'YAR MAFIYA Part 5
.
Jabir da Najwa sai keta tsaunuka sukeyi sai da suka isa wani kogon dutsi suka tsaya yada-zango don su huta a gun. Najwa da ta gama galabaita ga tabo a jikinta cikin murya gajiya da wahala ta ce“Jabir nagode da ceta na da kayi nasu damar da zan k'arasa d'aukar fansa na".
.
Jabir da Najwa sai keta tsaunuka sukeyi sai da suka isa wani kogon dutsi suka tsaya yada-zango don su huta a gun. Najwa da ta gama galabaita ga tabo a jikinta cikin murya gajiya da wahala ta ce“Jabir nagode da ceta na da kayi nasu damar da zan k'arasa d'aukar fansa na".
Murmushi Jabir yayi ya ce“karki damu na tai maka miki ne don nima ina da wani kuduri akan Samar ina so mu had'a hannu da k'arfe muga bayansa kamar yanda yasaka muka kawo iyayen mu da masoyan mu".
Najwa tayi murmushi ta ce“ni kuma ina matuk'ar k'aunan samar bazan iya cutar da shi ba sai dai fansa n akan Yasirah ne ita zanga bayanta".
Jabir ya numfasa yana nazrin kalaman Najwa amma sam bai ji zai fasa abunda yayi niya ba.
A can dajin *KARAMGATURA* cikin gidan Sarauniyan Aljanu *Samriyana* tana ta kula da Yasirah wanda tsafin yasoma tasiri a jikinta. Duk jinyan da take mata a banza ne wana hakan yasa tafara tunani taya zata tai maki wannan yarinya don bazata tab'a mantawa da alherin da mahaifin Yasirah ya mata ba shiyasa a ko da yaushe ta ke bibiyarsa tana tunanin ta inda da zata rama wannan alherin don *Alkairi danko ne* baya tab'a fad'uwa kasa banza haka.
Ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe idonta tare da gyara dogon gashin da ya suuka har kusa da gwiwar k'afanta tana kara nazarin rayuwanta.
WACECE WANNAN SARAUNIYA SAMRIYANA?.....
MAI NENE ALAK'ARTA DA BABAN YASIRAH WATO S MARAFA?....
Don jin wa'yan nan amsoshi ku kasance da
Rash
Sarauniya Samriyana ta kasance ya d'aya tilo ga sarki Sarki Sarguna sarkin aljanu na k'arni goma da ya wuce, ya kasance Sarki ne mai kwatanta adalci a tsakanin mutanen garinsa *KARAMGATURA.* Suna jin dad'i mulkinsa kuma suma masa biyayya da kyautata masa a matsayinsa na shugaba. 'Yarsa d'aya tilo ita ce Samriyana yarinyn da ta gado halin mahaifinta ga son tai makon jama'a.
Samriyana ta kasance mai son zaga duniya taga mai ke gudana wata rana ta fito ita kad'ai ba tare da hadimanta ba ta iso k'asar Nigeria sai da ta zagata har ta iso garin Bauchi, tayi kwanaki a garin tana zagawa sabida yanayin garin ya burgeta hakan yasa tayi kwanaki a cikinta tana yawo.
Wata rana cikin irin yawon da takeyi a garin Bauchi ta bullo ta wani unguwa, da alaman unguwan na masu hali ne gashi ta galabaita da yawa don yunwa ta keji ga kishin ruwa.
Taje gida yafi nawa a rin yanayin da tarikid'a takoma kamar mai bara sai su wulakanta ta su kure ta a haka har tazo bakin titi ta zauna ta zuba tagumi sai hamma take yi. Sani Marafa ne ya fito daga makaranta tun kafin yayi aure yana matashi lokacin ma a makarantar gaba da primary yake. Ya hangi wata mata cikin yanayin tausayaa da har zai wuce sai yaga tana hawaye tana magana a hankali bai jin mai take fad'a, cikin tausayawa ya matso kus da ita ya ce“bai war Allah lafiya kike zaune anan?". cikin yanayin wahala ta ce“ka tai maka min da ruwa yunwa nake ji". Cikin hanzari ya juya yaga gurin da suke da gidansu akwai tazara gashi bai da kud'i sai naira d'ari. Hakan yasa ya ce“bai Allah kiyi hakuri naira d'arine ya rage a jikina amma barin sayo miki ruwa da bredi kinji".
Da sauri ya nufi wani shagon da ke nesa da gun ya sayo mata bredi da ruwa ya kawo mata ya bata hakuri.
Sanah
Da sauri ta karba tana ci kamar mahaukaciya duk sai ta bashi tausayi sai da ta gama ci ya mata sallama ya ce“ni zan tafi gida gashi bani da wani abu da na tai maka miki amma kiyi hakuri". Ya mike ya fara tafiya.
Da sauri ta karba tana ci kamar mahaukaciya duk sai ta bashi tausayi sai da ta gama ci ya mata sallama ya ce“ni zan tafi gida gashi bani da wani abu da na tai maka miki amma kiyi hakuri". Ya mike ya fara tafiya.
Samriyana sai da taga yagi nisa ta mike ta bace ta na binsa ba tare da ya sani ba.
S Marafa yana isa gida ya gai da mamansa aka kawo masa abinci sai da yayi wanka ya sanya kaya ya d'auko kularsa ya zai ci abinci sai ya bud'e yaga girkin Mashaa Allah yayi sai kamshi ke tashi, yazo zai saka hannu sai ya tuna da matar d'azu a fili ya ce“ni yanzu gani zanci abinci mai kyau yayi da wasu ke nima kuma ina ci zan ban saura don haka barin raba biyu inci rabi in kai wa matar nan rabi Allah zai ban ladan tai mako". Murfin kulan ya jawi ya raba ya diba nasa yasa a murfi ya ci tukun ya mike ya nufi cikin gida.
Samriyana da ta biyosa duk abunda yake fad'a taji ta gani hakan yasa ta bace ta koma inda ya barta tana mamakin asai yanzu ana samun masu tausayi irin Sani.
Sani yana shiga gida friza ya bud'e ya dauko juice gora daya da goran ruwa ya fito ya d'auki kulan ya nufi inda ya bar matan.
Yana zuwa ya sameta a inda ya barta nan ya mika mata kulan sai da tayi godiya ta karba taci nan ya mata sallama ya koma gida.
Yana tafiya ta bace ta dau hanyan garinsu tana mai farin ciki ko da ta koma sai da ta sanar da mahaifinta abunda ya faru ya ji dadi ya ce“ina so daga yau kina bibiyansa da hadimanki duk wani abun taimko in ya taso masa kina masa in har baifi karfinki ba.
Sani Marafa washe gari da ya dawo bai sake ganin matan ba tun yana bibiyan gun har ya hakura haka kurum ya tsinci kansa da son tai maka mata don yana mata kalon ta haifeshi ko tayi jika da shi.
To kunji wannan shine dalilin da yasa Samriyana ta tai maki Yasirah wanda da badun Allah ya kawota a wannan lokacin ba da an shude tarihin Yasirah.
Rash
Sanah
Sanah
Kwanci tashi tsayin watanni ana neman Yasiraht amma babu ita labarinta.Jikin Yasar dai gashi nan yau fari gobe tsuma.
A haka aka samu numfashinsa ya dawo, saidai liitoci sun bada tabbaci zai iya rasa tunaninsa gaba daya.
A haka aka samu numfashinsa ya dawo, saidai liitoci sun bada tabbaci zai iya rasa tunaninsa gaba daya.
Yasiraht na cigaba da samun kulawa wajan Sarauniya sossai, saidai bata da karfin da zatai tafiya saboda jigatuwar da jikinta ya yi lokacin da Najwa taso hallakata.A hankalin ta soma takawa tana fita baki dajin tana kallon namun daji tare da taya Sarauniya farautar namun daji zuwa cikin dajin.
Kamar koda yaushe yauma tafe suke suna hira Yasiraht ta dubeta.
"Sarauniyya naji sauki ina son in koma gida saboda sanin halin da Yasar yake amma bakimun bayani wace ke ba".
"Sarauniyya naji sauki ina son in koma gida saboda sanin halin da Yasar yake amma bakimun bayani wace ke ba".
"Cikin murmushi tace zakisan wacece ni bada jimawa ba,amma menene alakarki da wanda suke bibbiyar rayuwarki?".
Yasiraht ta sunkuyar da kai idonta ya ciko da hawaye tasa hannu ta share ta cigaba.
"Kawai tasowa nayi na tsinci kaina a cikin wannan harka amma kafin mutuwar Emeka ta bani labari cewa:
Asalin kungiyarmu ta mahaifin Samar ce,haifaffan garin Kano ne mahaifinsa Malam Sammani da me dakinsa Saudatu. Mahaifinsa mutum ne mai kwadayi da san tara dukiya tun yana saurayi harya girma iyayansa talakawa ne sossai suna zaune unguwar Yalwa a cikin Kano.Fahimtar hakan yasa suke yi masa nasiha sossai, amma baya ji idan yaga masu kudi baya tunanin tayaya suka samu dukiyar kawai burinsa Allah ya bani itaku ko kuma ya dinga biy-biyarsu yana su bashi aikin yi shima yayi kudin hakan yana batawa mahaifansa rai sossai.Lokacin da yai auran fari kwatsam yana matakin karatu s college kasancewar duk da rashin mahaifinsa ya tsaya masa matuka kan karatu suna level one ya soma samun matsala a jarrabawarsa hakan yasa ya shiga damuwa sabida ya dogara da karatunsa sossai kwatsam ya samu kansa an masa tallar kungiyar kan cewar in dai ya shiga bashi ba faduwa a jarrabawa ga kuma kudi da zai dinga samu mudin zai bi dokoki bai jimaba ya amshi batun hannu biy-biyu lokacin bai yi auran fari ba sai da ya shiga aka soma jero masa dokokin kungiya babu fita in an shiga kuma duk wanda ya tona musu asiri kashe shi zasui.
Hajara itace diyar kanin mahaifinsa da ya mutu ya bashi a gidansu ta tashi itace yake matukar so, farkon shigarsa aka bashi kudi naira dubu dari biyar ganin kudin ya daga hankalinsa bai taba kama irinsu ba nan ya boye dubu dari uku ya nufi gida da dubu dari biyu nan ya zauna ya shiryawa mahaifansa karya kan cewar mahaifin abokinsane ya bashi aiki kafin ya gama makaranta suna yi masa aikin company wannan kudi an basu ne dan farkon daukane duk wata za a dinga basu dubu hamsin mahaifansa sunji dadi sossai har gida suka taka gidan daya daga manyan kungiyarsu a zuwan mahaifin abokinsa ne tafi-tafi watanni naja ya soma shirin auran Hajara watansu biyar da aure ta samu juna biyu nan dodon tsafi ya nemi jininta shi kuma yace atabau bazai bayar ba nan suka nemi jinin mahaifansa mahaifinrsa ya fara badawa kawai sai wayar gari akai aka ganshi a mace.Bayan wata uku da mutuwarsa Hajara ta haifi kyakkyawan yaronta namiji yaci sunan kakansa ake kiransa Samar.
Kwanci tashi Samar na girma kyakkyawa dashi, sun shaku da mahaifiyarsa da kakarsa mahaifin Samar kullum cikin bibiyar shuganinsa yake harya gama sanin makamar aiki kaf kwatsam aka nemi jinin mahaifiyar Samar a lokacin yai musu tawaye da hadin bakin wasu cikin manyan abokansa kaf suka kakkashe manyan ya maye kujerar shugabanci wanda saida ya bada jinin mahaifiyarsa sannan ya hau a cewarsu dalilin da yasa suke bukatar jinin mahaifa saboda mutum bashi da wanda yafisu mudin ya bada su to zai iya bayar da kowa tun Samar na shekara goma mahaifinsa yake koya masa zafi ya kware sossai sannan ya sashi makaranta ta hanyarsa suke samun shan jinin yara kanana tare da kswosu cikin kungiya. Samar na aji shida na firamari suka hadu da Najwa lokacin tana aji hudu shakuwarsu ta samo asaline daliin lesson na maths da yake musu tsakanin gidajansu gida kusan goma ne ya rabasu. Shakuwarsu tayi tsanani sossai a haka ya gama primary ya faɗa secondary ita ƙkuma tana aji biyar yana jss two akai masa jumping ya tafi aji biyar yazana jarrabawa ya shiga aji shida lokacin ta tafi form one yana aji shida ta shiga form two tana aji uku ya gama secondary mahaifinsa ya nema masa gurbin karatu a Cairo.
Lokacin da zai tafi tasha kuka sossai.Asalin mahaifan Najwa haifafun garin Jos platue ne Hajiya Moma da Najwa ke kira da Moma itace ta haifi mahaifinta tare da mijinta wanda ya jima da rssuwa.Alhaji Shazali shida yayansa Shamsudeen Shamsu deen ya rasu ya bar Shazali hakan yasa Moma ta dauki so ta dorawa Shazali lokacin da ya kammala karatunsa yai aure ya auri abokiyar karatunsa Maryam mace mai nutsuwa da hankali shekararsu daya da aure aiki ya dawo dashi Kano yaso tahowa da Moma taki amincewa haka suka rabu suna kewar juna.
Zamansu a Kano zamane me daɗi da kwanciyar hankali shekararsu ɗaya suka haifi yara biyu kyawawa Najwa da yayanta Nura wanda suke kira Nur sun taso cikin so da kulawar iyaye uwa uba Kakarsu duk hutu wajanta suke yi cike da so da kulawa bayan Najwa da Nur akwai Fadil da Fadila daga su iyayansu basu sake haihuwa ba.
Lokacin da Samar yazo hutun farko sai mamaki ya ƙkamashi ganin yadda Najwa ta koma katuwa da ita yana ziyartar gidansu akai akai kowa ya sanshi wani zuwa da Samar ya yi gidansu Najwa suna hira take bashi labarin tana son bording schl ba ƙkaramin daɗi ya jiba amma bai nuna mata a ransa yana ayyana wannan lokacine ya dace ya jawo Najwa kungiya yadda zasu ji ɗaɗin samun mata matasa cikin tafiyar.Samar babu abinda ƴya fasa na zafi daya je karatu saima gaba saboda ya damu waɗanda suka fishi gogewa kan harkar.Washegari ya zowa Najwa da tsafataciyar alawarsa ya bada babu jinkiri ta shanye a barta tun daga lokacin ta soma bibbiyar Samar sau da kafa kuma komai ya bukata babu jimawa take masa a haka yasa ta bashi jinin Fadil da Fadila kawai sai tsintar gawar yaran a kai a ruwan wankan su na boys quaters mutuwarsu ta girgiza kowa sossai bayan rasuwarsu aka kai Najwa makaranta nan ta soma jawowa kungiya member hakan yasa matsayinta ya girmama a cikinsu suna jss three ta bada jinin mahaifanta biyu saboda san samun kujerar Sarauta ta tsafi karshe ta faɗi bata cimma nasara ba.
Hakan ya yi matuka bata mata rai ta hakura Samar ya haye karagarta kwatsam Samar ya kawowa Najwa ziyara makaranta anan ya gani tun daga lokacin ya ke nunawa Najwa ta jawoni cikin kungiyarsu hakan zaisa ta zamo Sarauniya idon Najwa ya rufe kwata kwata mulki take so da wannan damar Samar yasata kawoni cikinsu ta hanyar yaudarata ta bani alawa kwatsam na riski kaina a cikinsu.Bangare daya kuma Samar soyayyata ce tai kaka gida a cikin zuciyarsa zuwana cikinsu yafi komai kwantar masa da hankali sai lokacin Najwa ta fuskanta zuciyarta tai zafi saboda tana burin ace itace matarsa kodan ta hau kujerar mulkinsa wnnan yasa ta soma bin wasu matsafa a boye harta kai ga bada jini Nur ya zamo bata da kowa sai Moma hakan yasa ko hutu akai to Jos take tafiya tarkacan tsafinta kuwa na gidansu na Kano fahimtar tsangwamar da Najwa take mun yasa Emeka ta soma taimakamun ta hanyar wani boka dake. garinsu a Ebira cikin dare take tashina mu tafi farkon shigata kungiya naso fita amma suka bani tabbacin mudun na fita zasu kashe mahaifana nikuma du duniya nafisan mahaifana fiye da kowa tsoron hakan yasa naki fita daga cikinsu abinda ya batamun rai na fitinin kowa cikinsu kuwa mutuwar Yasmen hakan yasa na soma yi musu barna nasoma daukar fansa akan Najwa wanda hakan ya haifar mana da gaggarumar gaba uwa uwa tsananin kishin juna. Gagarumar gaba ta cigaba da gudana tsakaninmu sai dai basa nasara a kaina saboda taimakon da Emeke kemun har sukai nasarar kawar da ita bayan ta mallakamun zoban kakanta ta sihiri ni kuma na hallaka Shanny daga nan muketa cudawa har zuwa lokacin aurena".
Murmushi Sarauniyya ta yi tace "kema ba sonki yake ba bibiyarki yake dan cikar burinsa kuma yana daf da cika Allah ya kawo Emeka kika fitinesu kuma ba wata bace Emeka nice Emeka nake bada kama ina bibboyarki duk wani wajan tsafi da kike ganin muna zuwa kawai rufa ido nake miki sabida banaso kisan kudirina a kanki cikin razana Yasiraht ta soma ja da baya tana nunata da yatsa.... wace ce ke?
Take tai murmushi tana dubanta amma kafun tai wani yunkurin magan Najwa ta bace bat bata tashi bayyana ba sai a gidansu ita da Yasar.
Cikin tashin hankali ta soma duba gidan, duk yayi kura alamu sun nuna ta dade a hannun Sarauniya kanta ya sara ta dafe tana tsananin takaci ji take kawai Sarainiyyaba bakinsu daya da Samar ta fito kenan ta hangi shigosar yan sanda nan da nan ta bace tazama inuwa tana bin bayansu cikin hirar da suke ta fahimci bincike suke kan gawar da suka riska gabanta ya tsananta faduwa ina Yasar kodai shi aka kashe?.
Take ta bude tafin hanunta tana karanta wasu dalamusan tsafi saiga Yasar kwance a kan gadon asibiti.Hankalinta ya tashi zuciyarta tai na'am data bayyana kanta amma tambayar kanta take ta wace hanya.
Dabara ce ta fado mata ta nufi gidansu,saida ta faki idon mutane ta fadi magashiyan dama ga ciwuka a jikinta ana nan fa aka zagayeta ana ga Yasiraht kwatsam motar mahaifinta ta nufo hanyar da hanzari ya dauketa zuwa asibiti akai emargancy da ita tana jinsu tai lakur tamkar mataciyya.
Yasar dai jiki sai godiyar Allah kasancewar asibitin suna da kwararun likitoci harya soma bude ido amma baya magana baya gane kowa kwakwalwarsa ta tabu.
Ranar da Yasiraht ta cika kwanaki uku ranar yan sanda da yan jarida suka soma yunkurin san ganawa da amaryar da aka sace a daran tarewa sai gawar maigadi da mijinta a galabaice a ka samu amma da ansoma tuntubarta saitasa kuka hakan yasa basu samu ganawa da ita ba suka hakura.
Da dare ta nemi a kaita taga Yasar,dake babu tazara tsakaninsu babu musu aka yi mata jagora suna shiga sukai sa a Yasar ya farka aikuwa yana arba da Yasirahr take kwakwalwarsa ta soma hautsunawa ya dafe kai yana kara a firgice ya furta.
"Ita ce! Ita ce!! Ita ce!!!".
Take Samar ya bayyana ya buga masa wani katako suka kwala kara shida ita suka zube a nann...
Take Samar ya bayyana ya buga masa wani katako suka kwala kara shida ita suka zube a nann...
Shin Yasar ya mutu ne?.
Ina batun Najwa da Jabir?.
Yaya batun Sarauniya?.
Shin asirin Jabir Najwa Samar da Yasiraht na tonuwa? Wake yin nasara tsakaninsu? .
Ina batun Najwa da Jabir?.
Yaya batun Sarauniya?.
Shin asirin Jabir Najwa Samar da Yasiraht na tonuwa? Wake yin nasara tsakaninsu? .
Nan da nan aka dauki Yasiraht akai bangaran emeegancy da ita,shi kuma Yasar likitoci suka dukufa a kansa binciken farko suka tabbatar da cewar kwakwalwarsa ce ta dawo dai dai amma wani abu ya tsoratashi ta sake samun matsala.
Yasiraht tunda ta farka take matsanancin kuka kamar zata shide Hajiya Yasiraht kuwa ko kallonta batai ba domin tayi zargin da hannunta a kwanciyar Yasar.
Tun bayan bacewar Yasiraht Sarauniya take yunkurin zuwa wajanta, amma babu hali saboda hadarurrukan da take riska a hanyarta.Kamar almara Hajiya Nafisa da Yasiraht na zaune saiga shigowar dan sanda da ankwa hannunsa rike da jaridar data tsoratasu.
Baban shafin Jaridar da aka buga a jiya mai dauke da hotan Baba Maigadi kwance cikin jini sai gefe kuma Yasar magashiyan abin mamaki Yasiraht ce a tsaye a kansu hannunta duk jini. A kasa anyi rubutu da manyan baki kamar haka.
*AMARYAR DA TA KASHE MAIGADINTA TA ILLATA MIJINTA YA RASA RUNANINSA A DARAN AURANSU SABODA WANI KUDIRI DA ITA KADAI TASAN HAKAN AN SAMU HOTUNAN DA SHAIDAR HAKAN NE A HANNUN AMINIYARTA......*
Cikin tashin hankali Hajiya Nafisat tasa kuka,suna ji suna gani aka tasa keyar Yasiraht zuwa kotu Najwa ta kyalkyale da dariya tana gefe tana kallo. Kwata kwata yanzu sun raba hanya ita da Samar da Jabir kowa farautar kowa yake yi.
Tunda aka nufi station da Najwa, mahaifinta yake shige da fice mahaifiyarta kuwa ta rantse babu ruwanta saboda ga zahiri kowa ya gani bata da abinda yafi mika kai bori ya hau da kyar da sidin goshi ya samu barrister Kurfi ya tsaya musu a shari ar saidai zuwansa uku Yasiraht ta kasa magana sai kuka take karshema tace ya nemamata afuwar mahaifanta ita tasan kasheta za'ayi hankalin mahaifonta yai tsananin tashi duk ya rame addu a ce kawai rake rike da shi ga jikin Yasar rai a hannun Allah.
Ranar Littinin itace aka tsayar ranar shiga kotu, kotun makil take da jama'a babu masaka tsinke nan aka taso keyar Yasiraht tana zubda hawaye nan lauyan gwamnati ya tashi ya gabatar da kansa.
"Sunana Barrister Husssin Abubakar Muhammad, wanda aka fi sani da Brr. HAM ni nake wakiltar gwamnati".
Cikin shigar kamala ya fito yana murmushi, ya shafi kasumarsa zuwa gashin bakinsa.Rash ta taboni "Sanahty wannan gayan fa?" na doke hannunta na sha kunu. "Madam muyi abinda yake gabanmu cikin hanzari ta saisaita kanta nai mata gwalo nace"namiki miji kwalellanki mijin Jiddona ne.Hankalinmu ya koma kansa.
"Sunana Barrister Abdurraham Sulaiman Kurfi, ni ne lauyan dake kare wadda ake kara".
Cikin takunsa mai gamsarwa ya koma ya zauna, nan Brr Ham ya fito yana cin magani.
"Malama Yasiraht ko zan iya sanin dalilin daya sa kika kashe maigadinki da mijinki a daran auranki?".
"Objection ya mai shari a Brr yana neman yiwa wanda ake kara tambaya,mai cike da tozartawa".
"Korafi bai karbu ba".
A sanyaye ya zauna, Brr, Ham yai murmushin mugunta yana duban Yasiraht.
Tana dago kai suka hada ido da Najwa ta nai mata murmushin mugunta a zuciyarta tace "kinyi nasara" a fili ta ce.
"Bani da amsar da zan baka saidai in ce nina kashe shi nima ku kashe ni.. ..".
Kuka yaci karfinta ta kifa kai rana shassheka,mahaifinta ya dinga share kwallar tausayi kamar zaije ya janyota.
Dai dai lokacin Samar na can yana yunkurin zuwa hallatar kotun Jabir ya daureshi tamau habu halin fitowa a tsuburin mula'ali.
Da sauri Barritar Abdul ya mike yace, " ina neman wannan kotu ta daga karar nan har sai an binciki kwakwalwar wadda ake tuhuma"
Haka kotun ta tashi babu wata gamsashiyar amsa, a ranar aka wuce da ita birsin dan jiran hukunci.
Haka kotun ta tashi babu wata gamsashiyar amsa, a ranar aka wuce da ita birsin dan jiran hukunci.
Jikin Yasar ya soma sauki an yi sa ar yi masa aiki kwakwalwarsa ta dawo dai dai tunda ya farka yaki magana da kowa cikinsu sai bi da ido yanajin yadda suke hira suna aibata Yasirsht mahaifintane kadai baya jin bakinsa.
Sarauniya ta cigaba da bibiyar lamarin Samar da Najwa cikin ikon Allah duk ta karya tsafin da suke takama dashi ta kamasu ta daure.Samar bai mata wuyar kamu ba saboda yana daure a tsuburin muli'ali.
Duk yunkurin Brr nasan ganawa da Yasiraht taki bashi fuska, hasalima in yazo bata sauraransa.Yasiraht ta kade ta rame, tayi baki sossai burinta kawai a yanke mata hukunci ta mutu ta huta.
KOTU ZAMA NA BIYU...........
Kamar yadda aka saba kowane Brr ya mike ya gabatar da sunansa sanan Brr Ham ya soma gabatar da binciken likitoci.
"Ya mai girma mai shari a,binciken likitoci ya tabbatar da cewar Yasiraht lafiyayya ce bata da matsala kota ciwon kai bale tabin hankali.Wannan ya bada tabbacin kisan da tai da nakasa mai gidanta da gangan ta aikata hakan.Ina rokon wannan kotu mai adalci ta gaggauta hukunta wannan azzalumar dan fitarwa da iyalan marigayi hakkinsu".
Cikin girmammawa ya ajiye sakammakon likitocin ya risina yai godiya ya zauna.
"Lauyan wanda ake kara ko kana da magana?".
"Eh ya maigirma mai shari a".
Kamar an keho su suka shigo kotun hakan yasa Brr dakatawa gaba daya kallo ya koma sama.
Samar ne da Najwa cikin galabaitacan yanayi,bayansu Jabir ne yana huci.
"Afuwan ya mai girima mai shari a mun katse muku hanzari amma hakan yana da muhimmanci saboda wadaanan Azzaluman sune silar komai".
Nan take kotun ta hautsine kowa da abinda yake fada, Alkali ya buga abin dakatawa kowa yai shiru.Sannan ya bawa Brr damar magana da Jabir cikin nutsuwa ya dubeshi".
"Malam munasan sanin sunanka da dalilinka da kawo wadsnan bayin Allah kan cewa sune tushan wannan matsala".
Murmushi Jabir ya yi yana dubansa.
"Cikakken sunana Jabir Adama Saulawa,ni haifafan garin Katsina ne sana ata shi ne kasuwanci bani da iyali.Kamar yadda kasani na gaya muku cewa wadanan mutane su ne tushan wannan fitina eh hakane amma zanfi so kuji daga bakinsu".
Barrister ya juya kan Najwa yana dubanta.
"Mallama ya sunanki?".
"Sunana Najwa".
"Shin menene alakarki da wannan shari'a?".
"Shin menene alakarki da wannan shari'a?".
Kai ta sunkuyar kasa tana share hawaye a hankali ta bude baki ta soma bayani.
"Tabbas nayi nadamar cutar da Najwa... ....." tiryan-tiryan ta dinga bayanin tun daga alakarta da Samar da yadda suka ja Yasiraht har zuwa yau.Kotun tayi tsit sai shashekar kukansu da take tashi,kowa na Allah wadai da Najwa da Samar masu tsinuwa nayi masu kuka nayi.
"Tabbas nayi nadamar cutar da Najwa... ....." tiryan-tiryan ta dinga bayanin tun daga alakarta da Samar da yadda suka ja Yasiraht har zuwa yau.Kotun tayi tsit sai shashekar kukansu da take tashi,kowa na Allah wadai da Najwa da Samar masu tsinuwa nayi masu kuka nayi.
Bsrrister ya dubi"Samar zancan da Najwa ta fada gaskiya ne?".
"Gaskiya ne Barrister".
"Samar mecece hujjarka ta cutar da karamar yarinya kamar Yasiraht?".Yai shiru na tsayin lokaci sannan ya soma magana.
"Gaskiyar magana tun ranar da naga Yasiraht na tuna da burina da nake son cikawa wato zama babban matsafi wanda zai dinga jagorantar Matasan jahar da nake ciki.Sai dai an bani tabbacin bazan samu ba saina kawo matashiyar budurwa mai kimanin shekaru ashirin da daya wadda ranar data cika shekarun za ayi aikin.Tunda aka lissafun yanayin budurwar nake fafutukar nema kwatsam nai gamo da Yasiraht saidai kash shekarunta basu kai ba hakan yasa nasamu nasarar dasawa Najwa son ta jawo mana ita tare da yimata alkawarin hawa kujerar Sarauta.Lokacin da Najwa ta kawo Yasiraht sai nabata sarauta dan san karfafa kusancina da ita hakan ya tunzurata ta soma nunawa Yasirahr tsana da hantara tun bata fahimta ba harta fahimta suka soma takun saka sai dai bata nasara kanta nasararta daya kashe Yasmine da tayi.Sai kuma wannan sharin da taiwa Yasiraht.
"Samar mecece hujjarka ta cutar da karamar yarinya kamar Yasiraht?".Yai shiru na tsayin lokaci sannan ya soma magana.
"Gaskiyar magana tun ranar da naga Yasiraht na tuna da burina da nake son cikawa wato zama babban matsafi wanda zai dinga jagorantar Matasan jahar da nake ciki.Sai dai an bani tabbacin bazan samu ba saina kawo matashiyar budurwa mai kimanin shekaru ashirin da daya wadda ranar data cika shekarun za ayi aikin.Tunda aka lissafun yanayin budurwar nake fafutukar nema kwatsam nai gamo da Yasiraht saidai kash shekarunta basu kai ba hakan yasa nasamu nasarar dasawa Najwa son ta jawo mana ita tare da yimata alkawarin hawa kujerar Sarauta.Lokacin da Najwa ta kawo Yasiraht sai nabata sarauta dan san karfafa kusancina da ita hakan ya tunzurata ta soma nunawa Yasirahr tsana da hantara tun bata fahimta ba harta fahimta suka soma takun saka sai dai bata nasara kanta nasararta daya kashe Yasmine da tayi.Sai kuma wannan sharin da taiwa Yasiraht.
A duniya babu abinda na tsana irin ganin Yasiraht da wani namiji hakan yasa na dasa mata tsanar kowa saboda an bani tabbacin mudin nai sakaci ta soma soyayya to aikina zai wargaje Marwan shine saurayin dana fara kashewa sannan na dasa mata bakin jinin dana saurayin da yake kulata.
Daganan ya dora bayanin kaf abinda ya faru bayan shigowarta kungiya har zuwa kashe me gadi da kwanciyar Yasar asibiti. - ISMAIL SANI
0 comments:
Post a Comment