== RAYUWAR NIHILA 1 ==
Nihila!!! Nihila!! Nihila!! Tana bacci taji mominta na kwala mata kira ta tashi jiki duk a mace ta amsa da naaam ina zuwa momi ta fita zuwa parlor wurin mommy ai dama aikin kenan baccin asara in bashi ba ba abunda kika sa a gaba ke kullun kenan aikinki bacci wuce kije ki daura dinner daddyn ku na dawowa tana magana a shagwabe tace momy bakya sani naji dadi tace au kaji mun yarinya daga cewa ki daura girki in baki daura ba uwar me zakiyi me amfanin mace ba girki wuce dalla tun kan nayi koli koli dake ta shige kitchen ta fara aiki gadan gadan spaghetti ta daura wanda yaji ganye da vegs ko ina ya dau kamshi bayan ta gama taje ta shiga wanka ta fito tayi sallah ta idar kenan taji wayanta na Kara tana dubawa taga Wanda tayi zaton ne kuwa.
.
Ta dau tana murmushi tace hello on the other side kuwa yace ran gimbiya ya dade tace tare da naka hayati ana ka wuni lafiya yace lafiya kalau sai missing dinki da nake tayi dats y nace barin kira tace nima ai kasan nayi yace to godia nake sweetheart a kullun dada kara sonki nake u have completely changed my life saina kiraki anjima tace toh babe tare da kashe wayan. Tunani fal a ranta akan hisham ganin in mamanta ta gane suna waya dashi zata shiga babbar matsala Dan ko tace bata yarda ba Allah be yarda ba.
.
Nihila Muhammad yarinya ce yar kimanin shekara 16 tanada chocolate complexion mai kyau wanda yaji madara idan ka ganta kaman black americans tanada kyau masha Allah ga dara daran idanu Allah ya mata lips pink masu kiran heart wanda sukayi daidai da fiskanta tanada shape wanda yayi fitting dinta daidai ba'ace bata dashi ba komai dai nata daidai yake batada makusa 'yace a wurin Muhammad Tahir Wanda Allah ya wadata da arziki masha Allah suna zaune a abuja a unguwar garki itace last born a gidan su tanada sisters biyu sausan da bahijja to kunsan dama ance Allah mai hadi jininta bai taba haduwa da sausan ba hasali ma itace silar shiganta matsaloli da dama duk da tana blood sister dinta kaman step sisters suke amma suna shiri sosai da bahijja wanda itace secret keeper dinta dan kuwa nihila tana rufa mata asiri sosai in tayi wasu abubuwan...
.
Ta hadu da hisham ne a social media wanda Allah ya hada jininsu daga frndship suka dawo soyayya shi kuwa a gombe yake da zama amma yana cyprus yana karatu watansu 8 da haduwa ko taba ganin juna basuyi ba amma in suna waya zakace Sun yi shekaru da sanin Juna.. sausan tasan da wannan maganan sabida haka ta gulmatawa momin su ita kuwa momin su tace allanfir bata yarda da wannan soyayyar ba mutumin da ko taba ganin shi batayi ba kuma suna nisan duniya tayi kuka sosai dan kuwa tana son hisham irin mazan nan masu shiga rai hes so caring n loving Dan haka ta biyema zuciyanta suka cigaba da waya.
.
Dan safe ta shirya tsaf abun ta ta tafi school kasancewar yau ranan Monday bta gaji da weekends ba da jimawa ba zasu fara zana paper gama ss3 tana ta dokin ganin frnd dinta habibaty tana zuwa ta rungumeta tace kai qawata nayi missing dinki tace nima haka ana haka sai ga jawad seat mate dinta kuma abokin shawaranta sun saba sosai dan kuwa tun suna jss 1 ajinsu daya jawad yana da hankali ga kuma tarbiyya saidai yana fiskantan matsaloli dayawa a gidansu irin na jarrabawar ubangiji Ga wanda yaso yace ooh kudai ba'a rabaku Kaman en biyu tace to ya zamuyi gamon jini.. daga bisani suka tafi assembly.
.
A break me take ba Wa jawad da habiba labarin yanda sukayi da mominta akan hisham sun dai bata shawarwari akan tabi abunda mahaifiyarta tace saidai inaaa tayi nisa batajin kira.. ( umm nima nace mata if u know wats good for u, u will listen to your mother) ..
.
Amma jawad yace mata ya kamata tayi bincike akan hisham dinnan tunda ba taba ganin shi tayi ba kuma garin su ba dayaba hasalima yana wata uwaduniya Itama haka.. Kwanci tashi asarar me rai Sun fara shirye shiryen sana paper dinsu na waec da neco suna ta faman karatu Dan kuwa sunada hazaka da son karamun.. Wani yammacin la'asar ta dawo daga makaranta tilis ta gaji sabida paper da suka rubuta a ranan saita gamu da bahijja a parlour tana ganinta ta fara washe baki tana ta sosa keya in ka ga bahijja tana haka to akwai wata er abunda ta hada da kawayenta tace sister na ya gajiya gaskia kin kwaso rana tawan..
.
wallahi akwai wata er barbeque din da frnds dina suka hada shine nakeso ki rufamun muje zan ce zamu je gaida kawata batada lafiya nace ummm beejay kenan hali baya canjawa tace ahh haba ke kuwa just do this for me once abu na lokaci guda rana daya aina me gayya ne in baki rufamun ba wa zaiyi nace to shikenan suka tambaya momi tace su je su dawo da wuri karsu kai maghrib suka fita sai beejay ke cema nihila to ke ba inda kikeso kije in yaso na ajiyeki inna dawo saina daukeki nace mata aa nikam ba inda zani muje kawai muna isa taje ashe ta taho da wasu kayan iskancin ta taje ta canja ta sa riga da wando. .
Ya muje zuwa ne?
Sunday, 21 January 2018
Home »
RAYUWAR NIHILA 1-END
» RAYUWAR NIHILA 1
0 comments:
Post a Comment