Blogroll

BANNER 728X90

Monday, 5 March 2018

TANA RAINA Page 21-25

77-78 Kamal ya janyo sabreen ya rungumeta a jikinshi ya tsunbaci kanta, d'ago da kanta tayi suna kallon juna tace ya jikinka, jiki da sauk'i sabreen kidena damuwa kinji zuwa gobe za'a sallamemu insha Allah, marairaice mirya tayi tace yah kamal yah suhail fa bai farfad'oba har yanzu ina tausayin hafsat sosai, sabreen suhail zai samu lfy insha Allah muyita mishi addu'a kinji? To yah kamal insha Allah zamuyi mishi addu'a Allah ya kare na gaba, ameeen wifeynah banaso kisa damiwa a ranki kinji? To yah kamal yanzu inane yake maka ciwo? Jikinane kawai nakejinshi wani iri amma bakomai, itama murmushi tayi sannan tasa zagaye hannayenta a bayanshi tare da kwantar da kanta a jikinshi tace bana so in rasaku yah kamal☹, bazaki rasamuba my luv i love you, kanta ta d'ago suna kallon juna suna murmushi tace me too.
Sallama sukaji daga waje, se sabreen tayi saurin barin jikin kamal ta saita kanta, sannan kamal yace bisimillah. Salma ce ta shigo tace kuyi hakurifa, sabreen tayi mirmushi tace hakurin me? Salma tace suhail ya farfad'o amma kuma wani yarene ko menene yaketa fad'a wai (SABSU), kamal yace SABSU kuma? Mekenan oho, sabreen ta had'iyi yawu tace kodai firgitanne? Salma tace eh hakama doc yace mana. Sabreen tace yah kamal inje in dubashi? Kamal yace jeki yana mata mirmushi segasu ALIYU sun shigo, sabreen da salma suka fita. Salma ta dafa sabreen tace duk d'akin babu wanda ya fahimce suhail seni, murmushi sabreen tayi tace thank God☺ sannan suka shiga d'akin. Se mummyn kamal tace to bari inje gun kamal, dedai lokacin d'ayan abokinsu yazo da UNCLE D bayan an gaisane se suka fita da mummy. Hafsat ce zaune a gefen gadon suhail, sabreen tace mum ya jikin nashi waiya farka? Mum tace eh amma dai bai bud'e idonshiba, sabreen tace to Allah ya bashi lfy, sukace ameen. Kamar a mafarki suhail yakejin muryan sabreen, ai kuwa seya sake cewa SAB... salma bata bari ya k'arasaba tace ko za'a kira doc ne, suhail ya fara bud'e idanunshi a hankali yana bin kowa da kallo har seda yazo kan sabreen kafin ya bud'e ido gabad'aya.
  Sabreen tana murmushi tace mum yah suhail ya farfad'o, mum tace Alhamdulillah, hafsatma dad'i taji sosai tace yah suhail, murmushi yayi mata yace ina kamal aminina, awani hali yake  mum? Mum tace yana halin lfy suhail, dad'i yaji har cikin ransa dan bayaso wani abu ya sami kamal. Sadiq ne suka shigo da doc se akace duksu fita waje, suna fita yanata bin sabreen da kallo. Gun kamal suka koma se kamal yace Aliyu ka mayar dasu sabreen gida, hafsat tace amma ya bari mugaisa da yah suhail tukunna, kamal yace to shikenan.
Bayan sun gaisa da suhail ne se Aliyu ya mayar dasu gida. Tunda suka dawo sabreen taketa murmushi tana jin dad'i a ranta kome dalili oho. Washe gari aka sallami su kamal suka wuce gidan mum harda suhail dayake jikin nashi da sauk'i.
Su hafsat sunyi girki abinsu sukaci, Aliyu da sadiq ne sukazo dubasu kuma suka gaya musu cewa an sallami su suhail, dad'i sukaji sosai se hafsat tace dama mun muku pepe soup gashi seku tafi dashi. Godiya sukayi sannan suka tafi.
      Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
      By Mmn Shureim
             (Nasd-Nas)
79-80 Bayansu Aliyu sun tafine, salma tace to ita zata koma se lokacin dinner zata dawo. 11:00am sabreen ta kira kamal, suhail ne ya d'auka tare da cewa hello sabreen kamal yana wanka, tace ok yah suhailina kwana, lfy lau sabreen ya kuke, lfyanmu kalau ya jiki, jiki alhamdulillah, toh Allah ya baku lfy Allah ya tsare na gaba, Ameen sabreen ga kamal d'in ya fito, ok nagode. Kamal ya karb'a yace hello wifey nah, murmushi tayi tace yah kamal ina kwana, lfy wifey kin tashi lfy? Lfy lau ya jikin, da sauki sosai wlh, toh Allah ya kara lfy, ameen yasu hafsat da salma, lfyansu lau salma ta tafi yanzunnan, ok se dare zata dawo kenan? Eh haka tace, to shikenan kuna buk'atan wani abune? A'a bakomai yaushe zaka zo? kinyi missing d'inane? Itama murmushin tayi tace nidai yaushe zakuzo, yace se dare, darefa kace ya kamal, to menene wifey me kikeso, ni kazo kaida yah suhail dan yanzu hakama hafsat ta dage wai zataje gida dan taga ya suhail kumafa ni kad'ai zata bari a gidan, mirmushi kamal yayi uace toba shikenanba indan tazo nima senazo gurinki in tayaki hira kafin tadawo koh? Nidai ban yardaba pls kuzo yanzu yah kamal, shikenan wifeynah yanzu zaki ganmu kinji? Okay sekunzo byee, yace mata byee sannan ya katse.
Sabreen tacewa hafsat to dai babu inda zakije suna zuwa yanzu, hafsat tace meya faru da wayan yah suhail baya shiga sam, sabreen tace wlh kuwa kinga ban tambayaba ammadai yanzu zasuzo, hafsat tace to bari na sake kimtsa gurin, sabreen ta mike sunayi tare hafsat tana cewa kefa amaryace jeki kwanta ki huta, dariya sabreen tayi tace kema kina tafe. Tas suka gyara guri suka kunna AC ga room freshner da turaren wuta kota ina gurin abin burgewa. Se bayan azahar su kamal sukazo shida suhail kawai sukazo abokansu na hotel. Hafsat ce taje ta bud'e musu kofa tasha ado sosai, k'amshine ya daki hancinsu ga sanyi da palon yayi, murmushi hafsat take musu tace sannunku da zuwa, bayan sun karasa sun zaunane, se hafsat tace bisimillah muje daining kuci abinci, ba musu suka wuce kamal yace ina wifey nane? Hafsat tace tananan fitowa, himar sabreen tasa har k'asa sannan ta fito, tunda take fitowa suhail yake satan kallonta shi kad'ai yasan meyakeji. Da sallama ta k'araso ta zauna kusa da kamal ta gaishesu se hafsat tace to bisimillah, suhail yace kufa, hafsat tace mu munci namu, abinci sosai sukaci sabreen tanata satan kallon suhail dama danta ganshine kawai yasa tacewa yah kamal suzo. Bayan sun gamane suhail da hafsat suka koma palo suna hiransu amma hankalinsa nagun sabreen. Kamal yace to gani munzo kinji dad'i? eh mana naji dad'i sosai, kamal ya kalleta sosai yace wifey yanaga idonki yayi jaa? Shuru tayi batace komaiba, hannunta ya kamo ya had'a da nashi guri d'aya yana shafesu yana magana a hankali wifeynah kinyi kuka ko? Kanta ta d'ago tana fiskantarsu suhail se suka had'a ido suhail yayi saurin kaucar da kansa yana kallon hafsat, sabreen tace yah kamal ai kuka dolene, kamal yace amma naki yayi yawa wifey pls kidena kinji? Murmushi tamishi tace toh yah kamal naji, yace sannan kuma inaso a canjamin suna yanzu niba yah kamal bane, tome kakeso in kiraka dashi? 樂yace "my one nd only" sabreen taji bazata iya kiranshi da wannan sunanba, setace ninafiso in kiraka da yah kamal dan sunan namin dad'i amma tunda bakaso zan kiraka da "SWEET" tayi maganan cikin wani salo, dad'in sunan yaji sosai abakinta yace yes naji dad'in sunan tnx ya tsunbaci hannayenta yace i luv u. Murmushi tamishi kawai suna kallon junansu, fiskansa ya kawo daidai da nata ya fara tsunbatar lips nata a hankali tana sauraronshi yanata tsotsonta kamar ya samu sweet, hafsat bata iya hangosu amma shi suhail idonshi na kansu. Sunkai kusan 3minit sannan sabreen ta janye bakinta tare da d'an matsawa gefe, kamal ya bud'e idonshi yana murmushi, ita kuwa kunyane ya kamata ta sunkuyar da kanta. Kamal ya mik'e tare da rik'o hannunta yace zamu wuce se dare zamuzo d'aukanku zuwa dinner, mik'ewa tayi suka taho har palo sannan ya saki hannunta yace toki koma ki huta kinji, murmushi tayi, suhail ya mike yace to amarya semunzo anjuma, tace to mungode sannan suka tafi.
            Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
81-82 Da dare angaye sun gama shirin dinner harda UNCLE D, suma mum ma sun shirya sunyi kyau sosai a cikin purple less iri d'aya ita da mummyn kamal sukayi d'aurin turai tare da gyalensu a kafad'a. Amare kuwa sunsha ango da mazajensune cikin wani  fararen kaya wanda nima ban tab'a ganinsuba d'inkin doguwar riga aka musu fitet da adon red yayi bala'in kyau sosai gashi daidai da jikinsu, sannan aka musu d'aurin gwaggwaro da red head, takalmi da pos ma red wayyo Allah nasan zakuso ganin sabreen da munna a wannan daren. Abokan ango da kawayema ba sauki, akazo d'aukan amare ko wani ango da amaryansane a bayan mota se kuma direba, abokai suka d'auki kawaye, hafsat tana motan suhail a gaba, ita kuwa salma tana gaban motan amarya da ango. Base na gaya muku yadda gurin dinan zai kasanceba kawai ku kwatantashi a ranku da cewa bikin yar DON akeyi. Anyi rawa kad'an da kid'a kid'i kam ba'a magana an zubashi sosai tunba suhail ba, abokaima sun nina bajintarsu irinna pakistan, hakama uncle d ga abokan Abbakar din munira abindai ba sauki. Bayan an gamane akayita hotunan sam salma taqi shiga ko d'aya, babu yadda sabreen batai da itaba amma sam taqi. Bayan an gamane akayita ciye ciye zuwa 11:00pm aka gama sannan aka maida jama'a gida, sannan abokai suka raka angwaye gun amarensu.
   Hafsat da salma ce kawai agun sabreen tanata kuka bayan tayi wanka ta sauya kaya, sunyita rarrashi harsin gaji amma bata dena kukanba har angwaye sukazo. Da kyar su salma suka fito da ita abokai sunata jawabinsu kanta a sunkuye tana hawaye, suhail ya daure yace haba amarya kukan ya isa mana, kinsanfa ke amaryace bai kamata kiyi zubar da hawayenkiba, nidai ga abokina kuma aminina mun kawo mikishi amana, dan Allah kuyi hakauri da juna sannan ki kasance mai biyayya agareshi ta hakanne zamuji dad'i ke kin kasance kamar k'anwace a gareni nasanki da biyayya dan haka ki kasance haka agareshi sabreen, duk abinda yamiki na kuskure ki sanar dashi ko kuma ki sanar dani zan d'auki mataki, sadiq yace matakin me zaka d'auka? Suhail yace zaneshi zanyi sosai da bulala, dariya sukayi dukkansu harda sabreen di'n. Suhail yaji dad'i datayi dariyan ya mike tare da cewa kokefa sabreen sam fushi baya miki kyau dan haka ki denayi abokaina ku tashi mu tafi, salma bari mu saukeki ko? Salma tace a'a MUHSIN yana zuwa yanzu d'aukana, suhail yace okay to idan yazo ki gaisheshi tunda kin hanashi zuwa dinner. Murmushi kawai tayi tace zaiji, sannan sukayi sallama da hafsat tabisu suka tafi sabreen tanata bin suhail da kallo shima haka. Bayan kamal ya rakasune seya dawo lokacin salma tana k'okarin fita suka had'u, kamal yace har zaki tafi, tace eh anzo d'aukana sena sake zuwa, kamal yace to mungode muje ingansa semu gaisa, bayan sun gaisa da MUHSIN ne seya musu godiya sannan ya shiga gida. Muhsin ya kalli salma yace kinsan me? Salma tace a'a, Muhsin yace rayuwarsu na birgeni musamman na suhail da sabreen kuma inaji ajikina suhail zai auri sabreen amma basan ya hakan zai faruba tunda yanzu tana tare da kamal, salma ta juya tana kallon Muhsin cikin mamaki tace meyasa kace haka? Yace hakan nakeji a raina kuma gaskya nafisonsu tare, salma tace hmm muje sannan suka b'ace.
      Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
83-84 Kamal ya shigo da sallamarsa ya kulle kofan, hara yanzu sabreen tana zaune a palo. Ya karaso gunta ya zauna kusa da ita tare dasa hannunsa ya d'ago ta kanta suna kallon jina, murmushi yamata yace a ina kikeso mi kwana? K'irjintane taji ya buga yau zata kwana da wani kuma d'aki d'aya gadoma d'aya樂, yace wifey ya kikayi shuru? Tace ko ina, d'agota yayi yace to muje d'akina, tace to bari na d'auko kayana a d'aki, yace no akwai kayan dana sayo miki a pakistan duk wani abu da zaki bukata yana cikin walldrop nawa. Hannunta ya rik'e suka shiga dama AC a kunne yake d'aki sanyi kamar k'ank'ara ga kamshi dayake tashi, bayan sun shigone ya rufe kofan ita kuwa ta zauna a bakin gado kamar wata bakuwa. Kamal yace wifey ki saki jikinkifa nan gidankine yadda nake iko dashi kema kina da wannan ikon pls ki dena jin kunyana mun zama MATA da MIJI kinji? Kai kawai ta d'aga mishi tana mirmishi, yace bari in watsa ruwa, tace to ina zan samu kayan baccina? Walldrop ya bud'e ya d'auko mata wani red nighty iya gwuiwa yake sannan bayida kauri sosai ya mik'a mata, kunua taji tasa hannu ta karba tace yah kamal ba wanine, mirmushi yayi yace akwai amma ni wannan nakeso kisa, toh tace mishi tare da sunkuyar da kanta kasa. Kamal ya cire kayan jikinsa daga shi se boxxer ya shige toilet kan sabreen a sunkuye, seda ta tabbatar ya shiga sannan ta cire kayan jikinta tasa kayan baccin ta nad'e wanda ta cire tasa a walldrop d'in sannan ta sake feshe turarenshi a jikinta dama bata jima dayin wankaba seta hau kan gado ta rufi da bargo. Kamal ya fito d'aure blue towel ya hangota kwance akan gado, yace wifey kije kiyi alwala muyi godia wa ALLAH, sabreen tace yah kamal bana sallah, yace okey toni bari inyi kinji karfa kiyi bacci, tace toh. Bayan ya idarne seya fesa turare a jikinsa yasa kayan bacci ya nufo inda take rufe da bargon shima ya shiga ya kwanta kusa da ita yace wifey tashi ki zauna, ba musu ta tashi zaune amma ta rufe k'irjinta da bargo, goshinta ya dafa yana karanto addi'a sannan yace bakya jin yunwane? Tace eh a koshe nake, yace toni inajin yunwa, tace to bari inje kichine in dafama wani abu, yace toh wifey, har zata janye bargon seta tuna da kayan jikinta tace eyyah ya kamal pls kaban himar nawa a walldrop, yace aiba himar acikin kayan, tace tokaban zanina dana cire yanzu da gyalena yana ciki, kamal yace nak'i bakina cemin kamal ba, ta marairaice tace pls sweet kaje ka kawomin, murmushi yayi yace ki zauna wifeynah zanje in d'auko kinji, nagode SWEET, murmushi yayi mata sannan yafita yaje palo bai jimaba ya dawo da leda a hannunsa kazane da ice cream se FARO WATER da juices.
        Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     BY Mmn Shureim
             (Sad-Nas)
85-86 Kamal ya jawo stul ya ajiye abincin akai, yace wifeynah matso in dinga baki, sabreen tace yah kama.. ya juyo yana kallonta wani iri setace sorry kasan nafi sabawa da sunanne se'a hankali zai fita a bakina, kamal yace nidai to bana so garaki saba da wuri. Sabreen tace to SWEET nidai nak'oshi amma zansha ice-cream kad'an, murmushi yayi tare da bud'e ice-cream d'in ya d'ibo yasa mata a baki haka yayita bata har tace ya isheta sannan yaci abincin ya mayar da komai kichine ya dawo ya wuce toilet ya kurkure baki sannan ya kashe wutan d'akin ya kwanta a bayanta tare da rungumeta, da sauri tasa hannunta a k'irjinta, kamal yace ya haka kuma wifeynah, "the property is mine so pls let me okey"? Shuru tayi tanaji ya cire hannuta a kirjinta yana cewa bakya tausayamain ne wifeynah, kinsan haka zamu kasance har tsawon 3month so pls ki barni da sauran jikinki kinji? Tausayinshi ya kamata tanaso ta mishi tambaya amma tana jin kunya, kamal yace pls kiyi hakuri sabreen, sabreen ta juyo tana fiskantarshi tace haba SWEET kamanta bana sallah ne, kuma ai nasan da hakan tun kafin in aureka, dan haka pls karkasa damuwa a ranka "its okay with me SWEET" dad'i sosai kamal yaji ya rungumeta a jikinsa yace nagode sabreen ke daban ce acikin mata shiyasa na zab'eki, peck ya bata a goshi, daganan ya fara shafa jikinta masu laushi da dad'in tabawa, wani iri sabreen ta faraji shi kuwa secigaba dayi yakeyi, a hankali ya fara kissing d'inta itama tana mayar masa da martani se tsotsan junansu sukeyi yana shafarta. Seda suka tsotsi junansu son ransu sannan yaci gaba da shafeta yazo kan bubs d'inta aiseya rufe ido☺, yau ne karo na farko da tab'a mace lumshe ido yayi yanata sarrafasu ga laushi dad'in tab'awa gasu a tsaye suke kuma a cike☺. Dad'i sosai sabreen takeji, shi kuwa kamal se had'iyan yawu yakeyi a hankali ya cire mata rigan jikinta daga ita se karamin wando rigan, sarrafata yakeyi sosai sannan ya fara tsotson bubs nata kamar zai had'iyeta, sabreen tana ji yadda kamal ya tashi ya tsaya sosai se abin yana mata mamaki. Hmmm abindai ba sauki se wani lasheta yakeyi sunfi 3hr ahakan sannan ya rabu da ita yana kwallah, rungumeta yayi ta baya hannunsa nakan bubs nata ahakan sukayi bacci ya k'ank'amesu kamar zasu gudu, ita kuwa gabad'aya kunyansa takeji amma kuma taji dad'in hakan.
  Da asuba kamal ya farka yaji sabreen ta sake shigewa jikinsa ahankali ya janye jikinsa ya tashi ya kunna wuta sannan ya rufeta da kyau dan sanyin yayi yawa seya shiga toilet. Yana shiga sabreen ta tashi ta d'auki riganta ta tafi d'akinta, toilet ta shiga bayan ta fitone ta shirya tsab cikin english wears riga da siket blue siket d'in har k'asa tayi wanka da turare ta nufi d'akin kamal. Abakin kofa suka had'u suka sakarwa junansu murmushi, d'agota yayi cak se kan gado ga wani kamshi mai dad'i da takeyi, himard'in jikinta ya cire yace woow luv kinyi kyau sosai, tace nagode ina kwana, lfy wifeynah kin tashi lfy, lfy lau, yace wannan kyau haka aiseki rikitamin lissafina, dariya tayi tace aika fini kyau SWEET, gyara mata kwanciya yayi akan kirjinsa da haka suka koma bacci basu suka tashiba se 10:00am. Bayan sun sake yin wankane se kamal yace ta kwanta ta huta sannan ya wuce kichine, tana biye dashi a baya yace luv banace kijeki hutaba, tace eh hira zan tayaka ai peck tabashi a kumatunsa kuma yaji dad'in hakan sosai. Had'add'iyar indomie ya dafa musu wanda yasa sauran kazan jiya aciki da soyayyiyar egg, koda sukaje dainning rufe ido kawai sabreen takeyi tana jijjiga kai alamun yayi dad'i. Shi kuwa kamal kallonta kawai yakeyi yanajin yadda k'aunarta yake k'ara shigansa yana murmushi.
        Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
      By Mmn Shureim
             (Sad-Nas)
87-88 Bayan sun gama breakfast ne ta tattara komai takai kichine ta wanke sannan suka wuce d'aki tana fama gyara gado se kamal ya fad'a akan gado ya janyota jikinsa yana cewa bana bukatan gyaran zoki gaya min wani university kike so? dad'i taji sosai tace sweet zaka barni inyi karatu? Peck ya bata a wuyanta yace zan iya yimiki komai domin samun farin cikinki sabreen, wannan shine k'aunar da nake miki, kiss mai zafi ta manna mishi a lips nashi tare da cewa "tahnkyou sweet" yace always my luv". Wayan kamal ne yake ringing sabreen ta d'aaga taga suhail ne, kamal yace d'auka, ta d'auka tasa mishi a kunne, seya cire a kunnenshi ya rike a hannu tare da sawa a hands free yace hello abokina yane, suhail yace an gaida ango mu gamu a waje ka fito kawai cikin shiri muje gunsu kaka muyi musu godiya dan kasan gobe su sadiq zasu wuce kuma nima zan bisu, kamal yace haba dai zaka bisu ai nine da tfy, suhail yace karka damu ango na hutar dakai idan nayi 2month zan dawo seka tafi, kamal yace to gani nan fitowa, kamal ya kalli sabreen ya tsunbaceta yace luv zamuje gidanku gaisuwa kindaiji komai ko? murmushi tayi tace to katashi kaje suna jiranka pls ka gaishemin dasu kakana tana shagwab'a, shikuwa yana mugun son shagwab'an sabreen rungume junansu sukayi yace zasuji bazan jimaba kinji, to Allah ya kiyaye hanya, yace ameen bazaki rakaniba, tace sweet banaso su yah suhail su ganni kunyansu nakeji ta karasa maganan tana b'oye fiskanta a jikinshi. Dariya yayi yace to shikenan sannan ya canja kayanshi suka tafi.
Kafin su dawo sabreen ta gama abincin tayi wanka tayi ado sosai gida se kamshi yakeyi, su suhail suka sauke kamal sannan suka wuce. Da sallama ya shigo taje tayi hugging nashi ya manna mata kiss a lips nata yace wlh nayi missing naki, murmushi tayi tace wlcum sweet ya hanya, alhamdulillah su kaka sunce a gaisheki, ina amsawa muje ka watsa ruwa to se muci abinci. D'aki suka wuce ta tayashi cire kayan jikinsa sannan ya shiga wanka bayan ya fito yaga kayansa akan gado yayi murmushi tare daji dad'i yasaka segata ta shigo, tace sweet kayi kyau, yace nagode da kika zab'o min su luv. Bayan sunci abincine yake ce mata zasuje yiwa mummy sallama anjuma dan gobe zasu wuce dukkansu dasu suhail, sabreen tace to bari naje na mata peppe chikeen.  Bayan sallan magrib suka tafi, hafsat se murna takeyi dan tayi missing d'in sabreen, bayan sun gaisa dasu mummy ne se suka wuce d'akin hafsat sunata hira ananne take gaya mata rashin lfyan suhail ya tashi jiya da dare ko bacci basuyi shiyasama zai tafi pakistan dan ganin doctor'nsu. Mamaki ya kama sabreen tace Allah sarki me yake damunsa? Hafsat tace yadai ce cikinsa kuma wai yana yawan jin jiri da ciwon kai sosai, sabreen tace eyyah yah suhail Allah ya bashi lfy, sukace ameen a tare sannan sukaci gaba da hira itadai sabreen hankalinta a tashe yake. Har kusan 9:30pm kamal yace sabreen ta fito su tafi, hafsat ta rakosu har waje segasu suhail sun shigo, sabreen ta gaida friends nasu sannan taje kusa da suhail itada hafsat shi kuwa kamal suna magana dasi aliyu, sabreen ta kalleshi har cikin ido tace yah yah suhail ya jiki, yace da sauki sabreen, tace Allah ya kara sauki Allah kuma ya kiyaye hanya, yace ameen nagode. Sabreen ta kalli hafsat tace toni zan tafi yaushe zakizo, kamal yakira hafsat setaje gunsu, da sauri sabreen ta mikawa suhail wani abu yasa hannu ya karb'a yana kallonta har cikin ido yace thankyou pls ki manta dani ki kulamin da abokina kawai nina hakura dake yanzu sabreen, toh yah suhail insha Allah sannan ta wuce gun mota tana hawaye shi kad'ai ya lura da hakan. Bayan sunyi sallama ne kamal yazo suka tafi.
   Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
    By Mmn Shureim
           (Sad-Nas)
89-90 Suna tfy kamal yake cewa Allah sarki abokina wlh bayi da lfy sam, kuma gashi ya dage seyayi tfyan. Sabreen ta daure tace Allah ya bashi lfy, kamal yace ameen. Bayan sun dawo gidane, yana rike da ita har suka karasa kofa ya bude suka shiga sannan ya rufe, d'akinta tayi niyan wucewa amma sam kamal yaqi wai yau anan zatayi wankan. Shiya fara shiga wqnka bayan ya fitone itama ta wuce d'aure da towel se kallonta yakeyi da alamun akwai abunda yake damunta.
Bayan sabreen tayi shirin baccine ta hau gado ta kwanta a gefe, matsowa yayi kisa da ita ya rungumeta ta baya yana cewa wifeynah lfy, meya faru naganki kinyi shuru kamar kina da damuwa? Juyowa tayi tana kallonshi tayi d'an murmushi tace bakomai, kamal yace kin tabbata pls karki b'oyemin ki gayamin abinda yake damunki, sabreen tace wlh bakomai sannan ta juya mishi baya, kamal yace to shikenan ki juyo indinga kallon fiskarki, ba misu ta juyo tate dayin murmushi tasa hannayenta akan sajenshi tana shafawa tace "i luv this" dad'i yaji sannan ya tsunbaci bubs nata yace "i luv this too" dariya sabreen tayi hakan yasa yaji dad'i data sake lokaci guda nan suka fara tsotson junansu suna sarrafa junansu cikin so da kaunan juna amma dai ba " SEX" saboda condition d'in kamal.
Da asuba suka tashi yau kam kamal yace sam tare zasuyi wanka, sabreen tace pls kayi hakuri sweet ina kunyanka, dariya yayi sosai yace to inaso kidena jin kunyana tashi muje, marairaicewa tayi tace eyyah pls yah kamal, yace yah kamal fa kikace dan haka semunje, tace sorry sweet kaje ka fara nidai kunyanka nakeji wlh. Kayan jikinta ya fara cire mata fiskanta a rufe da hannayenta yace meyasa zakiji kunyata bayan kullum ina tab'awa, tace eh amma ai bama ganin juna saboda wutan d'akin a kashe yake, yace waya gaya miki haka nidai ina gani sannan ya cire mata rigan ya fara goga hancinsa akan bubs nata, sabreen tace sweet bakace wanka zamujeyiba, yace eh idan baki bud'e fiskarkiba to zanci gaba dayin hakan, tace wlh bazan iyaba pls ka bari, wandon jikinta zai cire tace pls sweet kasanfa am off yau ne zanyi wankan sallah pls karka cire min, yace karki dami tunda kin gama ai shikenan ni zan wanke miki pant d'inma, shiru tayi tana mirmishi dan tana da tabbacin cewa babu jinin yau kam haka ya cire mata wandon sleeping dress d'in ya rage pant kawai seya d'aga sama kamar bby yana dariya yana cewa matsoraciya, tace eh d'in wlh yah kamal zan dinga kiranka kuma☺, murmushi yayi yace zako ki gane kurenki nanda 3month. Tace haba yah kamal kacefa bazaka cutar daniba, yace eh dakam haka nace amma nafasa tunda kince sunana yah kamal, tace am sorry sweet luv peck ta manna mishi a kumatu kuma idonta arufe. Bayan sun shiga toilet ne ya ajiyeta har yanzu dai fiskanta a rufe da hannayenta, murmushi kawai yakeyi sannan ya cire mata pant d'in jikin babu komai a jikin part d'in, toilet peper ya yanko dewa seyasa part d'in aciki ya nad'e sannan yasa a dosbin d'in dake toilet d'in seya wanke mata pant d'in tas ya shanya. Sabreen kuwa tunda taji ya cire mata pant setaji kamar ta tsaga k'asa ta shiga dan kunya, kamal se murmushi yakeyi ya kamata ya mata wanka tsaf kamar jaririya. Tace ya isa haka nagode zanje d'akina inyi wankan sallah da brush, kamal yace no kiyi anan barina juya bayana, da kyar ta bud'e ido taga baya kallonta setayi wankan tsarkin da sauri sannan ta rufe idonta ta tsunkuya a baf d'in tace nagam, towel ya ciro ya d'aura mata sannan ta bud'e idonta suka kalli juna ya mata gwalo, a hankai ta fito taje gun brush tanayi shi kuwa kamal ya farayin wanka, harta gama ko gefensa bata kallaba ta fita sauri ta goge kanta sannan tasa dogon riga da himar tana jiransa. Bayan ya fitone seyasa jallabiya yajasu sallah. Bayan sun idar ne ya juyo yana kallonta, tace ina kwana, yace lfy ya kika tashi, tace lfya lau, yace ki kwanta zanje inkaisu mummy airport kinji, rungumeshi tayi shima haka tace Allah ya kiyaye hanya, yace ameen thanks sannan ya tsunbaci lips nata ya fesa turare ya fita yana mata.
  6:47am kamal ya dawo gida sabreen tana cikin bargo jallabiyan ya cire seya hau gadon yana rike da kunnensa, sabreen tace sweet lfy? Yace wlh suhail ne yajamin kunne wai in kula dake sosai inba hakaba zai zaneni kinga har yanzu kunnen zafi yakemin, sabreen tayi murmushi tare da janyo kamal kan kirjinta tana shafan kunnen tace sun tafine? Yace eh sun tafi, tace sorry sweetnah sannan ta tsunbaci kunne, shi kuwa kamal dad'in hakan yaji Kansa nakan bubs nata se wani lumshe ido yakeyi da haka suka kombacci
         Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
91-92 Bayan sun tashine suka sakeyin wanka tare sannan ya shiryata cikin riga da wando tayi kyau sosai suka nufi kichine don girka breakfast.
Haka dai rayuwar kamal da sabreen yaci gaba da kasancewa cikin kaunar junansu sam bai tab'a b'ata mata raiba, kullum yana kokarin faranta mata rai duk abinda takeso shi yake mata, itama kuma biyayya sosai take mishi da kuma nuna mishi kauna zamansu abin sha'awa. Idan ya kira suhail yana had'asu su gaisa wata ran, hakama hafsat tana zuwa mata yini salma ma takan zo amma ba sosaiba. Kamal yakai sabreen kauyensu sun yini a gida kaka yaji dad'in ganinsu dan tayi kyau sosai abin dai se wanda ya gani, shima kamal jiki yayi ya kara kyau hankalinsu a kwance sunje gun kawarta munira canma yini tayi dan harse bayan magrib yazo d'aukanta. Gun mum ma tana zuwa gaisheta idan zataje kiwa girki na musamman yake yiwa mum takai mata.
Akwana a tashi ba wuya yanzu sabreen ta denajin kunyan kamal ko kad'an zuba soyayyarsu sukeyi son ransu, yanzu auren 2month harda 1 week gobene suhail zai dawo k'asar girki kamal yasa sabreen tayi musu dan anan zaizo yaci abinci shida hafsat.
Yaune kamal yaje airport ya d'auko suhail shida hafsat, gidan kamal suka zo lokacin sabreen ta gama shirya komai tasha wanka da ado sekun ganta. Tana zaine a palo taji slm, mikewa tayi taje ta rungume hafsat tace yah suhail sannu da dawowa, murmishi yayi yace yawwa amarya ya sameku lfy, tace lfy lau yasu mummy, yace mummy lfyansu duk sun gaisheki sosai da 'yan companynmi duk suna gaida amarya, mirmishi tayi tace ina amsawa bisimillah, sannan, suka karasa daining ta zuba musu abinci suhail se satan kallonta yakeyi yaga ta kara kyau da haske jikinta a murmure gwanin sha'awa. Kamal yace tunda ka dawo nima jibi zan wuce insha Allah, suhail yace da wuri haka? Kamal yace eh kasan lokaci yayi da yakama inga doc to shiyasa nakeso in tafi da wuri dan office ma yayi missing d'ina, suhail yace gaskya kam sunce wai kaje musu da amarya. Kamal ya kalli sabreen data dad'e da b'ata rai tunda yayi maganan tafiya jibi, yace haba wifeynah aiba jimawa zanyiba idan naga doc zan dawo semu tafi tare kinji? Yace nidai sedai mu tafi tare dan bazan iya zama ni kad'aiba, hafsat tace zanzo in dinga tayaki kwana kinji, murgud'awa hafsat baki tayi tace bana so, abin ya basu dariya sosai tunba suhail ba yace abokina ka tafi da ita kawai, kamal yace a'a friends bazan jimaba zan dawo semu tafi tare. Sanreen bata sake cewa komaiba hafsat tana ta zolayarta har suka gama sannan suhail yace to amarya mun gode zamu wuce, sabreen tace sweet nima zan bika mu saukesu a gida, yace to amma fa bazaki shigaba, tace eh nayarda sannan yaje tasa himar suna baya ita da hafsat, su kamal suna gaba har suka isa da sauri sabreen ta bud'e kofa suka fita ita da hagsat, kamal yace wifey ki dawo, gwalo ta mishi akan idon suhail se abin ya burgesa. Ta gaida mum sannan ta fito tazo gunsu itada hafsat, suhail ya bud'e mata kofan gaba tace nagode yah suhail sannan ta shiga ta zauna, hannunsa ya d'aga yana duba agogo nan idonta yakai kan zoben data bashi kafin su tafi an rubuta "SABSU" asaman, dad'i taji data gani a hannunsa, kamal yace mun tafi sena zo gobe, suhail yace okey "thanks" sannan suka tafi.
Ahanya kamal yace ni kikama haka ko wifey, tace "am sorry sweet" yace bawani "you are sorry" na fasa kaiki gida goben se jibi idan na tafi suhail da hafsat zasu kaiki. Atake ta marairaice tace haba sweet wlh ba haka mukayi dakaiba fa, yace tobakece kika kaucewa sharad'inaba, tace to "am sorry luv", yace naki sorryn. Kallonshi takeyi aise dabara yazo mata tasa hannunta akan ciyanshi tanata tfy da hannunta harkanshi atake yace "alright na hakura my luv am sorry too". Sabreen tayi dariya hahhh tace yaro yaji tsoro, dariya yayi yace koma dai menene naji muje gida tukun yana kallonta itama dariyan takeyi yanajin kaunarta yana k'aruwa a ranshi
       Sad-Nas






[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANATAINA
 
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
103-104 Kuka sosai sabreen takeyi dajin muryan kamal d'inta. Bayan sun d'an samu nutsuwa ne se Incle D yace yakamaya amaida sabreen d'akinta donyin takaba. Haka aka maida ita maman munirane tazo ta zaina da ita dasu kaka duk suna gurinta. Da akayi kwana bakwai da rasuwanne su Aliyu suka koma tare da uncle D amma mummyn kamal tana nan tare da sabreen agidan da kyar suke sata taji abinci. Desa mummy tayi 1month sannan suka tafi pakistan da suhail. Har kabarin kamal su sadiq suka kaishi nanma yayita kwalla suka mashi addu'oi sosai sannan suka tafi. Kowa seyayiwa suhail ta'aziya don kowa yasansu tare.
***
Sabreen tayi 4month 7day sesu mummy suka dawo nigeria ita da suhail da uncle D, saura 3days ta fita takaba.
Malamin,sunna suka samo lokacin data fita takaba aka raba gado domin saukewa mamacin nauyi, komai na kamal suhail ya tattaro ya mikawa umcle D, aka rabawa mummy da sabreen gadonsu. Inda aka barwa sabreen wannan gidan da take ciki da kuma kud'ade masu yawa. Tunda ake rabon taketa kuka tana tuna cewa yanzu shikenan bazaka dawoba yah kamal. Hakuri aketa bata har aka gama aka watse, kudin sanreen ta mikawa suhail tace aje a gina masallaci dashi ayitawa mijinta addu'a Allah ya gafarta mishi.
Yadda takeso haka akayi gidanne kawai suke zaune a ciki itadasu kaka.
Kafin mummy su tafine aka taru mummy tace suhail kaji abinda kamal yace bakace komaiba, shuru suhail yayi baice komaiba, uncle D yace sujail lokaci yayi da zakayi aure tinda dama akwai maganan aurenka da hafsat to kar'a tsaya b'ata wani lokaci seka auresu dukkansu biyun, mum tace tabbas haka ya kamata suhail kayi hakuri, sabreen tace mummy kuyi hakuri bazan iya auren yah suhail ba. Mummy tace sabreen nasan abinda kikeji dan kiwa nima ya faru dani amma ki daure kodan cikawa mijinki burinsa. Sabreen tace mummy kuyi hakuri hakan bazai yubane seta mike zuwa d'aki tanata kuka. Baban munira yace inaga da an kara mata lokaci tukunna, uncle D yace haka za'ayi suhail ka zauna mu zamu koma pakistan ke kuma hafsat kiyi hakuri kinga ba haka akasoba amma muna namu ALLAH na nashi, fatanmu shine Allah ya sanya alkhairi, mummy tace dan Allah suhail ka shawo kanta dan ayi da wuri, suhail yace to uncle naji kuma na amince zan aure su biyun. Sukace Allah ya baka albarka Allah ya sanya Alkhairi aka amsa da ameen sannan suka watse.
Wasje gari su mummy suka tafi bayan nasiha datayiwa sabreen ita da uncle d. Kaka dasu maman munirama sukace ta amince ta aureshi ai zata dinga ganinshi a matsayin kamal tunda aminaine, musammanma kaka dayan komai. Ita dai sabreen batace musu komaiba se hawaye da takeyi.
Tun daga wannan ranan hafsat bata sake zuwaba, kuma ko so d'aya bata kira sabreen a wayaba. Abin ya dami sabreen kuma tasan dalilin hakan, koba komai hafsat ta zama kawarta sannan kuma ace zasu had'a miji d'aya, kai wani se mutuwa ko sabreen ta kira wayan hafsat bata d'auka harta gaji ta dena kira.
Rarrashi sosai mum tayiwa hafsat tate da nasiha amma duk bai shige hafsat ba, dan aduniya idan akwai abinda ta tsana shine KISHIYA sannan kuma ace kawarta sabreen, inah gaskya da sake.
Wata bakwai kenan da rasuwan kamal, yaune mum tacewa suhail yazo gurin sabreen ta batun aurensu, hafsat tana jin haka ta wuce d'aki rai ab'ace suhail yana ta binta da kallo yace mum wannan abun zaiyu kuwa? Mum tana tausayawa d'an nata tace zaiyu insha Allah menene damuwarka? Suhail yace mum hafsat bazata tab'a amincewaba, mum tace zata amince tashi kaje gun sabreen ka barni da ita, ba musu ya wuce se gun sabreen. Bayan sun gaisa dasu kakane se maman munira taje ta kira sabreen himar nata har k'asa tazo palo ta zauna ko kallonshi batayiba bare tace mishi wani abu.
Suhail ya rasa me zaice har na tsawon mintina sannan yace sabreen ya karin hakuri? Tace Alhamdulillah, yace to Allah ya jikanshi ya mishi gafara, tace ameen tana hawaye. Suhail yace sabreen nasan kinsan abinda ya kawoni, ina fata zaki amince da bukatar kamal dukka cewa haka ya d'ade a zuciyata nikam, dan haka kiyi hakuri sabreen dan Allah ki amincemin, sabreen tace yah suhail kabar zancennan nizan zauna haka wlh, suhail yace bazan yadda da hakanba sabreen pls ki amincemin, sabreen tace yah suhail hafsat fa, kasan ko wayat ta dena d'auka yanzu, ina mutunta kawancemu bazan iyaba kayi hakuri kawai. Suhail kamar,zaiyi kuka yace sabreen pls kinsan na soki tun farko amma daga baya na hakura nasawa raina cewa zan auri hafsat amma ki sani bazan iya kaushewa abokina kudirinsaba inaso in cika mishi burinshi ne sabreen, duk kaunar da nake miki ban tab'a fatan kamal ya mutu in aurekiba wlh inason kamal kamar yadda nake son kaina sabreen pls
Sabreen zata bud'e baki da nufin cewa bata yardaba se SALMA ta toshe mata baki sannan tayi muryan sabreen d'in tace shikenan yah suhail na amince. Dad'i yaji sosai har cikin ranshi yace "thankyou sabreen nizan tafi kijeki huta, salma tace toh sannan ya tafi...
        Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
      By Mmn Shureim
             (Sas-Nas)
105-106 Sabreen ta juyo tana kallon salma sannanne salma ta sake mata baki tare da cewa kiyi hakuri sabreen. Sabreen tace salma baki kyautaminba wlh, salma tace nasani sabreen shiyasa nace kiyi hakuri, sabreen kin dad'e kina son suhail a ranki shi kuma kinsan ke kad'ai ce a ranshi bayan ke ba wata se hafsat 'yar'uwarsa da ake son had'asu. Sabreen tace salma shine matsalan ai, salma nafi hafsat kishi nesa ba kusaba, sannan kuma hafsat kawatacefa tare muke komai idan na auri mijinta na mata adalci kenan, yanzu haka bama ko sannu da hafsat salma abin yana damuna sosai da wanne zanjine, da rashin yah kamal nah, koda fushin hafsat agareni? Salma tace duk nasan da haka sabreen inaso kisan cewa kamal yatafi kenan bazai dawo garekiba har abada, kuma duk soyayyar da kike mishi wanda ya baki aronshi ya fimu sonshi, sabreen kamal addu'anki kawai yake bukata a yanzu, kinji da kunneki abinda yace miki, yace indai kina sonshi to lallai ki auri suhail amininsa hakan zaisashi farin ciki, sabreen karki damu da hafsat kishine namu na mata kuma koda kece a matsayinta haka zakiji, hafsat zata koma normal zata fahimta amma se daga baya, for now kibar hafsat pls sabreen. Kuka sosai sabreen takeyi tace duk naji salma, kinsan matsalata kuwa, inada mummunan kishi salma ina tunanin zaman da zamu da hafsat ne, inada hakuri akan komai amma banda kishi. Salma tace na fahimceki sabreen karki damu kiyita addu'a nima,zan tayaki Allah ya saukaka miki kishin dake da hafsat d'in dukka. Rungume juna sukayi sabreen tana ta kuka salma na rarrashinta.
Suhai da hafsat ne zaune yana mata nasiha hafsat ki sani cewa ita kanta sabreen baso takeyiba wlh da kyar ta amince badan komaiba sedan wasiyan abokina, hafsat kinfi kowa sanin halin sabreen dan haka zakuyi zaman lfy da ita, kuma nima ba kahan nasoba ke kin sani, amma idan bazaku bani had'in kaiba shikenan duk zan hakura in auro wasu daban tunda nima so kuke kuga na dena numfashi. Da sauri hafsat ta d'ago da kanta tana hawaye tace shikenan yah suhail na amince, amma ina da sharad'i, suhail yace ina sauraronki, hafsat tace dukda dai naji ance rana d'aya za'a d'aura aurenmu amma nice uwar gida, kuma gida d'aya zaka ajiyemu. Suhail yayi ajiyar zuciya yace na amince hafsat kece uwargidana, kuma zan had'aku gida d'aya dukda dai bani da niyan hakan amma na amince. Hafsat tayi murmushi tace nagode.
Sabreen tana kwance tana tunanin kamal se wayanta ya fara ringing, number suhail ta d'auka hello, suhail yace hello sabreen ya gida, tace lfy, yace dama inaso muyi magane akan bikin, sabreen tace inaji, yace sabreen za'a d'aura auren nanda 1month kuma gida d'aya nake son had'aku, sannan pls kiyi hakuri za'a fara d'aura na hafsat ne kafin naki. Sabreen tace banida matsala yah suhail, duk yadda kayi daidaine aguna. Dad'i yaji har cikin ransa yace "I LUV U SABSU" i luv u so verry much. Hawaye itama sabreen d'in takeyi batare datace mishi komaiba. Suhail ya kira sunanta a hankali SABSU? Hawayenta ta share tace inaji, suhail yace "are you okay"? Cikin muryan kuka tace "no am not" am missing him soo much suhail. Kukane yazowa suhail bai iya ce mata komaiba seya katse wayan...
   Hmmm soo sad
      Sad-Nas
TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
107-108 Tun daga wannan ranan suhail sedai ya kira sabreen a waya amma baya zuwa gidan kamar yadda ta sharad'a mishi nata sharad'ad'in. Dukda cewa yana son ganinta, amma sam tak'i.
Aunty rukayyace wanda ta koyawa sabreen girki a gidan kamal ita tazowa sabreen ta'aziya, daga nan sabreen take gaya mata zancen aurenta da suhail aminin kamal kuma su 2 zai aura. Washe gari aunty rukayya ta dawo gun sabreen da tsumi kala kala masu kyan gaske ta bata, godiya sosai sabreen tayi kuma tana amfani dasu koda yaushe. Biki saira sati ne aunty rukayya ta kawo mata cida kaza wanda akeyinshi da nonon rakumi da kuma rid'i a gabanta sabreen ta cince tas tana hawaye tace aunty rukayya ko lokacin airena na farko banyi wannan ba. Da kyar aunty rukayya ta rarrasheta har dab magrib kafin ta tafi.
 
Suhail ya kasa hakurin rashin ganin sabreen 3weeks kenan baisata a idoba, yau dai biki saura 5days sabreen taje saloon wanke kanta se suhail yazo gidan kakane ya gaya mishi inda taje. Suhail ya bita har saloon d'in yana jiran fitowanta a waje, can segata ta fito tana sanye da after dress black tayi kyau sosai. Kan titi ta nufa tana jiran keke nape sega wata had'add'iyar mota harta wuce seta dawo ta sauke glass saurayine handsome yace salam 'yan mata pls 2minit, sabreen tace kayi hakuri ka wuce, yace bazan iya wucewaba seya bud'e mota ya fito. Da sauri suhail yanifo gunsu tare da bud'e mota yazo har inda sabreen take tsaye yace am sorry wifey na ajiyeki dewa let go yanayiwa saurayin wani irin mugun kallo. Ita kuwa sabreen wucewa tayi ta shige motan suhail ta zauna, shi kuwa se kallon juna sukeyi da saurayin sannan yajuya ya shiga motanshi amma bai tayar ba. Suhail ma ya wuce motarshi yaja suka tafi a 260 ranshi a b'ace. Wannan saurayin take ya canja kamanninsa zuwa MUHSIN da SALMA se dariya sukeyi daga nan suka tafi.
Sabreen setaji tsoron suhail ya kamata yadda taga ranshi a b'ace ko kallonta baiyiba har suka isa wani gurin hutawa flowers masu kyaune agun. Bayan ya tsaya da motanne ya juyo yana kallonta ranshi a bace yace meyasa bakicemin zakije saloon ba inzo in kaiki? Shuru tayi tana sauraronshi kanta a sunkuye, yace sabreen dake nakeyi cikin miryan mai had'e da tsawa, nan take ta fara hawaye seyaji tausayinta ya kamashi, hannunta ya kamo yace am sorry sabreen rainane ya b'aci lokacin danaga wani kusa dake "pls stop crying", sabreen ta janye hannunta tare da d'aga kanta ta kalleshi tace tun baka aureniba ka fara sani kuka yah suhail amma kamal bai tab'a ko b'atamin raiba kana nufin haka zan kasance a tare dakai kenan? Suhail ya sake kamo hannunta yace am so sorry swteetheart hakan bazai sake faruwa pls kinji, hanki ya ciro yana share mata hawaye tace "take me home"  suhail yace "sabreen pls talk to me" tace just take me home suhail tare da sake janye hannunta. Jikinshi a sanyaye yajasu se gida, har zata fita yace tunda bakya sona yanzu gara nima inje inda kamal aminina ya tafi yafimin. Sam bataji dad'in magananba amma haka ta wuce batace mishi komaiba tanaji yadda ya fisgi motan da karfi ya fita, hankalinta a tashe ta wuce d'aki ta cire kayan jikinta sannan ta d'auki wayanta ta kira suhail harya fara ringing seya katse ya kira, ta d'auka hello yah suhail kayi hakuri pls, dad'i yaji aranshi yace toki fito ganinan dawowa, tace ok sannan ta kashe wayan.
Motan ta bud'e ta shiga fiskanta a sake tace sannu da dawowa, dariya suhail yayi wanda ya sake fito da kyawunsa dukda dai yarame sosai, sabreen tace nadad'e banga dariya a fiskan kaba, yace aike kike hananiyi, ajiyar zuciya suka sauke atare se suhail yace yau zanci abinci sosai sannan zan kasance cikin farin ciki. murmushi sabreen tayi sannan ta ciro zobe daga post d'inta tabawa suhail, wannan zobennedai wanda aka rubuta SABSU a saman, karb'a yayi yace "thankyou" tace ai dama nakane. Kud'i mai yawa yasa mata a pos d'inta yace kiyi hidima dasu idan bai isaba kigamin itama hafsat na mata nata, sabreen tace nagode. Suhail yace su sadiq sunce ayi dinner kina so? Sabreen tace duk yadda kuka tsara, suhail yace sabreen are you okey? Tace yes am fine SABSU, dariya yayi amma yasan akwai abinda yake damunta tak'i gaya mishine kawai, ya sake cewa sweetheart tell me something pls yana rik'e da hannunta, kallonshi takeyi har cikin ido setana ganinshi a matsayin kamal sweet d'inta, shi kanshi suhail ya lura da irin kallon da take mishi take jikinshi yayi sanyi kumaya kasa dena kallonta kawai seyaga tana hawaye tana cewa sweet tare da shafar fiskar suhail ta matso da fiskanta dai dai da nashi seta fara kissing nashi tare da rufe idanunta, shi kuwa gogan naku tsabar rikicewa se tsotsonta yakeyi
Nidai Sad-Nas haka nayi

0 comments:

Post a Comment