Blogroll

BANNER 728X90

Sunday, 4 February 2018

BUDURWAR KAUYE Page 31-35


BUDURWAR KAUYE Page 31-35
.
Washegari da safe juhaina ta kira munnir a waya tasanar masa saqon papa  Da yamma kuwa lis sai gashi nan da kayansa ya dawo inda yasamu ansaka halliru mai wanki da guga ya gyara masa ko ina    *WANENE MUNNIR* Mnnir shuaibu shine ainahin sunansa, iyayensa sun jima da rasuwa tun yana dan qarami  Ahannun baffansa ya taso wato qanin mahaifin sa  Tun tasowan munnir ya taso da rigima ba ta kadanba  Gashi da son karyan kudi sai dai Allah bai bashi ba  Tunda ya kammala makarantar sakandire bai cigaba ba sabida halin rashin kudi  Daganan bashida aiki sai bin yaran masu kudi sune party sune biki ahaka ya tabe  Watara sunje birthday party na wata budurwar abokin abokinsa anan ya hadu da juhaina lokacin tazo hutun qarshe wadda daga shi ta kammala karatunta  Lokacin da juhaina ta kyalla idanu taga munnir sai taji ya birgeta har tana sonyin alaqa dashi  Daga nan tazo tasameshi inda yake zaune nan ta nuna masa cewar tana sonsa  Shikuma tunda yaganta ya fahimci akwai yayan banki atare da ita nan ya bada kai bori ya hau  Tundaga ranan juhaina suka dinke da munnir itace kemasa komai na hidimar rayuwa   Tasaya masa waya mai tsada   Ta saya masa kayan sawa ta bashi kudin kashewa  Har lokacin komawarta singapore yayi   Bayan ta komane ashe tana da shigar ciki na wata daya, acan ta zubar dashi bayan tafadawa munnir abinsa ya farru   Juhaina sosai takeson munnir dan araayinta idan ta tashiyin aure shidata aura haka shima ya amince da batun aurenta tinda shikam ya samu tana masa komai  Bayan ta qare karatunta ta dawo nan suka dora daga inda suka tsaya itada munnir  Lokacin da papa yazo mata da maganar aure bata boyewa munnir ba   Amma shi saiya ce sam baisan zancen ba kuma ba auren da zatayi ta barshi  Nan tace masa wane shi harya isa ya hanata aure dama itace tace data aureshi kuma tafasa sai yaya  Duban bakida wayo yamata yace wlh intayi aure sai da yardarsa dan zaije ya samu saurayin nata yafada masa gaskiyar abinda ke takaninsu inyaso yaga yanda zatayi  Sanin munnir zai iya bin diddigi ya samu inda papa yake yasa ta lallaba shi dan tana matuqar son papa sosai  Dakyar tashawo kan munnir ya amince amma da sharadin suna tare koda tayi aure   Haka ta amince akan bayan bikinta zata sama masa koda gidane inda zai zauna saiya dawo bh da zama harma ya fara karatu    Wannan kenan  ***** Bayan sallar magribah papa da juhaina suka fita basu jimaba suka dawo dama abinci sukaje sayowa  Bayan sunyi parking Abdu yazo dasauri ko da akwai abinda zai shiga dashi ciki  Cikin girmamawa yace barka da dawowa oga  Aha Abdu shine abinda yafada yana miqo masa abincinsu adaqike yace gashi na hutar dakai fita  Juhaina ta fito da leda guda uku ahannunta yayinda uban gayyar shima ya fito   Har zata wuce sai papa yace my queen  Juyowa tayi ta amsa da yess my king  Inaga mu miqama munnir abincinsa idan munshiga ciki basai munfitoba ko  Ok muje to tashi dashi  Munnir kuwa tunda suka shigo yake tsaye ajikin window yana kallonsu cikin baqin ciki  Dan wani haushin papa yakeji cos y rage masa jin dadi ganin sun nufo wajensa yasa cikin sauri yasauqe curtain ya koma kan cussion ya zauna yana latsa wayarsa  Norcking suka masa   Daga ciki yace yess come in  Suna shigowa dasauri ya tashi cikin murmushin dole yace barkanku da shigowa  Papa yace yawwa amma yana tsaye cos baxama zaiyiba  Miqomasa take away nasa tayi tace bross ga abincinka sai da safe  Allah ya kaimu yafada yana bin bayanta da kallo  Nace sai kayi ai matar wani ce
.
  Bayan sun ci abinci papa ya dubi juhaina amma bada wasa ba yace my queen yakamata kifara dafa mana abinci tunda kinga yanzu ga munnir ma bai dace kullum muriqa bashi abincin wajeba   Ganin yadda yayi maganar bada wasa ba ya kuma sha murr yasa tace shikenan Allah ya kaimu  Washegari da safe ta dafa masu indomie  Sai dai satisfactory haka sukaci dan bai wani test ba  Da rana kuma haka aka kwaba white rice da stew dikda kajin dake ciki amma sam kasa ci sukayi dagashi har ita   Sauran mutanen gidan kuwa banbi takansuba  Ai daga kan dinning yace mata kada tamasu dinner tabari kawai dan yafahimci bata iya girkiba  Haka sukaci gaba da zama ahaka inda azuwa yanzu yafara gajiya da halayenta sam  Gashi bata kunyar idan yace tamasa abu tace bayanzuba  Satin bikinsu biyu TJ ya kwanta rashin lfy fever mai tsanani har saida papa yaje ya saka masa ruwa agida da allurai  Amma abinda ya birgeshi da gidan TJ shine tsaftar matarsa ko ina kyalkyal kamar baa takawa sai qamshi kawai dake tashi ta ko ina  Gashi ya lura da tana son TJ sosai ba irin sonda juhaina kemasa ba tinda dik abinda yakeso shi take masa  Agidan ya wuni ranan bayan tagama abinci ta kawo masu amma TJ sai ya gagara ci  Papa kuwa haka yaci yaqoshi yana santi aransa har yana inama ace matarsa haka take  Ganin yakasa cin abinci dik ta damu sai tambayarsa take mezaici adafa masa  Yace tamasa faten irish potatoe da hanta da alayyahu   Nan da nan ta daho ta kawo masa balaifi yadanci kuwa sai anan hankalinta ya kwanta  Sai gab da magriba ya tafi yana fitowa wayar juhaina ta shigowa  Doguwar tsuka yaja kafin yadau wayar dan  Tun bayan laasar juhaina take kiransa awaya yaushe zai dawo   Cikin jin haushi yace wai meyene kika dameni aidai zandawo ko ko ancemaki bata zanyi yana fadin haka ya kashe wayar dan wani haushinta yakeji yanzu dayaga yarinya qarama yadda ta iya komai da kula da miji   Ita kuwa banda abiya mata buqta batada aiki  Yana tafiya yana tunanin gaskiya dole dasake inma makarantar koyan girki da gyaran gida zata shiga sai dai tashiga dan zamansu ahaka bazai yiyuba  Itakuwa tasamu dama suna sheqe ayarsu da munnir shiyasa ajima kadan ta kira taji koya kusa dawowa kada ya dawo yasamesu atare   Amurtuqe ya shigo gida direct room nasa ya shige sai bayan yayi wanka sannan ya fito   Juhaina ta dubeshi tana zaune afalo tana kallo tace wai lfy kuwa hooney kaketa bata rai   Nakira ka awaya kana wasu magana gashi kadawo kuma ranka abace  Yace eh kawai zamanmu ne yakamata mu gyara   Gyara zama tayi tace toh kamar me kenan  Yace yanxu ace ko girki baza ki iya yimana ba komai idan inason nagani da kyau sai dai inni nayi haba  Kawai nayanke shawara zan maki register a school na koyan girki da kula da gida   Dubansa tayi nan taji ranta ya baci wato raini ne yasa zai zo yana fada mata haka  So kawai gobe zanje na mak........   Hannu ta daga masa tace heeyheey ya isa haka Alamin kul karkasoma wannan maganar   Da mamaki ya dubeta yace ni kikecema hey har kina dagamun hannu  Tace anfada maka din so what  Kuma ko cemaka akayi mai aikice ni da zaka fara tsiro da wani abu aidai ciyar dani dolenkane  Ko ance maka agidanmu inayin girkine har zakazo kanamun wasu surutai da shouting   Cikin bacin rai ya dubeta yace lalle juhaina nikike fadama haka ba kunya  Tace nice ma kai kajiko  Hannu ya daga zai mareta sai yafasa  Wata dariya ta sheqe dashi tace ya kafasa lalle da kamari mai tsada dan wlh ramawa zanyi tsaf ni banza bazata shani ba  Ko ashaye kazo kada ka taba kwatanta dukana dan ni bazan tolarating nonsense ba   Dubanta yatsaya yi dan baitaba tunanin tasan yana shan wani abu ba tunda boye mata yake   Itama dubansa tayi ido cikin ido tace yess ko ka dauka bansan kana shayeshaye bane kawai kallonka nake so kada kafara abinda zai dameka kaji nafada maka tana fadin haka ta wuce shi tabarshi awajen   Tsabar mamaki da bacin rai yakasa koda motsi kamar wadda aka dasa......   Wai ina labarin mutan Abujane kam
.

Ahankali ya wuce ya nufi room nasa yama rasa wanne irin tunani zaiyi guda daya  Tun daga ranan ya shareta ya fita aharkarta shi atunaninsa zatazo ta basa haquri  Amma har sukayi 5days ahaka itama bata kulashi kamar yadda bai kulata  Abincima sai dai ta tura asayo mata   Papa kuwa abin ya masa yawa wai suna yana da mata amma babu abu daya dayake amfanuwa dashi ata bangarenta  Dan abinda yake samunma yanzu baisamu tunda sun kancake  Gajiya yayi yaje yasameta ya lallaba ta suka shirya  2weeks later Yanzu hutun daya dauka awajen aiki ya qare hakan yasa juhaina ta bude sabon babin walawanta  Sassafe kafin papa ya tafi aiki munnir yake fita amma yana fita zata kirashi awaya ya dawo  Ta back door yake shiga wajenta yadda bawanda yake sanin shigarsa  Kullum suna shan shagalinsu da munnir hakan yasa yanzu ko papa bako yaushe yake samun biyan buqatarsa   Dan taringa masa hanya2 kenan aa daga tace batajin dadi sai tace bacci takeji   Idan ya matsa mata sai tace toh bata cikin mood din wannan abin  Gashi yanzu tamaidashi kamar ATM mashen sabida kullum acikin ya bata kudi take  Ga yawon tsiya da koyaushe sai dai ta dauki motarta ta shiga gari   Sau da dama haka zai dawo bai sameta ba  Yau dama tun bai fita ba yamata kashedin kada ta fita ko ina idan yadawo office zasuje gida sugaida daddy baiji daddy ba  Bayan ya dawo suka shirya sukaje basu jima ba ta dameshi da sutafi sabida yadda bata samu fuska awajen momcy ba haka aunty niima bata sake mata ba  Bayan sun tafi aunty niima ta dibi momcy tace momcy wlh matar papa ashe bayarinya bace yanzu naqare mata kallo da kyau  Cikin takaici momcy tace wannan ai idan bata girme masa ba toh saidai suzo saanni dan bai isah ya girmetaba  Aunty niima tace wai ya labarin fauziyya ne kam nakai 3days banyi waya dasuba  Momcy lfyrta qalau dazunma munyi waya da mabarukha tacemun tatafi makaranta  Aunty niima tace Allah sarki Allah ya bata miji nagari yarinya mai haquri   Momcy tace insha Allahu Allah zai canza mata da mutumin kirki  Haka sukayita hiransu suna jajanta abinda ya wuce  ***** Juhaina ce tsaye gaban papa ta riqe qugu ranta abace   Fiska a tsuke tace wai Alamin maeke damunka ne dannace kabani kudi shikenan sai kafaramun kididdiga kuma kana dashi bawai baka dashiba  Shima cikin fada yace ai banace bazan bakiba but i just want to know mezakiyi da kudinne ke kullum cikin abaki kudi kuma banga me kikeyi dasuba  Ahasale tace idan bazaka bani bane kawai kafadamum bawai kana wani kwana ba  Kallonta yayi dakyau sannan yace toh bazan bayarba ki kwata  Ok is that what u said tace dashi tana wani turo qirji  Yeah haka nace kin wani tsareni kamar wani danki kina turomun tsumma   Kutt qirjinawa ne tsumma ta fada cike da bacin rai  Adaqile yace toh meye acikin ido banda ruwa ni bani hanya kiga ina da abinyi  Naqi nabaka hanyan marar mutunchi kawai kuma ahakan kake kwantar da kwadayinka ba  Ya tsina fiska yayi yace eh arashin uwa ba   Nan sukayi tsiya tsiya kamar zasu daki junansu  Da kyar yasamu ya shige dakinsa ya kulle dan shakkar juhaina yake kuma ya tabbata idan ya daketa zata iya ramawa shiyasa bayi attempting dukanta  Kwanaki na tafiya, watanni sun shude   Haka rayuwa yaci gaba da tafiya tsakanin papa da juhaina   Zaman lfy da kwanciyar hankali sun qauracem papa kullum yana yawon wajen cin abinci kuma itama dole ya kawo mata nata inba haka ba bayi da kwanciyar hankali  Kudi kuwa ko yaso ko yaqi dolensa ya bata  Abunda yafi daminsa yanzu yawo da ta qara couse akai yakuma rasa inda take zuwa tunda bata da yan uwa bauchi amma kusan kullum bata yini agida  Munnir kuwa yanzu yayi sabuwar budurwa   Dazaran juhaina ta bashi kudi ita yaje zuwa ya kashewa shiyasa kullum acikin tambayarta kudi yake   Time to time kuwa yana zuwa kd yayi two weeks harma fiye da haka  Yanzu haka mota juhaina tamasa alqawarin zata canza masa  Itama can wajen yawonta tayi sabon kwarto shiyasa yanzu bata damu da mumnir ba   Ita yanzu hanyar da zata samu ta koreshi take nema shiyasa takeson tacanza masa mota ta lallaba shi ya koma kd   Wasa gaske yanzu aurensu ya doshi shekara amma shiru ko batan wata bata tabayiba sabida kwayoyin hana daukar ciki datakesha   Dan bata shirya haihuwa yanzuba acewarta zata tsufa da wuri kuma ma ita bata shaawar yara dan wai takura garesu  Ya zuwa yanzu dik wadda yake tare da papa zai fahimci akwai abinda ke daminsa kawai dai bai fito ya fada bane  Amma acikin zuciyarsa yafara danasanin auren juhaina tunda bai qareshi d komaiba  ***** Aunty mabarukha nagani tsaye ajikin mota da alamu fita zatayi unguwa sai dai kamar jiran wani abu take  Fauziyyah ce ta fito cikin shiga ta alfarma wadda sai danayi da gaske naganeta  Taqara haske taqara girma   Wata arabian gown ce pusher pink wacce ta matuqar shan adon duwarwatsu masu kyallin gaske  Ta rolling veil din rigan akanta hannunta riqe da wata waya mai dan banzan kyau  Cikin sauri ta qaraso wajen aunty  Tana cewa am sorry aunty nabarki kina jirana   Aunty tayi murmushi tace no badai kin gamaba muje bazama mujima ba zamu dawo sabida kada su daddy sudawo daga islamiyya  Ok ta fada tana shiga mota   Gidan wata qawar aunty sukaje suka karbo wasu kaya tadawo daga dubai   Bayan sundawo yara ma sundawo daga islamiyya suna hira afalo  Aunty ta dubi fauziyyah tace Fauziyyah inaga tinda yanzu kina SS2 kawai kizana SSCE inyaso bazaki fasa zuwa school ba   Idan paper yayi kyau sai munemi admission kawai  Fauziyyah tace toh Allah ya kaimu   Aunty tace inyaso idan anyi hutu bazuwa dambam sabida kisamu kiyi karatu sosai  Cikin ikon Allah fauziyyah tana cikin shekaranta na biyu da komawa makaranta ta zana SSCE  Kuma da ikon Allah papers nata sukayi kyau dan fauziyyah dagaske take karatu idan kuna magana da ita zaka dauka tagama university sabida yadda takware a turanci  Kuma tana daukar shawara da nasihar da aunty take mata akan karatu  Takan cemata kiqara maida hankali akan karatunki sabida kizama wani abu kema arayuwa kinga dai abinda namiji yamaki akan rashin karatu  Hakan yasa ita kuma tayi alwashin sai tayi karatu mai zurfi  Lokacin da paper  suka fito dikkansu suka taho bh   Daddy yayi murna sosai   Sannan yace meye shawarin aunty   Aunty tace yanzu dama sun sayi jamb form sun kuma sayi form na gwagwalada university  Daddu yayi shiru yace jiya sunyi magana da mr khan wani friend nasa dake india  Kuma yamasa magana akan asamawa fauziyyah gurbin karatu a jami'ar new delhi  Kuma ya tabbatar masa wannan badamuwa zai trying best nasa yace atura masa takardunta  Sosai sunji dadin shawaran da daddy ya yanke   Kwanansu daya ta wuce dambam abinta dan bata kaunar abinda zai hada ta da papa  Cikin watanni uku komai ya kankama na tafiyar fauziyya dan tasamu admission kuma agidan mr khan zata zauna dan abokin daddy ne sosai  Ranan talata su daddy suka kaita airport dake lagos dan tacan zasu tashi   Qarfe uku na rana jirgin su fauziyyah ya bar nigeria ya nufi india.

.
Dawuri ya dawo gida cos yana da sugery da yamma a asibitin daddy  Akwai wani mutum da zaamasa aiki a spinal cord nasa  Yana shigowa tin daga parking space ya gane juhaina bata nan sabida he did not see her car   Key nasa ya bude qofa ya shiga ciki dan inda sabo ya saba da hakan   Dik randa ya kuskure ya bar key nasa kuwa to zai zauna a gate jiranta   Sabida rana daddaya ne zai dawo yasameta agida  Room nasa ya shiga ya kwanta nan bacci ya kwasheshi sai pass 3 ya tashi  Cikin dauri ya shirya ya fito sabida 4:30pm zai shiga aikin  Fitowa yayi ya kulle dakinsa dan ya kuskura ya bari abude sai tamasa barna  Amma ga mamakinsa bata dawoba ficewarsa yayi kawai abinsa  Bashi ya fitoba sai wajen 7 sallah yayi sannan ya nufi gida amma sai daya tsaya a resturant yaci abincinsa sannan ya wuce gida  Dagangan yaqi saya mata yace taci yawon taqoshi yau bazai saya ba  Har lokacin daya koma gida nanma bata dawoba  Tabe bakinsa yayi yaje yayi wankansa yayi sallah sannan ya fito ya kunna press tv yana kallon wani program da sukeyi  Har wajen 9 sannan yaji shigowarta   Gyalenta a hannu ta shigo falo   Ganinsa azaune sai tayi kamar bata ganshiba zata wuce  Keh daga ina kike da wannan daran yafada yana kallonta  Ko cikanka bata ce dashiba zata wuce ta gefensa   Cikin sauri ya riqo hannunta yace bada ke nake maganaba nace daga ina kike   Hannunta zata fisge yayi saurin sake riqeta sosai sannan ya miqe tsaye   Yace juhaina wai me kika maidanine dan iskanci ina maki magana sai kiqikulani toh inkinga kinbar wajennan sai kinfada mun daga gidan ubanwa kike at this time  Wani walaqantaccen kallo ta wurga masa sannan tace daga gidan uban mai tambayar nake  Nan take yaji xuciya ta debeshi watoma harshi zata zaga  Aiko nan take ya daga hannu ya wanka mata mari mai kyau  Yana sauqe hannunsa itama ta daga hannunta ta zabga masa mari tana huci tace kai har ka isa kadakeni to ko ubana bai dukana baran kai banza a banza ta fisge hannunta ta wucectabarshi  Shikuwa mamaki ne da baqinci suka hanashi cewa komai ko ya tanka mata  Wani zafi ne kawai yakeji yana taso masa daga kasan zuciyarsa kamarshi ace matarsa har tadaga hannu ta mareshi   Tsabar bakin ciki nan take idanunsa suka caza launi suka qanqance  Dakinsa ya nufa ya bude fridge ya dakko wine nasa ko takan cup baibi ba  Ya dannan bakin kwalbar amma maimakon tamasa dadin sha sai yaji wani daci sabida yadda zucitarsa ke tafasa  Nan take sai tunanin fauziyyah ya fado masa   Yaune rana tafarko daya fara tunota tinda ya saketa  Tunanin yadda yake nada mata duka yakeyi amma koda wasa bata taba tunanin fada masa magana mai muniba baran tarama   Ya walaqanqanta ta son ransa amma yarinyar nan haka zata haqura sai dai tayi kukanta tayi shiru bata taba fada ma waniba  Anya kuwa yamata adalci kuwa nan yaji xuciyarsa tasake quntata  Kotana ina yanzu ko wani hali ta shiga lokacin daya saketa bada haqqinta ba  Nan take zuciyarsa tafara bugawa da sauri sauri  Nan yafara tuno irin yanayinta kyan fuskarta yanayin jikinta   Tuno rananda yafara ganin qirjinta yayi nan take yaji wani kewanta marar misaltuwa yana shigansa  Zuciyarsa take raya masa inama har yanzun itace matarsa ba juhainaba daya rungumeta tsakani da Allah da bai cutar da ita ba   Nan ya tuno qamshin girkinta idan tana dafa abinci amma zuciyarsa ta cuceshi ta hanshi aminta da ita  Cikin qunan rai yake zargin kansa da mai yasa tunda baiga wannan abubuwanba sai yanxu da bai masan inda takeba  Nan wata zuciyar tace wataqilanma tayi aure abinta  Damm yaji zuciysrsa ta buga wani zafi yasakejin yana mamayeshi har yana zufa dikda sanyin AC dake bugawa  Haka ya ajiye kwalbar giyar dan bazai iyama shaba   Yadda yaga rana haka yaga dare sabida tunani daya addabeshi ya kuma tabbatar ma kansa zuciya takaishi tabaro tunda gashi yau yarasa tudun dafawa   Tundaga wannan ranan tsanan juhaina ya dasu a azuciyarsa amma haka yake zaune da ita ya kuma kasa saketa   Hakadai suke zama marar dadi   Sai abinda yafi daminsa wato yadda tunanin fauziyyah ya addabi rayuwarsa ba dare ba rana   Wani matsanancin son kasancewa tare da ita yakeji   At last ya tabbatar ma kansa sonta yakeyi   Rasa mafita yayi yaje yasami TJ ya fada masa abinda ke faruwa  TJ yaso yayi masa dariya amma ganin halin dayake ciki sai ya danne   Yace toh wai bakada labarinta ne   Papa yace banma san inda takeba ko agidan momcy ban sake ganintaba   TJ ya nisa yace toh yanzu shawarn da zan baka kadage da addu a idan rabon kace tadawo gareka  Nikuma zan tambayi khairy tunda yar uwartace dole nasan tana da labarinta inma aure tayi inma ko me nene zamuji  Godia yayi ma TJ sosai dan har yadan sami natsuwa   Amma da TJ ya tambayi khairy hanya hanya tamasa kawai taqi fada masa gaskiaya  Shima haka dai yayima walawala ya qi sanar masa khairy taqi fada masa dan kada yaji haushinta  Haka rayuwa tayi ta tafiya inda papa yake cikin wani hali yakumayi dana sanin abinda ya aikata abaya kuma har gobe fatansa Allah ya nuna masa fauxiyyah ya roqi gafararta dan yanxu yagane cewar alhakinta ya ke bibiyarsa   Ba abinda ke qara daga masa hankali kamar yarda kullum sonta yake qaruwa acikin zuciyarsa   Watarana ankawo wata yarinya asibitinsu tasamu matsala a guiwarta daga faduwa   Aifa tun dayaji sunanta fauziyyah shikenan haka yaringa hidima da ita har aka sallamesu sabida yarda yake qaunar mai sunan  Kuma yasama ransa dik ranada yasan inda fauziyyah take kuma bata da aure tabbas koza ayi yaqi sai an maida masa da matarsa idan kuma basu sake haduwaba yasan sontane zaiyi ajalinsa    ***** Fauziyyah ta sauqa lfy, inda tasamu tarba na mutunchi awajen mr khan da matarsa da yaransa yan mata guda biyu  Kwanan ta biyu da zuwa tafara xuwa makaranta tanajin dadin karatunta sosai gashi Amisha tana taimaka sosai akan abinda bata ganeba   Cikin ikon Allah karatunta yana tafiya yadda akeso   Da haka har tacinye shekarar farko  *Bayan shekara biyu*   Fauziyyah ce zaune tana hada kayanta cikin farin cikin sabida gobe zata koma gida nigeria cikin nasarar uban giji ta kammala karatunta da saka mako mai kyau  Yanzu tazama cikakkiyar *PAMACIEST*  Cikin shekaru ukun datayi sau biyu kawai taje nigeria   Washegari jirgin qarfe 9 nasafe ta biyo sai gida  Acan nigeria kuwa su daddy ne da momcy da su aunty mabarukha harda aunty niima sukazo taronta dan akwai liyafar da daddy ya shirya mata a nan abuja   Jirgin na sauqa na hangota cikin jerin fasinjoji amma zaka rantse da Allah baquwace tazo daga india kuma zata koma sabida yadda fatarta ta murje tayi wani haske na musamman kyanta yasake fitowa   Kallo daya zaka mata kafimci zallan wayewa atare da ita dan tana daga cikin jerin mata masu class   Ko yadda take saqqowa cikin natsuwa kawai ya isa ya tabbatar maka cewa lalle wannan mace ce mai jida kanta   Daddy kuwa murmushi kawai yakeyi  Cikin sauri aunty ta qarasa ta rungumeta tana mata oyoyo  Wani daddan murya naji ya daki dodon kunnena hausa takeyi amma kamar maiyin indianci sabida yadda harshenta ya juye  Cikin farin ciki ta gaisa da kowa sannan suka nufi gida  Da yamma aka gabatar da liyafa mai kyau acikin gida   Sunsha hira sosai da daddare daddy ya kirata yace washe gari zasu wuce bh tare amma ita zata wuce dambam gida dagacan zai tura driver ya maidata abuja sai service nata ya fito sai tadawo bh tayi acan   Haka koh akayi watanta daya a dambam ta koma Abuja   Watanta biyu a Abuja service dinta ya fito amma jos aka turata nan daddy yamata cukucuku amaida ta bh  Tsabar tanada daurin gindi ko camp bata shiga ba   Sai byan an musu posting aka duba nata anturata teaching hospital na bh  Ana saura sati daya ta dawo bh uncle salim qanin mijin aunty yazo da abokinsa Barrister Nabil Abdullahi gidan aunty mabarukha    Wajen aikinsu daya a bh yanzuma wani aikine ya kawo su abuja kuma babansa shine commissioner for works n houses na bh  Tunda ya kyalla idanu yaganta ya nacewa uncle salim shifa yaga wata balarabiya kuma tamasa  Har saida ya kira aunty awaya yafada mata abokinsa dasuka zo tare yaga fauziyyah yana so kuma ya fada masa ta taba aure yace ko dik yaran duniya ita ta haifa yaji ya gani  Aunty kuwa hakan yamata dadi nan take ta tura masa phone no fauziyyah  Tunda yasamu no shikenan waya ba dare ba rana text ne meyene amma sam fauziyyah bata kulashi dan ba namiji aranta sam  Ranan sunday ta taho bh dan monday zata fara fita aikinta na service  Isowan yamma tayi lis dan basu taso da wuri ba hakan yasa tayi bacci da wuri   **** Papa kuwa yau tun daya tashi yakejin zuciyarsa wani iri kuncine meye ne baima saniba gashi yana da aiki a office gashi akwai maganar da zasuyi da daddy kafin ya fita office   Dolee yasa da wuri ya shirya ya taho gida daga can ya wuce office  Fauziyyah kuma qarfe bakwai ta tashi tayi wanka ta shirya amma tayi ligh make up sai pink jambaki data goga a lips nata  Kayan su na coppers tasaka ajikinta nan naqare mata kallo da kyau  Rigat ta kamata sosai inda na fulaninta da suke a cike dam gasu atsaye suka cika mata gaban rigan hakama wandon hips nata da bayanta sunfito sosai dan ya kamata sosai  Gaskiya wadda yasan fauziyyah lokacin tana gidan papa yaganta yanzu bazi ganeta sabida yadda tacanza komai najikinta ya canza ga wani kyau na musamman data qara   Kallon kanta tayi tsaf a madubi sai taji kunya bazata iya fita waje ahakaba   farar qaramar hijab ta dauka iya guiwa amma bata saka ba sai ta riqo ahannunta  Nima sake kallonta nayi da kyau nan naga zallan kaman datake da *Arti matar Yash na cikin film din married again*  Cikin natsuwa ta dakko yar qaramar jakarta mai kamar purse ta rataya hannuntabriqe da hijab  Tana fitowa falo da momcy tafara haduwa bayan tagaisheta momcy tayi murmushi tace masha Allah kiyi maza kije wajen daddy sai kizo kiyi break ko  Cikin muryarta mai dadi tace ok sannan ta mufi bangaren daddy  Da sallama ta shiga cikin faraa ya amsa bayan ta gaidashi   Yadan mata nasiha sannan ya miqo mata key din motarta sabuwa dal daya saya mata yace motarki tana waje Allah ya kiaye hanya ki kula da tuki  Nan taringa godia sabisa baqaramin dadi taji ba  Daddy yace kada kidamu jeki abinki kada kimakara  Papa kuwa yana zuwa gida afalo ya samu momcy bayan sungaisa yace bari yaje wajen daddy   Tace toh sannan ya wuce   Momcy kuwa jin fauziyyah shiru gashi kada time ya wure mata yasa ta kwala mata kira   Dauther kiyi sauri kizo kiyi break kada kimakara  Fauziyyah kuwa ta fito tazo daidai kan steps da zata sakko falo taji kiran momcy   Dama sauri take taxo ta nuna ma momcyn kyautar da daddy yamata  Itama cikin daddan  voice nata mai dadin sauri tace yess me arihoo momcy(ina zuwa momcy)  Daidai papa yasaka qafarsa zai haura kan steps da zai kaishi side din daddy yaji wata murya mai dadin gaske cikin harshen indianci tana magana  Saida yadan matsa baya data bugeshi dan cikin sauri ta wuce batama lura da mutum ba  Papa kuwa ganin kyakykyawar mace kuma ba india yasa yabi bayanta da kallo amma dake tariga da wuce sai bayanta daya kallah   Wadda hips nata yake masa gwaliyo  Lumshe idanu yayi ya bude gashi ta buleshi da qamshin turarenta  Cikin sauri ya riqe gini dan baisan yayi missing step ba  Jiki a mace ya shige dakin dadi amma muryarta sai yawo yake masa akwanyarsa   Bayan sun gaisa gagara haqura yayi yace daddy baquwa akayi agidanne   Daddy yace baquwa kuma   Papa yace eh kamar ma ba india ce kuma daga nan ta fito  Wani murmushi daddy yayi yace aa kam indai wacce tabar nan yanzune sai dai qanwarka   Papa yace qanwata kuma wacce qanwata nikuma inada qanwace   Daddy yace qanwarka fauziyyah mana yar gidan Abbanku na dambam  Cikin sauri ya dubi daddy yace Fauziyyah kuma itace ta fita anan   Daddy yace yawuce wai itace mana amma bar wannan maganar ina jinka yadda abin zai kasance yasa na ce kazo da safe   Ina papa hankali yayi gaba baimasan daddy yana yiba   Saida daddy ya lura baima tare dashi sannan ya tabashi yace kana jina Alamin  Cikin sauri ya firgita yace me kace daddy  Wani murmushi daddy yayi wanda shikadai yasan maanarsa........     .

Daddy yace maganar bude asibitin nan ne dama najika shiru haryanzu baka fadi wani suna zaa sama ba sannan wacce rana ya dace sabida buga IV  Papa dai yayi shiru yana jin dadi amma harga Allah dakyar ya tsinci kadan daga abinda yake fada masa  Sabida hankalinsa da tunaninsa baya tare da daddy  Cikin wani yanayi yace zanyi tunani akai zuwa gobe zan sanar maka   Yafadi hakan ne kawai dan yasamu ya tashi awajen dan ya tabbata bazai samu natsuwa ba har sai yayi tozali da farin cikin rayuwarsa dan yana da good assurance batayi aure ba tinda ya ganta agida da wannan lokacin  Daddy yace is ok sai najika toh   Aiko daddy na rufe bakinsa ya miqe cikin sauri yana cewa barinje office   Daddy yace Allah ya kiyaye hanya  Yana tafiya ya amsa da Amin  ***** Fauziyyah kuwa cikin sauri ta nufi wajen momcy tana murna  Rungume momcy tayi tana cewa dekho momcy meri gari key (kalli momcy key din motata) daddy ne ya bani kitayani godia  Cikin faraa momcy tace masha Allah, Allahu ya tsare hanya   Amin ya Allah ta Amsa  Momcy tace kije kiyi break kada kimakara  Toh ta amsa sannan ta wuce dinning, dan kadan ta iya ci sabida murna tadawo falo tace zata wuce  Har bakin qofa momcy ta rakota tana cewa ganan motar taki jiya dare aka kawota Allah ya tsare sai kindawo sannan ta juya ta koma ciki  Itakuma qarasa wajen motar tayi sannan ta bude ta shiga tana jin wani dadi aranta  Ahankali tamata key sannan tafara tafiya cikin natsuwa har bakin gate inda mai gadi ya bude mata gate ta fice  Direct NYSC office ta wuce sabida akwai abinda zatayi acan kafin ta wuce asibiti   ***** Papa yana fitowa yaga wayam bakowa afalo sai motsi dayaji acikin kitchen  Leqawa yayi sai yaga momcy ce itakadai   Ziciyarsa ce yaji ba dadi dan fauziyyah yaso yasake kallo  Asanyaye yace na wuce office amma idan nadawo zan biyo  Toh adawo lfy tace dashi sannan ya fice  Motarsa ya shiga ya wuce asibiti driving yake amma hankalinsa na wani waje   Tinani yake yanzu fauziyyah ce tadawo haka yarinyar da ya raina yanzu itace tazama big girl haka   Ikon Allah ne kawai ya kawoshi lfy yana parking ya wuce office nasa  Zaune yake amma yakasa tabuka komai tunani kawai ya addabi zuciyarsa har yafarajin yarasa maike masa dadi  Ya jima azaune amma ko file daya baigama dubawa cikin sauri ya ture su gefe ya miqe  Dan jin kansa yakeyi yamasa nauyi ga wani irin faduwar gaba da kunci dake damunsa  Gara ya tafi gida ya kwanta kawai   Wayoyinsa da key nasa ya zara ya fito   Cleaners da masinja suna gaisheshima amma hannu kawai yake daga masu   Yana fitowa ya nufi parking space sai yaga wata mota mai kyau kalar mata ta tsaya agefen motarsa   Kafin ya qaraso sai yaga ta fito tana rataya jakarta  Sake zuba mata idanu yayi tabbas fauziyyah ce amma badan daddy yafada masa ba bazai ganetaba  Sai alokacin ya lura ashe kayan NYSC ne ajikinta tambayar kansa yake yaushe kenan haka tafaru  Fauziyyah kuwa dago kanta dazatayi wazata hango yana nufota ya Alamin  Tabbas shine dan bazai taba bace mata ba dik da yadan canza yaqara kyau yadanyi qiba kadan sannan daganinsa naira tazauna masa fiye da da  Ahankali tasauqe idanunta tanajin zuciyarta tana bugawa da sauri sauri  Nan take taji wani zafi azuciyarta dan bata qaunar abinda zai hada ta papa ko ahanyane  Daidai da ya qaraso jikin motarsa amma ya qudira aransa zai mata magana dan bazai iyah ganinta ya wuceba  Itakuma yitayi kamar bata ganshiba zata wuce kamar daga sama taji muryarsa wadda kodaga bacci tafarka bazata manceba   Yan mata shine abinda ya furta yana kallonta   Cak ta tsaya dan jitayi kamar ya caka mata wuqa wai yan mata  Dagoda kanta tayi ta sauqe dara2n idanuwanta farare tas masu kamar madara akansa   Nan yaji wani abu wadda bai san mene ne ba kawai yasamu kansa da lumshe idanuwansa yana tasbihi ga ubangijin halitta dan fauziyyah ta tafi dashi gaba daya  Muryarta ta dawo dashi daga duniyar tunani daya tafi  Cikin halin ko inkula da rashin damuwa tayi kamar bata sanshiba  Ya tsina fiskanta tayi tana masa duban rashin sani tace konhei tum(wane ne kai)  Kutt dan zaro idanu kadan yayi sabida mamaki wai harshine fauziyyah zatace bata ganeshiba  Amma sai yadaure yayi wani qayataccen murmushi yace mera naam Dr Muhammad Alamin Abubakar(suna na Muhammad Alamin Abubakar)  Ya tsina fuska tayi ta wani juya idanuwanta tace eyyerh sowwie am not talking with people that i dont know  Tana fadin haka ta wuce abinta bata sake koda kallonsa ba  Shiru kawai yayi yabi bayanta da  kallo  Cikin qunan rai ya bude motarsa ya fada yana tuna irin walaqancin da fauziyyah tamasa ta yankwanashi   Afusace yafigi motar wadda dakyar yataka birki yabawa scurity pass sannan ya wuce  ***** Juhaina ce ta dubi munnir tace wai saurin me kakeyi ne kamar wadda ba agidan zaka kwana ba  Yace kinsan najima bangankiba wlh ina kewarki sosai muje ciki narage zafi  Murmushi tayi sannan tace haba dai kaida zakayi 1 week me zai dameka kuma Dr sai yamma shida yadawo   Yace ai har tunani nke next idan zanzo wacce qarya zamu masa tunda munce nazo gyara carry over ne  Dariya tayi tace wannan mai sauqine tunda shi baho ne inba hakaba sai kace ba mutumin daya shiga ajin ABCD ba  Komai aka fada masa sai ya yadda  Shima dariya yayi yace nidai muje toh pls mana  Riqe hannunta yayi suka shige bedroom nata   Nan suka fara mashaarsu da suka saba   Tsabar sunyi nisa basa cikin hankalinsu ko jin shigowar mota basuyiba  Papa kuwa ko parking mai kyau baiyiba haka ya fito ya nufi cikin gida   Ahargitse ya shigo falo dakinsa ya nufa  Yazo daidai dakin juhaina harzai wuce sao yaji kamar nishi  Saurarawa yayi da kyau sai yaji tabbas ba kunnensabane nishintane  Cikin sauri ya bude dakin dan atunaninsa ko batada lfy ne  Yana shiga yayi turus wani jirine yaji ya debeshi yayi saurin riqe qofar sabida abinda idanunsa ya gane masa  Juhaina da munnir kwance haihuwar uwarsu suna aikata zinah  Abinda bai taba tunaninba juhaina zataci amanarsa kuma ma da dan uwanta   Su juhaina kuwa jin anbude qofa yasa cikin sauri suka juyo ganin papa atsaye yana musu wani kallo cike da baqin ciki har idanunsa sukoma jajaye kamar gaunta bushashshe  Dasauri munnir ya tashi akanta itakuma cikin razana ta tashi zaune tanajan mayafi tana kare jikinta  Ahankali yasamu nutsuwarsa ta dawo maida qofar yayi ya rufe da key sannan ya nufo su gadangadan  tsabar tsoro ba juhaina ba hatta munnir jikinsa rawa yake  Yana zuwa ya shaqo wuyan juhaina yace cikin kakkausan murya kifadamun wane ne munnir kuma meye atsakaninku  Aifa cikin tsoro da firgita tace dan Allah kayi....  Wani gigitaccen mari daya zabga mata saida taga wuta shiya katseta   Cikin tsawa yace wane ne munnir zaki fadamun da bakinki kosaina kasheki shegiya tsinanniyah macucuciya Allah ya isa tsakanina da keh wlh kinci amanata  Ganin yadda kamanninsa suka sauya fiskarsa tayi jajur tsabar bacin rai   Murya na rawa tafada masa tsakaninta da munnir tace amma kayafemun wlh bazan sake ba  Bata gama rufe bakintaba ya saka hannunsa ya makata da gini nan tafadi a asume  Munnir kuwa tsabar tsoro ganin yadda yayima juhaina saida ya saki fitsari ajikinsa  Aikuwa da papa ya damqoshi yafara dukansa yana cewa munafiki kana zaune agidana kana zaluntata ashe ina tare da kwarto bansaniba  Mari duka harbi haka yake masa saida kansa bakinsa hancinsa ko ina jini yake amma zuciya ta hana papa ya kyaleshi  Hannunsa yasa yakamo gabansa da iyah qsrfinsa ya jawota ya murde wadda saida ya saki kashin azaba   Hannunsa ya kama ya buga da jikin drower ji kake kass kass ya karyashi   Axaba iya azaba saida yakasa motsi sannan ya kyaleshi ya nufi toilet ya debo ruwa a bucket  Zuwa kan juhaina yayi wacce ke kwance asume ya sheqa mata  Nan ta firgita ta farka aiko itama nan yahau jibgarta da waya yana harbinta  Saida jikinta ya faffashe fiskarta ta kumbura tayi sumtum tsabar duka  Tsabar azaba har saida ta kasa kuka cikin baqin ciki ya jawota har waje tana nade acikin zanin gado amma saida kamanninta ya canza dan ba dukan wasa ya mata ba  Sannan yace tsinanniyah kada nafito nasameki kificemun agida na sakeki saki uku muna fuka  Itadai batada bakin kuka ma bare bashi haquri  Mai gadi ya kira yace suzo suna biye dashi har dakin juhaina yace su fitar masa da munnir agida su kaishi can waje  Haka suka jawoshi kamar har sun kai qofa paoa yace ganan haqorinsa biyu kuhada dashi kufitamun dasu  Suna fita ya nufi dakinsa yafada agado ya fashe da kuka....  
.
Kuka yake mai cike da nadama, hawaye wani nabin wani haka suke zuba akan face nasa  Zuciyarsa cunkushe da zallar dana sani akan abinda ya aikata abaya   Tabbas yau ya tabbar alhakin iyayensa ne dana fauziyyah ke bibiyarsa   Kuma ya qara daukan darasi akan bijirema iyaye ba abune mai kyauba tunda gashi yaga saka makon abinda bai taba tunani ba  Wani irin nauyi yaji qirjinsa yamasa   Kuka yake sosai har abin tausayi domin dik abinda mutun ya aika matuqar yagane kuskurensa har yayi nadama nagaske ba tuban baqin muzuru ba dole ya baka tausayi  Sambatu kawai yakeyi yana cewa daddy, momcy, fauziyyah kuyafemun ashe gata kukamun na auramun yarinya yar mutunci kuma mai mutunci   Amma son zuciya yasa na bijire muku yau gashi abinda yasameni wayyo kaicona kaicon halina dama duk masu hali irin nawa...  Maganarce tasarqe qirjinsa ya cushe numafashi yafara masa wahalar fita  Dakyar ya dauki wayarsa yafara kiran layin TJ  TJ yana office saiya ga kiran abokinsa   Hello man shine abinda ya fada yana daukar wayar  Cikin wata raunanniyar murya datake nuna mai ita yana cikin wani hali   Yace pls kazo gida kasameni ina cikin wani hali  TJ baisan sanda ya miqe tsayeba cikin razana jin yadda muryar abokinsa take a hargitse  Meyasameka??? Shine abinda ya maimaita harsau uku  Ahankali papa yace TJ banida lfy juhaina zata kasheni kazo pls kataimakeni  Afirgice TJ yace ganinan zuwa ganinan zuwa am on my way yana fadin haka ya suri key din motarsa ya fito cikin sauri yacema scretery nasa idan bandawoba zuwa 2 ka kulle office kawai  Baijira amsar shiba ya fice cikin sauri da tashin hankali dan baisan yadda zai sameshiba  Cikin gudun balai har ya iso gidan papa wani mahaukacin horn yake dannawa 
.
Maigadima saida ya tsorata dajin irin horn dake masa   Aiko baibata lokaciba ya bude   TJ yana shigowa ko cikkakken parking baiyiba ya hnyar cikin gida daidai qofar falo yayi turus ya tsaya ganin juhaina lullube da zanin gado tana rizgar kuka dan sai alokacin tasamu kuka yaxo mata gashi ya kulle qofa bare ko kaya tasama jikinta baran tasannayi  Juhaina ina Alamin yake kekuma meya sameki naganki haka  Gagara magana tayi sai da hannu ta nuna masa qofar falo  Tura qofar yayi ya jita gam akulle bubbugawa yafara da iyaka qarfinsa dan abin yaqara bashi tsoro  Papa yanajin bugun qofa gakuma wayar TJ tashigo masa yasa ya taso ya fito falo ya bude qofar   Yanaganin TJ kawai saiya fada jikinsa yaqara saka kuka mai tsuma zuciya  Cikin rudani TJ yace waime ke faruwane man kamin bayani mana kozanji sauqin abinda nakeji  Sake qanqame TJ yayi yana cewa na cuci kaina na biyema san zuciyata na cutar da matata ta gaskiya na baqanta ran mahaifana yaugashi naga abinda bazan taba mantawaba  TJ ma kawai saiyafara hawaye nafarko tausayin papa dikda baisan meya faruba amma yadda yaganshi a hargitse yana kuka da idanunsa tabbas babban abune  Sannan murnan abokinsa ya gane gaskiya   Share hawayen fiskansa yayi yafara lallashin papa da kalamai masu dadi har papa yayi shiru  Sannan yafara bawa TJ labarin abinda ya faru yana furta abinda yagani sai da wasu hawaye masu zafi suka zubo masa  Cikin tashin hankali TJ yakejin abin kamarca mafarki   Nan ya fara tausan papa da banbaki akan ya kwantar da hankalinsa komai zai wuce   Papa yace hankalina bazai kwantaba har sai ka kaini asibiti anmin test na HIV tukunna   TJ yace insha Allahu babu abinda zaisameka ka kwantar da hankalinka  Taya hankalina zai kwanta matuqar ina dauke da wani mugun ciwo wlh jujaina ta cuceni ta shiga tsakanina da fauziyyah dan bayadda fauziyyah zata dawo gareni ina halin jinya   Tj yace ya isa haka muje asibitin inhar hankalinka zai kwanta dan yaga har numfashinsa yana samasama  Amma kabar juhaina ta suturta jikinta kafin ta tafi  Da kyar ya yarda yace amma kada yadawo ya sameta  Nan suka fito TJ ya kalleta yace kitashi kije kisuturta jikinki amma yace kada yadawo yasameki gidansa yanafadin haka ya wuce abinsa dan dama papa ya riga da ya wuce  Sai bayan sunfito TJ yace wanne hospital zamujene  Ka kaini asibitin daddy shine kawai abinda ya iya fada  Suna isa asibiti lab suka wuce  Maaikatan wajen suna gaisheshi baiko amsaba yace subashi abin gwajin HIV kawai   Damamaki kowa ke kallonsa cikin tsawa ya maimaita masu nan take suka miqo masa  Alluraya dauka ya caka wa hannunsa nan take sai jini yazuba yafara zaman zullumi   Bada jimaba saka mako ya nuna negetalive  TJ dake tsaye agefe yace Alhamdulillah bana fada makaba gashi ai d answer is negetive dafatan hankalinka ya kwanta  Shiru kawai yayi ya miqe dan baijin zai iya magana   Tashin da zaiyi ya yanki jiki ya fadi sumamme  Cikin razana TJ ya sumkuya yana kiransa amma ina baimasan yana yiba  Cikin sauri aka kawo abin daukar marar lfy aka turashi sai emergency  Nan suka bashi taimakon gaggawa har Allah yasa numfashinsa ya daidaita sannan aka maidashi dakin hutu amma dai bai farka ba tukun  In hankalin TJ yayi dubu to atashe suke   Sai a lokacin ya tuna yadauki wayar papa dake aljihunsa ya fara kiran momcy  Bugu uku ta dauka tana cewa hello son   Cikin natsuwa TJ yace ba Alamin bane Tijjani ne  Momcy tace ayya ya khairy da mubeen (dansune wadda bai wuce shekara biyuba)  Lfy qalau umm dama Alamin dinne bashida lfy yanzu haka muna asibiti  Salati momcy ta fara tace mai yasamu papa kuna wanne asibiti  Asibitin daddy muke naje wajensama bayanan  Momcy tace eh yau bai fita ba amma muna zuwa yanzu   Daddy ne ya dubeta yana cewa wai meya sami Alamin din   Cikin damuwa momcy tace nima bansaniba kam   Toh dauko mayafinki muje   Suna zuwa suka shige inda aka kwantar dashi   TJ suka sami yayi shiru yana zaune  Bayan yamasu sannu da zuwa daddy yace wai meke faruwane kam  Nan TJ yafada masu abinda yafaru yace shine dai sanadin sumansa  Sannan TJ yace dan Allah daddy kuyafe masa wlh yayi nadama kuma yanzu damuwarsa qaruwa zatayi matuqar baku yafe masa ba  Daddy yace hakane Allah ya yafemu gaba daya ya kuma kiyaye na gaba   Dik suka amsa da amin  Suna nan zaune ahankali ya fara motsi   Kadankadan idanunsa suka washe yafara ganin komai tass  Aiko yana ganin su momcy sai yafara hawaye zaiyi magana  Daddy ya kamo hannunsa yace kada kace komai Alamin munyafe maka duniya da lahira saifatan wannan yazama darasi agareka   Momcy ta matso kusa dashi tana shafa kansa tace ya wuce papa ka kwantar da hankalinka sannan matakin daka dauka akanta yayi daidai Allah yasaka maka sukuma Allah ya shiryesu  Cikin jin dadi ya yunqura zaune yace nagode daddy na gode momcy nagode sosai  Momcy tace sai mutafi gida tunda yasami sauqi  Daddy yace muje amaidaka gida sai muwuce   Girgiza kansa yayi yace bazan iya zama acikin wannan gidanba ni gida zan koma   Momcy tace toh shikenan kutaho a motar tijjani inyaso sai kuje kadauko kayanka    Ahankali ya miqe TJ na riqe da hannunsa har mota    Momcyma gida suka wuce Sukuma suna zuwa gida basu tarar da juhaina ba  Nan TJ ya hada masa kayansa suka fito sai anan yayi magana yabawa maigai key yace idan tazo kwasan kayanta ya bude idan tagama ya kulle ya ajiye key din awajensa  Suna tafiya a mota ba mai magana acikinsu   Papa ya kwanta ajikin kujera ya tallafe fiskarsa da hannunsa yayi nisa cikin tunani  TJ yace haba man karage tunanin nan mana haka yanzu ai saidai ka godema Allah tunda kagane gaskiya sannan Allah ya toni asirin munafukai    Cikin damuwa yake kallon TJ yace man damuwata fauziyyah tafi qarfina ta wuce  tinanina fauziyyah ta nuna batama sanniba yazanyi wlh idan ban auri fauziyyah ba mutuwa zanyi sabida ina sonta sonda bantaba jin inayima wata ya maceba aduniya ashe juhaina ma ba sonta nakeba fauziyyah nakeso na yaudari kaina nan idanunsa suka sake kadawa sukayi jajur  Cikin mamaki TJ yacecfauziyyah kuma a ina ka ganta   Nan yafada masa iya abinda yasani da haduwarsu   Tirqashi shine abinda TJ yafada dan yasan tabbas zaayi haka rananda papa ya komwa fauziyyah da sunan so   Papa cikin damuwa yace komai ya jagulemun man,kyiu wati hai bahaa??? Kyiu kyiu (mai yasa wannan canjin yanayin maiyasa maiyasa) ya qarashe maganar kamar zaiyi kuka  TJ yace komai zaidaidaita kaci gaba da addu a kakuma kwantar da hankalinka  Maganar fauziyyah zamu zauna muga yadda zamu bullowa abin  Da haka har suka qaraso gida...   ***** Fauziyyah kuwa tana wucewa awajen tamanta da shafinsa dan sam baya gabanta sannan tunaninsa tsabar tsanan data masa batayi  Qarfe uku ta iso gida sai dai bakowa su momcy basa nan  Wanka tayi ta daura alwala  Sai datayi sallan laasar sannan tayi kwalliya ta shirya cikin wata doguwar riga yar kanti lokacin da zata dawo nigeria tasayeta  Coppee da milk tasha ado mai kyau   Bata saka dankwaliba sai gashinta data kama da milk ribbon ta fesa turare tafito  Tana zuwa falo taga momcy tadawo tace sannu da dawowa momcy  Momcy tace yawwa kindawo baki samemuba munje asibiti ne papa bayada lfy amma ansallamesa ma  Allah ya sauwaqa shine abinda ta furta albarkacin momcy  Momcy tace naga motarki shine na leqa dakinki kina wanka   Tace eh wlh sai danayi sallah tukun nafito   Momcy tace kinci abinci kuwa   Yanzu zanci ta amsa   Kai daugther bakyason cin abinci ko mai yasa toh kije kici   Toh ta amsa sannan ta wuce dinning taci abinci  Falo ta dawo ta zauna kenan su papa suka shigo  Aiko yana kyalla idonsa akan fauziyyah yaji wani sanyi aransa dan baqaramin kyau tamasa ba  TJ ma haka yake kallonta da mamaki ya kuma jinjina abin lalle akwai aiki agaban abokinsa dan yada ko kanta bata dagoba bare tasan da shigowarsu saima wayarta dataketa latsawa   Momcy tace sannu tijjani Allah yabar zumunci papa kushiga mana katsaya anan  Wajema yasamu yazauna yana cewa aa zansha iska kadan anan   Fauziyyah kuwa kamar ta bar wajen amma sai taga kada ya rainata kawai ta matse abinta  Acikinsu ba maimagana dan shi papa kallonta ma yasashi farin ciki sai yaji tsoro kada yamata magana tama bar wajen shiyasa yaja bakinsa ya tsuke   TJ kuwa shakkar mata magana yake kada shima tace bata ganeshiba   Wayarta ce tafara ringing dubawa tayi taja tsaki axuciyarta ganin no Brr.Nabil ne   Yau batasan iya adadin kiran daya mataba kuma bata dauka ba shikuma bai haqura ba   Harta katse bata daukaba sake kira yayi sai taji shaawar ta dauka kodan tasamu hanyar barin wajen   Momcy kuwa miqewa tayi tace barin turo muku da abinci  Fauziyyah cikin daddar muryarta tadau wayar da sallama jin muryarta mai sanyi yasa papa lumshe idanu.....   
.

.
Murmushi yayi sannan ya amsa sallaman  Cikin natsuwa tace ina yini  Fara arsa ya fadada yace lfy dan wani dadine ya lillibesa jin yadda ta amsa da faraa sannan yau har gaisuwa ya samu  Cikin murya mai sanyi yace gimbiyar mata asassautamun mana aidai ko haka na wahala   Juya idanuwa tayi cikin murya mai jan hankali tace namefa  Murmushi yayi sannan yace tinsafe nake kira baki dau wayata ba pls ko shiruma nikiyi amma dai kidauka sai hankalina ya kwanta  Hakan daya fada shiyasa ta wani qayattacen murmushi wadda ya qawata face nata tace ayyah aifa ba dagangan bane ba bani kusane kuma yanzun bagashi nadauka ba  Cikin murmushi yace hakane nagode da kika bani lokacinki amma da zaa taimakamun abani dama nazo gida mugaisa   Shiru tadanyi dan harga Allah bata san takuri amma kuma yau sai takejin nauyinsa sosai   Maganarsa ce ta katse mata tunani  yana cewa ya kikayi shiru pls fauziyyah kibani dama na bayyana maki irin sonda nake maki wlh tunda nake arayuwana bantaba jin son wata mace aduniya kamar yadda nake sonkiba kuma ni inkika amince mun insha Allah zan zamar maki alheri arayuwa amma kibani dama domin kitabbatar da maganata  Jikintane taji ya mutu murus kuma ya tuno mata da wasu kalaman da papa ya taba fada mata abaya   Cikin sanyin murya tace bakomai ur always wellcome  Wani dadine ya lillibeshi yace thanks a lot my life insha Allah gobe da yamma zanzo  Cikin murya mai kamada shagwaba tace gobe kuma gaskiya is to early  Cikin rarrashi yace haba my life ai da zafi2 akan bugi qarfe amin haquri dai nazo goben kinji my life  Murmushi mai dan sauti tace ok Allah ya kaimu   Papa dayakai har wuya dan takaici dan tini ya fahimci da wani take waya   Jiyake kamar ya shige cikin wayar yazugamasa rashin mutunci dan wani kishine ya tirniqeshi dan ya fahimci ya samu waje tinda taketa zuba murmushi    Cikin qunar rai ya miqe afusace yayi side nasa  Ganin yadda ya tashi afuce nan danan fiskarsa ta canja hakan yasa TJ ya tashi yabi bayansa  Adaki yasameshi sai safa da marwa dayakeyi acikin daki  TJ yana shiga yace yadai man lfy kuwa lokaci daya kacanza  Cikin damuwa yace badole nacanba kana kallo cin fuskan da fauziyyah tamun  TJ yace haba man kada wannan ya dameka kabi ahankli mana kadaina bata ranka  Cikin fushi yace wani irin kada na damu bayan fauziyyah ta nuna batasanniba then gashi tana hira da wani awaya harda yimasa murmushi haba haba  Ya qarashe maganar kamar zaiyi kuka   TJ yace pls man cool down ur temper komai zaizo dasauqi da yardar Allah ammafa saikabi komai ahankali kuma daki2   Cikin sauri yace kamar me kenan pls tell me abokina wlh ruwan kaina ya qare i dont know what to do  TJ yace zauna kaji yadda zamu bullo wa lamarin  Zama yayi ya paying full attention nasa akan TJ  TJ yace dafarko abinda nakeso dakai kasauqe dik wani abinda kakeji dashi agefe sannan ka cire saurin fushi kadau hakuri kasa ma ranka  Wannan shine matakin farko dan dole sai kayi haquri   Sannan kasameta anatse kabata haquri akan abinda kamata kanemi yafiyarta dan inba hakaba bazaka taba samun fiska awajentaba matuqar tanajin haushinka tana kuma tuna abinda ya faru abaya  Amma idan har tayafe maka ta haqura to komai zaizo dasauqi  Papa yace wlh nima inada niyyar bata haquri saidai bansan ta ina zan fara ba tunda lokacin data gannima cewa tayi bata sanniba kuma wlh abin yacimun rai ya dameni kuma ya dagamun hankali  TJ yace tafada ne kawai sabida tanajin haushin abinda kamata shiyasa nace kafara bata haquri tukunna  Sannan katattara dik wani halin banza ka zubarshi agefe wannan shaye shayen banza da wofin ka haqura dashi dan ba macen arziqi da zataso mijinta da wannan halin  Papa yaja wani dogon numfashi yace hakane kamtunba yauba dama komai ya ficemun arai kuma dayardar Allah nabar shan komai tinda suma basa qaran mutum da komai   TJ yace good abokina naji dadin yadda ka yadda da shawarina da haka harya kwantar masa da hankali kafin yamasa sallama ya wuce  Fauziyyah kuwa cikin qunan rai bayan takashe wayar ta nufi dakinta dan aduniya ta tsani abinda zai tuno mata da papa baran tasashi a idanunta  Washe gari da safe papa baiko tashiba ta wuce hospital abinta  sai 3 kafin ta dawo gida  Bayan tayi sallah taci abinci sannan ta tsantsara kwalliya sosai    Wajen qarfe biyar saiga wayar Brr. Nabil kan cewar ya iso fa  Mayafinta ta dauka sannan ta fice  Wani murmushi tasake sabida yadda yamatuqar birgeta  Yana jingine jikin motarsa fara tass , sanye yake cikin wani danyen boyel mai kyau da tsada  farare sol wanda sin matuqar amsanshi  Fularsa ta dace da kayan jikinsa haka takalnan qafarsa farare sol, hannunsa daure da agogon azurfa sai kyalli yake  Haka kurum taji ya matuqar birgeta dan harga Allah tana matuqar son mutum mai kamala da shiga ta mutunci  Ahankali cikin takunta mai natsuwa harta qaraso wajensa sallama tamasa cikin siririyar muryarta mai dadin sauraro  Lumshe idanunsa yayi ya bude ahankali dan ta tafi da dikkan tunaninsa kwalliyarta kyan fiskanta uwa uba dirinta sannan daddadan muryanta su suka qara narkar masa da zuciya  Waalaikumussalam barka da fitowa sarauniyar mata  Murmushi tayi sannan ta sunkuyar da kanta ahankaki tace ina yini  Lfy lau ya gida da aiki  Tace dik lfy lau ya naka  Yace well um gaskiya aikinmu ba dadi sai dai shukrah  Tace ayyah Allah ya taimaka, Amin ya amsa  Gyara tsayuwarsa yayi yana cewa yau gani ga gimbiyata dafatan zan samu mazauni acikin zuciyarki   Murmushi kawai tayi batace komaiba dan nauyinsa takeji sosai  Nan yasake gabatar mata da kansa ya kuma tabbatar mata ba dawasa yakeba kuma bashida mata dan baitaba aureba   Cikin gamsuwa da baya nansa tace bakomai amma yabata time tadanyi nazari  Yace badamuwa ya bata kwana biyu ammafa zai ringa kiranta suna gaisawa awaya tace badamuwa  Papa ne ya shigo gida kamar wadda akace ya duba gefensa kawai yaga fauziyyah da wani mutum atsaye sai faman kallonta yake yana murmushi kamar zai cinyeta  Nan take yaji qirjinsa ya buga wani kishi ya taso masa,jiyake kamar yaje shaqesa   Da kyar ya lallami zuciyarsa yayi parkin motarsa ya fito   Cikin gida ya wuce zuciyarsa adagule  Brr Nabil yace to madam nizan wuce naga kamarma na takureki kinyi shiru bakiyin ko magana  Dubansa tayi aa nibaka takurenba kawai dai nagajine yau awajen aiki   Yace eyyerh kishiga gida kihuta toh inyaso da daddre zankiraki   Tace toh nagode sosai Allah ya kiyaye hanya agaida gida   Insha Allahu zasuji bude mota yayi ya miqo mata wata shopping bag mai kyau baby pink colour yace ga wannan bayawa kisha swt  Aa nikam kabarshi nagode   Bata fiska yayi da sigan lallashi yace haba dai pls kikarba badanniba   Yadda ya tsareta da idanuwansa yasa tasa hannu biyu ta amsa tace nagode   Yawwa dear saikin jini yafada yana tada motar  Itakuma juyawa tayi ta nufi cikin gida tana bude qofar falo zata wuce taji anjawo veil nata hakan yasa tayi saurin juyowa  Papa kuwa tunda ya shigo ya gagara shiga ciki dan gaba daya jiyake kamar yaje shaqe wanda yaganshi yana tsaye da fauzinsa   Ganin papa ne yasa ta tsuke fuska tace lfy malam wani abu kake nema  Dubanta yayi da kyau cikin shan mur yace wayene waccan dana ganku tare  Kallon uku saura kwata ta watsa masa tace mene damuwarka da son sanin wayeshi kumama kaidin wayene dazaka tsareni kanamun wasu silly question  Cikin zafin zuciya yace au bakisan niba kikecewa ma    Tace eh banma taba ganinka tunda kadamu kaji wayeshi mijin dazan aurane ar u satisfied now  Yace lalle kinyaudari kanki barin fada maki bakida miji saini kuma ke matata tace sabida haka da kin daiba yaudarin kanki  Wani murmushi tayi na takaici tace Allah ya sauwaqa ni nazama matarka kuma ma kaga mundace dakai ne  Kadubi yanayin Brr. da shigarsa ta mutunci da kamala shine yadace da mijina ba kai wadda ko shigar mutunci baka iyaba dan shayeshaye kawai mazinaci Allah ya mun katangar qarfe tsakani na da kai kuma ni kadaina iqirarin matarka ce bansankaba bantaba saninkaba arayuwata tana fadin haka ta wucesa abinta .........

  .

Jikinsane yayi sanyi jin yadda take fadan munanan halayensa wadda ashe tana riqe dasu acikin ranta  Yadan jima kafin ya nufi side nasa cikin tunani kalakala  Zama yayi yana nazarin hanyar da zaibi ya wanke kansa awajen fauziyyah   Yanason ya shafe dik wani tunanin dake akansa na halayen banza ta daukeshi a mutumin kirki  Shiru yayi yana nazarin hanyar da zaibi kuma tabbas dole ya dauki shawaran da TJ yabasa idan yanason gane kanta tinda haryanzu tana riqe dashi da abinda ya mata acikin zuciyarta  Cikin sanyin jiki ya dauko wayarsa ya lalimo layin TJ yafa kira   Bayan sun gaisa papa yace TJ pls gobe irin 10am inason karakani wani waje mana  Ok Allah ya kaimu ya jikin dai   Dasauqi sosai thanks saimun hadun  Yana ajiye wayar yafara tunanin gara yafara shigan mutanen kirki wataqil fauziyyah tacanza tunaninta akansa tunda har take kwatance da

  ******
Itakuwa tana wucewa dakinta ta shige zuciyarta namata zafi cos tunawa da irin azaban da papa ya mata abaya   Allah ya qara ta furta afili dan momcy ta bata labarin matar papa   Tunani take wani irin mataki zata dauka akan katsalandan dayakeson ya mata arayuwarta   Shiru tayi kafin ta miqe ta shige toilet dan kanta harya mata nauyi gashi dama a gajiye take  Washegari bayan papa ya fita office ya dan duba patients nasa ten thirty ya fito ya nufi office din su TJ  A office ya sameshi yace ya zamuje ne ko kana da ayyuka mubari sai da yamma  TJ yace ina zamuje ne kam   Papa yace inda kake sayan kaya daka rakani saimuje wajen tailor naka dinki nakeso amun   TJ yace lalle nayarda abokina kacanza   Papa yace wlh jiya fauziyyah tafadamun abinda ranta yakeso nan yabasa labarin yadda sukayi  TJ yace ainafada maka ajiye fushi zakayi agefe har kasamu kanta dan wlh dama can kasanta yar zafin kaice baran yanzu data san ciwon kanta  Nan suka fito suka nufi shago inda TJ ke sayayya nan yasayi shaddodi da boyel kala ashirin sannan yasayi huluna masu kyau da tsadar gaske   Daganan suka wuce wajen tailor inda suka bashi dinkuna suka biya shi kudin express dan basason ya jima  Office ya maidashi akan sai da yamma zai shigo gida  
.
Fauziyyah kuwa da wuri ta dawo gida yau da yamma ta shirya tsaf cikin wani sari sky blue wadda idan kaganta zaka rantse da Allah kace yar india ce  Nan tacema momcy zataje gidan khairy tinda tadawo batajeba  Momcy tace toh saikin dawo amma kada kiyi dare tinda ke kadaice zaki fita  Cikin ladabi tace toh momcy  me abi ayaho (saina dawo)  Momcy tace Allah ya kiyaye hanya adawo lfy  Tana fita gidan khairy ta wuce cikin murna khairy ta tarbeta nan suka zauna afalo suka fara hiran yaushe gamo  TJ ne ya fito dan khairy ta fada masa zuwan fauziyyah  Zama yayi agefen khairy yana cewa hajiya fauziyyah ce agidanmu kodama bata gane mutane amma dai kekam nasan bata mantakiba yafada yana kallon khairy  Murmushi tayi dan tafahimci inda maganarsa ta dosa   Tace habaya Tijjani ni na isa nace banganekaba  Yace ah ranan agidan momcy kikayu kamar bakisanmuba  Tace kasan kazauna kusa da baqon fuska shiyasa kaima sai kabacemun amma yanzun bagashiba nazo har gidanka  Fauzy kenan kinzo dai wajen khairy  Tace dikkanku dai wajen ku nazo    Yace toh ya aiki da haquri damu  Tace aiki mungode Allah saita juta zancen da fadin banga mubeen bafa ko baccin yamma yake  Khairy tace aa baya nanma tun jiya yaje gidan hajiya (gidansu TJ)  Tace ayyah nan sukayi ta hiransu dik akan karatu nema dan khairyma tayi jamb admission take jira  Can wajen magriba fauziyyah tace bari ta tafi   TJ kuwa da tun dazu ya fita ashe suna tare da papa awaje   Nan sukayi sallama ta rakota har bakin mota tana cemata tagaida momcy itama zatazo  TJ kuwa ganin fauziyyah ta fito yasa yayi sallama ma papa ya wuce cikin gida dan dama yafadama papa tazo  Shima cikin sauri ya mufo inda take tana qoqarin bude mota ga hadari ya hadu baqiqirin ashe suna ciki basusan da hadarin ba   Assalamu alaikum yamata sallama juyowa tayi dan bata taba tunanin shibane tinda a iya tsawon zaman da sukayi har zuwa yau bai taba yimata sallama ba   Juyowa tayi dan ganin waye acikin gidan kuma dai ba muryar TJ ba kawai sai taga papa tsaye ya harde hannayensa aqirji  Tana ganin shine ta wani hade rai ta tsuke fiska tayi kamar bada ita yakeba ta bude motarta ta shige  Hannunsa yasaka ya riqe murfin motar yace pls ba danniba ba dan halina ba kiyi haquri kisaurareni   Dagoda manyan idanuwanta tayi ta watsa masa wani kallo batace masa qala ba tasa hannu ta jawo murfin motarta  Saurin janye hannunsa yayi da ta buge masa hannu  Key tayi ma motar zata wuce ta barshi  Shiru yayi yarasa abin ma zaice saiyaji sauqar yayyafa akansa hakan yasa ya juya ya shiga motarsa yabi bayanta  Suna fita ruwa ya kece kamar da bakin kwarya hakan yasa tafiya take ahankali shima yana bin bayanta har suka iso gida   Yana shigowa gate ko cikakken parking baiyiba ya fito ya nufi wajenta  Ita kuma tanayin parking tunani tafara ta fito acikin ruwanne ko ta zauna ya dan ragu  Kura idanu tayi tana ganin yadda ruwan ke sauka sai ta hango papa ya nufota   Cikin sauri ta bude qofar motar ta gwammaci ruwan ya jiqata than ace yazo wajenta  Aiko tana bude qofar motar ta zura qafarta kenan ya qaraso ganin haka yasa tajawo qofar zata kulle  Cikin azama ya saka hannu ya riqe, ganin haka yasa ta maida qafarta ciki batace masa qala ba  Shima baiyi magana ba sai ruwa dake dukansa haryafara diqa  Yakai 5mins ahaka yana tunanin mai zaima fauzy ta saurareshi kawai saiya durqusa awajen cikin ruwa ga kuma tasama ruwa na dukansa  Kallonsa kawai takeyi   Cikin murya mai rauni yace fauziyyah banida bakin da zan baki haquri akan abubuwan dana maki abaya wadda son zuciyata ya jani aikata hakan  Kuma nasani bacin ran abinda namaki ne yasa kike nuna baki sanniba  
.
Amma kiyi haquri badan niba sabida Allah kiyafemun abinda namaki kozan samu salama arayuwata domin alhakinki yayita bibiyana kuma nagane kuskurena   Fauziyyah saima ta juyar da kanta dan bataji alamun zata sauraresa ba kuma ita dama matsa mata yayi ta wuce abinta dan batajin zata iya yafe masa abinda yamata   Ganin bata tankashi ba saima juyarda kanta datayi sake qasa da murya yayi kaman zaiyi kuka yace kefa musulma ce na roqeqi kiyafemun sabida Allah badan niba   Yadda ya marairaice murya saitaji tausayinsa ya kamata amma data tuna irin walaqancin daya mata abaya duka zagi azabtarwa sai taji wani sabon tsanarsa   Jakarta ta jawo afusace ta hankada murfin motar ta wuce tagefensa tayi cikin gida da gudu tana shiga falo wani kuka ya kubce mata direct dakinta ta wuce tana zubda hawaye  Papa kuwa yadda ta barshi awajen yakai minti goma baiko motsa ba yarasa wacce hanya zaibi ya samu yafiyarta wasu hawaye masu zafi yaji suna zuba akan fuskarsa   Kuma hakan datayi ko kadan baiji haushintaba sabida yasan abinda yamata bana kadan bane  Tashi yayi ahankali ya nufi cikin gida yana shiga shima ya wuce dakinsa cikin qunan rai ya dauko sigari ya kunna amma sam ko zuqa daya kasawa yayi haka ya kashe sabida alqawarin da yayima zuciyarsa yabar shan komai    Momcy da daddy suna tsaye jikin window suna kallon dik abinda sukeyi har suka shiga cikin gida  Momcy ta juyo tace daddy kaga papa ko tun bayauba nafahimci taketakensa kawai kallonsa nake naga iyaka gudun ruwansa    Daddy yayi murmushi yace aini tun rananda yafara ganinta nafahimci inda ya dosa sabida yadda lokaci daya ya birkice nan yafada mata yadda sukayi dashi   Momcy tace zaici qaniyarsa ai dan kuwa akwai wadda fauziyyah takeso har jiyama yazo da yamma  Daddy yace good haka nakeso Allah ya daidaita su shikuma zaigane kurensa   ***** Tana shiga daki ta kwanta akan gado tai kuka harta gode Allah kuma tarasa dalilin kukanta  TJ ne ya kirasa dan yaji yadda suka qare cikin damuwa ya zayyanema sa yadda sukayi yace TJ i dont know what to do nayi iyaka qoqarina amma ko saurarana batayi pls TJ help me out  TJ yayi shiru yace shikenan zansan abinyi amma kaci gaba da addua dakuma lallaminta harta amince  Suna gama waya TJ yasamu khairy ya fada mata halin da ake ciki ya roqeta taje gidan momcy gobe ta taushi fauziyyah   Da yamma washegari bayan fauziyyah ta taso aiki sukayi waya da khairy TJ ya kawota  Saida suka shiga daki bayan sun gaisa da momcy nan khairy tafara bawa fauziyyah baki akan ta haura tayafewa papa  Fauziyyah tace dake bake akaciwa mutunciba ko dole mijinki ya dauko yakawo mana saboda abokinsa   Khairy tace wlh ko kadan nibadan haka bane kefa musulmace kuma kada kimanta Allah ma muna masa laifi kuma muroqi yafiyarsa ya yafe mana  Kiyi haquri komai ya wuce wlh Dr yayi danasanin abinda yamaki kuma tunda harya baki haquri saiki hakura kodan albarkacin su daddy   Shiru tayi tana tuna irin walaqancin daya mata sai hawaye   Nan khairy taita lallashinta tace kimanta abinda yafaru abaya matuqar kina tunawa to bazaki taba haquraba   Tabbas kowa yasan abinda papa yamaki bai kyautaba amma ai yaga sakayyah nishawara nabakk ba doleba amma kiyi tunani akai  Fauziyyah tace nagode khairy Allah ya bar zumunci kuma insha Allahu komai ya wuce amma nance kifadama mijinki ba         Khairy tace oh miye laifin Abban mubeen wlh har kullum shi yana bayanki fa   Ya tsina fiska tayi tace tunda abokin ya Alamin ne shiyasa baruwana daku ai   Khairy ta sheqe da dariya tace toh amana afuwa     Dariya sukayi gaba dayansu sai bayan magriba sannan tamata sallama ta tafi..... 

.

Aranan bayan tafiyan khairy taita tunani takuma gamsu da shawarin da khairy ta bata kodansu daddy ma ya cancanci ta yafe masa kuma kodan tasamu yarabu da ita zata furta masa kalmar yafiya    Tindaga ranan suka shiga wasan boye, dik hanyar datasan zai hada ta da papa ta kaurace masa  Papa kuwa dik yadda yasan zai hadu da ita yanayi amma abin ya faskara   Har sati biyu rabonda su hadu, a hospital kuwa baiyi gigin zuwa wajenta ba dan kada ta yankwanasa acikin mutane gashi kowa yana ganin girmansa  Amma ya qudiri aniyar kota halin qaqa sai yayi magana da ita sabida haka yau da wuri ya shirya saida ya daidaici lokacin fitanta sannan ya fito  Cikin saa kuwa yasamu momcy da daddy ma dik suna break fast sabida daddy zaifita shima   Assalamu alaikum ya masu sallama yana ajiye jakar system nasa akan kujera a falo  Dik tsayawa kallonsa sukayi   Fauziyyah data debo abinci zata kai bakinta sai ta daga idanunta ta kalloshi itama abin mamaki ya bata   Yau sanye yake da wata dakakkiyar shadda army green tasha aiki mai tsadar gaske   Hularsa kalan kayansa ga wani agogon azurfa dagani ba tambaya kasan kudinsa dayawa  Abinka da farin mutum sai yafito kwarjininsa ya qaru akanna nada dan kayan baqaramun karbansa sukayiba  Abinda ya basu mamaki shine rabonsa da saka manyan kaya haka tun bikinsa da juhaina wadda shine na biyu daya taba saka jumper arayuwarsa  Amma kuwa saiya karbeshi sosai ya fito masa da kamalarsa na cikakken mutum  Qarasowa dinning din yayi yana cewa mornimg daddy morning momcy  Momcy tayi murmushi ganin sauyin da take gani awajen danta tace morning son har anfito yau da wuri haka  Umm inada wani aiki shiyasa na fito da wuri  Daddy yace Dr yaukuma aure zakaje daurowane ba katin gayyata  Murmushi yayi yana sosa keyarsa yace haba daddy kawai dan nasaka saiya zama aure zanyi  Daddy yace ah toh nasani tunda baswa kakeyiba saida dalili  Murmushi yayi yace aa kam kawai nayi shaawar sawane  Daddy yace ko kaifa amma mutum kullum cikin qananun kaya dik jiki atakure amma nasan yau kafi jinka very compotable haina(koba haka ba)  Hakane daddy ya fada yana daukan fork dan shima abincin zaici  Fauziyyah kuwa da tunda ta kallesa sau daya bata qara bin takansa ba bata kuma cemasa kala ba saima ajiye cokalinta tayi ta miqe zata bar wajen  Momcy tace badai kin qoshiba   Cikin shagwaba tace naqoshi momcy zan wuce office  Daddy natafi saina dawo  Momcy tace toh Allah ya tsare hanya daddy ma yamata addua adawo lfy sannan ta fice  Papa kuwa harta fice kallonta yake sabida komai nata birgesa yake baran ya kwan biyu baiganta ba  Haka muryarta baqaramun dadi take masa ba koda masifa take muryarta dadi takeyi baran yanzu dayaji yadda tayi magana ashagwabe sai yaji taqara birgesa  Zama yayi ya break nasa hankali kwance koba komai ganinta da yayi yasami natsuwa  Yau aiki ya riqe masa wuta sosai gashi ranan saturday mai zuwa zaayi bikin sabon asibitin da suka bude mai suna *NAMSA MEDICAL CENTER*   Tinda ya dawo suna tare da daddy har suka fita masallaci tare   Ranan saturday aka bude sabon asibiti hadi da walima  
.
Manyan mutane sun hallarta sosai sannan abin ya qayatar abin birgewa  Da yamma momcy ta shirya walimanta acikin gida inda itama ta gayyaci yan uwa da abokan arziqi  Fauziyyah kuwa tinda aunty mabarukha tazo suna tare har aunty niima tana mata tsiya   Papa kuwa tinda ya dawo yana kwance adakinsa dan yagaji sosai tashi yayi ya wanka ya shirya cikin wani danyan boyel ash colour wanda yamatuqar amsan fatar jikinsa ya kafa hulan nan kamar wani ango   Har ya juya zai fita sai yaje jikin window ya daga curtain dan yagani kozai samu ya fice dan tun daxu yakejin hayaniyar mutane  Kamar wasa ya hangi fauziyyah tasha ado da kwalliyah cikin wani matetial maroon colur dinkin doguwar riga   Ta kafa dauri tayi kyau sosai   Tana tahowa kallonta yake yaga inda ta nufa saiyaga ta shige lambu ta qofar baya inda ake shiga bayin fulawa aiko cikin sauri ya fito ya nufi lambu shikuma ya shiga tacikin falo  Can ya hango ta zaune akan kujera da waya akunnenta   Itakuma wayarta da aka kira yasata shigowa lambun  Qarasowa yayi inda take zaune yaja kujeran gefenta ya zauna  Dagowa tayi ta kallesa sai tayi kamar bata gansaba taci gaba da wayanta ita da Barr.Nabeel  Daure zuciyarsa kawai yayi yanajin yadda take fadan kalaman soyayyah dikda baisan itada wayeba amma yana tunani itada wanda yataba ganinsu tarennan ne  Takai tsawon minti goma tana waya sannan tayi sallama tana sauqe wayar akunnenta ta miqe zata bar wajen  Cikin sauri ya riqo hannunta juyowa tayi afusace ta wurgesa da wani matsiyacin kallo  Saketa yayi da sauri wanda abu biyu yasa yayi saurin sakemata hannun  Nafarko wani danbanzan shorck dayaji kamar wadda wuta ta jashi na biyu wani kallo data watsa masa  Fiska atsuke tace malam wayabaka izinin riqemun hannu  Atausashe yace am sorry pls badagangan bane   Juyawa tayi zata wuce yayi saurin cewa pls Fauziyyah kisaurareni mana tunda nazo wajenki kinsan da magana nazo  Ko kulashi batayiba ta wuce abinta   shan gabanta yayi hakan yasa dole ta tsaya   Pls fauziyyah nasan cewa namaki laifi amma mutum idan yagane kuskure ya roqi yafiya aisai ayafe masa   Kifadi abinda kikeso namaki danki yafemun   Shiru tayi tana sauraronsa yadda yake bata haquri kamar zaiyi kuka tabbas ya Alamin ya sauya  fiye da tunaninta  Roqo yake magiya yake haka ya durqusa awajen   Wani iri taji aranta tana tunanin yadda mutum ke sabawa Allah yaroqeshi gafara ya kuma gafarta masa asheko inhakne dole ta yafe masa  Cikin sanyin murya tace ya isa haka ya Alamin yawuce har abada Allah ya yafemu gaba daya amma dan Allah na roqeka daga wannan kada ka kuma shiga harkata koda magana bana buqatar yahadamu  Wani zufane ya yanko masa yace ashe ko inhakane baki haquraba kada kimanta kefa yar uwatace nidan uwankine  Tace yau kenan kasan da wannan yafiyakam nayafemaka har zuciyata kawai alaqa dakaine bana buqata tana fadin haka ta wuce abinta  Jiki asanyaye ya tashi ya wuce dakinsa yaji dadin yadda ta yafe masa amma yadda ta furta wai bata qaunar alaqa dashi shiya damesa gashi riqe hannunta da yayi shiya tuno masa wasu lokuta daya samu kansa acikin zamansu nabaya  Fitan dabaiyiba kenan ya kwanta jikinsa amace..... 

Soyayyah mai karfice ta shiga tsakanin Barr. Nabil da Fauziyyah   Soyayyah mai tsafta suke gudanarwa atsakaninsu  

.

Kamar wasa son Brr. Nabil ya shiga zuciyar Fauziyyah sabida kyawawan halayensa da son addininsa da kuma yanda yake nuna mata zallar kauna da baya gajiyawa da dik irin abinda take masa na halin ko inkula  Ayanzu ta amince da aurensa kuma tayi naam dahakan har zuciyarta   Afannin Barr. Nabil shima yayi farin cikin amincewarta  Inda yanzu har gidansu sun san yana nemanta   Ummansa tayi farin ciki sosai sabida bata da burin daya wuce ganin dannata yayi aure   Kusan kullum sai yazo gida sunsha hira abinsu dan momcy da daddy ma sunsan da zamansa haryazo ya gaidasu kuma sun amince dashi dan sun yaba da natsuwarsa  Wani lokaci yakanzo asibiti ya sameta sabida yanda yake qaunarta dik lokacinda yaji yana son ganinta saiya taho abinsa   Dik abinda kefaruwa papa yana sane kawai ba yadda ya iyane kuma abinna daminsa kawai baya da mafita ne  Dik lokacin dayayi niyyar yimata magana idan ya tuna kalmar datace wai bata buqatar yin alaqa dashi sai yaji zuciyarsa ta masa zafi  Yauma kamar kullum Brr. Yazo sun hira kasancewar saturday ne dik suna gida  Tun zuwansa papa yake tsaye jikin window yana kallonsu yana jin wani zogi acikin zuciyarsa dan ahar kullum son fauziyyah qaruwa yake axuciyarsa   Yakuma yi niyyar dik abinda zai faru saidai ya faru amma yagaji da wannan walaqancin da cin fuskar da take masa sabida zuciyarsa ta aminta kawai dagangan take masa haka  Itakuwa batamasan yana yiba dan baya gabanta baran tamasa abu da gangan  Yana nan tsaye yanajin zuciyarsa kamar tafashe dan baqin cikin yadda yahango su suna ta dariya abinsu basa da matsalar komai  Tinda yahango Brr. Zai tafi ya fito ya tsaya aqofar falo ya harde hannuwansa aqirji yana jiran isowanta   Kamar wadda akace Brr. Ya juyo aiko ya hangi papa fiskannan ba annuri  Duban fauziyyah yayi yace my life nikam wancan yayan nakin haka yake bai magana ma mutane ne  Cikin ko inkula tace me kagani  Yace sau uku muna haduwa ina masa sallama amma ko ya kulani last zuwana hospital wajenkima mun hadu zan fita shikuma zai shigo ina daga masa hannu amma yayi kamar bai ganniba  Tabe baki tayi tace next time kada kasake kulasa ka rabu dashi kawai  Yazakice haka baicin dan uwankine yafada yana kallonta  Tace to halinsa ne haka idan baiga dama ba kozaka kwana kana masa idan baiga dama ba bazai kulaka ba  Jinjina kai yayi azuciyarsa yace amma ko baida hali afili kuma yace Allah ya kyauta nizan wuce sai munyi waya  Tace toh Allah ya kiyayae hanya agaida umma dasu sis raudah  Toh zasuje sannan ya tafi  Aiko tana nufowa cikin gida tinkafin ta qaraso papa ya taho ganin haka yasa ta kauce ta wucesa   Fauziyyah Fauziyyah Fauziyyah yake kiran sunanta amma ko ta amsa baran ta tsaya  Pls kisaurareni mana ya ina maki magana zaki maidani dan iska   Har takai qofar falo tasa hannu zata bude dan bata da niyyar amsashi  Cikin zafin nama yasa hannu ya fincikota baya  Aiko nan tayo baya kamar zata fadi sabida da iyaka qarfinsa ya janyota dan ransa yagama baci   Cikin sauri ya tarota ta fado akan chest nasa   Wani yarr gaba dayansu sukaji lokaci guda wadda hkan yasa papa sauqe wata wahalalliyar ajiyar zuciya hadi da lumshe idanu  Wani kasalane ya sauqo mata jin yadda ya maqale hannunsa ya zagaye waist nata  Kome ta tuna cikin sauri tasa hannu biyu da iyaka qarfinta ta turesa   Amma kuma takasa barin wajen sabida yadda qafafunta suka mata nauyi  Cikin dakewar murya tace meyasa bazaka rabu dani nasha iska ba abaya kace yafiyata kake buqata kuma na yafe maka to yanzu kuma what else kake buqata ta qarashe maganar cikin fada  Shima da fada fada yafara magana dik da irin yanayin dayake ciki amma dake ta tabomasa indake masa kaikayi yace   Nagaji da irin azabtar dani da zuciyata da kike yi nagaji da ganin walanqancin da kike mun agabana kina tsayawa da wani da wani noo wlh kadana kuma ganinki da wani dan iska agidannan ko awani waje   Da mamaki take kallonsa kawai yadda ya haqiqance yana masifa kamar zai daketa   Cikin jin haushi tace toh miye damuwarka kuma miye hadinka dani dazakazo kanamun wasu magana marasa maana da dadin sauraro  Oh maganan tawace marar maana ya tambayi kansa wani haushi ne yasake kamasa kallonta yake ido cikin ido yace becouse meh tumse pyarr kartahoo( sabida inasonki)  Wani wawan kallo take binsa dashi tagagara cewa komai sai idanu kawai take binsa dashi cos she is totaly speechless   Ahankali bakinta ya furta pyarr(so)  Yess hah kahona pyarr hai(eh inasonki)  Girgiza kanta tayi cikin wani qunan rai dan ji take kamar ya watsa mata dafi  Tace kayi gaggawar fadin istigfari   sabo nayi yafada yana kallonta  Tace aiya wuce saboma inka manta na tuna maka  Kaikuwa mai zakayi da yar qauye qazama wawiya jaka yarinya qarama wadda batada abin shaawa baran na marmari      Wani zufane ya fara tsatsafo masa ta ko ina jin yadda take jero abinda ya dinga fada mata abaya wato bata manta ba  Gagara magana kawai yayi dan baya da tacewa bai kuma san ta ina zai fara ba   Tsabar bacin rai idanunta sunyi qanana da kakkausan murya tace wlh ka cuceni kuma baa taba fadamun baqar magana irin wadda kafadamun ayanzuba wai kana sona bakaji kunyar fadin haka ba   Nace bakaji kunya ba toh koda maza sun qare kaikam nayafe akai kaya masauqi  Sai anan yayi magana yace dik abinda zakifadamun kifada matuqar zaki huce all i know is i luv u with all my hrt  Tace nikuma i hate u n i really hate u ta zuga masa wani wawan tsaki ta wuce tace kana wasting mun time da alama bakada abinyi  Tana wucewa shikuma ya koma da baya ya nufi lambu cikin damuwa kozai samu sauqi da zogim da zuciyarsa takemasa  Tin daga ranan yake binta kullum cikin roqo da ban baki yake akan tasaurareshi amma sam baya samun fiskanta abin duniya yamata zafi yarasa madafa baran taka maimai  Ya rame ya fada sabida ko abinci bai iya ci damuwarsa fauziyyah ta aminta dashi ganin bashida mafita yasa ya yanke shawaran zuwa wajen daddy dik abinda zaayi ayi kawai shidai adawo masa da matarsa....

0 comments:

Post a Comment