Blogroll

BANNER 728X90

Thursday, 8 February 2018

ALJANA CE KO MUTUM Page 31-40

ALJANA CE KO MUTUM Page 31-40
.
ji yayi anta6a shi' yayi saurin bude idanunsa  yana  cewa nawwara kece kikazo, sai kuma yaga ashe kanwarsa ce mimi,  yace au sorry, auta ya akayi ne, mimi ta karasa zama  wajenda yake, tare da cewa hamma nah lallai kayi zurfi sosai  acikin son aunty sameera.
  
yayi murmushi, hamma pls karage wannan son da kake mata" don karya maka illa, don so bala'i ne idan yayi yawa , cikin mamaki yake kallon auta mimi, yace auta badai harkin fara soyayya ba?

me kagani hamma , yace to inba hakaba' tayaya kikasan so yanada illa idan yayi yawa?  dariya tayi tace kai hamman aiba abin mamaki bane don nasan kalmar so' da illar zurfafawa acikinsa" idan kayi la'akari da yanayin zamaninnan namu" damu yara muke tashi da kallace² ko karance²n littafan soyayya'    yace a lallai mimi  naga alama kin isa aure.to ke a ina kk san ma'anar so?
.
kai hamman ni bance aure nakeso ba, kawai dai nasan kalman sonne abakin kawayena dayake duk suna da samarai,  nice dai bana kula samari ,kuma suna bani labarin samaransu da irin sonda sukema juna, baki ta turo tace sannan kuma ma ai na isa auren tunda shekarata 17 yanxu, tana fadin haka tabar dakin da gudu don kunyar yadda taga yayannata ya kafeta da ido" saida takai kofa tace Dr awwal ne ke nemanka, OK, cemasa yashigo.
.
awwal  yashigo dakin da sallama nawwar ya amsa mai, bayan ya zauna suka gaisa , awwal yace wato kananan kana wannan banzan tunanin naka ko, hmmmm ajiyar zuciya nawwar ya sauke,  yace awwal ya kamata muje Kaduna plx, don zuciyata bazata iya hakura da sameera ba" ina so in fada mata abunda ke raina koda bazata amince min ba, zandai fad'a mata ne ko zuciyata ta daina zuginda take" awwal yace hakan ma yayi  inshaAllahu nasan zata amince maka. kai dai kacigaba da addu'a,.

yau jumma'a sameeratu zaune adaki suna hira da zainab kanwarta da umman su,  khadija tayi sallama tashigo, tare da gaida umma,  zainab ta gaisheta, umma ta basu waje, zainab kuma ta tashi don shirin zuwa islamiya, khadija tace sameera result  dina ya fito fa, na jamp kuma nasamu, nawwara tace natayaki murna sosai, nima abbana yace yaba da kudi azana min lokacin da su zainab zasuyi, khadija tace uhumm kedai nawwara  babana yace na fitar da mijin aure inyaso daga baya naci gaba da karatun adakin mijina.

sameera tace haba dai' kice  zamusha biki sosai, to waye gwanin naki! dry khadijat tayi" tace kema ai kinsan idan ba  mallam abdullahi na islamiyar muba sai rijiya mai kwalabe, dan ustaz dina, lallaima khadija, wato auren ma yakusa, shine sai yanxu kk gayamin" tayi murmushi, kedai bari kawai zamusha bikin ustazai".
.
Kema nawwara yakamata ace kin fidda mijin kafin abbanku ya miki maganar aure, kinsan halin tsofaffinnan namu" sameera tace kayya keleni nikam, ni haryanxu banga wanda nake soba, kai sameera baza ki daina ruwan ido ba ko,kina son zainab ta rigaki aure ne, to inta rigani sai me dubu nawa suke aure subar yayyen su, uhmm to mudai bamu fatan hakan ta kasance, sameera tace kinganni nan wlh ni soyayya ma tsoro take bani, ki kallafa kawar mu murja yadda nasan suke zabga soyayya da nasir dinta amma farad daya ya juya mata baya, ya nuna bai santa ba, sbd ya had'u da wacce tafita, duk gashi tazamo abar tausayi, kai al'amarin  maza yana bani tsoro wlh" Allah dai ya zab'a mana mafi alkhairi, ya bamu mazaje nakwarai, wayanda zasu rikemu da Amana amin.

sameera tace nikam ki dan rakani gdan yaya sauda mana , ina son kai mata kayan dinkinta ne wanda na karbo mata, khadija tace OK ba matsala sai muje, bayan tasanar da umma tace Allah ya kiyaye hanya , adai dinga addu'ah duk inda za aje, to umma in Allah ya yarda.

suna cikin tafiya sai sukaji wani sassanyar murya mai dad'in sauraro abayan su, ana cewa Assalamu alaikum, gaba ki dayan su suka amsa tareda juyowa,  zaune yake akan mashin dinsa  (wanda ake ce ma wayyo kudina) sanye yake da shadda pink clr wandansa dai² idon sahu , fuskarsa  dauke da saje wanda ya kwanta luff² gwanin sha'awa, idonsa  sanye da tabarau'  kallonsu yake cikeda annuri a fuskarsa"  atakaice dai ustaz ne  kyakkyawa ajin farko.
.
ya karaso wajan su nawwara, yace inbazaku damu ba  kudan bani minti biyu don Allah' nawwara tayi saurin cewa bakomai muna jinka, Khadija ta kalli nawwara da kyau cikin mamaki, abunda bata tab'a ganin nawwara tayiba kenan, yace da farko nidai sunana Yusuf mahammad ni dalibi ne a makarantar state universty (kasu)ina karantar islamic studies Kuma ni mazaunin kinkinau ne, ina yawan zuwa nan layin wajen aboki na,  Allah ne  ya hadani daku kuma take naji ina sonki kuma da aure nake sonki shiyasa bantsaya maki kwana2 ba' sonake  kizamto uwar y'ay'ana, khadija ta katseshi da cewa wacce daga cikinmu? yace wannan kawar taki yanuna nawwara, itako nawwara tunda yafara zance shitake kallo muryarsa mai dadi take sauraro' yadda yake fitar da lafuzan cikin kwanciyar hankali,  murmushi tayi,

shima ya maida mata da martani, ya kuma cewa ko zan iya sanin gdan Ku do nakawo miki ziyara, naga kamar tsaida Ku danayi anan bai dace ba , nawwara tace ba matsala, nan tayi mishi kwatancen gdan nasu, tare da fada mashi sunanta, sukayi sallama suka wuce.

sameeratu ta kalli khadija wacce ke binta da kallon, tace dijana yau naga irin mijin danake burin  aure arayuwa ta, yusuf yamin sosai khadija, khadija tace ikon Allah , kice faraddaya har kin kamu, amma gsky zaku dace, course din dakike son karanta gashi shima shiya keyi, amma nataya ki murna Kawata, nima naji ya kwanta min arai, suka tafa nawwara kamar an sata a aljannah"" Allah sarki nawwara ko ya zaiyi.

awwal ne da nawwar agaban mahaifin sameera sun zayyana mishi abunda ke tafe dasu, kuma yaji dadi sosai, dan yasan nawwar me kaunar yarsa ce, ko bayan ranshi baza tayi kuka da idanunta ba, yace musu shibashi da matsala, ya amince masa ya nimeta, idan sun sasanta kansu shikenan, sunji dadin maganar abban, Alhaji idrisa yasanar  da hjy maimuna itama ta nuna murnan ta, nawwara taji lbarin zuwan su nawwar, inda ummanta tace taje su gaisa,, don ba wanda ya fada mata abunda ke faruwa, su awwal na zaune a falo , sameera ta shigo cikin sallama. ta gaishesu cikin faran faran,  har suna zolayar juna, awwal yayi gyaran murya, sannan yafara jawabi game da abunda ke tafe dasu, ji yayi tace SO kuma da karfi.

.
so kuma, gaskiya ina jin kunyar ku, abar maganan nan dan Allah, awwal ya miki don basu waje" bayan fitarshi nawwar yace sameera Allah ne ya jarabce da sonki, bani na Dora mawa kaina ba, sannan kuma ke kika shigo rayuwata.

nawwara bazan takura ki soni ba, amma kuma rasaki arayuwata akwai Matsala, sameera munyi soyayya dake alokacin daki ke aljanna sosai amma yanxu wannan soyayyar ta rushe, Allah sarki dama da zata dawo, sameera ki zauna kiyi tunani sameera, idan nawwar ya dace da rayuwarki ki sanar dani idan kuma bai dace ba  kisanar dani ga katin number nah, cikin raunanniyar murya yace nawwara karki manta ina sonki ina kaunar, koda baki aureni ba bazan taba mantawa dake ba.

yana gama fadin haka ya fita yana share kwalla, awwal yace kayi hakuri Dr komai mukaddari ne Daga Allah, idan Allah yasa nawwara matar kace to tabbas ba makawa sai ka aure ta, idan kuma ba matar ka bace to sai ka fawwala ma allah lamarinka.

jikin nawara yayi sanyi da jin kala man nawwar don ya bata tausayi, amma kuma ita zuciyar ta Yusuf yake so, baza ta iya rabuwa da Yusuf ba.

bayan kwana biyu, sai ga Yusuf ya zo gdan su sameera , lokacin kuma Alhaji idrisa zai shiga GDA suka hadu Yusuf ya mai sallama, tare da durkusawa kasa yana gaishar da alhajin, Alhaji yace bawaye kaba dan samari, Yusuf yace dama nazo wajen Kane abba.

to bismillah mushiga har falo suka shiga yusuf ya zauna akasa,Alhaji yace me ke tafe dakai ne dan samari, nan Yusuf yafada mawa Alhaji komai game dashi, da kuma abunda yazo nema.
.
Alhaji ya gamsu da maganan Yusuf , kuma ya yaba da halinshi, yace yusuf inta wajenane babu matsala, sai Kane mi ita sameeran in kun daidai ta shikenan, Allah ya muku albarka, amin abba, nagode sosai.

bayan shigan abba cikin gda yace zainab tafada mawa nawwara tana da bako afalo Yusuf, nawwara naji taji dadi yarufeta sosai tasha kwalliya tafeshe jikinta da turare, tashigo cikin falon cikin sallama, ya amsa mata"" yana murmushi, itama ta maida mai da martani.

a'a gimbiyata kin karaso tayi murmushi  barka da zuwa habibina dafatan kana lfy, lfy lau , gsky naji dadin ganinki sameera,  Allah ko, eh mana malamina kenan, cikin zolaya  yace taya ya nazama malaminki.

ta kanne ido daya cikin shagwaba tace SBD zaka dinga koya min kalaman soyayya , kasan ance ustazai sun iya soyayya, ko ba haka ba aris dina, yayi dariya, baki da dama gimbiyata.

soyyay tayi karfi tsakanin nawwara da Yusuf, har ta kai da ta manta maganan da sukayi da nawwar, abvanta yasa aka kirata, yace mamana nikam wa aka tsayar ne amatsayin mijin?

tarufe fuska alamun jin kunya,  abba ni Yusuf nake so ,   kintabbata mamana, eh abba, , Alhaji yace kije kiyi tumani dai mamans, ki nutsu, kiga waya fi dacewa da rayuwar ki, to abba, tafita dakin tana tunanin maganan abba.

nawwar ne akwance cikin matsinacin wani hali yau kwana biyu bashi da lfy amma yaki yabari asani, turo kofan akayi, yana kwance cikin bargo sai rawan sanyi yakeyi, Mami hafsat ne ta karaso cikin Saudi tana nawwar lafiya naganka a kudundu ne.

zaiyi magana ne sai tari ya sarke shi, jinine ya dinga fita Daga bakin sa Mami ta rude, tana hamma meke damunka, ka boye bamu sani ba, tana ganin kamar numfashin shi yana sama, tasaka kara, Allah yaso sulaiman bai fita  ba, duk suka shigo harda Mimi, mami tace sulaima kusa shi amota mukaishi asibiti, , Mimi sai kuka takeyi ,nawwar yayi ma Mami alamu da hannu tazo daidai saitin bakinshi, yana cewa Mami kiyafe min, kwanana ya kare , dib sai taji shiru, Mami tasaka wani uban ihu, tuni ta sumu. innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kulli nafsin za ikatul maut.

,
An wuce da nawwar asibiti da gaggawa, sulaiman ya kira awwal yasanar dashi, sun amshe shi don ceto rayuwar sa, Mami kuma Mimi ce tayayya fa mata ruwa, ta tashi tana kuka, , tace Mimi nawwar ya rasu ko?

Mimi tace suna asibiti da yaya sulaiman, Mami tace maza tashi muje, a'a Mami ki kwanta ki huta ni zanje, insha Allah hamnan zai tashi da izinin ubangiji"" kai Mimi bazan iya zama agida ba ban San awani hali nawwar yake ba.

To Mami tashi muje, lokacin dasu Mami suka karasa asibitin suka CI karo da sulaiman , yana safa da marwa acikin asibitin"" , yana jirin fitowan likita, Mami tace sulaiman ya ake ciki ne, hamman ya rasu ko, yayi saurin cewa a'a Mami yananan da ransa addu'a yake bukata.

suna cikin magana ne Dr awwal yafito duk suka dumfaro shi Mami tace Dr lfy. yace karku damu mun samu kanshi yanxu hakama yasamu bacci insha Allah , zai dawo yadda yake karku damu.

Mami ta sauke ajiyar numfashi tace mun gode , dukkan su suka shiga dakin dayake yana kwance, Mimi ta karasa wajan gadonshi tarike hannun shi, tana Allah sarki hamman na, adalilin son nawwara ka kamu da wannan cuta, hamman na isha allahu nawwara matar kace INA ji ajikina.

sameeratu zaune adakinta ita da khadija, tana bata labarin abunda abbanta yace mata, khadija tace sameera me kika gano cikin maganar abba, na lura abba yana son na mijin dazai rike mishi ke sosai kuma ya kauna ce ki, shiyasa yace kije kiyi tunani.
.
hakane Indai wannan AI nasamu, tunda ga Yusuf yana matukar sona hakane, yauwa nawwara nikam ya zancen maganar nawwar ne, nawwara  tace ni Sam na manta da wani nawwar ma.

khadija ta kalleta da kyau tace sameera inda zakiji ta tawa ni aganina, duk duniyar nan babu mai sonki kamar nawwar, shi yafi dacewa da yazamo mijinki, ki kalla fa irin kasadan da yayi adalilin sonki, ya kamata kixau na ki duba zancena.

sameera tayi shiru kamar mai tunani, sai alokacin ta tuna da katin numbern wayan daya bata, ta sauke ajiyar zuciyarta, Allah dai yashige mana gaba amin, cikin mafarki sameeratu taji kamar ana ce mata.

sameeratun nawwara karki yada soyayyar da nawwar ya miki kimishi halarci, shine masoyinki na asali, mai kaunar ki, mai tausayinki, kuma shine mijin da iyayenki suke son ki aura ki daure ki amshi soyayyar sa, don yanxu haka yana cikin wani hali kitaimaki nawwar dan Allah.

tayi saurin bude ido tana dube dube cikin tsoro ta kudundune tana addu'a.

nawwar zaune a asibiti ya samu sauki Mimi na bashi abinci abaki tana mai hira yana dariya, Mimi tace hamma dan Allah ka daina dumawa in Allah y yarda sai ka auri aunty sameera, yayi murmushi, yace Allah ya yarda yar kanwata.

ansaka ranar auren nawwara da Yusuf sai shirye shiryen biki akeyi, abun mamaki kuma Sam nawwara bata zumudin yin auren Yusuf din , hankalinta na kan nawwara.

tana son sake ganinshi don tasan halin dayake ciki, SBD tana tayawan mafarkai mafar kai, duk ta sukurku ce.

biki sai matsowa yakeyi nawwar kuma ya warke amma har yanxu yana tunanin nawwara, kuma gabanshi na yawan faduwa, addu'oi kawai yasa gaba.

yau jumma'a ya kama ranar auren sameeratun nawwara da Yusuf, wajen daurin aure ya Tara mutane da dama ga ustazai ango Yusuf sai washe baki yake.

.
Ango Yusuf sai washe baki yakeyi, yayin da abangaren amarya ji take kamar tayi hauka saboda bakin ciki, jitayi bata son auren"" hankalinta y karkata kan nawwar.

tana son ta kuma sashi a ido kafin akaita dakin aurenta, khadija ne ta dafata tace lfy nawwara kike irin wannan tunanin? tun da'zu  nake miki magana amma hankalinki ya tafi wani wajen, gashi baki shirya ba kuma kin San ana sauko Daga daurin auren abokanan ango wajenki za su zo.

sameeratu ta sauke ajiyar zuciya tace khadija kin San Allah Sam bani son auren nan da da yadda zanyi Dana warware auren, vaki galala khadija ta bita dashi cikin mamaki.

tace nawwara kinsan me kike fada kuwa anya kina cikin hankalin ki kuwa?bafa auren dole ake miki ba, ke kika zaba mijin da kanki, ko kin manta ne, nawwara tayi murmushin da bai kai ciki ba, tace tabbas ni nazabi Yusuf daya zama mijina amma kuma yanxu Sam bani sonshi , hankalina y karkata kan nawwar, ina son Insan halin dayake ciki khadija.

sai ga hawaye yana gangaro a idanunta, ni ban San meke damuna ba, da nayi tunanin Yusuf shi yadace da rayuwata, sai Daga baya nagane, nawwar shine mijin dayafi dacewa dani, shine mutumin daya kaunace ni tun fil azal, har gida ya biyu ni, yana rokon barar soyayyata, ayayin da idonshi cike da hawaye, muryar shi adaushashe.

kalma na karshe daya furta min yace nawwara koda baki aureni ba, bazan taba daina sonki ba har abada, taci gaba da kuka , tace khadij sai yanxu nasan ina son nawwar fiye da yadda kike zato, amma ina lokaci yakure, nayi Dana sanin da banta bayi arayuwata ba khadija.

takara fashewa da kuka, khadija na lallashinta da ban hakuri, dakyar tasamu kanta har tashirya, alokacin kuma abokanan ango da shi angon sun isu har an daura aure.
.
Abangaren nawwar kuma tunda aka daura auren nawwara gabanshi ke fadi sai addu'oi yakeyi, duk kan su suna zaune afalo suna hira Mami da nawwar da sulaiman da Mimi, duk sunsha ado, Mimi tace hamman na yace na'am autar Mami, yau zan maka wani kyauta Dana Dade ina son in maka, yace Allah ko,.

eh mana ko bakaso ne, me zai hanani son kyautar da autar mu zata min sai suka saka dariya, yauwa hamman nah, shiyasa nake sonka, amma menene goron albishir dina, yace duk abunda kike so zan baki.

tace ko menene natambaya zaka bani , sosai ma, to shikenan Allah y kaimu anjima, Mami yaya sulaiman duk kuna shaida ko, suka ce muna sheda Mami tace Mimi yau yaushe zaki fitar mana da mijinki mugani , cikin shagwaba Mimi tace kai Mami dudu du nawa nake, amma koda yake nayi sabon saurayi very soon zaku Ganshi, sulaiman yace Allah yashirye ki Mimi Sam baki da kunya, agaban mu kike wannan zancen.

cikin shagwaba mimi tace hamman kana jin yaya sulaiman ko, yi hakuri rabu da sulaiman yana kishi ne din jiya budurwar shi tace bazata auri mai gemu ba sai ya aske, duk kan su suka kwashe da dariya.

karfe  biyar na rana inda za awuce da amarya gdan angonta dake kaduna , bayan iyayenta sun mata nasiha sosai tayi kuka rabuwa da iyayenta jitakeyi kamar ta gudu, da zainab kanwarta akatahu da khadija sai aunty sauda da kanwar baban su.

sun iso Kaduna lfy Inda aka wuce da amarya gdanta dake malali halliru dan turo, gdan da aka kai amarya ya basu mamaki, gdane tsararre komai nashi dadai, amma kuma basuyi zaton yasuf yana da kudi hakaba, SBD dan makaranta ne shi.

baki an vasu dakin daza su kwana ita kuma amarya tana dakinta tsakiyar gado sai sheshshekar kuka takeyi, tana bakin cikin kasan cewarta haka amatsayin matar Yusuf.

Mimi ce tace hamman kai fa muke jira sulaiman ma yashirya Mami tace nikam wai ina zaku hakane, wlh Mami wani waje zamuje, sai ga hamman ya fito cikin tsadacciyar shadda Wanda Mimi ta dinka mishi sai kamshi yakeyi, yafito a fillon shi saf, duk kansu sunyaba da kwalliyarshi, don yayi kyau, kamar wanda baida damuwa.

hon din mota sukaji awaje awwal ne shima yazo dashi za atafi, dukkan su suka fito haraban gdan , suka shiga muta suka wuce, hon sukayi mai gadi ya bude musu suka shiga cikin gdan, nawwar mamaki ne yacika shi, inane nan kuma, Yusuf ne da abokinshi suka karaso cikin murna suka tarye su, yayin da aka masu ISO cikin gda.

mimine tace hamman dina kaga wancen dakin to kashi ga kyatar Dana maka yana ciki , dan Allah ka isa ga kyautar nan hamma n kuma kamin alkwarin zaka karba kyautar nan.

yayi murmushi me hade d mamaki yace ya amince, yakarasa wajen daki gabanshi sai faduwa yakeyi, yabude dakin tare da sallama, nawwara dake kan gado taji gabanta ya fadi don bazata iya manta muryannan ba, icon nawwar ya sauka akan abunda ya hango kan gado yana mamaki yakarasa wajen batare da ta dago ba, kirjinshi na har bawa itama haka , cikin tsoro yasaka hannu ya  Daga gyalen dake rufe afuskar nawwara dago kai tayi, suka hada ido da nawwar kowannan su ya zaro ido waje cikin tsoro.

0 comments:

Post a Comment