Blogroll

BANNER 728X90

Monday, 29 January 2018

ZUMA SAI DA WUTA Page 21-30

ZUMA SAI DA WUTA Page 21-30
.
Tsaye Faiza tayi tanai kallon shi, saida yaga motar Salma ta bar gurin sannan ya taka zuwa tasa mota, shiga yayi ya zauna yana cigaba da murmusawa, jiki sanyaye Faiza ta shiga yaja, sunyi nisa babu mai magana da wani, kowa da abunda yake sak'awa a zuciya.
Dakyar dai faiza ta samu courage din yimai magana, duban shi tayi fuskar sa fayau ba damuwa tace.
"Mjay badai ka fara folawa yarinyan nan ba?"
Kallon ta yayi yace
"I dont tink so, amma koda ace na fola mata ai it isn't a crime ko ?
Marairace murya tayi
"Kawai naga she isnt d right person for you, kuma ma you deserve more.."
Katse ta yayi da cewa, "tnx for your concern,  i decide what i want and what i don't want"
Shuru tayi, ta shak'a ba kadan ba, sun danyi nisa yace "When are you ready to settle down
Aranta tace kai nake jira, afili tace "very soon, kasan komai lokaci ne kuma sai Allah yayi"
Daure fuska yayi Yace "kafin lokacin learn to respect youself bawai kina embarrassing kanki kamar yadda kikayi dazu ba, you ain't a kid any more"
Kallan takaici tamai, ita bataga wani bad abu datai ba dazai ce haka alhalin ita waccan data siyar da mutuncin ta lallab'a ta yaje yayi.
Bata iya cewa komai ba har suka iso gidansu, sauka zatayi taji yace "yaushe kike da class ?
Abunka da cool headed person, murmushi tayi tace "jibi"
"Allah ya kaimu" ya fada yaja motar yayi gaba.
Salma na isa gida ta hadu da Mom, fada sosai tasha da irin dressing din datayi, haushi biu ne ya hade mata, daki ta shiga tacire kayan sannan ta zauna kan gado tunanin abunda ya faru tahau yi, ta jima zaune daga bisani ta mike, hoton sa dake gurin tadau ta wurga ciki karamin trash can dake dakin sannan ta koma ta zauna zuciyarta na zafi.
***
Yau kam jikin Junaina ya warware, bataje skull ba saboda intervel na kwana biyu da take dashi, duk babu dadi takeji barin Mujahid gidan, ganin su Hajiya ko ajikinsu yasa ta nuna ita ma bata damu ba, tana son kiran shi awaya amma tana tsoro, ganin take idan ta kuma mai magana yar Mafia zata iya cafko ta.
Zaune Mujahid yake a office tare da abonkinsa Mubarak, sun dan tattauna issues daya shafin aikin su sannan Mubarak ya gangaro mai da cewa, "wai ya ake cikin da diyar Alhaji Abbas ?
Mujahid kam kaman jiran tambayan yake, ya jima yana son mai zancen Salma amma ya share,
Dariya yayi Yace "yarinyar nan bomb ce, nan ya tsarawa Mubarak duk yadda ake ciki tun farkon haduwan su sannan ya kara da cewa "d worst part of the story itace same Ummi da Hajiya take nema ruwa ajallo"
Ware ido Mubarak yayi in shocked yace "abokina mai kake jira, ai albishir zaka ma Hajiya, komai yazo cikin sauki"
Mugun harara Mujahid ya sakar mai yace "yadda na tsanin yarinyar nan bana fatan ganinta gidanmu, what am curious about shine ya akai ta koma diyar Alhaji Abbas sannan kuma why is she alway acting bitchy, deep down nasan akwai something good about her"
Nisawa Mubarak yayi
"Toh ai ita zaka tambaya bani ba.
Muhajid yace "She isn't stupid da zan tunkareta da tambayoyi ta amsa min"
"Ai dama ba zuwa xakayi kafara jero tambaya ba, make friends with her, you can pretend loving her, kasan mata da rauni daganan saika tatso information da kake son sani"
Dariya sosai Mujahid yayi sannan yace "ajiye love aside, yadda na tsane ta i can't even pretend, abu daya zan iya shine mu zama friends, when am done with her sai nayi destroying dinta for good kaga na rama abunda tamin"
Kallon shi Mubarak yayi aranshi yace "this is serious, i cnt wait naga karshen Drama dinga" Afili yace "Allah ya bada saa, if you need my help kamin magana"
"Bani address din gidansu". Mujahid ya fada.
Ba musu Mubarak ya bashi dan kuwa Gidan Alhaji abbas sanan nene.
Salma ta warware, cikin walwala take, duk wani abun da zai b'ata mata rai kawar dashi tayi, basu da lec sai gobe, kitchen ta wuni tana taya mai aikin su abincin dare, bayan sun gama, ta jere komai a dining sannan ta shiga ta kara wanka ta sanyawa jikinta doguwar rigan kanti, bayan sallah ishai ta nufi Dakin Mom, sun jima suna hira, mai aikinsu Lami ta shigo tace maigadi na magana wai wani na kiran Salma awaje, tsaki Salam tayi tace kice mai bana fitan dare, ba masu Lami ta juwa,
Mom tace "kinma isa, ai tashi zaki kije kiga waye, dama tuni na fara jin kamshin yan jikokina"
Dariya Salma tayi bata da niyyah tashi, ganin mom ta bata rai yasa ta mike, daki ta shiga tasa Hijabi sannan ta fito zuwa waje.
Jingine yake cikin motarsa, agogon hannusa ya duba yaga 8.30 tsaki yayi, maigadi ya fito yace mai Salma bata fitan dare, bai damu ba yasa aranshi gobe zai isketa a school, shiga mota zaiyi yaga wata mota ta danno gurin gate din, tsayawa yayi, Daddy ne a motan tare da Driver, Wining glass yayi yace "yaro aida ka karaso ciki, halan wa kake nema...
Kafin Mujahid yayi magana salma ta fito, gaida Daddy tayi aladabce, tana ganin Mujahid ta juya zata koma ciki, Daddy yace "salma jeki mana, ba gurin ki yazo ba"
Yaken dole tayi ta amsa da toh ta karasa gurin Mujahid shi kuma Daddy ya shiga gidan.
Dan nesa dashi ta tsaye hade da kawar dakai gefe, kallon yayi aransa yana jinjina yadda ta bawa Daddy respect, dan matso wa yayi kusa da ita, murya ciki ciki yace "baza ki gaishe da bakon ki ba"
Yadda takeji tsanan shi bazata iya tanka shi ba, juyawa tayi a fusace xata wuce,
Yace "Ummi".
Wani irin shocked taji, gabanta ne ya fadi, she can't recall wen last data ji Ummi abakin wani. Ganin yadda ta daskare agurin yasa Mujahid shan jinin jikinsa, sam baisan ya furta sunan Ummi ba, wayancewa yayi dacewa "Miemie, momy, ummita kinsan bansan sunan ki ba, dole yasa nahau guessing..."
Ajiyar zuciya ta sauke, saidai taji dadi yadda ya kirata da Ummi, juyowa tayi tace "Sunana Salma"
Yace "nice name" kalan ta yayi tamai kyau sosai.
Hararar sa tayi tace "kaga Malam miye ke tafe dakai, indai 500k dinka kazo amsa toh babu na zubar a titi"
Murmushi yayi.
"Karki damu nina yafe maki, nazo ne muyi sorting difference dinmu"
Shuru Salma tayi tanai mai kallon banxa.
Yacigaba "can we be friends ?
Mugun Dariya rainin wayo Salma ta face dashi, sannan ta daure fuska tace "you're not serious" juyawa tayi ta koma cikin gida, tana gudun dumamai zagi a zuciyanta.
Shima dariya yayi ya koma mota yaja yabar gurin.
Kicibis Salma tayi da Salim bakin gate, da alamun lekan su yake, hannuta ya riko
Fuskar daure yace "Salam ki gayamin gaskia, mike tsakanin ki dashi, jiya da yau sam bangane mai kuke nufi ba"
Fizge hannuta tayi, cikin daga murya tace "mind your business and stop acting like a fool" afusace tayi gaba ta barshi da sakin bakin Fool data kira shi dashi, kwafa yayi ya wuce part dinsa zuciyarsa na kuna...
****
Washe gari, 12 to 2 su Salma ke da lecture din Faiza, da wuri ta shiga skull, mutane sai mata congrats din face of gwagwalada suke, ko kallan su batai ba ta karasa Hall ta zauna, baa jima ba Faiza ta shigo Tafara masu lec, bayan ta gama ne ta sanar dasu test datai masu is cancelled, ihu sosai yan aji suka fara dan kuwa sunsa basu tabuka abun arxiki ba, Salma kam baki ta Tabe ko ajikinta.
  Faiza na shirin fita hall din ta kalli Salma tace "ki sameni a office".
Bayan kaman 10 mins Salma ta taka zuwa Department, office din Faiza ta shiga ta iske ta zaune, da alamun zaman jiran Salman take.
Zama Salma tayi kan kujera dake gurin ba tare data jira permission dinta ba.
K'wafa Faiza tayi tace "zan baki A a course dina kuma zan biyaki idan kikayi min alkawarin fita harkan Mujahid"
Mugun Kallo Salma takai mata aranta tace "what an insult, aiko banyi karatu ba ina iya cin B, kudi kuma ai baki dasu"
Afili tace "I assume kin kirani muyi magana woman to woman not lecturer to Student ?
Kad'a kai Faiza tayi tace "duk yadda kike tunani hakane".
   Mikewa tsaye Salma tayi tace "y not kibiyani na tursasashi ya soki, tunda naga har yanxu bakya gaban shi kuma shekarun ku na tafiya"
Hannu Faiza ta nuna mata alamun gargadi tace "karki kuskura ki zageni, cox am not your mate"
Dariya Salma tayi.
"Yes ma, amma abunda baki sani ba shine if you keep following him around like a fool, obeying is orders bazai tab'a sonki ba"
Afusace Faiza ta mike tsaye tace "enough, kawai ki fadi abunda kikeso"
"Ni banaso komai, ki rike kudin ki, grade dinki da Mujahid all for youself cox i dont give a fucking dammm about dem" juyawa Salma tayi, Faiza tace karya ne i know you love him".
Salma kam tagama kulewa, kallon ta tayi tace "love huh !!! Ki kalleni dakyau banda lokacin soyayyar shirme, infact the word love doesn't exist in my Dictionary"
Afusace Salma tabar office din hade da banging door.
Rai bace faiza ta zauna tana nazarin abunda Salma tace, kai ta gigirza tace "so take nadaina binsa na nadai obeying abunda yace kenan" tsaki tayi ta kuma cewa "karyan banxa sodai take nafita harka Mujahid danta samu shiga, toh yarinya kinyi kadan" kamar Tababbiya Faiza tahau surutu ita daya a office.
Ran Salma atafashe yake, tafe take tana zage zage ita daya, "wai harni zata siya saboda soyayar wani banxa da ban damu dashi ba, this woman is crazy how i wish ina son Mujahid da taga iskancin dazan mata" masifa tahau yi harta karasa gurin motar ta, key ta ciro zata bude taji murya kaman ta Mujahid abayanta,
"Hey" ya fada yana kallonta, tsaye yake a gefe inda ya parke motar sa.
Jin hadadan kamshin ya gauraye gun yasa ta tabbbatar shine, bata juyo ba saida ta bude motar, Bindigarta ta roba dake boye karkashin sit ta dauka, sannan ta juya gareshi afusace tanai nuna mar Bindigir, "am warning you, stay away from me"
Shikam kallonta yake, yau atamfa dogowar rigace ajikinta, tayi matukar amsar ta.
Dariya ya kwashe dashi ganin yadda ta nuna shi da bindigar ita a dole she's trying to scared a policeman.
"Whats funny huh ? Ta fada tanai kokarin pulling trigger kaman gaske.
Matsowa yayi kusa ya warce bindingar ba tare data ankara ba yace "Ummi wasan yara kuma kika koma yi.."
Kunya ne yakamata, sai yanxu ma tagano wawtarta.
Murmushi yayi Yace "ya labarin friendship dinmu?
Tabe baki tayi
"Am not interested"
Hannuta ya riko da saida yaji wani irin, itakam ko ajikinta yace " nasan you hate me but atleast find a place in your heart to accept my friendship"
Hannusa ta kalla dake rike da nata tace "sakeni" sakinta yayi, tace "i dont make friends with the enemy"
Rab'awa gefe tayi ta wuce ta fada motan taja tabar gurin.
"OmG" Mujahid ya fada hade da kaiwa hannu shi daya naushi, baiyi tunanin zatayi wuyan samu ba, ayadda yake ganin kuma she will never accept him. Rai bace ya koma motar sa baiko bi takan faiza ba yaja ya koma office.
Ajiyar Zuciya Salma ta saukr tana tunanin whats going on a zuciyan Mujahid, she isn't stupid da zatayi accepting friendship dinshi all of a sudden bayan ta gama swindling kudinsa through kidnapping sister dinshi, Girgiza kai tayi afili tace "it doesn't make sense, am sure he is up to something".
Mujahid na komawa Office ya nufi office din Mubarak, nan ya tsara mai abunda ke faruwa.
Tsaki Mubarak yayi yace "sai kace ba namiji ba, ka kasa karkato da hankalin ta.
Mujahid yace "am not used to shiga harkan mata, mostly suke manne min, ya kakeso nayi, nifa duk ta gama wahalar ni"
Mubarak yace "abu mai sauki tunda taki yadda da rokonta da kake, ai rik'ota zakayi, na tabbata ba dutse bace da bazatayi feeling wani abu ba, kaga daga nan kila adace"
Dariyan haushi Mujahid yayi yace "itakam Tafi Dutse, duk moves dinta ina observing, no matter yadda xan janyo ta jikina she wont feel anything"
Then try kissing her" Mubarak ya fadi.
Ware ido Mujahid yayi yace "what, gaskia i can't, tayama zan fara kissing dinta sai tayi tunanin ko sonta nake".
Mubarak yace "exactly abunda muke so tayi tunanin kenan, koda bata sonka she will forever remember dat kiss, daga nan kuma zata dan fara kulaka koda tayi fushi mayb na kwana biyu ne"
Murmushi Mujahid yayi, ya gamsu sosai da shawaran abokinshi, sun dade suna planing yadda komai zai kasan ce daga bisani ya koma office..
.
Sosai Ja'afar ya duk'ufa da neman Ummi, duk wata social media a duniya sai da ya garzaya neman masu sunan Ummi amma bai samu  actual Ummii da yake nem ba, harta Yaran yan Chibok da aka sace saida ya binciko fuska kowa babu ta Ummi. Duk da ya jima da ganin Ummi amma bazai manta da face dinta ba, kusan shekaru 11 da suka wuce ya tab'a kai Hajiyar su Gombe ganin Ummi, ranar kam tasha kuka ba yadda batayi ta biyo suba Matar Babansu ta hana dagabaya ma Baban cewa yayi su tafi karsu kara zuwan mai gida.
***
Salma kwance kan cinyar Mom a palo, latsar wayar ta take hankalinta kwance, Daddy zaune gefen dayar kujerar suna kallon tashar CNN tare da Mom.
  Maigadi ne yayi sallama daga waje ana kiran Salma, take gabanta ya fadi, Daddy yace "kaishi Guess palo gatanan zuwa".
Banza Salma tayi kaman bata san mi aka ba saida Daddy yace "maza tashi kije ki sameshi, na tabbata yaron dana gani kwanaki ne, na kuma yaba da hankalinsa"
Turo baki Salma tayi tahau gunguni tana fadin "bashi da kirki wlh"
Mom tace "banson shirme, ki biya kitchen ki kaimai na shashe baki"
Takaici ne ya cika Salma, daki ta shiga ta tsayan gaban mirror tana surutai, can kuma ta janyo kayan kwalliya tahau shafe shafe da manne manne, duk dan ta b'ata mai lokaci ta tsiro da hakan, nyt wear riga da wando ne ajikinta, dan tuni dama tara na dare ta gota, ciresu tayi, tama rasa wana kaya zatasa, can dai ta dauko wata pink doguwar riga tasa hade da yafe karamin veil din, kitchen ta nufa tadau bottle water da exotic juice tanufi guess palo.
Shikam tsaye yayi palon yana mumurmushi dani kaina basan maanar sa ba, iya haduwa yayi, sanye yake da tsadadun kananu kaya sai zubai bala'in haddadan kamshi yake. Tana turo kofar palon ya maida duban sa gareta, shigowa tayi sukayi 4 eyes, gabanta ne ya fadi, wani mugun kyau da kwarjini yayi mata, ta bangaran sama kusan hakanne, sunfi 2 mins staring at each other sannan ta tabe baki, ta karasa shiga ciki, bata bi takan saba ta wuce bayansa ta tsaya rike da ruwan da lemon, wayarta dake hannunta tahau latsawa.
   Dariya ta bashi ba kadan ba, juyowa yayi ya matsa kusa da ita yanai mata wani duba,  cikin cool voice nashi yace "Ummi ba gaisuwa ?"
Tsaki tayi, tadan jan baya, gabadaya ya gama tafiyar da tunanin ta, dakyar tace
"Kaga officer ba zama nazoyi da kai bai, ruwan nan kuma bazan bayar ba tunda ba gayyatarka nayi ba" cilli tayi da ruwan da lemon kan kujera.
Wani killer smile ya sakar mata yace "kinyi kyau"
Cikin k'aguwa da tsayuwar ta zauna bisa kujera dake gurin, d'aure fuska tayi tace "kaga dare nayi, wai mi kakeso dani ne, na riga na fadama am not interested da kudurin ka"
"Kinsan miya kawo ni." Ya fada yana kokarin zaman kan 3 sitter da take zaune, kaman an tsikareta ta mike tsaye "nizan tafi sai anjima" hanyar fita tayi yayi sauri rikota ta fado bisa kirjinsa, wani mugun feeling sukaji atare, ahasale ta dubeshi tace "what the helll..." Kallon daya zuba mata yasa kalamanta mak'alewa a mak'oshinta, gabad'aya ya tsareta da manyan idanuwan sa, Lumshe ido tayi yau kam takasa resisting charms dinsa dole ta tsaya tapping current, tuni ta manta duniya da take, bata ankara ba taji bakin sa kan nata, cikin wani salo taji yanai kokarin masu tsotsan Allah tsine uwar shegu, shi kanshi ya dauke wuta kokarin saisaita kanshi yake ya kasaa, Salma kam anji zuma ganin ba Sarki sai Allah yasa ta fara maidawa kura aniyarta, tuni suka fara fita hayacinsu, ringing din waryata ne ya katse masu hanzari, akidemi ta dawo daidai, janye jikinta tayi gefe tanai kokarin daukan wayar da tuni ta sullebe daga hannuta, "na shiga uku" ta fada ganin call din Mom.
Jiki mace yake kallon ta, baiyi tunanin zaiji wani pleasant feelings game da ita ba, ido ya zuba mata yana son ganin reaction dinta saidai taki dagowa ta kalle shi, durkushe take tana kallon screen din wayarta, aranta takaicin abunda ya faru take, wannan abun kunya damai yayi kama.
Murya sarke yace "Ummi
Afusace ta mike, bata iya dubanshi ba, tasa hannunta biyu ta rike kanta, kaman zatayi kuka tace "what were you tinking, are you crazy ?
Magana xaiyi ta katse shi da cewa "i cant believe this.." juyawa tayi da gudu tabar palon binta yayi yana kiranta, saidi tuni ta shige part dinsu da gudu.
Shafar suman kashi yayi yana cewa "oh my God, what have i done...." Wani mugun haushi kanshi yakeji, duk sai yaji dama hakan bata faru ba, ji yayi kaman ya bita bata hakuri, yasan bai kyauta mata ba, koma miye Mubarak ya jaza masa, rai bace ya fice yabar gidan.
Da Gudu Salma ta fada cikin gidan, babu kowa palo sai motsin Mom da taji tana kusurniya a kitchen, dakinta ta nufa tayi cilli da wayanta  ta fada cikin bathroom, ruwan shawa mai sanyi gaske ta sakarwa kanta, ba karamin tafasa zuciyan ta yake ba, wani mugun tsanan Mujahid takeji aranta, haushi ta daya da yayi kissin dinta a banxa, yaci bulus alhalin babu So ko kauna tsakanin su. Kukan da ta dade batai ba arayuwanta ta fashe dashi, sosai take kuka ba kakkauta, saida tayi awa biyu sannan ta fito daure da towel bayan ta cire kayan jikinta, dakyar ta iya fadawa gado ta zube kaman mataciya, hawaye take tadau wayarta dake gun ta tura mai text msg kamar haka .
"i hate you with passion," sannan ta kashe wayar.
(Ni xarah nace Salma you too dey exaggerate, d'an kiss kawai duk kin ishe mu da kuka as if you know enjoy am).
.
Mujahid na komawa gida kasa zaune yayi, nan tsakiyar palo ya tsaya yana kai komo kaman wani zautacce, ganin text msg dinta yasa shi gigicewa, "nashige su, meke faruwa ? Ya fada, flashes din abunda ya faru ke yawon mai akai, nan yahau tryping no dinta yajita akashe, cilli yayi da wayan ya shiga daki, dakyar yasamu yayo wanka ya kwanta kan lausassiyar bed dinsa amma tuni bacci ya k'warace ma idanunsa, juyi yayi tayi akan gado da tunanin barkatai, abubuwa da dama zuciyarsa ke sakarmai saidai ya kasa gasgata komai, mikewa wa zaune yayi yana fadin "no, it cant be...", ganin zuciyar sa na neman tarwatsewa ya mike ya dauro alwala yahau nafilo da neman gafaran Ubangiji.
****
Washegari Salma ta tashi da zafanfan zazzabi da saida aka kwantar da ita asibiti, hankalin Mom sosai ya tashi dan tunda take bata taba ganin Salma cikin yanayi haka ba, kwanan su uku Salma ta fara dawowa daidai, data tuno encounter dinta da Mujahid wani mugun bak'in ciki take ji, haka dai suka dawo gida ta koma sabgogin gabanta bayan tama kanta alkawari fita harkan Mujahid koda ace zai kasheta bata kuma tanka shi.
Acikin kwanakin nan Mujahid shi kadai yasan irin tashin hankalin daya shiga, kullim da salmw yake kwana yake tashi, ba yadda bai ba dan yakaceta aransa amma ya kasa shi kuma yasan ba sonta yake ba, kiranta awaya da tura mata aplogy text ba wanda baiba saidai shuru kota kansan bata bi, gidansu yaje yafi adurga bai samun ganin ta.
Yau da wuri ya shirya cikin kananu kaya ya fita office, office din Mubarak ya nufa yahau shi da masifan yaja masa matsala, Dariya sosai Mubarak yayi yace "bafa sonta kake ba, miye kuma xai dameka dan taki kulaka har yanxu"
Haushi ya kama Mujahid yace "ai bance ina sonta ba, hakuri nakeson bata dan nayi realizing ban kyauta mata ba"
Tsayar da Dariyan Mubarak yayi yace "inada wani plan"
Harara Mujahid yakai mai yace "banso wani absurd plans dinka, tashi zakayi muje gidansu ka gyara abunda ka bata..
Ware ido yayi "ni kuma asuwa mi zance mata..Salma kiyi hakuri nina turo abokina yayi kissing dinki..." Cikin salon rainin wayo da Dariya Mubarak ya karashe maganan.
Takaici ne ya rufe Mujahid, afusace yabar office din, mikewa Mubarak yayi yabi bayansa yana fadin "muje kafin kayi kuka" bai kuma bar dariyan ba.
***
Fitowa Salma tayi haraban gidan, jikinta sanye da cikin red & creamy less, da madaidaicin crem veil yafe bisa kafadarta, Yau bata da lecture, sunyi da su Shehu zasu hadu Central Library yin wani Assignment da aka basu.
Motarta ta shiga ta kunna hade dayin reverse.
Mubarak ne ke tuka Motan, fuskar Mujahid Murtuke cike da haushi dariyar da abokinsa yake, suna shigowa anguwan ya hangi Motar Salma ta fito daga gidan, can hanyar titin gabansu yaga tayi, tab'o Mubarak yayi yace "kai tsayar da motar gatacan ta fito"
Tsayar da motan Mubarak yayi, Mujahid yahau kokarin bude motar dan fita.
Mubarak yace "yaukam indai taki kulaka, ka shareta kawai for good" ln serious tone yayi maganar.
Shuru Mujahid yayi ya fita daga motan, Keke napep yayi saurin tarewa ya fada ciki hade damai nuni da yabimai bayan motar dake can gabansu.
Tuki take tanai bin wakar "Love will Remember" na Selena Gomez, fuskar ta fayau bata da damuwa, bata ankara ba taga keke napep a gefen ta yanai kokarin over taking dinta, tsaki taja ta kuma baiwa motar ta wuta, ta mugun tsanan ayi overtaking dinta, shikam Muhahid sai yiwa mai napep masifa yake akan yayi sauri ya shiga gabanta, wuta Sosai Salma ke bawa mota ayayinda Keke ke binta da Kero, Ranta ya mugun bacci, kwanar Babban high way tabi taga Mai keke baibar binta ba, afusace ta gangara gefen titin hade kashe motar ta fito afusace cin durun uwar sa, tsayar da Napep din yayi gaban motarta sann ya fita da sauri bayan ya biyasa.
   Mutuwar tsaye Salma tayi ganin Mujahid, bata iya taku gaba ba, tayi sauri juyawa bakin motar ta bude murfin, nufota yayi da sauri hade da rike murfi.
Amarairece yace
"Salm plz ki saurarani, we need to talk"
Ko kallan shi batai ba ta dauke kai gefe, fuskarta ta daure tamau.
Hannusa ya daura bisa hannunta dake kan murfin motan, da sauri ta zame nata hade matsawa gefe,
Am sorry" ya kuma fada kaman mai shirin kuka.
Wata civic ce tazo wucewa, har tayi gaba tayo baya, maza uku ne suka fito suka tsaya gaban Salma, dayan su yace "Yammata lafiya kuwa ?
Kaman zatayi kuka tace ba "ba lapia ba, wannan mutumin ke takurani
Mugun kallo suka kaima Mujahid, yace "ba wani matsala kanwatace"
Ware ido Salma tayi tace "nikam bansan shiba, mayb ma dan yankan kai ne"
Tsorata Mazan sukayi, aikuwa suka janye Mujahid suka haushi da Duka.
Da sauri Salm ta fada motan hade da sauke ajiyan zuciya, shegen nacin tsiya ta fada aranta, kunna motar tayi ta maida dubanta baya danyin reverse, abunda tagani yayi mugun girgizata, duka sosai Mazan kema Mujahid kaman an aikosu, shikuwa baya da niyyyan guduwa balle tanka su, jibga kawai suke kaman an aiko su.
     "Oh my God" ta fada cike da kidema, bude motan tayi da sauri ta karasa gurin su.
"Dan Allah kuyi hakuri ku bari, yayana ne" kaman zatayi kuka tayi magana.
Tsayar da dukan Mujahid sukayi hade da kai mata mugun kallo, dayan su yace "dama yayanki ne kika b'ata mata lokacin tsayawa dukan shi, toh kinyi kadan wallahi, sai kin biyamu dan ubanki"
Iya kidima Salma takai, dagudu ta koma mota tadau jakarta, 2k kadai ke ciki da sauri ta ciro ta mika masu, basu karba ma suka raina, hakuri ta basu fir sukaki yadda, wayar ta iphone 7 ta mike masu tace "kuyi hakuri da wannan, it worth alot of Money"
Tsaki sukayi, suka juyawa suka fada motan su suka ja.
Hankali tashe Salma ta nufi Mujahid dake kwance yana tarin wahala ga jini ta baki da hanci.
Akidime ta d'ago kansa bisa ciyarta, duk ta gama gigita tama rasa abunyi, rokon shi tahau yi akan ya tashi su bar gurin kafin maza su kuma dawowa, tari sosai yahau yi kaman wanda zai shid'e, mikewa tayi ta taimaka ya tashi sannan suka karasa motar ta, baya ta bude ta shigar dashin sannan ta fada gaba taja motar.
  Tuki take amma gabad'aya hankalinta na kanshi. Murya sanyaye tace "miyasa baka gudu ba, inda sun kashe ka ya kenan ?
Yunkurowa Mujahid yayi hade da sakin dan kara, hannu yasa ya shafi gefen bakinsa dake jini, dakyar yace "i dont care koda sun kashe ni tunda ke kanki ba kaunata kike ba, gwara na mutu ki daina gani na"
Nisawa tayi tace "ko bana kaunar ka altleast kana da parent, siblings da friends da suke kaunar ka"
Tari ya kuma yi bai iya cewa komai ba.
Ta cigaba "am begging you, don't ever risk your life because of me"
Ciki ciki yace miyasa kikace haka ?
Share tambayan tayi kaman bata jiba, chemist ta tsaya, ta taimaka suka shiga ciki akamai treating ko ina hade da hadomai da magunguna, sun fito ta tambayashi gidansu dan dropping dinsa, can gidansa dake Louis house ya mata kwatance, bata damu ba taja suka kama hanyar gidan, sosai take tausayamai.
    Sun iso gidan, ta rikoshi suka karasa ciki, tsoro ne yakamata ganin cewa shi daya ke gidan, dakewa kawai tayi ta zaunar dashi kan one Sitter dake gurin sannan ta ajiyemai ledar maganin gefen.
  "Mai kake bukata ? Ta tambaye shi
Ruwa yace yakeso dan shan maganin, hanyar kitchen ya nuna mata ta shiga ta dauko bottle wara tare da glass cup, zubawa tayi sannan ta mika mai, hannun sune ya hade tayi sauri sakar mai da cup din, Murmushi yayi yace "ki zauna mana ?
Kai ta girgiza alaman a'a, bai damu ba yahau shan maganin hade da kurban ruwa, Salma kam kuramai ido tayi tana kallon kyakyawan fuskar shi, dukda some part sun kumbura bai hana kyansa fitowa ba, murmushi ta saki adaidai tym din daya kalleta suka hada ido, daburcewa tayi tahau fadin "xan shiga kitchen wanke hannu" da sauri ta juya ta fada kitchen hade da sauke ajiyar zuciya, saida tayi mintuna Uku sannan ta dawo palom, nanta iske shi yana kokarin mikewa tsaye, ganinta yasashi komawa ya zauna yace "na dauka ko bacci kike ai ?
Kaman marar gaskia tace "a'a ni tafiya ma xanyi" kanta na kallon hanyar fita tayi magana..
Yace "inda na mutu ya zakiyi ?
Sai sannan ta kalle shi, tace "ya zanyi kuwa ? Life goes on"
Kallonta yake saidai this tym around bai fahimci komai game da ita ba, yace,
"Amma miyasa kika taimake ni ?"
Tabe baki tayi tace "friends don't abandon friends".
Lumshe ido yayi yace
"Thank you"
You're welcome" ta fada, juyawa tayi takama hanya fita, bakin kofar ta tsaya sannan ta juyo tace "Get well soon" bata jira abunda zaice ba ta fice.
Mikewa Mujahid yayi da axama ya tsaya bakin window kallonta, saida yaga ta shiga mota taja sannan ya ciro wayarsa dake aljihu ya kira wata namba, bugu daya aka dauka.
Cikin  masifar yace " wato kasheni kukai niyyan yi ko ?.
Daga can mutumin daya dauka yace "Oga kayi hakuri, amma ai kai ce muyi making komai ya zama real, thanks goodness yarinyar tayi intervening da wuri.
Dogon tsaki Mujahid yayi ya katse call din.
.
Bayan Kwana biyu da aukuwan lamarin sannan Mujahid ya fara fita office. Bai kuma bi takan Salma ba. Da azahar bayan ya fito sallah Masallacin su na office ya hadu da Salim tsaye yana waya, cike da farin ciki yake wayan, da alamun kuma da mace yake, Mugun Kallo Mujahid ya watsa mai sannan ya wuce zuwa office dinsa, zama yayi yana tunanin kardai da Salma yake waya, haushi ne sosai ya turnuke shi, Wayarsa  ya fiddo ya lalubo lambar salma, son kiranta yake amma baisan abunda zaice ba asalima tun ranar yake saurara kiranta kodan tamai ya jiki, amma shiru. Dabaran Turo mata text msg yayi.
Salma zaune a kan kujerun dake ajiye gefen faculty dinsu tare dasu shehu da wasu yan ajin su suna tattaunawa game da wani course da zasu shiga test, wayarta ke kunnata tana waya da Salim, murya kasa kasa hade da dariya, katse wayan tayi, shehu yace "wannan dariya fah ?.
Tabe baki tayi, tace "yayana ne, lallab'ashi nake yakai min motata gyara ban iya jure shiga taxi"
Yace "kai yaune fah kawai kikazo da taxi, Yayan nan naki kodai dashi zaai ?
Wani mugun kallo takaiwa Shehu, ba shiri yayi azaman kama kanshi, lumshe Ido Salma tayi hade da kallon wayarta wanda tun ranar take tunanin zai kirata amma shuru, tanason sanin ya yanayin jikinsa yake, taso zuwa office din Faiza tambayar ta, saidai ta fasa gudun kar girma ya fadi kasa wanwas.. Karar shigowan sakone ne ya katse mata hanzari, tayi azaman budewa ganin Mujahid.
"Hi, kwana biyu, dafatan kin isa gida Lapia ?
Murmushi ta saki, aranta tace "sai yau ya tuna dani"
Reply ta rubuta mai, "ya jikin ka, kashe maganin?
Dadine sosai ya kamashi, baiyi expecting tamai reply da wuri haka ba.
"Am okay, when are you less busy nazo na maki special godiya for saving my life..
Gabanta ne yafadi, itakam bataso su kuma haduwa da daddare dan kuwa tsoron shi take, saidai kuma tana son ganin kyakyawan fuskan sa, tunani ta hauyi can dai tasamo mafita ta turo mai "ina skull yanxu, zamuyi cA test, kana iya zuwa kasame ni by 4pm"
Yana gani murmushi yayi, Mikewa sukayi suka tafi Hall kasancewar lokacin test din yayi.
***
Hudu nayi Mujahid ya karaso yayi parking can gaba da inda Hall din yake, lumshe idanu yayi yahau zama jiranta.
Cikin nutsuwa Fa'iza ta kankamce office dinta, sannan tadau jakarta ta fito, yau bata zo da motar taba kuma batayi tunanin Mujahid ya fito aiki ba saboda condition dinshi, can gaba da faculty tasamu taxi ta tare shi ta shiga yaja, sun shigo round kenan ta hangi Motarsa, saurin tsayar da taxi din tayi tahau duban motan, saida ta hango fuskan shi ta tabbatar shine.
Murmushi tayi aranta tace "ashe ma yazo daukata" wayarta ta duba bataga call dinsa ba tayi tunanin ko rashin netwrk. Sauka tayi daga taxi din ta nufo motarsa sa cikin sauri.
     Shikam Mujahid kallon saitin gaban shi yake dan ganin tahowar Salma bai ankaraba yaji anbude kofar gefe an shigo, kallon ta yayi cike da mamaki.
Gyara zama tayi tace, "Mjay aida security ka tura office ya kirani, instead of kayi ta jirana"
Bata rai yayi yace.
"Aiba wajan ki nazo ba, kuma am not your driver..
Dariya tayi, cikin rashin kula da yanayin sa tace "wasa kake, gurina kazo kawai haushi zaman jiran da kayi kake.."
Mujahid kam bai iya cewa komai ba, hankalinsa tuni ya koma kan Salma dake tahowa tana duban cikin jarkata tana lulube, komi take nema, oho, yafada aransa, takaici ne ya kama Faiza ganin inda idanuwan sa ke kalla.
ID card dinta take tunanin kota manta a Hall yasata alube, tana gani  ta zuge jakar ta maida hankalinta kan tafiyar ta, murmushi tahau yi ganin motar sa, kadan ya rage ta isa gurin ta lura da Faiza dake hakince kan sit tanai kai mata mugun kallo, gaban Salma ne yafadi, saurin shanye murmushi tayi hade da bata rai, kaman ta fasa karasawa gurin sai kuma ta dake ta karasa saitin gurin da Mujahid ke zaune, kawar dakai tayi gefe tace "sannu"
Kallon ta yayi tamai kyau, kwana biyu nan ya lura ta daina shigar banxa data saba, jallabiya ce baka jikinta tayi rolling da veil din, kallon Faiza yayi da gefen Ido kaman yahau ta da duka, yace "ya test din ?
Haushi ne yakama Salma, "wato bazai ce shigo motar ba nice sanda mai jure tsayuwa, wlh kunyi kadan" aranta tayi magana, Afili tace "Nina tafi sai anjima" kaman zatayi kuka tayi maganar, tafiyar ta tayi bata jira cewar saba.
Tsaki Yaja ya kalli Faiza dake cika tana batsewa yace
"Miyasa kike son janyowa kanki raini, gurinta fah nazo bake ba, anjima kuma idan ta hukuntaki kihau kuka".
Kallon takaici tamai
"Ai tare ta ganmu, kuma ma aina fita matsayi agurinka"
Kasa tankata yayi dan haushi, kunna motar yayi  yaga Salma na kokarin Tsayar da Taxi, dasauri yaja inda take yace "Kizo nayi dropping dinki
Sai sannan ta dubeshi, Murmushi tayi hade da ciro 1k dake jakarta sannan ta nuna mai tace ina da kudin motar haya basai an lab'a niba" karawa gaba tayi abunta.
Kulewa Faiza tayi tace "kaga ja'ira ni take gayawa maganar banza baka ce komai ba"
Dogon tsaki Mujahid yaja hade da watsa mata Harara, yace "ki tafi da motar gida zanzo na dauka" bai jira cewarta ba ya bude murfin ya fita, Sakin baki Faiza tayi cike da Mamaki rashin M irin nasa, k'wafa tayi cikin tsananin haushin Salma sannan ta fito ta zagaya gurinsa ta zauna hade da data motar.
Salma na shiga taxi data tsayar, taji an bude kofar baya inda take zaune an shigo, adan tsorace ta kalleshi, magana zatayi taji yacewa mai taxi su tafi, mamaki ne yakamata, "ina ta sa motar" ta fada aranta, batasan ya fito fili ba..
Lafewa yayi kan sit din hade da fuskan tarta sanan yace "nabarwa Auntyn ki ta tafi gida dashi tunda kinki shigowa.."
Kunyace ta kamata, aranta taji dadin abunda yayi tasan kam Faiza taji haushi, matsawa kadan tayi tahau bude wani handout tada ciro ajakar, Murya kasa kasa tace "ya jikin ?
Shuru yayi baice komai ba, dagowa tayi suka hada ido ta wayance da cewa "ba lafi, bruises dinma sun warke," dauke kai tayi tahau bude pages din handout din.
Dogon ajiyar zuciya ya sauke hade da lumshe ido yace, "Miyasa baki kirani awaya ba ?
"Hmm, nayi bizy ne, soon zamu fara exams"
Magana zaiyi Wayarsa tahau ringing, dubawa yayi yaga hajiya, gabansa ne ya fadi, yaushe rabo dayaji motsin su Hajiya tun randa yabar gida, gyara zama yayi sannan ya dauka, gaidata yayi ta amsa ciki ciki, sannan tace "kazo gida kasameni ina da magana da kai ."
Dafe kai yayi kaman yayi ihu, sanin maganarta batada nasaba da wacce take kusa dashi, murya kasa kasa yace "Hajiya yamma tayi, gobe insha Allahu zan shigo"
"Allah ya kaimu" ta fada hade da katse wayan.
Satar Kallon shi Salma tayi tace "wace ce ?
Yak'e yayi yace "mama nace"
Cike da fara'a ta dubeshi tace "i would like to meet her, wana unguwa take ?
Tashin hankali ne ya diran mai, dakyar yace "ba anan take ba, can Sokoto suke zama"
Harara takai mai cikin salon wasa tace "kodai bakaso nasanta ne, naga ai sister dinka anan take skull.."
Dariya yayi wanda da gangan ya tsiro shi gudun karta dago shi, yace "Amina wai, ai sunyi hutu tama koma gida can sokoto.."
Murmushi Salma tayi tace "ayyo" aranta kuma tana tunanin Amina dayace dan kuwa ba Amina sister dinshi tace sunanta ba, bata damu ba ta kawar da tunanin kasancewar taje gidan shi kuma bata ga alamu yana da yan'uwa ba.
Shuru ne ya ratsa tsakanin su har taxi ya iso gidan su.
Kallon shi tayi, gabadaya baya cikin hankalinsa, tabosa tayi, adan firgice ya kalleta, murmushi tayi tace "kana da abun dariya, kodai dukan yafara tab'a kane.."
Murmushin k'asaita yayi, irin wanda yake fizgar zuciyar wanda aka yiwa.
Yace
"Kije ki huta, i'll call you later"
Okay, bye ta fada ta fice a mota.
  .
Gidan su fa'iza ya wuce amsan motarsa. Isketa ta yayi tsaye haraban gidan jingine bisa motar. Da ganin sa tahau cika da batsewa, cikin koya kula da yanayin ta yace tabashin mukullin. Kaman zatayi kuka tace "Mjay miyasa zaka min haka gaban yarinyar nan, shikenan ta gama raina ni yanzu gani zatayi daidai nake da ita tunda kana kulata"
Kallon takaici yayi mata.
"Keda ita ba d'aya bane, you're my friend ita kuma she is nothing.."
Cikin rashin gamsuwa da kalamansa ta tab'e.
"ban yadda ba saboda dazu kallon da kake mata baiyi kama da babu komai ba, kuma na tabbata ka fara sonta"
Murmushi gefen baki ya saki wanda shi kadau yasan manufarsa, yace "tabbas na kamu da sonta saidai son da nake mata baikai na kasance tare da ita ba, kin dauka zan barta taci bulus ne bayan tamin rashin mutunci "
Nisawa Faiza tayi, aranta batai na"am da koma mai yake niyyan yiba, tunda har ya furta yana sonta ba lailai ne ya rama abunda zaiyi ba
"What are you planning ?
Girziga kai yayi yace "i dont know yet, ina dai tunani gagarinmin abunda zanyi na koya mata hankali, so nake tayi kuka da idanta"
"Daganan kuma saika rabu da ita kenan ? Faiza ta fadi.
Tsaki yaja
"Kinga enough of your questions, you're just a friend banaso ki wuce limit dinki" ya fada, amshe mukulli hannuta yayi ya fada motar yaja ya barta nan tsaye baki sake cike da takaici.
Salma na shiga Gida daki ta wuce ta kwanta, zuciyar ta fal da farin ciki,   tunanin Mujahid take tana tuna farkon haduwa su izuwa yau, kwata kwata takasa gane kanta, shin sonshi take komi, kullum dashi take kwana ta tashi, girgiza kai tayi, sam babu lissafi soyayya aranta, bata tab'a yi ba saidai na baya data gani sun wahalu daga karshe ma tsana ce ta biyo baya shiyasa take bala'in tsoron fadawa soyayyar wani. Tana son Mujahid  amma bazata nuna mai komai ba ayanxu har saida tabbatar he won't break her heart.
****
Tun daga ranar lamari ya canza tsakanin su, soyayya da kulawa sosai Mujahid yake nunawa Salma saida bai fito yace yana sonta ba, har ilah yau bai kuma canza kudurin sa na koya mata hankali ba, ta bangaran Salma kuwa zuciya daya take zaune dashi takan yi mamaki sai kace ba kwanakin baya suke casa juna ba, aranta takanyi tunanin anya kuwa Mujahid baida wani mugun nufin akanta, saurin kawar da tunanin take saboda tsananin yadda yake damuwa da lamarinta.
Daddyn Salma ne tare da Ja'afar a office dinsa. ja'afar yana daya daga cikin lauyoyi da Alhaji Abbas ya aminta saboda tsananin rike gaskia da Tsoron Allah da yake azuciyarsa, sau tari yawan idan zaiyi harkar canji da dollars ko euro yafi yadda da damk'awa jaafar takardun shaidan komai dan yasan bazai cucu saba.
Zaune suka suna magana akan wani fili daya siya a Kaduna, copy na takardu shaida da komai ya mikewa Jaafar, karba yayi yana dubansu
Daddy yace "ka adana su da sauran"
Hade takardun jaafar yayi cikin briefcase nasa sannan ya mike da niyan yimai sallama, dakatar dashi Daddy yayi hade da cewa "ya maganar mu ta kwanaki, naji shuru baka kara waiwayar zancen ba.."
Zama jaafar yayi had'e da kirkiro murmushi dole, shikam yama manta da zancen, shuru yayi yana tunanin zancen da neman amsar bawa Daddy, bazai yaudari zuciyan saba dan kuwa yana son Junaina, saidai kuma ba damuwa tayi dashi ba ga kuma Daddy da yakeson ya hada shi da Diyar shi dako sanin ta bai yiba balle ma yasota, shi kuma auran bayama cikin lissafinsa yanzu kokarin Nemo Ummi kawai yake dan farin cikin hajiyarsu kuma baima isa ya tunkareta da sunan yana son aure ba, ana takai wa yake ta kaya.
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhaji wani hazari ba gudu ba, maizai hana mu hadu da diyar taka, idan ta amicin dani saina yadda karya zamana ko tana da wanda takeso"
Farin ciki sosai ya lulube Daddy, kasancewar ta bangaran Salma ba matsala koda batason Jaafar yasan zata mai biyayyah, kuma ma baiyi tunanin Salma nada wani da takeso ba.
yace "ba matsala, gobe kazo gidana mu kara tattaunawa saika ganta
Yake jaafar yayi aranshi yace "Allah yasa karta aminci, afili yace "saidai yau nazo, saboda gobe da safe ina da aiki a Kaduna"
"ba damuwa, Allah ya kaimu zuwa dare" acewar Daddy.
Godiya yama Daddy sannan sukai sallama ya fice azama.
Tun ranar da Hajiya ta kira Mujahid tace yazo gida bai samu daman zuwa ba sai rana ta yau acewarsa aiki yamai yawa bacin kuma da gangan yaki zuwa.
   Fuska ba yabo ba fallasa Hajiya ta tarbeshi, nan tahau mai fadan barin sa gida akan abunda baikai ya kawo ba, Mujahid kam shuru yayi yana sauraran ta dan ya kagara ta gama ya wuce aikinsa, tace "Bani hotunan Ummi dana baka kwanakin baya"
Sosa keya yayi alamun marar gaskia yace "mi zaai dasu, an ganta ne ?
Hajiya tace " baa ganta ba, kawai hoton zaka bani tunda ba nemo ta zakayi ba, tuni Jaafar ya dukufa da nemo ta kuma am sure zai samota aduk inda take"
Ware ido Mujahid yayi adan kidime yace "jaafar zaki bawa hoton ?
Mugun kallo takai mai, tace "ko babu hoto Jaafar yasan fuskan ta, kaida ba saninta kayiba yasa na baka hoton"
Gabansa ne ya fadi, fatan shi Allah yasa kar Jaafar ya hadu da Salma, nisawa yayi yace "Hajiya basai jaafar ya nemo taba, nida kaina zan kawota gidan nan very soon."
"Ka ganta ne" Acewar ta.
Kai ya girgiza alamun a'a, aranshi yace "ki bani time very soon zaki ganta amma saina koya mata hankali yadda idan ta shigo gidannan bazata yadda ki had'ata aure da niba".
Tashi yayi ya mata sallman zai wuce office ya fice waje, nan suka hadu da Junaina ta dawo daga gidan wata kawarta dan tuni sun gama Neco.
   "Yaya kyan tafiya dawowa" ta fada tana dariya.
Tabe baki yayi yace, "ce maki akayi nadawo"
"Oh Allah, he will never change, ni ina can ina missing dinshi amma koya kula dani" aranta tayi maganar, Afili tace "yaya akwai abunda nakeso kasani, sumtin is going on in this house"
Kallon gefe yayi babu mai dubansu sannan ya jata gefe danjin wana abu ke faruwa, sau tari dama ita ke kaima rohoton abubuwan dake faruwa agidan dan ba zama yake ba.
Murya kasa kasa tace "bansan full story dinba, naji dai Hajiya na Waya da Aunty Bilkisu akan wani abu, i dunno ko kudi ne ko gida ko kuma ince sumtin is missing i dont really know, naji Hajiya tace tunda kai kaki nemo wa idan ya jaafar ya nemo shi zata 
bawa ta fasa baka"
Hankalin sane ya tashi danya gane inda Zancen ya dosa, saidai bazai bari Jaafar yaga Salma ba much less ya yadda da auran suba.
Dakewa yayi yace "little sis kinsan mi zakimin"
Kur tayi tana kallon shi, yace "inaso ki sawa Jaafar ido, idan kinji yana waya akan wata mace ko bincike ki bani feedback kinji"
Kai ta girgiza alamun toh, murmushi ya sakar mata. "yauwa my beautiful sister, you know i like you alot"
Dariya tayi tace "nidai yaya kadawo gida plz, wlh i missed you alot".
"Karki damu nakusa dawowa"
Dadi sosai taji, sun jima yana biyeta sai shagwaba take zuba mai daga bisani ya lallab'a ta ta tafi ya koma motarsa yaja yabar gidan.
   Tuki yake yana neman mafitan yadda Jaafar bazai hadu da Salma ba, idan yayi sake kuwa yanaji yana gani zaiga Salma a gidansu, dabara ce ta fadowa mai yadau waya hade da dailing no din Salma.
Alokacin kuwa had'e book dinta Salma tayi cikin jakarta sannan tabar dakinta, gurin Mom ta shiga ta mata sallama ta fito cikin sauri, library na skull takesan zuwa karatu saboda jibi ne zasu fara exams.
    Kokarin bude motar tayi taga kiransa, murmushi tayi ta dauka.
Daga can Bangaran cikin sweet voice dinshi yace "Angel of my life, son kowa kin wanda ya rasa"
Dariya tayi kasa kasa, tace "ka fara koh, how am i even sure am your angel"
Yace "believe me, ba karya nake ba, idan ma baki yadda ba God knows it.
"Kaga ni library zani, inada exam jibi, kana ina?
Yaji dadi abunda tace, aranshi yace "perfect, nasan abunda zanyi"
Afili yace "ina driving, ki jirani nazo nayi picking dinki saimuje inda babu wanda zai dameki dan kisamu kiyi karatu, nasan ki da tsokana kar kije kiyi dambe da mutane a library" karashe maganar yayi cikin zolaya.
Shagwabe fuska tayi kaman yana ganinta, tace "nifah bani da tsokana, ko dambe ban taba yibaaa.."
"Hmm, kedin, ki jirani am coming" katse call din yayi, ta fita can bakin gate jiran shi, baafi 20 mins ya karaso ta shiga motan ya kama hanyar office dinsa, tagane hanyar, tace "lailai ma office dinka ne bazaa dameni ba?
Wani shumin kallo yayi mata da saida taji shi a kwakwalwar kanta, murya kasa kasa yace "duk wanda ya dameki cikin cell zan wurga shi..
Ware ido tayi adan tsorace, "cikin cell sai kaca a film"
Dariya yayi bai kuma cewa komai ba ganin yadan tadan tsorata, suna isa parking yayi, suka fito suka shiga elevator har zuwa cikin office dinsa, ita batama san akwai elevator ba kasancewar ta stair security yabi da ita kwana kin baya.
    Office din babba ne mai shegen kyau can gefe inda Couch da center table yake takarasa ta zauna shi kuma yA karasa gurin table dinsa ya zauna kan kujerar sa hade da fara aikin danna laptop din gabansa, sosai yaci serious da abunda yake batare daya dubi Salma ba.
   Itakam abunda take so kenan, bude handout dinta tayi ta dukafa da karatun General studies da suke dashi.
      Bayan kaman awanni uku Mubarak ya shigo office din, ganin Salma yasashi dariya, zama yayi gurin mujahid yana zolayar shi murya kasakasa, b'ata rai Mujahid yayi, yafara magana cikin fad'a, duk ahankali suke magana, Salma bataji komai ba kuma bata damu dason jiba, sund'an jima sannan Mubarak ya fice office din.
Gyaran murya yayi, Salma ta dubeshi
Yace "bani labarin samarin ki ?
Dariya tayi
"Banda saurayi, infact ni bana soyayya"
"Miyasa ?
Ajiye pen din hannuta tayi hade da yin tagumi, amaraice tace "Sanadin So Ummata tasha wahalan rayuwa, daga karshe ma Abbana ya rabu da ita da tsowon ciki, bansan lokacin ba, bansan anyi ba amma ayadda naji labari yadda komai ya faru yasa kwata kwata na cire so araina"
Kallon tausayi yayi mata, tunda yake gida bai tabaji labarin Ummanta abakin Hajiya ba, saidai zaiso sani..
Kaman wanda baisan da rasuwan Umman ba yace "ina umman take ?
Kaman zatayi kuka tace "ta rasu, lokacin daban santa ba, i was 3years old tym din".
Maida dubansa Mujahid yayi bisa laptop din yace "bai kamata ki cire so aranki ba, tunda iyayan ki daban ke daban"
"Hmm, am sacred banso ayi breaking heart dina"
Shuru Mujahid yayi baice komai ba, bayason cikata da surutu, bari yayi sai kuma gobe ya kara jeho mata wata tambayar.
    Cigaba da karatun Salma tayi, lokaci Sallah azahar nayi ya nuna mata toilet dake office din sannan yafice zuwa masallaci, bayan ya dawo ya tura aka kawo wa salma abincin take away, godiya tayi.
Karfe bakwai Daddy ya dawo Gida, nan ya tsarawa Mom batun zuwan Jaafar, sosai taji dadi da batun daddy dan kuwa ta kagara Salma tayi aure ko zata nutsu, nan daddy ya shaida mata bayan Sallah Isha'i Jaafar zaizo ganin Salma, dadi sosai taji, wayarta tadauka dan kiran Salma.
Bayan Salma ta idar da sallar Magrib, Qur'an dake ajiye a office din tadau  ta karanta sannan ta ijeye ta cigaba da karatunta, lokacin Mujahid yafita masallaci bai dawo ba, kirar Mom tagani tayi azaman dauka.
Aladab ce ta gaidata, Mom ta amsa sannan tace "Salma kibar duk abunda kike kidawo gidan yanzu nan, Daddy zai baki wani Surprise"
Farin ciki ne ya kamata, tace "momy miye ne, dan Allah gayamin i cnt wait saina zo"
Dariya momy tayi tace "idan kinason sani kizo maza yanzun nan, kuma kiyi sauri" katse call din Mom tayi, cike da Murna Salma tahau tattare books dinta ajaka, Mujahid ne ya shigo, ganin tana hade komai yace "keda kika ce sai 10 zamu tafi, kin fasa ne ?
"Eh nafasa, kaini Gida" cigaba tayi da hade komai zuciyar ta fal murna.
8.20 Jaafar ya iso gate din Gidan Daddy, bai tab'a zuwa gidan ba yasa yakira Daddy awaya dan tabbar da gidan ne, nan take Daddy ya kira mai gadi aka budewa mai gate ya shigo gidan, cikin palo gidan Daddy yamai iso, ya shiga yagaida Mom aladabce, sosai mom ta yaba da hankalin sa, sun gaisa sosai, mai aiki ta kawo mai na shasha baki, shikam Jaafar gaban sane keta faduwa, har yayi dana sanin kowa kanshi gidan.
Mom kam murmushi kawai take tana saurara isowan Salma....

0 comments:

Post a Comment