Blogroll

BANNER 728X90

Wednesday, 17 January 2018

SANADIN SELFIE Part 7 to END

===== SANADIN SELFIE 007 =====
Abbas be zame ko ina ba sai guest house nasa inda shaidanun yammatan sa suke
Jagwab ya fada kan kujerar dake falon wata matashiyar budurwa ce ta taho da daauri lapiya kuwa darling naganka haka me yasa me ka
Daga mata hannu yai yace I need rest pls ya tashi ya bar mata wajen dakin sa ya nufa Yana tunanin wannan kuma wane tare da masoyiyar sa me tsakanin su wacce alaka ce da hada su
Koma mene zan yi bincike haka ya kwanta yana sakawa.da kwance war yanda zai billowa lamarin  Wannan Ke nan Ita kuwa Naureen wani farin ciki ne ya lullubeta tun jin yanda take d Sameer din ta
Cikin sauri ta kira Aunty Najma hello sweet sis mene kuma bayan ko ma ki dan zo sabida.su Abee sun dawo an mata damu a'a zan zo ne sisi yanxu ma wani labari zan fada miki
Allah ko eh mana albishirin ki goro fari tas kin san me a'a sai kin fada hmm zaki yi mamaki in kin Ji abinda zan fada miki  Ke ni in zaki fada ki fada kin wani tsaya kina jama mutane rai
Aunty Ashe my Sameer yayan su mas'uda ne ban sani ba Ke me kike so Kice min ya Sameer shine Sameer din da yake sona Da gaske kike ko kuwa haba aunty kin san dai bazan hada wannan zance ba wllh shine
To amma ya akai baki gane shi ba ko nace baku gane juna ba oho haka ma mameen sa tace tab To sai ki fara shirin rabuwa dashi najma ta fada gaban Naureen ne ya fadi me kike nufi aunty ta tambaya cikin kidimewa
Sai da tai dariya me Isar ta sannan tace au har kin mata Ke nan aunty wai menene ki fadan wllh hankali na a tashe yake Sai ki rabu da shi tunda kince bazaki auran zumunci ba kai aunty bame raba ni da Sameer sai Allah
Shine fa partner life dina fa in babu shi babu ni ah lallai kanwata kinyi nisa Allah ya san ya alkhaeri Ameen aunty Wallh da har kin rudani ina my baby tayi bacci yaushe zaki zo najma ta tambaya zan zo ne aunty ki gaida ya suhal zai Ji sannan zan fada masa wannan abin alkaerin kai aunty ni ban ce ki yaya tani ba sai da safe
Washe gari sai gidan hajiya kaka in da ta tarar da dadyn su Asif da Abee sai kuma hajiya hadiza sannan kuma Baffa aminu 'yayanta ne dai kadan ne babu a cikin su
Da ka gani ana ganawar sirri daya dakin na shiga ya Asif na gani ah yaya na yawwa daman yanxu nake kokarin zuwa na taya ki murna me ya faru ta tambaya cikin rashin fahimmata
Dazu Sameer ya van wani labari me dadin gaske amma naji dadi Allah ya inganta kai ya Asif bazaki cw amin ba rufe fuska tagi cikin jin kunya  Baki ga ana assembly ba a ina su hajiya kaka mana dariya suka kwashe gaba daya sannan suka fara hirar su ta zzumunci
To ya Asif kai kuma wace sarauniyar taka hmm zamuyi maganar amma ba yanxu ba na dauka tare zaku tawo da Sameer shima yace zai zo Ah nidai gaskiya yau ban son kowa yazo sabida zamu gana da hajiya kaka ganawar sirri sai yau bayan kin yi fushi da ita ae ta huce tuntuni
Su dady ne suka fito au Kaga yar tawa anan yaushe kika shigo na dan dade Gaishe su nayi cikin kunya munji abin alkhaeri Allah ya kuma hada kan ku Ameen na fada a kunya ce
Suka fita ni kuma na shiga dakin hajiya kaka mamee ce Ke kokarin fito wa nan ta fara tsokanata kamar ba wadda nake shirin zama sutukar ta ba
Na shige dakin hajiya kaka...............
.
Kuyi mana bayani mamee ita ce,ita wa Sosa Ke yarsa yai salma danake baki labari oh gaskiya anji kunya yanxu yar uwar taka ce baka gane ba har kuka fara soyayya gaskiya kun ban mamaki
Kuma noke kanta tai a jikin mamee ni dagani marasa zumunci kawai cikin mamaki mas'uda ta karaso wajen ta sis shine wanda kike ban labarin sa Da gudu tai dakin mamee cikin jin kunya aka bar mamae da su mas'uda suna mamaki wanna lamarin
To ya Sameer ya akai baka gane ta ba ban sani ba, ya bi bayan salma dakin mamee tana ganin sa ta cusa kanta cikin pillow zama yai kusa da ita au yau kuma kunya ta ake Ji kada masa kai tai alamr a'a to tashi ki fadan ya akai baki gane ni ba
Lallai ma ya Sameer ae kai ya kamata ka fara gane ni tunda ka.....ah ba wani nan Ashe Ke yar uwata ban sani ba kike wahalar dani gaskiya naki dadi kayana sun tsinke a bakin kaba dariya tayi cikin jin dadi haka suka ci gaba da hiran su a dakin mame ba kunya
Uhmmm mamee kin ga ikon Allah ko,saleem ya fada Allah ya hada su batare da sun sa yan uwa bane kuma da cewa akai za'a hada su ba zasu yarda ba
Gaskiya naki dadin wanan lamarin daman tun sanda yazo min da zance nace ina ma a cikin yan uwan sa ya gano Sai yamma lis sannan ta shirya zata tafi cikin jin kunyar mame ta fito zan tafi mamee au yau kuma aka fara jin kunya ta hmm yayi kyau sai na zo wajen Abee din kamin sannan zani gidan hajiya kaka naji dadi wannan hadin naku Allah ya tabbatar rufe fuska tai da hannu tana dariya suka fita mas'uda da Yasmin suna tsokanar ta
Sai da Sameer ya fito sannan suka saurara suka koma cikin gida shi kuma ya daukko suka kama hanyar tafiya gidan su,Naureen Na'am yaya ah ban yarda ba ba wani yaya ki cigaba da fadan sanan da kika saba uhmmm kinga yanxu komai ya zo a sauki sai kawai a fara maganar auran mu haka sukai ta hirar su har ya kaita gida
Ko mu biya gidan hajiya kaka yanxu mu juya a'a ka bari gobe ma hadu a can Tom ki gaishe su au baza ka shigo ba, da akawai inda zani ni dai gaskiya sai ka shiga ta fada a shagwabe to muje ya fada yana kwaikwayon muryar ta dariya suka sa gaba daya wannan Ke nan
Shi kuwa Abbas tun lokacin da ya dawo nigeria ya fara binciken ina zae gano ta haka ya baza komar sa dayake dan har kalla ne cikin Sati daya ya gano wace ita da kuma unguwar da take da zama
Parking yai da ja gefen gidan su Naureen daidai lokacin da su dawo ita da Sameer tun da suka tawo ya kafa musu ido har aka bude musu gate be dauke idon sa daga kan su ba
Wani kishi ne ya lullube shi ganin irin niahadin da suke da wanda suke tare wanda ya kamata ace da shi suke a nasa tunanin fa readers kuji karfin hali ??
Cikin bacin rai ya figi motar sa yai gidan susu Abbabs shima dan aslin garin kano ne wanda yake business a kasashe daban daban yaro ne me tashe da kudi wanda yammata Ke rububin sa Abbas cikakken mayaudari ne ajin farko wanda in dai ya ga mace tayi masa sai ya san yanda akai yaja hankalin ta
Gashi yanada boyayyen hali wanda ba kowa ya san.shi da shi ba Uhmm ko zai masu nasara akan Naureen kuwa ? Kuma wane hali yake da shi haka ? Ku biyo ni dan Ji wannan amsoshin............
.
Abbas be zame ko ina ba sai guest house nasa inda shaidanun yammatan sa suke Jagwab ya fada kan kujerar dake falon wata matashiyar budurwa ce ta taho da daauri lapiya kuwa darling naganka haka me yasa me ka
Daga mata hannu yai yace I need rest pls ya tashi ya bar mata wajen dakin sa ya nufa Yana tunanin wannan kuma wane tare da masoyiyar sa me tsakanin su wacce alaka ce da hada su
Koma mene zan yi bincike haka ya kwanta yana sakawa.da kwance war yanda zai billowa lamarin Wannan Ke nan Ita kuwa Naureen wani farin ciki ne ya lullubeta tun jin yanda take d Sameer din ta
Cikin sauri ta kira Aunty Najma hello sweet sis mene kuma bayan ko ma ki dan zo sabida.su Abee sun dawo an mata damu a'a zan zo ne sisi yanxu ma wani labari zan fada miki
Allah ko eh mana albishirin ki goro fari tas kin san me a'a sai kin fada hmm zaki yi mamaki in kin Ji abinda zan fada miki Ke ni in zaki fada ki fada kin wani tsaya kina jama mutane rai  Aunty Ashe my Sameer yayan su mas'uda ne ban sani ba Ke me kike so Kice min ya Sameer shine Sameer din da yake sona
Da gaske kike ko kuwa haba aunty kin san dai bazan hada wannan zance ba wllh shineTo amma ya akai baki gane shi ba ko nace baku gane juna ba oho haka ma mameen sa tace tab
To sai ki fara shirin rabuwa dashi najma ta fada gaban Naureen ne ya fadi me kike nufi aunty ta tambaya cikin kidimewa Sai da tai dariya me Isar ta sannan tace au har kin mata Ke nan aunty wai menene ki fadan wllh hankali na a tashe yake
Sai ki rabu da shi tunda kince bazaki auran zumunci ba kai aunty bame raba ni da Sameer sai Allah  Shine fa partner life dina fa in babu shi babu ni ah lallai kanwata kinyi nisa Allah ya san ya alkhaeri Ameen aunty
Wallh da har kin rudani ina my baby tayi bacci yaushe zaki zo najma ta tambaya zan zo ne aunty ki gaida ya suhal zai Ji sannan zan fada masa wannan abin alkaerin kai aunty ni ban ce ki yaya tani ba sai da safe
Washe gari sai gidan hajiya kaka in da ta tarar da dadyn su Asif da Abee sai kuma hajiya hadiza sannan kuma Baffa aminu 'yayanta ne dai kadan ne babu a cikin su
Da ka gani ana ganawar sirri daya dakin na shiga ya Asif na gani ah yaya na yawwa daman yanxu nake kokarin zuwa na taya ki murna me ya faru ta tambaya cikin rashin fahimmata
Dazu Sameer ya van wani labari me dadin gaske amma naji dadi Allah ya inganta kai ya Asif bazaki cw amin ba rufe fuska tagi cikin jin kunya Baki ga ana assembly ba a ina su hajiya kaka mana dariya suka kwashe gaba daya sannan suka fara hirar su ta zzumunci
To ya Asif kai kuma wace sarauniyar taka hmm zamuyi maganar amma ba yanxu ba na dauka tare zaku tawo da Sameer shima yace zai zo Ah nidai gaskiya yau ban son kowa yazo sabida zamu gana da hajiya kaka ganawar sirri sai yau bayan kin yi fushi da ita ae ta huce tuntuni
Su dady ne suka fito au Kaga yar tawa anan yaushe kika shigo na dan dade Gaishe su nayi cikin kunya munji abin alkhaeri Allah ya kuma hada kan ku Ameen na fada a kunya ce
Suka fita ni kuma na shiga dakin hajiya kaka mamee ce Ke kokarin fito wa nan ta fara tsokanata kamar ba wadda nake shirin zama sutukar ta ba Na shige dakin hajiya kaka...............
.
Hajiya ta nayi missing naku wllh Ke tafi nan bayan fushi kike dani badan iyayen ki sun zomin da labari me dadi da ba abinda zai sa na kula ki haba my kakas kin san bama haka da Ke
Nan muka cigaba da hira har Sameer ya karaso kai wannan zuwan na hadin baki ne sai da Kaga ta zo shine zaka biyota ka hana mu hira hajiya kaka ta fada
Aa hajiya ni ban ma san tazo ba ah yaran nan wai wayo kuka fimu ko me wannan plan din naku yayi Suka sa dariya nan tasa musu albarka Abbas kuwa sai da ya binciko alakar dake tsakanin Sameer da Salmah indai da raina sai na raba wannan soyyayar dan da ni da ta dace
Da yamma ci ya shirya tsaf sai gidan su Naureen.sai da me gadi yai masa tambayoyi sannan ya bude masa ganin be taba ganin sa a gidan ba Tana zaune a parlo suna hira da Ammee aka shigo kiran ta Kace bata nan
Wane ko kiran ki nima ban sani ba ammee kuma ba ya Sameer bane dan bamuyi zai zo ba kuma in shine shigowa zai yi  Ki tashi kije ki ga wane sannan ki dakarta dashi dan ma karya shigaba da zuwa ayi miki fada Ammar baya nan da shi zai fita
Cikin mamaki na karasa wajen sa to ya akae yasan gidan mu sallama nai masa ya amsa cike da murmushi  Kin yi mamakin ganina anan eh to ki daina mamaki kin san so ba inda baya kai mutun
Yanxu me kazo yi anan ne man soyayyar ki uhmmm kayi haquri dan yanxu haka ma ankusa biki na Allah ya baka wadda ta fini na barka lapiya nai shige wa ta cikin gida
Lallai ma wannan yarinyar baki sannan ni ba indai nace onay son abu sai na samu komene Kwafa yai sannan ya shige motar sa Ya Ammar sun dai dai ta da mas'uda,ita kuwa Rauda ya Affan ne Ke son ta da gidan Baffa aminu shi kuwa ya Asif Huda ce zabin sa
Da yake duk lamarin na gida ne haka yasa ba'a ja wani lokaci me tsaho ba wata daya ne kacal Haka su dady suka shirya dasu da majajen suka tafi kasahe daban daban suka hado lefe daga nan sukayi odar kayan dakin amare
Shirye shirye ake ta ko'ina iyaye mata sun dage wajen shirya amare ba inda suke fita ko da takama.dole sai sun sa nikaf sannan driver ya kai su kusan kullum aunty najma tana hanyar gida
Ran I gobe kamu wani daka cikin masu aiki ya shigo yace ana magana dani ya suhal ne ya fita dan ganin wane  Abbas ya gani sama sama sukai gaisa ya Kaine kazo wajen Naureen eh to dan Allah kayi haquri Kaga yanxu ma hka shirin bikin ta ake yi
Kayi haquri kai mata fatan alkhaeri tunda ya fara maganar gumi yake keto masa ga wannan ya mika masa invitation card  Da kyar ya iya cire hannun sa ya karba sai anjima ya suhal.ya fada ya shige cikin gida
Gaba daya kasa sa daga jikin sa yai dan son Naureen ba karamin kamu yai masa ba a haka ya ja jiki ya shiga mota da kyar ya kai kan sa.gida Yau ne kamu amare sun yi shiga ta alfarma sun yi kyau kamar ka dauke su ka gudu
Lecture akai musu akan zaman aure ta ratsa jikin su bama su kadai ba har wanda suka hallaci wajen dan Nagano Bakanoma da ka gefe tana share hawaye,
Yanayin da Fatima ta shiga da kaganta kasan wa'azin ya shige ta haka aka yi aka gama  Washe gari akai get together inda amare da angwaye da aboka nan su suka halatta
Hak akai ta shagali iri iri abin gwanin ban sha'awa sai dai muce Allah ya san ya alkhaeri ya bada zaman lapiya Yau dubban jama'a suka sheda daurin auren emmta hudu da samari hudu a gidan hajiya kaka aka dibi amare har kuka sai da hajiya kaka tayi sabida farin cikn wannan auren na jikokin ta...........????
.
Haka aka kai kowacce gidan ta tana kukan rabu da iyaye Rayuwa me kyau Naureen da Sameer suke a gidan su cikn jin dadi da kwanciyar hankali in ka ganta sai ka kuma kallon ta sabida tsaban kyau da jikin ta yai har wani kiba ta dan yi
Tunda aka fara harkar biki kullum Abbas sai en leken asirin sa sun hallara a wajen da dai da gidan su sai da suka bin ciko masa Yau kima nin wata uku da bikin su suna zaune sun gama breakfast fast Naureen ta dora kan ta akan ciyar sa tana ta faman zuba masa shagwaba haba zaujee yau fa kace zamu je gidan su ya Asif Kaga duk sun zo mune kawai bamu je musu ba
Ni ban san ki wahal min da kan ki da babyn mu shiyasa Da sauri ta tashi wane baby kuma ana zaune kalau a ina yake anan ya nuna ta ah ba.wani baby ni gaskiya in ba muje ba sai nayi fushi
Kar ki fushi anjima zamu je har gida zamu a'a haba Kaga fa ba inda na taba zuwa ta narke zata fara kukan shagwaba sorry zaujatee zamu sai ma mu fita fa wuri dan mu sami damar zuwa ko ina kiss ta manna masa sannan ta dane jikin sa cikin farin ciki
Haka kuwa sukai ta zaga gidan yan uwan su amare ko wacce tana kunshe da babyn ta a jikin ta fir ita taki yarda tana da shi sai da dare sannan suka je gidan hajiya kaka daga nan sukayo gida a gajiye
Kinga sai mun Kwana biyu baki fita ko gate ba sabida me kin wahalr min da kanki da kuma toshe masa baki tai da hannu to naji shikke nan abar maganar
Sai da sukai wanka sannan sukayi shirin bacci Cikin bacci suka Ji karar harbi innalillahi a firgece ta tashi zaujee kamar karar bindinga ki kwantar da hankali ko kan ya kuma wata magana yan fashi ne suka shigo sanye. Suke da bakin kaya ga kuma fuskar su da suka kunshe da bakar safar fuska
Tsawa suka daka musu kara zata yi yasa hannu ya toshe mata baki  Wata mahaukaciyar dariya wani daka cikin su ya saki lallai munjo mutaya ku murna auren ku kallon junan su sukayi yes munzo mu taya ku cin amarci daga nan mu tattauna inda ya kamata aje honeymoon
kai wane Naureen ta tambaya saurin me kike da sannu zaki sanni ki kwantar da hankalin ki,dan Allah kuyi haquri ku fadi duk abinda kuke so abaku karkuyi mana komai
Ae baku da kudin da zaku bamu wani ya fada amma Akwai abinda kuke dashi d zaku bamu komene ku fada in da zan iya zan Baku Sameer ya fada cikn hanzari
Dan Allah malamai kuyi kuyi ku fadi abinda kuke bukata kun tsaya gashin kanta ya fisga wata kara ta saki ki iya bakin ki dan wannan tsiwar bazata yimi ki amfani ba ha watsata gado kanta ya fada kan abin gadon har fitsari sai da ya zubo mata tare da kurma uban ihu dan janyo hankalin makwabta ina ae ba me jiyo su sabida irin wanan uguwoyin ne
Kuyi abinda zamuyi kar su bata mana lokaci Kuka ta fara tana musu magiya suyi haquri har kasa Sameer ya durkasa yana basu haquri amma ina sam basu saurare su
Daga bindigar su sukai suka harba sama wata kara ta saki tare da sulalewa a sume kan Sameer ya yunkurin yin wani abu sun sammace shi sun kwada masa bindiga aka take shima ya fadi a sume
Daukan sa sukai sannan suka fita suka sa shi a mota suka tafi Karfe ukun dare suka isa gidan suka fara shewa wata budurwa ce wadda take sanye da wasu shaidanun kaya ta zauna kusa da shi tana shafa sajen sa da ya kwanta luf luf a fuskar sa kai gaskiya wannan guy ya hadu da yawa
Mari aka sakar mata wanda yasa ta tsuke bakin ta batare da ta karasa maganar ta ba Wani likita ne ya matso yai masa allurar bacci angama oga ya fada  ya takardun ka kammala su eh an gama ko mai oga gobe 8:00am.jirgin zai tashi aikin ka yana kyau
Wasu kudi ya ciro wajen bandir uku ya bashi ah ba hak mukai da kai ba Kasan aikin nan fa yana da hatsari biyar mukai fa nan ya kara masa biyu sanan ya tattara kayan aikin aa ya fita....
.
===== SANADIN SELFIE 008 =====
Da asuba makwabat suna waje suna jimanin gidan da aka shiga fashi wani me gadin daya gidan ne ya fadi gidan sabida ya makale yaga inda suka fito hanyar shiga sukai suka ga me gadin gidan kwance cikin jini sun harbe shi a kafa
Karasawa haraban gidan sukayi ana tunanin ko Sameer zai fito amma shiru ba alamun sa to in akwai me number nasa ya kira wani da ga cikin su abokin sa ya fara kira amma be dauka ba  Kai gaskiya da matsala fa wani ne ya fara kwala masa kira nan ma shiru to Allah yasa ba kashe su suka yi ba
Daya Ke abokin Nasa yasan Asif nan take ya kira shi yace yai maza maza yazo gidan Sameer ba lapiya kamin ya tawo ya kira Ammar ya fada masa a rude suka iso  Direct cikin gida suka shiga bakowa sun duba ko ina basu nan bamu shiga bed room ba suna shiga suka ganta a sume a guje suka karasa wajen jini yana zuba ta gefen gashin ta Jijjagata suka fara amma sam taki motsawa Cikin tashin hankali Ammar ya kira Abee ya fada musu yana kuka tana ina yanxu mun kan hanyar kaita asibiti shi Sameer din fa bamu ganshi ba
Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un ya Ke ta ambata Ammee dake gefen sa ta kagu taji waya kira da asubar nan lapiya alhaji gidan Sameer ba lapiya en fashi sun shiga kuka ta fara Su Asif kuwa suna kaita aka huce da ita emergency Abee ne ya kiran mahaifin Sameer ya fada masa to ae sai muje asibitin muga halin da take  Ko ta san inda ya tafi cikn kan kanin lokaci dangi sun Ji wannan mummunan labarin haka aka cika a asibiti ana jiran farfadowar ta
Sukuwa 7:30 suna airport sun shirya tsaf koda aka zo checking wannan fa suka nuna Sameer dake kwance kamar me bacci am bashi da lafiya shine zamu fita dashi a duba shi a can takardun sa wanda suka hada dana asibiti suka nuna 8:00am suka daga sai Malaysia Har Kusan 12 bata farka ba duk wanda kagani hankalin sa a tashe matan kuwa sai da aka tsawatar musu suka daina kuka
Dadyn Asif ne da Abee sai kuma alhaji su Sameer suna wajen asibitin alhaji tunda har yanxu bata farka ba yakamata akai report wajen police mana gaskiya ne zama haka bamu san abinda zani haifar ba nan suka kira sauran mazan suka ce a kakkasu a je ayi report
Duk wani bincike da en sanda sukai ba'a cimma nasara ba haka suka dawo jiki a salube Suna shiga dakin mamee wadda tunda taji labarin take kuka ta tawo da sauri ya ake ciki sai addu'a dan duk inda muka je ba wani gamsashen bayani
Daki ne ya kaure da kuka wanda yai sanadiyar farkawar Naureen bude idon ta tayi ganin halin da jama'ar dakin suke yasa ta tashi tana kokarin tsige Karin ruwan da akai mata  Rike ta aka fara da karfi ta fara kuka tana kiran Sameer kana ina dan Allah ku kyale shi kar ku kashe min shi
Ae kuwa nan kowa ya fara share hawaye ni kaina bazan iya jure ganin halin da ta shiga ba fitowa nai ina share wasu en matan hawaye Da sauri ya suhal ya fita ya kirawo likita fada ya dinga yi sosai yaza kusata a gaba kuna kuka gaba daya bata cikin hankalin ta hakan zai iya ja mata wata matsalar ta daban
Allura ya kuma yi mata in few minutes bacci ya dauke ta Anya kuwa wannan ba masu garkuwa da mutane ne sukai wannan aikin ba kuwa Asif ya fada
ni ma wallh na fi wannan tunanin amma tunda police sun ce zasu bincika sai dai mu cigaba da addu'a Allah yasa yana lafiya aduk hannun wanda yake...........
.
Kullum sai anje wajen police amma amsa daya ce ba'a sami wani cikakken bayani ba Ita kuwa Naureen baci ba sha sai kuka duk ta fita hayyacin ta ta rame kamar wadda ta shekara tana jinya
Gashi likita ya tabbatar tana.da shigar ciki na wata uku duk wanda yagan ta sai ya tausaya mata me saurin kuka kuwa sai ya zubda hawaye Haka aka sallamota dga asibiti akai gida da ita Ammee ce zaune a gefe gadon da take rike da cup din tee karbi ki sha bazan iya sha ba Ammee dan Allah ku kyale ni ni kadai nasa yanda nake Ji a raina nasiha tai tai mata harta karba amma ba wani sha take ba
Shi kuwa Sameer bayan sun sauka wani gida suka zarce da shi suka shimfide shi a parlo sai bayan 2hours sannan ya farka jiyai kan sa yai masa nauyi a hankali abunda ya faru jiya ya fara dawo masa bude idon sa yayi da sauri
Mamaki ne ya baibaye shi ganin inda yake tashi yai ya cakumi wani dake gefen sa ina kuka kawo ni me kuke nufi dani ina Naureen tana ina wallahi in har wani abu ya same ta to ku tabbatar gaba dayan ku sai kun rai na kan ku
Wani ne ya karaso cikin takun isa da tunkaho kayi haquri da sannu zaka gane inda kake kuma kasa a ranka har abada kun rabu da Naureen Karya kake wallahi baka isa ka rabani da ita ba wata mahaukaciyar dariya ya saki sai a lokacin ya juyo yana kallon Sameer
Kurrr Sameer ya kafa masa ido yana so ya tuno inda ya san shi hmmm basai ka wahal da kan ka wajen tuno ni ba  Wasu hotuna ya mika masa kalli wannan zasu baka amsoshin tambayar ka  Da sauri ya karba pictures din bikin.Sune suna dariya shi da Naureen wani a gefen su dayan ya duba inda suke musabiha da wannan guy din sauri kallon sa yai dan tuno lokacin. ( sunana Abbas ina tayaka murna auren ka da wannan kyakkyawar matar taka nagode ya ce masa tare da sakin hannun sa)
Hope kagane ni yanxu to wanene kai me kake nufi da mu me mukai maka Ni sunana Abbas kamar yanda na fada maka ranar auran ka ni ne wanda nake son Naureen kuma inda ina son abun bana yi masa kishiya sannan inda naga abu ina so to ko ta halin kaka sai na samu
Karya kake wallahi Naureen tai maka nisa baka isa ba wani naushi Abbas ya kai masa ka iya bakin ka kuma ina me tabbatar ma kaiwa Naureen nisa kar ma kayi tunani koma mata yanxu Cikin zafi rai sameer ya kai ma Abbas duka hoho kan kace me dambe ya kaure a tsakanin su naushi suke kai wa junan su ta ko ina tun Abbas yana kokarin karewa har Sameer ya fara masa illa
Yaran sa ya shiga kwala ma kira a guje suka shigo ganin halin da ogan su yake ciki suka yo kan Sameer suka fara dukan sa  daman ance sarkin yawa yafi sarkin karfi nan take sukai masa jina jina suka barshi anan Sai bayan wasu lokuta sannan ya dawo hayyacin sa. Wani daki kankani yaga an maida shi yunkurin tashi yayi ya kasa sabida irin yunwar datake addabar sa ga kishirwa kamar ta kashe shi
Turo kofar  aka shigo Abbas ne da kumburarran bakin sa fuska duk tasha naushi wato nunan karfin ka zakai ko to zan ga ta inda zaka fita anan zakai ta zama har lokacin da burina zai cika na auren Naureen sannan kai kuma na yanke ma hukunci da na shirya ma
In aka zo min da gaddama yanda yana dauko ka ba tare da wahala ba haka ita ma zan daukko ta Wallahi Allah ya fika bazaka taba samun nasara akan ta ba ina Allah ya yarda kuma da sannu asirin ka zai tuno
Asirina bazai taba tunowa ba dan nayi nisa daka inda za'ae kokarin cetonka Ya fita yana masa dariya mugunta wani mutun ne ya shigo dauke da da wani karamin plate ya mika masa
Kallon sa Sameer ya Ke kamar me nazarin wani abu har zai fita yace dan Allah in bazaka damu ba zan tambaye ka........
.
Kallon sa Sameer ya Ke kamar me nazarin wani abu har zai fita yace dan Allah in bazaka damu ba zan tambaye ka Dawowa yai ya tsaya batare da yace uffan ba a ina nake anan matsowa yai daf da shi sannan ya dafa kafadar sa yace  kana Malaysia
A zabure ya tashi me kake nufi bana nigeria to ya akai aka kawo ni nan zai kuma magana yaji motsin tafiya da sauri ya fita yana ga abincin ka nannan
Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un kawai yake ambata to ya akai suka kawo ni nan kuka ya fara me tsuna zuciya yana tunanin halin da Naureen da duk wani wanda yashafe shi zai fada
Fara cin abincin yai badan yana so ba sai dan yunwar da take kokarin illata shi ko ruwa babu haka ya fara waige waige Wata karamar kofa ya gani a  hankali ya tashi ya nufi wajen ya tura bude wa tayi karamin toilet ne bakomai a ciki sai sink da kuma wani fanfo murdawa yayi take ruwa ya fara zuba
Kafa kansa yai ya fara kwankwada yana sha ba kakkautawa har sai da ya ishe shi take cikin sa ya kulle yafara murkususu anan Sai da ya lafa masa sannan ya tashi ya daura alwala ya fito ba wani abunda zai shimfida haka ya goge wajen
yafara sallah ko da ya idar tashi yai ya leka wata karamar window Inda yaga gari ya fara duhu alaman anyi magarib take ya fara jera salloli tundaga kan farillah har nafila
Sai da yaji suna kokawa da bacci sannan ya haqura ya kwanta sai juyi yake sabida wata karamar katifa ce duk ta motse gashi ko blanket babu bare abun rufa
A haka bacci yai awon gaba da shi sanyi asuba ne ya tashi shi A irin wannan yanayi Sameer yake rayuwa ga tunanin Naureen da yan uwansa kullum sai yayi kuka tun yana kuka ya haqura ya dangana ya barwa Allah
A cikin masu kawo masa abinci Akwai wani wanda yake dan sakarma Sameer fuska yauma shine ya kawo masa Lekawa yayi sannan ya dawo ya zauna bawan Allah ina taya ka jaje na shigowa hannun wannan azzalumin
Nima wallh larura ce tasa na shigaba da zama a karkashin sa sunana salmanu na fara aiki ne shekara biyu data wuce sakamakon halin matsi da muka tsinci kan mu nida mahaifiyata da kanne na na nemi aiki sai dana shigo sannan nasan halin sa da irin sana'ar da yake yi
Kuma duk wanda ya fara aiki a nan to balalle ya fita sai wani ikon Allah dan yace duk wanda ya san sirrin sa bazai bar wajen sa ba in mutun yayi yunkurin gudu wa yasa aje akashe shi dan kar ya tona masa asiri
To wane hali ne da shi haka Sameer ya tambaye shi Abbas mugun dan damfara ne wanda ya shahara yake yi kasashe daban daban sanna dilan hodar ibilis gashi be dauki rai a bakin komai ba bashi da imani  wannan kadan daga cikin halin sa Ke nan
Tab aiki ja to kai me ya hada ka dashi har ya kawo ka nan Wani murmushi me ciwo Sameer yayi sannan y kwashe abinda ya faru ya fadawa salmanu
To sai dai mu cigaba da addu'a Allah ya kawo mana mafita dan nima hanyar kubuta daga hannun sa nake nema to tun daga wannan lokacin in dai gidan bakowa salmanu yake shigowa wajen Sameer suna hira
Suku wa Sa'ad da Mahmud abokan Sameer sun ci aniyar nemo Sameer a duk in da yake Haka ma Asif da Affan ba'a bar su ba baya ba dan Asif har kasaahe yace zai fara bi neman sa kuma bazai gajiba har sai Allah ya bayyana Sameer...........
.
Kullum haka ake addu'a da bincike akan Allah ta bayyana Sameer gashi yau an kwashe wata shida Cikin Naureen ya shiga watan haihu yau ko gobe A wannan hali mas'uda ta haihu ita da Huda Da yammaci Naureen tana daki ita kadai tasan abinda take Ji daurewa take kawai
Tana addu'a Allah ya sauke ta lapiya cikin ikon Allah ta sunbulo jaririn ta su mame da Ammee suna parlo Hajiya me nake Ji kamar kukan jariri kai kodai kunnen ki ne
Ammee ta fada kukan jariri ne ya cika gidan gaba daya dagu Ammee da mamee sukai hanyar dakin ikon Allah Ashe haihuwar ce nan suka ga ta haifi santalelen yaro
Nan suka fara gyarata inda mamee ta fara duba ta da yake abinda da ta karnata Ke nan ba ta sami wata matsala ma nan aka shirya su ita da babyn ta
Amma Naureen me yasa kika shiru baki fadawa kowa kina jin ciwo ba shiru tai ba amsa nan aka fara tururuwar zuwa ganin jariri Kuka ya fara aka miko mata shi tun d ta dauke shi ta kafa masa ido kamar sa daya da Sameer har yaso ya fishi kyau itama kukan ta fara
Mamee ce a gefen ta tuni tausayin su ya kamata ga tunanin dan ta ko a wane hali yake oho rungume su tai ta fara kuka abin cike da tausayi Duk wanda ya zo barka sai ya yaba da kyaun yaron masha Allah kuma ya tausaya masa
Hajiya kaka ma an kawo ta sai da aka fitar da ita daga dakin dan daukan yaron tai tana kuka Dadyn Sameer ne da Abee suka shigo wajen Naureen tana kwance babyn yana wajen Nassarah yar albarka Na'am Abee ta fada tana tashi zaune
Shin kun taba hira da Sameer akan sunan da za'a sama baby girgija kai tayi idon ta cike da hawaye.  Ta tuno lokacin da suke zaune suna hira
(anya kuwa ba babyn na ann kuwa a ina ta tambaya nuna cikin ta yai haba ba wani baby)Shi be tabbatr tana da ciki ba ma a ranar aka sace shi kuka tasaki me ban tausayi
Dadyn Sameer ne ya where wata zufa da taketo masa to yanxu wane suna kike so ae masa huduba dashi dady asa masa ko ma wanne ta fada tana kuka a'a ki fadi wanda kike so
Abee ne yake rarrashin ta cikin muryar kuka tace asa masa *Sameer* A wannan karon sai da kalla ta zubowa dady ya fita yana share ido shi kuwa Abee daurewa kawai yake yi haka sukai masa huduba da Sameer suna kiran sa da *junior*
Koda daddyn Sameer yaje gida ya fada ma mamee kuka sosai suka fara mas'uda da yasmeen sai kuma saleem dake gefe shima yana nasa sam dady kasa rarrashin su yayi dan abun da ciwo
Duk wanda yaji sunan da aka sama yaron sai ya tausaya Asif ne ya shigo shida Affan tunda suka shigo junior yana hannun Asif Kur ya kura masa ido cike da tausayi
Naureen ki cigaba da addu'a yanxu haka nima sallama nazo yi miki zan tafi neman Sameer haba ya Asif karka je kaima su sace ka dan Allah kar ku tafi kuka take bata Masan me take fada ba.
Haka yai ta bata haquri gani tai shima in yazauna zata karya masa zuciya ya tashi ya fita ya kuka rashin dan uwansa aminin sa dan tare suka taso tun suna yara
Haka Naureen kullum ta kasance in dai junior yana wajen ta sa shi take a gana tana kallon sa tana kuka da sambatu iri iri haka yasa Ammee ta hana ta zama a daki ita kai dai dan karta haddasawa kanta wata cutar
Sameer kullum azaba iri iri Abbas yake gasa masa tati baki ya rame sai ka kura masa ido sannan zaka gane shine,Suna  parlo wayar Abbas ta fara ringin ta akai ya fada daga daya bangaren aka ce yallabe matar tasa ta fa haihu tun tuni wata dariyar mugunta ya saki har da buga kafa shikken nan sai mun shigo
Wata matashiyar budurwa ce tace yallabe me yafaru kake wannan dariya haka fada mata abinda aka fada masa tayi ah dole kai murna oga yanxu ya za ae shirya wa zamuyi muje in mun karasa nigeria sai na fada miki yanda za'ayi tom ogaoga........
.
Shirye shiryen su suke haka yaba Sameer da salmanu damar gana sosai ,Abbas ne ya shigo dakin cikin takun isa dora kafar sa yai akan cinyar Sameer yana wata dariya ka shirya an kusa sauran aure da masoyiyata ya hankada kujerar da sameer yake kai
Faduwa yai cikin zafin nama ya tashi wallahi karya kake ko mutuwa nai Naureen bazata aure ka ba wallahi tashi yai da niyar rarumoshi wani karfen dake hannun sa ya kwada masa aka jiri ya dibi Sameer ya fadi nan
Sabida wani business d yatawo min ni na fasa zuwa amma Ke ki tafi in kinje sai tsila ya kai ki gidan ga wannan ya nuna mata wata akwati Karki kuskura fa ki batan aiki zan kiyaye oga
Nan yasa driver ya kaita airport tana sauka wasu yaran sa suka tare ta cike da kallon tsana ta kalle su tare da shiga motar Sai da ta biya ta gidan sannan tai wanka ta shirya ta ci abinci ta fito tsila yai mata jagora zuwa gidan su Naureen, Saleema Ke nan yarinya me kyau sam ba irin yammatan sa bane
Allah ka kubutar dani daga hannun wannan shegen wallahi dan kar nai yunkurin guduwa yasa akashe ni amma da tuni na gudu,ko Mene ya hada su da wannan Allah ya karewa daga sharrin sa ta fada a zuciyar ta share hawaye tayi dai dai da karasowar su kofar gidan
Me gadi ne ya fito yana tambayar su am ni kawar Naureen ce nazo mata barka ne jin haka yasa ya bude musu gate. Sai da ta kuma gyara fuskar ta sannan ta fito tayi kyau doguwar rigace Arabian gown baka mayafinta ma baki sai jakar ta da takalmi silver both tsila ya bude ya fito da akwati ita kuma taja zuwa cikin gidan
Tun a kofar parlon take sallama sai can taji an amsa hakan ya bata damar shiga zauna wa tai tana karewa parlon kallo kai amma ya hadu iya haduwa ko meya kawo Abbas gidan nan ku kuma damfarar su zai yi sannu muryar wata mara ta katse mata tunani kyakkyawa ce
Murmushi tai ta durkusawa har kasa ta gaishe ta cikin fara'a Ammee ta amsa daman nazo barka ne ni matar abokin Sameer ce
Allah sarki tana daki taso muje bayanta tabi tana yaba irin mutuncin matar dakin suka shiga tana kwance kamar me bacci Salmah tashi kinyi bakuwa au Ashe ma Kusan suna nan mu daya murmushi tai sannan ta zauna a daya dg cikin kujerun dakin Ammee ta miko mata junior sannan ta fita
Gaisawa sukai ba Yabo ba falsa  amma ban gane ki ba Naureen ta fada am sunana Saleema ni matar abokin mijin Kice bamuji da wuri ba sai jiya shine yace nazo duk da baya nan da tare xamu zo
Allah sarki na gode shiru nai ya bakunci dakin ita kuwa Saleema tunda ta karbi yaron take kallon sa cike da so kamar ta fadi inda yake amma ina baza ta iya ba,dan ita ma kanta satota Abbas yayi a Wayan ce ta goge hawayen da suka tawo mata sarai Naureen ta kula amma sai tai tunanin ko tausayin yaron ne yasa ta
Waya ta ciro ta fara daukan junior a photo tai masa ba adadi au baki ma fadan suna babyn ba Saleema ta fada fuskarta cike da annauri hada ido sukai sannan tace Sameer muna cema junior
Amma wannan dan kamar na tafi dashi nake Ji murmurshin yake kawai Naureen tayi bayan wani lokacin ta  ajiye shi cikin gadon sa sannan ta bude jaka ta zaro bandir na en dubu dubu ta bata wannan kyauta tace a Siyama junior turare wannan kuma gashi ta tura mata akwati na tafi sai anjima
Ta fito haka kawai itama Naureen Taji matar ta kwanta mata tashi tai ta rako ta a parlo suka ga Ammee har kasa ta kuma durkusawa tau mata sallama sannan ta tafi
Tana isa mota tsila ya fara kinje kin wani zaman ki kallon banza ta watsa masa na zauna din mara mutunci da abunda zakai ne ta shiga mota shi kuma ya ja daga nan airport ya kai ta domin komawa Malaysia sai da ya tabbatar flight din ya tashi sannan ya juya
Naureen suna zaune suna ganin kayan da ta kawo Ammee ce take taya bawa da kyaun su ga su kuma masu tsada kudin da ta bata ta mika wa Ammee kinga ita kuwa ta bani 100thousand to ki barsu a wajen ki hira suka taba kadan sannan ta koma dakin ta cigaba da tunanin da tasaba
Tun a jirgi ta turawa Abbas photo amma Guda daya kacal wanda yace ta daukar masa Tana isa yaran sa suka dauko ta zuwa gidan sa Da karfin gwaiwa Abbas ya isa dakin da Sameer yake sai da tai dariya me Isar sa sannan ya nuna masa wayar sa wani photo ne na jariri me kyau  gaban sa ne ta fadi ganin kamar sa da yaron
Dagowa yai ya kalle shi zaiyi magana yace basai ka tambaye ni ba danka ne wanda masoyita ta haifar maka kan Abbas ya kuma magana Sameer yayi jifa da wayar take ta tarwatse wani karfi ne yazo masa ya cakumi Abbas ya fara kai masa duka ta  ko ina kiran yaran sa Abbas yayi suka fara dukan Sameer kamar su kashe shi sai da yaga ya daina motsa sannan yace sukyale shi.........????
===== SANADIN SELFIE 009 =====
Haka suka tafi suka bar Sameer a sume be san inda kan sa yake ba har dare yayi be farka ba koda me kai masa abinci ya kai ya ganshi haka ajiye wa yayi yai fucewar sa
Washe gari Kusan karfe ukun yamma salmanu ya shiga kaima abinci a sume ya ganshi ya rikice sosai amma sabida kar ya fito a haka Abbas ya gane sai da ya tsaya ya sai ta tunanin sa sannan ya fito yallabe har yanxu wancen be farka ba fa tashi yai ya nufi dakin da Sameer ya Ke da kafa ya tura shi amma ba alaman rai a jikin sa waya ya ciro ya kira doctorn sa kai maza kazo ya kashe wayar
Saleema ce ta biyo shi ganin hali da Sameer ya Ke ta fara kuka amma abbas bazaka gama da duniya lapy b wllh mari y sakar mata Ke har kin isa ki fadan wata magana mara dadi dan kinga har yanxu ban miki wani abu ba
Ganin na kusa samu masoyiyata shiyasa sam naji bana sha'awar wata mace wllh Allah bazai barka ba au akan wannan kike fadan magana daman na lura Ke yar zafin kai ce
Mugu kawai bayan damfarar da kawai iyaye na saida ja sato ni matsiyaci wanda ba....bata kara sa ba ya fara kai mata naushi bari n hada da Ke in yaso sai ku hadu dashi a lahira kasani wallahi asirin ka ya kusa tuno wa,
Da karfi ya hankadata ae sai dai in kinje lahirar ku hadu ku tona ya buga kanta a bango kara ta saki sannan ta zube kasa a sume,
Doctor ne ya shigo ya same shi a parlo yana huce kamar wani zaki lapiya ya tmby in patients din nuna masa dakin yai shiga yai tun kan ya karasa ya ci karo da jini yana ambaliya gasu nan ka kyale su kai ka san me kake fada in sun mutu a ina zaka zubar da gawar su to yanxu sai kai treating din su ina wannan ae yafi karfi na sai dai na taimaka ma ka kai su asibiti
Ba dan yaso ba aka kwashe su akai asibiti da su emergency aka nufa da su kan kace me an rufa akan Sameer sai da suka samo shi da kyar sanan aka fito dashi aka sama sa oxygen ita ma suka bata treatment sannan suka ba'a bukatar me jinya
Abbas badan yaso ba ya tafi gida yana tunanin abinda zai musu in basu mutu ba Shi kuwa Asif tun da tafita yake zaga kasaahe ko zai sa'a amma ina shiru har ya haqura ya yanke hunkunci komawa gida sam be son komawa sabida yaiwa Naureen alqawarin bazai dawo ba sai da Sameer
Daga Dubai ya hau jirgin Malaysia zai je wajen wani abokin sa  Sameer da Saleema suna asibiti ana basu kulawa ta mussaman cikin ikon Allah Saleema ta farfado sabida ita bata sami wani mugun rauni ba tayi alqawarin ko zai kashe ta sai ta tona asirin wannan azzalumin mara imanin
Sai da Sameer yai Kwana shida a asibitin ya farka da sauri nurse t fita ta kira doctor da sauri yazo ya cire masa oxygen din suna murna samun nasara
Nan suka bashi tea ya sha sai bayan 4hours sanan hankalin sa ya dawo jikin sa Salmanu ne a office din doctor shi da Saleema suna magiya abar su su ga Sameer da kyar ya yarda
Yana kwance suka shigo yayi murnanr ganin sa nan salmanu ya rungume shi yana kuka shi kuwa kallon Saleema kawai yake ya taba ganin ta a gidan Abbas likita ne ya shigo cikin yaren malay salmanu yace karya sanarwa Abbas cewar sun farka sannan kar ya bari ya shigo dakin sai da ya wayar wa da doctor kai sannan ya yarda
Bayan Kwana uku Sameer ya Ji sauki sosai inda su salmanu da Saleema suke kula dashi A wannan yana yin Saleema ta kwashe labirinta ta fada musu to yanxu yazamuyi mu kubuta salmanu ya tambaya mu sami wani doctor me amana mu fada masa
Suna zaune doctor ya shigo basu magani dan tun da Saleema ta farka ta dawo dakin da zama ko bacci zatayi sai ta yi anan ba irin fadan da nurses basuyi mata ba amma tai musu fun furus hk suka kyaleta
Wani matashin ne likinta ya basu yana sannan ya duba su muna sa ran gobe zamu iya sallamar ku kallon juna sukai zai fita Saleema tai saurin magana doctor can you help us about what y tambaya nan suka kwashe halin da suke ciki suka fada masa
Ya tausaya musu yace su jira shi zuwa nan da wani lkcn sannan ya fita......
.
Yana fita dadyn sa ya kira ya fada masa kadawo gida yace masa ya kashe wayar yana isa ya fada masa komai nan take dadyn sa ta kira commissioner of police da yake baban sa minister ne nan take commissioner yazo aka fada masa komai take ya sa police suka tafi asibiti wajen su Sameer
Suna zaune sai ga police sun kusa 10 tsaye suka tashi doctor ne ya shigo sai a lokacin hankalin su ya kwanta suka yi baya nin
To amma muna son sheda ina da ita Saleema ta fada amma a cikin waya ta kuma tana gidan sa Nan da nan aka sa police suka tafi da ita sannan aka kewaye gidan da police Abbas yana zaune wani yaron sa ya shigo a guje yallabe ba lapiya ko kan ya karasa police's sun shigo tare da Saleema Ke ina zaki ya fada
Kayana zan dauka karka damu Abbas tashige daki ta daukko Jakarta da abinda take bukata ta fita shi kuwa tuni hankalin sa ya gama tashi tana fitowa suka sawa Abbas ankwa da shi da yaran sa suka iza kyar sa zuwa police station
Nan ta shiga kunna videos din da take labewa take daukan sa ta ma wasu da aka yi a gaban ta kan kace me tuni en jarida sun fara yadawar ankama wani babban dilan hodar iblis kuma dan damfara wanda ake neman sa ruwa a jallo
Saleema da salmanu sai kuma Sameer suna zaune suna hira cike da farin ciki zasu far shin komawa gidajen su  Shi kuwa doctor Adam ne yake shiri wai ina zaka bayan Kasan yau zan koma gida zani wajen wadan da nake fada maka mana kazo muje daga nan sai na kai ka airport mana
Kai ni bana son wani biye biye hankali na tai gida kai Asif kana da matsala haba Adams bayan na fada maka ba lapiya ce ta baro ni dg gida ba to ya isa haka nan suka fito sai asibitin da Adams yake aiki
Asif ne biye dashi har dakin da Sameer yake ciki suna zaune suna ta hira sam hankalin sa baya kan su  Adams ne yai magana ah Sameer Kaga yanda ka kuma haske kamar ba kai ba juyo wa Asif yai da sauri ganin wanda aka kira da Sameer
Murza idon sa ya kuma yi da tabbatar da ba mafarki yake ba da shima cak Sameer ya tsaya yana kallon sa da gudu Asif ya karasa wajen Sameer ya rungume shi kuka suka fara sosai 
Kallon kallon akae tsakanin Saleema salmanu dakuma Adam ganin kukan  karewa bane yasa Adam ya karasa wajen ya isa haka Asif kun bar mu a duhu we need more explain
Shine ya fada yana nuna Sameer dake kuka kamar mace shine wa Adam ya tambaye shi,shine wanda na fito nema nan ya kwashe komai ya fada musu gidan su Adam suka wuce suna murna Asif kam ya rike Sameer kamar wanda zai kuma bata
Dadyn su yai ma baya nin sannan  taya shi murna nan ya sanar musu cewa an kama Abbas koto ta daure shi na tsawon shekara ashirin A Daren sam basuyi bacci ba kunnen Adams ne suka ja Saleema daki su su kuwa su Sameer Kwana akai ana murna Asif ya dau waya zai kira ya fada wa gida Sameer ya kwace yace ka bari ma basu mamaki,
Kai ni fa baka nuna photos din Naureen ba nan take ya fara nuna masa dana babyn su hawaye ne ya fara zubo masa kira min ita naji muryar ta Ah yanxu dare ya fara kabari sai gobe haba bayan gobe duk inda 12 take muna tare haka dai suke ta hira basu Ankara ba suka Ji kiran assalatu
Tashi sukai su tafi masallaci suka dawo aka fara shiri 7:00am driver yaja su Sameer,Asif, salmanu,Saleema sai kuma Adams dan rakiya kar fe 9:00am flight din su ya daga sai kasa nigeria????.........
.
Wani sanyi ne ya ratsa ran su kamar me a hankali jirgi ya fara sauka cikin farin ciki suka fito da ka gansu Kasan suna cikin farin ciki mara misltuwa motar office din su Asif ce ta kwashe su dukan su sai gidan su Naureen
Da gudu me gadi ya bude gate ganin ko wane ita kuwa Naureen tana zaune tare da junior gaba daya en gidan kamar hadin baki suna gidan Asif ne ya shigo sai kuma wasu suka rufu masu baya da sauri Naureen ta tashi ya Asif Allah yasa an.....bata karasa ba sabida ganin ko wane a tare da Asif murna dakin ya kaure ganin Sameer tsaye take kamar mutun mutumi nine Naureen ga Sameer din ga gudu ta tafi ta rungume shi amma ina sai a sume ta karasa
Tuni dangi sun fara zuwa ta ko ina kan kace me gida ya cika makil kowa yana farin ciki ido ta bude ganin sa yasa ya tabbatar da ba irin mafarkin da ta saba bane
Nan aka shi ka sha Hajiya kaka ce tace wai Asif baza kafada mana yanda kuke kuka hadu ba nan ya kwashe komai ya fada shima ya fadi irin azabar da Abbas yai masa kowa sai d ya zubar masa da hawaye daman tun ganin Huda Saleema tace ta Santa a abuja nan akaima mahifin Huda waya sannan ya akaima gidan su Saleema cikin kankanin lokacin suka shigo da gudu ta tafi wajen mahaifanta ta rungume tana kuka sai da tabawa kowa tausayi
To Ke Mene ya hadaki da Abbas dady ya tambaye ta Sai da ta share hawaye sannan tace 
.
   *SANADIN SELFIE*
.
Gaba daya dakin suka kuma maimaitawa  *SANADIN SELFIE* Eh wata rana naje beach shan iska kamar yanda nasaba zuwa duk yammaci ina zaune ina shan iska sai naji in son Karasawa wajen wasu flowers ina isa na daukko waya ta na fara selfie ina yi kwai na hange shi Karasawa nai wajen sa nace zamu iya photo yace yace ba matsala nan na fara mana selfie nida shi??
Tun daga wannan lokacin yake bibiyata har sai da ya damfari dady wasu makudan kudin sannan ni kuma ya sace ni duk in da yaga dama yana zuwa dani amma badamar na gudu
Nan shima salmanu ya basu labarin sa aka jajanta musu A ranar salmanu ya tafi gidan su da alkawarin zai dinga kawo musu  ziyara
Tun a ranar sa'ad da Mahmud suka zo da kyar Sameer ya samu ya tafi gidan su tun da yazo yana tare da dan sa Sameer Karami da matar sa duk abinda Saleema take akan idon Sa'ad dan gaba daya yaji ta kwanta masa arai??
ita kuwa a kano suka Kwana sai Washe gari suka tafi aka musayar contact
,
*Two months later*
,
Sameer ya kuma warwarewa nan aka shirya musu walima inda duk wani masoyin su ya halatta salmanu da Saleema ma sun zo tun da tazo Sa'ad ya Ke manne da ita inda Mahmud da Sameer suke tau masu dariya
Kwance sosai Saleema da Salmah wato Naureen suka fara sun shaku sosai nan tai mamaki pretending din da tai a matsayin matar abokin Sameer
Anyi taro lapiya kowa ta koma gida lapy a ranar aka raka Naureen sabon  gidan ta kamar wata amarya ita da junior wanda ya girma yai wayo sosai nan suka nuna ma juna soyayya kamar wasu amare
shi kima tsowon gidan aka barwa salmanu ya daukko Babar sa da yar uwar sa sannan ya far shirin aure Shi kuwa Sa'ad nan yace yasamu mata cikin kan kanin lokaci aka fara maganar bikin su inda aka tsaida wata daya kacal lokaci yazo akai biki aka kai amarya gidan ta kano duk da tayi kukan rashin iyayen ta akusa amma tai murna sabida kasancewar dangi Sameer sun dauke ta tamkar yar su...........
.
Shima salmanu yayi aure nan suka cigaba da zumunci kamar en uwa abin gwanin sha'awa
,
    *One years later*
Naureen ce dauke da ciki yau ko gobe junior suna ta wasa shida Sameer wooooo ayi mata dariya bazata iya ba shima junior ya fada cikin gwaran cin sa a Daren ta haifo yaran ta en biyu gwanin sha'awa mace da namiji
Murna kuwa kamar me tun ranar da akai haihuwa kullum Saleema tana gidan inda itama take fama da katon cikin ta Ranar suna aka sama macen suna Hajiya kaka wato Salmah kuma sunan uwar ta suna kirana ta da sultan namijn kuwa aka sama Ibrahim sunan kakan su wato mijin Hajiya kaka suna kiran sa da sultan
A salma event aka hada wani kasaitaccen party wayyo kar kuso kuga kyaun da Sameer da salma sukayi abin gwanin sha'awa  Nima ba'a barni a baya ba dan sai da naje duk inda sukai sai na bisu mun kwashi *selfie*
inda naga maryam yar mama da Aisha Meerah kuwa suna ta kwasar shoki ga Fatima Ameen ya'u ana ta harrkawa,ita kuwa Bakanoma da zee autar Hajiya suna ta kwasar kudin liki
Ungiyar Online Hausa writers Nagani sun karaso maza ta mata sun tafi suna kwasar *selfie* Haka aka gama suka koma gida a gajiye nan Sameer Salmah (Naureen) Sameer(junior) sai kuma sultan da sulatna nan Sameer ya rungumosu suka fara kwasar selfie turo kaina nayi wani kallon ya watsa min nan na wuce sim sim????
.
*Bayan shekara ashirin*
Zaune suke salma da Saleema sai kuma Sameer da Sa'ad suna zaune junior ya shigo dan shekara asirin da daya da kannen sa en mata da samari sai kuma zee yar saleema me kimanin shekara 19 ita ma da kannen ta har kun dawo eh mome nan suka zauna aka baje kaya ana ci tun tuni sun lura da soyayyar da zee da junior suke yi kuma sun yi farin ciki da hakan
Hankalin su ne yai kan TV dake kunne ana global news a yaune koto ta saki wannan shahrarran dan dafarar wato Abbas da sauri Naureen ta dau remote ta kashe oh dunyi haka take gasu cikin farin ciki shi kuma ya tsufa a prison.
Anan na kawo karshen wannan littafin nawa me suna *SANADIN SELFIE*
.
*Tammat bihamdillah*
Ina godiya ga Allah da ya bani ikon fara rubuta wannan littafin nawa kuma ya bani ikon gamawa lapiya
Abinda nayi dai dai Allah ya bamu ladan wanda mukai kuskure ya ya yafe mana
_So my dear friends don't take *selfie* at everywhere_
NAKU
ABDULLAHI JAFAR ZARIA (AYS)
CALL or SMS
07066508080
WHATSAPP
07066656752

0 comments:

Post a Comment