Blogroll

BANNER 728X90

Tuesday, 6 February 2018

'Yar Talakawa Part 6 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI


'YAR TALAKAWA Part 6
.
Ta ware manyan manyan idanunta, kirjin ta kuwa kamar zai bullo, fitsari kawai ya rage tayi, a tunanin ta barawo ne ya shigo musu gidan.
Prince ya jawo hannun ta da karfi, sukayi tafiya har wurin da kawai haske.
   Neena kuwa sai bin sa kawai take, gashi ya juya mata baya, bata gane ko wanene ba.
     Har sai da suka iso bangon kusa da kicin din mum, ya sake jawo ta ta dawo gaban sa, ya jinginar da ita da bango kamar dazun.
     Sai lokacin neena ta ganshi, amma har lokacin a tsorace take, mai ya prince keyi anan?
      Bata idasa tambayar kan  taba, taji yace da silent voice dinshi, ina kikaje?
Yayi maganar yana daure fuska, neena tayi blinking(kyafta) idonta sau biyu, ta nuna kanta da yatsan ta, Ni?
Prince yace a'a ni, neena ta hadiye yawu da kyal, gaba daya ya dawo mata prince dinshi.
    Yayi two steps, sai gashi dab da ita, bude kofar sukaji za'ayi , yayaB ce, ta fito rubar da ruwan zafin data gama kasa kafarta..ai ni zubaida kada ma kimin magana, har nace miki kizo ki kasan kafa, ki wani turo dan bakin ki kamar biro, dan kina amsa waya ko.....
   YayaB na maganar ne tana shirin fitowarta....kuma dole ne idan ta fito ta gansu.
Prince ya rike hannun neena, ya fisgota sukayi baya sosai, ga wurin yayi duhu sosai, ya jingina da bango, sannan ya jawo ta jikin sa, neena ta kware baki, dan yayaB taji ta, ta taimaka mata, a zaton ta prince sai ya bata punishment din dawowar dare da tayi, dan ta taba jin su zarah da zuby na fadin, idan sukayi dare ya prince na cin uban su.
.
Prince ya daure fuska yayi saurin rufe mata baki, ya sa dayan hannunsa a lips dinsa, meaning tayi masa shiru
Gaba daya ta kasa sukuni, sai neman kwace wa takeyi, prince yayi dan tsaki, ganin yarinyar zata tona shi, gashi wannan yayaB din surutu kamar radio. .yasan ta gansu, kowa ma sai yaji a gidan...
   Ya sake janyota sosai, har suna jin lumfashin juna, hancinsu na gogar na juna, idanunsu na kallon juna, take neena ta nutsu, dan wani irin kyau da kwarjini da prince yayi mata..
   Shima prince dai kawai controlling kansa yake, ya kasa dauke idonsa daga kallon cute face din neena, (shes darm a pretty dude) zuciyar prince ta fada masa... (ni kuwa afrah dake tsaye ina kallon ikon Allah,, nace make I play aashiqui song 4 dem"sunn raha hai" lolz).
Sai da sukayi minti 10 a haka , sannan sukaji rufe kofar yayaB, lock lock ta saka key ta rufe gaba daya tana cewa, sai ayi ta barin kofar nan a bude, bacin kowa na ciki mtsw, ta fice daga kicin din tana kashe wutar kicin din....
.
Neena ta fisge da karfi, daga rikon da prince yayi mata, tayi saurin karasawa wurin kofar tana bubbugawa, ta leka ta window tana kiran sunan zuby! YayaB! Amir! Mum!... amma shiru ba wanda yasan ma tanayi....
   Kamar zatayi kuka, ta saki kayan hanunta, tayi tsaye hawaye na fita, wayyo yau a waje zata kwana kenan?
Gashi bata da waya a hannunta, wanda ya sadeeq ya bata kuma ba caji bare simcard...
Prince kuwa tsaye yayi, sai data gama nata rakin , sannan yazo, ya murda yaji gam, yaja tsaki, ya leka windows yaga an ma rufe kofar kicin din, yazo wurin neena.
   Yace, ya zamuyi kenan? Neena kamar ta shake shi, duka bashi ya jawo ba, da yanzu tana daki abunta, ta rufa da bargonta mai laushi, dan sanyin wajen nan yayi yawa, gashi bata son sanyi...
    Bata san ma hararar prince takeyi ba, tana tunanin nan, shi kuwa, burge shi ma ta kara yi...har taso ta basa dariya, yadda duk ta wani shagwabe fuska, zata kuka..
Neena tace ya prince ka kira zuby please, prince yace gud idea, ya saka hannun sa cikin aljinu, yaji wayam...
  Neena ta kura masa ido, tace badai ka manta wayan a ciki ba?? Kamar zata fashe da kuka tayi maganar...
     Prince ya kada mata kai, neena ta kwashi kayan ledojin ta, bari naje sashen mami na duba ko basu kulle ba...
   Ta tafi da sauri, prince ya saka hannunsa a aljihu ya koma , wurin rumfar garden , ya zauna.
.
Neena taje taga sun rufe suma, kamar ta fasa ihu, ta sake dawowa, ta hango prince a zaune abunsa, mtsw shi bai ma ko damu ba, dan yana da jacket dinshi zata rage masa jin sanyin nan, ni fa, ta kalli jikinta...
   Gown ta saka, mai guntun hannu, sai gyele bamai kauri bane sosai, ko dan kwali bata daura bama, tana zangin zuwa wurin yaya habu...
  
A sanyaye tazo ta zauna itama, prince ya jinginar da kanshi a kujera ya lumshe idon shi.
Neena tasa gyelen ta, ta rufe jikin ta, still tana danjin sanyin, ta takure sosai...
     Sai data dauki minti sha biyar a haka, duk tsoro takeji, amma tana kallon prince taji she's save, tunda yana kusa, tayi murmushi , sannan tasa kanta a table, barci yadan dauke ta...
    Prince ya bude idonsa a hankali,
  Ya taso yazo wurin ta, gashin ta yadan sauko a fuskarta, sai barcin ta takeyi, amma a takure da gani dai tana jin sanyi..
    Prince ya cire jacket dinshi, ya rufe mata jiki, sannan ya jawo kujera, ya zauna dab da ita, ya sa hannun sa, yadan janye mata gashin daga fuskarta, ya kura mata ido, tun daga idanunta, gashin idonta masu tsayi, zuwa hancinta, medium, yayi fitting din fuskarta, zuwa cute pink lips dinta, suma sunyi daidai da fuskarta.
Prince yakai hannunsa ya shafi lips dinta, take ya sauke ajiyar zuciya...
      Ya mike kadan, ya sumbaceta a goshin ta, a hankali ya motsa bakin sa.
       Zai furta.......
Fans na bar muku amsar abunda prince zai furta....
Lols sai naji guesses dinku zanci muku gaba
Love u all muah....
.
Sai daya lumshe ido ya bude ahankali _yace_ ji yadda take barci so soundly a waje, is she dat careless?  yayi murmushi ya shafi gefen fuskarta,yace   sleeping beauty. ..
Ya matso da kujera, ya zauna dab da ita, ya kwantar da kansa yana facing din fuskar neena sosai ya jawo hannun ta ya rige gam, kamar wani zai kwace masa ita, yana ta kallon ta, har barci ya dauke sa...
Neena tajibwuyanta ya fara mata ciwo, ta bude ido a hankali sai ganin prince tayi dab da ita, ta ware ido👀, mai ya kawo ya prince nan?, tazo sa hannunta ta goge idanunta dan tabbatarwa kanta ko shine din?
Taji hannun kamar an rike, tayi saurin kallon hannunta taga prince ya sarke hannuwan su, ta sake kwalo ido, ta kalli fuskar sa,  ya prince ya hadu karshe, tayi murmushi Allah ya mallakamin kai my prince, ta zare hannun ta daga nasa a hankali, ta kai hannunta ta shafi gashin sa mai laushin gaske da yasha gyara sai kamshi yakeyi, ta shagala da shafar gashin nasa.... 
   
Prince ya bude idon sa ahankali sukayi ido hudu da juna...
Neena tayi saurin dauke hannunta, duk ta rikice tayi baya da sauri, kujerar ta ta tafi suuu....
    Ta fadi gwajab.....
Prince ya mike da sauri yana kallon ta...
Neena ta runtse idonta, oh God, ta matse bakin ta dan taji dan zafin faduwar...Duk kunya ta isheta...
Prince kuwa yadda ta runtsee ido ta matse dan bakin ta sai abun ya basa dariya...
   Ya hau mata dariya, neena ta daure fuska shi kuma kullum idan mutum ya fadi instead of  ya taimaka masa sai yahau masa dariya...
   Ta shagwabe fuska tace ya prince. ...
  Prince ya tsaida dariyar sa ya mika mata hannunsa, maganin marar gaskiya kenan ai..
  Neena ta kama hannunsa ta mike...
  Tace har yanzu dad bai fito sallah ba,, ko karfe nawa yanzu??
    Jin ta taka wani abu yasa ta kalli kasa, jacket din prince ne, ta duga ta dauka tana cewa mai ya kawo jacket dinnan nan? A zuciyarta tayi maganar...
   Prince ya amshe da sauri ya zauna abunsa, neena ta tabe baki itama ta zauna...
   Barcin ma fita daga idonta yayi, data dago ido sai suka hada da prince, tace kai Allah ya masa kallo..
   Prince shi kam mamakin kansa yake  baya gajiya da kallon ta ko kadan...
Suna nan zaune har karfe biyar tayi sukaji bude kofar dad...zai tafi masallaci...
Prince yace wa neena ki buya kasan table dinnan, neena tayi saurin boyewa shima ya shige karkashin table din...bugewa sukayi...sukace auuusshh... a tare kuma suka daurawa juna finger a lips shiiiish!...
     Abun kuma sai ya basu dariya sukayi wa juna murmushi. ..
   Dad na wuce wa suka fito
Prince yace ki shiga now, bari naje sallah nima..
  Neena ta kada masa kai ta dauki ledojin ta ta shige gidan...
.
Ranar da safe, _sallah_..
  Tunda safe suka shiga aiki, mum da mami da inna ladi ke abinci...
  Neena da zuby da zarah suna sashen mami, tare da deeja  suna ta hada snacks, neena tace ohh God na manta, ta mike da sauri ta tafi sashen mum..
Zuwa tayi ta dauko kayan da ya habu ya bata...
Tazo wurin su zuby, anty zuby gashi inji yaya, jiya ya bani yace na baku...
  Zarah ta amsa ledar, wooow.. zuby kalla  exactly irin wannan ne da muke nema..
   Zuby ta amshe, eh na sani ya tambaye ni ko inason irinsa, neena ta basu nasu, zarah tace gaskiya munayi da ya sadeeq..
Zuby tace da kuyi da kada kuyi dashi, ni inayi dashi...
Deeja da zarah suka kwashe da dariya...
An dawo sallar idi, faruk da sadeeq suka shigo falo..
  Sadeeq ya gaishe dasu mum da mami...suka amsa masa a sake...suna taya sa murnar kammala karatunsa.
Har yamma yana gidan, zubaida da shi suna compound sai fira sukeyi..
Neena dake zaune ita da amir a dakin yayaB.
YayaB tace neena jeki wurin zarah kice ta bani lemon nan na madara..
   Neena tace toh ta mike, taci gayun ta cikin riga da skirt sun amshe ta sosai, hips dinnan ya fito, ga shi ta gyara gashinta yayi das dashi cikin daurin dankwalinta, zuby ta mata simple makeup, amma tayi kyau kamar a sace..
.
Ta fito zuwa side din mami, ta iske zuby da ya sadeeq suna soyewar su, tayi murmushi, yaya ashe baka tafi ba..
     Ya sadeeq yayi murmushi, ina nan tare da mrs sadeeq taki barina na tafi, zubaida ta mike bana son sharri sadeeq, ta nufi cikin gidan ina zuwa 2mins...
Neena tadan zauna a kujerar da zuby ta tashi tace yaya kayi dacen mata fa...
Sadeeq yace itama tayi dacen miji ba...
Neena ta kwashe da dariya...
Dai dai lokacin prince ya shigo gidan tare da wani frnd dinsa mahmood..
Hango neena yayi zaune da wani sai washe baki takeyi tana dariya....
Neena tace yauwa yaya muga wayar ka, ta kai hannu jikin sadeeq....
Prince ya fusata sosai...
Tana daukar wayar tayi selfie, yaya ka nunawa umma wannan, sai nazo mata yawo gobe...ta mike tsaye, ta mikawa ya sadeeq  hannu daman sun saba shaking hands abunsu...
Ya Sadeeq ya mika mata nasa shima...
Prince bai ma san lokacin daya karasa wurin su ba, yana lumfashi kamar wani zakiii...
    Wace _wat d well r u doing_
.
Neena da ya sadeeq sukayi saurin kallon shi, prince ya karaso wurin su, ya nuna sadeeq, kai kuma daga inaa?
Neena tace ya prince , yayana ne fa..
Prince ya kalle sadeeq, sai lokacin ya lura da kamarsu da neena harta baci.
Dai dai nan zuby ta karaso tana cewa, ke neena yayaB nacan na jiran ki fa..
    Neena tayi saurin wucewa tana cewa, oh God na manta ma wallahi..
   Zuby ta kalli prince dake tsaye, fuskar nan a tamke, tace ya prince ga yayan neena ku gaisa..
     ya sadeeq yayi murmushi, ya mika masa hannu, prince yadan sake kadan ya basa hannu suka gaisa, sannan yaja abokinsa suka shige ciki..
    Sadeeq ya kalli zuby, yace, ya prince dinku amma soja ne ko? Zuby tace lah ya akayi a gane?
  Sadeeq yayi dariya, kowa ya ganshi zai gane ai...
   Amma akwai wani abu tsakanin su da neena ne?
    Zubaida tace babu komai, amma nima na taba zargin nan, sadeeq ya kada kai kawai, amma kuwa yaga kishin neena karara a idon prince.
   Sadeeq har dare yakai, suna tare da faruk , sai fira sukeyi, an kawo masa baby ya gani, ya kuma bawa deeja abun arziki.
Washe gari tunda safe neena ta shirya dan zuwa wurin umman ta.
    Ta samu dad da mum da zuby tare da amir a dinning,  ta duka ta gaishe su, dad yace har an gama shirin ne neena..
    Neena tayi murmushi ,eh na gama dad, mum tace saboda zangin ganin umma ko breakfast baza'ayi ba kenan.
    Neena dake shafa kan amir, tayi murmushi, dad ya kalli mum, ya maganar da mukayi da yayaB jiya..kin sanar mata kuwa?
   Mum tace aff na manta ma wallahi, neena zo nan ki zauna, mum ta nuna mata kujerar dake kusa data zuby..
    Neena ta kalli mum da sauri, zuby ta jawo hannunta, zauna mana ke kuma, neena dai sai binsu takeyi da ido, mum tace, daga yau _kin tashi daga nana_ din amir, daga yau kin zama yar mu..
     Neena ta saki da ido da baki da hanci...ta nuna  kanta, niiiii..
   Dad yayi dariya yace kwarai kuwa, mami da abbanku sunyi sunyi mu basu ke, hakama yayaB, amma sai nayi musu shigar sauri...
  Jiya naje wurin umman ku, munyi magana sosai da ita, tace ita kam ta bamu ke halak malak, dan halaccin da muka mata,
    Neena da hawaye suka fara zuba daga idon ta, tace mun gode kwarai da taimakon da kuke mana, bamu hada komai daku ba, amma kuma kun dauke mu a matsayin yan uwan ku, kowa na kirana *Yayan Talakawa*  da b'asan asalin su  amma...ku...kuka ya kufce mata, zuby ta rungumo ta tana lallashin ta, mum tace is ok my daughter, komai ya wuce yanzu, dad yace zubaida, jeki kira zarah kuzo kuje, kuyi mata shopping ko?, mum tayi murmushi, yau za'a kawo gadonsu ma, sai a gyara musu dakin zuby , tunda yafi girma, zuby ta rike hannun neena, tashi muje daga can sai muje mu gaida umman ko...
.
Sunje sunsha shopping sosai, duk wanda ya gansu sai sun burge shi, dan sai ka rantse da Allah yan gida daya ne..sun fito daga supermarket din kenan, neena taci karo da wani sausari, yaci gayun sa cikin suit mai tsadar gaske, kayan hannun ta duka suka zube...
    Zuby tace malam baka gani ne ko mai?
  Neena ta tsaida zuby, anty zuby ba laifin sa bane shi daya, harda ni daban kalli gabana ba, saurayin ya kalli neena, yayi murmushi, maganar da tayi yasa yaji ta kwanta masa,   ya duka zai kwashe mata kayan, neena ta duka itama, noo ka barshi pls. Zan kwashe...
    Ya dago kansa ya kalle ta, itama lokacin ta kalle shi...
Guy din ya hadu gaskiya, yayi mata smiling,  yace no I have too...
   Tare suka kwashe kayan, ya mika mata , ta amsa tace thanks, suka tafi wurin motar su..
   Har zata bude ta shiga, saurayin nan ya dawo da sauri..
   Amm pls ya sunanki? Neena uwar saukin kai, tace neenah,yayi murmushi, sunana naseer, pls zan iya samun num dinki?
   Neena tace I dnt hv a sim tukun, zarah ta leko, tace neena shiga mana muje, neena ta bude ta shige abunta...shi kuwa saurayi ya bita da kallo...
Sun kusa isa gidan umma, zuby dake driving ta kalli side mirror , tace, wannan guy dinfa mu yake bi..
Zarah tayi dariya, ai naga alamar sis din tamu ta tafi da zuciyarsa, neena tayi murmushi, ni ba ruwana anty zarah...zuby tayi dariya, guy din ba laifi hes cute...neena ta rufe kunnen ta, nidai ba ruwana am nt even present here.....
Sun iso gidan umma, suka gaishe ta, sannnan suka shiga fira sosai, neena tace ina yaya sadeeq? Umma tace yaje wurin saka furnitures din sabon gidan sa, neena ta ware ido, sabon gida? Yaushe ya gina? Umma tace tun yana jordan aka fara,Ginin , neena ta kwanta jikin umma, shine ni ba'a ko fada min ba, umma ta shafa kanta, aike yanzu ba yar nan gidan bace ba, na bawa mum, neena ta shagwabe fuska kai umma, ni gida biyu gareni fa, kuma iyaye biyu kin ga ni yar baiwa ce..yanzu koh?...
  Aka kwashe da dariya. .
  Sai yamma suka bar gidan, har lokacin naseer na biye dasu...
.
Suna isa gida, yayi parking shima, ya shigo compound din gidan, su zuby da zarah suka kwashi kaya sukayi ciki...
  Neena tazo daukar ragowar, taji an mata sallama, ta amsa ta kalle shi, mai yasa kake ta bin mu ne?
Lafiya dai ko? 
Naseer yayi murmushi. .
Eh lafiya dai ba lafiya ba.
Neena ta gyara tsayuwarta, ban gane lafiya ba lafiya ba..
   Naseer yace, tun haduwar mu dazun, naji kin kwanta min, can be frnds pls?
  Neena ta tabe baki, duk wani namiji baya burge ta, prince dinta kawai ke burgeta...
   
Prince ya fito kenan daga gymnasium (dakin motsa jiki) ya hango neena tsaye da wani, yaja tsaki, wannan yarinyar wai meyasa bataji ne uhm, wani haushi yaji kamar yaje ya shake naseer...
     Neena nacikin tunanin nan, ta kyallo prince, tsaye bakin kofar gymnasium, tace a zuciyarta, sai shegen girman kai, ai kuwa zan maganin ka...
   Ta sakar wa naseer murmushi, hmm ba damuwa, amma nifa har yanzu secondary school nake, naseer ya washe baki, noo ba damuwa ai, neena tace okay yanzu zan shiga ciki, nasan sisters dina nacan na jirana..
  Naseer yace ok sai gobe ko, ya daga mata hannun, neena ta daga masa itama, sannan ta kwashi kayanta tayi ciki...tana shiga falo ta kwashe da dariya...dan yadda taga yanayin fuskat prince, yayaB da amir dake kallo a falon suka kura mata ido, sai dariya take kamar zararriya...
    Tana juyowa taga ita suke kallo, ta hadiye dariyar ta haura sama.
   YayaB ta kalli amir, shima ya kalle ta, suka tabe baki sukaci gaba da kallon su...
   
.
Prince yayi tsaki, mtsw mai yasa na kasa share sha'anin yarinyar nan ne? Ya dunkule hannun sa ya naushi dayan...sannan ya yafa karamin towel dinshi a kafada ya nufi cikin gidan.
An gyara dakin zuby sosai, gadaje biyu ne yanzu, masu kyan gaske, sannan an sake musu closet (wurin ajiye kaya) zuwa babba, dakin gwanin sha'awa, dai dai na yan'mata.
Washe gari akayi liyafar suna, an saka wa baby suna, fatima (sunan mami) bt zasu ringa kiran ta intesar.
Da daddaren ranar ana falo gaba daya, mum, dad, mami, yayaB, zuby, zarah, faruk, deeja da babyn ta intee, sai neena da amir dake zaune a kasan carpet tana koya masa homework, prince ne kawai baya nan, yaje shopping din kayan coffee dinshi .
Inna ladi ta shigo falon, tace sannun ku da fira, abba yace yauwa sannu inna ladi, dad yace inna ladi sai kije kema kiyi hutu gobe da jibi ko, inna ladi ta washe baki, ai kuwa na gode sosai, mum tace lafiya dai ko inna ladi? Ko naman har yayi ne?
   Inna ladi tace, uhm uhm , yama yake da suna, hamza mai bawa fulawoyi ruwa, yazo yace nayi wa niimatu, magana wai ko tana da bako,neena ta dafe kirji, inna ladi ni kuwa, kodai sis zarah?
    Inna ladi ta soshi kanta, a'a ke yace niimatu..
   mami tace, tashi dai kije ki gani, neena ta mike a kunyace ta fita, dan dama da hijabi a jikin ta...
   Zuby tace , sisi kodai wannan guy dinne na supermarket jiya?
   Zarah tayi dariya, ai kuwa dai mayb shine, yayaB tace toh sarakan gulma, faruk yace aikin su kenan.
.
Neena na fita, ta fara yan dube dube, tana tsaki, yanzu haka wannan naseer dinne..
Ai kuwa sai gashi ya karaso dauke da murmushi..
   Neena tayi dan murmushin yake, ina wuni?
  Naseer yace lafiya cutie, ya kike ya daren..?
  Neena tadan gyara tsayuwarta lafiya yau, naseer yace ya sisters dinnan naki fa?
  Neena tace suna lafiya lau, naseer zai yi magana motar prince ta shigo compound din..
   Neena na ganin shine, tace great, mr girman kai ya dawo, ta saki murmushi, tace wa naseer, ammm kai daga wane state ne?
   Naseer yayi murmushi, ni dan yola ne, amma a nan nake aiki...
Neena ta sake murmusawa, lokacin prince ya fito mota dauke da leda..
    Ya wani watsa musu harara, gaba daya ya neme calmness dinsa ya rasa..
   Wani abu ya tsaya masa wuya, ji yadda take wani washe wa banzan cen baki...mtsww I hav to do something really. ...
Ya karaso wurin su, a fusace ya kalli naseer, kai kada na sake ganin ka a gidan okay????
Neena zatayi magana ya fisgo hannunta da karfi.....
  Ya nufi cikin gidan da ita...
  A bakin kofa ya tsaya yana sauke lumfashi sama sama...
  Ya jawo ta ya hada da bangoo..
Duk wannan abun bai ma lura da mutane a falon ba...
Kishi ya rufe masa idoo..
     Ya nuna ta da yasta...kee mai saya bakya jine uhm..
  Nasani tun ba yau ba, kina sona...
  girman kanki da yanga ya hana ki fada....
   Neena ta ware ido,
Ta tabe baki, ni bana sonka, prince ya kasa controlling din kansa, dan yadda yaji kalmar ta rasta zuciyarsa, _bana sonka_ bai san lokacin da ya wanka mata mari ba....
Dad da abba suka hada baki wurin cewa, prince!!! Lafiyarka..
  Prince ya juyo fuskar nan tayi jaaa, an bata zuciyar maza...
YayaB tace kajimin yaro, mai ta maka zaka mare ta uhm.?
   Prince yace iske ta nayi tana fira a wajee..har kamar ta duka nawa take..?
   Dad yace idan batayi fira ba, ita zata auri kanta..?
    YayaB tace atooh, dan kuwa neena tare dasu zuby zamu hadata muyi mata auree....
    Prince ya juyo da sauri ya kalli yayaB idon shi kamar zai zazzago....
Yace ba wanda ya isa ya aure neena, *nine nan mijin ta*ya nuna kansa....
Haha (maza kenan)
.
Gaba daya suka ware ido suna kallon prince..
   Neena kuwa kafafunta kasa daukarta sukayi..
   Sulale wa tayi kasa ta zauna gwajab, bata taba tunanin prince zai iya furta sonta a gaban kowa ba...
YayaB tace kaji min yaro, hausawa fa sunce mace allura ce a cikin ruwa, mai rabu ka dauka..
   Dad ya kalli abba, sukayi murmushi, sannan suka fice zuwa falon dad..
  Mum da mami, suka zo wurin prince, na'im kwantar da hankalinka, prince ya kalle su kawai ya haura sama, yana kallon yayaB..
   YayaB tayi tsaki, ni bari kallona..
  Zuby da zarah harma da faruk, duka mamaki sukeyi, prince ke son neena?, kuma baiji kunyar kowa ba ya fada...
   Deeja tace, ya prince manya, sannan ta kalli neena dake zaune bakin kofa..
  Neena tashi mana, neena ta mike da kyal, tazo zata haura sama, yayaB tace munafuka, harda wani cewa bata son shi, ranar nan fa na taba hango su suna fira a waje...
   Zuby tace nima haka na taba ganin su...
  Faruk yace haka nima..
  Zarah tace tab ashe ni kadai aka bari a duhu....
  Suka kwashe da dariya dukkan su...
Sa safe abba da dad, tare da yayaB suka zauna meeting, mum da mami suka shigo tare da umma, da suka dauko dan tattauna maganar...
Umma na shiga falon idon ta ya sauka akan yayaB, dake zaune tana shan tea...
     Umma ta ware ido, tana ja baya...
Mum ta rike ta, lafiya Aisha??
Lokacin yayaB ta kallo bakin kofar, suka hada ido da ummma.....
Ta mike da sauri, har tea din da ta rike ya rubar mata a jiki, amma bata damu ba...
    Ta nuna umma, aisha! Aisha! Kece nake gani ko kuwa gizo kike mini.....
Umma ta saki kuka, ta karaso wurin yayaB ta duka a kasa, tana kuka tana cewa, ki yafe ni goggo, ki yafe ni.....
     YayaB tayi saurin dukawa kusa da umma...
  Aisha tashi tashi, ba lokacin kuka bane, kuma nice zan nemi gafarar ki...
   Ki yafe ni , kuma ki yafe wa almustafa..
  Umma ta kalli yayaB tana zubar da hawaye...goggo ina almustafa? YayaB taja lumfashi ta dauke ido daga kallon umma, tace, almustafa yana kasar Italy,ni kaina rabun dana kansa shekaru wurin ishirin kenan....
Dad da abba, mum da mami sai kallon ikon Allah sukeyi, dad yace yayaB dama kinsan umman neena?...
YayaB ta mike da sauri, ta nuna umma, aisha ce umman neena daman....
Abba yace kwarai kuwa, itace...
Dad yace, ya akayi umman neena tasan yaya almustafa? 
    YayaB ta zauna tace, bazaku shaida aisha ba, dan lokacin da almustafa ya auri aisha, kuna kasar Egypt. ..
   
,
Almustafa ya hadu da aisha ne, a garin kano, lokacin daya je wani aiki acan..
  Yaso ta sosai, yazo yake bani labarin ta, marainiyace, wanda kawunta ke rikon ta, amma kuma matansa ke azabtar da ita..
    Na tausaya wa aisha tun kafin na ganta..
   Almustafa yace yana son ya aure ta, dan ya taimaka wa rayuwarta..
  Nace masa nima na amince.
   Bayan wata daya, na tura kawu ku maringayi isma'ila.
   Sukaje akayi komai, bayan sati daya aka dauro aure , aka taho da aisha.
  Bayan ansha fama da matan kawun nata.
   Sun zauna cikin kwanciyar hankali, kullum aisha cikin kyautata mana takeyi..
   Saboda ita, rayuwar mu ta samu kyakkyawan canji..
   Har Allah ya bata ciki, ta haihu abubakar, munyi farin ciki sosai.
   Almustafa kuwa ba wanda yakai sa farin ciki, bayan wasu shekaru..
   Ya samu karin girma, kuma aka mayar dashi lagos..
  Yayi yayi aisha ta bisa taki, dan bata son nayi zaman kadaici...
   Tofah tunda yaje lagos, sai yayi watanni shida har bakwai bai zo ba...
  A haka muke ta zaman mu, duk da aisha bata nuna tashin hankalinta ba, ni na gane yarinyar na cikin damuwa kwarai...
   Ranar da almustafa yazo, nayi masa maganar, ya tafi da aisha nizan dauko yarinya daga kauye mu zauna tare..
  Sai ya hau bala'i da masifa...
    Toh fa tunda ya koma lagod dinnan, bai dawo sai bayan shekara, hankalina a tashe, dan ganin da wata bayarrabiya da nayi...
    Yace mana matar sa ce, hankalinmu ya tashi, take ma aisha ta fadi a sume...
    Baiko damu ba, nice nan na rika mutane aka kaita asibiti, likita yace ai tana da shigar ciki...
   Mun dawo da farin ciki dan sanar wa almustafa, sai iske takarda mukayi...
    Ya tafi kasar Italy aiki, kuma ya saki aisha saki biyu....
     Hankalinmu ba karamin tashi yayi ba, gashi duk bakwa nan a lokacin, cikin satin isma'ila ya rasu..
    Na tafi kauye zaman makoki, dawowar dazanyi na iske wata takardar, aisha tabar min..
   Wai ta tafi......kuka yaci karfin yayaB...
   Umma ta ta shiga rera nata....
  Mum da mami suka shiga lallashin su...
   Neena da zuby da zarah dake bakin kofa , sunzo fadawa iyayen su zasu saloon, suka iske yayaB na bada wannan labarin...
.
Kuka sosai suka sha, su abba da dad ma dan goge hawaye....
Prince da faruk ne suka shigo..
  Suka iske falon duk anyi jigum, neena na jikin umma tana kuka...
YayaB tace komai ya wuce yanzu, duniya zata koya masa hankaliii....
  Umma tayi saurin cewa a'a goggo kada kiyiwa almustafa baki...
    Dad da abba sukace, zamu nemo yaya inshaAllah...
  Amma yanzu, umma da sadeeq zasu dawo nan gidan da zama, abba yace kwarai kuwa, har sai mun nemo yaya, sannan asan abunyi...
YayaB tace sai muyi maganar data kawo mu koh..
Dad yace ku kuma sai kuzo ku zauna ko, kukayiwa mutane tsaye..
   Prince da faruk suka karaso ciki...
   Abba yayiwa umma bayani...
    Zatayi magana, sadeeq yayi sallama ya shigo...
  YayaB ta mike da sauri, fuskar sadeeq ba karamin tuna mata da almustafa tayi ba..
  Tazo ta rungume sa...
Sadeeq ya tsaya kamar status. .
   
An zauna, dad ya sake bawa yaran labarin da yayaB ta basu..
   Kowa ya tausaya wa umma...
  Umma tace komai ya riga ya wuce,  ni kuma na yarda *na bawa na'im ,neena har abada*....
   .
*Bayan wata biyu*
.
Neena ta kammala exams dinta, zarah ta fito da wani saurayinta, mai suna Yusuf, yana aiki a banki,  sadeeq  da faruk ke tafiyar da aikin company dinsu dad da abba.prince na bakin aikin sa a lagos, kullum suna busy.
Yau ana gobe daurin aure....
  Prince ya shigo garin, direct family house ya  wuce anan ya samu su faruk da sadeeq, da abokinsa mahmood.
Mum da mami, sun dage wurin gyara yaran nasu.
   YayaB da umma ma sun dawo gidan, sai kuma bayan biki su koma.
   Kullum cikin hidima suke.
  .
Neena, zuby, da zarah anbar musu sashen mami, da kawayen su, kawar neena daya mai suna batool.
     Mum ce ta shigo dakin da suke, tace wai ko maiyasa bakwa jine uhm, wannan maganin tun yaushe mamin ku ta kawo shi.
    Zarah tace nidai nasha nawa mum ta haye kan bed abunta, neena tayi saurin boyewa bayan wata suhaila kawar zuby, zuby tace nima nasha nawa I think neena ce bata ba....
     Mum ta shiga neman neena, ina neena take, daman nasan sai ita ai...
    Neena ta mike da sauri zata fice, mum ta cafko ta, dawo nan sai kinsha shi..yarinya kamar shazumami..komai sai da zaki zata sha shi.
   Mum ta mikawa neena , neena ta wani kuntse fuska, tana sha kamar zatayi amai, har sai data shanye, mum tace ko ke fa...
Prince suna zaune a falo, sadeeq yace wa abokinsa, bari na kira mrs sadeeq,duk  yau bamuyi magana ba, I fill like seeing ha ryt nw wlh, abokin yayi dariya, yace nawawo dis  kind of love...
     Faruk yace, ai yayaB ta kwafsa muku wallah, bikin mutane uku, amma bako dan party...
   Mahmood abokin prince, yace, ai kakus din taku, da gani malamace..
  Prince yayi tsaki, yayaB ko rigima, bakuji yadda take bala'i ba..
  Wai nace inason aure amma, naki zuwa, wai sai ta hana auren...ma
   Aka kwashe da dariya...
Faruk yace ai kaine yaya, bafa wanda yayi tsanmanin kanason neena...
Ni nan da da ita zanyi second wallahi..
   Prince ya wurga masa harara...
  Faruk yayi dariya, amma seriously speaking, neena will b a good wife, she will be far better than,  *LATEEFA*......prince yayi saurin kallo faruk..
  Mahmood yace harka tuna min, na hadu da lateefa ma a turkey,  ta dame ni da tambayar ina prince ina prince, u knw I hated dat bitch, tace mata aure ma zakayi..
Prince ya mike a fusace ya saura sama abunsa..
  Sadeeq yace, wacece lateefa???
Faruk yace lateefa matar ya prince ce, amma fa ex-wife dinsa.....
.
Washe gari dubun nan jama'a suka shaida daurin auren *NA'IM NAFI'U alkali  AND NIEMA ALMUSTAFA*
         SAI
_ZUBAIDA NAFI'U alkali AND ABUBAKAR ALMUSTAFA_
          *DEN*
_ZARA'U SA'EED  alkali AND YUSUF ASHAFA_
Bikin daya tara mutane, masu  kudi , , masarauta da ma  yan kasuwa..
Karfe bakwai aka fara daukan amaren...
  Neena zata zauna a gidan prince na abuja..wanda ke maitama.
    Zarah zata zauna gidan yusuf dake gwarinfa.
   Sai zuby da zata zauna a wuse 2 gidan angon ta sadeeq.
Alhamdulillahi, ankai amaren lafiya, mum da mami sai da suka rubar da hawaye, zasuyi missing lovely daughters dinsu, yayaB da umma ma sun dan share nasu hawayen.
.
An kai neena dakinta, basu taho da amir ba, sai bayan kwana biyu mum tace za'a kawo shi.
Neena tunda kowa ya tafi aka barta ita daya, gaban ta nata faduwa, tana nan zaune shiru, taji an bude kofar dakin.
   Bugun gabanta ya karu..
Tana jin kamshin turaren ta gane prince ne..
  Ya zauna kusa da ita, ya sa hannunsa ya riko nata hannun, dayaji hennan lalle mai kyaun gaske..
   Neena ta sauke lumfashi...
Prince ya shiga murza yan yatsun ta, yana cewa, at last sai da kika mallake ni ko?
     Neena dake cikin mayafi, tadan kalle shi, sai data mallake sa?mai yake nufi..?
   Prince ya dago kai, suka hada ido...
  Ya dan daure fuska, eh mana, nasan kin dade kina addu'ar Allah ya mallaka miki ni....
  Neena ta turo baki..
Prince ya yaye mayafin, yace , ki kara turo min bakin nan ki gani.
   Neena ta juyar da kanta, prince yayi murmushi, anyways,  tunda kin same ni, ni zanyi dan maneji dake...
   Neena ta tsoke baki, tace , kai fa da bakinka kace wa yayab ranar"ba wanda ya isa _ya auri neena  saini_ ta kwaikwayi yadda yayi maganar...
Prince ya kwashe da dariya...
Neena ta juyo tana kallon shi cike da mamaki, dariya har yana faduwa..
   Ya mike ya zauna yace, ni din nan nace haka?
  Neena ta kada kai eh man..
  Prince yace no way, wazai soki, ni ya nuna kansa, god forbid. ...
    Neena ta sauko daga gadon, ta rike kugu tana kallon shi, tadan harare shi, tayi hanyar fita daga dakin...
     Prince ya mike shima, dawo kisha barcin ki yarinya, ni dakina zani...
   Neena ta juyo ta kalle shi, yace taga dan handsome ta makale, ta kara bata fuska kamar zatayi kuka...
   Prince ya fice yana mata dariya...
  Yana zuwa dakin sa, ya fada kan bed, she look much cuter idan tana fushi...yayi mirmushi, I wont force ha..amma for sure after shekara daya, by den mun shaku sosai, *I will make her mine*...
Yayi dariya ya murgina ya jawo wayar sa, pic dinda ya dauke ta dazun nan ne, lokacin daya shigo dakin, bata lura ba cos tana kallon kasa..
   Yayi kissing wayar ya furta *I LOVE U MY NEENS* - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment