=== CIWON IDANUNA 11 === .
Ido na a zazzare nace "Hamma!" ya lumshe idonsa a hankali sannan yayi murmushi yace "Hamma kuma?, ku shigo daga ciki" harshensa a juye, alamun hausan ba ta zauna ba,ya wangale kofan , rike da jakakkunan mu muka shiga bani kadai ba hatta yaa kamal sai daya bisa da ido, Ammi ce ta sauko biye da Fido(yarta ta fari, wacce muke sa'oni da ita) da sauri ta rungumoni nikuwa abun al'ajabi yamin yawa sai kallonshi nake nace mata "Ammi yaushe Hamma Aliyu yazo nan?" ta kalleshi sannan ta juyo ta cemin " Hamma Aliyu kuma? Fahad dai ko?" na saki jakar hannuna bakina a sake, inaaa ai raina mun hankali zasuyi da hankalina, ya za'ayi ina ganin Hamma Aliyu acemin Fahad, nace "Ammi kina gani kuwa da kyau? Hamma ne fa!" ta yi murmushi sannan tace " Fahad taimaka kaje ka haura mata da kayannan sama, inaga stress ke damunta kasan da sauran ciwonnan ajikinta" tafiya yayi yabarni nikuma Fido ta rikoni mukaje dakin da aka sauken, wanda shine dakinta, babban dakine komi pink kana gani kasan dakin yan'mata ne ya sha ado da komi, muka zauna ta kunnamin heater na shiga nayi wanka na samu tafito min da dogon riga na sanya nayi sallah sannan muka sauko kasa, duk da riga da wando ne ajikinta ta tumbuke gashin kanta, Yaa kamal na kan dining yana aika sakon abinci abunka da mai ci, ya kallen sannan yacewa Ammi " Ta zauna anan tunda zamanta acan rikici take janyo mana da kayan kunya, idan tasamu makarantan ma dukka, ni dai gobe zan wuce" ina zama na riko cokali sannan nace " idan na tabbatar da Hamma Aliyu ne na gani dazu bazan bika ba, Amma idan bashi bane zan bika" zura min ido sukayi a lokacin shima ya sauko jallabiya ce a jikinsa tayi matukar yi masa kyau, ya zauna akan dinning din sannan ya fara cin abinci yana danna wayan hannunsa, idona kyam a kansa ina kokarin fitar da cewa shi dinne Hamma Aliyu ba wani ba, Amma ina duk abunda nagani ajikinsa tsak na Hamma, sai dai shi yafi Hamma manyan ido da kuma ginin jiki( wato six packs) daga gani baya wasa da lafiyarsa, namiji ne a zube, hannu fido ta sakamun na juyo sai da naji kunya domin duk idonsu na kaina tace " kinsawa Bappah na ido" na harareta ta gefe sannan naci gaba da jefa shinkafar da ke gabana duk da bawai tamin dadi irinna gida nja bane. ******** Washegarin ranan Yaa kamal ya bar dubai ya koma nja ya barni da jimami da kuma ganin ikon Allah, duk ya ajiye min magunguna na da komi da zan bukata, ko da iby yakirani nace masa a a nafasa tafiya, Fido na zuwa makaranta da sauran yaran Ammi guda hudu dukkansu maza, Mubarak,Alhassan,kabir, da Abbakar sai ita fido dukkansu suna makaranta acan haka zalika Ammi na da shago a cikin kasuwansu don haka takan fita tace , Fahad yana aiki shima duk da bansan gun aikin ba gidan anwatse anbarni ni kadai kamar mayya sai masu aiki, na kimtsa kayana na ajiye sannan na sauko na kunna tv, bana gane yaren nasu don haka na kashe na dauko wayata. Ina kewar gida don haka nakira Abamama, ya dauka cikin sanyin jiki na gaisheshi ya amsa sannan yasamin albarka " Kiyi hakuri ki cire ranki akanshi kinji? ina nan muna miki adduan wanda yafishi alheri, zaki gani kema kiyi addua Allah zai musanya miki shi da wani" "Amma Abamama shi nakeso fa" "kina wasa da ikon Allah ne? ke kam kiyita addua kinji?" da haka na kashe, na kira hajiyati, Ammaty da kuma su yaa Amir da su yaa ahmed, dukkansu yayuna sai dana kira, kowannensu wa'azi daya yake min na nutsu nayi karatu sannan nacire Hamma Araina, wanda idan sun fada dariya nakeyi banjin akwai halittan da nakeso fiye dashi alokacin arayuwata. kwankwasa kofan akayi da sauri na sauka naje na bude a zatona Fido ce ko Ammi saikuma na ganshi, gabana yayi mummunan fadi sannan nace " Ina wuni" bai amsa ba sai murmushi da yake min yashigo ya rufo kofan sannan yace " baki gaji da zama ke kadai ba?" " na gaji mana, gobe zanbi ammi kawai" ya yi murmushi sannan yace " zo kiga" na tsaya ina kallon shi dasauri ya janyo abayata sannan yayi dani ta bayan gidan, wani irin teddy bears na gani ajere a ajiye, juyowa nayi na kalleshi sannan nace " na waye haka?" " wata budurwa ta ce, kullum idan na kai mata sai tasa adawomin dashi, shine nake ajiyewa ko akwai wacce zata dauka wataran" na dauko daya na rike wani irin kamshi teddyn yakeyi na rungume ina lumshe ido tunanina aina nasan turaren, gabana tayi Dam ta fadi dana tuna cewa na Hamma ne, dago idon da zanyi na ga shima kallo na yakeyi nan ma gabana ta kara fadi dasauri na bar wajen, yau nikam nashiga uku bugun zuciya zata kasheni a gidannan idan banfice ba, falon na koma shima sai ya nemi gu yazauna ya hade kafansa daya kan daya yana danna waya, nashiga uku haka Hamma yakeyi idan zai zauna shima, zura masa ido nayi ko kyaftawa banyi "wannan kallon ba zaisa na shake ba kuwa?" muryarsa ce ta katseni a razane na kawar da fuskata sannan nace " wani kallo fa, tunani nakeyi" "tunanin Hamma ko?" na gagara amsawa shikuwa ya tashi yabarni a falon, nan ma nabishi da kallo tabbas idan ban tattara kayana na bar wannan gidan ba zan iya karamin hauka.
***** Sati na daya agidan Ammi na dawo tamkar yar gida, don asai munsaba dasu zuwansu dubai ne last year yasa bama haduwa, shima aiki yazo yi mijin nata na shekara biyu yana gamawa zasu koma acewar Ammi domin ita batason zaman can tafison zaman nan musamman ma da Mammy ta rasu hankalinta yadawo nja, kauna duk sun gwadamin banda abun cewa sai godiya, Abu daya ke cimin kwarya a tuwo, ko cin abinci Fahad yakeyi sai naga kaman Hamma ne, gashi sai shigemin yakeyi mutum ne mai son mutane, fara'a dakuma saukin kai, haka zai jamu nida fido muyi yawo mu dawo gida, sannan duk fita sai yadawo mana da kunshin leda, ina matukar jin dadin zaman gidan Ammi sannu a hankali na fara mantawa da duk wani abu dake faruwa dani haka zalika shakuwa ta shiga tsakanina da Fahad, ko chewing gum naci sai na ajiye masa, haka zalika shima ko me ya samu sai ya ajyemin, hankalin Abamama ya kwanta sosai atunaninsa bazanyi maraicin uwa ba kuma hakanne sai dai kuma a duk lokacin da na ga yadda Ammi take dasu fido sai na tuna da Mammy ko Hamma na kan shiga toilet nayi kuka har sai kuka yafita araina, in rarrashe kaina, babu wanda yasani har wata rana da Fahad yashigo kirana kawai yaji shishikan kuka dasauri yarinka buga toilet din na bude yaga yadda idona ta kumbura tayi jajur, tuni ya lallaboni muka zauna akan kujeran dakin, zuramin ido yayi yana jira na masa bayani amma na kasa nan ma wani sabon kuka na farayi don tuna min da Hamma da yayi zuciyata na ciwo, wani irin kaikayi nakeji aran nawa, ina zansa kaina naji dadi , wayyo Allah na Hamma, wayata naciro da sauri na fara kiran numbanshi duk da nasan ba dauka zaiyi ba tunda naje kusan kullum sai nakira numbanshi amma baya dauka, nakira bugun farko ya dauka a razane na tashi sannan nace "Hamma!" bai ce komi ba sai dana kara kiran sunan nasa "Hamma!!" " i taught nace ki daina kirana, ke wacce irin mutum ce?" ji nayi an fizge wayan , juyowan da zanyi kawai na ga Fahad yadda yakarba haka yakarba ya tika wayan a kasa, Tasssss ya fasata idonshi tayi jajur tunda nake ban taba ganin shi awannan yanayin ba, nashiga uku. Ba tare da ya kalleni ba yajuya yafice nikuwa na tsugunna na tattara wayan sannan na koma daki, bakin ciki da takaici wayata mai uban tsada ya kama ya fasamin wallahi zai ga madarar rashin mutunci, zuciyata ta cigaba da kuna shi kuwa ban kara ganinsa ba aranan.
***************** BAYAN SHEKARA DAYA Lafiya akace uwar jiki toh haka ta kasance dani, domin kwanciyar hankali na samu nayi bulbul kwata kwata bana da damuwa, na so shiganakaranta, don har transfer na nema anma bansamu ba domin cgpa na ya sauka sosai, American university dinsu na cika , gashi kuma archictecture and art desighn shima almost shekara biyar, Ammi tace na bari kawai tunda mun kusa dawowa nja,don haka sai dai na raka Ammi shago, muyi yawo mu ga duniya , shakuwar dake tsakanina da Fahad ya zama hatta abinci tare mukeci, bana ci idan baya nan safe idan yafita aiki haka nake zama jugum sai dai mu wuni muna chatting, wani lokacin har skype mukeyi , ni nake gyra masa daki sannan na wanke masa a machine idan sunyi datti mu hada akai guga, yayuna kuma mu kanyi waya dasu, su hajiyati da Abamama duk hankalinsu ya kwanta ganin ina cikin kwanciyan hankali, alokacin har na fara jin haushin kaina , meye na gani ajikin Hamma? idan kammanine gashinan sak ajikin Fahad , hallayar da nake nema ajikin namiji kuwa shima gashinan, saukin kai, kyauta, fara'a ga ilmin addini domin Fahad har karatu yana kara min, duk munayi to ahaka na shaku dashi shakuwan da yasa na kanyi sati biyu zuwa uku ban tuna da Hamma Aliyu ba, ga Adduoi da Hajiyati da Abamama suka dade suna min , Hajiyati kam saukan alqurani ta saka aka rinka min Alhamdulilah na dawo asalin Nadrah ta, kwanciyan hankali saikuma maraicin uwa duk banyi shi ba sai dai na tuna da ita.
****** Mijin Ammi ya gama aikin da yazo, don haka tuni muka tattaro muka dawo gida nja, gidansu na bauchi kerarriya a gra wanda duk wanda zai wuce gidan dole ya juyo yakara ganin wannan gidan, mun tarar da gidan tsaf tsaf ga mamakina na ga Amrah da wata dattijuwa yar gayu daga gani ita ta haifi Amrah, na gaisheta tana da fara'a sosai naga sai barkwanci sukeyi abun yaban mamaki sosai, sun san juna ne? sannan aina suka san juna da su Ammi? na kalli Fido na ce mata "meye alakarsu? " abun ya matukar bata dariya, don haka sai kawai tace " ki bincika da kanki zaki sani" nayi mamakin ganin gidan, domin kuwa kowa da dakinta nida fido sai dai fanninmu daya ne, haka sauran yaran Ammi. kayan mu kawai muka ajiye amma gidan babu abunda babu, sanin garin fiye da Fido yasa muka fito da ita na tambayi Ammi mota ta kuma bamu akan zamu je ko jifatu mu siyo abubuwan da muke bukata su tootthbrush da sauransu, sanye da abaya duk muka fito munyi matukar kyau idan aka cire kyan fatanmu da kuma kyalli da mukeyi , duk inda muka wuce sai an juyo an kalle mu, muka shiga cikin jifatu muka tsinci abubuwan da zai mana amfani , sannan muka fito muka dawo gida, shigowar motata yayi dai dai da lokacin shigowar motarshi , Gabana ne ya tsinke ya fadi haka kawai amma kuma murmushi ne a fuskata, sauke glass din motar yayi ganin fido yana murmushi ita kuwa tace "Cousin!" annurin fiskata gaba daya naji ta dauke don sai alokacin na tabbatar da cewa ba fahad bane Hamma ne, hannuna na rawa na dawo baya kadan duk da glass din dake idona baisa na gagara mishi kallon muzurai ba, suka gaisa da fido sannan ya juyo yace " daga ina?" tace " mun fito jifatu" kallona yayi amma jikina ya na bani baigane ni ba to ko ya ganeni ma kadan daga aikinsa yayi banza dani, ya ja yawuce nima na shige ciki , ina shirin parking motan tace " baki gane shi bane?" "na ganeshi mana" " na ga kin shareshi" " banda case da shi" mamakine ya ciko fuskanta don dai tasan cewa inba mafarki take ba hotonsa nake damunta ada dashi nace inasonshi, tasan tarihin soyayyata bawai bata sani bane, gashi ina nema na raina mata hankali. Har dare ban ga Fahad ba nima dama na gaji sosai don haka wanka nayi na sauko kasa gun Ammi tana kan dinning tana gyra plate na ce mata "Ammi meye alakar Fahad da Hamma?" ba taso na mata wannan tambayan ba don haka ajiye cokalin hannunta tayi sannan tace " Nadrah! dawowan mu banso shi ba saboda ke, nayi iya kokarina na hana fido ko duk wani acikinsu su fada miki wani abu dangane da Aliyu, tunda ga halin da kike shiga akansa don haka kawai kiyi hakuri kibar maganan nan kicire ranki kinga kin samu lafiya yanzu hankalin kowa ya kwanta,
Abamama ma baya garine da kin ganshi yanzu amma su kamal ma suna tahowa don haka bana so ki tayar musu da hankali" na gane me take nufi don haka kawai nace mata " wallahi Ammi na hakura da Hamma , na daina sonshi ni yanzu ba ruwana na miki alkwarin ba zakiji wani matsala a tattare da ni ba, don Allah ki fadamin kinga yanzu na ganshi a waje, kuma ban kulashi ba" "Nasan zaki yi mamakin kammaninsa, kammaninsa da Fahad yayi yawa, duk da cewa kanin Babansu fido ne wannan kam kin sani ai amma da Hameed tofi wato mahaifin Aliyu da kuma Babansu fido,Uncle Usman, da Fahad uwarsu daya Ubansu daya, ma'ana dai a takaice Fahad yana matsayin Bappah wa Aliyu" tsananin mamaki ya kamani, haba mana dole mana, kammanin yayi yawa ace kuma munyi zaman sama da shekara amma ba'ataba fada mun ba, lallaima Ammi sannunta da kokari, na girgiza kai cikin mamaki sannan nace "Ammi da gaske kar ki damu ni dai ba zaki kara jin wani abu daga gareni ba" ina gama fadin haka na mike na koma daki ina tsananin tunani duk da cewa ina jin dar-dar araina ayanzu shakuwar da nayi da Fahad yafi karfin tunanin mutum, akashi dari cikin son da nakeyi wa Hamma kashi 60 yanzu wa Fahad nake wa, Allah ya gani yanzu son da nake masa ba kaman da ba, na manta da al'amarinsa duk godiya wa Allah da taimakon adduan yan'uwa yasa yanzu ni kaina na huta. damuwata da addua'na shine tunda ina cikin kwanciyan hankali Allah yasa na dauwama ahaka tunda ni ban iya controlling love life dina ba, Ashe ni kam Nadrah ina nawa Allah na nashi tashin hankali rikici da kuma damuwa na dawo cikinta kenan. (zan ci gaba insha Alah jibi, kada ku manta its a true life story) . #ays
=== CIWON IDANUNA 12=== .
Karfe tara na dare su yaa kamal suka shigo cikin gidan, ina zaune da gyada a hannuna ina barewa da sauri na zubar akan carpet din na rungumoshi, yaa Amir da yaa usman suna bayansa dukka rungumosu nayi ina kukan murna, yaa kamal harda dan kwallanshi shima , muka zauna sai tadi anan na tabbatar da yayuna sunyi kewata, sama na hau na debo akwati na kwaya daya nace zanbisu, Ammi abun mamaki tace " sai ina?" "Ammi zamuje muyi kwana biyu da fido don Allah Ammi" Fido da rawan jiki ta hau sama ta hado kayanta nikam tsabar rawan jiki fita nayi na shiga mota ina jiransu su gama gaisawa da Ammi na saka kayan a booth sannan na jingina jikin motan ina danna wayan hannuna , horn akayi a bakin gate din lekawan da zanyi naga wata benz ce take shigowa tsayawa nayi don nasan bazai wuce masu zuwa sannu da zuwa bane, suka bubbude kofan suka fito, wasu tsoffi ne guda biyu sai mai tukawan da ban ganeshi ba don yana ciki kafanshi ne kawai ta waje, na je na risina na gaishesu suka amsa suna zolayata duk da ban ganesu ba amma summin farin sani, har na juya zan gaidashi kawai annurin fuskta ta dauke gabana ya tsinke ya fadi, tuni na danne raina na bata rai sannan na koma jikin motan, ina kallonsa ya fito sanye da farar riga da jeans ta masa kyau sosai ya saka hannu a aljihu yanda akayi halittan dutse haka yayi nima kuwa na shareshi amma nasan da ace da ne dasauri zan nufeshi naje ina rokonshi ko ina masa magana, tsoffin suka shige ciki shi kuwa ya jingina da motar, nima tsayawa nayi har da daukan hotuna ina turo baki, yaa kamal ne suka fito suna tadi suna dariya cikin nishadi, ganin sa yasa suka nufeshi suka mimmika masa hannu, suka gaisa cikin mutunci duk da nasan gaisuwan bai kai zuci ba na yaa kamal, don idan akwai halittan da ya tsana toh yabiyo bayan Aliyu, acewarsa shi yayi sanadi Mammy ta rasu da baizo da wuri ba, sannan nima ciwukan da nayi duk shine sanadi sauran su yaa amir ne kawai suke kulasa, ba karamin danne zuciyata nayi ba gurin ganin yadda suke masa murmushi yadda nake jin haushinsa so nake kawai kowa ma kar ya kularsa, na rasa dalilin jin haushin duk da cewa gabana yana fadi idan na ganshi bayan kuma tsoronsa da nakeji da bansan ya akayiba domin da bana tsoronsa ko kadan. Bayan sun karaso ne fido tasa kayanta dake motan sienna ne dukka muka duru ciki sannan muka zauna, tuni aka fara tadin yaushe gamo, fido kuwa ta gagara sakewa na lura kuwa yaa Amir sai kallonta yake har dai muka isa, dakin tsaf tsaf ma'ana sun gyra da sukaji na dawo , Allah sarki dukka masu aikin gidanmu sun hallaru suna jira, harda hawayensu da suka ganni, nima sai da naji kuka musamman dana tuna da Mammy ina share kwalla har muka kimtsa kayanmu tsaf. Daren ranan dai bamuyi bacci ba sai tadi da fido da su yaa kamal, Anan ya Amir ya kirani falon Abamama na zauna ina kallon tv domin na lura magana mai muhimmanci zai min "yanzu ya zakiyi maganan skul?
kinsan differing kikayi kije tunda ana hutun second semester zaa shiga first semester kije ki duba, and ki tabbata this time around you don't mess up please i beg you!, ki ajiye namiji a rayuwanki kiyi karatu mazan ma inkinyi karatu sunfi mutunta ki, namiji in baki da ilmi he wont respect you kamar yadda idan kina da ilmi, sannan ko aure kikayi kiduba rayuwa kigani komi na tafiya da zamani, azamanin yanzu duk auren da za kiga anyi mace mai ilmi da wacce bata da ilmi akwai banbanci, namiji idan ya san ya sakeki sannan kina da ilmin ki yasan zakije ki nemi aiki you have nothing to loose amma wanda yasan ko ya sakeki zaki wulakanta bazai damuba kuma ki duba dakyau mace mai ilmi tafi zamaan daraja kinemi ilmin addini da boko i know dukka kina kokari amma ki kara kafin ki tafinnan gaba daya kin dawo shiru ne, sannan Abamama yabiya muku hajj ke da fido yayi hakan ne appreciation na rikeki da sukayi da gaskiya zakuje kuyi aikin hajj ku dawo idan time yayi" kafin ya karasa na yi samansa na rungumosa shi kanshi yayi mamakina saboda yanda nake dan tsoronshi fiye da sauran yayun nawa, ina zubar da hawayen farin ciki ban taba kawowa zan koma aikin hajji kusa ba tunda muntaba zuwa da Mammy Allah sarki mammy na, sallama ta yayi sannan na koma daki, yaa kamal na ganina yace " amir ya sanar miki?" ban amsa ba na nufi kan fido ina cewa " taho masoyiya habibaty, an biya mana aikin hajji insha Allah zamu tafi ooo" fido ma murna takeyi sosai tsabar farin ciki ranan sai bayan asuba mukayi bacci. Washegari sai karfe biyu muka tashi, karyawa mukayi sannan mukayi wanka na dauko mukullim motata nayi kewarta sosai, ba mu nufi ko ina ba sai gidan su Ammaty munyi farin cikin ganin juna, sai anan take cemin aurenta saura sati biyu raina yayi matukar baci domin bata fada mun ba sai take cemin ai ta bari sai na dawo ne, muka samu tama ajiye mana ashobe da yake sun saba sosai da fido tun acan ganin junane basu taba yiba, ta ajiye mana ashobe kyauta, naji farin cikin wannan labarin har raina harda kwalla ta, hajiyanta ma taji dadin ganina Allah yasa damu zaayi da zanyi bakin ciki sosai, fitowar mu take cewa Amrah ta aiko kudinta domma ashoben bata dade da fitar wa ba don haka ko zamu samu mu kai mata, banso ba sai sai kar Ammatyn tayi tunanin ko da akwai wani abu tunda na gwada mata anzama daya, nan na karba ashoben guda uku na tuka muka nufi gidansu Amrah, babu komi araina nidai kawai kunya nakeji kar na hadu da hajiyansu duk abunda nayi abaya, horn nayi muka shiga ciki, A falon kasa muka sami Amrah tsalle tayi tana murnan ganina, na kalleta duk da nayi kewanta amma na boye mata saboda kar tayi tunanin don yayanta ne, ta jani muka hau sama fido na biye da mu agida, bayan gaisuwa take cewa " dama inada magana, nasan ko na miki awaya ba zaki yarda da batu na ba" na kalleta nace " me yene?" ta ciro wani album ta mikomin hade da diary bude page din farko naga sunana, dasauri ta rufe tare da cewa " ba'anan zaki duba ba, tafiya zakiyi kije gida ki nutsu ki karanta" na gyada kai tare da cewa toh muka sauko kasa bayan mun mika mata ashoben , duk na matsu na ga meye ina shiga motan text message ta shigo wayana budewan da zanyi na ga fahad ne yaturo kaman haka "
Nadrah tun randa na fara ganinki kika zamto wani sashe na rayuwata, sai dai abun yadawo love triangle ganin cewa wani kikeso bani ba yasa na baki fili ki fito daga kangin dakike ciki tukunna, Alhamdulilah naga yanzu kinyi sanyi burina ya cika, Nadrah burina a yau na aureki, Nadrah ina sonki " jikina a sanyaye nayi murmushi sannan na bude diaryn don son ganin meye aciki page na biyu na duba hotunana ne suka zubo, wanda nake makaranta, nake lectures, na asibiti da dai sauransu , sai kuma wani printed copy na rubutu sai naga ashe text messages na draft akayi printing alamun anason atura akafasa duk anyi printing dinsu, na farkon " Nadrah i love you" " Nadrah am sorry" " Nadrah ba laifina bane" "Nadrah kyi hakuri ki karamin lokaci" " Te amo!" " i love you in every language " dasauri na cigaba da karantawa domin na rude in bude bayan naga Aliyu Hameed tofi innalilahi wainna ilaihi rajiun Sauran pages din na bude aikuwa sai ga wani dan karamin envelope, ina budewa naga zobe ya fado, zoben Mammy ne da ta bani na nemeshi na rasa ashe yana gunsa, kwalla ke biyomin kasan idona duk na rude riko fido nayi da take gefe nace " fi -fi - fido kiga? fido dama yana sona boyemin yakeyi? fido na shiga uku naji dadi innalilahi fido" Daure fuska tayi ta kwace ta wurga ta baya sannan tace " meye hakan? i thought mun wuce maganar nan just because kinga wannan messages din doesnt mean he has confessed, ga mai sonki don Allah don haka ki bar zancen wani can da baisan darajanki ko ciwonki ba " shiru nayi na gagara cewa komi domin tunda nake rabon da naji farin ciki irinna ranan tun mammy na da rai, ganin banda niyya tukamu yasa ta karbi motan sannan ta ja mu, har muka tafi bata kara tanka min ba, nikuwa aduniyan Allahn nan hankalina ya bala'In tashi na rasa ya zanyi har muka shiga gida ina makale da takardun, Fahad kuwa jin shiru banyi replying ba yasa yayi tunanin ko bana so ne nan da nan hankalinsa ya tashi yahau kiran wayata alokacin tsabar gigicewa kasa daukan wayan nayi ina kallo cikin minti sha biyar sai gashi ya shigo gidan. A.C ne a falon amma gumi ne yake fito min sai yake nakeyi, ya kallen ya kura min ido nima da naga haka sai na juya kaina, zama yayi dirsham ya kalli fido sannan yace " Meya faru ne ?"
tana harara na ta mayar masa da komi yayi gum kaman bazai ce komi can dai ya daure yace " yanzu should i await reply?" gyada kai nayi da sauri domin bani da amsar basa alokacin bai tashi ba haka zalika nima ban motsa ba, Amma duk na matsu yabar gidan, muna zaune sai ga yaa kamal ya shigo suka gaisa sannan ya shiga ciki, Fido ta mike itama ta bamu wuri, sai harara na takeyi da ido nidai ban kulata ba domin ni kaina bansan wani irin hali nake ciki ba,can dai ganin babu maganan da zanyi yasa ya mike sannan yace " zan tafi, zamuyi waya anjima kinji?" "Allah ya kaimu" Yana fita na mike da sauri nayi daki na tattaro komi da hotunan na ajiye agabana ganin ba zan gane komi ba yasa na dauko wayata nakira Amrah, "Amrah bangane kan abun da kika bani ba" "Dama nasan za ki neme ni yanzu meye daya kike son ji?" "Aina kika samu? shi ya baki ki bani?" " a'a abunda nasani shine bayan tafiyarki kinsan shi da problem din shaye shayen nan, toh alokacin yayi accident and fortunately da ya farka sunanki ya kira, munyi mamaki sosai amma da ya farka yayi denying yace bashi ya fada ba, secondly na shiga dakinshi gyrawa naga wadannan pix din, daga abunda na gano shine yana stalking dinki ne while kema kinayi which means ke ce baki san yanayi ba, duk abunda kikeyi yasani ignoring yakeyi wanda har yau ba wanda yasan dalili, ni kuma ganin haka nayi risking life dina na nemo duk takardu da pics har wayanshi na dauke na dauko wadannan messages din, last news and the bad one shine Hajiya tayi mishi mata last three months,bai taba zuwa ba sai jiya yanzu dai maganan da nake miki yarinyan tana sonshi sunanta zahra, Sonshi takeyi kaman tayi hauka barin ma yanzu da take ganin yafara kulata zaki sha fama don mahaukaciya ce bata da dadi duk stalkers dinsa ta koresu" Kaina naji na sarawa wani bakin ciki naji ya tokareni yawun bakina ya kafe, har wani daci daci nakeji a makoshi daukan takardun nayi na watsa a dustbin din dakin, jiri naji yana kokarin dibata, Arayuwa ganin Aliyu da wata shine the least i've expected a tunanina tunda yakini toh zai ki kowacce mace, to meye amfanin takardun tunda gashi ya fara son wata wannan labari bai min dadi ba ko kadan, kirjina naji na bugawa da karfi kaman zai fita rarrafe nayi na janyo kwayan maganina na hadiya sannan na jinginu da wardrobe din dakin ahaka Fido tazo ta samen, tambayan duniyannan tamin naki amsa mata, "Aliyu ne?" shiru "Fahad ne?" nanma shiru jan jikinta tayi tafita takira Yaa kamal zuwanshi ganin yadda nake ya daga ni ya daurani kan gado hankalinsa atashe fido tana masa bayanin meya faru, tsaki ya ke taka kaman zai cire bakinsa "Wacce irin Mahaukaciya ce Amrahn nan? Meya fara kaiku gidan?
Waima ya zaayi daga dawowa sukara jawo mana balai wannan ai jahilci ne" mitan da yakeyi yashigo dasu yaa Aamir da suke falo yana matsifa yana cewa Amrah bata da hankali, Fido kuwa ta tsorata domin bata taba ganina haka ba, hawaye na bin idona tsananin kishi na cinyeni su suna faman nemomin lafiya ni ina tunanin hanyan samun wannan zahran, Amma Hamma baida kara duk shekarun danayi ina sonsa rana daya yaje yana son wata , Fahad ne ya fadomin arai to ko nace inason Fahad nasan yaudaran kaina nakeyi saboda son da nake wa Aliyu ya ninka na Fahad babu hadi, nikam na shiga uku da na sani da zamana nayi acan ban dawo ba. Abamama a daren ya dawo , Tunda nake bantaba ganin bacin ransa ba sai aranan "Nadrah me kikeyi haka kaman bakida mafadi? kin taba ganin anyi son maso wani? toh wallahi bari kiji in fada miki wannan karon bazan dauki hauka ba, Soyayyan banza soyayyan wofi akanki aka fara? Ina Kamal? wuce ka kira min Fahad tun suna can yake gwadamin yana sonta dawowansu ma yazo ya samen, ka kira min shi idan har zai iya yazo a daura musu aure juma'a na gaji da haukan banza haukan wofi.
. #ays #whatsapp #07066508080
=== CIWON IDANUNA 13=== .
Ji nayi kaman an zuba min garwashi a raina, idona na kekkeshe nace "Abamama wallahi bazan auri Fahad ba, Abamama wallahi Aliyu nakeso don Allah" ina fada ina kuka ganin Abamama bai kulani ba yasa na riko kafansa, tun da nake arayuwata bai taba saka hannu ya dake ni ba amma ranan sai da Abamama yamin dukan ba bantaba ji ba, yamin dukkan da har duniya ta nade baza'a min irinshi ba tun yaa kamal na kallo har yazo yana rike Abamama amma da igiyan inji Abamama ya faffasamin jiki yana haki yace " Ki mutu! nace ki mutu!!
yarinya zaki jamin abun kunya fisabililah ana ganin mutuncina a gari bazan dauki rainin hankali ba" ficewa yayi numfashina na daukewa amma bai ko juyo ya kalleni ba yaa kamal ne yakaini sama don ma fido bata gidan sai yamma tadawo a daren zazzabi mai nauyi ya dauken, Ban damuba na fito da magrib alokacin ba kowa a falo ban nufi ko ina ba sai TH rike da takardun da Amrah ta bani,alokacin nasan yana asibitin motanshi na gani naje na tsaya ina jira yafito kaina na ciwo sosai numfashina ma dakyar yake fitowa, na fi minti talatin kafin yafito daga asibitin yana kokarin cire farar rigar dake jikinsa idonsa sanye da farin glass na likitoti yana isowa yabude motan alokacin na tsaya agabansa dago idonsa yayi ya kallen sannan yace " lafiya?" " kana sona me yasa baka fada mun ba, gashi za'amin auren dole ka fito amana aure" tsayawa yayi yana kallona baki a sake sai da ya ajiye rigan ta bayan motan sannan ya juyo yace " wa ya yaudareki da wannan kalamun SO? na ce miki bana sonki! ba zan taba sonki ba ki fita a idona, ganinki kadai na samin ciwon kai" riko shi nayi hannunsa yasa da karfi ya tunkude ni hawaye na bin idona na mika masa takardun "wannan fa? wannan meye ne?" Kallon takardan yayi amma bai ko kula ba ya buge ya fadi sannan yashiga motarshi alokacin ya leko yace " Ki daina wahalar da kanki! bana sonki bantaba sonki ba sannan bana tsammani zan soki, kije kiyi ladabi a gidanku" yana tafiya da gudu na shiga motata nima na bishi a baya, yana tafiya ina binsa har ya isa Wani hotel na kalli hotel din ban taba shiga ba balle nasan ya yake, ni dai binsa nakeyi abaya, ya dauko wani jaka yashiga nima na bisa, a reception ya tsaya ya karbi mukulli sannan yashige, naje na tambayi matan dakin da yake tace nayi hakuri basu raba information akan customers dinsu, zaman jira nayi har dare bai fito ba ganin wayan yaa kamal yasa nafice , ina isa gida na ganshi a kofar gida rike da akwati shida fido na zaro ido sannan nace " ina zamuje?" " zaku koma gidansu fido ne, anan baki da mai lura da fitanki dukkanmu ba zama mukeyi ba ki koma wajen Ammi" yaa kamal ya fada cikin damuwa domin kuwa fuskarshi harta fada fido ma duk ta bi ta damu bance komi ba, don ni dukan da nasha banason na kara shan irinsa agun Abamama. Ko da muka koma gidan su Fido Ammi zaunar da ni tayi tana min wa'azi amma yadda maganan ya shiga haka ya fita, ta samu dakyar ta lallaba Abamama akan yabari mu sasanta da Fahad kafin a daure mana auren, dakyar ya yarda, nikuwa Fahad dauke masa wuta nayi gaba daya ya gagara gane kaina na koma ruwa tsundum ba juyin duniyan da baiyi ya lallabani ba amma nayi kunnen shegu sai madaran wulakanci da yake fuskanta nima nake kwasan nawa agun Hamma Aliyu.
******** Rayuwa ta ci gaba da tafiya So dana keyi wa Aliyu sai gaba takeyi, wayata password Aliyu, screen saver na hotonshi laptop dina ma komi Aliyu, magana ta Aliyu, duk da ankoma skul amma ina nan idan yana gari ina makale a asibiti agefenshi har ya saba ma, a bakin fido naji tana cewa yacewa Zahra zasuyi soyayya amma sai tayi hakuri don yanada wata mayyar yarinya incase in mun hadu da ita tayi hakuri ta shareni, ni kuwa innaganta kukan bakin ciki nakeyi, idona har ya zama kumburerre tsabar kullum ina hawaye, gashi bai daina shaye shaye ba, ganin Ammi zata takura min akanshi surutun mutane ya fara samin ciwon kai yasa na tattara naje na kama daki a off campus, Fido kuma cathering skul tashiga kafin ta samu skul anan din, ban tashi sanin obsession din da nake wa Hamma Aliyu da gaske bane sai da naganni a bayan gari naje neman cocaine, tunda cocaine take sha shima, kiri kiri na dawo yar shaye shaye don Hamma yanayi, Amma kasancewar ni kadai ce ba wanda yasani, duk abunda nasan Aliyu na so shi nakeyi hatta Abinci nan nalura bai son cin danwake tuni na washi dan wake, haka ma kifi shima har Amai nakeji idan naji karninsa da kuwa inason kifi kamar me, na lallace na dishe karatun ma kawai yi nakeyi anytime soon atbu zasu iya korana amma ban damu ba,
Aliyu kuwa duk inda naganshi sai na bishi duk da nasan zai disga ni amma ban damuba, bawan Allahn nan ko sense of humour bai dashi balle tausayi, duk abunda nake tunani shine maybe ko yana boyemin yana sonanen bayan ga komi a hannuna, sau dubu nakan zubar a dustbin amma haka nake lalumawa na dauko abuna, nayi photocopy yakai fifty copies incase in zan manta shi awani wuri, hotunan da text dinma dukka ina kallonsu, sai da wata rana nafito kenan daga aji nace bari na leka asibiti ina isa kuwa na ganshi nafito da takardun ya kallen sannan zai wuce na mika masa tareda cewa " don girman Allah ka taimaka don Allah kaduba kaga menene aciki" fizga yayi da karfi yabude alamomin mamaki ta bayyana a fuskanshi sannan yace "Aina kika samo wannan forged papers din?" cikin jin dadi nace "Amrah tabani" "Toh Amrah ta yaudareki , ba ni nayi ba, karya takeyi, if thats the reason why kike bina toh kicire hope wallahy bani nayi ba" ya wurga min sannan ya wuce ban yarda da magananshi ba amma jin yayi rantsuwa yasa nakirata awaya tace mun tana gida don haka naja mota na nufi gidandu tana tsaye kaman mai jirana akofar gidan, nace " takardun nan" "wanne fa?" "wanda kika bani ki kace Hamma ne yayi yace bashi bane" " am sorry, ba shi yayi ba amma nayi ne so that karki cire hope dinki akanshi i want you guys togeda" bansan lokacin da na rikota ta wuyan riga ba na dunkule ta kaman zan mata duka idona cike da hawaye yana shirin zubowa fuskana kuwa bansan wani matsayi yake dashi ba sannan nace mata " Amrah! kin ma san me kikayi kuwa? me yasa zakiyi haka? ni fa mutum ce and you dare play with my feelings? har ina zaman zamana na manta dashi kin dawo kin cusamin shi kinsa sai son maso wani nakeyi, Haba mana ashe baki da imani? you are very heartless, i hate you to the co" ina gama fada na saketa na shiga motana na kwantar da kaina nayi kuka kaman raina zai fita, da ina da yadda zansa kaina na daina son hamma wallshi tallahi da nayi, bakin ciki kaman ya kasheni sai da nayi kukata mai isata sannan na ja motan nafice. Ranan yadda naga rana haka naga dare, damuwan duniya tamin yawa nayi kuka, kukan da na dade banyi shi ba idona ya kumbura, anan na tabbatar Aliyu ya zamo min CIWON IDO, adakin na rufe kaina sati na daya banje lectures ba, sannan banje gida ba, ko Ammi takirani yi nake kaman karatu nakeyi haka fido cikin saa bata leko ba gashi a satin zamu fara bikin Ammaty, na karbo dinkina na shirya sai dai duk wanda yaganni yasan ina cikin damuwa, yayuna ko dun nemeni cemusu nakeyi ina karatu ga shaye shaye da na saka agaba, tun inayi aboye har batu ya zaga atbu kasancewar abu arewa its very awkward mace da shaye shaye, nan zagi yakoma kan Abamama domin cewa akeyi shi ya sakalta ni, yabani mota at young age masu zuwa gurina ma masu kudi ne sai dai duk namijin da zaizo min kallon mace na ke mishi, babu human feelings, wulakanci suke kwasa hakan yasa suke hakuri, dr.Hisham ne kadai nasan yana yawan kirana kuma nake kulashi shima don baya gari ne da kullum zaizo yaganni yatafi yin wani course acan kasan waje, ban damu ma nasan wani kasa bane nikam. Bikin Ammaty yazo day 1 muka fara da bridal shower a matsayina na babban kawa nayi kokarin boye damuwata na shiga cikin kawaye mukayi shagali sosai, washegari akayi walima sai mothers night, duk wannan events din gidan amarya ne kuma naji dadinsu sosai kuma alhamdulilah yadda nayi kokarin boye damuwata munsha goggoro munyi rawa. Ran asabar aka daura aure da yamma akazo kai amarya, duk motoccin da sukazo na gani da fada ne, na shirya tsaf akan zansamu motan da zanshiga nida fido saboda Amarya da tsoffi zata tafi, ina tsaye wasu yanmata biyu suma kawayen Ammaty ne, suka zo suka tsaya ta baya na duk da basusan ina gun ba inaji suna zage zage "dan rainin hankali me yake gadara dashi? don yaga yana da kyau, ai laifin wannan jakar ce Nadrah ko wa take, ba tasan haushin da take bani, ina zata kai dan shaye shaye har za'a shiga motansa yana koran mutane wawa kawai, itace asararriya ai" dayan ta karba da "kullum na ganta sai bakin ciki ya zo min kina mace iya mace to wani iskanci ne kuma wannan kina makale wa wani, na jima ance ansa aurensa da Zahra ba? itama sai wani ji da kai take gayyan mahaukata" Zuciyata tana tafasa na rasa yadda zanyi da rayuwata duk naji karfina yakare idona yayi jajur na juya ina kallonsu alokacin suka ganni dukkansu jikinsu yayi sanyi sun tsorata, sai dai bance komi ba amma na juya don zuwa neman motan da zan shiga fido ma da ta tsaya waya tuntuni barinta nayi agun, ji nayi wani abokin ango yana cewa ga mota ba tare da wani tunani ba na bude gidan baya na shiga, su biyu ne agaban ban dai lura ba da ko su waye shi na gefen ne yake ta surutu yana cewa "
kai kam Aliyu kana bani mamaki, yan mata suna sonka kaima sai ka so su, use her and dump the fool, ji yadda ka wulakanta wadancan abun bai min dadi ba, haka kake tozarta wannan Nadrahn ji yadda take sonka, zata iya komi akanka yarinya ga kyau ga kudi ga ilmi mtsww abokina ba kayiba" Aliyu dake gefe wanda farawan maganan abokin yasa na gane shine hankalina yabi ya tashi yace " if magananta zakamin ka fita min a mota, nace ma zahra nakeso bana son wata bayan ita wallahi na tsaneta, mace ba kamun kai kaga zahra da hijab da liqab take yawo, bata hawa mota so she wont dare challange me" bazan iya hadiye kukana ba fitowa nayi a motan na fita da gudu, motata na shiga na buya inagani fido na kirana naki dauka, nayi kuka, nayi kuka har numfashina yana neman dauka, in dai abunda yakeso kenan insha Allah na daina yawo haka, gida na wuce ban nufi ko ina ba, haka akayi dinner banjeba asali ma kashe wayata nayi, aka kai amarya hankalin kowa ya tashi amma ban damu ba sai bayan kwana biyu da gama biki na kunna wayata naje gidan Ammi, hankalinsu yatashi sai dai ni ko ajikina Abamama yamin fada sosai yace kar na kara kashe wayata. Tun daga ranan da naji kalamun abokin Aiyu bayan fitowa ta daga gidan Ammi na tattara naje kasuwa na siyo hijabai guda goma sha biyu, liqab guda biyar da safa guda biyar, duk wasu english wears dina na ajiye su agefe , motata na ajiye agidan haka nake shiga makaranta, duk da wahalan da nake sha amma haka nake zuwa, duk saboda Aliyu ya tausaya wa rayuwata ya taimaka min ya kulani, da farko bai saniba saida na koma asibiti da naji yana gari randa ya fara ganina da liqab yayi matukar mamaki sosai, abun ya daure masa kai, don har dariya yayi abunda ban saba gani yana yi ba, bugun farko yace " karen hauka ne ya cijeki?
=== CIWON IDANUNA 14===
. Na kalleshi ina hadiyan bakin ciki "A'a ba karen hauka bane karen sonka ne ya cijeni" yaja tsaki ya girgiza kai sannan yace "matsamin nikam" haka ina kallonsa ya manna min hauka ya tafi.
Tuki nake yi a dai dai titin zaranda,go slow yayi yawa sakamakon gidan mai da aka kawo mai kuma ana wahalan mai,don haka kawai na tsaya jira a dan ragu, Aliyu na gani tsaye a bangaren titi agaban motarsa alamun ta tsaya masa, na fito da sauri na nufi gabansa, ina kokarin masa magana ya wurgo min wani harara da bansan da shi ba na tsaya ni kuwa ina kallonsa " bace min anan" hararansa nayi ta gefen ido for the first time in my life naji babu tsoro araina nace masa " naki din" na lura batir din ce ke da matsala don haka na koma cikin lumana na bude tawa motan, na ciro ta abunda ban taba yi ba arayuwata duk da nauyin da nake ji baisa na je nakai masa ba na ajiye agaban motan tare da cewa " ciro na ciki kasa wannan" bai kulani ba nikuwa na daga batir din nazo zan cire na ciki wani wawan fizga naji yamun sannan ya wirgani gefen titi, fadi nayi don sai da hannuna yafitar da jini, wata mota ce ta tsaya agefen titin wani mutum dattijo fari sol bafulatani ya nufoni da sauri, "Subhannalahi baka da hankali ne?" dago ni yayi yana min sannu da jiki, kafata ta gagara mikewa sai kuka nakeyi don azaba, duk da babu alamun damuwa a fuskarsa amma akwai alamun tsoro a lamarinsa, yana gaida mutumin amma bai kulashi ba da tsawa yace " riketa mu sata mota , ashe baka da hankali ban saniba? mahaukacin inane kai?" suka jawoni suka sa ni a motan, yasa Aliyu ya rufo dukka motan shi kuma ya nufi asibiti dani, ahanya yace nakira wani danuwana nikuwa nakira yaaa kamal, a gigice yace gashinan zuwa dama yana kusa da asibitin. Cikin minti goma aka wanke min gurjewan da nayi, sai likitan yace akira mai gyra kawai aja kafan don targade ne, anan nayi zuru zuru da ido alokacin yaa kamal ya isoshi duk ya rude, yana tambayan me ya faru? Dan tsohon cikin takaici yace " kayi hakuri don Allah wani Da na ne ya bugeta, don Allah kuyi hakuri yanzu dai mai gyra zaa samo" yaa kamal yace " bakomi baba" juyawan da zaiyi yaga Aliyu abaya yana mikawa Tsohon key din motata, ya ce masa " me kuma ka zo yi anan? ko ka zo kasheta ne?" yadda yake maganan da tsantsan tsana shikuwa tsohon yana ta bawa yaa kamal hakuri " Baba ba kasan abunda bawan Allahn nan ya ja mana ba, ya lalata mana dangi, ita kenan tilo kwaya daya mace, amma ta ruguza rayuwanta saboda shi" anan fa yabawa bawan Allah labarin haduwa a da Alliyu rasuwan mamy, wulakanci da yake min, barina kasan da duk wani abu dai, yana kai kuwa sai ga Fahad da fido a gigice sun iso, tarar da labarin wanda yaa kamal ke bayarwa fido ta fada musu abunda ya gigita su gaba daya nacewa ina shaye shaye kuma shima sanadin Aiyu, dogon salati sukayi gaba dayansu cike da mamaki, fido ta basu labarin wulakancin da nake sha wanda yaa kamal bai sani ba harda saka hijabai dana fara ma shima duk bata bar aya daya ba, tsohon nan yayi salati yayi salati cikin jimami yace " aikuwa naji dadin sanar dani da kukayi wannan bayanin, don kuwa daga nan babu inda na nufa sai gidan Hameed tofi wato mahaifinsa, kanina ne uwa daya uba daya kuma ni nan nace muku kuje ku kira min mahaifinta ma'ana wakilanta, na muku alkawari babu mahaluki da ya isa ya hana aurennan, in kunga baayi ba sai wani ikon Allah inma ni ko mahaifinsa mun mutu ko kuma shi Allah ya dauki ransa, ko kuma yarinya da bakinta tace batason auren, in babu ko daya toh wallahi za'a daura gobe, waye mahaifinta?" yaa kamal cikin mamaki da bata barshi ba, mamakin jin ina shaye shaye yana jira a watse yaci ubana,yace "Ahmed Ahmed" " tazo gidan sauki tunda na mishi farin sani yamin farin sani, bari ma nakirashi".
Ciro wayanshi yayi sannan ya jira , dukkan mu mamaki mukeyi can dai yace " Alh hameed kwana biyu dai yagarin?" " oh Allah sarki don Allah kana gida ne?, zanzo ne yanzu da wata babban bukata" "sai nazo" haka kuwa ya kashe wayan sannan yace " kuje gida, nan da awa biyu mu zaku ganmu " binsa mukayi da kallo, Aliyu ma yabishi duk gumi ya fito masa, alamomin tashin hankali a tattare dashi,fido kuwa sai murna takeyi adole ita zanyi aure, nikuwa bazan san wani yanayi nake ciki ba, farin ciki ne ko meye? Allahu a'alam har muka shiga gida Abamama na zaune da abokinsa ya tarbeni yana min ya jiki alokacin yaa kamal yake mayar masa da abunda ya faru nikuma muka haura sama don na huta. Muna zaune mukaji karan motocci muka leka aikuwa motocci muka gani, Suka shiga falo da babban riga, hankalina ya gagara kwanciya sai yawo nakeyi a daki na kasa zama guri daya, sunfi awa biyu duk na matsu su tafi musan me ake ciki, Addua ta Allah yasa Abamama ya yarda, gabana sai fadi yake, yanayin da nake ciki bansan ya zan misalta ba, suna tafiya nayi sauri na shiga toilet don gani nakeyi ba zasu yarda ba, hankalina ya tashi sosai sai addua nakeyi ko wanne yafito daga bakina, muryan Abamama naji yana cewa "ina autan take?" Hannu na rawa na bude kofan toilet din na fito sannan nace "ga-gani" murya na rawa nafito ahankali yajuya nikuma na bi bayansa, ganinsa nayi da yayuna duk sun nutsu a falon kowa sai bina yake da kallo, can gefe kuma buhun goro kwaya biyar da katon din chewing gum da buhun gishiri su kuma ban kirga nawa nawa ba, anan naji numfashina ya yi daidai koma meye na san Abamama yakarbi goron gaisuwa, na nemi gu a lungu sannan na zauna kaina akasa " Da farko inaso ki sani, Duk abunda kikeyi, kikayi, kike kuma kanyi da ban saniba yau nasani, nagode da abunda kikayi min, kin tozarta ni agun jama'a tarbiyan da na baki kenan? kin zubar akan titi? saboda soyayya? akanki aka fara shi? toh insha Allah tazo gidan sauki" ya jefo min bandir din dari biyar guda hudu sannan yace " ga sadakin ki, ran jumaa insha Allah za'a daura aure, sannan ga wannan"
ya miko min atm card,nasa hannu na karba ba tare da na duba naga nawani bank bane " ki kai wa Ammi kuje kano gobe ku suyo kayan daki, akwai taron da Mammy ta dade tana miki, ita Ammin zata nuna miki, Allah ya shiryeki, ya kuma miki albarka, ya kareki, domin wannan aure na amince ne don nasan ko nace a'a ni zaki tozarta, kisani duk wulakanci da zaki fuskanta awannan gidan ke kika siya da kudinki, domin kuwa shi Aliyun ba yaso, iyayensa kadai ke so, a labarin da yazo min ma ance mahaifiyarsa tace danta bazai auri yar shaye shaye ba bansan yaushe kika fara shaye shaye ba amma kinga ance kinayi alhali ba kiyi" wani wawan yawu na hadiye gabana na fadi addua ta kar yaa kamal yayi subutan baki, " toh kinga irin wannan wulakancin yanzu kika fara shanshi, zai wulakantaki zai koya miki darasi, sai dai duk abunda yamiki karki kuskura, Na maimaita miki karki kuskura ko da gigin hauka ki dawo min gida, bazan lamunci zawarci ba, tunda ke kikaji kuma kika gani" Ni dai ko oho damuwata ta biya , bansan lokacin da naje na rungumo Abamama ba, idona cike da hawaye, "nagode Abamama, nagode Abamama, i love you" Dukkansu sunyi mamaki sosai , yaa kamal kam juya kai yakeyi cikin bakin ciki "Amma Abamama don Allah don annabi fisabilalah kasan gidan wahala zataje, wahala zatasha, anan fa nake gaya maka yace sai dai ta zauna da kanta shi baya sonta" " kai kam banace ka daina mai da magana baya ba?" Abamama tsawa yayi masa tuni ya sunkuyar da kansa, nikuwa ko ajikina hankalina akwance na shige ciki fido na kan gado na fada kanta ina tsalle, can dai na sauko nayi sujjada, na daga hannu na gode wa Allah hawaye na bin idanuna amma ban damu ba nidai bukatata ta biya, insha Allahu ko Aliyu yana dukana yana marina ne zan yarda na aureshi, zan kuma zauna dashi, wayana na jawo naga messages guda biyu, daya Amrah daya Fahad Tayani murna yayi aciki sannan ya nuna bakin cikinsa na rasa ni yakuma ce, aduk lokacin da na shirya ko na fito na gaji da zama da Aliyu yana shirye da ya aureni, tsaki na ja tare da cewa oho dai duk kowa gani yakeyi kaman ba zan taba zama da Aliyu ba, ni kuwa nayi alkawari abunda zai sa na hakura da Aliyu babu shi a fadin duniya, rabuwa da Aliyu sai dai mutuwa ce ta daukeni. na Amrah kuma hakuri take bani akan abunda tamin sannan tace tana tayani murna na shigowa danginsu. Washegari da sassafe Fahad ya kawo Ammi, Duk da abun ya bata mamaki atake ta nuna bata yarda ba, acewarta zanje na wulakanta ne na tozarta, Abamama ne ya jata suka shiga cikin falo bansan me yace mata ba suka fito na ga tana Allah sanya alheri, mota muka shiga muka wuce kano alokacin na fito da atm din na ga na first bank ne, Ammi tace in munje sai dai kawai mu basu atm su cire ta p.o.s haka kuwa mukayi, Nida fido agefe Ammi tana biye damu naje na zabi kayan daki duk abunda nakeso shi nake diba, sai mu basu atm su cire sai mutafi, mukayi bill akan za'a turo bauchi , tunda ga kayan kicin har kayan daki duk da ni bansan ya akayi Ammi tasan daki nawa bane cemin tayi sun ce mata daki uku ne falo biyu, haka mukayi siyayyan dukka muka sauka a hotel washgari muka dawo. Duk tadin da nake muku ban saka Aliyu a idona ba kuma ban damu ba, tunda nasan ya zama nawa yanzu duk rikicinsa zai dawo hannuna,Allah sarki ni, su Ammi da su hajiyati da dai sauran yanuwan mammy duk sun cika gidan, yanuwan Abamama ma duk sun iso akan washegari zaa daura aure nikam nace ko walima ba zanyi ba, Allah Allah nake akaini, anje ammin jere, nikuma ina fama da mai dilka da take zanzarani, yayuna kaf dinsu sun dawo sun gwada min so kowa so yake ya faranta min duk da bawai suna son mijin bane amma ya zasuyi da ransu, aranan aka kawo kayan aure akwati set biyu, akwatuna takwas tabbas sun samin kaya alhamdulilah na godewa Allah,abu dai sai matsowa yakeyi, Ran jumaa da karfe goma na safe aka daura aurena da ALIYU, Ranar farin cikina, ranar cikar burina, Ranar alfaharina, Ranar farkon alherin rayuwata, rana da bazan manta ba, an aura min farin ciki na, hasken rayuwata, ruhina, abun bege na, abun kallo na, zuciyata, sanyin idaniyata sannan sunan na musamman da naga na dace na sanya masa wato CIWON IDANUNA
=== CIWON IDANUNA 15=== .
A ranar na yarda cewa SO shine mahadi na rayuwa, Yayuna suka taso ni agaba kowanne jiki a sanyaye nikuwa ko ajikina,damuwata shine akaini gidan mijina, Yaa kamal ya zaunar dani yamin waazi haka Abamama dadu Hajiyati duk dauriyata sai da naji na karaya, anan nayi kuka sosai musamman dana tuna da Mammy Allah sarki Mammy na, Abamama yasa na masa alkawarin babu ruwana da kayan shaye shaye, yace natuna mammy ya za taji idan tana raye? nayi kuka sosai su Ammi ne suka sakani a mota da akazo diban amarya, ba laifi motocci sunzo iya zuwa, muna isa gidansu aka ware mana fanni daya kamar yadda aka saba da al'adan yan bauchi sai Amarya ta kwana a gidansu ango kafin washegari su wuce hakan ta kasance dani aka kaimu aka bamu sashi daya, Amrah ce ta shigo da wasu maaikata a bayanta suna rike da trays na snack wasu kuma drinks , ta gayshe da mu sannan ta ajiye har tana zolaya ina amaryan? su Fido ne agefena da Ammaty su Ammi kam tunda suka damkani suka tafi, Wata mata tashigo da akwati a hannunta tace " gashi kayan da amarya zata saka, za'ayi dinner anjima" tana fita Fido ta ajiye agefe, suka gyra min bayan gida nayi wanka nayi sallah sannan na fara shiri haka yan kawayena da basu wuce guda biyar ba, mai kwalliya ma Amrah ce ta shigo da ita tamin kwalliya nasa gown din tasamin head da komi nasaka takalmi sannan muka fito tafiya multipurpose gun dinner, awaje aka bude min mota na shiga gefena Aliyu ne, yasha babban riga yayi kyau sosai Riganshi kalar rigata milk colour, kamshinshi ya cika motan sosai, Fahad ne yake jan motan, na ga kokarinsa da dauriyansa, nasan dannewa yakeyi amma yana cikin damuwa, shi dai yace mun ko shekara nawa ne zai zauna ya jirani,Fido na gefenshi suna yi suna zolayana, Amma tunda na shiga motan Aliyu bai gwada ko ajikinsa yasan akwai halittan mutum agefensa ba, nidai ko ajikina, atunanina shine tunda an daura aure anyi mai wuya, muka fito muka tsaya muna jira a sanar da zamu shiga alokacin ya juyo ya kalleni sama da kasa sannan yaja tsaki yajuya, oho dai oooo tunda ba yanda zakayi dani,gurin yasha ldecoration kam ba laifi ko ni kaina sai danaji dadi araina nishadi nakeji har muka shiga muka zauna a gun da aka tanadar na zaman mu, tuni masu daukan hoto, masu video kowa yayo caaa yana daukanmu don tsananin kyau da mukayi, Ba karamin alafahari bane ace mace irina ta mallaki Aliyu, mata da dama suna jira suka matarshi ikon Allah ganinan kuwa, toh Allah yasa gidanane, nidai nasan zan jura komi. Dinner yayi dadi alhamdulilah duk da mutumina kam yaki murmushi ba yabo ba fallasa, Hajiyansa ma da tazo mana manni sai da tace "Hamma ina alkawarin da kamin?" tuni yahau murmushin dole, Amrah ma sai shige min take ba yadda na iya dole na sake raina da ita, ko da aka koma gida ta jawoni falo tace zata min magana anan tace " Nasan abubuwan da nayi bai dace ba, amma bazan gaji da baki hakuri akan ki yafeni ba, Aliyu na dai gaya miki bawai yanason wata bane, wacce Hajiya ta hadasu zahra ma yanzu magana ya lalace, ta kuma ja masa kunne akan ya faranta miki rai haka zalika ta haramta masa sakinki, tunda an daura aurenku duk wani abu mai sauki ne, kiyi hakuri da danuwana nasan kina masa SO na hakika, Ubangiji Allah ya barku tare, ya kade fitina, ya kareki daga sharrin yanmatan waje, mugun ji da mugun gani, magana ta biyu shine zan ce miki Aliyu danuwana ne kinga tare muka tashi idan kina so ki mallake shi ki san hannunki, maana girki,
tsafta da ladabi wadannan abubuwa dasu zaki sayeshi" godiya na mata sosai, washegari akayi budan kai da yamma akayi hawa daredare aka kaini asalin gidana, mutane sun watse ina jira ango yazo, tun karfe sha biyu da naga bai shigo ba nacire raina, mikewa nayi na yi wanka nasaka rigan baccina ina shirin kwanciya naji ana buga kofa, da sauri na fita ta falon don ganin waye, ina bude kofan ya fado ajikina, warin giya yakeyi da sauri na toshe hancina ina kare masa kallo, na ja jikina a hankali na kwantar dashi zan mike ya jawo hannuna yana cewa "Zahraa, Zahraaa" wani bakin ciki ya gulloni amma haka na mike na jawoshi da kyar ina kokarin gyra mishi kwanciya kawai ji nayi ya kwararo min amai ajiki, ohh Ni nadrah anfara kenan! na cire riganshi na barshi da singlet nikuma na shiga na cire rigan na sanyo towel da katon hijab sannan nazo na goge masa jiki na feshe shi da turare, na tashi zantafi ya janyo hannuna haka na zauna agefenshi ina kallonshi yayita tikan baccinsa, haka nayi bacci azaune kiran sallahn farko ya farka ji kawai nayi an tunkudeni kasa na buge kaina ajikin centre table " Baki da hankali ko? wa ya baki izinin taba jikina? wa ya baki daman cire min kaya? kina da hankali kuwa? ke jahilar inane? kinsa ammin auren dole bai isheki ba zaki min fyade? mtswww doluwa kawai" yana gama fada yaja jikinsa ya tafi, wanka yaje yayi ina kallonsa yacire kayan yazo yaje ya zubar ashara acewarsa na taba shi kuma kyankyamina yakeji, Allah sarki ni Nadrah.
Wanka yayi yazo falo ya zauna, alokacin ni kuma na zaga gidan na gani dakyau masha Allah komi ya zauna dai dai, na shiga kitchen na soya chips, na soya kwai sannan na hado da kayan tea na jera akan dinning, na zo na durkusa agabansa nace " na gama breakfast, ko na kawo maka nan kaci?" idan inda Allah yayi halittan dutse toh haka Aliyu ya mayar dani, na mike jiki a sanyaye naje nayi wanka naci kwaliyyata don atamfa ta na saka riga da skirt ruwan goro nayi dauri sannan na feshe jikina da turare, na fito cikin mamaki na ganshi da indomie agabanshi yana ci ya hada tea, zama nazo nayi akasa agefensa nace " kayi hakuri ban san indomie kakeso ba na maka chips, gobe insha Allah zan gyra" nan ma bai kulani ba yana kallon bbc news dinsa, nima sai na zauna kawai a kasa ina wasa da yatsuna, haka kawai naji ya fara tsaki " ke wacce irin wawiya ce? kin zo kin sakani agaba sai shakewa nakeyi na ci kudinki ne ban biya ki ba ko meye?" mikewa nayi tsum tsum na bar falon saboda kar ma ransa ya baci yace zai bar gurin. Yan zuwa kallon gidan Amarya sai zuwa sukeyi akai akai, sa'a ta daya bai fita ba yamin kara , ko ince yabi umurnin mahaifinsa, sunzo sun gama ganin gida, Aliyu ba ruwansa dannewa yakeyi wani lokacin yake kulani agabansa nikuwa naji dadi ko ba komi bai tozarta ni ba, sati biyu ana zuwa ana tafiya, sai dai Aliyu bai taba cin abincina ba, ba yamin magana mai dadi in har yamin magana to fada zaimin, bai taba shigowa muhallita ba, balle yakiran nasa, dama ni bansa raina ba, tsanani yasiyo abinci yayi sallah ko ya dauki waya yayita waya wanda jikina yana bani da zahra yakeyi sai dai ban tabbatar ba, inaso rana daya na tabbatar da cewa ita ce dinne, sati biyun cif da safe na dafa indomie da tea na hada masa a dinnig yau kam na fara yin wanka ne saboda rashin mutunci da zan farayi , yayi na marmari yanzu zan fara masa hali na, tunda har ni matarsa ce ya zama dole akansa ya sauke hakkinsa na miji na ko ta wani fanni, balle na saba ganin matsifarsa don haka bana jin tsoronsa. Da farkon fari daurin ture kiga tsiya nayi, daurin da wasu ke kira da na kilakai, na cikaro daurin gaban kaina na jera komi akan dinning yana zaune na zo na tsaya akanshi "abincinka ya dahu" bai kulani ba, as usual dama nasani don haka na nemi gu na zauna, ganin banda niyyan tashi yasa ya mike zai shiga kitchen na bishi abaya, ya ce " matsamin" ganin na tare masa hanyan shiga, na rike kunkumina sannan nace " bazan matsa ba!!! nace maka bazan matsa ba! wallahi tallahi sai kaje kaci wancan abincin bazaka sani asara ba" mamaki ta cika a fuskarshi don idona har yayi jajur ya dauko hannu zai matsar dani wani kara nasaka masa da karfi nace " Kar ka kuskura ka tabani, wallahi kar ka fara!" juyawa yayi simi simi yaje ya zauna a dinning din yana kallon idona ina kallon nasa, ya bude ya fara ci , gabans fadi yakeyi domin kwakwaran tsawa yamin zan iya sake fitsari a wando, amma haka na danne na cije don yaga kalan hauka ta daban ne da nashi, yana ci kaman yana cin kashi nace masa " meye kaman kana shan magani?" " babu, when last kikayi adduoinki?" wani dariya ne yakeson ya kufce min amma na daure, ohh kar dai yana tunanin ina da aljannu ne? ah lallaima to, sannunsa, ban amsashi ba sai da ya gama ci na tattare gun sannan na koma falon na zauna, ganin ban kula sa ba yasa ya ci gaba da kallonsa a nutse, daki naje na kira Amrah, " yayanki na tsoron aljannu ne?" dariya tayi sosai sannan tace " da aljannu da mage baya son su ko kadan" na mata godiya na kashe wayata, nakira fido nace inason mage ta kawomin yau don Allah, duk da tayi mamaki don tasan banaso amma tace toh , dawowata falon naji yana waya, baza kunnuwa ta nayi don jin me zai fada, " haba zahrah ki bari gobe zanzo" wato jin zahra da nayi mikewan da zanyi nayi kansa na kufce wayan na wurgata a kasan tiles ji kakeyi taaaaass akasa, a harzuge ya miko yakai hannunsa kaman zai dakeni ni kuwa na zura masa ido don babu alamun tsoro araina, ya kamo kaina sai da dankwali na yacire gashin kaina ya tamko idonshi kaman zai fadi , ya zaro su " waya baki izinin taba min waya, ke wawiyar wacce gari ne?" " Wawiyar ka ce ni, haka kawai ina matar ka ta sunna zaka zo kana waya da wata agabana, akan meye toh? wallahi tallahi sau dubu kayi waya agabana sau dubu zan fasa" wurgani kasa yayi da karfi yaja tsaki ya shiga dakinsa sai gashi ya fito da kwalba , salati nakeyi araina ina kallonsa ya bude ya kwankwada yasha, yana sha yans kallo, ina takure agefen kujeran falon wani hawayen bakin ciki ya fara zubo min, nashiga uku na Aliyu, ai kuwa ban idda tunani na ba naganshi akaina, finciko ni yayi yana shinshina gashin kaina kaman kare, nayi nayi na kwace kaina amma fuzgata yayi yana kokarin yaga min riga, banda mai ceto na awajen, abun bakin ciki abun takaici, mijina na sunna ya keta min haddi a yanayin maye, ya sanni a ya mace acikin maye, baya hayyacinsa, bai ragar min ba ko kadan ,haka yabarni agun ya juya yayi baccinsa, nayi kukan bakin ciki kaman raina zai fita, idona ya kumbura sosai amma ya zanyi da raina, nace naji na gani zan iya, ban isa nace bazan iyaba. Kafin ya farka na lallaba rayuwata naje na kimtsa kaina na rufo kofan dakin don karma na ganshi , ban fito ba sai dare alokacin yana kallo ko ajikinsa bai nuna yasa akwai abunda ya faru ba, duk da dingishi da nakeyi na wahala. Sabuwar waya na gani a hannunsa, wato har yaje yasiyo sabuwa, toh ni kuwa bazan gaji da fasawa ba. Rayuwa ta ci gaba da tafiya min, duk wata ya mace da tayi aure tana yin haske tayi kyau tayi fari tayi jiki, ni kuwa na rame nayi baki, gashi makaranta ma munkusa komawa hutu duk da strike akeyi,
Fido ta kawo min mage alokacin da ta kawo yasa mai gadi ya fita dashi, in inaso yaci abincina rikice masa nakeyi kaman mai aljannu in bahaka ba sai dai nayi asara, shaye shaye kuwa sai dai bai dawo daga aiki ba, dama Babansa ya nema masa transfer zuwa nan, idan yaje yagama ganin patients yadawo sai kuma yahau shaye shaye dama shi hes not a fan of friends, shi kadai yake rayuwansa, in kuma yayi shaye shaye toh ranan inada tabbacin zan kwana cikin kunci domin kuwa fyade yake min, in yana hankalinsa yayita kyankyamina in baya hankalinsa kuma kaman ya cinyeni ya rinka sumbatu kenan, shi kenan na dawo inji , ahaka na gano inada ciki daga laulayin da na fara, na yanke shawaran sanar masa, da sharadin zan zubar wato ranan sai da na gwammaci kida da karatu domin kuwa gwadamin yayi zai iya hallakani idan na zubar da cikinnan "burin hajiyata ta samu jika, don haka dole ki haifa" bansan lokacin dana mayar masa da magana ba nake ce masa " Sau dubu kasha giya na gani , sau dubu zan zubar da cikinka sai dai kasa iqwa ka kasheni bayan biyayyen auren da na nuna maka, iskanci kala kala yau da na kwana da kai gwara na kwana da kare" wani wawan mari ya saukemin wallahi sai da naga wuta a fuskata, kafin na karasa dagowa ya kuma sakemim wata marin. (Do not forget ITS A TRUE LIFE STORY)
0 comments:
Post a Comment