BUDURWAR KAUYE Page 36-40
.
Kwanansa biyu yana shawarin taya zai tinkari su daddy baicin abinda ya faru abaya Cikin kwanaki biyun nan damuwarsa ta tsananta sosai Har momcy ta gaza haquri sunayin dinner tace baba na lfyrka kuwa two days dinnan Dagoda kansa yayi hadi da qaqalo murmushin dole yace mene kika gani swt momcy Naga dik kacanza irin u look so sad haka kamar bakada walwala Sake murmushi yayi yace babu komai sai dai stress din aiki kawai Toh Allah ya taimaka tafada amma badan ta yarda da abinda yace ba Washegari bayan sallan ishai ya yanke shawarin zuwa wajen daddy Bayan yayi sallah gami da adduoi akan Allah ya dorasa akan daddy dan yasan idan daddy ya amince zance ya qare Falon daddy ya nufa zuciyarsa na dukan uku2 da sallama ya shigo yasami waje ya zauna Daddy ne kadai yana kishingide yana kallon tashar CNN Dago kansa yayi yana amsa sallamar Zama yayi yayi shiru yana tunanin ta ina zai soma magana Daddy ne ya katse masa tunani da fadin yadai Alamin kaxo tayani hira ne Dan sosa kansa yayi yace um eh daddy naxo taya ka hirane sannan akwai maganar danazo da ita Ok inajinka ya akayi Cikin dakewar murya yace umm dama daddy alfarma nazo nema wajenka Uhum go on name fa daddy yafada yana kallonsa Cikin sanyin murya yafara magana daddy dan Allah badan niba kataimakamun yadda Allah ya taimakeka kadawomun da matata wlh nayi nadama kuma nagane kuskurena bazan sake aikata makamacin abinda yafaru abaya ba Kallonsa daddy yake sosai yace Alamin banfahimcekaba explain to me further Cikin murya mai rauni yace daddy nayi nayi iyaka qoqarina fauziyyah taqi ta saurareni wlh daddy inasonta zan iyah shiga wani hali matuqar fauziyyah ta gujemun Dan Allah kasa baki daddy kataimakeni tunda tanajin maganarka yaqara maganar kamar zaiyi kuka Daddy yace kafazomun damagana adunkule kafito straigh forward kayi magana mana Toh daddy gaskiya matata fauziyyah nakeson adawomun da ita Wani kallo daddy yake binsa dashi kamun ya tashi daga kishingidar dayake ya zauna dakyau yana dubansa Yakai minti biyu kafin yace Alamin kana da hankali kuwa kasan me kake fadi kuwa tohma ta ina tazama matarka ko kamanta da ba aure atsakaninku Daidai shogowar momcy kenan Zama tayi agefen daddy tace lfy kuwa meya faru daddy? Daddy yace wai cewa yake adawo masa da matarsa Cikin takaici momcy ta dubesa tace ashe bakada hankali bansaniba Ta ina kataba ganin anmaida aure akan saki uku eye? Nadauka kayi hankali ashe dasaurnka haryanzu daka samu Allah ya taimakeka ya rabaka da raqai dakuma lfyrka shine zaka tono wani abinda baxai yiyuba Daddy yace baki fahimcesa ba ashe ai gara yace amayar masa da matar da yayima saki uku akan abinda yazo dashi amma gaki gashi ya maki bayani da bakinsa Duban papa tayi cikin rashin fahimta tace nifa kunasani aduhu wai meke faruwane Kansa tsaye yace matata fauziyyah nakeso adawomun da ita What? Shine abinda momcy tafada tana kallonsa kafin tace toh gaka ga daddy wannan ba magana ta bace Daddy ya kallesa da kyau yace kasaurareni da kyau kaji abinda zanfada maka Abinda nakeso dakai kada nasakejin wannan maganar abakinka koda kuwa awasane Daddy dan .... Daga masa hannu yayi yace banason jin wata magana daga bakinka ingar akan shirmen banzan nanne Juyawa yayi wajen momcy yace pls momcy kitaimaka mun ki.... Itama katsesa tayi tace papa tashi kafita saida safe dan banason damuwa kajiko Daddy yace oyah tashi kabani waje stupid kawai Jiki asabule ya miqe ya fito harjinsa yake kamar bashida nauyi tsabar yarasa tudun dafawa Ranan haka ya kwana idonsa biyu cur tsabar damuwa da rashin madafa Tunani iya tunani yayi amma yaga bayada mafita dole wajen daddy zai koma amma bari ya bari sai bayan kwana biyu Cikin kwana biyun nan dik wanda yagansa yasan yana cikin damuwa matsanan ciya Idan ya fita aiki acan zai wuni daya dawo ya shige side nasa sai dai sallah ke fito dashi ko cin abinci bai zuwa yadawo shiru abinsa iya da safe ya gaidasu kafin ya fita ko break bai tsayawayi Bayan kwana uku yauma yasake dawowa wajen daddy Daddy naganinsa ya bata fiska yace yadai kagama fishin da kake damune? Girgiza kansa yayi yace wlh ko daya nibana fushi daku taya zanyi fushi daku kuma Dan Allah daddy kasaurareni kataimakeni kamayar mun da matata kuma ko wanne irin sharadi ka shimfidamun na amince zanbi zanbi Daddy yace kai banace banason sake jin wannar maganar ba Idan har aure kake buqata ko a inane ka nemo zan shige maka gaba amma banda fauziyyah Yarinya mai hankali da natsuwa ba irinkaba ai kaikam da ita kunyi hannun riga dan bata dace dakaiba baka dace da ita sabida haka kwarya tabi kwarya Kuma aidai kana sane cewar aurenta ma ya kusa ko Dam yaji gabansa ya buga Yace yes aurenta ya kusa ko atunaninka zaa maimaita irin abinda ya wucene asake rabata da masoyinta na gaskiya abaka kaje ka wulaqan tata aidai ko kulya mutum ya ajiye zai kula da ita bare mutum dan adam bayan kagama azabtar da ita hakan bai makaba sannan kazo gabana kamata sakin walaqanci ka tozartani ko kana tsammanin na mantane wannan cin mutuncin dakamun haba haba cikin tsawa yace katshi kafita agabana kada kasa nayi abinda banyi niyyaba kafita nace Durqusawa yayi yana hawaye ya riqe kafar daddy yana cewa nasan nayi kuskure kuma ban kyautawa kainaba daddy nayi danasanin abinda na aika ka taimakeni daddy kada karabani da fauziyyah wlh inasonta kuma itace rayuwata kada karabani da rayuwata Daddy yace baka sotaba saida kaga tazama mutum ko kuma aikai kanisanta kanka da ita sabida haka kaje kasamo uwar mata ka aura wannan yarinyar ba saarka bace Riqe daddy yayi yana kuka yana roqonsa amma daddy sam bai saurareshiba saima kwace qafarsa yayi ya wuce abinsa yabarshi durqushe awajen yana kuka .....
.
Momcy da ta taho wajen daddy tinkafin taqaraso taji kamar alamun gunjin mutum na kuka Cikin sauri ta qarasa hankali tashe bako sallama ta fado cikin falo Turus tayi ganin papa durqushe yana kuka Dasauri ta qarasa wajensa tana tambayarsa papa meya faru nace meya faru Bai amsataba sai rungumeta da yayi yana kuka Cikin tsanin tashin hankali dan batasan meke faruwa ba tace am asking u kya hua(ina tambayarka meke faruwa) Da kyar ya iya furta momcy pls help me wlh inasonta inasonta bazan iya rayuwa ba ita ba kitaimakeni ki lallashi daddy yayi fushi dani yana magana yana kuka kamar qaramin yaro Wani iri taji har cikin ranta kuma yadda taga papa ya gigice tabbas yanzu yanason fsuziyyah kuma so mai tsanani sai dai ba yadda zaiyi saidai yayi haquri tunda dama shiya sake damarsa tun farko Wani irin tausayinsane ya kamata haka takejin kukansa har cikin ranta amma haka ta danne zuciyarta Tace toh me kakeso namaka papa baicin what ever happens is all ur fault Yace i know momcy nina janyo ma kaina kuma wlh nayi dana sanin kuma tun fauziyyah bata dawo nagantaba nake fama da matsanancin sonta bawai yanzune nafara sonta ba kiyi wani abu momcy Ganin yadda ya birkice yaketa surutai yasa ta saka hannunta tana patting bayansa smoothly hadi da lallshi Haba papa ya kana abu kamar qaramun yaro uum Ya isa haka nan ka kwantar da hankalinka ko so kake wani ciwon ya kamaka Look at ur self ya kacanza just in two days haba Nidai kawai kitayani bama daddy haquri sannan hankalina ya kwanta Naji amma saika kwantar da hankalinka tukunna Shiru yayi ya kwantar da kansa akan cinyanta yana sauqe numfashi Miqewa tayi tariqe hannunsa suka nufi side nasa Fauziyyah dataji maganar momcy cikin firgici baicin tare suke zaune ta wuce wajen daddy ta barta hakan yasa tabi bayanta da sauri Tana zuwa bakin qofa ta tsaya jin maganar dasukeyi akantane Cikin damuwa itama ta fara hawaye kuma jin yadda alamu momcy zatabi bayan danta tunda gashi ta nuna damuwarta akansa Wani iri taji har ranta yadda momcy ta dauketa tamkar yarda ta haifa acikinta amma ace tasanadinta ta janyo mata tashin hankali Sai dai duk da haka batajin zata iya komawa gidan papa gara ta sanarma Brr. Ya turo kawai tinda dama ya matsanta mata itace take dan jan abin Jin takun fitowansu yasa tayi saurin barin wajen ta nufi dakinta tana hawayen da batasan dalilin yinsa ba Dakinsa sukaje tace maza jekayi wanka barinzo ko Abinci ta kawo masa ta lallabashi yaci sosai sannan tace ya bari zuwa kwana biyu zata lallami daddy amma sai inhar ya kwantar da hankalinsa Bayan kwana biyu da faruwan haka suna zaune da daddare dikkansu afalo daddy yace ma fauziyyah daugther dama inason sanar dake kifadama Nabeel ya turo iyayensa maganar aurenku amma kafinnan zanyi magana da Abba muji wacce rana ya dace asaka zuwannasu Wani irin tsinkewar zuciya taji wadda batasan dalilin hakanba Papa kuwa da kyar yasamu ya lalimo numfashinsa wadda yayi barazanar daukewa Ahankali ta furta toh daddy Momcy kuwa shiru tayi harga Allah tanason papa da fauziyyah tunda yagane kurensa amma kuma tunda ita fauziyyah bata sonsa bawani mafita ya haqura shine kawai Saidai tana tunanin irin halinda dannata zai shiga kallonsa kawai take tana nazarin yanayin dayake ciki Fauziyyah ma dakinta tawuce tafada gado tana kuka tabbas tasan tanason Brr. Amma kuma batajinsa aranta kamar yadda taso Yasir Nan tasakejin tabbas tayin rashin masoyinda takeso har abada Papa ma haka ya miqe ya nufi dakinsa ya sanya makulli ranan kwana yayi acikin wani yanayi marar dadi Washegari kasancewar saturday yasa har yamma bai fitoba Zazzabi mai zafine ya rufesa shiyasa ya wuni a kwance Gashi daddy yahana momcy zuwa ta duba lfy bai fitoba Sai da yamma tukun ya lallaba ya fito Fita yayi ya nemo magani awani pharmacy dake kusa dasu Bayan yadawo da kyar ya sha dan ruwan tea yasha maganin namma saida momcy ta matsa masa afalonta ya kwanta Daddy ya shigo momcy tace yanzu zanshiga wajenka dama Alamin ne baida lfy Cikin ko inkula yace Allah ya sauwaqa kicema fauziyyah tafada ma nabil ranan saturday suna iyah zuwa dazu munyi magana da Abba Yana fadin haka ya juya Nan papa yasake birkicewa zazzabi ciwon qirji momcy harta tsorata Amma cikin ikon Allah washegari yadan samu sauqi dan yasha magani Kullum cikin lissafa kwanaki yake har anci kwana uku Tunani badare ba rana yakeyi ta ina zaisamu mafita Yanzu hanya dayace ta rage masa baibiba shine Abba Kuma gaskiya yanajinjina taya zai kalleshi bayan abinda ya aikata abaya S ai dai kuma yaduba yaga baya da wani option gara yaje yasami Abba wataqil yadace acan tunda yasan Abba mutumin kirkine...
.
Shikadansa ya gama shawarinsa baikuma fada ma kowaba Gari na wayewa sassafe asuban fari ya dauki hanyar dambam Cikin ikon Allah qarfe tara ya shiga garin dambam Gidan Abba ya nufa saidai zuciyarsa tana ta bugawa dan baisan yadda Abba zai karbi maganar ba shinko zai sauraresa ko zaimasa irin abinda daddy yamasa Da haka harya qaraso qofar gidan yana isowa Abbah yana qoqarin fita Parkin yayi cikin dauri ya fito dan harya shiga mota Saida yazo har jikin motar sannan Abba ya ganesa dan yasha jumfer har qasa ga hula hakan yasa Abba baikawo shibane Da faraarsa ya bude motar yana qoqarin fitowa cikin sauri papa ya tsugunna yana cewa sannu Abba Aa tashi tashi zaka bata jikinka ai tashi muje cikin gida mana Tare suka shiga side din Abba dan mama bata gari sunje biki jos Harqasa ya duqa ya gaisheshi Shima da faraa ya amsa yace amma dai agarin ka kwana ko Cikin ladabi yace aa yanzu isowana Ah lalle kayi sammako yasu daddy dasu hajiya Dik lfynsu qalau ya amsa Masha Allahu yayi kyau Shiru ya danyi kafin yace dama wajenka nazo Abba Abba ya gyara zama yace toh lfy daikam inasauraronka Qasa da murya yayi yafara magana cikin nadama yace Abba tabbas nimai laifine awajenku kuma nasan nayi kuskure amma kuyafemun badan halina ba kuyi haquri... Katseshi Abba yayi da cewa ya isa haka Alamin kaifa danane kum ni bakamun komaiba sabida haka komai ya wuce kuma naji dadin yadda naganka cikin kamala ubangiji Allah ya yafemu gaba daya Cikin jin dadi yayita godia Abba yace bakomai ya wuce Sannan yasake qasa da murya yace dama Abba nazo roqon alfarmace awajenka Abba yace namefa Aminullah Yace dama Abba fauziyyah ce nakeso tadawo dakinta shikuma daddy yaqi amincewa nan ya zayyane masa yadda sukayi da daddy Abba dan Allah badan halina ba kutausayamun yanafadin haka yayi shiru dan jinsa yake kamar zaiyi kuka Abba ya nisa ya dubesa cikin kulawa kafin yafara magana Yace da darko sai ince Alhamdulillahi daka fahimci kuskurenka kuma naji dadin yadda kaxo kasameni kaitsaye tun abubuwa basu kwabe Kuma gida bai qoshiba aibazaa bawa dawo ba Amma alhji bai kyautamunba yana sane da kanason maida matarka ya hana sannan ya shigoda wata magana Kuma shi wadda yake neman nata aibaasan halinsa ba Tunda Allah yasa kazo kasanarmun halinda ake ciki to tazo gidan sauqi insha Allahu gobe zanzo bauchin muyi magana da Alhajin Wani dadine marar misaltuwa yaji yana ratsashi ta ko ina Sake risinawa yayi yana godia sosai Abba yace dakaida fauziyyah dik daya kuke awajena sabida haka ka koma abinka kasa aranka fauziyyah matarka ce insha Allahu Godia sosai haryasa kalmar dazaiyi amfani da ita tsabar murna Haka yayima Abba sallama ya kamo hanya zuciyarsa wasai Rabonsa dayaji farin ciki irinna yau harya manta ranan Gabda laasar ya iso gida wanka yayi ya fito yaci abincinsa hankali kwance Momcy dai tayi mamakin canzawarsa amma dai tayi shiru batace komaiba Yana nan zaune afalo tafito ta wucesa tinda yaga fitanta awannan lokacin yasan wannan man dinne yazo ko ajikinsa saida yagadama sannan ya tashi ya dauko car key nasa da wayoyinsa yayi waje Motarsa ya shiga saida yazo dafda su sannan ya sauqe glass ya nunasa da hannu yace hey kada kabari nadawo nasameka tareda matata kuma zaifi maka sauqi idan katafi kada kasake dawowa Duban papa yayi da kyau yace matar ka kuma ta ina tazama matarka Yace bani da tym inada wajen zuwa amma katambayeta ita zata amsa maka ai yana fadin haka ya daga glass din motarsa ya wuce abinsa Fauziyyah kuwa abu biyu su suka dameta nafarko yadda ta boyema Brr cewar papa shine mijinta na farko sannan yadda papa yake iqirarin wai ita matarsa ce Brr. Ya kalleta da kyau yace wane ne wannan awajenki Ahankali tace yaya nane Yace kada kimaidani bitacan mana inason kifadamun gaskiya miye alaqarki dashi dan najima da fahimtar akwai abinda kika boyemum game dashi Nan idanunta sukayi raurau tace wlh ba abinda nake boye maka kawai dai banason tuna abinda yafaru abayane Yace naji amma kada kifadamum shine mijin da kuka rabu Murya na rawa tace shi shine Wani baqin kishine ya taso masa cikin fada yace i see shiyasa ashe yakemum abinda ya gadama kekuma kikaqi sanar dani ashe dama tsakaninmu akwai yar boye Tace bahaka bane Yace toh ya ne inba haka ba kawai bakida abinda zaki fadamun Haka taita bashi haquri dan ta lura ransa ya baci shima haka ya tafi yana tunani kalakala Washegari Abba yazo inda suka zauna da daddy akan maganar su papa Amma fir daddy yace baisan zancenba idan har papa aure yakeso ya nemo awani waje Abba yace toh shikuma baiga dalilin da zaa hana papa fauziyyah ba Nan dai suka ringa muhawara har Abba yayi nasaran shawo kan daddy amma da sharadin sai fauziyyah ta amince Abba yace batun wannan yaron sai adakar su amma aini har raina ya baci ace taya zaka hana alamin fauziyyah Daddy yace bawai hanashi nayiba kawai abinda ya aikatawa kansane Abba yace aiyawuce Allah ya kiyaye nagaba Abba yace toh shizai tafi amma yanason magana da fauziyyah Bayan tazo Abba ya dubeta yace mama na ya aiki Lfy lau Abba ya mama sai gobe zadu dawo tacemun ko Yace eh sai gobe insha Allahu ai anyi biki kam kuma sunyi ziyra Tace hakanekan Abba yace mamana ya maganar yaronda yake zuwa wajennaki kinsanar masa ya turo dinne Shiru tayi tana tunanin dama akan jiyane zata sanar masa saikuma yatafi cikin bacin rai hakan yasa bata fada masa ba Abba yace baki amsamunba Ahankali tace aa banfada masa ba tukunna Abba yace Alhamdulillah dabaki fada masaba amma kisaurareni kiji abinda zanfada maki Dafarko nahadaki aure da dan uwanki baason rankiba wadda zan iyacewa dole namaki Toh yanzun lokaci yayi daya kamata ace kina da aure tunda dik abinda ake nema na rayuwar duniya kinsamu daidai gwargwado Toh wannan karon bazance ga miji na zaba mikiba amma amatsayina na mahaifinki zanbaki shawara idan har ta miki Batun maganar Alamin ason raina shine ki amince ki koma dakinki Cikim sauri ta dago kanta tana kallon Abba Abba yace bafa nace lallai bane aa shawarace kiduba kiga yanda iyayensa suka daukeki tamkar su suka haifeki Sannan dik yadda suke tayaki kin Alamin kisani bayadda suka iyane tunda kema kin nuna bakyaso amma suna son dansu kuma sunason farin cikinsa Kuma nima har zuciyata inasonki da alamin sabida haka kije kiyi tunani da kyau akan maganata Kuma tunda mutum ya maka laifi ya kuna nemi gafara aisaika yafemasa Fauziyyah dai nan take tafara hawaye Abba yace aa nifa banace tilas bane inhar kinfison wancan din shikenan amma ni shawara nake baki kuma kije kiyi tunani mai zurfi Tsabar kuka gagara magana tayi har Abba ya miqe yace zaitafi shikam Dakyar ta iya cemasa Allah ya kiyaye hanya Ranan kasa runtsawa tayi lalle maganar Abba gaskiyane kodan su daddy yakamata ta amince da ya Alamin saidai kuma bata sonsa Wata zuciyar tace shima Brr. Aiba wani sonsa kikeba Tunani kawai take taya zata koma zaman aure da ya Alamin tayi kuka har idanunta ya kumbura Kwana biyu da zuwan Abba abubuwa sun dameta gashi Brr koya kirata awaya bata dauka dan batasan mezata cemasa ba Shikuma yadauka bata huce bane tun abinda ya faru Kwanan Abba hudu da zuwa tayanke shawaran amincewa da Alamin amma badan tana sonsa ba saidan farin cikin Abba dan tafahimci yanasonta da Alamin ya boyene sabida kawaici Haka su daddy ma tasan kawaici kawai suke mata Ranan tayi kukan rabuwa da Brr hartaji ba dadi Waya ta kira Abba ta sanar masa ta amince ta zabi ya Alamin Abba ya ringa samata albarka da mata adduoi sannan yace toh tasanar ma daddynsu shiba ruwansa kada daddy yace shiya tursasata Suna zaune afalo da daddare tasamu momcy tace tafasa auren Brr. Ita ya alamin zata aura Momcy tace aa fauziyyah kada kitauyema kanki haqqifa Tace aa ta amince har zuciyarta Tashi momcy tayi taje tasamu daddy da maganar Yace ta kira masa fauziyyah tana fita papa ya shigo bada jimawba suka dawo tare Bayan ta gaida daddy daddy yace yanzu mom dinku tazomun da wata magana inasonjinta daga bakin Qasa tayi da kanta sannan tace haa daddy me tayyarki shaadi ya Alamin(hakane daddy na amince da auren ya Alamin) Wani lamarine mai sanyi papa yaji yana shigarsa tindaga qafarsa kamar anjiqashi da ruwan qanqara Idanu kawai ya zubawa fauziyyah yanajin wani sabon sonta har cikin ransa....
.
Wani farin cikine ya ziyarci daddy jin abinda fauziyyah tafada da bakinta Murmushi yayi mai cike da annushuwa yace zonan yar gidan daddy matso kusa dani Babu musu ta tashi tamatso kusa da qafafunsa ta zauna ta sunkuyar da kanta Cikin murya mai taushi daddy yace daugther na kifadamun gaskiya dakanki kika amince zaki auri Alamin ko kuma Abbane ya tursasaki Girgiza kanta tayi cikin natsuwa tace aa bashibane ba baima da masaniya akan hakan Alhamdulillah Allahu ya hada kanku ya kuma kauda fitina ALLAH ya maki albarka ya baki yara masu biyayya kamar yadda kika mana Momcy tace amin ya Allah dan itama wani farin ciki takeji marar misaltuwa tana kuma jin son fauziyyah har ranta Daddy yace tashi kije abinki Allah ya maki albarka Asanyaye tace amin sannan ta miqe ta fice dakinta tana shiga tafada kan gado ta bude sabon shafin kuka Daddy kuwa tana fita ya maida hankalinsa kan papa wadda shikuma yabada full attention nasa akan hanyar waje inda ta fice ya bita da kallo ya kuma gagara dauke idanunsa Daddy yace toh nadawo kanka yafada yana kallonsa Jin muryar daddy yasa ya juyo yana kallon daddy Kasaurareni da kyau kaji abinda zanfada maka Nafarko kagodewa Allah da mahaifin fauziyyah mutumin kirkine sannan itakuma yarinyace mai biyayya Toh kagama bin kafa har kasamu burinka ya cika Amma kasani bazan lamunci kwatankwacin abinda ya faru abaya ba Matuqar kanason zama inuwa daya da ita saika sake halayenka tass Cikin ladabi papa yace insha Allahu zankiyaye daddy Daddy yace Allah yasa sannan tunda burinka ya cika saika tattara kakoma gidanka gobe dan bazaka zauna karinga takura mata ba Ko ajikinsa yace shikenan daddy Allah ya kaimu Daga haka ya musu saida safe ya fice zuciyarsa fari qal qal Yana fitowa ya nufi dakin fauziyyah cikin saa kuwa qofar abude take Falon shiru sai qaran AC gami da wani sansanyan qamshi wucewa yayi har cikin bedroom nata Da sallama ya shiga kwance ya hangota tayi rubda ciki akan bed kuma bata amsashiba Wani kasalane yaji ya sauqo masa ta dalilin abubuwa uku Nafarko sanyi da qamshin daya doki hancinsa na biyu tsaftan dake tattare da dakin kamar kada ya fita haka yakeji Na uku yanayin kwanciyar da tayi saiyaji kamar ya qarsa ya kwanta ajikinta dan saiyaji dik hankalinsa ya tashi Gashi dama wata yaloluwar doguwar rigace ajikinta dazataje wajen daddyne ta daura hijab akai tana shigowa kuwa ta cire Dik tabi jikinta ta manne sannan ta bayyana illahirin suran jikinta Wani yawu ya hadiya yana godema Allah daya sanya fauziyyah zata zama mallakinsa Itakuma tanajin motsin bude qofa da sautin muryarsa taji wani baqin ciki yasake kamata Banza tayi dashi kamar batasan da shigowarsa ba Ahankali ya tako har bakin gadon leqa fuskanta yayi nan yagane idanunta biyu kuma kuka mq takeyi dan ganan hawaye shabeshabe akan fiskanta Nan take yaji ya damu gashi baisan dalilin kukan nata ba Cikin murya mai tattare da natsuwa da kulawa ya kira sunanta My Fauzy Wani dam taji zuciyarta ta buga sakamakon tuno mata da yasir da yayi dan shine kadai ke kiranta da wannan Anatse yasake kiranta My Fauzy sunotoo(kinajina) Nanma banza tayi dashi kamar da dutse yake magana Zama yayi agefenta ya riqo hannunta dake gefensa ya sake qasa da murya cikin sanyi yace My Fauzy pls jababdo(ki amsamun) Bata kulasaba sai yunqurin kwatan hannunta daya riqe takeyi Saqe riqe hannunta yayi gagam ganin baya da niyyar sakinta saita rabu dashi kawai Tambayarkifa nake why ar u crying n baki amsaniba yafada atausashe Ganin batada niyyar yimasa magana yasa ya cigaba da fadin Koma meke daminki pls kiyi haquri kibar kuka banson kanki yayi ciwo ko idanunki yayi ja Nazo namaki godia ne akan amincewa da kiyayi zaki aureni Inkuma qara baki haquri akan abinda namaki abaya My fauzy inaroqonki kibani dama na nuna maki irin sonda nake maki Nayi nadamar abinda na aikatamaki abaya U don't know how much i regret everything that i have done to u I luv u my fauzy i luv u with all my hrt Magana yake yana murza dan yatsun hannunta masu laushi da taushi kamar na jarirai Maimakon taji sanyi aranta sai tasakejin wani zafi aranta nan tasake fashewa da wani sabon kuka mai sauti ahankali Nam yayita lallami da maganganu masu dadi amma abanza harya fahimci maganarsane batasonji akan dole ya miqe ya fita yanajin kukanta har cikin zuciyarsa Adaren ya kira TJ ya shafa masa halin da ake ciki TJ yayi murna sosai ya kuma sake bashi shawara mai kyau akan kada gaba ya kuma gangancin kwatanta abinda ya faru abaya ******* Washegari daddy ya tafi dambam nan suka zartar da maganar biki sai nan da watanni biyar masu zuwa Kafinnan angama ginin sabon gidan da zaa kai fauziyyah Yan uwa kowa yayi murna da samun labarin komawar fauziyyah musamman saida aunty mabarukha tazo bh takuma dauki nauyin gyaran amarya idan lokaci yayi Haka maman fauziyyah da farko taqi yadda saida Abba yamata nasiha sannan ta amince takuma sanya Albarka Da aka sanarda papa lokacin auren sai cewa yayi shifa lokacin yamasa tsayi gaskiya Momcy harta qulu tace tosaika rage tunda ka isa da hakan Cikin sati daya magana tagama kankama har daddy yabada contract na ginin gidan sabon gidan papa amma wanna karon a kusa dasu nan *Gida Dubu* Wani filin daddy dake kusa da gidan Aunty naja dambam sukayi shawaran gina masa Momcy tace gara kusa da auntynsa tunda koba komai yafi shiri da ita kuma zatana leqasu akaiakai taga inda yayi ba daidaiba tasashi ahanya Dan abinda ya faru abayama harda rashin wani babba akusa wanda yake leqasu Daddy ya amince da shawarin momcy Daddy ganin har sati guda papa baida niyar komawa gidansa yasa ya kirasa yace ayau dinnan yayi parking inba so yake ya saba masa ba Babu musu ya hada kayansa ya loda a mota sai abinda baa rasaba ya bari saidaga baya zaizo ya dauka nan ya nufi gidansa dake sokoto road wadda rabonsa da gidan tun rabuwarsa da j uhaina.... *Wai ina labarin juhaina kam[truncated by WhatsApp] 🌾🌾🌾🌾🌾🌾 🌾🌾🌾🌾 🌾🌾🌾 Budurwar Qauye🤷🏼♀🤷🏼♀🤷🏼♀ Written by Faty Mmn Faty September, 2017 *This page goes to Aunty Faty G Dambam, Nagode da qaunar da kike nunama littafina, Insha Allah 2019 Bauchi sai Proffessor, Mmn Faty Luvs u 😍😘* 5⃣6⃣ Hankali kwance yake driving har ya qaraso Amma yana isowa gate sai yaji ransa ya baci cos nan take kwakwalwarsa tafara recalling masa abinsa yafaru lokacin rayuwar da yayi da ex wife nasa juhaina Horn yafara mai gadi ya bude masa gate dan yasan da zuwan ogan nasa cos ya kirasa awaya kan cewar agyara gidan before ya yazo Qarasa shiga yayi har parking space yayi parking motarsa Qarema gidan kallo yake saiyaga ya canza masa kodan ya jima rabonsa da gidanne oho Koda kudin buqatar maigadi da sauransu saidai suyi waya yazo ya karba Wani iska mai zafi ya furzar kafin ya bude qofar motan yana tattara wayoyinsa Yana fitowa daidai da isowar maigadi kenan Sannu da zuwa yallabai ya fada yana risinawa Cikin kulawa yace yawwa ya gidan dai hope babu wata damuwa Aa babu konai yallabai ankuma gyara ko ina kamar yadda ka umarta sai dai daki daya wadda yake akullene da baa gyara ba sabida acikin keys da suke wajena babu nasa aciki Ok babu damuwa i think key din yana wajena barin qarasa ciki zan fito saika shigar mun da kayana idan kuma Abdu ya iso shikenan Toh yallabai afito lfy Wucewa yayi ciki inda yabar maigadi da mamakin canzawar ogan nasu Tun bayauba ya lura da sauyin idan yaje wajensa but nayau dabanne lura da yadda ya bada time nasa sukayi magana ta fahimta Falo ya bude ko ina tsaf sai qamshin room freshner da sanyin AC Ba komai acikin falon sai carpet dake tsakiyar falon Wucewa yayi falonsa nanma komai agyare yadda yake ba kuma abinda aka taba Kallon dakin juhaina yayi kamar ya wuce amma sai ya qarasa ya bude nanma bakomai ciki da sauri ya jawo qofar ya rife hadida rintse idanu sabida tuno da abinda ya faru da yayi Cikin sanyin jiki ya wuce dakinsa key yasa ya bude qofar Qurakam baa magana ko ina yayi qura kallon dakin yake sosai fridge ya bude nanma da sauri ya kulle ganin kwalaben wine iri da ban daban Ga wasu kwalabe a zube aqasa ga kuma kwalayen sigari da dai sauran kayan shaye shayensa Lokaci guda yaji kyaman dakin ya kamasa fitowa yayi ya shiga kiran layin Abdu bada jimawaba ya daga hello oga sir am sorry pls na kusa isowa Ok am ka tsaya ahanya kasamomin kwalaye manya mana ammafa empty Ok badamuwa ya fada Bada jimawaba ya qaraso da manyan kwalaye kamar yadda aka sashi Karba yayi ya shiga loda tarkacen aciki saida ya kwashe su tas sannan ya manne su tass ya kira Abdu yace yayi waje dasu ya loda su a boot Falo ya dawo ya zauna ya jira Abdu ya gyara masa dakin nan ko ina ya tsaftatu kamar bashiba Kayansa suka shigo masa dasu daganan ya wuce toilet ya watsa ruwa hadi da alwala Agurguje ya shirya ya nufi masallaci Sai da yayi ishai sannan ya dawo Yabawa Abdu kudi ya samo masu abinci Bayan yayi dinner ya jawo system nasa ya kunna ya duba wasu abubuwa sai dai ya gagara samun natsuwa Jingina yayi da jikin kujera ya lumshe idanunsa ya tuno fiskar luv of his lyf Jiyake inama yana da no wayarta daya kira yaji muryarta ko zaisami sukuni Gashi ya na zaune shiru shikadansa dik kadaici ya damesa Wayarsa ya jawo ya kira TJ Amma baidaukaba harta katse sake kira yayi akaro na biyu sannan ya dauka Hello man how far Papa yace cool ya khairy n mubeen All ar fine ya amarya Wani murmushi yayi mai natsuwa kafin yace tana gida amma dai lfyrta lau Kaikuma kana ina kenan at this tym Ina sokoto road daxu nayi parking wlh daddy ya matsamun wai sai dai na qaura Hhh Tj ya sheqe da dariya yace aikam daddy ya birgeni dan wlh nasan takurin fauziyyah zakanayi Tsaki ya danyi yace aikaiba nasan iya abinda zakace kenan tokoma mene ne dai nikasamun no wayarta now now TJ yace toh nikuma a ina zansamomaka kuma yanzu adaren nan Tsuke fuska yayi kamar yana kallonsa yace banason iskancifa kawai inajira tinda komai saika maida shi wasa Toh naji naji barin karba awajen madam saina turo maka shikenan Eh shikenan thanks Nyt saika ganito Ok nyt yafada yana sauqe wayar amma bai ajiyeba jira kawai yake yaga message ya shigo Aiko bada jimawaba saiga message cikin sauri ya bude ya dauko dayar wayarsa ya shigarda no din Dialling no yafara saidai yaji user busy Sake kira yayi nanma yaji user busy Nanfa ransa ya fara baci todawa take waya awannan daren haka Itakuwa fauziyyah Brr nabil ne ya kirata awaya harda kukansa akan maiyasa ta yaudaresa tasan ba aurensa datayiba gidan mijinta data koma Daddy ya kirasa ya masa bayani akan yayi haquri shinefa ya shiga cikin damuwa zuciyarsa take ganin yaudaransa kawai fauziyyah take shiyasa bata daukar wayarsa Dik iya bayani da rantsuwa data masa yaqi ya yarda sabida kishi ya rife masa idanu kawai gani yake dagangan tamasa haka Shinefa suka dauki time suna magana har ya kira yaji busy Ya kira yafi sau ashirin cikin saa yaji wayar ta shiga Harta kusa katsewa sannan yaji ta dauka cikin sanyin murya tace pls ka amince dani wlh wannan auren sabida iyayena zanyi badan so ko wani abuba nifa kaine araina kuma kaina keso bayadda na iyane kawai na amince da auren ya Alamin Itakuma tadauka Brr ne ya sake kiranta dake da wata no ya kirata shiyasa dataga no ne yanzuma saikawai tadauka shine tafara magana Wani daci yaji maqoqoronsa ya masa jin yadda take jadda da bata sonsa kuma mawani take fadama haka Lallai akwai aiki agabansa dole ya danne zuciyarsa haryasamu gurbi acikin zuciyarta Jin yayi shiru yasa tace pls talk to me mana ka amince da maganata muyi rabuwar mutunci bakadaukeni mayaudariya ba Cikin sanyin murya papa yace My Fauzy Alamin ne Abazata taji maganar hakan yasa tayi shiru ta gagara magana Sharewa yayi yace My Fauzy kina jina Nanma shiru ba responde Yace nasan kinajina meyasa bakiyi bacciba har yanzun while dasafe zaki fita aiki Dama na kirane naji muryanki mai dadi mai sanyani natsuwa kuma gashi kinqi kimin magana amma da kika picking call nawa i appreciate it so ki kwanta kiyi bacci but do not forget kiyi addua kafin ki kwanta Allah ya tashemu lfy kiyi bacci mai dadi n swt dreamz Dik yadda yake maganar cikin wani salo mai matuqar dadin sauraro Hakan yasa tabar dai wayar akunnenta tanajinsa bata kuma kasheba Yana fadin haka ya zame wayar akunnensa ya kashe yana tunanin ta yadda zai samo hanyar dazai shawo kan fauziyyah dan tabbas yasan akwai ga garumin aiki agabansa Itakuma jin ya katse wayar ta sauqe daga kunnenta hadi da jan tsakin dabatasan miye dalilin yinsa ba Message ta rubutawa Brr ta tura masa sannan ta blocking layukansa kafin ta kwanta amma batayi bacciba tana tunanin abubuwa da dama ******** *Waikam ina juhaina ta bace ne???* Tunda tasamu ya amince mata akan tashiga tacanza kaya amma kada ya sameta agidansa Suna fita itama taja jikinta cikin wahala taje tahada abubuwanta masu amfani ta canza kaya kafin ta fito Motatta ta shiga ta fito tana waigen inda zataga munnir sai tahangoshi kwance aqasa baya ko motsi agefen wani lungu bakowa kasancewar yanayi. Layinnasu da bayawan mutane Fitowa tayi ta koma cikin gidan ta shiga dakinsa ta dauko jakar kayansa ta dawo da kyar tasamu tasaka masa kaya sannan ta koma ta ringa roqon mai gadi har ya amince yazo yasaka matashi a mota ta nufi asibiti dashi Wani private hospital ta kaishi amma sukaki karbansa saida ta zube masu kudi masu yawa sannan suka amince suka dubashi Nan itama ta kwana sai washegari ya farfado Tana samun ya farfado tace dashi toh yanzu alaqansu ya qare tinda yamata sanadin aure kuma ta kawo shi asibitine dan bayida mai taimakonsa sabida haka ita yau zata tafi gida kada ya kuma tunanin yasanta arayuwa idan yaji sauqi yaje yadauki motarsa acan sannan idan yana buqata ya kwashe kayan dakinta yasayar ya san inda dare yamasa kada ya kuma nemanta Tana fadin haka ta fice ta barshi yana kukan danasani ga jinya ga karaya ga babu haqora guda biyu Itakuwa tasha taje tasamu fasinjan daya iya mota yajasu zuwa kaduna Gida ta nufa tana shiga ta ringa kurma ihu dik su mom dinta suka rude gashi duk jikinta shatin duka ya faffashe Dakyar tafada masu ai papane ya saketa yamata dan banzan duka Mom dinta tace tabbas saitayi qaransa dan bai isa ya dakar mata ya abanzaba Dad ne yace aa anemi iyayensa dai aji kanmagana Nan juhaina tace ai agaban iyayensa yamata haka da saninsu Mom tace kajiko saina daureshi dan ubansa ta inda take shiga batanan take fitaba Dad yace indai hakane baiga amfanin wata sharia ba kawai abarsu da Allah su suka sani Da kyar ya shawo kan mom ta amince inda juhaina taji dadin hakan dan kada asirinta ya tonu..... ✍🏻Faty Mmn Faty 🌾🌾🌾🌾🌾🌾 🌾🌾🌾🌾 🌾🌾🌾 Budurwar Qauye🤷🏼♀🤷🏼♀🤷🏼♀ Written by Faty Mmn Faty September, 2017 5⃣7⃣ The following morning after ya tashi yayi subh prayer baikoma bacciba Wajen seven ya shiga bathroom ya taking bath Shirinsa yayi tsaf cikin wata sky blue half jumfer wadda tasha dinkin zirii Kansa ba hula sai suman nan tayi lufluf which means tasha gyara sosai Agogon gucci ya daura as usual then yasaka baqaqen half shoes nasa na zallar fata Designers perfoms ya feshe jikinsa nan da nan ya karade ko ina da qamshi Breif case nasa ya dauka da woyoyinsa ya fito hannunsa riqe da car key nasa Babu wadda zai kallesa bai sake ba koda kuwa tare suke kwana daki daya dan papa yayi no lie Yana fitowa ya tarar anwanke masa mota sai sheqi take Maaikatansa sukazo one by one suka gaidasa sannan ya bama Abdu kudin Abincinsu yace idan yaqare yayi magana shi ya wuce office idan ya dawo zaije gida ya taho masa da motocinsa Ya amsa cikin ladabi sannan ya masa adawo lfy Motarsa ya shiga ya kunna Ac hadi da wani daddan music Ahankali yake tafiya harya fice direct gidan daddy ya nufa cos he wanna see his darkan(heart beat) Lokacin daya shiga bakowa afalo sai talatu mai aiki Bayan sun gaisa yace ina masu gidan Tace yanzu hajiya ta koma amma bada jimawa ba zasu fito karyawa tunda 8 tawuce Zama yayi abinsa ya danna wayarsa Momcy ce ta fito daga side din daddy ganin papa zaune yasa tace papa lfy kuwa kaxo early morning Dago kansa yayi yana murmushi yace morning momcy Morning dear baka ansamun tambayar danayi maka ba Dan shagwabe fiska yayi yace haba momcy mutum da gidansu danyazo sai antambayesa kawai nayimissing naku a lot that's why naxo early morning naganku kafin na tafi office Dariyama abin ya bata cos ta fahimci abinda yake nufi Tabe baki tayi tace good saikataso kayi break toh Yana tashi daddy na fitowa shima cikin mamaki yace Alamin qalau kuwa naganka sassafe Lfy lau daddy nazoyin breakfast ne fa Yace yayi kyau to muje Saida ya gaidashi kafin ya haura dinning ya zauna a permanent seat nasa Fauziyyah ce ta fito cikin shirinta yau takusa makara dan jiya batasamu bacci da wuri ba Ganin papa yasa tadan hade rai shikuma sai wani mayetaccen kallo yakebinta dashi Saida ta gaida daddy da momcy tukun tadanyi kasa da murya kamar dole tace morning ya Alamin hakanma dan su momcy na zaune ne yasa ta gaishesa Da faraasa yace morning dear kesi ho tum(yaya kike) Me tikke ta amsa masa(lfyna lau) That's great ya fada sannan ya cigaba da cin abincinsa Itama zama tayi tayi break nata kafin ta miqe ta masu daddy sallama wadda dama shi ya koma falo ya zauna Tsulum papa ya miqe yace shima ya tafi idan ya biyo to idan kuma bai biyoba sai gobe Suna fita ya nufi motar fauziyyah tana budewa ya shige gefenta ya zauna abinsa Juyowa tayi tana kallonsa akufule tace yeh he kya karehe tum(meye haka kake aikatawa) Dubanta yayi yace kyah(kamar yaya) Tace taya zaka shigomun mota haka baicin kanaga fita zanyi Oh sorry dear nima ai fitan zanyi shine nakeso kuragemun hanya Tace pls kafitamun amotana Yace eyyerh pls kiragemun hanya mana tinda office zani Tace no i cant pls kafita if not gashi ta miqo masa key namotar tace nisai infita Qarema hannunta kallo yake wadda yasha lallen rani Yace aakam keda motarki daman tawance tasami problem amma tinda kinqi shikena Duban jerin motocin sa takeyi amma yace baya da motar da zaifita tabe baki tayi tace shikenan kafin ta tada motar suka tafi Ahanya ba yadda baiba kan tayi maganar amma sam taqi Haka ya haqura ya kyaleta......
.
Har suka iso hospital kallonta kawai yake yana murmushi cos ta matuqar birgesa D way take driving anatse shiyasake birgesa gashi ta tsuke dan qaramun cute bakinta Saida tayi parking tana daukan jakarta sannan ya bude ya fita Zagayowa yayi ta side nata ya sunkuyo sosai lokacin itama ta bude zata fita Wani killer smile ya mata cikin wani soft voice yace mata shukhriya(nagode) Yana fadin hka ya wuce abinsa baijira amsarta ba dan yasan abune mai wahala ta kulasa Kallo ta bisa dashi kafin ta dauke idanunta ahankali Azuciyarta tace jibesa kamar mutumin kirki baicin dik wata kalar iskanci babu wadda bai iyaba Tsaki tayi kafin ta fice itama dan kada ta makara Shikuna yau hankali kwance ya shiga office nasa koba komai yau ya jima kusa da pyarinsa(mosoyiyarsa) Saida ya kusa tashi kafin ya kira Abdu yazo office ya samesa ya bashi key din motarsa akan yaje ya kawo masa
******
Kwanci tashi babu wuya awajen Allah kwanaki sun shude hakama satittika tareda watanni Yanzu biki saura sati uku kacal duk wasu shirye shirye babu wadda baa gamaba Kama daga kan gidan da zasu zauna su lefe komai anshirya masa sai sauran abinda baa raasa ba Papa kuwa yafi kowa doki da murnan karatowan bikin sai dai haryanzun ya gagara gane kan amarya Daidai da maganar fatan baki bata hadsu sai yazama dole Bayadda baibi da itaba taxo suje gidanta tagani amma fir taqi yadda Haka ya haqura saidai shirye shiryensa bai fasa ba dan biki zaayi na kece raini Biki saura sati dasu wuce dambam acan zaayi hidimar biki sai bayan biki dasu dawo bh Aunty mabarukha kuwa yau take hanya yaranta kuma sai saura two days biki zasuzo da babansu sabida exams dasuke a school Acan dambam ma baa barsu abaya ba dan shiri sosai su Abba suke suma Momcy kuwa tunba yauba tafara hidimar gyara yarta ta kuma surkarta Ita dai fauziyyah dik abinda ake bai dametaba hasalima ma da zaa qara lokacin tanaso Kullum tunaninta ko wanne irin zama dasuyi da ya Alamin Dik da sosai tana ganin canji atare dashi amma dik da haka zuciyarta taqi aminta da shi sabida sanin halinsa boyayye datayi Ita tasan kawai jikinta yakeso yadda kullum bai gajiya da fada mata da turo mata messages na soyayyar qarya Tabarwa Allah zabin alkhairi kawai amma batajin zata yadda tasakeyin zaman qunci agidansa Da daddare suna zaune afalo tare da aunty mabarukha suna ta hira harda aunty niima itama tazo masu sai anjima mijinta zaizo sutafi Aunty mabarukha tace mata sis dubamun abinda na daura awuta mana kada ruwan ya qone sosai idan yayi kauri kawai kisauqeshi ya huce Tace toh sannan ta miqe Tana shiga kitchen papa nashigowa hangota da yayi saiko yayi saurin wucewa yabi bayanta Tana sauqe tukunyar yana shigowa Juyowa tayi taga wane ne ganin shine yasa ta dauke kanta ta kunna famfo tana wanke hannunta Qarasowa yayi ya tsaya abayanta matsota yayi sosai hartana jin sauqar numfashinsa akan dokin wuyanta Shiru tayi tanajin wani iri hakanan ajikinta Murya qasaqasa yace meri darkan(my hrt beat) Menayi ne kike guduna uumm Shiru tayi batace komaiba Sake maimaita mata yayi cikin wata iriyar murya mai kashe jiki yace yakamata ya zuwa yanzun kimfahimci kyakykyawar manufata gamedake Wlh bantaba tunanin na aureki dan na walaqantaki ko wata manufa ta daban ba Inason kisan cewar dik wani hali nawa da kika sani ada yanzun munyi hannun riga dashi Idanma wannan kike tunani toh ki cireshi daga ranki Jin tayi shiru ganan ruwa na zuba takasa qarisa wanke hannunta yasa ya qara samun courage dan yaga kamar magangannunsa sun shigeta kuma sunyi tasiri akanta Sake matsota yayi har kirjinsa na gugan bayanta ya saka hannunsa biyu ya riqo nata yafara wanke mata hannayen dashi baiga wani abu ajikiba da harta tsaya wankewa Santsin hannunta acikin ruwan shiya masa dadi har ya rajaa yana murzawa ahankali Bakinsa ya kawo daidai kunnenta yana cewa idan kina tunanin wani abu nakeso ajikinki kinyi kuskure Nafara sonkine tun kina yanda kike abaya tunkuma banganki ayanzuba Sonki acikin jinina yake pls My Fauzy kibani dama na nuna maki irin kalan sonda nake maki na kuma wanke laifina na baya Yana fadin haka ya kashe ruwan yace i luv u my pretty sannan ya juya ya fice Nan ya barta kamar andasata dan gabadaya maganganunsa kemata yawo akwanyarta Saidai dik da haka bataji wani canjin akan tsanar da tamasa ba
*****
Washegari da safe ya kira aunty mabarukha akan ta lallama masa fauziyyah da yamma zaizo su fita zata rakashi wani waje Saida aunty ta wanasa kafin ta amince Haka ta fadama fauziyyah ta shirya 4pm papa zaizo sufita Batayima ta musu ba dan tana matuqar ganin girmnta Haka badan ranta yasoba ta shirya cikin wata doguwar rigar material rainbow colour wacce ta matuqar qarbanta Earing dogi tasaka blue colour sai bangles nata suma passion design ne combination colour Saita yane kanta da blue veil madaidaici Waya ya kirata yace pls ta fito yana mota yana jiranta Takalmanta masu tsini tasaka suma blue colour saita riqe yar qaramar purse nata itama blue colour Masha Allah nan tafito kamar asaceta agudu dan kyau Tunda ta fito ya zuba mata idanu yana kallon takunta cikin natsuwa dan tamatuqar birgesa kuma kwalliyar tayimasa 100% Saida takusa qarasowa ya fito ya bude mata motar Tana isowa yace bismillah My preety Shiga tayi ta zauna sannan ya rufe ya zagayo Ko kallonsa bataiba baran ta gaidashi Inayini rankishi dade yafada yana kallonta Shiru tayi kamar bada ita yakeba Marairaice murya yayi yace haba My Fauzy ko gaisuwan nawama bazaki amsaba Sai anan ta juyo ta kallesa tace pls idan abinda yasa katakureni nafito kenan toh sai anjima tafada tana kokarin bude motar Da sauri yace aa am sorry idan ranki ya baci daga haka baikuma cewa komaiba Ahankali yake tafiya dan yanajin dadin yanayin yau sosai Saida ya iso wani babban super market yayi parking awajen Kallonta yayi yace mujeko n pls kidauki abinda kikeso kinji Rai ahade tace bana buqatar komai I know baki buqatar komai amma irin kinmin rakiyan nan aibai kamata kikoma empty hand ba Tace toh bani buqata Muje to yafada atare suka shiga inda yayima kansa shopping abinda ya kawosa sanna yacigaba jibga kayan ciyeciye da wasu abubuwan amfani na qamshi wannan na fauziyyah ne Harta gaji tace nafa gaji Yace ainagama muje sunzo daidai wajen teddy sai wata baby girl wadda shekatunta bazasu fice uku ba tazo tasha gabansu tanata dariya tana cewa daddy ganan teddyna Daga bayansu sukaji ana cewa fauziyya stop there stop there Jin an ambaci sunan fauziyyah yasa dik suka juya Saidai wa fauziyyah zatagani mutuminda ko ta shekara dari rabonta dashi zata ganeshi dikda kuwa canzawar dataga yayi Shima kallonta ya tsayayi yana tabbatarma kansa itace bawai dikda rabonsa da ita yayi shekaru amma kamanninta bazai bace masa cos her immage is in his heart Qarasowa sukayi shida matar dake gefensa wata black beauty amma ita saita qarasa ta dauki babyn tana cewa oh My Fauzy meyasa bakijin magana kinason kinasani gudune eh Kallon babyn papa ya kumayi jin ankirata da sunan dayafi qauna Murmushi Fauziyyah tayi masa tace uncle yasir dama zansake ganinka arayuwa Shima murmushi yayi yace Fatima Papa ne ya juyo yana masa murmushi tare da miqa masa hannu jin yadda fauziyyah ta kira sunan saiya tuno masa da me wannan sunan Gaisawa sukayi kamar sunsan juna Bayan sungaisa da fauziyyah ya nuna mata matar dake riqe da baby yace this is my wife Jalila n my dauther Fauziyyah Kallonsa tayi tace wannan babynkane kuma sunanta fauziyyah Murmushi yayi sannan yace yeah Gaisawa tayi da matarsa tana kuma mamakin yadda yasir baimanta da itaba tasan kobai fada mataba takwara ya mata Ganin tadanyi shiru yasa yace wannan ne maigidannaki yafada yana nuna papa Gyada masa kanta tayi tace eh nan suka sake gaisawa da papa sannan ya dauki little fauzy Yace mata babyna kinason teddyne Eh uncle tafada tana maqalesa yace ok zabi wadda kikeso insaya maki ko Da fara arta ta dauki manya guda biyu yace sukadai kikeso Tace eh uncle Yana riqe da ita ya qarisa wajen biyan kudi katinsa ya bayar nan aka hadamusu kayayyakin Yariqowa little fauzy nata ya dawo da ita wajen daddynta sannan sukayi sallama suka tafi Haushin yasir ne ya kama papa ganin yadda mood din fauziyyah ya canza daga ganin yasir saikuma aside guda yanajin son babynsu inama su barmasa ita......
.
Fitowa sukayi daya daga cikin masu daukan kaya na biye dasu har mota Saida aka loda kayan a mota sannan ya zagayo side din datake tsaye ta jingina da jikin motar da alamun hankalinta yayi nisa awajen tunani Bude mata qofar yayi kafin yace shall we Saida yasake maimaitawa kafin ahankali ta matso ta shiga ya rufe Zagayowa yayi ya zauna sannan yama motar key yafara tafiya yana tunanin yanayin data shiga one time Zuciyarsa ce ta aminta kan ya tambayeta mene ne damuwarta Juyowa kadan yayi ya kalleta kafin ya maida hankalinsa kan titi Cikin sanyin murya yace My Fauzy kya hua(meke faruwa)naga mood naki ya canza Shiru tayi kamar bada ita yake ba Sake maimaita mata tambayar yayi yana cewa lokacin damuka fito ba haka yanayinki yake ba but lokaci guda kincanza kyiu(meyasa) Pls My Fauzy ki amsamun mana wlh bani qaunar ganinki cikin damuwa Ahankali ta kallesa kadan tace ya Alamin dan Allah kadaina kirana da wannan sunan na roqeqa ta karisa maganar kamar zatayi kuka hawaye na ciko idanuwanta Meye laifi danna kiraki da My Fauzy keba tawa bace uum ko kina manta cewar remain few days kizama mallakina so banga wani damuwaba danna kiraki da My Fa... Baikaiga qarisawa ba yaji tafashe da kuka sosai Subhanallahi haba dear danna fada maki wannan sunan shine bakiso harda kuka to kiyi haquri i promissed u barin sakeba Ganin yanata surutansa ko kulasa bataiba saima cigaba da kukanta da tayi yasa ahankali ya gangara gefen titi yayi parking Lallaminta yafara hadi da bata haquri kancewar bazai kuma mata abinda batasoba kuma tayafe masa Amma fir taqi sauraronsa saima kuka datake sosai Shikuma jin kukan yake har cikin zuciyarsa ganin baya da option kawai saiya dan matso ya jawota jikinsa ya rungume Cikin muryar lallashi yafara magana yana cewa swt hrt am begging u kiyi haquri kibar kukan nan namaki alqawarin koda wasa barin kuma fada makiba tunda bakiso Banason jin kukanki yana tabamun zuciya har cikin raina nakeji Cikin kuka tafara qoqarin janye jikinta tana cewa kadaina bani haquri kabarni nayi kuka shikadaine zai ragemum radadin abinda nakeji Sake riqeta yayi sosai ajikinsa yana patting bayanta smootly Yace nasan abinda yasaki kuka n banson tuna maki kuma saidai inason roqonki kibani damar na gwada maki kalar sonda nake maki wlh nayi alqawarin zan kula dake har qarshen rayuwata bazan taba cutardake ba Kuma da kike kuka sabida ganin yasir bagashiba shima harda matarsa da yarsa So pls kimanta da baya da abinda yafaru kidauka komai Rubutaccen Alamarine bazai kuma canzuba Haka yaita lallaminta da kalamai masu dadi harya samu ta tsagaita kukan sai ajiyar zuciya datakeyi Sunfi 30mins kafin yasamu kanta ahankali ya janye jikinsa daga nata ya tashi motar Suna isowa gida tafice cikin saa tasamu bakowa acikin falo sabida haka ta wuce dakinta kawai ta kwanta Shikuma fitowa yayi ya dauki iyaka kayanta ya wuce ciki dasu Dakinta ya shiga nan yasameta kwance Baice da ita komaiba ya ya ajiye mata ya fice ***** Afannin yasirma ganin fauziyyah ya tayar masa da abinda ya jima yana damunsa amma haka ya danne zuciyarsa ya haqura gudun kada matarsa ta fahimta Kuma baya samum matsala da ita so baison tawajensa asamu rashin jituwa tunda dama tasan da labarin fauziyyah yaukuma taganta ido da ido Kimanin shekaru hudu kenan da auren yasir Bayan sundawo daga dambam akan baisamu auren fauziyyah ba lokacin ya shiga matsanancin hali sosai Saida ya kwanta jinya tun abin yanabawa iyeyensa haushi yafara basu tausayi Da kyar suka samu kansa yadan warware shinefa baffansa ya bashi yarsa ya aura Baiyi musuba ya amince dan yanason ya manta fauziyyah aransa tunda yasan tamasa nisa har abada Itama bataqiba dan dama tajima tanason yasir babanta yana fada mata ta amince Bayan bikinsu da yadda take kula dashi take nuna masa qauna har ta shiga cikin ransa yafara sonta Koda ta haihuma baiboye mataba yace sunan yarsa fatima yakeso kuma ana kiranta da fauziyyah Nanma bataqiba dan burinta ta faranta masa Wannan kenan ***** Tunda aunty mabarukha tazo bata zaunaba sai hidimar gyaran amarya take musamman da wadanda ta dakko masu gyara Dinkunanta ma dik ita ta bada wadda zatayi fitan biki Kuma tundaga ranan papa baikuna saka fauziyyah a idonsaba Saidai yaqaraci surutansa awaya nanma text dan bata daukar wayarsa kam Cikin sati biyu babu abinda ya rage na shirin biki komai ya kankama sai ranan biki kawai ake jira Fauziyyah kuwa tayi natuqar kyau na birgewa dan baqaramin gyara tashaba ga wani sheqi da da santsi da fatarta tayi Washe gari suka tattara suka nufi dambam amma gidan Abba aka kaita sabida dagacan zaa dauki amarya Kuma washegari zaa fara shagalin biki Papa kuma sai aure saura 3days zai iso sabida wasu abokansu sa zasu taho tare kuma ananne zaayi hidimarda zai halatta.....
.
Washe hari aka fara hidimar biki amma na gargajiyar aladarsu Amarya tayi kyau kamar ba gobe,dikkannin wadan da suka halarcin wannan hidima sunyi san barka dayima papa murnan samun mace kam tare damasa adduar Allah yasa yadda yanayinta yake haka halayenta suke The following day ma haka akasake wani hidimar nanma haka aka watse taro lfy lau Papa nacan bauchi jiyake wane yayi tsuntsu ya taho yaga gimbiyarsa Bayadda baiyiba da Aunty Mabarukha kan ta turo masa pics din Fauziyyah na hidimar biki amma fir taqi tace mene kake sauri badai kaima daka xoba kuma gidanka zaakawo maka ita so nothing to worry about Haka ya dami aunty niima itanma sammaqal dan hada baki sukayi sunfison yaganta azahiri yaga yadda tadawo akwanakin da baiganta ba Ana gobe papa zasu iso da abokanansa akayi sakun lalle namma guri ya burge dan yan uwa anhadu both side na ango da amarya Sai wajen 10pm aka tashi daga taro Jamaar garin dambam sun shaida ana biki afada dan yadda tako ina manyan motoci ke shawagi abinka da bikin manyan mutane maaikata da yan kasuwa Ga yan uwan Abba dana Mama gari gari dik sonzo saikace shine aurenta na fari Papa kuwa yayi juyin duniya akan tadau wayarsa koda muryartane yaji kozaiji sauqin abinda yakeji azuciyarsa Amma sam taqi text kan text daya dametama saita kashe wayartama dan gaba daya bata son damuwa
*****
Tunsafe suka kamo hanya inkagansu kace daukar amarya akatafi yadda sukayi comboy na motoci Zumudin papa har bai boyuwa burinsa kawai yasaka tauraruwarsa a idanunsa 12:30pm suka shigo dambam Direct gidan daddy suka wuce inda zasu zauna da friends nasa acan tunda su daddy afada suka sauqa Bayan sunci abinci suka dan kwanta kafin lokacin tafiya KAMU Amma sam papa ya gagara kwanciya burinsa kawai 4pm tayi su wuce wajen KAMUN Ana kiran sallan laasar sunayin sallah suka fara shiri daya daga cikin abokansa guda uku da sukazo daga india yace shikam yau jumper zaisa dan yana shaawar kayan shiyasa yasaka aka dinka masa dan yayi shigar hausawa Ango ne nagani ya dau wanka cikin wani coppee brown yard mai kyau da sheqi Kyansa shiya bayyana tsadarsa Sum matuqar karban fatan jikinsa abinka da farin mutum Ya kafa wata tsadaddiyar huwa Brown covvers yasaka aqafarsa sai agogon azurfa dake daure ahannunsa Ga wani uban qamshi dayake xubawa na musamman Tabbas ya fito a Ango sak👌🏻 Nan fa su Dr khalid suka fara tsokalansa anata barkwanci TJ ne ya kirasa awaya yana dauka yace yane kuna inane Papa yace muna gida amma yanzun zamu wuce TJ yace shine ka azalzalemu ashema baku fitoba to gashinan yanzun haka muna hanya mun dakko amarya Papa yace to sarkin mita naga dai munfiku kusa dawajen ko kafin ku qaraso mun iso muma Ok toh saimun hadu Nan suka fito suka shishshiga motocinsu suka wuce wajen da zaayi KAMUN Su papa suna isowa su TJ ma suka iso Sunsamu angama taruwa amarya kawi da ango ake jira TJ yace basai kunfitoba barin su qaraso naga suna tahowa sannan shima ya fice Ta cikin glass take hangosa shida abokansa suna tahowa sunkuyarda kanta kawai tayi wadda ita kadai tasan yanayin datake ciki Suna qarasowa yasa hannu ya bude motar datake ciki Ya salam shine abinda ya furta ahankali ganin irin kyan datayi Sanye take cikin wani less pich colour mai toches na coppee brown Dinkin riqa a siket wadda yamatuqar qarbanta kaman ba gobe Fiskantannan yasha makeup Dan qaramin bakinnan anlailayesa da pinks jambaki Kyaukam baa magana gashin kantannan sai sheqi da qamshi yake andaureshi waje guda da pich ribbon Sai head na kanta shima coppee brown jeweries natama wasu passion ne dik suma coppee brown masu adon duwarwatsu pich n white Takalminta da purse nata dik coppee brown Ahankali yake sakin wani murmushi wadda shikadai yasan maanarsa Daurewa yayi ya daidaita muryarsa ya kira sunanta cikin wani tattausan murya yace my princess Dago daradaran idanuwanta masu yarwar lashes tayi ta amsa da muryarta mai dadin gaske naam Wani lumshe idanu yayi sannan ya bude yana kallon kwayar idonta wadda yasha kajol da maskara tare da siririn line eye liner Sannan yace meet my friends yana kirga mata sunansu Dik saida suka gaisa kuma sun yaba da zaben abokin nasu Daga qarshe ya introducing mata abokansa uku da sukazo daga india yace yeh he Himesh(wannan shine Himesh), Salman aur Imran(da) Cikin sakin fuska suka gaisa nan TJ ya qaraso yace man kukadai ake jirafa Papa yace ok muje toh duban Fauziyyah yayi yace my princess muje ko Cikin natsuwa ta sako qafarta nan yasake shagala wajen kallon lallen da aka qawata qafarta dashi na zallan jan rani Jerawa sukayi cikin takun qasaita dan jin kansa yake asama qasaisatar ta motsa jinin sarautar ya tsinke Fauziyyah kuwa dik saita jita atakure dake ita bawasu qawaye ke gareta ba kwakwata su shidane sai Suna shiga cikin hall din waje ya kaure da tattausan waqa mai dadin gaske
.
Wajenda aka qawatashi da ado sosai kuma kalan kayansu hatta ballons da aka decourating wajen pich n coppee brown ne Wasu kujeru ne guda biyu iri daya masu kyan gaske suka qarasa suka zauna sai kuma na abokanai da qawaye da aka ajiye daga bayansu Kowa ya shashe ranan angwangwaje naira tayi kuka ko motsi tayi saiyace yadai baby kingaji ne sabida yadda yakeji kamar ya maida ciki dan so Fans na Mmn Faty Novel ma baa bassu abayaba dan sun nuna murnansu sunkuma nunama ma fauziyyah gata Kodagakan irin liki da sukaringa mata shima abin ajinjina masu ne Baa tashi ba sai gabda magriba sannan taro ya watse Ahanyar su ta komawa gidane papa yaga canji yayi juyin duniya fauziyyah tayi magana amma taqi sam shikuma harga Allah baison shirunta shifa ko zaginsane garatayi yasan tayi magana dan baimanta lokacin data kullaci abu aranta tadaina masa magana Haka suka sauqeta suka dawo gida Washe gari Thursday akayi Family n Friends day Nanma sunyi kyau ba qarya Ranan friday akayi Hafla Sai washe gari Saturday misalin Qarfe sha daya na safe dubban jamaa manyan mutane maaikata yankasuwa hadda sarakuna da sauran Alumma suka shaida daurin Auren Dr Muhammad Alamin Abubakar n Fatima Usman abisa sadaki 100k lakadan ba ajalanba Papa dai bakinsa bai rufuwa daka ganshi kasan yana yanayin farin ciki lura daga kayan jikinsa komai fari tass Sai gaisawa yake da jamaa kawai Makada da maroka kuwa sai wasashi sukeyi abindai abin birgewa sai muce Allah ya kade fitina kawai Da yamma akazo daukan amarya Wata goggonsu papa wadda take yace awajensu daddy ita tabada wata Alkyabba ta musamman tace asawa amarya ita Fauziyyah tai kuka harta gode Allah sabida nasihan da su Abba suka mata mai ratsa zuciya da dikkan gangan jiki Da mata adduan Allah yasa sai gawanta zaa fitar agidan Alamin Haka aka wuce da ita fada su anty papa aka samu a side din da zaa sauqi amarya Nan suka karbi amarya da murna da farin ciki gami da mutunchi Nan suka shiga hidima da baki dan Aunty naja(Auntyn Papa ) batada rowa kuma batason harkan qaranta Dik wadda yazo kawo amarya ya yaba da irin kaunar da yan uwan papa kema Fauziyyah sai fatan alheri suke musu Bangare guda Aunty papa ta sauqi Fauziyyahs' team Kuma sun yaba sosai dan Aunty papa bata musu qarantaba ta nuna musu cewar biki ake na dan gata Har wajen magriba fauziyyah taqi yin shiru sai kuka take Saida Aunties dinta suka shigo suka lallasheta sannan tayi shiru Anayin sallan ishai Aunty mabarukha ta kawo mai kwalliya akayima Fauziyyah Wani mterial ne dinkin doguwar riga milk n golding colour tasaka wadda yasha ado sosai yakuma matuqar yimata kyau Kwalliya sosai aka mata sai dan veil din rigar wadda shima golding colour ne tayane kanta dashi Wani danqareren saitin gold Aunty Mabatukha takawo mata tasaka hadda bangkes dinsa manya guda biyu Takalmin hill ne sosai da purse dinsa suma golding colour Wasu turaruka na musamman tafesa wadda dik aunty Mabarukha ce takawo mata su Nan tafito a amaryarta ba qarya Members na Mmn Faty Group sunsha anko dinsu na material Fauziyyahs's team sunyi ankon material golding colour Sai papas' team sukuma ankon material milk colour sukayi Nan aka fara tafiya dinner kowa ya tafi sai Fauziyyah ita kadai akabari dan wannan umarnin Ango ne Tana zaune abakin bed shiru itakadai sai taji motsin bude qofa Bata dago kanta ba amma qamshin turarensa daya gauraye dakin shiya tabbatar mata papa ne Sanye yake da wani dhegen gezna maih danbanzan kyau da tsada Milk colour Dikin yamatuqar amsansa ga hularsa da ta dace da kayan hafi da takalminsa Qaremata kallo kawai ya tsaya yi yana yima ubangiji tasbihi acikin zuciyarsa daya mallaka masa ita amatsayin mata Ahankali ya tako har bakin gadon datake zaune Maganama ya kasa kawai hannunta ya kamo ya riqe gam acikin nasa Wani taushi dayaji shiya haifar masa da kasala lis ajikinsa Dayan hannunsa yasaka yana murza bangles din hannunta Da wata iriyar murya yace my princess pls na roqeki kimun magana kinji Kallonsa tadanyi ta kasan idanunta ta dan turo baki tace to mai zance maka pls kasakemun hannuna Cos yadda yake wasa da hannun nata dik sai taji ta takura Shikuma gyara zamansa yayi yama manta da yabar mutum awaje nan yafara barbada mata maganganun soyayya Qarar wayarsa yasashi yin dan qaramin tsaki dan yana tsaka da jin dadin yadda yake manne da ita bata kuma turesaba Ganin TJ ne yasa yace yane akayi TJ yace lallema toh kawai kace inje insallami mutane tunda kai kasamu waje bazaka fitoba Papa yace oh yaushema nashigo to naji gamunan fitowa Baby nah mujeko kinga wannan dan damuwar da takurin yafara mita Batace dashi komaiba hannunta ya riqo ta miqe suka tako ahankali suka fito.... .
.
Hannunsa riqe acikin anata har bakin mota TJ dake tsaye yana jiransu shiya bude mata Da murmushi afiskansa yace bismillah Amaryanmu Batace komaiba sai murmushi datayi sannan ta shiga tazauna Ya rufe kafin ya zagaya ya shiga shima Papama ta gefenta ya zagaya ya zauna Tafiya suke suke bamai cewa komai itadai ta sunkuyar dakanta tana wasa da ring din yatsanta Papa kuwa ya wani matso jikinta kamar wadda zai shige cikinta amma baicewa komai cos hakanma he is totaly satisfied TJ kuwa katse shurun yayi da kunna wani tattausan music mai dadin sauraro Da haka har suka iso Batare da bata lokaciba abokai da qawaye suka rufa musu baya zuwa cikin hall din Lokacin da suka shigo nan aka fara musu ruwan wasu flowers masu kyan gaske da qamshi mai dadi DJ kuwa waqar da aka masu ta biki ya kunna nan waje ya birge sosai Cikin takun natsuwa suka qarasa wajen zamansu kafin kowa ya sami waje ya zauna Baqarya wajen ya qayatu ya kuma matuqar birgewa dan naira tayi kuka Nan aka fara gudanar da programs iri da ban da ban Idan ka kalli Amarya da Ango ka rantse kace wasu couples ne masu mutuwar son junansu Yadda fauziyyah tasake fiskarta kamar bawani abu aqasa Shikuma uban gayyar dama sai faraa yake kamar gonan auduga yana wani shige mata ganin yadda ta saki jikinta tamkar ba itaba Kowa ka gani awajen yasha ado da kwalliya gaskiya bikinsu papa ya matuqar tsaruwa sai fatan zaman lfy Sai wajen 12 aka tashi Saida kowa ya watse ya rage su papa aka bari kafin suka taho suma Ahanya papa yacema TJ man kadaukomin saqona daiko TJ yace waneni namanta yana gaba nan qasan seat Papa yace ok thanks Suna isowa gida TJ ya bude mota ya miqo masa ledan take away sannan ya fice Itama bude qofar motar take qoqarin zata fice Riqo hannunta yayi Juyowa tayi ta sauqe daradaran idanuwanta akansa kafin dan qaramin bakinta ya motsa gami furta lfy daiko Yadda tai maganar ba walwala afiskanta yasa ya marairaice murya yace pls kiban 15mins acikin lokacinki Pls mana dear badan niba dan Allah Komawa tayi tazauna Thanks yafada sannan yasake mata hannu Take away din ya bude pepper chikchen ne wadda yasha hadi sosai Kallonta yayi da kyau kafin yace baby pls bawasa nakeba kici abinci kuma kada kice aa dan nasan wunin yau kaf da wuya idan kinci wani abin Shiru tayi tana tuna tabbas yau bataci wani abinkirkiba Bude motar yayi ya balle bottle din ruwa ya dauraye hannunsa Naman ya kutsiro ya miqo mata saitin bakinta Ba musu ta karba tafara tauna ahankali Ganin yadda batai gardama yasa yaci gaba da bata abaki tanaci Matsowa yayi sosai yana lallabata harta ci sosai kafin ta kauda kanta Ruwa ya bata tasha sannan ya bude mata roban juice sai anan ta kauda kanta tace umum Murmushi yayi yace thanks a lot wifey nagode muje narakaki ko Aa kawai tace dashi tafice abinta ***** Washe gari sunday akayi walimah dasafe daganan wasu suka fara tafiya garuruwansu Amma su papa sai gobe dasu koma bh Abdu yasa ya maida su Himesh bh sabida gobe jirgin safe zasubi zuwa lagos dagacan su wuce Abokanansu dik sun koma TJ ne bai tafiba sai gobe zasu wuce tare da Ango Itama qawayenta dasukazo daga bh guda biyu sun koma sauran ukun dama yan uwane Haka ta yini shiru itakadai su aunty mabarukha ma basu zannaba sabida sallamar baqi Shima haka ya wuni sallama da baqi gashi sunje gidan Abbama sunjima acan Sai dare aunty mabarukha ta shigo nan tace tana da magana da ita
.
Gyara zamanta tana sauraronta Aunty mabarukha tace abinda zan fada maki kidauka ni yar uwarkice kuma ciki daya kikuma dauka bansan papa banida alaqa dashi Taci gaba dacewa inason kidauki wannan auren yana cikin kaddaranki arayuwa wanda baki isa kikaucewaba Kuma tunda har Allah ya rubuta haka inason ki haqura kidauki qaddara ki rungumi mijinki kimasa biyayyar aure Dik halin da kuke ciki da papa ina sane amma yanzun tunda andaura maku aure zance ya qare Kuma bama fata abinda zai kuma rabaku sai dai mutuwa Jikintane yayi sanyi kuma ko itama tunanin datake aranta kenan tunda Allah ya qaddari haka tafaru gara ta dau haquri suzauna lfy Aunty mabarukha tace sabida haka kidauka dik abinda yafaru abaya kamar bai faruba kuma bama fatan ya kuma faruwa Kuma ina da tabbacin hakan bazai faruba sabida yanzun papa yana sonki so mai tsananin gaske kuma zai iya komai akanki Amma bawai ina nufin dakunkoma bh kibada kai bori ya hauba aa ki nuna masa cewar kema mace ce Saikin dan wanasa tukun saiki saqqo ku zauna lfy Allah ya albarkaceku Sannan kada ki kuskura kiyadda kunya ta cuceki dan matuqar zakiji kunyan yin wani abin toko zaki kwari kanki Gobe akwai kayan dazan kawo maki idan kinkoma bh Su zaki ringa sawa agida kina kwalliya tareda yin qayataccen girki kuma kada kihanasa Kibashi dik tarkone yadda zaiji kawai bazai iya rayuwa bakeba kuma komai kikace yamaki zai maki Amma kada kimanta kina riqe da class naki harsai yagane kuransa yadda koda kudi akabasa bazai tabayin gigin batamaki raiba Dafatan kinfahimceni Cikin sanyin murya tace insha Allahu aunty zanyi yadda kikafada Aunty tace yawwa qanwata Allah ya maku albarka sannan zanyi magana da Aunty naja(Aunty Papa )tace zatana aiko maku da abinci zance tabari kawai sabida musamu tarkon ya kamashi Tace toh aunty nagode Allah yabar zumunci Miqewa tayi tace barinje wajen momcy sabida shirin tafiya amma zandawo mukwana tare Tace toh saikin dawo itakuma ta fice Shiru tayi tana tuna maganganun da aunty tafada mata tabbas gaskiyane Da haka har bacci ya kwasheta sabida dama agajiye take batamaji shigowar Aunty ba Washegari wajen laasar suka iso bh Direct gidanta aka wuce ta da ita wannan umarnin daddy ne Shima papa gidan ya taho yayi wanka sannan ya fita amsa kiran daddy baiko leqa taba dan yasan tana tare da mutane Aunty ma cewa tayi bari taje gida zata aiko hannatu mai aikinta wadda tare sukazo da driver su kawo mata wannan sakon Nan sukayi sallama akan suma gobe zasu wuce Su Aunty niima ma cewa sukayi tafiya zasuyi dik suka watse suka barta ita kadai Suna zolayarta ainty ce tace Allah ya kaimu next year kamar haka muzo musha suna Aunty niima tace aikin kai da nisa dama cewa kikayi nanda 9months kinaga yadda papa ke rawan kannan ai kinsan basauqi Itadai batace komaiba dan kunyama suka bata Bayan sun tafi itama ta fito tafara zagaya gidan Tana kallon yadda aka barar da dukiya tundaga kan ginin har izuwa kayan cikin gidan Ta jinjinama daddy takuma gode masa dan baqaramin rawar gani ya takaba Tsayawa fasalta kyan gidanma bata lokane mai karatu fasalta da kanka kawai Sai datayi sallan magriba da ishai sannan tashiga qayataccen toilet dinta ta sheqa wanka Kwalliya tayi sosai cikin atamfa lemon green mai matuqar kyau Tayi kyau abinta dambun naman da momcy ta aiko mata lokacin da aka kawo mata saqon aunty mabarukha shitaci ta koshi abinta Lfyr gado tabi tadau wayarta ta hau facebook tana maida saqon fatan alkhairi da aka turo mata na biki Papa kuwa ahanyarsa ta dawowa gida saida ya tsaya ya sai masu tsaraban irin wadda ango ke kawoma Amarya Hankalinsa dik yana wajen Fauzynsa dan yasan ita kadaice agida Yana zuwa bakin gate ya danna horn maigadi ya bude masa ya shige Parking yayi sannan ya dauko ledodin daya saya ahanya ya nufo gida Kamar zai wuce dakinsa amma saiyaji ina baxai iyaba saiyaga lfyrta tukun Tana kwance taji anturo qofar anshigo tare da sallama Dago kanta tayi kallo daya taimasa tasauqe kanta Cikiciki ta amsa sallamarma Shikuma wani murmushi yayi ganin yadda kwalliyar tamata kyau saita sake shiga ransa Takowa yayi ya ajiye ledodin hannunsa ya qarasa bakin gadon ya zauna kusa da ita Sai anan ta dago kanta fiska atamke take kallon yadda ya wani zauna kamar zai rugumeta Why have u come here? Tafada tana kallonsa Murmushi yayi mai qayatarda face nasa yace nazo ne naga yadda kika yini nakuma miki bangajiya konayi laifine yin hakan baby na Eh,tafada Cikin sauri ya dubeta yace bakiso kenan na duba lfyrki Banaso nanma tafada kanta tsaye tareda juya masa baya Jikinsane yayi sanyi cikin sanyin murya ya fara magana I really understand why u ar very angry Juyowa tayi tace ya Alamin i don't want any discussion, it will be better for u to getout of my room, pls go now Shiru ya danyi kafin yafara magana da muryar nadama yace baby i do not have the courage to look in to ur eyes N there's no doubt that i had made a mistake n it is true that i regret everything that i have done Naji naji pls saida safe banason dogon zance tafada tana juyawa Yace to kifadamun abinda zanmaki wanda zai zama punishment agareni ke kuma ki huce Tace maganace banason kamun inhar ba nice na nema ba thats all Shiru yayi yana jinjina maganar amma bayadda ya iya dole ya amince Cikin murya mai sanyi yace ok naji inhar hakan zaisa kihuce kuma kiyafemun i accept this punishment Yana fadin haka ya miqe jiki amace tare dace mata ga Abinci kici kada ki kwanta da yunwa kafin yafice zuciyarsa wani iri yana sakejin tsanar kansa dan yasan shiya jama kansa.....
0 comments:
Post a Comment