi ne".
Gaishe shi sukayi suka bar wajen, lokaci ka?an Hajara ta dawo mishi da kayan abinci, Aysha ta mik'e zata bita yayi saurin taka k'afarta, 'yar k'ara ta saki yayi yayi saurin ?agawa, lokacin har Hajara ta fita, ya tsuguna wai yana hura mata k'afar, dariya ya bata don ita ba zafin da taji rakine kawai, amma ta k'unshe dariyar, zama yayi a kujerar da yake fuskan tarta, yak'ira sunanta a hankali, ?agowa tayi ta zuba masa ido, ya ce "kinga mahaifiya ta ko"?
Ta ?aga masa kai kawai, ya ce "tana sonki sosai, don ke tazo gidannan".
Zaro ido tayi, yace "eh, tun ranar da ruwa ya miki duka kika tafi da imani na, nasan idan narantse miki ko baccin kirki banayi ba tare da tunanin ki ba bazanyi kaffara ba, ban ta?a so ba, kada ki watsamun k'asa a ido, nayiwa Mahaifin ki magana kuma ya bami ke".
Binshi kawai takeyi da kallo har yagama, jin maganan shi na k'arshe ne ya jefata a damuwa, tunanin ta ?aya idan tayi aure shikenan bazataga Ays ba, fashewa tayi da kuka da iya k'arfin ta, hankalin shi in yayi dubu ya tashi, "don Allah kiyi shiru baki sona ko?
Bazan miki dole ba kiyi tunani, amma wallahi idan baki amince ba akwai matsala, ki tausayamun Aisha".
har k'asa ya suguna mata, sai a lokacin ta rage kukan, yace "Baki sona ko".
Ta girgiza kanta, "to meyasa kike kuka".
Nanma girgiza kanta tayi, ya ka?a kai yace "bani wayarki nasa miki numbata, idan kinyi tunani duk hukuncin da kika yanke ki fa?amun".
A hankali ta ce "banida waya".
Shiru yayi can ya ciro ?ayar wayarshi ya mik'a mata " Ki rik'e wannan zan k'iraki nanda kwana biyu".
har tasa hanu zata kar?a ta tuna Abbahn ta, ta ce "kabarshi kawai, Abbah na yahanani rik'e waya".
Da?i yaji aranshi wannan ma wani tsaro ne, ya ce "ki kar?a, zanyi wa Abbah bayani, bazai hanaki ba".
Hanu biyu tasa hanu ta kar?a, da zolaya ta ce "bafa aro ba, kyauta".
Yayi dariya ya ce "zan iya baki kyautar kaina balle waya".
Murmushi tayi tace "nagode". Zuciyarta fal farinciki tayi ?akinsu Hajara da gudu, tun kafin su san me takeyiwa dariya suka hau tayata ('yan abi yarima asha ki?a).
wayar ta mik'a musu, me tsadan gaskene sosai, Hajara ne ta ?ata rai ta ce "kinsan Abbah ya hana ko".
"to 'yar bak'inciki sai kitsaya kiji bayani, nasan wannan kallon da biyu, nafi matsuwa naji me yakawo su gidannan".
Sadiya ta fa?a tana gyara zama, dungurin ta Aysha tayi ta ce "ke tsaya nahau Fcbk sai nabaku labari".
Sake baki sukayi suna kallon ta suka kasa magana, tsawon lokaci Hajara ta ce "Aunty anya ba asiri aka miki acikin fcbk ?innan ba kuwa, daga baki waya...
Sadiya ta katseta, "tayani wannan tunanin, kuma babu abunda takeyi aciki dazai amfaneta sai kallon sunan wannan ?an Aljanin".
Itadai batace musu komai ba tahaura abunta, sak'onnin nasa ta duba duk sallama ne yafi goma, ?ata rai tayi aranta ta ce "baimayi kewata ba yaronnan".
amsa mai sallamar tayi kafin ta sauk'a.
tajuya duban ta ga k'annenta da suka zuba mata ido, ta ce "menene haka kamar zaku cinyeni, to ai banma hauba, bari nabaku labari, Faruq wai sona yakeyi".
nan tayi musu bayanin inda sukayi, hhh tsalle suka fara suna murna sunga kyakkyawan saurayi, "Aunty kada kitsaya jan aji don Allah yaha?u, kuma kinga Mahaifiyar shi tana sonki, me yarage miki, zakiyi ta haifan nyawawan yara".
murmushi tayi ta ce "shikenan tunda kuna so nima inaso na amince, amma sai ya k'ira nanda kwana biyu zan fa?a mishi, rungumeta sukayi su duka suna murna.
???

0 comments:

Post a Comment