Blogroll

BANNER 728X90

Monday, 12 February 2018

CIWON SO Page 1-5

CIWON SO Page 1-5
.
    Na Hafsat ( Hafsy baby)
.
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai.
.
Yan Mata guda biyu  sunata shiri zasu school  adauki  wannan A shafa wannan  cikin sauri  Meenat tadauko kaya tasa Amma safeeya  batada niyyar tashi A bakin mirror  har Meenat tasa cikin fada Meenat tace Amma kinsan yau  muda lecture din Dr Ahmed kuma shine first, kuma kinsan idan ya shiga  class babu wadda zai Kara shiga Amma  kintsaya sai wani lindar fuska kike.  Safiyya tace sorry, sis  yanzu Zan tashi  kikara hakuri. Tana idarwa  ta wuce ma' adanar  kayansu(wadrope) tasawani red din  material  Masha  Allah tayi kyau  Abinka da farar Mace  suka fito  suka iske  umma da Abba bisa dinning table domin break fast  suka hada baki morning umma, morning. Abba, umma da Abba suka ce lafiya twins din Umma da dady. Sukaja kujera  suka zauna sharp sharp sukayi break fast.  Suka mike umma nd Abba muntafi school.  Suka A dawo lfy. Suna. Fitowa  safeeya tace pls, my sis  kiyi driving zuwa school  banason bata kwalliya na. Meenat tace chabb!! Sai dai  muyi late sai inatukamu  cikin fuskar rarrshin safeeya  tace pls my sister nandai ta rarrsheta sukaje  ( ummaru musa yar aduwa university).bayan sun isa  suna shiga  Suka nufi class  suka zauna  ko 5 minutes baayi ba saiga Dr Ahmed.ya shigo  nanda    kowa ya shiga  hankalinsa   yan Mata kuwa kowace  jiki yace morning class. Sukace morning sir, yarubata test   bisa Allo  kowa ya firgita da hakan  30 mints yabada kowa yagama. Nan safeeya ta kalli  Meenat masu   niyya suka Fara masu maida hankali  Akan Abinda Ake  saffiya ta tambayi  wani question  tabata ganeba  Dr Ahmed  ya Lura  da itah  yace  ke get out, tace pls. Sir Am sorry  yace I say get out  cikin sanyi jiki ta tashi  tabar class din.
.
Safeeya  na fita ta nufi wani wajen da babu mutane sosaitazauna tayi tagumi  tafada tunani zuciyata meyasa kikayiman haka nafada cikin son Dr Ahmed  mutumin daya tsane ni bayason ganina ba batasan sadda hawaye ke tsiyaya da fuskar ta ba    saboda  CIWON SO Dr Ahmed kedamunta kullum kara yawa yake tare da itah. Kamshi wani turare taji mai kamshi ya ziyarci   A hanci  tadago  fuska ta ga waye sai sukayi Arba da Dr  Ahmed ya wuce da  barandar datake zaune. Can taji wasu  yan Mata na gulmar suna cewa keh Aseeya wallahi Dr Ahmed ya hadu Amma ya cika miskilanci. Rannan naje office din Amma kinga fuskar yadda kikasan bataba dariya haka yadaure  fuska  nayi sallama nashiga nace sir inayini cikin daure fuska ya Amsa yaceman meke tafe Dani  nacemasa Dama wutowa nazo yi nace bari nashigo bebari na ida ba ya kwasaman wata. Tsawa  yace nabarmishi office dinshi cikin sanyi jiki. Nafito nagayamiki. Safeeya taja wani tsaki tana takaicin wasu matan dake bada Kansu ga wasu mazan domin ita ko ciwon so zai kasheta bazata taba tarar dr Ahmed tace tana sonshi ba. Can kuwa bayan Meenat sun fito tana ta neman safeeya. Tarasa  can tagasu  wadda. Suke gaisawa. Ta tambyesu sunga safeeya suka ce tana baya can tanufa   ta iske ta zaune. Tace shine zaki bani wahala ko tace sorry sis Meenat ta nemi wuri ta zauna  tace wai sis mekika yima Dr Ahmed yake miki  haka ne safeeya  tace wallahi  sister bansan Abinda nayi masa yakeman haka. Tace yanzu yazakiyi da test din datawuceki tashi ne yau.  Kizo muje office dinsa mubashi hakuri  safeeya  tace. Sister kinsan hali Dr Ahmed bazai yiba tace  kedai   tazo muje. Cikin sanyi jiki ta tashi suka nufi Amma sai sukayi rashin sa' a office din kulle yake.
.

   Cikin damuwa Meenat tace kinga bayanan ko sis safeeya tace Eh mujuya gobe nashigo  dakaina da  munshigo school  din nabashi hakuri suka juya suka koma cikin makaranta  bayan sun idar da lecture din dasuke da itah suka hau mota suka nufi gida suna isa gida suka nufi dakinsu suka wasa ruwa Dama lokacin sallar Azahar yayi suka sallah Meenat ta Lura yau safeeya bata cikin walwala sosai  bata surutun nan Nata data Saba  tace wai sister meke damunki na Lura tun school bakya walwala meyafaru ne  ko tun abinda Dr Ahmed yayi miki  baki manta bane. Safeeya tace yazaayi na manta sis mutanan yatsaneni ban San Abinda nayimasa sister Abinka kadan ya  zan masa ya disgani cikin mutane kina kallo yau fa bani kadai nayi magana Amma nikadai ya hango yafiddo ni. Bata Ankara sai hawaye shar shar. A fuskarta domin wani ciwon so Dr Ahmed ke tasomata A zuciya  Meenat tace safeeya meyakai na kuka safeeya tace Abinda yakeman yasani kuka( batasan ciwon so Dr Ahmed  bane yasa safeeya (Hawaye.   Tace kiyi hakuri taso muje kinsan Umma batasan dawowar mu ba  suka nufi daki umma su  suka isketa zaune bisa darduma tana lazimi sukayi sallama suna shiga tagama laximin bayan ta idar tace yan biyun umma Andawo Eh, umma mundawo har munyi sallah ma tace toh madallah kuje  ga Abicin kucan bisa dinning koh. Sukace to umma suka nufi  dinning safeeya tura kawai take domin batasan  Meenat tafahimci halin datake ciki.  Bayan sun idar suka tashi suka nufi dakinsu. 
Bayan sallar isha' I suna zaune falo da suna kallon labarai  da Abba su duka dai. Har wajen  karfe goma.  Sannan sukayi ma iyayen nasu sai da safe suka nufi dakinsu. Meenat naxuwa tafada gado  domin bacci takeji sosai. Safiyya tabi bayan ta Amma  takasa Bacci tunani Dr Ahmed kawai take sai juye juye take.har dai bacci yadauketa. Asuba tagari

Washe gari
Abba yashiga kwankwasa kofar su safeeya domin sallar Asuba domin kullum dayatashi sai yaxo   yatadasu  shikuma ya nufi masallachi. Bayan sun tashi sunyi sallah sai kuma su shiga kitchen domin shirya break fast domin umma batada yar Aiki bata bukatar ta  daga itah  sai yayanta. Bayan sun kamallah. Sukaje sukayi wanka  nanfa suka hau shirin school. Safeeya tajawo wata Arabia gown  tayi rolling da blue din gylen  Masha  Allah gaskiya tayi kyau domin sai da Meenat tace Kai sister kinga kyan dakikayi KO sai kace balarabiya. Safeeya tace Kai sister banason zolayafa tace Allah kuwa kin wanku. Nan suka yan Mata biyu kyawawa dasu suka gaida iyeyensu sukayi break suka nufi school cikin motarsu. Suna parking suka  fito  suka nufi class. Sungama daukar lecture ta farko sai kuma karfe 2:00 pm bayan sunfito. Safeeya tace sis bara naje office din Dr Ahmed naji yazamuyi dashi  game da test din jiya  Meenat tace muje tare mana safeeya tace A, a bara dai naje naje ni daya kinsan halinshi fa nan Meenat tace shikenan kije ki iske ni inda nadaki jiya . Safiyya tace OK , tajuya ta nufi office din Dr Ahmed cikin sa' a ta iskeshi bude gabanta na faduwa tayi sallama ta shiga.
.
Safeeya nashiga  ta iske Dr Ahmed bisa table yana rubutu   tace sir Inayini  bai dago fuskar  yaga waye ba yace lafiya lau  yacigaba da rubutun sa  ta kusan 15 minutes tsaye sannnan yadago fuskar sa  cikin daure fuska yace meke tafe dakene. Nan kwarjinin sa yayima safeeya yawa domin ya tsare ta da manya idanuwansa. Tace sir hakuri nazo baka Akan test din dakayi jiya  kayi hakuri kasakeman wata. Yace sai dai kiyi hakuri kitari wata. Domin nawuce wannan Kuma. Kisake laifin haka nakara koranki. Ya sunkuyar dakanshi ya cigabada Abinda  yake. Cikin sanyi jiki safeeya  tafito ta nufi inda Meenat tace ta sameta can ta tanufa ta iske Meenat tana duba wani book.  Tace yane sis kindace tace A, a yace saidai natari wata kuma nakara Abinda nayi nakara  fita. Sister narasa abinda nayima  Dr Ahmed yatsaneni haka. Nan tafashe da kuka domin zuciyar ta wani zafi take Mata Meenat nace kiyi hakuri ki kyaleshi sister kinji ko nan ta rarrsheta. Lokacin  shiga lecture dinsu yayi suka tashi suka shiga. Bayan sunfito  suka nufi gida  Amma kowaya  san yau safeeya bata cikin walwala  daki tawuni yau. 
Washe gari kamar yadda suka Saba sun isa school  suka nufi class Amma me suna shiga suka tarar da Dr Ahmed   ciki yafara lesson .  Amma yabada baya cikin sanda suka shiga  suka zauna  Joyowar  dai zaiyi saiyaga safeeya. Zaune yace keh!!!! Bakisan  dokokina ne ba fita kibarman class har Meenat ta mike zata bita yace kan yajuyo kwanta  yace badake nakeba ita kadai nake. Cikin fushi safeeya tatashi tafita cikin wani irin kuka mai ban tausayi  tafita  taji ma ta iya tsaya cikin school ba fitowa tayi ta tsaida nepep tanufi gida. Umma kawai ganni kawai tashigo tace lafiya safeeya kika dawo yanzu cikin dauriya tace umma bana lafiya ne  tace subhanallah!!! Meyasameki tace zazzabi ne tace jeki daki bari  nadauko miki magani safeeya tanufi dakinsu ta wurgar da mayafin da jakar tafada gado   ta kwanta bata jimaba  saiga umma da magani   takawomata tace maza  sha gabana nasan ki da kin magani. Nan tasha umma tace to Allah sawwaka tajuya tafita. Can kuma  Meenat tafito daga lecture Dama yau daya garesu. Taduba duk inda take tsammani  safeeya Amma bata Gantaba. Sai kawai takira wayanta. Safeeya tace tatafo gida.  Meenat kawai tashiga   mota tanufo gida. Ba. Inda tazame sai dakinsu ta iske safeeya kwance  tace  sis baki lafiya ne tace  inafitowa wani zazzabi ya rufeni kawai sai na tafo. Meenat tace har kinsa hankalina ya tashi wallahi. Meenat tace gaskiya Abinda Dr Ahmed yakemiki yayi yawa. Kodai ki manta Akwai Abinda yahadaku ne. Safeeya tace Wallahi sis babu Abinda  nayimasa.Tsane ce kawai. Amma  gobe bazan duba kwarjini dayakeman Zan tunkareshi naji menayimasa ya tsaneni haka.
.
Meenat taja wani numfashi tace kinaga hakan zai yiyu kuwa sister safeeya tace hakan shine mafita sister   domin nagaji dahakan dayakeman kamar ni kadai  A fadi school. Meenat ta mike  tace ke bari naje dakin umma batasan nadawo ba domin nan kawai nayo domin hankalina yatashi wallahi. Daban ganki cikin school ba  tana shirin fita sai ga umma tashigo   tace Ahh,Ahh, yaushe kikadawo ne ke tace yanzu nashigo umma da Ina niyyar shiga   dakin ki sai gaki  kinshigo  umma tace nashigo ne dama naduba jikin  safeeya naga yajikin karfe Safeeya tace umma da sauki sosaima yanzu zantashi nayi  sallah ne. Umma tace to kitashi kiyi ga dan gidanki can nayi miki dan' wake  kiyi sallah sai kici  Nizan deka gidan  Kawunku   naji Alhaji nafadi dazu hajiya murja ta tazame da tayils ta goce da kafa  Anjima kinkara  jin sauki sai Ku leka kuganota. Safeeya tace sai kindawo umma.  Umma tajuya tafita.
Bayan sallar Magariba safeeya da Meenat suka nufi gidan kawunsu domin ga gida ga gida  suke suna shiga suka iske.  Haidar zai fita( dan kawunsu ne) haidar yace yafara washe hakora kamar me tallar close up,  safeeya takara daure fuska Meenat ce kawai tadan Saki fuska tace yaya haidar  Ina yini yace bazan Amsa ba Ku baa ganinku sai da dalili ko yanzu ma don mamy tagoce  dab aza gankuba ko Meenat tace wallahi karatu yadau zafi ne shi yasa . Haidr ya juya bangaren da safeeya take yace ke kurma ce  dabazakiyi ma mutane magana ba safeeya inayini bata jira ya Amsa ba tashigewar wata ciki  bata jira Meenat ba   Haidar ya kada Kai domin CIWON SO  Safeeya nadumshi tun lokacin da yafada Mata ta canza mishi. Bayan sun shiga ganin marar lafiya ne sun dan jima  suka fito suka nufi gida  bayan sallar Isha' ne suna zaune  A falo bayan sun gama cin Abinci dare  kamar yadda suka saba wajen karfe 10: 00 pm kowa ya nufi makwancin sa. Amma safeeya babu Abinda take sai juye juye bisa gado  domin wani fitanenen ciwon so Dr ke tasomata  kuma koda zai kasheta bazata iyah tunkarsa tace tana sonsa. Kuma gobe tayi Alkawarin tunkaranshi taji meta iyimishi ya tsaneta haka. Nan tana juye juye har bacci yasadodo ya saceta.Asuba ta gari yan  biyun umma.
.
Washe. Gari kamar yadda suka saba  tashi suka gama Abinda suke suka nufi school. Suna fitowa safeeya tace zataje gun  Dr Ahmed. Meenat ta dakatar da itah tace tabari sufito daga lecture  sai taje office dinshi . Meenat suna  tafiya zuwa class take cewa nidama kin kyaleshi wallahi sister  duka kingi one year mu ida school din  fa, basai  yakara ganniki ba sannan zai miki. Nan gaban safeeya yafadi ta tuna kingi  shekara daya fa  su ida school  tadaina ganin muradin  ranta(Allah sarki So duk irinda Abinda yakemata bata gani zuciyarta taki fushi dashi)  Meenat tace sis yanaji kinyi shiru ne. Takakaro wani  nurmushi tace Ahhh,, babu komai sis  tunani nake wai kingi shekara daya mu ida  school. Daganan firar su tazo  karshe domin su iso class,   Bayan sun fito daga lecture ne   Meenat batasan zamewar safeeya tanufi office din Dr Ahmed.  Tana isa ta iske yana kokarin rufe. Office din  tayi sallama yajuyo yaga waye yanaga safeeya yace yakara daure fuska. Yacemata mekawoki wajena ba tunjiya mukayi magana dake ba  nakuma baki Amsa. Ya bita ta gabanta zai wuce. Safeeya tayi saurin shan gabanshi. Tace sir bawannan yakawoni  cikin fada  take magana yayi mamakin haka daga bakin safeeya  Amma benunamata ba yace  mekawoki  domin ina  da Abinyi Ina sauri ne nabaki  5 minutes kifadi Abinda yakawoki. Tace bazan wuce hakan ba domin banga Abin  tsayawa wajenka ( Karfin hali)
Sir naga duk cikin school babu wadda katsana kamanta. Mekake takama dashi, Kudi, mulki, kyau,   komai daza kadinga wulakanta mutane yadda kakadama kasani babu Abinda  yakai mutum daraja Amma Kaine Abin wulakacika, Kullum duk Abinda kake takama dashi fa Akwai wadda yafika. Ina sanar dakai kabi duniya  A sannu  ba matabbbata. Ba wurine dazamaba nar har Abadaba. Wulakanta mutane kuma kacigaba. Banyi maka wannan Maganar daka daina tsanata ba Ahhh, na tunatar dakaine.  Nabarka lafiya. Safeeya tajuyo. Tatafi kawai  tabar Dr Ahmed tsaye kamar butun butun butumi domin tunda tafara Maganar ya kuramata Ido nan yaji wani Abu yanayimasa yawo  Akai ( tofa meye wannnan)    A bangaren safeeya  Kuma ba nufi wajen Meenat can baya takoma inda babu mutane tasha kukanta ta koshi har inda ta yacanza Allah sarki safeeya ciwon so Dr  Ahmed  na  Amma tadaure tayimasa magana. Haka .
.

Safeeya nan wajen Tasha. Kuka tagaji taji kanta na ciwo. Tana niyyar mikewa taji wayanta na ringin taduba taga Meenat ce. Tace hello, Meenat cikin fada tace Ina kika shigane Ina nemakin tundazu  tace sorry sis ganinan zuwa. Bayan sun idar da lecture din suka nufi  gida. Kamar yadda bayan sun idar da Abinda suke sukayi ma iyayensu bakwana kowa yanufi makwancinsa   safeeya tafara tunanin datasaba kullum dare. Takasa bacci ma baki daya tatashi tayo Alwalla tayi sallah ra' ka biyu.  Ta roki  Allah yayemata son Dr Ahmed inba Alkairi bane. Tare da itah. Bayan tagama  tatashi tahau gado  ta kwanta can sama sama bacci  yafara daukar ta taji wani zafi  A kirjinta   tun tana daurewa har takai datafara numfashi sama sama. Can. Meenat taji kamar   A mafarki  taji numfashi  firgice tatashi ta kunna   lantarki taga safeeya ce cikin wannan halin   A firgice tace sister! Sister!!! Amma taga numfashinta sama sama kawai yake   A firgice ta Doro. Daga bisa Gado  ta nufi  Hanyar waje domin kiran Umma da Abba  tazuwa tashiga knocking din kyauren  Daki Abba. Da karfi A firgice umma da Abba suka farka  sukaji buga kyaure ba kaukautawa Abba yazo ya bude  kyauren  yaga Meenat yace meyafaru  Amina( domin haka yake kiranta) cikin kuka tafara magana Abba.. Safeeya bata lafiya gayanacan numfashi ta ....bebari ta ida yanufi dakinsu  da sauri    saidai umma tabi bayansa itada Meenat  suna shiga   suka iske safeeya tana ta numfashi sama- sama  da sauri Abba yace mikar da ita kafinan na fiddo mota cikin sauri Abba yafito don fiddo mota domin tafita Asibiti  yana fiddota su umma suka fiddo da safeeya tallabe baya Meenat suka shiga  Alheri clinic suka nufa domin can suke da file  suna isa suka fiddo da safeyya wadda takejin su sama sama. Suna shiga Akabata gado. Sunyi sa' a kuwa sun iske doctor dinsu wadda kedubasu. Nan danan yashiga duba Safeeya  yaga Abinda kedamunta yayi mamakin dayaga ciwon zuciya kedamunta har  yana nema yimata illah. Cikin zuciyarta. Yasan dai ba su rasa ci ba balle  kayan sawa tomeke damunta  ne nan yafito yacemusu  suje gida sai dasafe sudawo domin yanzu zasu ajeta dakin Hutu bata bukatar hayaniya  Abba yace doctor bazan barta ko yar uwata bace yace karku damu Alhaji daki dazamu ajeta bata bukatar kowa. Abba yace doctor jikin dai sauki yace da sauki mumata wasu Allurai yanzu. Tana bacci zuwa gobe insha Allah zata warware  Abba yace toh Allah yasan haka. Doctor yace  Ameen.




Abangaren Dr Ahmed kuwa tunda Safeeya tama gayamasa  magana  tajuya  tatafi   yakusan Minute 10 goma tsaye  yana tunanin  sannan yatuuka motar yabar makarantar  babu inda ya nufa sai gida yanashiga ya iske mahaifiyarshi  A falo  tana kallo  yayi sallama yace  Hajiya tace naa' m Babana meyafaru naga yanayinka ya canza ne. Yace babu komai tace Anya babana babu komai inbaka fadaman waza kafadamawa  ne yayi murmushi babu komai hajiya.  Yatashi zai shiga ciki tacemasa Ga Abincika can  kitchen naajemaka fa.  Yace yanzu dai bari nashiga ciki nayi wanka. Nadan kwanta  Ina fitowa zuwa Anjima naci  hajiya   taceshikenan sai kafito   yajuya ya shiga ciki hajiya tabisa da ido har yashige  ciki  tace nasan Akwai Abinda kedamun yaron zurfin cikinsa da miskilanci bazai Bari yafadaman ba tagirgiza Allah sawakka karya jama kansa wani ciwo Dr Ahmed nashiga babu inda yazarce sai dakin sa   yashiga toilet yawtsa ruwa yana fitowa  jallabiya kawai ya zura yahau gado domin yasamu bacci Amma inah  babu bacci magaganun Safeeya kemasa yawo.  Nan yafara tunanin  komai yacazama masa tsanar kowace mace cikin  Ranshi

Bayataba mancewa shekara 2 datawuce yadawo  daga  Kano yanacikin tafiya.....

.

WAYE DR AHMED

.
DR Ahmed Dane ga  Alhaji Ibarahim kwangila   da hajiya Saudat.  Shi daya  Allah yabasu. Aràyuwa  yayi karatu   A kasar  Engalnd primary dinsa kawai yayi Akasar Nigeria. Yakai matakin har PHD  akasar Engaland   sunso rikeshi A kasar Amma yace kasarshi zaidawo Dr baya cikin wañaann shashan ya masu kudi wadda idan  Akatura  karatu sutai sharholiya.

Abokinsa daya  Hafiz. Shi kuma dan garin kano ne  shima Hafiz babu ruwansa karatu suka  sa gaba.  Babu ruwansu da shaye shaye ko neman Mata.suka dawo gida Nigeria  Dr Ahmed yasamu Aiki  A ummaru musa yar aduwa university.

Dr Ahmed zayakai 32 years fari dogo  ga hanci   gashi sumar sa  kamar kamar yanashafa Mata mai . Kai gaskiya Dr Ahmed ba karya ya hadu( dole saffeyya ta rude.

Maihifinsa yarasu shekara daya data wuce hanyar sa tadawo daga Abuja. Hajiya saudat taji mutuwar mijinta uba danta  domin Allah ne gatanta mijinta gata ta domin  yan garin    Rimin local government  ita dashi tatashi  A hannun kishiyar maihafiyarta domin wajen haihuwarta mahaifiyarta tarasu su ukku ita da yayyenta  yaya sule, yaya mustapa sai itah  kishirya maifiyarsu masiffatace Muguwa  domin fuska biyu gareta in maihaifinsu nan zata nunamsu Amma da yasa kafa yabar gidan  zata Fara dukansu har tagaji.Abinci ma bata basu sai in maihaifinanan. Daga baya ma saita Asirce maihaifin nasu ko gaban idonsa dukansu take.Abinci saitagama dabasu nan ta tilas tawa sai yakai yakai mustapha da  Sule karatun Allo tundai mahaifin nasu ya kaucewa domin yana son  yayanshi sharrin Ade ne kawai (Allah yaravamu da mugunta)

Har dai taci galaba kanshi  yakaisu garin katsina Karatun Allo. Daganan fa Hajiya  saudt( mahaifiyar Dr Ahmed) tazama baiwa komai na gidan itakeyinsa   Har takai Kimanin shekara17 samari sukayo Mata Ricah domin kyakyawa ce ga babu wadda tafidda ciki sai Iro. (Maihaifin dr Ahmed)   nan dai Akayi bikin babu abinda Aka kaimata sai tabarma da fillo da cooler kwara daya taso ayi bikinta yayayenta nan nan Amma tun lokacin da babansu yakoma malamin yace  tun   wanilokacin dasuka fita bara bai kara  ganinsuva. Maihaifin so yadawo hankalinshi tashe. Yana fadima Ade Amma data murza kambu Asiri sai yabar maganarsu.
Ayin bikin saudat babu dangi maihaifiya.   Domin tun lokacin  DA. Mahaifyar su saudat tarasu   sukaso su tafi dash Amma maifinsu yahana sukayi fushi suka tafiyar su basu kar waiwayensuba. Haka Akayi bikinta  Bayan wata daya  bikin Iro yaje cikin katsina yagamu da Abokinsa wadda sukayi karatu yasamu Aiki daganan har yayimasa hanya yasamu Aiki.daganan yakoma Alhaji ibarhim kwangila. Anabashi kwangilar makaratu  masallachi,   rijiyoyi. Kumabaya  ha inchi cikin Aikinsa  shiyasa  yayi Suna . daganan sukadawo cikin katsina  suka gyara gidansu na rimi saidai insu dawo su sauka ciki dawowarsu da katsina shekara daya Aka haifi Dr Ahmed.

Abin yasamo Asali dalilin dayasa Dr Ahmed yatsani mace.  Wata rana yadawo daga kano wajen Amininsa  Dr Hafiz  yakaimasa ziyara yazo daidai welcome to katsina saiyaga mace tsaye da hijabi tana daga hannu   beyi niyyar tsayawaba  Amma wata zuciyar  tasa yayo baya  cikin sauri tazo gabanshi ta tsaya yace  cikin fuskar damuwa tace ya taimaka Mata mahaifiyar tace Asibiti bata lafiya.  Yamikata gashi kuma bata da kudin zuwa . nan ya tausayamata domin ko yanayi shigarta  zaka  San  tana cikin  talauchi.
.
Dr Ahmed yace shigo tanashiga sunfara  tafiya yace wane hospital ne , tacemasa General hospital,  yace OK, sun isa General. Yakaita har can ciki  tafito tace masa nagode. Yace babu damuwa yafito yace mushiga  naga marar lafiya . domin nasamu Lada ko tayi murmushi  tace nagode. Sunashiga cikin haske Dr Ahmed yaga wannan budurwa kyakyawace Amma   talauchi yamaidata wata kalah.

Sun isa dakin da Aka kwantar da marar lafiya  Dr duk yayi ma majinyyata sannu har suka isa gadon  da wannan tanufa  tanazuwa tazuwa ta tambayi wani. Yaro dabazai wuce 14 years ba Khalipa yajikin Inna ne  khalipa wadda ta tambaya  yace gayanan tunda kikabarta tana bacci haryanxu shi take  yi kinsamo Kudin maganin domin tafiyarki Doctor yashigo sai fada yake Akan rashi sayen magani Kan lokacin.

Dr Ahmed yaji tausayi yaratsa masa zuciya  yayi gyaran murya  yace muga takardar magani kalipa yace Yaya Basma wannann waye.  Tace shine naroki Alfaarma yarageman hanya Akan dawowata daga gidan Kawu Yusuf.  Dr Ahmed ya Amshi takardar daga hannun basma wadda yaji sunanta bakin  Kanneta   yanufi pharmacy din cikin Asibiti yasiyo magagunan duk daaka rubuta  yakawomusu    yace su Kira likita sai ya gwadamusu  yadda zasuyi Amfani dasu yace saidayaga komai ya kammalla. Yajuya zaitafi  Basma tabishi daga baya.

Tace nagode Allah saka da Alkairi  bawan Allah daban samu wannnan daga gareka Daban san yadda Zanyi yau ba. Dr Ahmed yace babu damuwa har sukaxo wajen motarshi zai shiga tace kabani number ka  koma ringa gaisawa ko.  Gashi zakatafi bansan sunankaba.   Yace sunana Ahmed
Tace wow nyc name, nan yakaaranto masa number wayansa tasa. Yajuya yanufi hanyar gidan su dake Kwado.
Basma kuma tayi murmushi tace cikin ranta  burina yakusa cika Zan Auri mai  mota.Kuma kyakyawa  (Tofaa daganin sarkin fawa)

One week later

Dr Ahmed ne  zaune yana duba wasu papers,  yaji wayansa naringi yana dubawa yaga new number ne  Kamar bazai dauka Amma kawai yadauka yayi shiru can  Akace hello yaji murya mace hello wake magana.  Akacemasa  Basma ce  yace Basma wace vasma dominshi har ga Allah yamanta da bayaninta cikin ranshi tace Wadda kataimakawa rannnan  nan tayimasa bayani  yace Ayya!! Sorry nagane  ykk yamaijiki tace dasauki har An sallememuma.  Yau kwana Ukku Inna natayimaka godiya nancema tayi nakiraka  kayiman kwantacen gidanku zatazoyi maka godiya. Dr Ahmed  yace kicemata na hutar da ita  basai tazoba  saidai kibani Address naku inasamu time zanshgo  ganinanta wani dadi yaratsa Basma (Tofah)
Nan tayimasa kwantacen gidansu Unguwar Yammawa.

Basma tana datse wayar ta waiwayen wajen wadda suke zaune tace burina yakusa. Cika munerrat  wadda aka Kira da munerrat tace shakaman meyafaru Kawata  Basma tace kinsa yau ko sati biyu baayi da kwanciyar umma Asibiti ba  nan tafada yadda suka hadu Dr Ahmed.  Kuma   kinsa wani Abu Kawata wallahi  yahadu daganinashi Akwai Kudi.  Shiyasa Zan likemashi Har sai nasamu soyayar  shi. Munerrat tace nadauka wannan burin yafita daga ranki  nabaki Auren talaka sai mai Kudi  Basma tace chabb!!! Inanh burina nanan na wayagayamiki Auren  soyaya Zanyi Ai ingayimiki Ko yanzu nasamu wadda yafi Ahmed wallahi komin tsufanshi Zan Aureshi nataso cikin talaushi Kuma na Auri  dan uwana talaka. Munerrat  tace shegiya Kawata kina wuta,  tace kedai bari. Dai muga zuwa Ahmed din.
****************************
****************************

Abangaren Dr Ahmed kuwa saida sukayi kwana biyu da waya da basma sannan yazo Gidansu Dayazo saiyakira wayanta wadda yayi saving da help, tafito tayimasa iso wajen innata  tashiga dashi aga ibo masa ruwa. Cikin kwano duk lamba yanakaiwa yaji wani karni Amma hakanan yadaure yayi mashi kurba daya don karsu gane hakan.

Inna tayimasa  Godiya kamar me  nan yamike nan yana mikewa yazaro bandir   yan 200 ya ajemata  yace gashi  nan. Inna kamar tayi Kuka taitayimasa godiya. Yafito waje  Basma  tabiyo bayansa Yaya Ahmed Angode Allah saka da Alkairi tana ta fari da idanuwa  tasa wata Atamfa yellow da red. Wadda ta Aro wajen  kawarta munerrat. Yace babu damuwa yashiga mota yabar unguwa.

Daganan tun lokacin Basma tashiga isar Dr Ahmed da waya tun bai kulata   yana shareta  har yana  har yakai yana daga wayanta.  Daganan fa  soyayya tashiga tsakanin Dr Ahmed da basma. Domin basma tana da kyau ba laifi.

Daganan  Dr Ahmed yaga halin dasuke cike yagyara musu gidan  dasuke   ciki, yashiga dinka Basma sutura Kala Kala masu tsada   Daganan Basma tashiga wani girman Kai, tadinga jinta Kamar diyar shugaban Kasa, bata iyi ma yan unguwar su magana.   Bata harka da sai da yayayen masu Kudi,

*********************************†**************†*******

Soyaya tayi  Nisa tsakanin Dr Ahmed da Basma   fa babu Kama Hannun yaro. Har yana niyyar fada ba. Daddy dinsa Akan Aiko Gidan su Basma domin ayi Maganar Maganar Manya kwatsam!!! Rannan Basma taje bikin wata kawarta   diyar masu Hannu da shuni( domin Basma tacika  shige shige inhar yayan masu shine)

.
Basma Anje bikin kawarta Anata yatsina saikace  batasan wani Abu talauchi ba.
Anharde bisa Kujera Anata latsa wayar Tecno C8 wadda ko sati daya batayi ba Dr Ahmed yasiyamata  itah.   Saitaji sallama bisa Kanta  tadago Kanta ta Amsa ciki ciki yace ko gimbiyar Mata zata bani damar zama. Tadago fuska tasake kalleshi taga bakalar talaka bane( kuji Basma da karfin hali)

Tace babu damuwa zauna yajawo Kujera Kusa da itah yazauna yacemata  Barka da dare tace yauwa yace da farko sunana  Mahmoud  Kabir Nakowa. Basma tadago fuskarta A razane koshi yalura dahakan yace Kina mamaki ne Ko  tace wadda nakeji A gari bama A gariba duka Nigeria Kowa yasan shi  yace  Shikam. Basma ta jinjina Cikin Ranta  ( LaiLai)

Yace tunda kikashigo wurinan naketa hangeki Kuma naga kinyi mini Inasonki  Kozan samu karbuwa wajenki Kuwa???  Basma tayi Murmurshi tace Hmmm.

Mahmud bai wurinba saida suka Kulla soyaya da Basma  ya Amshi phone number ta tabashi Address din gidansu Ataikacedai shiyamaidata gida. Da akatashi daga party.

**********************************************************************************

Daganan fa Komai yacanza tsaninta da  Dr Ahmed ta fara canza mishi inyakirata  saitaga dama tayi picking yace Mata meyasa hakanan sai tace bata Kusa da wayar(kuma kunsan wani Abu duk tarrayar da Dr Ahmed betaba fadamaata wayeshi ba).

Rannan  Dr Ahmed yazo Suna tsaye Basma wayanta sai ringin yake Amma taki dauka. Dr Ahmed yace Mata waye ke kiranki ne kinki dauka tundazu. Tace wata friend dina plashing danazo Dauka zata Katse ne. OK  suka cigaba da zance   Amma Abu takama waige  waige dahaka sukayi dai bakwana yatafi yazo fitowa yaga wata mota itama tashigo Kuma bangaren Gidan su Basma tanufa Amma bekawo ma ranshi komai ba yatafi.

************************************************************************************

Kwatsam!!!!! Rannnnan Dr Ahmed bai Sanar da Basma zai zoba kawai yazo  yanazuwa. Kofar gidansu yaga motar dayagani rannnan nan yakira wayar Basma saidayayi Mata Kira 3 Kawai yaga Basma tafito daga cikin wannan motar tana dariya. Naciki Kuma yaja yabar wurin jiyowar da Basma zatayi kawai taga Dr  Ahmed ta firgita dagannishi Amma kawai tabasar tanufo wurinshi tace yallabai shine ko A sanardani zakazo ne. Yace kawai wurinki naji Ina shaawar zuwa ne.Basma Ina. Wayar ki nayi miki Kira Ukku bakiyi picking ba  Kuma waye yazo wajenki yanzu  questions 2 yajero mata duk tare sorry my dear wayana silance take banji Kirankabane. Wannnan Kuma wadda kaganni saurayin munerrat ne yakawo kararta Akan Abinda takemasa ne. Nan dai ta Dr Ahmed yadaina Zancen. Suka cigaba da firar har lokacin tafiyarshi yayi yatafi.

Lokaci natafiya kwanaki Suna Kara Yawa.Basma ce zaune. Ita da kawarta  munerrat  A dakin  Basma wadda  yasha yagyara. Munnert kecewa basma  Yanzu ki kyauta Kina tarrayya da Ahmed  Kuma Bikin da  Mahmoud kingi  1 weeks. Bazaki Sanardashiba Gaskiya bazaki Aureshi ba??

Basma taya tsina Fuska tace  dama Ai bamuyi yarjeniyaya dashi zau Aureshi  ba  ga ida Zan huta. Na hau motar danake so. Saina tsaya ma mai mota daya( 😊Rashin Sani) kyauttata da Ahmed bata wuce 10k zuwa 20k. Iyakarta takenan kiduba Mahmud Ko  A sandiyar kyautar dayakkeman  nabude Account yanzu Haka Ina  2 million ciki. Inbaki mantaba nafadamiki bazan taba Aure soyaya ba Aure Kudi Zanyi. Ahmed Kuma dama  nafadamasa mun tafiya  kauyen su Baba  kawai sai dai yaji Sanarwa. Suka kwashe da dariya. Munerrat  tace Amma baki kyautaba Kawata. Basma tace  Kinga tashi mushiga  Kasuwa Akwai Abinda  nakeson siya.

  *****************************************"**************   Bayan Sati daya

Dr Ahmed zaune dakinsa yanajin labarai yanata trying din number Basma  taki shiga domin yanason yasanar da itah cikin sati nan zai turo iyeyensa ( nufinshi inya fadamata gobe sai yasanar da daddy)

Anagama labarai kawai yaga Anhasko  wani hall da Da mutane ciki anata cashewa can aka hasko fuskar Amarya DA  Ango yaga kamar yasan fuskar Amarya Kamar sunsa Abinda ke ranshi  Aka Kara dallaro fuskar zata ba Angonta Cake A baki. Kawai yaga fuskar Basma  ya mike razane  yace karya ne Ba Basma danasi bace Basma bazata yaudareniba. Kawai yaji Ana wakar Bikin Amarya Basma da Angonta Mahmud sunyi Aure. Dr Ahmed yazauna ragwab!!! Bisa Gado  yace  Basma nizatayi makahaka nixata yaudara Amma bata  tabs nunaman ko Afuska ba .Amma babu komai Kanta ta cuta

Basai lokacin daya dauka yana  tunanin ba shigowar text  yaji  awayashi shine   yadauka yaduba yaga Basma ce. Tarutabamashi kamar haka

Aslm Ahmed dftn kana lafiya. Bawannan ba nasonka mutum  ne  mai Kallon  labarai  A kodayaushe. Kuma nasan zakaga wani Abu. Yabaka mamaki. Ba Abun mamakibane  Domin ba muyi  yarjejeniya dakai Zan Aureka. Inkuma   Kana  bukatar kudinka   tundaga wadda kabiyama   Inna Asibiti harzuwa yanzu zaka iya  zuwa  office din mijina  Mahmud kabir  Na kowa zaa biyaka bye bye.

Dr Ahmed yaja numfashi yagoge text din da number Basma baki daya
Daganan fa Dr Ahmed yatsani kowacce mace  Aranshi Domin tunanishi  duk haka suke( Anya kuwa)
 
Tofa shine Safeeya tafada ciwon so Dr Ahmed. Zata  cimmma burinta kuwa. Kuwa .???

Wane hali take yanzu A Asibiti ???

KUBIYONI...........

0 comments:

Post a Comment