'YAR JAMI'A Part 008 .
Bayan fitar Alhaji da kusan awa guda sai ga d'an ladi ya shigo hannunsa rik'e da bak'ar leda guda biyu,zarcewa ya yi d'aki inda ya iske sameer kwance akan katifa yana waya da ummah waje ya samu ya zauna har ya gama sannan sameer ya jiyo yace haba mutumina yau ina ka shige haka daga cewa ka bani waje na kafa soyayyarka azuciyar yarinyar nan kawai sai ka b'ace sai yanzu?murmushi d'an ladi ya saki yana d'an girgid'a kai ya d'ago idanunsa sama yace ai yau babbar rana ce agareni kaga kuwa bai kamata nayi wasa da ita ba,tun bayan rabuwarmu dai ban zame ko ina ba sai wajen aminina d'an mai gari can naje muka sha hira duk na baci labarin komai game da hajara kai in tak'aice maka labari shine ya bani naira d'ari biyar da na siyo mana wannan naman!janyo ledar d'an ladi yayi ya mik'o d'aya yace kaga wannan shine namu shi kuma wancan daka ganshi a k'ulle na gimbiya ne"dariya sameer ya saka can kuma ya nisa yace Allah mutumina?kace yau dad'i zamu ci,ai tana can shiga ka mik'a mata kafin tai bacci,washe baki d'an ladi ya shiga yi yana k'ara gyara zaman hularsa akai sannan ya d'akko ledar ya jiyo ya kalli sameer yace ya ka gani d'an birni!jinjina kai yayi da zummar gamsuwa da yadda ya ganshi yace wannan kwalliyar tayi mijin hajjo!cike da jin dad'in sunan da sameer ya kirashi dashi haka ya bar d'akin! Wai wa yaga 'Yaar jami'a an yi auren k'auye??ai kuwa da musamman zan d'auki katin d'aurin aure na kai jami'a ko dan asha dariya!maganar da sameer yayi kenan cikin raha bayan fitar d'an ladi! . Kwance take beauty duk da ba bacci take ba, amma kana ganinta kasan hankalinta baya tattare da ita tuni ta lula duniyar tunani,har d'an ladi ya zaune nesa kad'an da ita amma bata san da zaman saba,sunanta daya kira ne ya maido da ita hayyacinta,a d'an tsorace ta d'ago kai gani d'an ladi zaune gefenta yasa ta saki wata k'aramar tsuka ta koma ta kwanta!gyaran murya ya fara yi sannan ya mik'o mata ledar!ganin bata karb'a ba yasa shi aje mata ledar ya mik'e zai fita kenan yaji tace ka dawo ka d'auki ledarka na k'oshi!bai bi ta kanta ba d'an ladi ya fice abinsa yana mai cike da farinciki na ko ba komai dai ta kalleshi kuma yasan abun sune kawai na mata na filako amma tana da buk'ata! Baba yagana dake kwance can lungu da gado ta rufa da abin rufa ta bud'e tace in kin k'oshu ji mik'o min na lashe tunda abin wariyar launin fata ne bai kawo min ba ya biye miki!yamutsa fuska beauty tayi sannan ta mike zaune ta janyo ledar ta bud'e nama ta gani sai k'amshi ke tashi nan tai faro da ido tace loh tashi baba mu ci nama ne ashe!haka baba yagana ta sakko suka nad'i namansu tas suka cinye shi,ruwa suka sha suka koma gado anan ne kuma hira ta b'arke tsakanisu,tun fara hirarsu babu abinda baba yagana ke wa beauty nasiha dashi in banda sirrin zaman gidan aure,duk wasu hanyoyi na tarairayar miji da neman soyayya wajen mai gida babu wanda baba bata labarta mata ba,har takai beauty na mamakin yadda baba tasan wad'an nan bayanan ita da take k'auye,basu suka tsagaita da hira ba sai can tsakiyar dare suka samu suka bi lafiyar gado!! . . _11:00a.m(na safe)_ . Tsoho ne tsaye bakin k'ofar d'akinsa shirye cikin farar shadda da malin malin waxce tasha guga,Alhaji yayi sallama ya shigo cike da girmamawa haka suka gaisa suka nufi hanyar fita waje har sun kai zaure Alhaji ya dawo ciki ya nufi d'akin su d'an ladi suna zaune suna hira shi da sameer koda ya shiga suka gaisa nan ya kalli d'an ladi yace maza ka tashi ka shirya ka sameni kai d'aya a babban masallacin juma'a na tsakiyar gari!toh d'an ladi ya bisa dashi da haka Alhaji yayi waje ya basu waje! . A b'angaren baba yagana kuwa tun tashinta asuba take tsaye gaban murhu sai girke girke take yi ga wata tukunya can k'arama da lokaci zuwa lokaci takan bud'e ta motsata,bud'ewar da tayi ne na k'arshe taga tukunyar tayi don haka ta juye ta a k'aramin kwano ta nufi d'aki da ita! Tana shiga ciki zaune ta tarar da beauty tayo wanka tana kwalliya sosai yau kwalliya take cab'awa abinta na komawa gida,kallo d'aya baba yagana tayi mata ta saki dariya tace lallai yau ana gayu anan ita kuma wannan kwalliyar fa?juyi tai da ido beauty tana d'aure d'an kwalin doguwar riga pink data saka,tace wannan kwalliyar komawa gida ce don ni duk na k'agu mu tafi na huta da surutunki!kwanon baba yagana ta ajiye gabanta sannan tace bari zumud'i nan da awa biyu zuwa uku zaki tafi gida nina na huta yanzu dai gyara zamanki kici wannan!yamutsa fuska beauty tayi sannan takai hannu ta bud'e kwanon,kaza ta gani ciki tasha kayan had'i ga romo jikinta sam babu kayan miki,d'ago kai tayi ta dubi baba tace wannan kuma meye?kaza ce mana!ku kuma haka kuke dahuwar kazarku anan toh ni dai d'auki kayanki na k'oshi,da jin haka baba yagana ta samu waje ta zauna,ai kuwa baki isa ba nai miki dahuwa kice kin k'oshi ko ya ya ne sai kin ci,cewar baba!ba don ta so ba haka beauty ta zura hannu cikin kwano ta d'an d'eb'o kad'an ta saka baki!cauu...taji abu ya kama bakinta,su beauty abin nema ya samu ai tuni ta gyara zamanta ta fara kwasar romanta,sai da taci kusan rabi da kwata na kazar nan banda romo da ta sha ta k'oshi sannan ta ture kwanon gefe guda tace Alhamdullah,cike da jin dad'i baba ta janye kwanon daga gabanta ta fice abinta ba tare data tanka mata ba! . 12:00p.m( na rana) Busa sarewa da ganguna kad'ai ke tashi ta ko ina,duk unguwa ta karad'e da hayaniya,ko da sameer ya lek'o ya tambayi baba ko lafiya sai ce masa tayi itama bata sani ba jiran dawowar su Alhaji take! Ba'a yi minti 30 da maganar ba sai ga tsoho ya shigo gida da sallama cikin sauri ya nufi ma'ajiyar tabarma ya d'auka yayi waje"zaure yajeya shinfid'a wa manyan bak'i sannan ya dawo ciki,sunan yagana ya shiga kira haka ta fito a d'aki da sauri tana lafiya?abincin bak'i zaki mik'o da alamar fahimta haka baba yagana ta nufi inda ta jere kayam abinci data gama ta jidi mik'a masa yana fitarwa waje har ya gama! Bayan wasu mintina da basu fi goma ba sai ga Alhaji ya shigo gida yana kiran sunan sameer,sameer dake tsugunne gaban k'aramar jakarsa ta kaya yana k'ok'arin zuge zip d'inta don ya gama shirya kayansa tsaf ya ji muryar Alhaji,amsa shi yayi ya fito hannu rik'e da jaka"sororo Alhaji yayi yana kallonsa sai kuma can yace ina zuwa haka?susa gyeya yayi sannan yace dama zan kaita motane kafin ku dawo muyi sallama!ahiyar zuciya Alhaji ya sauke sannan yace toh ajeta anan gefe kazo muje zaure ana buk'atarka acan!umarnin da aka bashi yabi haka ya bi bayansa bayan a jae jakar suka nufi zaure! . Daga fitar baba yagana bata zame ko ina ba sai d'akinta inda ta tarar da beauty kwance tana ta waya abinta dariya sosai take yi da alamar wayar da take tana jin dad'inta,waje baba ta samu ta zauna tana jiran gamawarta,ba wani lokaci mai tsawo ta d'auka ba sai gashi tayi sallama sa wadda ta kira da zee-zee sannan ta kashe wayar,kallo ta kai wa baba sannan tace ma,aikaciyar tsoho ya kayi ne?harara baba yagana ta watso mata sai tace saboda kin rai na ni nice ma'aikaciyar tsohon?dariya beauty ta maida mata ba amsa,gyara zamanta sosai baba tayi sannan ta juyo ta fuskance ta sosai,sunanta ta kira,beauty ta amsa tana k'are wa wayar ta kallo"hajara ina so ki nutsu kuma ki saurareni da kyau kisan cewa ita wannan duniyar kome muke aikatawa dama muk'addari ne daga Allah sannan mafiyawancin abubuwa na rayuwa da muke ganinsu ba alkhairi bane toh sune mafi Alkhairi a wajenmu amma mu bamu sani ba,don haka ina yi miki umarni amatsayi na na 'yar uwar mahaifiya a wajenki wacce nasan ko ita mahaifiyar taki zan gaya mata taji,daki ji tsohon Allah a zamantakewarki ta rayuwa,sannan yi biyayya ga na gaba dake domin abinda suka hango miki na ci gaban rayuwa ke bazaki tab'a hango shi ba,nasan yanzu baza ki fahimci me nake nufi ba Amma in kika koma gida ummanki zatai miki cikakken bayani,a k'arshe ina miki addu'ar Allah yayi miki albarka! Beauty ta amsata da ameen! Tana kaiwa nan a maganarta baba yagana ta mik'e ta nufi jerin samirunta dake mak'ale a cikin kwabot ta zaro wata k'aramar samira bud'eta tayi ta janyo k'ullin dake ciki a rufe a bak'ar leda,beauty dai na biye da ita da ido har ta dawo ta zauna,hannun beauty ta riko ta saka mata shi sannan ta maida ta rufe nan tace hajara ki adana wannan zai miki anfani duk ranar da Allah yasa kika tarr a d'akin mijinki ko bayan rai nane kafin mu'amala ta auratayya ta had'aku ki tabbata kin jik'ashi da ruwa kin sha"hannu ta kuma kaiwa k'ark'ashin gado inda ta janyo wani farin mayafi ta yafawa beauty sannan ta saki murmushi tace toh haka yau zaki komawa ummanki nasan zatai farin ciki in ta ga wannan gyalen jikinki! Kalaman baba yagana duk sun gama d'aurewa beauty kai inda kunya ta gama lullub'eta dan jin maganar baba ta k'arshe na abinda ta bata,don duk wasansu basu tab'a magana irin haka ba! . Suna cikin wannan hali ne suka ji shigowar tsoho da Alhaji,sunan yagana suke kira baki d'ayansu dan haka cikin sauri ta fito tana tambayar ko lafiya?Alhaji ya tambaye ta ina yaran suke?suna cikin d'aki! Yana jin haka ya shiga kiran sunayensu a tare,sameer ne ya fara fitowa d'an ladi na rik'e da hanunsa gaba d'ayansu fuskokin nan babu alamar annuri,sai can ga beauty ta fito rike da jaka a hannu,tsoho na ganin yanayin beauty sam babu alamar damuwa ko b'acin rai a tattare da ita cike da zolaya yace lallai yaran zamani wato ke farin cikin tafiya ma kike ki barni ko?itama dai cikin wasan ta maida masa da ehh mana ni daman duk a k'age nake na koma garin mu,dariya tsoho ya saki sannan ya tsagaita tak'aitacciyar nasiha yayi musu sosai mai tsuma jiki inda duk ciki jan hankali ne da hak'uri ga al'amuran rayuwa sannan ya sanar dasu cewa basu kad'ai zasu tafi can ba har da Alhaji da wasu mutanen!toh kawai suka amsa da shi sannan suka fiddo kayansu baba yagana na rik'e da hannunta har suka fito waje! Cincirindo na mutane da motoci,beauty ta soma gani tun fitowarta inda nan take gabanta ya yanke ya shiga fad'uwa cike da d'unbin mamaki ta kalli baba tace wannan mutanen fa haka baba?da yake baba yagana ta shirya ma amsa wannan tambayar tuntuni don tasan ba makawa sai ta afku nan take ta bata amsa da nad'in sarauta akayi shiyasa kika ji unguwar ta rikice Alhaji aka baiwa muk'ami don haka in kunje can gida an nutsu sai ki masa tayin murna!toh ta amsa ta dashi da haka ta kaita har inda motar sameer take ta bud'e ta shiga gidan gaba ta zauna,haka tana kallon Alhaji ya shiga wata mota doguwa fara tare da wasu jama'a kana ganinsu kaga mutane 'yan alfarma,inda d'an ladi ya rako sameer har bakin mota sukai sallama beauty na masa bankwana amma yadda yayi shiru uwa bai ji taba don haka itama ta basar don ta lura da yanayin nasu gaba d'aya yai sai a hankali,ko b'acin ran rabuwa da juna ne oho musu! . Tafiya suka shiga yi cikin nutsuwa haka yake tuk'in inda motoci uku ke bayansa a jere,tun bayana shigarsu mota babu wanda ya iya ko da kwakwkwaran motsi baran tana magana,dukkan ninsu tunani tsagwaronsa ke cinsu sak'a wannan kunce wancan haka har suka yi nisa sosai a tafiyarsu,k'ishi daya taso masa ne ya janyo ruwa faro dake gefe dashi ya bud'e a hankali ya shiga sha,d'agawarsa ta k'arshe ne yasa shi kwarewa da sauri ya sauke ruwan ya shiga tari,jin yadda yake ta faman tari da alama ya kware da yawa ya saka beauty d'ago kai ta sauke dara-daran idanunta akanshi ba tare da wani tunani ba tace masa sannu ya sameer!banza yayi da ita uwa bai ji mai take cewa ba yaci gaba da tarinsa,ko zaka tsaya da motar ya fad'a maka?a raunane ya d'ago kumburarrun idanunsa ya sauke su akanta,kallon da yake watsa mata kad'ai ya isa ace tasha jinin jikinta,d'auke kai tayi daga kansa ta maida kan titi wanda hakan baisa ta tsaya da maganarta ba taci gaba,hmmn yanzu dai ba da bane da zaka kashe mota ka jibgeni,kuma kar kai tunanin abinda kai min abaya yanzu zan d'auke shi,wallahi bazan k'ara tsayawa wani namiji ya tab'a lafiyar jikina ba,kar kaga na saurara maka dama can saboda tsorona da Alhaji ne amma kaga yanzu yadda na d'akko hanyar gidan nan komai ta fanjama-fanjam,cikin b'acin rai da d'acin zuciya haka kalaman beauty ke dokar kunnuwansa,wato wani wawan damk'a daya kai hannu yayi mata saman kanta cikin zafin nama ya kai gab da gaban motar kenan zai buga,kamar daga sama ya ji maganganun baba yagana na dawo masa ....kaji tsoron Allah kuma ka sani hajara ta zama abin kiwo a wajenka......a sulale ya iya zare hannunshi daga kanta wanda tuni beauty ta gama sakin jiki taji inda kanta zai kasance taji an sake ta,hannunsa ya buga jikin sitiyarin motar yace"wallahi an cuce ni"an cuceni"why me? Dariya beauty ta saki ganin yadda yake ta faman haki kamar wani mayunwacin zaki,fari tai da ido kamar yana ganinta tace Allah dai ya kiyaye maza basuyi abun kunya ba,in banda matsoraci wake dukan mace?dariya ta k'ara sakar masa,inda abin duniya ya gama cika sameer CD na motar ya kunna ya k'ure k'arar motar k'ira'ar sudais ta hau tashi sosai ya shiga binsa ko ya samu sassauci a zuciya! . Misalin k'arfe 12;00p.m(na rana) a agogon hannun sameer wanda yayi dai-dai da shigowarsu gidan dady a parking space ya aje motar haka sauran motocin suma suka aje nasu!bara dai na wullar da kwallon mangwaro na huta da k'uda haka beauty ta fad'a tare da bud'e marfin motar ta fita abinta,hanyar shiga babban falo ta bufa ta kai hannu kenan zata bud'e k'ofa taji an riga ta turo k'ofa matsawa tai da baya gudun kar ta bige ta tsaya tana jiran ganin mai fitowa,ido ta zaro waje da gudu kumaa ta fad'a jikinsa dady ta gani tsaye ai kuwa ta shiga rero kukan shagwab'a tana bubbuga k'afa a k'asa,idan ran dady yayi dubu tuni ya gama rikicewa don babu abinda ke dagula masa lissafi irin kukan beauty,tambayarta ya shiga yi ko lafiya amma sam tak'i tanka masa,Alhaji da mutanen wajen haka sukai sororo suna ganin ikon Allah ganin abin nasu ba mai k'arewa bane yasa Alhaji yayi k'arfin hali ya k'araso wajen ya daka mata tsawa don yanzu ba halin dukan matar wani,dole ta janye jikinta daga na dady tabi gefe ta shige gida da gudu,babbar rigar jikin dady ya shiga gyarawa yana cike da fara'ar gani amininsa mahaifin sameer da d'an uwansa har da wasu mutum uku daga danginsa,cikin girmama juna haka ya k'arasa wajensu suka gaisa tare da yiwa juna murnar abinda ya had'a tsakani,haka sameer shima ya fito kai a k'asa ya gaida dady ya amsa,iso dady yayi musu dasu k'araso ciki nan suka d'unguma suka nufi falo,sameer dake tsaye yana k'ok'arin yin sashensa kamar yadda ya saba yaji Alhaji ya rik'o hannusa yana nuna masa hanyar falo dole ba don yaso hakan ba ya bi bayansa suka nufi ciki,ji yake a halin yanzu babu abinda yafi buk'ata irin kad'aituwa ba tare da wani ya shiga lamarinsa ba amma ya ya iya da lamarin Alhaji!. . A babban falo suka sauka nan hira sosai ta b'arke a tsakaninsu bayan nan ummah ta fito suka gaisa da yake tun safe tana kitchen da ma'aikata ana had'a abincin tarbar bak'i,nan da nan kuma aka shiga jere kayan ciye-ciye da tand'e-tand'e,sameer dai ido kad'ai yake iya binsa dashi don gaba d'aya tunaninsa baya wajensu,ga wani uban tagumi daya dasa kamar wanda akaiwa mutuwa,lura da hakan dady yayi nan ya kalloshin sosai yace sameer ki zaka je ciki ka d'an watsa ruwa ne?dady bai gama rufe bakinsa ba kamar dama jira yake sameer yace ehh dady!yana kaiwa nan ya mik'e ya nufi waje sai sashensa! . _4:00p.m (na yamma):_ Sameer ne kwance saman gado ya rufa da bargo duk da ba bacci yake ba amma dai idonsa a rufe yake,ya ji an bud'e k'ofar d'akin an shigo,bargon dake rufe a jikinsa yaji an yaye an shiga daddab'ar shi a hankali ya bud'e idanunsa karaf ya sauke su akan na Alhaji,cike da mamaki Alhaji ya k'ara kai hannunsa a wuyan sameer inda yaji zafi, meke damunka sameer?tambayar da yayi masa kenan!lumshe ido sameer yayi nan take kuma ya bud'esu ya sauke akan Alhaji, ya bashi amsa da babu komai!jinjina kai yayi na alamun bai gamsu da maganar sameer don haka yace toh tashi zaune muyi magana,ba musu sameer ya zauna ya zuba ido yana sauraronsa,sunansa ya kira samee sannan ya ci gaba da magana, A hak'ik'a njn gaskiya sameer na lura da rashin amincewarka da wannan abin alkhairi da nayi,tunda duk cikinmu ba yara balle su kasa gane halinda kake ciki,amma kasani banyi haka don na muzguna ma rayuwarka ba a'a sai dan na inganta ta,duk da nasan halayyarka da hajara ba d'aya bace sai dai kuma kai kad'aine zak iya zama da hajara a halin da ake ciki,don kuwa in har zaka iya rik'e sirrinta toh mene kuwa baza ka iya jura nata ba"ka d'auka wannan aure da aka had'a cigabane na rayuwarku baki d'aya kuma in har kayi hak'uri nan gaba zaka ji dad'in abin! Shiru dai sameer yake,kai k'asa yana jinsa don haka ya ci gaba"sameer a yanzu ne ake auren soyayya mu da mukai namu ina muka san wata aba soyayya ai sai wacce iyaye suka zab'a maka amma kai fa har halayyarta ka sani kuma nasan duk wani abu nata ba wanda baka sani ba ciki da bai,sai dai bazan tauye maka hak'k'in ka ba sameer kai ma d'ana ne yanzu kamar yadda hajara take 'ya a wajena,gaya min meke saka kuka da har damuwa takai ka ga zazzab'i don daga jin jikin nan naka ba lafiya! Mai makon sameer ya bashi amsar tambayarsa sai hawaye da suka fara bin kuncinsa,nan Alhaji yayi juyin duniyar nan amma sameer ya k'i magana har sai da yaji yace bari ya kira masa mahaifinsa ko shi zai iya gaya masa sannan yayi k'arfin hali murya can ciki yace Alhaji ni fa ina zargin hajara kuma kaga aure ai bazai yiyu da zargi ba?cike da mamaki Alhaji ya ke duban sameer had'e da nanata kalmar zargi a cikin ransa, dayake Alhaji bana yau bane kuma yasan halin da duniya ke ciki nan ya kamo hannun sameer yace,hakane maganarka d'ana aure baya yiyiwa da zargi amma ina rok'onka wata alfarma,nan sameer yace wace irin alfarma kuma alhaji?gyara zamansa yayi yace ina neman alfarmar ka tare da hajara a gidan nan kuma yau d'in nan idan har ka sameta yadda kake so toh shike nan idan kuma ka samu aka sin haka wanda bana fata toh ni zan baka alk'ami da takadda ka rubuta mata saki uku kwarara"d'ago kai sameer yayi yana kallon Alhaji yadda yake maganar da sigar gaskiya ainun!shiru yayi kafin nan ya gyad'a masa kao da niyyar amincewa sannan ya k'aro wani k'orafin yace"a aure na na ci burin yin shagali na gani na fad'a gashi hakan bai yiyu ba!nan ma dai murmushi Alhaji ya sakar masa sannan ya kuma ce waya gaya maka burinka bazai cika ba? Ai tun shekaran jiya dady ya dawo garin nan kuma na labarta masa komai ta wayar mai gari,kuma ni na umarceshi da karya sanar da hajara har sai ta dawo gida ta ganshi,yanzu haka maganar da akeyi yana can ya tarasu ita da mahaifiyarta ni yake jira mu sanar da hajara halin da ake ciki!da zarar ta sani zuwa dare dadynta da mahaifinka sun had'a k'ayatacciyar walima ko dinna ko me?a wani k'aton waje kuma duk sun gama gayyatar duk wasu wanda ya kamata a halarta kaga bayan daren yau duk shawarar daka yanke,inda yiyuwar ka tsara naka walmar daga baya kun tsara kai da matarka!yanzu dai bara naje can naga yadda zamu kasance!yana kaiwa nan ya tashi yayi waje ya bar sameer da wani sabon tunanin! . Beauty dake zaune gefen dady ta d'aura hanneyenta saman cinyarsa yana matsa mata su a hankali sai ummah dake gefe guda saman kujera inda ta bisu da kallo da haka suka ji sallamar Alhaji,k'ara so wa yayi ya samu waje shima ya zauna,wanda hakan ya dawo da beauty cikin hankalinta,take ta janye jikinta ana dady tanutsu sosai kamar ba ita ba,k'ara gaisawa Alhaji yayi da ummah sannan ya kalli dady yace masa toh Alhaji ai ina ganin sai ka sanar da ita komai ko!wasu k'anana muzurai da ido dady ya somayo alamun Alhaji yayi magana kawai shi basai yayi ba,don haka ya d'ora daga inda ya tsaya"hajara"Alhaji ya kira sunanta,cikin sanyayyar murya beauty ta amsashi tana sauke kai k'asa,Alhaji ya soma magana,wannan zama da mukayi anan ko kuma ince wannan taro da kike ganin ana ta yin shi tun daga can k'auye har kawo nan ba ana yi don kowa bane sai don ke"cike da mamaki beauty ta d'ago suka had'a ido da dady nan take dady ya kauda kai gefe,wanda hakan ya baiwa Alhaji damar cigaba a magana ina so ki saurare ni da kunnen basira kiji me zan gaya miki,a matsayinmu na iyayenki wanda suka gi cancanta da mu gina miki rayuwarki kuma mu zab'a miki mijin aure don haka yau mun sauke hak'k'inmu akanki mun had'a ki aure da d'an uwanki sameer !firgigit beauty tayi take kuwa ta mik'e tsaye cikin d'imauta tabi Alhaji da kallo idanunnan sun gama cika da hawaye amma sun kasa samun muhallin zuba k'asa,dumm...taji kanta yayi mata ta yadda take ganin abin uwa mafarki,lokaci d'aya kuma ta saki wata irin k'ara ta shiga shure-shuren k'afa uwa zararriya,dady ne ya yunk'ura zai yo kanta Alhaji yayo saurin tsaidashi da hannu badon ya so ba haka dady ya tsaya shima tuni hawaye ya gama cika idanunsa na tausayin 'yar tasa,wata irin gigitacciyar tsawa Alhaji ya watso mata take ta shiga hankalintabta tsaida shurin k'afar amma ta kasa dai na wayayen don tasan basu tab'a wasa irin haka da Alhaji ba,abinda ya faru tun daga had'uwarsu da sameer,zuwanta k'auye,kai kawo yai da zasu bar garin minjibir babu wanda ya k'ace mata a tunani,yadda baba yagana ta gaya mata nad'in sarautar Alhaji ashe duk ba haka bane,kukan da ya sameer yake yasan da aure na dashi ne?toh waye ya k'ulla abin nan,sameer?Alhaji ko kuwa tsoho?tunani sosai beauty ta duk'ufa yi ganin ba mafita yasa ta sulale wa kasan kafe ta shiga maida ajiyar zuciya mai cike da kukan zuci,ba ummah ba hatta shi kan shi alhaji sai daya tausaya wa halinda take ciki mazantaka kawai ya nuna don yasan aikin gama ya riga ya gama,a karo na biyu ya k'ara kiran sunanta,shiru ta bishi dashi,don haka sai bai damu ba ya ci gaba da magana cikin fad'a"aure d'aurashi yau akan sadaki dubu d'ari,wanda tuni na damk'asu ga mahaifinki,sannan ki zauna da shirin biyayyar aure ba hauka ko wauta ba,in kuwa naji wani abi sab'anin zaman lafiya, zan wanko k'afa har muhallinki na baki mamaki,kin dai san ni sarai?sannan daren yau ki shirya za'a yi walimar biki akai ki d'akinki! . Ko da Alhaji yazo nan a maganar shi sai ji tayi beauty ta kasa d'aukar girman maganar,ace yadda zamantakewa tasu take da sameer yau ita za'a kai d'akinsa?ai tuni ta mik'e wiwi ta shiga kuka tana buge-buge surutai barka tai marasa kan gado,sosai beauty take sharar kukanta kowa ya ganta a halin da take ciki dole ya tausaya mata,kasa jure hakan dady yayi da saurinsa ya k'arasa gabanta bai bi ta kan Alhaji ba tsum ya rungumota ta fad'a jikinsa ta shiga rero wani sabon kukan,kasa danne zuciyarsa shima dady yayi kafin kace me sun had'a kai da juna suna kuka, Sororo Alhaji yayi yana kallon abin mamaki,takaici duk ya gama cika shi na yadda dady ya gama sangarta beauty,wani dogon tsaki ya saki tare da fad'in toh Allah dai ya kyauta,da haka ya nufi hanyar fita yayi b'angaren bak'i inda aka tanadar wa mahaifan sameer! . Bayan fitar Alhaji ne kuma ummah ta mik'e jiki ba kwari ta nufi wajen da su dady ke tsaye rungume da juna,hannun beauty ta rik'o a hankali ta d'ago kai tana kallonta,janye ta ta shiga yi daga jikin dady nan tayi hanyar d'akinta da ita amma har lokacin hawaye bai bar zuba a idon beauty ba" K'ofar d'akinta ta bud'e tare suka shiga ciki, ta nufi bakin gado ta zaunar da beauty k'aramar kujera dake sak'ale gefen gado ummah ta janyo ta jinginata gaban gado ta zauna suna kallon juna! Sunanta ummah ta kira,cikin kuka beauty ta amsata"nan kuma ummah ta fara magana"ya kamata ace kin tsaya da kukan nan hajara don bazai anfanar dake komai ba,tunda Alhaji ya zartar da hukunci,duk da d'an uwana ne amma a zahirin gaskiya ban ji dad'in sigar da yabi ya sanar dake wannan al'amari ba,sai dai ki sani hajara mu iyayenki muna sonki kuma baza mu tab'a aurar dake ga mutumin banza ba!amma abu d'aya da na lura dashi daga ke har sameer d'ib babu mai farin ciki da wannan abu,kamar yadda na lura da ranar tafiyarku minjibir karo na farko da kuka had'u a tsakar gida razanar da ki kayi bayan kin ganshi ce ta tqbbatar min da kun san juna a baya,don haka hajara ina miki magana a matsayina na mahaifiya agareki da ki ji tsoron mahaliccinki ki sanar dani shin meke tsakaninki da mijinki sameer??!!. . Meke tsakina da mijina sameer kuma?yanzu shike nan kowa kallon matar sameer zai na yi min?zancen zucin da ya k'are zagayensa cikin zuciyar beauty kenan,jin kuma ummah ta tab'ota da hannu yasa ta dawowa daga matsakaicin tunanin data shiga,hawaye na bin kuncinta haka beauty ta shiga zayyano wa ummah duk abinda ya faru bata b'oye mata komai ba kama daga kana principal d'insu har zuwanta k'auye'salati da sallallami ummah ta shigayi bayan da beauty ta gama bata labarin cike da mamakin yadda d'iyar cikin jal a duniya wannan abu ya faru da ita,abinda take ji a gari yau gashi a gidanta,ganin hakan bazai anfana mata da komai ba yasa ta share mak'alallen hawayen dake manne idonta ta d'ago kai tana duban beauty kafin daga bisa ni ta ci gaba da magana"hak'ik'a hajara na so tarbiyyarki ta k'arfafu fiye da yadda kike zato,na so na baki soyayyar da ke kanki sai kinyi alfahari dani nan gaba,amma ina kaddara ta riga fata,mahaifinki ya d'auki son duniya ya d'aura miki inda har ya cusa miki wasu d'abi'u da har kike ganin tamkar na tsaneki,baya son ganin laifinki akan komai,yanzu wa gari ya waya?ke kuka shi kuka,don ma Allah ya taimake mu raya sunna zaki ba wani abu ne maras kyau ba hajara da ya zami da kanmu,yanzu kina ganin da wanda zai miki kallon mai mutunci a jamiar da kike ikrarin wai ke 'yar jami'a!hak'ik'a ban ga laifin sameer don yayi kuka da aurenki ba!don shi ya san mai ya gani na aibu game dake!sai dai kuma koma meye hannunka baya lalacewa ka yanke ka wurgar dole nid'in nan dai nice uwa wacce kukan ki dana mahaifinki ya zama dole na share muku,zanyi anfani da kowacce irin hanya ta gari naga na dawo miki da martabarki ta 'ya mace wacce nasan shi kanshi sameer zai dawo yayi alfahari dake! Yanda kuka ke bin kuncin beauty haka dariya ya bayyana saman fuskarta,da sauri ta matso gaban ummah ta rumgumeta ta shiga wani sabon kukan tana mai jin son uwartata sosai a rai! . _8:00p.m(na dare)_ Bugun k'ofar da ake a cikin gidan ne ya sanya sameer da ke kwance lullub'e da bargo fitowa daga ciki ya nufo a tsammaninshi zai ga Alhaji,saurin ja da baya yayi abin da ya gani yayi matuk'ar d'aure masa kai,amininsa ameenu ya gani tsaye cikin wata dakakkiyar shadda,fuskar nan d'auke da fara'a,dariya ameenu ya saki ganin yadda sameer yayi sororo yana kallonsa,tureshi ya d'an yi da hannu da zummar ya bashi waje ya shigo,haka ya matsa masa ya wuce ciki ya bar shi nan tsaye!kunya duk ta gama cika sameer ga mamaki tsagwaronsa da yake yi ta yadda ameenu yasan gidan dady,dole ya katse tunaninsa a daddafe haka yabi bayansa!zaune ya sameshi gefen gado don haka shima ya nemi waje ya zauna,kana ganin sameer kallo d'aya zakai masa kasan damuwa ta gama cika shi,fahimtar haka da ameenu yayi ne yasa ya kira sunansa a sanyaye ya amsa ba tare da ya kallo shiba,bai jira cewar ameenu ba ya yi gaggawar furta,wallahi ameenu ni kam an cuce n....hannu ameenu ya kai ya toshe bakinsa yace kar ka yi sab'o ko ka zargi iyayenka sameer,dady yayi min bayanin komai game da lamarin kuma ni banga wani ai bu ba tunda iyaye sun aminci wannan gyaran tsakaninku zaku yi shi,ba tare da wani yaji kanku ba,ka d'auka duk abinda ya faru tsakaninku a baya k'adsara ce da silar ganawa,wasu zafafan hawayen bak'in ciki ne suka fara kwaranya fuskar sameer,sosai ameenu ya tausaya masa amma ya zaiyi dole ya danne damuwarsa akai yayi masa nasiha kamar yadda dady ya umarce shi,nasiha da lallami sosai ameenu yayi masa wanda tun yana kukan harvya fara sauka a hankali yana biye masa a maganar,in da a k'arshe ameenu ke shaida masa ya rok'i dady da ya janye maganar dinner daya shirya a daren zuwa wani lokaci ba da jimawa ba ta yadda za'ai abu kowa na so ba ana ganin bak'in juna ba" haka kuwa dady ya amince,ya mutsa fuska sameer yayi kawai bai tanka saba don shi baya tunanin da ranar da zai iya son beauty a ransa!haka suka ci hirarsu ta ranar wanda duk akan maganar aurensu ne har dare ya fara ratsawa ameenu yayi sallama da sameer akan gobe zai dawo da yamma!! . Ko da ta fito beauty cikin kaya na atamfa riga da skirt d'inkin umbrella shape kayan sunyi matuk'ar karb'arta sai wani d'an yalelan gyale data bi jikinta dashi bayan jaka da takalmi k'irar vinci data cakare jikinta dashi, cikin nutsuwa da jin kunya haka ta k'arasa bakin motar da taga alamun mutum aciki duk da bata tab'a ganin motar a gidan ba da alama ya nemi anfani da itane don kar a gane suna tare, wanda ta ke da tabbacin tuni yana ciki ita yake jira,a hankali ta bud'e marfin motar,jikinta har wani gyarma yake wanda ita kanta ta rasa dalilin hakan ta shiga ciki ta rufo k'ofar,wani sanyin dad'i daya doki hancinta na turarensa yasa ta lumshe ido a hankali kuma ta bud'e su,ya sameer ina kwana,abinda ta iya furtawa kenan murya can k'asa!shiru taji tare da tada mota kamar bazai amsa ta ba har suka isa fita gate sannan taji yace lafiya,daga haka bai k'ara cewa komai ba har suka yi nisa da tafiyarsu amma da mamakinta maimakon su nufi hanyar jami'a sai taga ya karya kan motar ya shiga wani titi,zagaye ya shiga yi yana 'yan dube-dube da alama wani abu yake nema can taji yace yes tare da take burki,gaban wani kanti da aka rubuta womens parlo a saman shi,fita yayi ya nufi kantin, haka bai wani jima sosai ba sai gashi ya dawo hannunsa d'auke da leda mai layi-layi,haka ya shigo yaci gaba da tafiyarsa,bai zame ko ina ba sai bayan ZAHRAIN TWINS THEATER inda yasan yau lecture d'inta ana zatayi,waje ya samu ya tsaya tare da bud'e ledar kallo d'aya yayi mata yaga kalar kayan dake jikinta don haka wata hijab pink colour ya zaro ya wulla mata,kallonsa kawai tayi ba ikon magana don haka ta d'akko hijab d'in ta bud'e tare da sakawa,duk abin nan da take idon sameer na kanta har ta gama ta shiga k'ok'arin bud'e k'ofa zata fita,ke???ya fad'a wanda ya tabbatar da ita yake,tsayawa tai ta juyo ta kalleshi,kansa ya mayar a titi duk da duhun motar yace ki aje wayoyinki cikin motar kafin ki fita sannan in kin gama ki same ni anan sannan ki saka a zuciyarki yanzu ba da bace!daga haka bai sake cewa komai ba,ganin haka yasa beauty zaro jakarta a hankali tayi kamar yadda ya umarta sannan ta fita!.hannu sameer ya buga da k'arfinsa a kan sityarin motar had'e da cije harshe yace u re my destiny!can kuma kome ya tuno a hankali ya shiga jero addu'oi kafin ya kunna motar ya wuce office d'inshi! . Duk wani iri take jin ta cikin hijab karo na farko kenan da ta tab'a shigowa jami'a da hijab,duk inda ta waiga sai gani take kamar kowa kallonta yake duk ta gama tsarguwa da kanta,haka ta nufi cikin theater d'in can lungu haka ta manne jikin ta da bango,ta kuma kwantar da kai a jikin tebur d'in wajen,ba ita ta d'ago kai ba sai da taji alamar shigowar malami ciki,tana juyo fuska ido hud'u su kai kicib'is da wata d'aliba wacce idan bata manta ba a wasu lokutan baya itace wacce ta watsa wa jan biro jikinta sakamakon yabonta da sameer yayi,saurin kauda kai tayi zuwa gabanta nan ma dai idonta ya sauka akan lecturern da ya shigo Prof KAS ta gani sanye da tabaronsa hannu rik'e da marker yana 'yan dube-duben wasu takaddu,tun da tayi tozali da wad'annan abubuwan biyu beauty ta sadda kanta k'asa a kan wata k'aramar jotter dake gabanta ba ita ta d'ago ba sai da ta tabbatar da an rufe darasin d'alibar gefenta na shirin tashi rik'o hannunta tayi ta zaunar da ita,hak'urin abinda ya faru a baya beauty ta rok'a tare da nuna nadamarta akan hakan,da ya ke yarinya ce mai sauk'in kai nan take ta yafe mata,su beauty dai har da karb'ar lambar waya kafin su rabu! Kayan karatunta beauty ta had'a itama ta nufo waje da shirin fita inda anan ne kuma kowa ya fahimci wace acikin hijabi sakamakon shigowarsu ba d'alibai kamar yanzu da yawa kafin kace me,cece kuce da gulmace-gulmace suka fara yawo,kowa na tofa albarkacin bakinsa,wasu dan tsabar gulma har lek'e suke dan tabbatar da abinda suke zargi,ganin haka cikin sauri beauty har tana tuntub'e haka ta fito a ciki ta nufi bayan theater kamar yadda sameer ya shaida mata,can gefe ta hango motarshi don haka ta nufi wajen,tana k'ok'arin bud'e motar taji kamar daga sama an kirs sunanta cikin kid'ima ta juya me zata gani? K'unyar nan da suka sameta wani lokaci a baya a stop and chop har sukai mata tayin shiga k'ungiyarsu,take suka shiga nuna mata wani mugun salo suna kashe mata ido,bata jira wani abu ba tai azamar bud'e k'ofar kamar wacce aka wullo ciki haka ta fad'o ta rufe k'ofar tana ta faman mai da numfashi! . K'arewa 'yan matan nan kallo sameee yayi tas sannan ya dawo da kanshi wajenta,ita dai kallon nata yayi bai iya ce mata komai ba ya tada mota ya bar wajen,cikin nutsu haka yake tuk'in motar yana zagaya makarantar har ya kai ga muhalin da yake son zuwa,waje ya samu ya tsaida motar ya fito a ciki sannan ya sunkuyar da kai yace mata fito,haka beauty ta fito don ta fahimci inda ya kawota ta bi bayansa suka nufi ginin dake gine a wajen,basu tsaya ba sai da sameer ya kai ga office d'in Prof KAS,nan yayi sallama aka basu izinin shiga suka shiga,zaune suka sameshi ciki kamar kullum yana nazarin littafi,gaisawa sukayi cikin girmamawa amma fuskar beauty ta kasa b'oyuwa a gareshi,duk da sameer ya bashi labarin komai da safe,don haka sai bai yi mamakin ganin 'Yar jami'a cikin wannan shiga ta kamala ba,sameer ne ya juyo cike da izzah ya watso mata wani irin mugun kallon da ya sa tuni tasha jinin jikinta,sunkwi da kai tayi kafin yace baki iya bada hak'uri ba ne? A sukwane beauty ta zube k'asa ta shiga rok'on Allah prof ya gafarta mata abinda ya faru a tsakaninsu,cike da mamaki prof yake girgiza kai na jin dad'in Alk'awarin da sameer ya d'auka masa na cewa sai ta durk'usa da k'afafunta ta nemi gafararshi,yau ga 'yar jami'a k'asan gwiwoyinta,haka dai prof ya amsa mata sannan yayi musu nasiha sosai game da zamantakewar aure,bayan nan kuma suka fito zuwa gida inda a kan hanyarsu na koma gida ne sameer ke tambayarta akan 'yan matan da ya gani,beauty bata b'oye masa komai ba haka ta kwashe labarinsu ta bashi,tab'e baki kawai yayi da jin haka ya ci gaba da tuk'insa! . Haka rayuwa ta ci gaba tsakanin beauty da sameer kullum shi yake kaita makaranta kuma ya d'akko ta tun jama'a basu gano komai tsakaninsu ba har suka gano,bayan da kuma ya nema mata malamin islamiyya kullum bayan sallar magriba yake zuwa nan gida suyi karatu,haka takan ware wani yanki na dare tana bitar karatunta,duk da babu wata kafa tayin anfani da waya gashi yanzu zee-zee ta daina shugowa makaranta kuma sameer ne ke kaita ya kuma dawo da ita babu damar ziyararta don ba wani hira ke shiga tsakaninsu dashi ba!a b'angaren ummah kam abin ba'a cewa komai don kullum da had'i na musamman da ake wa beauty hakan yasa duk ta ciko tai wani haske abinta! . A kwana a tashi ba wuya, yau ya zama ranar da su beauty zasu farar jarabawar k'arshen zangon karatu (wato 2 semester exams),tun safe ta gama shirinta tsaf,haka suka tafi a mota tana ta bitar karatunta sosai sameer yake yaba kwazo irin na beauty,kullum haka take fama da wannan karatun indai zasu tafi don ranar da bashi da aiki a jami'ar dole don ita yake shiga,da haka har ta gama jarabawarta! . Wayewar garin yau ta kasance asabar,sameer na zaune saman kujera cikin d'akinsa daga shi sai singlet da short yana zuma revenge game hankalinsa sosai ya raja'a a game d'in yaji knocking,k'afa ya d'na buga k'asa da alamun rashin son tsayuwa a game d'in sannan ya danna pause ya mik'e kanshi tsaye ya nufi bakin k'ofar don yasan bazai wuce Ali driver bane da yake jininsu yazo d'aya yanzu kusan kullum suna tare a d'aki yana masa tad'i,hannu yasa ya bude k'ofar lokaci guda kuma yana fad'in you are late... bai iya tsaida numfashinsa ba karaf idanunsa suka sauka akan beauty dake tsaye cikin kamala hankalinta naga hijabin da take 'yan wasanninta dashi,jin an bud'e itama yasa tai saurin d'ago kai,sak'onni suka fara saukarwa junansu ta ido cike da mamaki,har wani kyarma jikinta yake sanin bata tab'a ganin sameer cikin yanayin irin haka ba yasa tayi saurin kai hannu fuska ta rufe tace kazo dady na kiranka!tan kaiwa nan da gudu beauty ta ruga ciki cike da jin kunya,kamar wanda aka tsayar sameer ya bita da kallo har ta shige ciki sannan ya maido da dubansa anan murmushi ya saki mai cike da d'unbin tambaya yana susa kai,komawa ciki yayi ya zuro jallabiya a sama sannan ya fito! . Kwance beauty take saman cinyar dady yana wasa da gashin girarta,inda ummah na gefensu zaune tana binsu da kallo,sameer yayi sallama fallon ya shigo kai k'asa ya k'araso ciki,gefe ya tsugunna ya gaishesu kafin nan dady yayi masa iso daya zauna a kujera!bayan ya zauna ne dady ya kira sunansa a hankali sameer ya amsa shi cike da ladabi,cigaba dady yayi da magana" Dama na kiraka ne badan komai ba sai dan na ji meye shirye-shiryenka game da beauty nah saboda a halin da ake ciki ta gama jarabawa kuma kamar yadda mahaifinka ya shaida min da zarar ta gama zaku tare,wannan shine mak'asudin kiran naka! Eh dama dady ina shirin da nake nayi sallah azahar dama na shigo nan domin na sanar maka akan cewa sati mai zuwa zamu wuce abuja tunda ranar asabar mukayi passing out na bautar k'asarmu, cewar sameer da har kawo yanzu kansa na duk'e k'asa!jin jina kai dady yayi sannan yace toh Allah ya kaimu lokacin!ummah ta amsa shi da ameen,shiru dai beauty take duk jinta take wani iri tun bayan shigowar sameer wanda kawo yanzu hira suke tayi a tsakaninsu banda ita can taji dady ya lakato hancinta yana fad'in yanzu zan huta da rigima,sai kije can kiyi ta masa shagwab'ar taki!cuno baki gava tayi uwa mai shirin kuka tace dady ni d'in ko?yadda tayi maganar a shagwab'ance yasa dukkansu sakin wata dariya,sameer ne ya mik'e yana k'ok'arin barin waje dady ya kira sunansa,har lokacin dariya na d'auke saman fuskarsa yace tsaya ta biyo ka can ku bamu waje muyi magana da mahaifiyarku!hannu yasa dady ya shiga d'agota tana nok'e kai wani kallo da ummah ta watso mata yasa tuni tasha jinin jikinta tayi tsum ta mik'e tana wani cuno baki gaba ta bishi sukao waje! . Tafiya yake sameer tana biye dashi har ya shiga d'akinsa gaban gado ya samu ya zauna ya barta anan tsaye,ganin bai yi mata tayin zama ba yasa itama neman waje gefe k'ad'an dashi ta zauna har lokacin hannunta na rik'e da gefen hijab d'inta tqna 'yan wasanninta dashi! Wayarsa sameer ya janyo yaci gaba sa game d'inshi wanda a zahirin gaskiya kana ganinsa kansan hankalinsa da inda ya raja'a yana cikin haka yaji an masa game over,take ya saki wani guntun tsaki yayi cilli da wayar saman gado,sai kuma shiru ya biyo baya!ganin wannan shine karo na farko da masoya biyun suka tab'a keb'e kansu sai ya zamana fargaba ta mamaye su,k'arfin hali sameer ya d'anyi ya katse shirun nasu da cewa?kin yi shiru kamar bakya magana?ganin yadda yayi maganar cike da izzah yasa ta maido masa amsa dai-dai da tambayarsa"ai naga wajen daga ni sai kai kar nai magana yau ma ya zama laifi,shiru sameer yayi maganar ta d'an so ta dake shi don ya fahimci inda ta dosa haka ya ci gaba da magana yana fad'in"ai yanzu kin girma baran dake ki ajiki ba sai dai a zuci?baki bud'e beauty ta juyo tace a zuci kuma?ai dad'in ta dai ita zuciya ba'a ganinta bare ka illata min ita"har wani yamutsa fuska take yayin maganar"wanda hakan ya baiwa sameer damar sakin wani guntun murmushi sannan yace ni ko a gani na kafin na kai hannu jikinki zuciyarki na fara kaiwa,domin idan baki manta ba ranar da kika fara shiga lecture a jami'a bayan kin gama kin shiga econs faculty wanda har ki ka fad'arwa wani kyakykyawan matashi wayarsa,alokacin basarwa kawai nayi na wuce sanin cewa dana jima tsaye zaki iya suma don azabtaccen kamun da nai wa zuciyarki,haka ne?yanda yayi tambayar yasa beauty tsuke fuska tamau tamkar bada ita yake ba, tabbas ta tuna yadda taji lokacin da tayi karo dashi don har tana iya kwatanta kyawun fuskarsa a idonta!dariya sameer ya soma sosai ganin ya gama gano lagwanta,da haka kuma sannu a hankali hira mai k'arfi ta fara shiga jakanin masoyan biyu,damar da sameer ya samu ne yasa shi labarta wa beauty abinda ya faru cikin satin inda ya shaida mata cewa an kori malam umar daga jami'a sakamakon wata sabuwar d'aliba da yayiwa ciki,iyayenta suka k'i yarda sannan ya sanar mata yasa an chafko principal tare da discipline master yanzu haka suna hannun jami'an tsaro kafin a tura su kotu! Shiru beauty tayi tare da juyar da walwalarta zuwa fushi,tausayi tsagwaronsa kake iya hangowa a idanunta ga wani mak'alallen hawaye dake shirin zubowa! Take sameer ya dawo gabanta ya tsugunna had'e da tarba hannunsa a fuskarta yayi sauri tarbar hawayenta a hannunsa,a hankali ya shiga share mata yana lallashinta,sai daya tabbatar da samun nutsuwarta sannan ya tallabo kumatunta ya shiga magana"Ban yarda a gaban idona ko abayana ki zubar da hawaye ba,kamar yadda ban yarda ki sake wata rayuwa nan gaba ba tare da ni ba, a baya na jahilci kai na game dake ashe abin ba haka yake ba,shiyasa a kullum nake d'aukar abinda ya faru akanki matsayin k'addara a gareki,a kullum ina godewa Ameenu don ya zamanto aboki na gari shine yayi ta nuna min yin hak'uri da juriya don samun alkhairin abu,yanzu princess d'ina gani tsugunne gabanki ina neman yafiyar laifina! Da jin haka beauty tayi saurin rik'o hannayensa ta shiga yi masa nuni da ya tashi amma sam sameer ya k'i ala dole ta iya furta masa ta yafe! . . godiya sosai yayi mata sannan ya shiga yi mata nasiha"inda aciki yake cewa" hajara yau na kira sunanki akaro na farko ba dan komai ba sai dan na sanar dake abinda jami'a ta k'unsa,ki sani ita jami'a da aka kira sunanta mahad'ace ta kowanne irin abu hala mai kyau ko akasin haka,muhalli ne na kazo nazo da mutumin kirki da na banza duk zuwa suke kuma kowa da manufarsa,yawancin iyaye ko jama'ar gari sukan kawo cewa a jami'a ko wane masha'a da alkhaba'i ke faru,wanda ba hakan take ba,tarbiyya ana fara tane tun daga gida,rashin samun kyakykyawar tarbiyya kamar wata k'ofa ce na bud'e b'arna ga al'umma,kinga wasu matan sukan yi anfani da jikinsu,wasu kuma suyi an fani da kud'i haka ma daga mazan yake shiko malami buk'atarsa d'aya kuma da ya samu toh ya wuce wajen,amma kinga duk da haka akwai na Allah wad'anda a komai nasu tsantsar gaskiya da rik'on amana suka saka a gaba,kamar dai Prof KAS,saboda haka na yanke shawarar canja miki jami'a sakamakon fahimta da nayi yanzu kin kasa sakewa da nan d'in,mutanen ciki kamar dodonni kike ganinsu,sanadin canjawa da kikayi kina ganin kamar kowa na miki kallon 'yar jami'a ta baya,bayan mun koma abuja zaki ci gaba da zuwa jami'a kuma karatu zaki yi har sai kin gaji tun da dai matar tawa ta kira kanta 'yar jami'a!duka na wasa beauty ta kai masa yayin da yayi saurin gocewa yana dariya!jan hankali sosai sameer ya yi mata kafin ya canja labarin zuwa yadda shagalin dinner d'insu zai kasance wani satin! - ISMAIL SANI
Saturday, 30 December 2017
Home »
'Yar Jami'a Complete
» 'Yar Jami'a Part 8 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI
0 comments:
Post a Comment