Blogroll

BANNER 728X90

Saturday, 30 December 2017

'Yar Jami'a Part 7 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI

'YAR JAMI'A Part 007 . 

Cikin sark'ak'iya tare da b'acin rai haka beauty ta mik'e ta shiga zagayen d'aki kai kawon da take ne ba tare da samun wata mafita ba yasa ta tsagaitawa da zagayen nan ta shiga laluben d'akin,a saman wata ghana most go taga sallaya tare da hijab ai kuwa cikin sauri ta janyota ta zunbula har tana jan k'asa nufo k'ofa tayi da niyyar fita,amma ina tana kaiwa bakin k'ofa sai tai turus ta tsaya jin sautin hirar da suke a tsakar gida shi ya bata raunin gwiwar fita,ta d'an jima nan tsaye sai kuma can dabara ta fad'o mata labulen k'ofar ta janyo ta bud'e shi kad'an ta lek'a kanta ta shiga magana da k'ara tana cewa"d'an ladi ka je mota ka duba jakata na ciki ka d'akko min! . Hira suke sosai abinsu su sameer su kaji kamar daga sama ana magana!jimmn sameer ya d'an yi kad'an kafin nan ya tuna ashe kayansu na mota!d'an ladi ne ya fara cewa murya k'asa"d'an birni kaji wai jakar gimbiya na mota,murmushi sameer ya saki da jin kalmar gimbiya sai kuma yace toh je ka d'akko mata!kallo ya watso masa yace ai kasan ban iya aiki da na'urar bud'e mota ba!auff ashe fa haka ne muje toh,haka suka mik'e sameer na gaba yana biye dashi suka fita ba'a wani jima ba sai gasu da kaya nik'i-nik'i sun shigo,mai makon jakar beauty ta kasance a hannun d'an ladi sai gata a hannun sameer,yana k'ok'arin wucewa d'akin baba da k'aramar jakar sameer don ya kai mata sameer ya tsaida shi yace a'a wannan fa malam tawa ce kai min ita d'akin ka bara na mik'a mata tata!toh kawai d'an ladi yace ya wuce, shi ko sameer ya nufi k'ofa, a bakin k'ofar shima dai ya tsaya amma bai kai ga d'aga labule ba,wanda har lokacin beauty na tsaye wajen sai dai ta saki labulen ta jingina da bango ta ji sautin magana! Tabbas mai hali baya tab'a canja halinsa,a gaskiya dai anyi asarar shekaru,girma ya fad'i,wallahi ina mamakin kasancewarki tsatson wannan dangi na mutunci da girmamawa,sai dai kuma ta wani fannin ba laifi bane don naga haka don ko 'YAR JAMI'A shahararriyar karuwa ce!mai neman maza,wacce bata son kamun kanta ba,wacce take ikirarin kanta da beauty ma'ana kyakykyawa ko?toh Allah dai ya raba mu da kyawun d'an miciji!ameen! Yana kaiwa nan da maganarsa sameer ya wulla mata jakar ciki da k'arfi har ta kai ga buge k'afarta!amma ba yadda ta iya dole ta toshe bakinta da rad'ad'd'in da k'afarta ta bayar lokaci d'aya! Sameer ko daya wurga mata bai zame ko ina ba daga nan sai d'akin d'an ladi,itako beauty abinka da wacce rai bai saba b'aci haka ba komai ace dady sai ya zamana sabon abu a wajenta,haka ta daure ta ja k'afar da tuni dama ta gama tsami don dukan da ta sha da rana a asibiti,ta k'arasa gefen akwatin ta bud'e wata doguwar rigar kalar ruwan toka(ash)dai ta k'ara janyowa ta zura da yake duk dogayen rigunan ta kwaso don tasan halin tsoho sarai tun tana yarinya ba'a shigo masa ita gida da k'ananan kaya! Haka ta kammala shiryawarta tsaf tayi sallah sannan ta ci tuwo,Alhamdullah ta fad'a bayan ta gama cin abincin, duk da ba wani cin kirki tayi masa ba!abinka da ba'a saba ci ba! Tana k'ok'arin hayewa gado ne taji muryar baba yagana tana fad'in toh ina kuma kuke shirin fita haka,ko wacce amsa suka bata sai ji tayi tace toh ku jira ku kai min kifin rijiyata yawo tun zuwanta ba inda ta lek'a, Kafin ta iya wani kwakwkwaran motsi ina har baba ta shigo,yi tayi kamar bata ji shigowarta ba ta ci gaba da hayewa gado,ke meye haka kuma hajara?bacci tun yanzu?ai kuwa baki isa ba tasowa zaki ku tafi,kai baba mu tafi kuma ina? Fuska sake baba yagana tace dandali mana kije kisha kallo in da rabo sai ki sama wa d'an ladi mata daga nan ma! Don naga da alama ruwan ido ya masa yawa!cuskune fuska beauty tayi kamar me shirin kuka tace dan Allah ni dai su je kawai gajiyar hanya tayi min yawa gobe naje ni,had'e girar sama data k'asa baba yagana tayi ta matso saitin kunnenta tace mata kaga ja'irara banza mara wayo,ki shigo da yaro santalele fari sol wannan k'auyen ko kishinsa bakya yi ai ya ci ace duk motsinsa kuna tare,haka d'azu fa ina kallo suka fito ko ki bi su,saurin katseta beauty tayi ta shiga bubbuga k'afa na shagwab'a tana cewa ni wallhi baba yagana ki shiru don tsakaninmu ba dangin iya bana baba kawai had'in ummah ne tace ya rako ni! Janyo ta baba yagana tayi cikin fushi ta tsaya k'em a tsaye sannan tace toh yi maza zura takalmin ki mu wuce,yadda taga baba tayi fuska ba annuri yasa ta tilas ta zuwa suka fito daga d'akin a jere da juna! . A daddafe beauty ke binsu da kallon mamaki, to shin me d'an ladi ya shirya musu haka?kallo takai ga inda su d'an ladin suke nan taga sameer tsaye gefen dama sai wani matashi wanda da alama shine d'an mai garin, a hankali ta k'arasa inda suke badon taso ba haka ta koma gefen sameer ta tsaya don ta tabbatar ta tsaya d'ayan gefen sai ya mayar mata da magana! Tun tsayuwarta a wajen wasa ya fara kad'e-kad'e da wak'e-wake ke tashi sosai,a inda ko wane makad'i ke baje irin nashi basirar a salo na gargajiya,murna da farin ciki sosai kake iya ganowa a fiskokin kowane saurayi dake wajen inda kuwa 'yan mata ke cikin fili suna taka rawa d'an ladi da d'an mai gari sunai musu lik'i,wayarsa sameer ya fitar daga cikin aljihunsa a yayinda ya shiga vedio ya hau yo saboda wannan shne karonsa na farko da yaga abun gargajiya irin haka,sai ya zamana abin ya k'awatar da shi nesa ba kusa ba,beauty dake gefensa tana tsaye jugum tana binsu da kallo sosai ta shagala da kallo bata ankara ba taji an janyo hannunta cikin tsakiyar fili,d'ago kai tayi don taga wacece ai kuwa tayi ido hud'u da wata matashiyar bafulatana fuskarnan cike da fara'arta ta shiga juya mata hannu da nunin su yi rawa,duk da yadda rawa da wak'a suka zama jiki a wajen beauty sai gashi yau ta tsinci kanta da jin kunyar hasali ma duk sai take jin nauyin kasancewarta a filin,haka bafulatanar nan ta ci gaba da juya mata hannu amma sam tak'i yadda ta taka,ganin haka d'an ladi jiki na rawa yayo kanta ya shiga yi mata lik'i,can gefe guda kuma ya hango sameer tsaye sai d'aukar su yake a waya ai da saurinsa ya k'arasa ya kamo hannunshi sameer na kaucewa amma ina sai da ya kawosa cikin fili,kunya ya aje gefe sameer ya kamo hannun d'an ladi suka sha rawarsu suna yiwa juna lik'e,haka dai sukai ta sharholiyarsu a ranar abinda aka jima ba'a yi irinsa a dandalinba,sosai daren ya k'awatu ga kowanne saurayi da budurwa,ba su suka tashi a dandali ba sai 12:30,da haka ne kuma kowa ya kama hanyar gida inda su sameer suma suka nufo gida,beauty kuwa anyi k'awa bafulatana don har k'ofar gida ta rakota anan sukai sallama ta kuma shaida mata sunanta ladiyo! suna shiga kai tsaye d'akin tsoho duka suka wuce,beauty da ge gaba ita ta fara shigewa ciki inda ta iske d'akin cike da mutane har kawo wannan lokacin ga tsoho na kishigid'e gefe yana dariya wanda hakan ya nuna abin dariya akayi,sallamar tace ta katse su don haka suka juyo baki d'aya zuwa ga k'ofa,a d'an razane beauty ta ja da baya sanadin fuskar data gani yana dubanta,jiki na gyarma ta zube k'asa ta shiga gaisuwa,Alhaji ina wuni? Fuska d'aure wanda ta kira da Alhaji ya amsa da lafiya lau! ya wajensu ummantaki? Duk suna lafiya!sannan ta iya gaishe sauran bak'in dake wajen wanda da alamun Alhaji ne da iyalansa suka shigo don dattijuwar mace ke gefensa da matashin yaro!baba yagana ce ta katseta da tambayar ina kika baro mazan kuma? Nan ta amsata da gasu nan tsakar gida tsaye!bata kai ga rufe baki ba Alhaji ya jefota da tambayar ke wane maza kuma?yarda take mutuwar tsoron Alhaji yasa ta kasa basa amsa sai baba ce ta tari numfashinsa da cewa loh ai su d'an ladi ne sai kuma bak'on da suka taho dashi daga birni,bara na kira ku gaisa,nan take ta kwala musu kira suka shigo cikin girmama wa dukkan ninsu suka gaisheshi kafin nan tsoho cikin murya k'asa-k'asa yace sannu dai d'an nan naga magunguna dazu bayan fitarku yagana ta kawo min kuma nasha kamar yadda kayi mata bayani,ubangiji Allah yayi maka tukwici da gida ln aljannah yasa kaima kasamu mai yi maka!d'aki kowa ya amsa da ameen! Alhaji ne ya nemi su tashi su tafi tunda ya zama kamar al'ada duk dare sai sun raba hira a gidan k'anin nasa!haka sukai sallama suka fita har Alhaji ya kai bakin k'ofa ya juyo ya kalli beauty ake zaune manne da bango yace zuwa gobe sai ki shigo da bak'on naki waje na ina nemanku!mutuwar zaune kusan beauty tayi don da an auna jininta awannan lokacin babu shakka ya daskare!tsawa ya doka mata sosai yace baki jini bane, asukwane ta amsa da toh sannan ya fita! Mtsss kai Allah dai ya shirya wannan muguwar zuciyar taka wallahi ace mutum zafi kamar zaki,tsoho yayi maganar yana k'okarin mik'e,da sauri beauty ta taso ta fad'o jikinsa ta shiga rero kuka don tasan yadda ya yink'ura d'in nan wajenta yake son zuwa,babin lallashi da bada hak'uri sabo tsoho ya bud'e inda duk suka zama 'yan kallo a d'akin!can beauty ta tsagaita da kukan ta d'ago kai tana ajiyar zuciya tace wallahi tsoho shiyasa ko ummah tace nazo bana son zuwa kai kana sona amma Alhaji baya sona kullum fad'a se duka!janyota tsoho ya kuma yi ajiki yace yi hak'uri mutuniyar maza ce yagana ta kai ki d'aki kiyi bacci gobe in jiki na ya k'ara sauki zaki sha labarai!murmushi beauty ta sakar masa sannan ta tashi ta bi bayan baba yagana suka fita,inda suma dai su d'an ladi sukai bankwana dashi suka nufi d'akinsu! . _Karfe 07:00 na safe!_ Zaune take beauty ta gama cin karin kumallo kenan bayan wanka data gama,tashi tayi ta janyo wata jar doguwar riga mai ratsin fari a ciki ta saka kayan masha Allah abinka da farar mace sun karb'i jikinta ainun,k'aramin gyalen kayan ta yale kanta dashi kamar yadda ta saba ta shirya tsaf,baba yagana dake kwance saman gadonta na k'arfe tace sai ina kuma?fari beauty tai mata da ido tace sai d'akin tsoho kema dai kinsan wannan kwalliyar tsoho ce!dariya baba yagana ta kwashe da ita sannan tace ja'irar banza kya dai gyara zancen naki,don kin rai nani zaki ce haka mana tunda jiya da murnarki kika dawo daga dandali,toh kar dai ki manta da zuwanku gidan Alhaji,lokaci guda beauty ta d'aure fuska ta juyo ido narke tace dan allah baba yagana ki wani abu akai wallahi ni bana son zuwa don nasan tabbas fad'a kawai zan sha kinsa fa halinsa!fuska baba ta yamutse da jin maganar beauty sannan ta iya cewa toh ni me zance akai bayan kinsan halin kayanki,yanzu dai tsoho bacci yake don tun safe ya ci abinci yasha magani ya kwanta,ki tashi ki yiwa bak'onki jagora ki tafi can gidan tun safe kafin ya fita gona don kinsan ya d'akko zafin gona kanki zai huce!dariya duka suka saka tare sannan beauty ta zari takalmi da jakarta tayi waje! Tsaye take beauty bakin k'ofa ita bata shiga ba kuma bata koma d'aki ba,can dai ta lura tsayuwar nan ba yi mata zatai ba dole ta matso daf da k'ofar ta manne jiki da bango murya k'asa-k'asa tayi sallama,d'an ladi ne ya amsa mata amma da mamaki sai gani tai sameer ya bude labulen k'ofar ya fito,kallo d'aya yayi mata ya kauda kai,ita d'in ma dai kauda kan tayi k'asa tana son gaishe shi amma tana tsoron dizgi,dole ta iya bakinta ganin bata da niyyar magana yasa shi tamke fuska a kasalance yace zaki iya wucewa mu tafi ko?ba tare data tanka masa ba beauty ta shige gaba abinta ta nufi hanyar fita waje,bin ta tayi a baya,haka suka yi ta tafiya da yake safiya ce babu duk jama'a sai harkokinsu suke yi haka har suka isa k'ofar gidan, anan ne kuma ta ta tsaya a tafiyar ta juyo ta kalleshi tace nan ne gidan!wani kallon raini sameer ya fara binta dashi kafin yace in nan ne gidan ni zan shiga nai miki iso ki shiga kome?ta ji haushin kalamin nasa sosai duk da dama tasan bai zama lallai ya bata kyakykyawar amsa ba haka ta saka kai gaba ta shige gidan!kusan minti uku da shigarta sai gashi ta fito tace da sameer wai yace ka shigo! Kallonta kawai yayi ba tare daya ce uffanba, da haka ta fahimci abinda yake nufi ta shige ciki shi ko yabi bayanta! Alhaji na zaune tsakar gida rike da ludayi a hannunsa sai gabansa da kwanon koko ya cika shi taf,a hankali yana surb'ar kayansa yana had'awa da k'osai ya ji sallamar sameer!ludayin hannunsa ya maida cikin kwanon lokaci guda kuma ya shiga gyara babbar rigar dake sanye jikinsa,zama na kamala da manyance Alhaji yayi kafin yayi wa sameee iso daya zauna dama dashi,k'ok'arin zama beauty tayi kafin kace wani abu Alhaji ya da mata wata uwar tsawa ke shige ciki ki baiwa mutane waje, jiki na gyarma haka beauty ta afka cikin d'aki!kallon sameer Alhaji yayi akaro na farko ya sakar masa murmushi inda sameer ya sunkwi da kai cikin jin kunya a ladabce ya gaishe sa,amsa Alhaji yayi da fara'arsa har yanayi masa tayin koko,cikin dariya sameer ya amsa masa daya gode,shiru ya biyo baya na 'yan wasu lokaci sannan Alhaji ya nisa yace yaro ya sunanka?cikin nutsuwa ya amsashi da sameer! Jinjina kai Alhaji yayi na gansuwa da hakan kafin yace toh malam sameer tak'aitaccen tarihin rayuwarka nake son ji,sannan ka sani a hira dani ba'a k'arya don haka sai ka kiyaye,tom sameer ya amsashi sannan ya k'ara gyara zama sosai ya shiga motsa leb'ensa! . Da farko dai sunana Sameer Al-qaseem maji dad'i ni haifaffen garin yola ne mahaifina Alh.Alqaseem maji dad'i ya kasance k'asaitaccen d'an kasuwa a garin yola gashi kuma d'an siyasa,bayan sarautar gado da muke da ita ta maji dad'i da aka nad'a masa,hakan ne yasaka bayan zab'en da akai shekara uku baya muka dawo garin abuja da zama sakamakon zab'arsa a kujerar senator da akayi,mu uku ne a gurin mahaifina,na kasance babba sai k'anne na biyu mata aysah da salaha wanda duk suna zaune yanzu haka da mahaifana a garin abuja suna karatu,ni kuma nayi karatuna tun daga matakin karatu na primary kawo yanzu dana kamala jami'a nake bautar k'asa da nake yanxu a garin kano,gaba d'aya nayi a garin abuja wajen yayan mahaifina Alh.Aliyu maji dad'i da yake shi can yake zaune sai ya zaman to tun tashi na babana ya maidani wajensa saboda Allah bai bawa matarsa haihuwa ba sai dai in anyi hutu naje wajensu!bayan karatu na kuma a b'angaren kasuwancu yayan mahaifina tare muke harkokin company d'insa dani yanzu haka jira yake na gama bautar k'asa d'ina takaddun company daya bud'e min yana nan a garin lagos inda zan fara jan ragamar kula dashi dazarar na gama bautar k'asa! Wannan dai shine tak'aitaccen tarihin rayuwata! Ajiyar zuciya ta gamsuwa da abinda ya fad'a Alhaji yayi,yadda ya lura da tsantsar hankali da nutsuwa irin ta sameer yasa shi umartarshi daya rubuta masa lambar wayar mahaifin nasa dana yayan mahaifinsa a takarda,haka kuwa akayi sameer ya janyo wani k'aramin memo daga aljihunsa na gaba tare da biro ya rubuta masa,karb'a Alhaji yayi ya linke takardar ya zura a aljihu,da haka suka shiga 'yan k'anan hirarsu wacce duk bayanine akan sameer da zuriyarsa! . Duk labarin nan da sameer ke labartawa Alhaji akunnen beauty dake mak'ale baki k'ofa tana jinsu da yake d'akin bak'i ne sai ya zamana babu kowa ciki,shiru ya biyo baya nan take kuma ta shiga nazarin rayuwar sameer da yadda taji tsantsar nasaba da girma irin na gidansu,lallai wannan mutumin mai girma da karamci ne dole ya ki ni da duk wata halayya tawa toh yanzu da ace yana nan akai birthday d'ina inda muka sha rawa da maza a lokacin ai da bansan daga jiya zuwa yau wane irin zagi da tozarta zansha ba!tana cikin wannan tunane taji kamar daga sama Alhaji yana magana,lallai indai wannan itace rayuwarka ka tashi gidan girma da mutuntaka kuma ka dace duk inda kaje kaga abu kuma har ka yaba dashi toh abaka,don haka yanzu inaso ka gaya min gaskiya domin Allah daga saninka da hajara zuwa yau wane irin halayya ka fahimta tattare da ita! K'ululu.....k'arar cikin da sameer ya bayar kenan don shi kam anyi masa tambaya mai matuk'ar tsauri wanda shi kansa bai ma san ta ina zai fara ba inda akan rayuwar beauty ne,a yayinda beauty tuni ta gama daskarewa jikin k'ofa tana jiran shigowar Alhaji tasha duka don tasan yau kam kashinta ya bushe, jin yadda sameer yayi shiru yasa Alhaji k'ara jefo masa tambayar ta wata siga,yace kar ka d'auka na tambayeka haka da wata manufa ne a'a illah dai kawai ya kamata ace kasan wacece hajara sosai don kuwa ni azamana da ita akwai matsananciyar soyayya dana lura a tsakaninta da mahaifinta wanda hakan ya sanya ta sangarta mafi muni,har ya janyo bata ganin kowa da gashi ga shiga mara ma'ana amma zuwansu na k'arshe garin nan na horar da ita mafi k'ololuwa don a lokacin tana gab da fara shigarta jami'a don haka nake rok'onka daka gaya min meke wakana tun yanzu na gyara ta basai tayi aure abin yafi k'arfi na ba!duk da haka shiru sameer yayi don duk wasu k'ofofin kansa ji yayi an gama kulle masa su wai yau shine ake wa tambaya akan beauty haka?kafin yayi wani k'wak'wk'waran motsi suka ji sallama daga waje!tuni sameer ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya don kuwa yasan neman Alhaji akazo yi! Yun k'urawa Alhaji yayi yace ina zuwa daga haka yayi waje!bai jima ba sai gashi ya dawo nan ya nufo sameer ya zauna yace kaga abokin tafiya ta gona wato makwabcina yazo don haka zan baka damarka ka je gida yanzu,bazan d'au lokaci da yawa a gona ba saboda wannan muhimmiyar maganar dazarar na dawo can gidan malam zan nufa sai mu k'arasa maganar tamu! Cike da murnar zuci sameer ya amsa shi da toh Alhaji, Kwalawa beauty kira Alhaji yayi cikin sauri sai kuwa gata ta fito hannu rik'e da takalma don rikita,kallonta yayi yace ki mai dashi gida zuwa anjima zan shigo bai jira cewar taba ya nufi hanyar fita ya fice abinsa bayan daya d'auki kayan aikinsa a gona yayi waje! . Duk da jikinta ya gama bata sameer ita yake kallo a lokacin amma sam ta kasa d'ago kai ta kalleshi balle kwakwakwaran magana, takalmin dake mak'ale a hannunta ta zaro ta saka sannan ta nufi hanyar fita!ba tare da shima ya damu da hakan da tayi ba sameer ya bi bayanta! Shigarsu zauren gidan ne kuma labari ya canja don beauty ta gama fahimtar tabbas sameer zai tona mata asiri dole ya yanke shawarar ta sauke koda kad'an ne daga cikin girman kan da take ji ta nemi gafararsa!don hakan ne kad'ai zai ceceta yau a hannun Alhaji,yanke hukuncinta yayi daidai da tsayuwarta haka kuma sukwane ta juyo har suna kusan cin karo da juna ta tsaya, shima dai tsayawar yayi da sauri ganin yadda jikinsu ke kusan had'uwa yace lafiya dai?? Murya can k'asa beauty ta kira sunansa"ya sameer!! Shiru yayi yana bin ta da wani wulak'an taccen kallo har sai da ta k'ara kiran sunan nasa"ya sameer fa magana nake"anan ne ya iya samun bakin magana ya amsata"ya sameer kuma?yaushe na zama yayanki?ko kuma ince yaushe daddynki ya gaya miki bayan ke ya haifa miki wani d'an uwa sameer? Bata damu da zancen da yake ba haka taci gaba da magana,ya sameer don girman Allah kayi hak'uri da duk wani abu daka sani nayi maka ko kaji labari nayi ma wani wallahi sharrin shaidan ne!!what?? Kinsan kuwa me kike fad'a 'Yar jami'a??shaid'an fa kika ce?yarinya karki kuskura kiyi wa shaid'an k'azafi don kuwa bai miki komai ba!ganin yadda sameer lokaci guda ya tada jijiyoyon goshi yasa beauty sulalewa da gwiwoyi k'asa ta d'ago hannayenta sama tace ba don hali na ba ya sameer don girman mahaliccinka ka taimaka ma rayuwata,wallahi kana son jefa min rayuwata acikin mawuyacin hali! Dariya sosai sameer ya sakar mata har yana sark'ewa,sororo beauty ta bishi da kallo don tasan tabbas hakan zai faru dama!ke malama ki tashi muje ki nuna min hanya na koma gidan tsoho na jira Alhaji acan lokaci na k'ure min!cewar sameer yana gyad'a kai na mugunta!narai beauty ta kuma yi da ido tace haba ya sameer yanzu lokaci kake dubawa ba hatsarin da rayuwata take ciki ba?yanzu ashe yadda kake kiran sunan Allah dama duk a baki ne?ya sameer ka tausaya min mana!ganin yadda beauty ta duk'ufa da rok'onsa yasa shi had'e rai a karo na biyu ya daka mata tsawa"wai ke wace irin mace ce? nace ki tashi muje ko in baza ki ba just tell me sai na nemi mafita ama ba ki tsaya kina min wani zance mara anfani ba! . Ajiyar zuciya beauty ta saki can kuma ta mik'e jiki ba kwari ta kad'e k'asa da ta shafi kayanta ta shiga tafiya,bin ta sameer yayi tayi yana kuma k'ara gane hanya sosai har suka iso,har ta sa kai tana k'ok'arin shiga zaure taji yace ke? Da sauri ta juya kamar dama jira take tace na'am ya sameer!wani irin duka ya kai ma bango a zuciya kafin nan ya d'ago kai da tuni sun rud'e sun ja jur yace ba na ce karki k'ara kirana da ya sameer ba?call me wit my real name sameer don bana karb'ar tuban d'an muzuru,sannan kisani in har kina so asirinki ya rufu sai kin min Alk'awarin zaki sanar min da duk wani labari naki da dalilin da yasa kike wannan mummunan halayyar taki!saurin d'ago kai tayi jiki na b'ari beauty ta amsashi tana nuni da hannu wallahi duk abinda kake son ji zan gaya maka amma ba yau ba sai ana gobe zamu koma kaga yanzu lafiyar tsoho ya kamata mu kula da ita,kai kuma in Alhaji ya kiraka sai kasan abinda zaka gaya masa wannan shine kad'ai alfarmar da za kai min! Kallo mai cike da buk'atar amsa sameer ya jefeta dashi ran nan sam babu alamar annuri haka yasa hannu ya tureta can gefe daya ya shige gida abinsa! . Bai takura mata sameer ba har sai da tayi kukan ma'ishinta don kanta ta tsaya,sannan ta d'ago kai a hankali ta kalle shi,har lokacin sameer kan shi na gareta don haka ya kauda kansa a sanyaye ganin yadda beauty tai narai da ido,murmushin k'arfin hali ta saki mai cike da tambaya sannan ta dai-daita nutsuwarta ta shiga magana,"yau zata zamo rana wacce ban yi tsammanin kasancewarta a rayuwata ba,sai dai ina k'addara ta riga fata,babu yadda na iya dole na bud'e sirrin da bai kamata na bud'e shi ba don kuwa bani da wata mafita,ya sameer kamar yarda kasha kirana da sunan karuwa ban tab'a inkari akan haka ba, don duk wanda yasan hajara da halayya irin tawa dole duk sunan da aka kirani dashi na amsa,sai dai abinda baka sani ba koma ince jama'a basu sani ba game dani shine,wannan d'abi'a dole ta sakani yinta ba don naso ba!don kuwa na samo wannan halin ne" Adalilin principal d'in makarantarmu ta secondary school,da jin haka k'ara gyara zama sameer yayi sosai yana fuskantar ta don jin abinda ta ambata,nan ta ci gaba da magana,eh haka ne magana ta ba k'arya principal d'inmu itace ummul abaisi na duk rayuwar da muka tsinci kanmu aciki,sanin kan kane dai dady bazai sani makaranta mai arha ba,makaranta ta ajin k'arshe wajen tsadar kud'i wanda duk 'ya'yan masau kud'i yawancinsu nan suke yi anan nayi primary don haka bayan na gama na d'ora secondary,anan ne kuma wata rana muna zaune a aji da yake mun zo s.s.s3, bazan tab'a mantawa ba muna karatun geography sai ga discipline master yazo har aji ya kiramu mu uku,jiki na gyarma muka bishi duk mun gama bayarwa dukanmu zaiyi,sai bayan da muka fita ne yake shaida mana cewa principal ke nemanmu,haka ya samu gaba har office d'inta,bayan daya kaimu ne labari ya fara canjawa dayake mace ce principal d'in tana washe baki ganinmu ta shiga zayyana mana buk'atarta ta hanyar wayo da dabara"ta shaida mana cewa yanzu mune ajin k'arshe sannan tasan fatan kowannenmu shiga jami'a nan ta cigaba dacewa ita jami'a ba'a shigarta haka nan sai an shirya haka dai taitayi mana bayani muna ganewa ta kuma shaida mana da tazab'e mu muyi mata wani aiki ne saboda tasan 'yan gidan masu hannu da shuni kamarmu babu zancen takurawa ko matsantawa ta iyaye a tattare damu!bamu gama gane inda ta dosa ba sai da discipline master ya k'ara wayar mana da kai da cewa duk kanmu yana so mu kar muyi applying makaranta d'aya ta yadda zamu cimma burin janyo hanakalin malamai maza,ko wacce d'aliba ta yi k'okarin kawo nata toh darajarta zata k'aru sannan akwai wasu mak'udan milliyoyin kud'i da bayan shekara hud'u za'a bata!jin yadda suke jaddada miliyoyin kud'in anan yasaka kowannen mu amincewa,hakan ya saka bamu tashi a wajen ba duk sai da aka bamu somin tab'i na naira dubu d'ari biyu da hamsin!tare da yarjejeniyar ya zama sirri a tsakaninmu,toh tundaga wannan ranar kullum sai mun je office d'in principal bayan an tashi a makaranta ta k'ara wayar mana da kai yadda zamu janyo hankalin malaman jami'a yayin da muka shiga! Hankalin ummah ya fara tashi in ban manta ba tun daga ranar data fara ganin d'abi'u na da tarbiyyata ta canja duk da dama ba wani tsauri nake samu ba tunda dady na nan kuma baya son b'acin rai na,kullum rigimar daddy da ummah bata wuce akai na,haka har mukayi jarabawar waec da neco amma duk ummah ta lura ba wani karatu nake ba illah dai kad'e-kad'e da wak'e-wak'e da suka zama jikina,ga kud'i da nake kashewa baji ba gani,wasu dady ke bani wasu kuma principal ke turamin ta account tunda duk ta bud'e mana account,wata rana dana karb'o kud'i daga banki ko dana shigo gida na taradda dady a parlo dole nima na zauna,dana tashi mik'ewa ne tsautsayi hannun jakar ya bud'e wasu mak'uden kud'i suka zubo,wato a lakacin ba ummah da dady ba harta ni kai na sai da gaba na ya yanke ya soma gyarma,amma da yake dady baya son ganin laifi na sai yayo sauri mik'ewa ya fara kwasar kud'in ya mayar min jaka sannan ya kamo hannu na mukayi d'akina,turani ciki kawai yayi shi kuma ya wuce nashi d'akin a ranar ne ummah ta fara gaba da ni wai na fara samun kud'i daga waje,wanda ni kuma tun daga lokacin na fahimci ummah bata so na,bata son cigaba na arayuwa daddy ne kad'ai ke so na! . Haka rayuwa ta jin dad'i da daula taci gaba da wanzar min har ya kawo lokacin da na samu admission zuwa jami'a ranar ji nayi tamkar na zama millioner gani nake nesa tazo min kusa,da murna haka na kira na shaida musu,wanda suma murnar sukai tayi min! Tun kafin sati d'aya da fara shigowata jami'a tuni na ziyarci duk wani kanti na kaya,mak'il haka na cika drawers dina kaf da k'ananan kaya,takalma da jakunkuna,duk da naso siyan gyale ko da k'anana ne amma principal ta hanani acewarta zasu rage min kwarjini kuma zasu b'oye min kyaun halitta! Shiru beauty tayi da ta kawo nan a hirarta ta kai hannu fuska,mak'alallen wahayen dake shirin sauka a kuncinta ta goge had'e da jan majina!tsintar kanta tayi beauty ta k'in ci gaba da labarin har sai da ya nemi da taji gaba sannan tayi gyaran murya taci gaba! Tun daga ranar dana shiga jami'a tunani na bai wuce ta wacce hanya zan samu na cimma burina cikin sauk'i ba,sai kuwa gashi na samu malam umar,mutum na hannun dama a b'angaren neman mata da kud'i na iya samo kanshi don na sakar masa kud'i iyakar sakarwa kafin ya had'a file guda na duk wasu sirrika na malaman makarantar ya bani,ita kuma k'awata zee-zee tunda na fahimci 'yar abi yarima asha kid'a ne sai na rik'eta na fara sakar mata kud'i don sune matsalarta duk da agidan ma bata tsiraba,mahaifinta mutumin kirki ne ga kula da hak'k'in iyali amma mahaifiyarta 'yar Allah bamu musamu ce,ita dai a bata kud'i shiyasa kullum cikin samari masu mota take wai a haka baban na sa ido kenan! Ina ganin wannan shine abinda kake son ji ko? Tana tambayar ne tare da maida dubanta ga sameer tana kallo!d'ago kai yayi shima dai ya kallota don abinda yake da muradin ji har kawo yanzu bai jiba nan take kuwa ya fara jefo mata tambayoyi! "Daga shigarki jami'a zuwa yau malamai nawa kika had'ata dasu?kuma ke nawa ne sukai anfani dake? A kid'ime beauty ta zaro ido cike da mamakin tambayarsa ta k'arshe inda shima ya zaro mata nasa da zummar eh amsarta yake jira!tab'e baki beauty ta yi sannan ta kauda kai gefe guda cikin murya can k'asa tace mutum goma na kai mata,ni kuma babu,ban gane babu ba?babu me?sameer ya tambaya! sunkwui da kai sosai beauty tayi don tasan bai zama lallai sameer ya yarda da amsarta ba ta k'ara nanata masa da babu d'a namiji ko d'aya da muka tab'a keb'ewa ko ta minti biyar a wajen makaranta dukkan ninsu a waya muke magana bayan na fahimci yanayin mutum toh sai na bashi address nata,wannan shine silar da ya saka ko wane course bana fad'uwa tun shigata jami'a kawo yanzu! Shima prof KAS da kaga abu ya had'amu na zagaya kuma na zagayo na ga babu wata hanya da zan iya samun makin da nake so dole sai nayi masa abinda nayi masa shiyasa hakan ta faru,bata kai ga rufe baki ba wata tambayar tabiyo baya"toh abincin da kike rabawa na stop and chop shi kuma sadaka ce ko kuwa zakkah?kai duk'e tana kallon k'asa tace shi kuma neman suna ne kawai da son shahara don sun tabbatar min hakan zai saka kowa ya san da zamana a jami'a! . Shi kuma kamal dana ganku tare a mota wancan satin darasi yake koya miki? a'a beauty ta bashi amsa sannan tace shima munje can sau biyu! Wani gauran numfashi sameer ya saki mai cike da tuhuma ta b'angare d'aya kuma yana jin dadin yadda yake kallon gaskiya tsagoronta a idanun beauty !dole ya danne yanayin da yake ciki kwallon hannayensa wanda yake wasa dasu ya watsa mata su cikin zafin nama wanda hakan ya matuk'ar raxanata ta d'ago kai a tsorace ta dubeshi"ta mau fuskar nan babu alamar wasa balle murmushi haka ya shiga binta da wani mugun kallo sai can kuma cikin dakewar murya ya shiga magana yana nuna ta da yatsa"kin cuci kanki wallahi,banza, wawuya, asharariya,wacce bata san ciwon kanta ba balle na wasu shin kina tsammanin da haka zaki samu kud'i da wannan mummunar d'abi'ar,amma dai tur da halin kawaliya mace mai neman maza a gari tana kai wa wata can!kin zama akuya mai komai tq samu ya zama nata!don haka ina so ki sani wannan labarin naki karki tsammani abin so ne a wajena,babu abinda ya haifar miki illar tsantsar k'iyayya a fili wanda in kin lura zaki ganta cikin kwayar idanuna!kuma da kike batun kina samun nasara a jami'a toh ki rubuta ki ajiye wannan semester d'in sai kin samu matsala da course d'ina,don na d'au alwashin haka tun ranar da kika tozarta prof a gabana,kika wulak'anta tsohon da bai ji ba bai gani ba!maganata ta k'arshe a wajenk kuma sak'oni d'an ladi ya bani cewar yana sonki da aure,kuma a matsayina na wanda Alhaji yake ganin girma har yakan zauna muyi wasa da raha na furta masa na bashi ke,sai dai kuma kash ina ji masa takaicin namiji salihi zai auri mace mai hali irin naki wacce take wa kanta kirari da 'yar jami'a! Yanda ya gama lura sameer da k'ofofin kan beauty sun riga da dun gama kullewa da munanen kalaman da yake jefarta dasu ga wasu zafafan hawaye da suka kasa tsayuwa a kumatunta ya sashi mik'ewa a fusace har yana buge k'afarta ta hagu yayi gaba ya barta nan jikin bishi cike da damuwa! . Cike da damuwa tare da danasani haka beauty ta mik'e ta nufi gida cikin mawuyacin hali"shiru ta samu gidan wanda hakan ya tabbatar mata cewa tsoho sun fita da Alhaji zagayen yamma don ya motsa jikinsa, bata zame ko ina ba sai d'akin su d'an ladi a ganinta wannan shine mafi kyawun lokaci daya dace ta yi magana da sameer,sallama biyu tayi amma duk ciki babu wacce ya amsa mata,ga kuma takalmansa a bakin k'ofa wanda hakan ya k'ara tabbatar da ita cewa yana ciki,ba ta damu da jin haka ba sai ma kamo labulen d'akin tayi ta rik'e ita bata shiga ba,ita kuma bata lek'a ciki ba ta fara magana cikin murya k'asa uwa mai rad'a"nasan ya sameer duk abinda ka kira ni dashi wallahi na cancanta amma kayi wa girman Allah wannan magana ta zama sirri tsakanina da kai don idan har sirrina ya tonu a gidan nan wallahi na mutu,nasan dai zuciyarka akwai Allah a ciki,kaji k'aina ya sameer tunda kaga dai ban b'oye maka komai game da ni ba,kai ma ka tausaya min!dariya sosai ta juyo daga ciki har kana jiyo shak'ewarsa saboda dariyar mugunta can kuma sai ya nisa yace ho ho ho gaskiya yaro a kullum dai yaro ne,ke baki ji kunyar aikata laifi ba sai ni kike rok'on naji kunyar tona miki asiri,ai ki d'auka asirinki a fili yake,yanzu dai ki shirya karb'ar hukunci daga Alhaji kawai!cikin wani mawuyacin hali na jin sunan da sameer ya ambato yasa ta yaye labulen da saurin ta ta afka cikin d'akin tana fad'in kayi wa Allah kayi hak'ur.... chak ta tsaya tsaye idanunta suka kafe waje d'aya sakamakon toxali da idonta yayi da sameer kwance saman katifa daga shi sai vest da k-aramin short,kasa dauke ido daga kallonsa tayi wanda shima a tsorace ya tashi zaune yana d'an kare jikinsa da hannu!ganin abin bana k'arewa bane haka yasa shi saurin mik'ewa ya nemi jallabiyarsa ya zura sannan ya juyo a fusace ya wurgo mata wani mugun kallo yace lafiya zaki shigo min d'aki ko sallama babu!a sanyaye beauty ta iya sauke kanta k'asa don bata da abinda zata iya cewa yanzu!komawa sameer yayi gefe da gadon ya zauna yad'anyi shiru! Dan girman Allah ya sameer kayi hak'uri mana tun d'azu fa nake baka hak'uri ko dan kaga ana lallab'aka shine kake ta wani ja min rai"cike da b'acin rai beauty ke d'aga murya tana maganar!bata tsaya nan ba taci gaba abinta,toh wallahi kaje duk wanda zaka fad'a mawa ka gaya masa tunda kai baka da tausayi,kaje kai tayi,juyawa tayi ta nufi k'ofa sai faman banbami take ita ala dole rai ya b'aci!tana kai k'ofa bakinta ya furta"bama Alhaji ba kaje ka gaya wa mai garin garinnan shine zaka nuna min cewa kai sunanka sameer! Yaye labulen d'akin tayi a zuciye zata fita taji tayi karo da mutum tsaye!k'ara kai hannu tayi beauty ta yaye labulen baki d'aya!karaf ta dawo a baya ganin tsoho tayi tsaye gefensa Alhaji duk kanninsu fusa babu annuri musamman Alhaji,k'arasowa cikin d'akin sukayi baki d'aya kafin kowa ya ankara ji kake tasss ... Alhaji ya kaiwa wa beauty wani zazzafan mari! sululu beauty tayi nan wajen ta zube k'asa sumammiya!wani irin tsalle sameer yayi sai gashi gaban beauty yana jijjiga ta!amma ina babu alamar motsi take duk wani launi na sameer ya rikid'e daga fari zuwa ja don rikita,ganin yadda ta kafe bata motsi yasa tsoho fashewa da kuka yana fad'in wallahi zuciyarka ta sa yau ka kashe min jikata d'aya da bani da kamarta a doran duniya!kuka sosai tsoho ke yi yana sambatu,lura da haka da sauri Alhaji yayi waje bai jima ba sai gashi rik'e da butar ruwa a hannu baba yagana na biye dashi domin bacci take tayi abinta kukan tsoho ya tasheta!ruwan sameer ya karb'a ya shiga yayyyafa mata inda baba yagana ke jijjigata,wani gauran numfashi na wahala beauty ta saki a hankali kuma ta fara bud'e idonta wani dishi-dishi ta fara gani har ta kai ga bud'e idanunta gaba d'aya"sannu kowa ya shiga yi mata ita dai ba magana sai gyad'a kai,hannun Alhaji tsoho ya kamo yace tashi muje waje mu basu waje,ba musu haka ya tashi ya bisu ya rage saura su uku,baba yagana itama mik'ewa tace bara je na samo miki ruwa ki sha!tana fad'in haka ta fice!k'ara lumshe idonta tayi can ciki-ciki ta ji sameer ya ce sannu!ido rufe ta amsa shi,daga nan kuma shiru ya biyo baya! _08:00p.m(na dare)_ Tsoho ne zaune gefensa Alhaji sai sauran mutanen gida in banda d'an ladi da duk yammacin yau baya gida!gaba d'aya suna zaune a d'akin tsoho kamar yadda ya umarta!bayan da suka gabatar da sallar isha'i!" Sallama da salati ga fiyayyen halitta ya farayi wanda hakan ya ke nuna akwai wata muhimmiyar magana da zaiyi sannan ya fara da"na taraku ne ba don komai ba sai dan abinda ya faru ga jikata hajjo,duk da dai bamuji komai akan hirar da kuke d'azu ke da yaron nan sameer ba amma tunda har kike rok'on kada Alhaji ya sani hak'ik'anin gaskiya abin bazai xamanto mai kyau ba,don haka baza mu takura ku da sanin wani sirri game daku ba sai dai yana da kyau duk yanda nake ji dake hajjo in naga kinyi wani abu ba dai-dai ba na tsawatar miki don hakan shine mafi k'ololuwar soyayya da zan nuna miki! haka tsoho ya cigaba da yi musu nasihohi masu tsuma jiki da sanyayasu,bayan ya gama ne Alhaji ya d'aura daga inda ya tsaya duk da Alhaji kusan duk fad'a ne nashi da jan hankali,sosai nasihar ta shige su musamman beauty da taron don ita ne! Inda daga k'arshe tsoho ya rufe taro da addu'a yana musu albishir da su xauna cikin shiri gobe akwai abin al'ajabi A k'auyen nan!Dariya duka suka saka inda anan beauty ta samu bakin magana tace watak'il in tsoho zai raka mu mota in zamu tafi zai mana rawa da k'afa d'aya don ya tabbatar mana ya samu lafiya!baki daya suka k'ara kwashewa da wata dariyar tsoho yana mai bata amsa da in har ta kama gobe na juya jiki ai sai nayi!cikin raha,da wasa da juna haka suka rabu kowa ya nufi d'akinsa don kwanciya shiko Alhaji yayi sallama dasu ya fice! - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment