Blogroll

BANNER 728X90

Thursday, 15 February 2018

CIWON SO Page 21-25 (The end)

CIWON SO Page 21-25 (The end)
.
Hajiya tanashigowa taga halin da Ahmed yake ciki fashewa tayi da kuka  tace Haffez dauko mota, mutafi Asibiti dasauri  ya fiddo mota,
Ya ciccibi Ahmed hajiya tashiga suka nufi Asibiti,

Suna shiga  Asibiti  Aka turo keken marar lafiya Aka dauki Dr Ahmed  Akashiga dashi
Hajiya da Hafeez sai zagaye suke hankalinsu tashe,

Kamar wajen minti 30

Doctor yafito Daga dakin daaksa Dr Ahmed  yace su same shi office,
               Bayan sun shiga sun zauna doctor yace ma hajiya Saudat kice mahaifiyar sa   tace Eh,
Shikadai gareni  doctor yakalli Hafeez, Kai kuma fa Hafeez yace Amininsa ne,

           36

Doctor yaja Numfashi yace gaskiya yana cikin damuwa sosai daf take ta taba zuciyarsa  Akwai. abinda yakeso, taredashi Asamomasa koma meye inbahakaba zai taba zuciyar sa Daganan kuma zuciyar na iya buguwa Ku rasashi,

Hajiya saudat tadafe Kai kome ta tuna tamike. Hafeez kaini gidan. Su safeeya inkasani

Hafeez yace safeeya tace Eh wadda Ahmed keso
Hafeez yace hajiya mezakiyo tace kaidai muje

Hafeez suka fito Daga office din doctor yaja mota suka nufi har unguwar su saffeyya,,

Har ciki suka shiga Hafeez yace tashiga yanan

Hajiya saudat tashiga tayi sallama. Meenat da umma suka Amsa ta domin sukadai ne zaune falo saffeya takoma yar cikin daki,

Suka Amsata  umma tace sannu ki shigo hajiya saudat tace yauwa tazauna bisa kujera

Umma tace Meenat tashi kidaukomata  ruwa,

Hajiya saudat tace A,a Alhmdlh,

Ummm tace saidai banganeba 
Hajiya saudat tace mahaifiyar Ahmed ce  Umma tace Ahmed  domin bata ganeba,

Hajiya saudat tace wadda keson safeeya

Dama Alfarma nazo nema wajenku don Allah kutaimaka kuba Ahmed Aure saffeya shikadai gareni  Aruyuwata,

Umma taja numfashi tace gashi kuma Abba nasu benan kuma ni babu Abinda Zan iya cewa

Kuma yatafi office dawowar sa sai dare,

Karar mota sukaji umma tace kamar motarshi, to meya msidosh mantuwa yayi ne,
Toro kofar Akayi tare da sallama hajiya Saudat suka Amsa,
Dagowar fuskar dazatayi

Tamike zumbur yaya sule!!!!!

Abban su safeeya Colin tsananin firgita yace  saude!!!!

.
Hajiya saudat Cikin tsaninin firgita tace yaya, sule!! Yace saude,
Kawai sai Hajiya saudat tafashe da kuka,

Umma Cikin mamaki take kallonsu  sunyi tsaye cirko cirko, Hajiya saudat Cikin kuka tace yaya sule dama kuna raye,
Kuka manta dani nashiga halin rayuwa,

Kullum tunanina haryazuwa yanzu inazanganku   Amma kunmantadani,

Cikin fushi tajuya zata fita,
Abba yace saude. Dawo don Allah zanfadamiki komai,

Cikii  kuka hajiys saudat tace mezaka fadaman yaya sule, kabarni natafi kawai nakarasa rayuwata haka tunda baka bukatata,

Cikin rararshin Abba yamaidota,
Daga waya yayi kawai yace kazo Nan gidana kaida matarka,

Kamar minti 10 Aka toro kyauren Akashigo,

Mustapha ne maihafin  Haidar tare da matarshi, sukashigo, 
Yayi sallama, yazauna kujerar  kusada Abbansu Saffeya, mustapha cikin,

Mamaki yace Yaya kace muzo yanzu  kuma nasan bayanzu kakedawo ba kace mutafo,

Abba yace kalli can yanuna bangaren da Hajiya saudat kezaune,

                  
                  Cikin  tsananin firgita mustapha cikin rawar murya yace saude... Tace yaya mustapha yace kece tace nice yaya mustapha, ba gizo idanuwanka sukemakaba,

Hajiya saudat ta mike dasauri domin sai yanzu tano dabaro Hafeez  zaune cikin mota,

Abba lafiya saude kika mike ne
Tace wadda yakawoni  ne namanta wallahi Kuma  Ga Ahmed kwance Asibiti,

Abba yace tokutashi mutafi Asibitin  mana domin bayari saude takara sakemashi,
Nan da umma sai Abba, sai kuma kawu mustapha da matarshi hajiya murja,suka tashi suka runguma sai Asibiti,

Duk Abinnan daake Meenat da safeeya basu saniba  domin Meenat Hajiya saude nazuwa tabar falon,

Tashiga ciki,

Tashin motocin kaawai sukaji taleko ta Meenat ta leko ta Window saitaga kawu mustapha da umma sai mamyn su Haidar sunshiga mota,

Saiwanna bakuwar tatazo tashiga itama,

Anbudemasu Gate sunfita,
Meenat meke faruwa ne,

Batada Amsar wannnan tambaya kawaintasaki labule. Takoma tazauna tana saureren dawowar su,

Abba sun isa Asibiti suka fito suka nufi dakin daaka kwantar da Dr Ahmed
Suka iskeshi har yanzu bacci yakeyi,
  Saiga Doctor yashigo yayi salllama domin yashigone yakara duba jikin. Dr Ahmed kowa yafarka,

Nan yadubashi yace karsu damu nan da one  hour sai farka insha Allah,
Sukace Allah yakaimu

Shikama Hafeez mamaki yake mail yahada Hajiyarsu Ahmed da iyayen safeeya, harsuka tafo tare Asibiti,
                  39
Bayan hour 1dakamar minti 10

Dr Ahmed ne yafara bude idonsa yaganshi bisa Gadon Asibiti sai yatunano Abinda yafaru dashi  bayan yagama bawa Hafeez labarin Abinda yafaru,

Yakara bude idonsa sai yaga Hajiya sa tare wasu baki yana Kara waiwaya yaga maihafin safeeya dakuma kingin bakuwar fuskokin dabasai kowaye ba,

Hajiya saudat tamatso wajen sa da sauri Ahmed kafarka yace nafarka Hajiya tace yanzu inayake maka ciwo yace zuciyata ke ciwo Amma basoisaba  tace zatabari Ahmed insha Allah,

Tace Ahmed  yau kukana yakare naga,yayyena, kaganasu,
Yaya sule, da yaya mustapha,
Tanuna maisu,

               
BAYAN KWANA BIYU
.
DR Ahmed yaji sauki Alhmadullah, yayima hajiya Alkawalinan bazai sake kara sama Kanshi damuwa,

Falon  su safeeya ne Abba, kawu mustapha, umma,Hajiya saudat  Hajiya murja,  Haidar,  Dr Ahmed,
Saffeya, Meenat,

Abba yayi gyaran murya yace Alhmdullah Allah mungodemaka  Allah shine Abingodiya, A kodayaushe,
Dayahadamu da kanwarmu, Wato saude, bayan dadewar damukayi bamu haduba,
Sai kwannan datazo nan gidan Akan tana Neman Alfarma Akan Aba Ahmed danta Aure saffeya, dasauri safeeya tadago fuskarta jin wannan batun jin Dr Ahmed dan uwanta ne,

Abba yace kafinan kowa zaishiga duhun jin nace saude kanwarmu ce ko  nida mustapha to saude kanwarmuce uwadaya ubadaya Daganan yabasu labari daga farko, har barowarsu kauye

                    41
            TUNA BAYA

Abba yadora yace bayan Baba yakawo makaranta bekara waiwayrmu.
Gashin malamin Azzulumine inkaje bara kadawo kasamo Abinchi kwacewa yake,
Dahaka mukai tahakuri domin bamu da makwancin kwana sainanan
Anahaka nida mustapha muka Fara shiga kasuwar central market munadago muna samun Abinchi dazamuchi muka daina bara, 
Damunyi dako munchi Abinchi lokacin tashi yayi sai mutafi makaranatar da Akawomu, mu kwanta daan tashi dasafe munyi karatu, Antashi ma karanta sai mutafi, cikin kasuwa, ko makarantar marece daake zama bamu zuwa, Amma malamin besaniba domin shi babu ruwanshi,

Anahaka wata Rana nadauko ma wani  Alhaji kaya,   shinkanfa  yabude boot domin nasakamashi,

Ashe ya fiddo wata jakka baka.

Ya aje bayan nasa masa shinkafa yarufe boot din. Ban luraba  sai daya tada naga jikka Aje  nadauka nabishi Dagudu inbashi domim ya manta Amma nakasa cimmashi,

Nadauki jikka nan na nufi wajen mustapha nace mustapha kaga Alhajin danayima dako  yamanta jikkashi,

Mustapha ya Amsa yace mugani mustapha yana Amsa yabuda yagani yana budawa yaga dame dame kudi  yace yaya sule!!! Kudi ne ciki,

Naduba naga  kudine ciki nace rufe mustapha, nace taso muje,

Nan najashi muka nausa canciki inda babu mutane kuma nagaka babu mai hangenmu nayi rami na rufe jikkanan,

Kullum rokonake Allah yahadani dawannan mutumin.

              42

Kwatsam rannan ina yawo cikin kasuwa naga wannan mutumin yashiga wani shago naji rash har yafito, nabishi daga baya nace Alhaji,  yawaigo dominshi har yamanta dana taba daukarmasa kaya, yace yaakayi yaro nacemasa Alhaji kamantani ne,
Nine wadda yataba daukar maka shinkafaa har kamanta wata jikka,

Dasauri , hannu na cikin murna yace nataono yaro nacemasa muje nadaukomaka muka nufi har inda na binne jikka, nabashi,

Yabuda yaga kudin yadda suke haka suke, yarufe yace Alhmdlh nagode nagode. Yaro naji dadi,

Yasunanka nace masa sule yace suleman nagode, yace dan wane Gari nacemasa rimi, yace Kai daya ne nace nida kanena ne,

Daganan Alhaji Muhammad yafara taimakonmu nida mustapha, yabudeman shago cikin kasuwar central  market  muna saida Atamfofi,
Alhmdlh muna samu dganan Har Alhaji Muhammad yabanj jari  nakaina Aruyuwata bazan taba mantashi,
Dagannan nace mustapha yafara zuwa makanta yabarni shagon 
Daganan akayimasa cukun cukun takardun primary kawai yatafi secondary,
Yanabarina shago nikuma,

Munata sanaarmu cikin rufin Asiri, har yakammalaa
Yatafi FCE can suaka hadu da murja suka Fara soyaya ,
Akace yaturo iyeyensa Alhaji Muhammad yayi mana tsaye har Akayi bikinsa,

Nan muka yanke shawarar tafiya dauko saude  munje mun isa lafiya Amma bamu Bari kowa yasan dazuwanmu ba sai Abokina Ilu nan yake gayaman bayan tafiyarmu Anyi bikin  saude da Iro,
Subar garimamn
Nan ranmu yabaci kowajen maifinmu bamuje ba domin munsa bamu gabanshi Azzulumar matarshi tarabamu dashi,

Saidai mustapha yayi shekara 5 da Aure sannan nayi na Auri Khadeeja sannan An haifi haidar yana shekara 4 tanazuwa sayayea shagona,

Nanma Alhaji Muhammad yayimani  tsaye akayi bikina  Aruyuwata bazan manta Alhaji Muhammad ba Allah yajinkanshi,

Khadeeja haihuwarta na farko ta haifi hassana da hussaina, wato saffeya da Ameena,
Daganan haihuwarta ta tsaysmata, shima mustapha haka,

Daganan muka bude company mustapha yana zuwa kasashen waje sari,

                 43

Muka sayi fili muka gina gidajennan nida mustapha,
Tuntashi safeeya da Haidar suka shaku dgaann mukayi Alkawrin hadasu Aure,
  Falon kowa yayi shiru kakeji,
  Daganan Hajiya saudat ta Dora itama harysxuwa yanzu,
Dr Ahmed halin dayashiga
Sanadiyyar safeeya,
Dr Ahmed yace hajiya  bantari Numfashi kiba tunda  haka Akayi Abba sunyi Alkawsrin Sure hada Aure  itada  Haidar Nina Hakura kidaina  tunanin haka insha Allah Zan cire damuwa ,
Inayimusu fatan Alkairi,
Ya mike yafita, daga falo
Domin wani Abu yaji ynaamasa ciwo,
        

  
              44

Safeeya itama tashi tayi tashige daki tana Kuka,

Tofa Rana bata karya  yau daurin Auren safeeya.

Hajiya saudat tashigo  daki ta iskeshi kwance tace  Ahmed bazakaje daurin Auren ba  kuma kace kafidda damuwar komai,

Yace Hajiya namanta  ne Bari natashi natafi,
Tace yauwa dan Albarka,

Dr Ahmed yatashi  yashiga toilet ya shirya bayan yashirya yakira Hafeez yace suzo suje sauri Auren saffeya,
Bayan ya I so suka nufi masallachi  unguwar su safeeya inda   Ake daurin Auren,

Suka iske Anfara taruwa  Ana niyyar daurawa,

Dr Ahmed kasa daurewa yayi, yafito daga masallachi nin
Yanufi baya yazauna kasa sai Kuka share share Hafeez yaga fitar yaviyo bayanshi yana  rarrshin sanarwa daakayi cikin lasifika!! Shine ya tsaida numfashi Dr Ahmed cak!!!

Cak numfashi Dr Ahmed yatsaya jin Abinda me lasifika yace.

Andaura Aure. Safeeya suleman tare da Angonta Ahmed Ibrahim, Akan sadaki, 50k

Zumbur Ahmed yamike Hafeez  ma cikin kidemawa, yace Ahmed kaji Abinda  naji Dr Ahmed yace nadauka nikadai nace nazauce Akan saffeya,

Hafeez yace taso muje, ko mantuwa marokin yayi ne,

Dr Ahmed  yakkabe rigarshi suka nufi wajen daurin Auren,

Suna fitowa nan Dr Ahmed yaga dangin maihafinshi,

Yaga har da Abonkasa wadda suke koyawa  A ummaru musa university,
Sun nufoshi sunata yimasa Allah sa Alkairi,
Dr Ahmed Binsu kawai yake da ido domin tsabar rudewa,

Haidar yaga yanufo wurin shi, yaya Ahmed inayi maka fatan Alkairi Allah yabaku zaman,
Ahmed besan lokacin da wasu hawaye suka zubomasa saboda ya fidda rai daga zai Auri saffeya,

Haffez yace Kuka kuma Abokina,

"Dr Ahmed yace na murna ne,Abokina, bantaba tunanin Aure saffeya tare daniba tuni " nafiida, rai daga hakan

Abangaren safeeya Kuwa,  Agogo ta kalla taga 11:30 Am
Fashewa tayi da Kuka tace yanzu harnazama matar Haidar ba Dr Ahmed ba,

Wayyo ni Allah, na
Meenat dake gefenta tace sai kitashi kinsan Aikin gama yagama, yanzu kinzama matar Wani sai kifidda, shi daga cikin ranki,

Gidan kawu mustapha falonshi Abba ne tare da   Hajiya saudat sai haidar sai Ahmed,
Abba yace zakaji Abu kamar mafarki ko Ahmed,
Jin Andaura Aurenka da saffeya ba daura Mata da   Haidar,ba

Abinda yafarune kingi kwana biyu Adaura Auren Haidar yasameni Akan yanason Afasa dashi Adaura dakai,
Tunda kaima nagidane kuma safeeya tafi sonka,
Naki yarda da hakan kawai sai yafasheman da Kuka sai Na Aminche,

' nadauki waya kawai nakira mustapha nace yazo inasan ganinshi yazo nacema haidar ya maimaita Abinda yace yakuma maimaita,
Nace meyasa yake fadin haka, yace saboda ya Lura safeeya tana matukar kaunarka kaima kanasonta,

Kuma  duk Abinda kaso ma dan uwakan musulmi ladanka yana wajen Allah, shiyayi jihadi yabarma Ka safeeya, shikuma Allah yazabamasa mafi Alkairi,
Amma yace kar Afadimaka sai kaje daurin Auren saikaji,
Kaji yadda Akayi,

Dr Ahmed yajuyo wajen hajiya Saudat yakalleta, tace Hakane Ahmed Andaura Aurenka da safeeya, ance Karna fadamaka, kuma Anyi sanarwa gidan radio kaine bakajin radion da kuma Karin kana cikin damuwa,shiyasa babu Abinda zakacema haidar sai godiya,
Dr Ahmed yajuyo wajen  Haidar ya rungumeshi nagode nagode. Dan uwana Allah yabar zumunchi, kawai yafashe da Kuka, Haidar yace babu komai yaya Ahmed, karka damu.

Saffeyya kuma sai fama Ake da ita tatashi tayi wanka Amma tace  bazatayi ba
Umma ce tashigo dakin fusace waike wane irin yariyane, wallahi Zan daka miki shegen duka  yanzu koki tashi kishirya, yanzu,  tashi  kishiga toilet din gabana,
Safeeya cikin Kuka tatashi ta shiga toilet tayi wanka tafito,

Meenat tahau shiryata itada wasu friends dinsu wadda sukazo tasa wani coddles, pink And pupurle,

Masha Allah  Allah Abin godiya safeeya tayi kyau,

Nan wata kanwar mamansu taja xuwa. Dakin Abba domin bakwana suka iske umma da Abba zaune  Auntysadeeya. Kanwar umma tace ga safeeya,
Nan tazo muku bakwana,
Abba yayi gyaraa murya yace safeeya tace Na' am Abba cikin sheshekar Kuka,
Yace Aure ibadane da dukkan wata ya mace

Kiyima mujinki biyayah saidai iyawarki inayi Bari nabari Aljanarki tana karkashinsa,
Komai yace kibari kibari
Nan Umma tadora tata itama
Bayan sungama Abba Allah  yabda sa'ar shiga gidan muji.

Aunty sadeeya taakmo hannuta domin motici sun Akejira,

Safeeya tajirce ita batazuwa Akyaleta wajen ummata sai kuka,
Umma itama daurewa kawai tayi,dakayar Akafita da safeeya.
Bayam sunfita Abba kefadama umma da Dr Ahmed Akadaura bada haidar, yafada duk yadda Akayi, umma tayi mamaki Amma tace Ikon Allah kenan.

Bayan Akai safeeya gidanta dake Dutsin safe low cost,
Bayyana kyau gidan yayi kadan na bayyanashi cikin yar mitsitsiyae wayata,
Amma nabaku Gari,

Dakyar Aka banbare Meenat da saffeya Daga jikin juna domin safeeya tace babu inda zata, tabarmata,
Dakyar Aka kwaceta,

Kowa yatafi   yabar safeeya  ita kadai, sai kuka take,

Ahmed kuma sai zanzarar Hafeez yake yazo yakaishi  gidanshi yake. Shikuma yana ta tsokanarshi,

Dakayar yajashi suka tafi..

Safeeya tanajin karar mota. Dasauri tatashi ta kulle  dakin  takoma ta kwanta domin kosan ganin  Haidar din( Anufinta ba haidar Aka daura Mata Aure dashi,
 

Tafashe dakuka yanzu nazama matar Haidar ba Dr Ahmed,

Nantayi sauri istigafari domin tace Astagafurallah,

Allah yafeman na Ambaci wani  dakuma Aure bisa kaina,

Tadora pillow bisa kunneta domin karma ya isheta da hayaniya

Shikam Dr Ahmed Suna shigowa dakin safeeya yazarce  Amma me sai ya iskeshi kulle,
Murmushi kawai yayi yadawo wajen Hafeez dake  falo yazauna,
Yace Abokina kaga ta kulle kofar tadauka Haidar domin.
Haryanxu baasanarmata dakowa Aka daura Auren ba,
Hafeez yace yanzu yazakayi to???

Dr Ahmed yace kyaleta nima zankyaleta kamar 1 week sannan na bayyana Mata kaina,

Hafeez yayi murmushi yace shikenan nibari natafi ko 
Yarako sa har Bakin Get,
Sannan yakoma ciki yashuri ledar dayashigo da ita yanufi dakinsa,

Itakama haka tayi bacci kudundune Kamar  wadda zaasace,

Kiran sallar Asuba yatadata  domin Akwai masallachi kusada dasu,

Anatada sallah tatashi tayo Alwalla,

Lokacin datake Alwalla shima yatashi domin tafiya masallachi,
Yaji motsin ruwa, yasan tatashi shima masallachi yanufa kawai,

     
Bayan ta idar da sallah ne komatayi ta kwanta, bacci yakomata sabo,

Bata farka ba sai wajen 11 am
Tana farkawa taga 11 tayi    dasauri taduro Daga bisa gado, tace wai nadade Ina bacci Ashe,

Tanufi toilet tayi brush, 

Tanufi Hanyar waje domin gano kitchen domin Cikinta yafara kiran,

Ciroma,tea kawai tahada mai kauri  tadawo  falo tazauana,

Hango wata fara takarda tayi Bisa  table din tsakiyar falo din tadauko ta tabuda taga,Antubuta,

```My``` ```Wife``` ```Good``` ```Morning ```

```nadan``````Fita``` ```Sorry ``````Luv``````you

     

Tsoki  saffeya kawai tayi tace Kama ka dawo bana raayin ganinka Kama,

Nan tagama Abinda zatayi tashigewarwata daki domin bata raayin kallon fuskarshima, nace uhumm safeeya duk A cikin rashin Sani ne,

Shikam Dr Ahmed yana dawowa Daga massalaci shima yadan kwanta,

Wajen Goma yafarka yatafi wajen Hafeez inda yasauka,

           

Abuna yanata tafiya safeeya batasan haryanzu  Dr Ahmed ne mijinta kuma Suna waya Dr Meenat lafiya lau, bata taba sanar da itah
Domin Dr Ahmed yacema Meenat kartasake tafadamata shine mijinta hartaganshin takanta,

Yau safeeya tatashi cikin murna domin sunyi waya da Meenat jiya yau tanan tafe, 

Tashi tayi taga Akwai Abinda zatayimata,
Tanufi kitchen,
Tabuda firji taga Akwai kaza da naman rago,
Kaza kawai tadauka zatayi Mata farfesunta,
Bayan tagama tayimata jallof rice taji kayan hadi sai  tashin Kamshi take,
Tahadamata juice pine apple And coconut
Tahadasu bisa table A  tanufi dakinta dominntayi. Wanka kafin taiso

Bayan tagama wanka tafito tayi sallar Azahar domin lokacin yayi tagama tanufi  mirror domin shiryawa
Tanagamawa, tafiido wani paper lace blue And yellow kyau da saffeya tayi baa magana,
Tafito falo domin jiran Meenat bada jimawaba saigata tashigo suka rungume juna cikin murna,
Nan safeeya taje suje  falo domin cin Abinchi data girka mata,

Suna zaune falo Suna firar su ta zumunchi,
Toro kyauren Akayi tare da sallama,
Saffeya tadago daga cin Abinchi datake tadago fuskarta kawai taga Dr Ahmed A razane Abinchi datake yadawo.....

Kinaganin  Abinda nake gani kodai idanuwana sufara Gizone soyaya zata Sani Hauka Dr Ahmed yanayimana Gizo, tafara kuka,   Meenat tataso Daga inda  take tadafata tace sister Dr Ahmed bagizo yakemakiba shine mijinki wadda Aka daura muku Aure dashi, saffeya tace bafa Haukacewa nayi ba. Sister da  bacin da  yaya haidar  Aka daura shine yanzu zaki fadaman Dr Ahmed aka daura Aure na,

_Meenat_ _tayi_ _Dariya_  _tace_ _wallahi_ _tallahi_  _sister_ _Dr_ _Ahmed_ _Shine_ _mijinki_  _wadda_ _Aka_ _Daura_ _muku_ _Aure_ _dashi_
.
Taso muje kiji yadda Akayi.
Shikam Dr Ahmed yayi tsaye bakin kofa sai murmushi yake,

Meenat tajawo hannu saffeya tace yadda Abu yafaru, Kuwa,tagayamata duk yadda Akayi, tana gamawa
Safeeya tafashe dakuka tatashi dagudu tashige daki,
Tafada bisa gado.

Dr Ahmed yacema Meenat Bari nabita Meenat tasabi  jikka da gyalenta tace nayi nan yaya Ahmed,
Sai Anjimanku

.  dr Ahmedyatura kofar dakin saffeya yahau bisa gadon datake,
Yace safeeya!! Amma taki dagowa sai Kuka take,
Yasa Hannu sa yajawo tafafa bisa jikinsa saffeya kukan mekeke kedayakamata kiyi murna kiyi farinciki Amma bazaki ta Kuka Haba my  heart beat pls Adaina kukan nahakanan,
Mugodema Allah daya cikamana burinmu, munzama mata da miji  nidake,
Cikin Ajiyar zuciya safeeya tayi  kamar yarinyar Goyo cikin shagwaba tace to meyasa Baa fadaman tun Ranar ba,
Dr Ahmed yace ninace kar asanardake, sainashigo kuma nashigo Ranar na iske ki kulle kofa nikuma nace sai nakara janki bazan bayyana Hakan garekiba  sai yau, sai gashi kuma nayi sa' a Meenat tazo kinfito falo, kuna zaune,
Safeeya Kara tura kanta tayi kirjin Dr Ahmed Ahmed shima Dr Ahmed yakara rungumeta Kamar zaa kwace ta ganin zai wuce  Gona da iri safeeya tace kai sir munbar sister A falo fa,
Dr Ahmed yace tatafi Ai,
Cikin shwagaba tahau dirara kafufuwa. Meyasa tatafi bata fadamata ba,

Dr Ahmed yajawota zokiji wata magana tafaada bisa jikinsa,

Daganan bacci yadaukesu Har zuwa wajen la' asar suka farka sukayi sallah tare,

Can nahango saffeya tare da Ahmed suna girki,  Acikin kitchen, Ana girki Ana love,

Bayan sungama suka zubo cikin plate daya wannnan yaba wannanan harsukaa gama,

Lokacin sallar magariba tayi Dr Ahmed yanufi masallachi yacema safeeya zai Kai isha' I zai je wajen  Hafeez,
Safeeya bayanan ta idar da sallah tashiga ta silalo wani wanka,

Tazauna gaban mirror tadinga lindar jiki Kamar zata canja fata,

Tana cikin lindar jiki tatashi ta maida isha' I

Tagama tadawo saida tafi minti 30 tana lindar fuska sannan, tatashi tajawo  wata Atamfa   pink And blue tasa,masha Allah saffeya tayi kyau,

Tadawo falo tazauna tajiran Hasken kalbinta,

Batayi minti goma dazama sai gashi yadawo tanajin horn din motar takara gyara zama, can ya shigo,
Yace wow Masha Allah my heart beat kinyi  kyauyabata kiss Akumatu. Yazauna kusada ita suka kalli labarai

   

Karfe Tara nayi yakashe kallon yace suje daki lokacin bacci yayi yasabi saffeya kamar jariyaya,suka nufi dakinshi,

Yana direta yace inazuwa yafita minti kadan yadawo da plate da bakar Leda yacemata My princess taso muci ko ya fiddo wata dankwaleliyar kaxa
Yayagi cinya yasakama saffeya baki nan dai suka ci kadan suka tashi,
Saffeya tamike tace Sir sai dasafe kada Kai kawai yace OK night,

Safeeya tanufi dakinta,  tacire kayanta na bacci

Tahaye Gado tayi Addu' a kwanciya bacci  can bacci yafara daukata taji An kunna lantarki Amma bata motsaba can taji Ance safeeya  cikin Almun bacci tafarka Taga Dr Ahmed tsaye,
Yace tashi muyi sallah  cikin bacci tace nayi sallah nifa, yace bawannan wadda ma'aurata keyi,
Tashi nida Alwallata tashi kiyo taki inajaranki
Safeeya tadiro daga bisa Gado tanufi kewayen tayo Alwalla,

Tafito suka tadda sallah bayan sungama sukayi Addu' Allah yabasu zaman  safeeya nahar Abada
Dr Ahmed Yayi ma safeeya wasu tambayoyi yaji  ta Amsa masa,
Nan tafaera gamma tace
Sir nafara jin bacci yace OK babu matsala mu kwanta  KO, face nan zaka kwana ne yace Eh, kokar nakwana  
Dakin matata face A a nidai Vance ba yajawo musu bargo suka lullube, can Dr Ahmed ya rungume  safeeya yafara, kiss  Daganan komai
Yacanza
Nima Daganan najawo musu kyaure nafito  Falo
Can nafara gyangyadi  Naji karar saffeya firgice natashi nanufi  dakin  saffeya,
Amma magen dasuke kiwo ita tamaidoni kusunssani   da tsoron mage sosai
Shiyasa suka a

jeta
 

Dagudu nadawo falo  nahaye kujera  can nakarajin ihun safeeya tana kiran  Umma da Meenat, Har Abba  nidai  babu halin ceto domin ganin magenan

Tun inajin kuka safeeya har bacci yadaukeni ceke da tsoron mage☹☹

Washe Gari

Safeeya ce tasauko Gado Anhakali domin wani zafi datakeji tanufi toilet domin hada ruwan dumi tayi wanka

Dr Ahmed yana lalubawa  yaji ba  safeeya sai yasaurara  yaji karar ruwa toilet dasauri yasakko yanufi toilet zanbishi ya wurgma man harara nadawo da sauri na nufi falo,
Can naji dariyarsu  firgit nafarka naga wai harsun shirya sunfito,
Falo Dr Ahmed yaja Hannu safeeya suka  zauna  mezakici my dear cikin shawgaba tace  tea kadai Zan sha,yace    Angma ranki yadade,
.
Soyaya tsakanin safeeya da Dr Ahmed sai Abinda yakaru suke.kowa yasan yafaranta makowa,

Yauma zaune take tanajiranshi falo zasuje gida  zasuje rimi kauyen su Abbansu wato rimi,
Duka zasu tafi,

Bayanan Dr Ahmed yashirya suka runguduma suka tafi Gidan su saffeyya domin can zaahadu,

Suna xuwa suka iske harsu Abba sun shirya, kawai suma mota, suka koma,

Safeeya gaba sai Dr Ahmed dake Jan mota sai Meenat da Haidar baya,
Can  kuma motar guda
Umma sai Abba sai kawu mustapha da mamy,
Sai Hajiya saudat,

Nan suka runguda sai rimi
Minti talatin yakaisu har kofar gidansu Abba,
Suka rufe mota,suka shiga shiga,
Har ciki suka iske wata tsohuwa zaune makauniya, zaure da sauri Abba yace Inna, cikin laluba tace waye   yace sule ne, tare da mustapha da saude

Cikin firgita tace sule Ashe kuna Raye,Abba yace munan da ranmu, Ade tafashe da kuka kuyafeni nayi kukskuren Arayuwata
Allah yajikan malam inama da ranshi
Abba yace Baba yarasu tace  tace Allah Yayi masa rasuwa Asanadiyar hawan jini bayan Asirin danayimashi yakare yafara tunaniku dgn yakamu da cuta har mutu yana maganar Ku,
Nikuma dama bokace duk Randa yamutu Zan makance,
Abba sukace Allah yajikan Baba yayimashi Rahma,
Cikin kuka Ade tace Ameen nacuci kaina,
Nan Abba yadubi Gidan yadda yaruguje yalalace, nan yace dayadawo sai dawo da magina daga katsina domin su gyara gidann

Bayan wata shida

Dr Ahmed shida safeeya sunfito daga Asibiti yakai safeeya Awon cikinta dan wata biyar,
Kawai yaga wata Mata tatsreshi bawan Allah Ataimakaman da sadaqar Abinda  Zan siyi magani
Dr Ahmed yazaro nari biyar ybata  cikin kyarma ta Amsa  nagode yace babu damuwa
Wadda yaba sadaqar cikin  rawar murya tace  Ahmed...
Yadawo yace vaiwar Allah inakikasanni,
Tace Basma!! Ce
Dr Ahmed yace Basma badai wadda nasaniba tace itace kayafeman Ahmed nayaudareka Arayuwa saboda kwadayi,
Gashi babu inda yakaini Ashe Mahmud manemin Mata dan Giya,

Bayan Auren mu dashi da shekara biyu ya kwanta ciwo Aka kaishi Asibiti Ashe cutar Aids gareshi badaidai Asibiti ya mutu  nima Aka Aunani Akaga inadata
Daganan komai nawa yakare gashi bahaihudashi balle nassmu gadonshi, shine nake fitowa nakesamun na magani,
Dr Ahmed ya girgiza  kawai yace Allah sawakka yaja Hannun saffeya sukabar wajen,

Bayan wata ukku

Safeeya naga tatafo falo da katon ciki rikeda da apple A Hannu Amma tayi tayi taka kafarta taki takuwa dasauri tafara  kwadama Dr Ahmed Kira, honey
Dasauri Dr Ahmed yafito daga dakin yana ganin halin datake yacuccibeta kamar jariyaya  sai mota  yasata yadawo yadauki Akwatin dasuke  sa kayan baby
Sai Asibiti dakin haihuwa da sauri Aka  Amshi safeeya  sai daki haihuwa,
Dr Ahmed yna zarya can yaji kukan jaririya saiga  nurse tafito tace inatayka murna Ansamu baby girl Dr Ahmed cikin murna yace Alhmdlh

Yadauki waya yakira hajeeya saudat  da Umma
Nandanan suka zo

Bayan Angyara jaririya da mahaifiyar ta Akabasu sallama,
Babu inda Aka zarce sai Gidan saffeya Hajiya saudat tace zata zauna ta kula da diyarta

Agurguje

Ranar Suna

Anyi suna Alhmdlh taron suna yakayatr dakowa
Diya taci sunan  Hajiya saudat Amma zaadinga kiranta   Bunayya
Nan Meenat kesanaer DA saffeya sun daidaita  da yaya Haidar
Dasun dawo bautar kasa zaayi bikin  dayake kingin sati biyu tafiyar Amma Dr Ahmed yace   zaayi yadda sukayitasu  cikin garinsu,

Haffez shima Yayi Auren yanazaune kusada DA Dr Ahmed

Dr Ahmed ya shigo dakin safeeya ya iske Bunayya sai kuka take  safeeya tana rarshinta dasauri yce meakayimatane safeeya tace rigima Dr Ahmed ya Am she ta yarungume yajawo saffeya yarungume yace  I luv you my mu wife tace iluv you my husband

Alhmdullah Anan nakawo karshen CIWON SO  SAI ATARENI A SABON LITTAFINA ..

0 comments:

Post a Comment