PHERTY PART 1-5
.
Tafiya take ah hankali kamar kwaii ya fashe mata a ciki ga ruwan saman da ake ta shek`awa kamar da bakin kwarya amman bay hanata tafiyarta cikin kwanciyar hankali ba da ka ganta kasan natsatsiya ce akwaii natsuwa a tare da ita jikinta duk ya jik`e kayan makaranta ne ajikinta ( uniform ) da gani na islamiyya ne doguwar riga ce ah jikinta ta yadi maiy ruwan kasa (brown) da farar abaya kayan duk sunbi jikinta wannan ne yasa nagano yanayin jikinta Doguwa ce maiy matsagaicin tsayi bata da jiki kuma baxa'a kirata rammamiya ba farace kuma ba fara sal ba tana da dogon hanci kamar al'k`alamin rubutuna bakinta dan matsa gaici lab`enta na kasa jajir yake gata da idanuwa masu kyau baxa kayi mata kallo daya ba kace baxa ka sake ba duk wanda ya kalleta so daya sai ya kara juyawa dan Allah yayi mata kyau wanda sai ka kureta kake gane hakan (k`ananan kyau kenan) Ta juya ta kalli titi taga babu kowa ba machine babu keke napep yau taci burin ko xata mutu sai tahau machine duk da gdnsu an hanasu hawan machine ko keke napep tunda driver ke kaisu duk inda xasu je yau kuma baixo daukarta ba gashi duk ta gama jik`ewa da ruwan sama dan danan ranka ya baci har fuskarta ta nuna idanuwanta sukayi jah ta sake juyawa gabas da yamma amman ba alamar abin hawa sai ga hawaye sharrr ta fara kuka kamar wacce akayi ma mutuwa Babu abinda take tunani sai nisan gidansu kawaii saita sulale ta xauna gefen titin ta bude jakkar islamiyyarta ta ciwo wayarta tana latsawa kawaii sai taga ba charge kafin tayi wani yunk`uri wayar ta dauke diiff charge ya kare wani irin takaici taji ya rufeta kamar ta hadiye xuciyar ta taita kuka kan titi ta saka kanta cikin cinyoyinta tanata kuka can taji hon din mota ah gabanta da sauri ta daugo kanta tana kallon wanda ke cikin motar Yana xaune a cikin mota amman da ganinsa kaga dogon mutum choculate colour gashi da sexy eyes idanuwansa ah waje suke kamar ya xaro su gashi da dogon hanci har baka gashin idanuwan sah gaxar-gaxar fuskarsah tasha gyaran fuska bakinsan dan karami sumarsah kwance luf akasan kamar wani black american fitowa yayi daga motar anan ne naga tsayinsah dogo ne sosai yana da k`ark`ar fan jiki kuma bai da k`iba kirjinsah ah bude yake kamar namijin xaki black jeans ne ah jikinsah da red shirt ya saka takalmi black cover shoe yana xuwa gab da ita ya fara murmushi wanda yasa kefen kumatun shi dukka biyu lotsawa (dimple's) .
.
Tana d`ago kaii ta kalleshi ta sake daure fuska tare da bashi baya cike da shagwaba cikin dariya yace sowrie baby kiyi mana uxiri plx mama ce fa ta aiki driver ni kuma kinsan ina office kuma nayita kiran wayarki a kashe yanxu haka daga islamiyyarku nake tunda ya fara maganar bai tsaya ya numfasa ba sai yanxu Shiru tayi tak`i kulashi bare ta bashi amsa ya dad`e tsaye kuma yasan halinta in xai shekara a gun baxata kulashi ba daman can miskila ce kamar shi barema tana fushi dashi yasan baxata taba kulashi ba hakan baisa yaji haushi ba saboda yasan halin yan kayanshi dole ya duk`usa ta gefen da ta juyar da kanta ya tallabi habbarta tare da cewa sowrie PHERTY! Kema kinsan babu yarda xa'ayi ah barki ah makaranta inma kinyi fushi dani to da gan-gan tunda kinsan bani ke xuwa daukar ki ba in kinga dama ki taso muje in bakiga dama ba kuma sai kiyita xama yana kaiwa nan ya mik`e ya nufi motarshi Tana kallonshi taga har ya shiga mota yana kokarin tafi aii da gudu ta kwashi takalmanta da jakarta ah hannu ta shige motar tanata haki tana shiga ta fara shan kamshi ta gefen ido ya kalleta yayi wani munafukin murmushi ah ransah yace a banxa bayan kin gama kwasa gudu gabana xakiyita min wasu yan harare-harare har suka isa gidan bai kulata ba itama haka ita ah dole fushi take da shi A motar ya barta yayi shigewar shi part din yayanta HAKEEM yana shiga ya same shi xaune yana kallon wani indian film your are family film ya dauko dadi yaji maganar abokin nashi da sauri ya mika mashi hannu tare da cewa ABDOOL DAN KWALISAH wanda aka kira da abdool yayi dariya mai k`ayatarwa Tare da cewa hakeem ya kuka baro pherty makaranta duk ruwa da bugeta hakeem yace wai bata dawo bane yace ta dawo yanxu na daukota lokacin dana shigo kana barci mama tacemin in dauko kasan mutuniyar batasan abin arxiki ba sai shegen miskilanci taki mgn har na tashi na shiga mota sai gata ah tsiyacee hakeem ya kwashe da dariya yace da kabarta miskilancin ya kawota gida aii inda nine wllh tafiyata xanyi yace ai da yakema cewa kayi inda kaine to bakai bane .
.
Tana ganin ya fita tayi k`wafa tare da fita tabar motar ah bude tayi cikin gida d`akinta ta nufa kaii tsaye tana shiga tayi wanka tare da saka wata doguwar riga marar nauyi dardumar sallah ta shiffid'a ta dauko xureran hijab sallah ta kabbara tayi magrib tana gamawa ta fara karatun alqur'ani tana nan xaune har aka fara kiran sallar isha'i tana gamawa tayi shafa'i da wutiri tana tashi tayi falo bataga kowa ba kuma bata nemi kowa ba ita ah dole fushi takeyi da mutanen gidan hanyar fita ta nufa Tana kaiwa kofar falon xata fita taci karo da yayanta kallo daya tayi maii ta rab`a gefen shi xata wucce ya rikota tare da cewa qanwas nima fushin akeyi dani shiru tayi ya saki hannunta tare da cewa inma kinyi fushi dani ke kika sow tunda kinsan ko da wasa ban taba kaiki makaranta ba bare daukoki bata ce mashi komaii ba har ya gama maganar shi sannan tace to bani hanya in wucce in kagama shiru ya mata kuma yaki bata hanyar sunanan tsaye sai ga abdool ko inda take bai kallah ba ya mik`ama hakeem hannu suka gaisa ya wucce cikin falon daki mama ya nufa kaii tsaye sai tym din hakeem ya bata hanya ta wucce
.
Tana fita gidansu abdool ta nufa da sallamarta ta shiga gidan a falo ta samesu durk`usawa tayi har kasa tace dady barka da dare yace mata kin yini lafiya "yata" tace lafiya qlau ta juya tace momy ina yini momy tace takwara duk yau bamu ganki ba halan laifi mukayi murmushi tayi kasa-kasa tare da cewa momy ummie na daki ne tace eh dakin ta nufa tana shiga ta had`e raii ta had'e girar sama da ta k`asa ummie na kallonta xatayi magana ta rigata tace da kika taho kika barni ruwan bai kasheni ba kuma ban rasa wanda zai daukoni ba harara ummie ta bita da ita tare da cewa Aii naso ruwan ya kashe ki kuma ki rasa mai dauko ki tunda da akaxo daukata ban miki magana ba kikace baxaki bini ba inama amfani kedaii wllh mijinki ya shiga ukku da k`orafin ki da shegiyar mita mtsww inama amfani wannan abun irin ku ne kullum sai kunyi fada da miji kin canxa hali dan wllh yah abdool bai sown yawan nanata magana kullum complain yake dake ina ga anyi auren pherty batace komai ba har sai da ummie ta gama masifarta tukuna tace to sannu mama aii da tashi kikayi kika bugeni sai fadan naki yafi shigata koda yake ba laifin ki bane ni na sow daga ke yar yah abdool din fuska na baku shiyasa duk maganar da taxo bakinku kuke gayamin Tana kaiwa nan tayi gaba abinta koda ta fita falo bata tarar da kowa ba ah gun fita ne taci karo da yah abdool ta wani bala'in dauke kaii tare da gugar kafad`ar shi xata wucce da sauri ya fisgota ta fado kan kirjinshi yayi mata kyakyawan ruk`o itako sai mistilniya take yace haba mami (sunan da yake kiranta dashi kenan cos sunan momynshi ne da ita) meya faru ne kiketa faman fushi tace nidaii sakarni xaka wani rungumeni kamar wata "diyarka" ko matar ka yace aii kedin matata ce ko kin manta yah abdool i realy luv u so much irin maganarta yayi cike da tsokana tace yah abdool i realy hate uu da sauri ya daugota yace karya kike ta gantsara mashi cizo ah kirji tare da muguda baki tace kace ka fasa aurena dan nima ban sown miji mai yawan kawo complain dina gidansu tana kaiwa nan tayi wajen abinta ta barshi tsaye cike da mamaki.
.
Harta fita get din gidan bai dena kallonta ba metake nufi da complain wato ummie tayi Mata wata magana kenan tunda gashi har ta ambaci baxata auri mai yawan kawo k`arar ta ba shakka babu sunyi fada da ummie harta fada mata hakan Dakin Ummie ya nufa kanshi tsaye da shigarsa ya fara tambayarta ke mekika fadama maminah cike da nuna halin ko in kula tace metace nace mata wata tsawa ya daka mata tare da cewa keni sa'anki ne ina miki mgn kinamin fusge-fusge answer mee fuskarta a daure ta fada mashi yarda sukayi yace to wannan ya xama na karshe daga yau wani abu ya sake hadaki da ita ku sakoni cikin shirmenku inbada munafunci da hadin bala'i miye nace mata kullum ina complain da ita yaushe nayi dake ? Yaushe na xauna dake nagaya miki hakan shiru tayi tare dayin kasa da kanta amman ta k`udurama ranta sai sunyi fada da pherty sai dai in kasheta yah abdool xaiyi ya kasheta. Tana fita gidansu ta wucce mama na xaune a falo har ta kusa shiga dakin ta mama tace phertymerh xo man dawowa tayi tare da xama gefen k`afar mama tace kinci abinci kuwa tace uhm mama tace kiban amsa eh ko a'a tace eh naci ta fada tana wani cika tana batsewa ita a dole fushi take rankwasar Mata kai mama tayi tare da cewa kedai kin bani da bakin hali wllh kin wani bi kin chanxa hali tana kaiwa nan ta tashi ta barta gun aii kamar jira takeyi ta mik`e kawaii saita saka kuka tare da ihu waii ita an tsaneta dan anga abbanta bainan an matsa mata kamar ba'a kaunarta tana cikin kukan abdool ya shigo yanayi sallamah ya ganta tsugune tana kuka yace ohhh mami kin cika rigima matsawa yayi kusa da ita tare da rik`o kafad`arta jikinshi tare da cewa sowrie sweet sis meyasa kin cika rigima ne kuma waye yace miki ba'a sownki ana kaunarki ko abban yaga abinda kikeyi xai miki fada kwata-kwata kin sake hali ne ga wani fushin banxa da kika gane maras amfani ya kamata ki sawa xuciyarki salama duk kin wani harmitsa kanki kin sakama ranki damuwa da k`orafi komai Na magana ne gunki wai meke damunki ne?.
.
Gyara kwanciyarta tayi akan k`irjin shi yace kiyi hak`uri ki dena halin nan plx tace uhum uhum yace why Tace to yo bakai bane naganka makaranta daxu da wasu yammata yace tofa dawa kuma kika ganni? tace halimcy mana yace wacce halimcy kuma tace kafi ni sani yace kamar ya? tace kamar yarda kaji tana gama fadar haka ta tashi d`akin ta ta nufa ta barshi nan xaune yana kallonta tare da murmushi a fuskarshi yace mami uwar kishi Yana gama fadar haka ya tashi part din hakeem ya nufa tare da wak`a abakinshi yana cewa (pherty pherty ina kira kiyo amsawa sanadin kaunarki ne take sani tsuma pherty) hakeem yayi dariya harda durk`u shewa kasa sbd dariya dan danan abdool yasha murr yace miye haka .
.
Kakemin dariya kamar kaga wani xararre cikin dariya hakeem yace yo kaima dai dan kwalisah naga kamar ka xaren ne kawaii karamar yarinya ta birkita ka duk ka wani xama kamar xararren duk kwalisar nan babu ita tsoki abdool yayi mai tsayi mtsswww aikai naga ummie aysha ba xararra da kai tayi ba hakeem ya daure fuska Yace aiidai kasan ummienah tafi maminka hankali wata harara abdool ya xabga mashi tare da cewa a hakan hakeem yayi murmushi yace eyeee ashe har irin harararta ta koya ma abdool yace saima kaga na rikid`e na xama phertyn Hakeem yace lallaikam da bakayi dace ba cikin bacin rai abdool yace hakeem yafa isheka wllh dan raina ya sake baci har dakuwa xamu iyayi dakai Hakeem ya saki baki galala yana kallonshi yace akan phertyn yace kwaraii in kuma kanajin wasa mu xuba kawaii sai ka xauna kayita kushemin mata to wllh xamu iya raba hanya dakai akanta yana gama fadar haka ya fita fuuuu hakeem yabi bayanshi da kallo tare da cewa ba shakka.
.
SHIN WAII WACECE WANNAN PHERTYN KU BIYONI DOMIN JIN WACECE QAWAR NAN TAWA
Thursday, 1 February 2018
Home »
PHERTY 1-END
» PHERTY PART 1-5
0 comments:
Post a Comment