❣🤦🏻♂ KUSKURENA❣🤦🏻♀
{The story is Interesting! Attractive! Impressive! to cut a long story the story is a fascinating story the readers will entertain and enjoy it.}
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
**************************************
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
_*BY*_
_*©, RAMLERT Y SALIS*_
_*(NAZRA /FIRRAM )*_
~08164530838✍🏻~
*_No part of this book maybe an object of privacy✖_*
Sun , March 17 , 2019.
_*Page 10......*_
Dayake momy idan zatayi waya a handsfree take sawa, sakina dake la6e tanajinsu har abinda Karina take fad'a.
Hawayene suka fara wankewa sakina fuska fargaba tashin hankali ta tsinci kanta aciki, Kisa kisa tayi ta maimaitawa a zuciyarta aranta tana cewa" Innalillahi wa'inna"ilaihirraji'un, Dama momy bata tsoron Allah? Momy zata iya kashe mutum dama? " ta Shiga rud'ani sosai hankalinta yayi matuk'ar tashi mamaki ya mamayeta k'irjinta sai dukan 3_3 yake.
Da wanine yace mata mahaifiyar zata aikata haka bazata yadda ba amma sai gashi taji da kunnanta, momy ce taciga da cewa, kinga idan nabawa 'yan aiki suka Sa mata da taci sai lahira idan yaso ko d'aga bikinku dashi sai ayi tunda za'ace matarsa ta mutu dole za'a d'aga.
Karima Tace, momy kisa? Anya bazamu aikata *Kuskure* ba momy kuwa, gaskiya ina tsoro momy Mu canza wata shawarar amma banda kisa momy.
Ke ! momy ta daka mata tsawa, Matar da zata zama kishiyarki itace kike tausayi? Kinsan ita me zata shirya miki ne?
Karima Tace, momy ba wai hk bane kawai ina tsoron wani Abu ya biyo bayane, Ni a ganina a kuma gara a kuma yimata sharrin kwarto da akasheta amma yadda kika gani momy.
Momy Tace, baki da hankali wlh waya fadamiki hk ta bar safraz idan ba ta asircesa ba ya za'ayi adaren aurensu na farko ya kamata da kwarto amma yacigaba da zama da ita kiga pa sharrin da aka kulla mata a daren aurenta na farko amma babu wani Abu daya biyo baya.
Karima tace, hkne momy amma Be kamata Mu aikata kisa ba sabida ina tsoro wallahi.
Momy taja tsaki sannan Tace, shikenan dama ai ke zanyiwa gata tunda hk kikace yawuce, amma kisani pa nacire hannuna a cikin wannan lamarin ko safraz ya aureki ko bai aurekiba matsalarkice.
Hankalin karima ya fr tashi domin tayi nisa a son safraz idan bata auresaba gani take kamar mutuwa zatayi, Da sauri Karima Tace, momy pls kiyi hakuri Dan Allah I don't mean that, shikenan shikenan ayi yadda kikace momy.
Momy Tace, ko kefa amma da kina Neman kawo matsala, yarinya ina hango miki daula da rayuwar jin dad'i safraz yana da makudan kud'i hkm mahaifinsa ga mulki kuma.
Wani dad'i Karima takuma ji Tace, shiyasa nk jidake momcyna Allah ya barmanake.
Hirarsu suka cigaba dayi daga bisani sukayi sallama, sakina dake la6e a bayan falon tana jinsu tuni gumi ya gama jikata, da k'yar take d'aga k'afarta tayi hanyar get ta fita a gidan.
Kai tsaye gidansu aminiyarta Asma ta nufa, Sun dad'e suna hira sannan sakina Tace, Asma Inason fad'amiki wata mgn.
Asma dake fito da littatafai a jaka Dan suyi karatu Tace, Tom sis inajinki Allah yasa ba lbr wannan bazan lecturer zakimin ba danni na tsani ko lbrnsa wlh.
Sakina tayi murmushin k'arfin hali Tace, ba lbrnsa bane tunda kince bak'ya yinsa aybaza'a miki dole ba.
Asma Tace, menene sis naga fuskarki kamar akwai matsala ?
Sakina da ta kasa daurewa sai hawaye ya fara fita a idonta.
Subhanallah sis meye hk wlh kinsa zuciyana ya karye, cewar Asma.
Sakina ta goge hawayenta ta kalli Asma Tace, akwai matsala babba sis bawai zan tona miki asirina bane narasa wazan tinkara da mgnr ne.
Asma da tuni jikinta yayi sanyi Tace, Meke faruwa sis in sha Allah zamu samu mafita?
Sakina Tace, Asma akan lamarin aurena da safraz ne wani sabon al'amarine Wanda ban taba tunani daga mahaifiyata da Aunty karima , Sai hawaye ya fara bin kumatun sakina Anan ta kwashe dukkan abinda taji lokacin da momy da Karima suna waya.
Tun kafin ta gama fad',amata itama Asma tuni zufa ta fara jik'ata.
Sakina tacigaba dacewa, Wannan wacce irin rayuwa ce Asma nidai a yadda bake zuwa gidan uncle safraz na fahimci babu zaman lpy da jituwa a tsakaninsa da matarsa amma ban ta6a tunanin momy da aunty Karima sunada Sa hannu acikin ba, Asma wallahi ban ta6a tunanin mahaifiyata zata iya aikata kisaba. Sai ta fashe da kuka.
Itama Asma rasa abin cewa tayi, sai zuwa can tace , Stop crying pls wipe your eye sis, cry is not our solution now.
Asma taciga dacewa, Tabbas abun bazai miki dad'i ba koni nayi bak'inciki sosai Wanda nasan ke sai kin fini ji, To amma me we have to thank God tunda har basu kai ga aikatawa ba mukuma sai Mu warware lamarin cikin yardar ubangiji.
Sakina Tace, Asma yanxu what's the solution?
Asma ta nida zuwa can Tace, iya abinda tunanina ya bani babu Wanda yakamata Mu tinkara da maganar nan sai Aunty izzatu.
Dup ! Sakina taji k'irjinta ya fad'i , tana zaro ido Tace kamar Yaya sis? Aunty izzatu zan sanar da ita abundake faruwane?
Asma Tace a'a ba hk nake nufiba, kinga da farko bamuce zakije ki tinkari momy da wannan zancen ba Bazataso ace kinsan sirrinsu ita da yayarkiba inada tabbaci bazata saurarekiba kuma zata iya gargad'in idan wani yasani zata fad'i wani mummunan Abu akanki kinga ba yadda kika iya zakiyi shuru dole idan kikaji tsoron furucinta, idan kuma kikace Mami mahaifiyar safraz zaki tinkara da wannan zancen itad'in k'anwar mahaifiyar kice hakan zai iya lalata alakarsu da zumuncinsu dukda Mami mutum ce me sauk'in hali amma bazata ta6a jin dad'in kashe matar d'anta da yayarta take yunk'urin yiba dole safraz zai San zancen idan mahaifiyarsa tasanj zai dena ganin girman momy dole zai fasa auren aunty Karima itama aunty izzatu zata sani abun dai bazai kyauba, Amma kinga idan muka tinkari aunty izzatu da wannan maganar Mu dakatar da ita daga cin abinci 'yan aikin nata idan ta kama Mu sanar da ita abinda yake faruwa dole Mu sanar mata bazatak'i rufa asiriba sabida ke bakya tare dasu bakida wata manufar cutar da ita zata fahimta wlh, kinga anrufa asiri sukuma muyita musu addu'a Allah ya ganar dasu saiki ta yiwa momy nasiha cikin dabara tunda ba yadda kika iya mahaifiyar kice .
Sakina kuka ta fashe dashi me ban tausayi sai datayi me isarta sannan ta kalli Asma Tace, Hkne Asma wannan shawarar taki haka zanyi, Nagode sosai Asma ina alfahari da samun k'awa kamarki Dan Allah Mu rufe wannan maganar dagani sai ke.
Asma Tace, karki damu sakina zaki sameni me rik'emiki sirrinki in sha Allah.
Sun tattauna akan lamarin sosai sannan sukayi sallama ta nufi gidan Mami.
Momy tana zaune a falo Abu da ma'u suka shigo bayan sun gaisheta ta amsa.
Momy ta kallesu tace , Babu lamarin wasa a maganar dazan fad'a muku Ku kiyaye idan ba hk ba komai zai iya faruwa daku, Jakar dake gefenta ta bud'e ta d'auko wata farar roba kamar ta magani ta mik'awa Abu ta kar6a, Momy taciga dacewa, Inason gobe idan safraz ya tafi office Ku tabbata Ku zubamata acikin abinci taci kuma Ku tabbata ita kadaice zataci abincin kar safraz yaci na fad'a muku sai idan baya nan zaku Sa mata Ku kiyaye wannan.
Abu ta kalli momy Tace, Hajiya angama in sha Allah za'ayi yadda kikace.
Momy tace , Rabin murfi zakusaka mata sannan sauran ku zubar dashi Ku jefar da robar a inda kwata_kwata bazata gantaba.
Hk suka tashi suka baro gidan momy akan hanyar su komawa gidan safraz ma'u take cewa Abu "Ni gaskiya bazan aikata kisaba badaniba wannan aikin wlh idan kai kaga zaka iya to sai kayi Amma duk abinda ya biyo baya babu ruwana gaskiya, Son kud'i ba hauka bane Ni a gobe ma zan koma kasuwa incigaba da harka d'audu yafiyemin wannan mak'ircin da'ake shiryawa.
Abu Tace, Aikin bazan kai kasani takarema cikin talauci inaga kafison hk A sauka lpy har suka k'arasa gidan ma'u bata k'aracewa komaiba.
Lokacin da sakina ta k'arasa gidan Mami da alamun damuwa a fuskarta hakan yasa Mami ta dinga tambayarta Amma sai Tace mt ciwon kai take fama dashi, daga k'arshema sakina ta tashi a falon ta tafi d'akin Shaheeda tayi kwanciyarta har gari ya waye.
Da sassafe sakina ta shirya ta kalli Shaheeda tace , sis idan Mami ta tambayi inda naje kice mata akwai marasa lpy danzan duba a hospital zuwa anjima zan dawo, Shaheeda Tace, Tom Anty sakina a dawo lpy.
A dai_dai k'ofar gidan safraz adaidaita sahun ya sauk'e sakina.
~Sannu_sannu kwana nesa muje zuwa page 11 yau da gobe batabar komaiba.~
0 comments:
Post a Comment