=== CIWON IDANUNA 6 === .
Whatsapp dita na hau nafara duba ko yana kai sai dai banga alamun hakan ba, na gama tunanina tukunna na shige lectures, duk da naji wani sonshi yakaru mun, naji kaunarsa da kuma kwanciyan hankali a tattare dani duk saboda shi, wayata na dauko sakamakon ji da nayi ana kirana dubawan da zanyi naga sabuwar lamba da bansaniba, don haka na dauka ba tare da nayi magana ba "hello! Nadrah!! Amrah ce!!!" "oh oh sis yakike?" "lafiya lao ya karatun?, kinata inane?" " ina department dinmu amma yanzu zan fita daga school din, hope lafiya?" "yes jirani a department din naku, zanzo na baki sako ne" ina zaune ina jiranta duk da hankalina yatashi don son jin wani irin sako ne haka akeson bani, ina zaune motarta ta karyo kwana ba ita take tuki ba alamun tana tare da driver ne, nafito na tsaya itama tafito rike da wasu takardu, ta mikamin tana murmushi nima na amsa na yi murmushin. " komi game da rayuwarsa na cikinnan, nayi risking kaina na dauko miki, kisamu kiduba zuwa gobe kidawo min dashi domin yaje jos yau gobe kuma zai dawo, babu abinda zaki bukata a tattare dashi da babu anan" Na rungumeta tsantsan farin ciki sannan nace "gobe zan kawo miki insha Allah i promise" da sauri tajuya nima na koma motata,Ac na motan na kunna sannan nafara bude takardan hotunansa ne tun yana yaro tun daga first birthday dinsa har na talatin da yayi wata biyu da suka wuce, na duba date din sannan naga dai dai yake da nawa 27th May, hotunanshi da abokai yawanci turawa ko ince dukkansu turawa sai kuma nashi da Amrah sai Hajiyarsu da Babansu, family tree dinsu baida girma ko yawa donhaka tuni nagama gani, saikuma wani littafi kaman slum book da ya cika abubuwan da yakeso da wanda ya tsana, lonely message dakuma yadda dai yake rayuwa ina gamawa na rufe na nufi gida, Ranan banyi bacci ba har washegari inata rubutawa banyi niyyan shiga makaranta ba amma da na tuna Amrah zata shiga ba shiri nafito alokacin karfe sha daya, Mammy ce ta katseni " kije min mobile mart ki sayomin magic coal" na amsa da "toh" sannan nafice takardun suna hannuna don gudun kar rawan kaina ya kwasheni na yar dasu awani waje, ina shiga Amrah ta kirani a waya " kina ina? kiyi sauri ki kawo wallahi yana gari yanzu haka" dasauri na dauki coal din zantafi kenan naji na bugu da karfi, tuni takardun hannuna da hotunan suka watse a kasa, sanye yake da tshirt da jeans, gashin kansa ta kwanta luf luf, gabana ne ya tsinke yafadi ganin Aliyu ne, jiki na bari na fara tattarawa yayinda shikuma yaketa "sorry" da sauri na sunkuya zan tattaro littafannan kafin ya gani, aikuwa nayi kuskure domin kuwa idonsa cak akan hotonsa kwaya daya, a nutse yasa hannu don yadauko, bansan lokacin da na sunkuya kasa ba zan dauko, hannunmu ya gogi juna, sakewa nayi da karfi domin jin zirrrrr tun daga saman kaina har kasa, bazan san yanayin da idonsa take a farko ba amma a sanina dashi Aliyu na da fararen ido sabanin wannan lokacin hada ido da zamuyi idonshi ta kada tayi jaa, ya tattaro files din gaba daya ya rike a hannunsa ya bude daya bayan daya yana gani,alokacin ji nayi kaman wata barauniya kaina a kasa inajira naji saukan mari ko duka, gashi tsabar rawan kaina har da photo copyn wasu, na shiga uku ni, " what is this?" ya tambayen cikin dagaggiyar murya mai alamun fushi, bance komi ba don haka ya kara tambaya ta " babe am asking you what is this?" jiki na rawa bakina ma haka nace " Am so sorry" riko ni yayi da karfi yafito dani daga shagon yaciro wayansa wanda bansan wazai kira ba " kina ina? .
kizo yanzu ki samen a mobile mini mart" na danji sanyi domn jikina yabani cewa Amrah yakira, daya daga cikin maaikatan yafito yana tsaye da tsawa Aliyu ya kalleshi tare da cewa " what?!" " kudin coal din hannunta ne bata biya ba" yafada jiki na bari, a wulakance yacire gudan dubu daya kwaya biyar ya jefeshi dashi "keep the change" tuni ya dauka ya shige ciki, muna tsaye hankalina a tashe yayinda shikuma ko kallon inda nake baiyiba balle inyi tsammanin tausayi, lallai yau zanga wulakanci, yayima ko zan iya zuciya dashi don ni kaina dawainiya dashi tafara damuna nadena karatu kamar yadda nakeyi da tunda na hadu dashi, muna haka sai ga motan Amrah wannan karon itane tazo, da sauri tafito ganina a tsaye kamar almajira , binta yayi da kallon tuhuma sannan yace " how did my original credentials and diary get to her?" kallona tayi alamun na kwafsa ta juya za tayi magana yasa mata hannu alamun tamasa shiru, "get lost" sannan ya juyo kaina alokacin ya kare min kallo daga sama har kasa sannan ya wurga min a gabana ya matso kusa dani ya sunkoyo yadda zan iya jinsa sosai, sannan yace " kar kisha wahalan nacin sai kin saya zuciyata, zuciyata is too high for your liking, you cant deal with me, dubunki sunyi sun hakura , me zai hana ki hakura? ki dena wahalar min da kanwa" yana gama fada yajuya ya kalli Amrah sannan yace " sai kinzo". . Numfashi ta tsayawa tayi cak na wasu dakikai tsantsan yadda gaba na take fadi, Oh rabbi am ina kallonsa ya shiga motarsa ya fice dasauri Amrah ta karaso kaina ta rike hannuna tana tambaya ta "Meya faru hope bai miki komi ba?" na gyada kai alamun ae sannan tajani muka shiga motata sai dana zauna na dafa kaina kan steryn motan sannan tace " . jiki na yabani zai soki, saboda yanzu da wata ne nayi imani da Allah sai ta kwashi wulakanci but kiga yadda yayi miki harda miki magana fa" nayi murmushin takaici sannan nace " kinsan meya fadamin ne?" anan na sanar da ita tayi murmushi sannan tace " kar fa kice zaki hakura wannan ba wani abu bane, kingama da files din na tafi dashi?" na gyada mata kai ta cire wanda nayi photocopy sannan ta waresu tarike. "Hamma Aliyu likita ne nasan kinga komi but amma yau dasafe yake sanar damu cewa TH na nan bauchi sun daukeshi aiki, i mean finally ya yarda ya musu aiki don tunda yadawo ake safa da marwa, ya yarda akan ran thursdays zaina zuwa duba duk masu problem na zuciya agun har kuma idan bazai yiwu anan ba sai aturasu can abuja, Ammaty ta gayamin cewa kema kina fama, this might me an oppotunity for you kije wannan karon, .
sannan nasan Ammaty kawarki ce sosai, karkice bata sonki sosai wallahi tana gudun miki wulakanci ne tunda tasan Hamma amma kinga Hamma baya miki ai ko?" ni farin cikin labarin datake sanar dani yasa na ma manta metake nufi bansan lokacin da na rungumota ba , akaro na farko a rayuwata ina farinciki da ciwon zuciyan da nake dashi, zan yi amfani da wannan daman , muna sallama tafice nikuwa na wuce makranta lectures dinma ba ganewa nakeyi ba , na samu nayi submitting assighnment dina nafito na nufi hostel gun Ammaty, tana ganina ta daure fuska nikuwa ko ajikina haka muka wuni taki sake jiki sai mita takemin akan Aliyu nikuwa hotonsa na dauko nasa a wallpaper na wasu kuma sakawa nayi nahada video, sai yamma na tafi gida, aikuwa ina isa gida naga motoccin samarin gidanmu a cikin gida har inacewa meya faru yau basu je aiki bane, ina shiga ciki naga Yaa kamal da Abamama sun riko mammy a gigice na wurgar da jaka na dama Mammy na da ciwon zuciya wanda dukkanmu kowa na kyautata zaton ko gadonta nayi, hawaye na bin idanuna abayan jikina nacire dankawalin na yafa a kafadata ina kuka ina rike da hannunta da sauri yaa kamal ya tukamu yaa amir na biyomu a baya muna isa aka wuce da ita TH muna isa ICU aka kaita , Abamama yafara magana da likitotin wasu sun rufa akanta amma naga Abamama sai waya yakeyi dana matso kusa hawaye na bin idanuna na ce " Abamama zata samu sauki ko?" yajuyo ya kalleni sannan yayi murmushi " insha Allah auta na zata samu karki damu, yanzu akwai kwararreb likitan zuciyan agari ana nemansa ne yazo ko zai dubata bai dauki wayan ba" dasauri nace " meye sunanshi?" " Dr. Haidar tofi, sun ce so far shine kwararre sosai wanda zai iya dubata ba tare da wasu naurori ba yagane meke damunta" . bansan lokacin da na bar cikin asibitin da gudu na nufi mota ba , wayata na dauko sannan na kunna, na kira wayan Amrah bata dauka ba , nakra wayan Aliyu shima bai dauka ba, kara kiransa da zanyi yana dauka a gigice nace " nasan ka tsaneni don girman Allah ka taimakeni, mahaifiyata rai a hannun Allah wallahi na maka alkawari in ka taimaketa yanzu zan dena takura maka wallahi, don girman Allah" cikin sanyin murya yace " waye ne?, daga ina?" wasu zafafan hawaye suka zubo a idona nace " Hamma don girman Allah ni ce wacce na dauki credentials" sai kuma yayi shiru sannan ya kashe wayan, in kara kira naji a kashe , jinginuwa nayi agefen motan ina kuka zuciyata kaman zai fadi yayuna ma kowa a rikice a duniya inason iyayena fiye da duk wani abu da nake dashi gashi rayuwar mahaifiyata yana rawa, wayata naji tana kara ina dauka na ga shine dasauri na dauka hannu na bari, " kin tabbata inna dubata bazaki kara damuna ko kanwata ba?" jiki a sanyaye nace " ae i promise" ya kashe wayan , yayinda nikuma na zurawa wayan ido, nafi minti sha biyar agun har na mike zan shiga naganshi yashigo yana dan sauri yana nannade hannun riganshi sanye da farin coat dinsu , .
na bishi da sauri yana shiga suka gaisa da Abamama har zai shiga nace " Hamma!" ya juyo ya kallen daga sama har kasa sai alokacin na lura ashe kaina ba dankwali gashin kaina duk ya zubo kasa, anan yajuya yafice nikuwa nayi ajiyan zuciya adai dai lokacin muka hada ido da Abamama kafin ya tambayen nace " Yayan kawata ne" sai ya juya baice komi ba, muna zaune har mintuna arbain sannan yafito Abamama yabishi suka fice nan ma suka share mintocci sannan yadawo, yace " zamuje abuja saboda akwai aikin da yake son mata nan kuma basu da kayan aiki, yanzu yasata akan magunguna yakuma min bayanin ciwon dalla dalla , sai yanzu nasan na hadu da likita duk yawace yawace da mukeyi banji bayanin da ya kama min hankali irin wannan ba, yanzu yace a barta ta tashi a bacci tukun" ajiyan zuciya nayi don farin ciki su yaa kamal ma sai yanzu suka iya zama tunda muka zo, gashi su yaa ahmed sai waya sukeyi suji ya jikin mammy, ficewa nayi don shan iska naje gefen motan ina zaune, wayata naciro ina duba hotonshi gashi na masa alkawarin rabuwa dashi inya duba Mammy yanzu ya dubata , toh ta ina yasan cewa Mammy ce? ko Abamama yamishi bayani shima kuma yaganmu tare?, . gashi bazan iya saba alkawari ba don haka bazan kara takura shi ba zanna kallonsa daga nesa inyaso ciwon sonshi sai ta kasheni kawai , hawaye ne suke bin idanuna ji nayi mutum akaina daga idon dazanyi naga shine " Ciwonta ba mai tsanani bane sosai ana mata surgery zakuji shiru" yana fada yana mikomin tissue na karba ina goge hawayena sannan yace " da fatan baki manta da alkawarinki ba?" nan ma na gyada masa kai , yayi murmushi sannan yace " na gode" yajuya zai tafi na kamo riganshi ta gefe hawaye na bin idona sannan nace " Nasan duk wata mace da zata ga ko taji abunda nayi zata ji haushi iya matuka domin na bada mata, amma ban damu ba yau zan fada maka irin son da nake maka, naga kana dangantani da sauran matan da suke binka wallahi ni daban ce kuma wataran zaka shaida so ne dana ke maka donAllah ba don abun duniya ba, ba kuma zandena ba karkaga don zandena takura ka yazama na dena sonka wallah ko kadan , sonka yanzu na fara sai dai na mutu" shiru yayi yana manaki a sanyaye yafice nikuwa na ruguje da kuka alokacin na lura ashe Abamama na tsaye a bayanmu yanajin bayanina. . #ays
=== CIWON IDANUNA 7 === . Ya karaso a hankali sannan yace " meya faru? har kike fadan wannnan kalamun wa namiji?" jikina a sanyaye na saka kaina a kasa domin na balain jin kunya a duniya bana boye komi wa Abamama don haka sai naji wani iri jin yaji yakuma gane me nake nufi, ganin ban bashi amsa ba yasa yace " idan munje gida zamuyi magana" na gyada kai biye da ajiyan zuciya, kafin nan zansamo bayani ko amsan da zan bashi, wucewa nayi nabi bayansa muka tsaya dasu yaa kamal dukkansu suna jimami, har lokacin Mammy bata tashi ba, ganin na gaji da zama yasa na cigaba da yawo a asibitin cike da tunanin makomar son da nakewa Aliyu, tsaye na ganshi da wani suna gaisawa hakan yasa na tsaya ina kare masa kallo, ya matukar burgeni wani dadi nakeji idan ina kallonshi har suka gama gaisawa yabiyo ta hanya ta, da sauri na kau da kaina ina neman hanyan buya kar yayi tunanin da gangan nake binshi aikuwa nayi latti domin kafa ya samin nayi tuntube na fadi, . screen din wayata ce tafashe na dauko a hankali na karkade gyale ta sannan na dauko wayan ina dubawa, ko kadan zuciyata bata tunkushe ba balle naji haushi duk da tsananin son wayan da nakeyi, wayar yayi da kuma tsadai bala'i amma nayi murmushi kafin na dago har ya fice, girgiza kaina nayi sannan na ci gaba da tafiya. Ban koma ba sai magrib , ina isa naga suna ta alwala suna shirin Zuwa masallaci , yaa kamal na ganina yace " kiyi sauri ta farka dama ke muke nema ina kika kai wayanki?" sai alokacin na duba ashe wayan da ta fashe ta mutu, nayi murmushi nace " wayar ta fadi a hannuna dazu ta fashe ne wallahi" kallon mamaki suka bini dashi don abinda bantaba yi ba kenan, fasa waya! suna wucewa na shige ciki Mammy na zaune sanye da drip a hannunta murmushi tamin dasauri na isa gefenta na zauna, "mammy ya jikin?" "da sauki lele ta" na rungomota na kwanta ajikinta kadan, duk da dan nauyi da nake dashi, bai hanata rikoni ba, jina ajikinta yasa hawayen da suke makale suka karasa fitowa, tuni nayi rafin hawaye a jikinta, zama tayi da kyau tare da cewa "lafiya? ba fa yau na fara kwanciya ciwo ba, ko akwai abunda ya sameki ne?" ai kaman ta kara min hawaye, wasu zafafan kuka naji tuni nafarayi da karfina, ita kuwa tsayawa tayi tana ganin ikon Allah, har su Abamama suka shigo cikin dakin ban bar kuka ba sannan bantashi nayi salah ba, yana shigowa ta bishi da kallo shima kallon nawa yakeyi duk da babu mamaki a fuskansa, tace masa " ka ganta fa, tun da tashigo take kuka, ko akwai abunda ke samunta ne? tana daga min hankali" hanyoni yayi muka fice waje, ya zaro min ido " baki da tausayi ne? .. kina ganin halin da mahaifiyar ki take ciki amma kina so ki daga mata hankali meye amfanin haka? karki kuskura ki gayamata komi har sai ta samu sauki kinajina ko?" gyada kai nayi tare da wucewa toilet na dauro alwala, nayi sallah yaa kamal kuma suna gefen Mammy hartayi bacci, likitan da yazo dubata yace dasauki kar a daga mata hankali sannan kar atasheta a bacci, washegari za'a wuce da ita abuja, suu yaa kamal sun tafi gida ni kadai narage da umma lami kanwar mammy da tazo bayan isha har lokacin Mammy bata tashi ba, mu zamu kwana da ita duk da damuwan da ya cunkushe min bai hanani addua wa Aliyu da mahaifiyata fata ta shiryuwan Aliyu ko zai bar shaye shayen da yakeyi musamman da na tuna Amrah tace mun karfe goma na dare zuwa sha biyu toh duk acikin maye yake yinta, a wannan lokacin nake masa addua har bacci ya kwashen. Can acikin baccin naji Umma lami na salari farkawan da zanyi naga Mammy tana aman jini, . a gigice na mike ina kiran sunanta amma shiru babu amsa sai amai, ficewa nayi ko dankwali babu na nufi corridorn tunda aka fito da ita daga ICU ankaita ward nurse nagani na rikota ta biyoni ganin halin da mammy take ciki ta fita da gudu don kiran likita, alokacin na fara kiran wayan Aliyu bai dauka ba can na kara kira bai dauka ba sai data kusan tsinkewa cikin maye ya dauka alokacin na duba naga lokaci karfe sha daya saura, wasu zafafan hawaye suka biyo sahun idanuna da karfi nace " ka taimaka Mammy babu lafiya sai aman jini take don Allah ka bar mayennan kazo ka ceceta" dulum naji ankashe waya, a gigice na wurga wayan lokacin likitoti sun shigo kenan aka fitar damu , tunda nake bantaba shiga tashin hankali irin wannan ba mammy na kwanciya a asibiti amma bata aman jini minti sha biyar cak sai gashi sunfito, kowa a sanyaye don alokacin har su abamama sun iso asibitin dasu yaa kamal, likitan ya tambayi waye guardian dinta abamama yace shine anan yake cewa Allah ya dauki ranta, INNALILAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN jiri naji yana diba na sai kawai gani a kasa bansan inda nake ba. . Bude idona da zanyi banga kowa ba illa shi da yake tsaye, rike da takarda ahannunsa yana kalla, daga gani anyi echo ne ko scanning wanda dama ba sabon abu bane aguna tsantsan yawaita yi da nakeyi, sai dai bansan dalilin kwanciya ta ba na tsaya tunanin me ya faru dani, cak na tuna da rasuwar mahaifiyata bansan lokacin da na fara kokarin mikewa ba hakan ya jawo da hankalinsa kaina, dasauri ya riko hannuna da nake kokarin cire calula da akasamin na ruwa, ba tare da yace komi ba ya mayar da hannun ni kuma idanuna ya cike da hawaye nace masa " da wasa ne ba ta mutu ba ko?" === CIWON IDANUNA 7 === . Ya karaso a hankali sannan yace " meya faru? har kike fadan wannnan kalamun wa namiji?" jikina a sanyaye na saka kaina a kasa domin na balain jin kunya a duniya bana boye komi wa Abamama don haka sai naji wani iri jin yaji yakuma gane me nake nufi, ganin ban bashi amsa ba yasa yace " idan munje gida zamuyi magana" na gyada kai biye da ajiyan zuciya, kafin nan zansamo bayani ko amsan da zan bashi, wucewa nayi nabi bayansa muka tsaya dasu yaa kamal dukkansu suna jimami, har lokacin Mammy bata tashi ba, ganin na gaji da zama yasa na cigaba da yawo a asibitin cike da tunanin makomar son da nakewa Aliyu, tsaye na ganshi da wani suna gaisawa hakan yasa na tsaya ina kare masa kallo, ya matukar burgeni wani dadi nakeji idan ina kallonshi har suka gama gaisawa yabiyo ta hanya ta, da sauri na kau da kaina ina neman hanyan buya kar yayi tunanin da gangan nake binshi aikuwa nayi latti domin kafa ya samin nayi tuntube na fadi, . screen din wayata ce tafashe na dauko a hankali na karkade gyale ta sannan na dauko wayan ina dubawa, ko kadan zuciyata bata tunkushe ba balle naji haushi duk da tsananin son wayan da nakeyi, wayar yayi da kuma tsadai bala'i amma nayi murmushi kafin na dago har ya fice, girgiza kaina nayi sannan na ci gaba da tafiya. Ban koma ba sai magrib , ina isa naga suna ta alwala suna shirin Zuwa masallaci , yaa kamal na ganina yace " kiyi sauri ta farka dama ke muke nema ina kika kai wayanki?" sai alokacin na duba ashe wayan da ta fashe ta mutu, nayi murmushi nace " wayar ta fadi a hannuna dazu ta fashe ne wallahi" kallon mamaki suka bini dashi don abinda bantaba yi ba kenan, fasa waya! suna wucewa na shige ciki Mammy na zaune sanye da drip a hannunta murmushi tamin dasauri na isa gefenta na zauna, "mammy ya jikin?" "da sauki lele ta" na rungomota na kwanta ajikinta kadan, duk da dan nauyi da nake dashi, bai hanata rikoni ba, jina ajikinta yasa hawayen da suke makale suka karasa fitowa, tuni nayi rafin hawaye a jikinta, zama tayi da kyau tare da cewa "lafiya? ba fa yau na fara kwanciya ciwo ba, ko akwai abunda ya sameki ne?" ai kaman ta kara min hawaye, wasu zafafan kuka naji tuni nafarayi da karfina, ita kuwa tsayawa tayi tana ganin ikon Allah, har su Abamama suka shigo cikin dakin ban bar kuka ba sannan bantashi nayi salah ba, yana shigowa ta bishi da kallo shima kallon nawa yakeyi duk da babu mamaki a fuskansa, tace masa " ka ganta fa, tun da tashigo take kuka, ko akwai abunda ke samunta ne? tana daga min hankali" hanyoni yayi muka fice waje, ya zaro min ido " baki da tausayi ne? .. kina ganin halin da mahaifiyar ki take ciki amma kina so ki daga mata hankali meye amfanin haka? karki kuskura ki gayamata komi har sai ta samu sauki kinajina ko?" gyada kai nayi tare da wucewa toilet na dauro alwala, nayi sallah yaa kamal kuma suna gefen Mammy hartayi bacci, likitan da yazo dubata yace dasauki kar a daga mata hankali sannan kar atasheta a bacci, washegari za'a wuce da ita abuja, suu yaa kamal sun tafi gida ni kadai narage da umma lami kanwar mammy da tazo bayan isha har lokacin Mammy bata tashi ba, mu zamu kwana da ita duk da damuwan da ya cunkushe min bai hanani addua wa Aliyu da mahaifiyata fata ta shiryuwan Aliyu ko zai bar shaye shayen da yakeyi musamman da na tuna Amrah tace mun karfe goma na dare zuwa sha biyu toh duk acikin maye yake yinta, a wannan lokacin nake masa addua har bacci ya kwashen. Can acikin baccin naji Umma lami na salari farkawan da zanyi naga Mammy tana aman jini, . a gigice na mike ina kiran sunanta amma shiru babu amsa sai amai, ficewa nayi ko dankwali babu na nufi corridorn tunda aka fito da ita daga ICU ankaita ward nurse nagani na rikota ta biyoni ganin halin da mammy take ciki ta fita da gudu don kiran likita, alokacin na fara kiran wayan Aliyu bai dauka ba can na kara kira bai dauka ba sai data kusan tsinkewa cikin maye ya dauka alokacin na duba naga lokaci karfe sha daya saura, wasu zafafan hawaye suka biyo sahun idanuna da karfi nace " ka taimaka Mammy babu lafiya sai aman jini take don Allah ka bar mayennan kazo ka ceceta" dulum naji ankashe waya, a gigice na wurga wayan lokacin likitoti sun shigo kenan aka fitar damu , tunda nake bantaba shiga tashin hankali irin wannan ba mammy na kwanciya a asibiti amma bata aman jini minti sha biyar cak sai gashi sunfito, kowa a sanyaye don alokacin har su abamama sun iso asibitin dasu yaa kamal, likitan ya tambayi waye guardian dinta abamama yace shine anan yake cewa Allah ya dauki ranta, INNALILAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN jiri naji yana diba na sai kawai gani a kasa bansan inda nake ba. . Bude idona da zanyi banga kowa ba illa shi da yake tsaye, rike da takarda ahannunsa yana kalla, daga gani anyi echo ne ko scanning wanda dama ba sabon abu bane aguna tsantsan yawaita yi da nakeyi, sai dai bansan dalilin kwanciya ta ba na tsaya tunanin me ya faru dani, cak na tuna da rasuwar mahaifiyata bansan lokacin da na fara kokarin mikewa ba hakan ya jawo da hankalinsa kaina, dasauri ya riko hannuna da nake kokarin cire calula da akasamin na ruwa, ba tare da yace komi ba ya mayar da hannun ni kuma idanuna ya cike da hawaye nace masa " da wasa ne ba ta mutu ba ko?" ba tare da tsagaitawa ba kawai yace "da gaske ne" wani karfi yazo min tare da tsantsan tsana a fuskata na kalleshi sannan nace " tunda ka kashe min mahaifiya ai dole kazo ka danne ni anan, ka barni naje naganta!" da karfi nake fadan maganan sai dai kuma babu alamun tsoro ko mamaki a fuskanshi da nake furtawa, fizge hannuna na yi da karfi ina kokarin saukowa, da karfi ya rikoni yayinda yakira nurse dasauri ta shigo dakin suka fara kokarin danneni amma ina ihu nakeyi ina kuka abarni naje naga mahaifiyata, ga munanan kalamun da nake jifanshi dashi don gani nakeyi rashin zuwansa da wuri ya kara janyo dadewan rasuwanta, wani irin kuka nakeyi alokacin da ya damkoni da karfi idona yana kallon nashi " meye haka?" "kina nema ki kashe kanki, do you have idea how many days kikayi anan?, keda ya kamata ki zama kina mata addua amma kina kuka kaman bakida tawakkali?" sauran hawayen da suke fuskata su suka kara makalewa alokacin ya sakeni ya jingineni, yace nurse din ta kawo min ruwan tea na sha, karewa asibitin kallo nayi sai dai bangane dakin ba, tsantsan yawan kwanciya a asibitin TH nariga nasan kalan dakunan su, wannan dakin babbane sannan babu kowa aciki sai nurse mai kula dani sai shi dayake tsaye ya zura min ido, damuwata mahaifiyata ban iya danne raina ba donhaka nayi kuka ta mai isa na dukkansu ba wanda ya lallasheni na rasa ta inda zan fara tunanin cewa mammy ta rasu ta barni, wuni nayi ina kuka kuma abun mamaki har lokacin yaki fita a dakin anzo ankirashi yaki fita hatta wani tsoho wanda nake tsammani babbanshi ne yazo yakirashi yace bawanda ya isa ya fiddashi sai dai yabar aiki a asibitin haka suka hakura suka fice, sai magrib yafita yaje sallah, alokacin na tambayi nurse din wani asibiti ne ganin bata da niyyan ko lekawa waje, tace national hospital abun ya matukar bani mamaki me yakaini asibitin? nida nake bauchi? sai dai na hadiye komi na tsaya tunanin toh ina yanuwana kaman tashiga raina aikuwa tace " brothers dinki suna zuwa dare dare su ga yakike, ba'a barin kowa ya zauna ne sai nurses" shiru nayi hawaye na ci gaba da zubo min har bacci ya kwashen. Bude idona da zanyi naga shine a zaune a gefeta yana kokarin gyra min bargo na, hannu naja zan rufe jikin da kaina don gudun kar ya tabani bai kulani ba sai da ya rufe sannan ba tare da ya kallen ba yacewa nurse din " idan zata iya mikewa kisata tayi sallah, its over a six days tana kwance ba full abinci babu sallah babu wanka" bansan lokacin da na zaro ido sosai ina kallonsa ba, yanzu yana nufin kwanana shida bana hayyacina? lallai na jijjiga Allah sarki ko ya abamama yake ciki yanzu sai Allah, ankai Mammy kenan babu ni , Allah sarki mammy na,da taimakon nurse din ta mikar dani sai da naji jiri tsantsan babu karfi a jikina muka shiga bandakin ta min wanka duk da gardaman da na mata sai da naji Aliyu na cewa in ban tsaya ba zai shigo yamin nasan zai rina donhaka tuni na nutsu na yi wankan na dauro alwala, ina fitowa naga kaya akan gadon ya siyo ita ta taimaka min na sakasu sannan ta shimfida min sallaya na ma rasa hanyan da zanfara biyan sallolin dake kaina, gashi bazan iyayi a zaune ba donhaka da na zauna sai dana biyasu kaf sannan namike na kwanta agun bansan bacci ya kwashen ba. Hannu naji akaina bude idon da zanyi naga yaa kamal da yaa Amir dukkansu sun rame sunyi baki can gefe Abamama ne dasu yaa usman, wani kuka yafito min ba shiri kawai na fara, dukkansu ba wanda ya iya lallashina hatta Abamama dake gefe yana sharen hawaye, yaa usman ne yazo yake cemin " ki daina kuka addua zaki mata karki manta kema baki da lafiya kuma ciwonki baya son tashin hankali kidena damuwa kinji?". ba tare da tsagaitawa ba kawai yace "da gaske ne" wani karfi yazo min tare da tsantsan tsana a fuskata na kalleshi sannan nace " tunda ka kashe min mahaifiya ai dole kazo ka danne ni anan, ka barni naje naganta!" da karfi nake fadan maganan sai dai kuma babu alamun tsoro ko mamaki a fuskanshi da nake furtawa, fizge hannuna na yi da karfi ina kokarin saukowa, da karfi ya rikoni yayinda yakira nurse dasauri ta shigo dakin suka fara kokarin danneni amma ina ihu nakeyi ina kuka abarni naje naga mahaifiyata, ga munanan kalamun da nake jifanshi dashi don gani nakeyi rashin zuwansa da wuri ya kara janyo dadewan rasuwanta, wani irin kuka nakeyi alokacin da ya damkoni da karfi idona yana kallon nashi " meye haka?" "kina nema ki kashe kanki, do you have idea how many days kikayi anan?, keda ya kamata ki zama kina mata addua amma kina kuka kaman bakida tawakkali?" sauran hawayen da suke fuskata su suka kara makalewa alokacin ya sakeni ya jingineni, yace nurse din ta kawo min ruwan tea na sha, karewa asibitin kallo nayi sai dai bangane dakin ba, tsantsan yawan kwanciya a asibitin TH nariga nasan kalan dakunan su, wannan dakin babbane sannan babu kowa aciki sai nurse mai kula dani sai shi dayake tsaye ya zura min ido, damuwata mahaifiyata ban iya danne raina ba donhaka nayi kuka ta mai isa na dukkansu ba wanda ya lallasheni na rasa ta inda zan fara tunanin cewa mammy ta rasu ta barni, wuni nayi ina kuka kuma abun mamaki har lokacin yaki fita a dakin anzo ankirashi yaki fita hatta wani tsoho wanda nake tsammani babbanshi ne yazo yakirashi yace bawanda ya isa ya fiddashi sai dai yabar aiki a asibitin haka suka hakura suka fice, sai magrib yafita yaje sallah, alokacin na tambayi nurse din wani asibiti ne ganin bata da niyyan ko lekawa waje, tace national hospital abun ya matukar bani mamaki me yakaini asibitin? nida nake bauchi? sai dai na hadiye komi na tsaya tunanin toh ina yanuwana kaman tashiga raina aikuwa tace " brothers dinki suna zuwa dare dare su ga yakike, ba'a barin kowa ya zauna ne sai nurses" shiru nayi hawaye na ci gaba da zubo min har bacci ya kwashen. Bude idona da zanyi naga shine a zaune a gefeta yana kokarin gyra min bargo na, hannu naja zan rufe jikin da kaina don gudun kar ya tabani bai kulani ba sai da ya rufe sannan ba tare da ya kallen ba yacewa nurse din " idan zata iya mikewa kisata tayi sallah, its over a six days tana kwance ba full abinci babu sallah babu wanka" bansan lokacin da na zaro ido sosai ina kallonsa ba, yanzu yana nufin kwanana shida bana hayyacina? lallai na jijjiga Allah sarki ko ya abamama yake ciki yanzu sai Allah, ankai Mammy kenan babu ni , Allah sarki mammy na,da taimakon nurse din ta mikar dani sai da naji jiri tsantsan babu karfi a jikina muka shiga bandakin ta min wanka duk da gardaman da na mata sai da naji Aliyu na cewa in ban tsaya ba zai shigo yamin nasan zai rina donhaka tuni na nutsu na yi wankan na dauro alwala, ina fitowa naga kaya akan gadon ya siyo ita ta taimaka min na sakasu sannan ta shimfida min sallaya na ma rasa hanyan da zanfara biyan sallolin dake kaina, gashi bazan iyayi a zaune ba donhaka da na zauna sai dana biyasu kaf sannan namike na kwanta agun bansan bacci ya kwashen ba. Hannu naji akaina bude idon da zanyi naga yaa kamal da yaa Amir dukkansu sun rame sunyi baki can gefe Abamama ne dasu yaa usman, wani kuka yafito min ba shiri kawai na fara, dukkansu ba wanda ya iya lallashina hatta Abamama dake gefe yana sharen hawaye, yaa usman ne yazo yake cemin " ki daina kuka addua zaki mata karki manta kema baki da lafiya kuma ciwonki baya son tashin hankali kidena damuwa kinji?".
07066508080
07066508080
=== CIWON IDANUNA 8 === .
Bude idona da zanyi banga kowa ba illa shi da yake tsaye, rike da takarda ahannunsa yana kalla, daga gani anyi echo ne ko scanning wanda dama ba sabon abu bane aguna tsantsan yawaita yi da nakeyi, sai dai bansan dalilin kwanciya ta ba na tsaya tunanin me ya faru dani, cak na tuna da rasuwar mahaifiyata bansan lokacin da na fara kokarin mikewa ba hakan ya jawo da hankalinsa kaina, dasauri ya riko hannuna da nake kokarin cire calula da akasamin na ruwa, ba tare da yace komi ba ya mayar da hannun ni kuma idanuna ya cike da hawaye nace masa " da wasa ne ba ta mutu ba ko?" ba tare da tsagaitawa ba kawai yace "da gaske ne" wani karfi yazo min tare da tsantsan tsana a fuskata na kalleshi sannan nace " tunda ka kashe min mahaifiya ai dole kazo ka danne ni anan, ka barni naje naganta!" da karfi nake fadan maganan sai dai kuma babu alamun tsoro ko mamaki a fuskanshi da nake furtawa, fizge hannuna na yi da karfi ina kokarin saukowa, da karfi ya rikoni yayinda yakira nurse dasauri ta shigo dakin suka fara kokarin danneni amma ina ihu nakeyi ina kuka abarni naje naga mahaifiyata, ga munanan kalamun da nake jifanshi dashi don gani nakeyi rashin zuwansa da wuri ya kara janyo dadewan rasuwanta, wani irin kuka nakeyi alokacin da ya damkoni da karfi idona yana kallon nashi " meye haka?" "kina nema ki kashe kanki, do you have idea how many days kikayi anan?, keda ya kamata ki zama kina mata addua amma kina kuka kaman bakida tawakkali?"
sauran hawayen da suke fuskata su suka kara makalewa alokacin ya sakeni ya jingineni, yace nurse din ta kawo min ruwan tea na sha, karewa asibitin kallo nayi sai dai bangane dakin ba, tsantsan yawan kwanciya a asibitin TH nariga nasan kalan dakunan su, wannan dakin babbane sannan babu kowa aciki sai nurse mai kula dani sai shi dayake tsaye ya zura min ido, damuwata mahaifiyata ban iya danne raina ba donhaka nayi kuka ta mai isa na dukkansu ba wanda ya lallasheni na rasa ta inda zan fara tunanin cewa mammy ta rasu ta barni, wuni nayi ina kuka kuma abun mamaki har lokacin yaki fita a dakin anzo ankirashi yaki fita hatta wani tsoho wanda nake tsammani babbanshi ne yazo yakirashi yace bawanda ya isa ya fiddashi sai dai yabar aiki a asibitin haka suka hakura suka fice, sai magrib yafita yaje sallah, alokacin na tambayi nurse din wani asibiti ne ganin bata da niyyan ko lekawa waje, tace national hospital abun ya matukar bani mamaki me yakaini asibitin? nida nake bauchi? sai dai na hadiye komi na tsaya tunanin toh ina yanuwana kaman tashiga raina aikuwa tace " brothers dinki suna zuwa dare dare su ga yakike, ba'a barin kowa ya zauna ne sai nurses" shiru nayi hawaye na ci gaba da zubo min har bacci ya kwashen. Bude idona da zanyi naga shine a zaune a gefeta yana kokarin gyra min bargo na, hannu naja zan rufe jikin da kaina don gudun kar ya tabani bai kulani ba sai da ya rufe sannan ba tare da ya kallen ba yacewa nurse din " idan zata iya mikewa kisata tayi sallah, its over a six days tana kwance ba full abinci babu sallah babu wanka" bansan lokacin da na zaro ido sosai ina kallonsa ba, yanzu yana nufin kwanana shida bana hayyacina? lallai na jijjiga Allah sarki ko ya abamama yake ciki yanzu sai Allah, ankai Mammy kenan babu ni , Allah sarki mammy na,da taimakon nurse din ta mikar dani sai da naji jiri tsantsan babu karfi a jikina muka shiga bandakin ta min wanka duk da gardaman da na mata sai da naji Aliyu na cewa in ban tsaya ba zai shigo yamin nasan zai rina donhaka tuni na nutsu na yi wankan na dauro alwala, ina fitowa naga kaya akan gadon ya siyo ita ta taimaka min na sakasu sannan ta shimfida min sallaya na ma rasa hanyan da zanfara biyan sallolin dake kaina, gashi bazan iyayi a zaune ba donhaka da na zauna sai dana biyasu kaf sannan namike na kwanta agun bansan bacci ya kwashen ba. Hannu naji akaina bude idon da zanyi naga yaa kamal da yaa Amir dukkansu sun rame sunyi baki can gefe Abamama ne dasu yaa usman, wani kuka yafito min ba shiri kawai na fara, dukkansu ba wanda ya iya lallashina hatta Abamama dake gefe yana sharen hawaye, yaa usman ne yazo yake cemin " ki daina kuka addua zaki mata karki manta kema baki da lafiya kuma ciwonki baya son tashin hankali kidena damuwa kinji?". Gyada kai nayi amma na gagara tsagaita kukan saiga Aliyu yashigo ganin yadda nake kuka harda tari ya karaso kaina da sauri yace " don Allah kuyi hakuri ku barta haka, ganinku daga mata hankali yake and kunsan yanayin jikintan na muku bayanin ciwonta" ba shiri suka fara ficewa aikuwa na mike da zummar na bisu, rikoni yayi da karfinsa amma ina daujewa tare da yin wani irin kuka dukkansu da kuka suka fice sunan Mammy kawai nake kira ina cewa " yaa kamal don kunga mammy bata nan shine zaku tafi ku barni ko? Abamama harda kai ? don Allah kudawo kukaini gun Mammy wayyo Allah na nashiga uku" da karfi Aliyu ya kwantar dani nurse din tamin allura saikuma bacci.
In tagaita muku rayuwata Ni Nadrah rayuwan da na shiga sakamakon rashin mahaifiyata yasa har wani hauka hauka nakeyi na mintuna, ga ciwon dake damuna wanda duk yan gidanmu boye min sukeyi babu mai fadamin, kullum suna guna a asibiti duk da ba ko yaushe ake barinsu su zauna aguna ba don da zaran na gansu Mammy nake tunawa to anan zanfara kuka yakai ga har zuciyata inajin abu a tokare tamkar fata haka ya cunkushe sai wani lokaci jini yabiyo kasan hancina, gashi Hamma Aliyu da na sani ya canja domin kuwa baya bari kowani likita ya kula dani sai shi sannan a fadin yaa kamal tunda aka kawoni asibiti garin yadena zuwa bauchi safe rana dare hidima ta yake, sai dai har lokacin maganan da ta wuce minti goma bamu tabayi ba, gani nakeyi da yana kusa baiyi wannan shaye shayensa da Mammy bata rasu ba, A hankali na fara samun sauki da taimakon adduoi da yanuwana suka sani aciki da saukan qurani tuni na warware nan aka fara batun sallama, Randa zaa sallamen ina kan gaba don ko ba komi zan ga hasken rana da na farin wata rike da hoton Mammy na akirjina wanda na dauka acikin kayan yaa kamal ba yadda baiyi nabashi ba naki yarda, Aliyu ne yashigo dakin yace duk su fita zaimin magana suna ficewa ya kallen sama da kasa sannan yace " sallamanki ba yana nufin kije ki kwakulo wani sabon ciwo bane kidaure ki lallashi zuciyanki da damuwanki karki kuskura zuciyanki ta buga ta biyu saboda ta buga ana farko kuma ke kanki kingani bai miki ta dadi ba, nayi bayanin ciwonki wa mahaifinki ki sameshi zai gaya miki dallah dallah harda na mammynki , last but not the least karki yadda ki fara soyayya a yanzu!"
shi kanshi da ya fadi maganan jira yakeyi yaji me zance aikuwa na bashi mamaki tare da cewa "toh" sannan na fito duk da cewa ya kaikaya min inda ke min zafi amma ban nuna masa ba muna fitowa na shiga motan Abamama yana gidan baya sai driver agaba muka nufi hanyan airport sai bauchi kawai , shigowata gidan sai naga tamin girma jira nakeyi naga mammy amma har lokacin shiru, a hankali na nufi dakinta ina dubawa kaman zan ganta zama nayi akan gadonta na bude wani sabon shafin kuka, Umma lami ce tashigo dakin ta rikoni amma ina itama sai kuka sai da mukayi mai isanmu nayi alwala nayi sallah rakaah biyu na mata addua, duk sai naji gidan yamin girma duk da akwai yayuna da sauran mutane Abamama kam kana ganinshi kaga damuwa aranshi duk da cewa mutum ne mai dauriya da hakuri sai dai akan mammy sai addua kawai. A yammacin ranan Ammaty tazo donma umma tace min da ita akayi sadaqan ukun mammy kullum tana zuwa da kuma yan ajinmu na makaranta duk sunzo su, alokacin ma sai zuwa akeyi taaziya mutane daban daban, aciki harda Amrah donma Sunzo da hajiyansu da nake asibiti a abuja, jikina babu karfi Amma haka na daure nake zama , Abamama yaje TH yadauko min likita da zai na duba ni duk da banso ba amma yace naje falon saboda gudun tashin ciwona, shigana falon yana zaune kansa akasa kare masa kallo nayi kallo daya, saurayine ban jin zai kai talatin, sai dai asain bahaushe ne mai kyau yana rike da wayansa na zauna, yayi murmushi sannan yace " yajikin naki?" " da sauki" " me da me yake damunki yanzu?" " ciwon kai ne kawai bayan nan sai jiri kadanina fada ina wasa da yatsuna dago idon da zanyi naga idonsa a kaina tuni na kawar da idona banason irin kallon da yake min, " ya karin hakuri?, Allah ya jikanta ya mata rahama" na amsa da "ameen" anan yayi gwaje gwajensa sannan ya koma ya zauna yace " ki rage tunani" shiru nayi alokacin yayi ta min nasiha masu shiga jiki, jikina yayi sanyi na share hawayen da suka zubo min sannan yace akawomin abinci da naki yarda da kanshi yake diba yana bani, yayi ta tadi yana son sani dariya tun bana yi har nazo na sake raina don ya cire min kawaicin dake raina, da na gama ci sannan ya tafi. Acikin satin na koma makaranta cikin ikon Allah Dr.Hisham ne yake kaini duk aikin da yakeyi zai yanke yazo ya kaini sannan idan na gama sai yazo ya daukeni, a duk lokacin da yaga ina kadaici nan zai debe min kewa abinci kuwa safe rana dare yana kansa da kansa yake bani, daga yayuna har Abamama godiya suke masa sosai domin kuwa yana taimakona yana ragemin kadaici, tuni na saba na fara dawowa yadda nake duk da tunanin Mammy da kuma tsananin son Aliyu da nakeyi wanda rabona dashi tun a asibiti a abuja kusan wata hudu kenan.
=== CIWON IDANUNA 9 === .
Mun gama exams din makaranta alokacin na dawo gida hutu , Umma lami ta tafi garinsu ya zama da ga ni sai talatu mai aiki sai masu gadi sai kuma yayuna da Abamama,inda Abamama yafara takurawa yaa kamal yafito da mata don yayi aure ko dan albarkaci na, Hisham kuwa munsaba duk da kokarinsa na nuna min yana sona, tsananin kulawa da yake nunamin dasauransu bai sa na fara sonsa ba, zuciyata tana nan akan bakanta na Aliyu, wani lokacin na kan kwanta a daki nayi kuka sosai na share hawayena na fito, Amrah kuwa munsaba sosai itakam har kunya na takeji intaji yayan nata baya nemana nima kuma ban nemeshi ba sai dai alkawarin da nayi masa ne ban manta ba nacewa bazan kara damunsa ba, " nikam yanzu kin dena son Hamma Aliyu ne?" cewar Amrah wata rana da tazo gidanmu "me kika gani?" " na ga kin daina sonshi" " ae mana, mutumin da baya sona ai dole na bar sonshi" "hmm, ban yarda ba" " me yasa?" " sai dai banyi tadinsa ba sai kin min, duk da baki nunawa kin damu amma na lura kina son sanin halin da yake ciki" zahirin gaskiya ta fada sai dai abunda yafi cimin rai shine duk kulawan da yamin a asibiti dama ba sona yakeyi ba? alokacin na dauka so na yake amma tunda na dawo bauchi bai kara waiwaiya ta ba abunda yafi komi cimin rai kenan, zanso na tambayesa akwai tambayoyi da ya kamata na masa,kaman ta shiga raina tace "
yau zai zo gari bansan ko kina son ku hadu ba" " ae inaso , saboda ina da tambayoyin da zan masa" " ba damuwa inyazo zan sanar dake" aikuwa yana isowa ta kirani a waya, yana asibiti na dauki mota na fice , dai dai shiga asibitin na hadu da dr.hisham yana ganina ya fara murmushi " yau abun mamaki kin zo ganina" yake nayi tare da cewa " a a gurin Dr. Haidar na zo" tuni annurin fuskanshi ta bace tunda yasan girman Aliyu araina kusan kullum sai nayi magananshi, ban jira yace komi ba nasa kai naje office dinsu yana shirin fita na shiga donhaka yakoma ya tsaya files din hannunsa yake duba ba tare da ya kalleni ba yace " lafiya?" " nazo na tambayeka ne" "inajinki" " kulawa da kayi da ni a asibiti me yake nufi?" " tausayi" " ban gane tausayi ba" " mahaifiya ta wuce wasa, alokacin kuma kin rasata, i was trying to be a good doctor" yana gama fada yazo zai wuce na sa hannu na toshe kofan, hawaye na zuba a idona don alokacin na gagara rike bakin cikina nace masa " kana nufin kace wasa dani kayi kenan?" " if its how you think YES" " Aliyu ina so ka sani, Soyayya ba karya bace, za ka yita kuma zakaji ko akwai dadi ko babu dadi" zuramin ido yayi na mintuna sannan yace " ko zanyi soyayya bazanyi dake ba, ballema bazanyi ba , me zaisa nasawa kaina ciwo akan wani abu wai shi soyayya, kiyi wa kanki nasiha domin sa soyayya ko damuwa aranki ba naki bane a wannan lokacin" yana gama fada ya fice nikuma me zanyi inbanda kuka kaman raina zai fita, Dr.Hisham ne ya shigo office din ya kalleni daga farko har kasa sannan ya zauna agefe yana kallona sai dana gama kuka na yaja numfashi sannan yace "yaushe zaki daina sawa kanki cutar da babu magani? yaushe zaki daina hangen abunda ba naki ba ki dubi abunda ke gefenki? shin baki lura da gefenki ba sai hangen nesa?""" Hmm! kayi hakuri dani ka daina sona Allah zai kawo maka sauki da wacce tafini" "tayaya za'ayi na hakura dake? bayan kuma kinsan irin son da nake miki, kin koya min yadda zan soki" " Yadda kake jin ba zaka iya rabuwa dani ba haka nima nake jin bazan iya rabuwa dakai ba, Soyayya ba karya bace, don haka bazan iya tursasa raina akan abunda nasan bazai yiwu ba" Shiru yayi kafin ya ce " ki fito mu tafi" " ba tare muka zo ba" girgiza kai yayi jin amsan da na bashi sannan ya fice, da kyar na sulale jiki na koma mota sai da nayi kuka mai isa na kafin na tafi gida. A lalacewan rayuwa har nayi exams dina na gama, yanzu ko Ammaty na fita hidimanta na ajiyeta agefe, rayuwata ta dawo ni kadai kamar mayya, yayuna daga masu makaranta sai masu aiki babu mai zaman gida haka ma mahaifina. ********** Rayuwa taci gaba da wuce min cikin daci da bakin ciki, domin wulakancin Hamma sai karuwa yakeyi baya kulani duk inda yake nikuwa ina makale awajen, sai dai ya tozartani ya wuce domin akwai ranar da mun shiga jifatu tare dashi bai san ina binsa ba keken hannunsa nake kalla duk abunda ya saka nima sai nasa, har akazo gun biya ban saniba na bugeshi da nawa juyowan da zaiyi yaga nine hannu yasa ya gaure ni da mari, alokacin na lura akwai guntun maye akansa, ya zageni sama da kasa ya kuma ce kar na kuskura na kara hada hanya dashi, hakika babu munin tozarta irin wannan hawaye ne suke bin idona sai dai bai gama maganar ba ya fadi agun da gudu naje na rikoshi hankali atashe mutane suka tayani kaishi mota na nufi asibiti dama kuma tun akan hanya na kira Amrah na sanar da ita, ta rigamu isa asibitin anan suka bashi gado ya sha baccinsa, ina zaune agun ya farka a razane na mike na bar dakin domin tun marin da yamin na tsorata dashi, a mota nan ma naci kuka na wanda ya zamo abinci agareni, A duk lokacin da nake kukan sai na tuna da Mammy domin kuwa da tana raye bazan yi wannan kadaicin ba, Uwa da dadi, .
koma wa ta gida na sami Abamama a falo yana ganina ya sauke jaridar hannunsa yace nazo, ina zama ya dafa kaina ya tsura min ido sannan yace " Meye matsalarki?" " yake nayi domin kuwa ni kaina nasan banda amsan tambayan anan yaci gaba da cewa " prof. ibrahim na department dinku yakiran, yace wannan semestern bakiyi kokari ba ko kadan, ke da kike da cgpa 4.76 me kuma yadawo dake 1.23? inyee? fisabililah meya sameki donAllah don annabi Nadrah!" a iya rayuwata zan iya kirga sau nawa mahaifina yakira suna na, yau muryarshi ta tabbatar min da cewa yaji ciwon result dina, katsemin tunani yayi yace "I am very disappointed in you! ya gayamin yace min ko kadan a aji in banda tunani ba abunda kikeyi, lectures ma baki zuwa, to ina kike zuwa? why would your cgpa drop massively like that? me yake damunki? worst result" tsaban bakin ciki bansan lokacin da na fara wani irin kuka ba, tsayawa yayi yana kallona bakinshi a bude " me kuma nayi? ba fa dukanki nayi ba!" "wayyo Allah mammy!" kukan da nake masa kenan, kawai sai na bashi tausayi nan fa ya fara lallabina sai hakuri yake ban nikuwa sai da nayi mai isata, duk atunaninsa batun mammy ne nikuwa harda batun Aliyu a alamarina, sai da muka gama sannan yamin waazi sosai yace na hakura da batun sa damuwa araina mammy insha Allah tana can tana aljanna, ban dai ce komi ba nan nashige daki, aikuwa dare nayi Hajiyatu takirani, Hajiyatu kakata ce mahaifiyar mammy, nan tayita lallabina itama sannan tace zata zo itama da kanta don umma lami ta tafi, sai da na nuna mata inajin bacci ta kwanta, anan nayi bacci sai dai rabi da rabi domin rabi mafarkin aliyu nayi.
********** Amrah tana IT a TH don haka na samu daman da zanna zuwa kullum don ganin Aliyu idan yana gari, duk da sai weekends yake zuwa nima sai weekends nake zuwa mata, in yana gari kullum tana office dinsa nima haka nake binta muje mu zauna, idan naje yadda ake ajiye dutse a manta dashi haka yakeyi dani sai dai ya kula kanwarsa amma nikam ko kallo banna isansa, ni kuwa zama nakeyi na zuba masa na muzurai musamman in yasaka kayansu farare na likitoti yasa gilashin idonsa kyau yakemin sosai kaman na hadiyesa, duk da shareni da yakeyi baya damuna damuwata shine in zan ganshi na gama biyan bukata ta, ko kuma inje inbi layin marasa lafiya in anzo kaina sai inshiga yana ganina yake daure fuska ko ya koreni ko kuma in yan mutuncinsa na kusa yaleko yacewa nurse karta barni nashigo takaini gun wani doctor bazai dubani ba kuma babu yarda na iya sai dai na hakura, ganin nafi sati biyu yana min haka da safe naje asibitin na kama layin inajira sai da naga saura mutum daya a gabana na fito da inhalern sannan nayita shaka, uhm ni ba asthma kuma inhalern ma mai karfi sosai, kuma dama nayi overdose din maganin ciwona atake agun na fadi , ji nakeyi kirjina yana nauyi sosai , sai suka yakemin kaman zai fadi, numfashi na yafara tsarewa dauka na sukayi cak suka nufi daki dani aka kirashi, yazo shi kaina idona ya tsaya kallona ya tsaya yi ganin ni ce yajuya ya tafi nurse din tana rikoshi amma bai juyo ba, tun ina gani har idona yarufe na sume bankuma san inda nake ba. Bude idona nayi a hankali sai kuma naga hajiyati, lumshe idon nayi don yaji da kuma iska da naji yana shiga min idon, riko hannuna naji anyi na kara bude idon a hankali sai kuwa naganta ido ya kumbura sosai bayanta kuma su yaa kamal ne da wata budurwa tana zaune itama cikin gyale tayi kyau sosai, hajiyati da sauri ta riko ni sosai sannan ta ce "ya jikin dai lele?" gyada kai nayi a hankali yayin da nake jin wani irin nauyi a kirjina kaman zai fadi kasa, ta daga kaina a hankali ta jingina da jikin pillow yaa kamal da wannan budurwan suka karaso kaina cikin sanyin jiki, cikin sanyin murya ta ce " ya jikinki?" na kalleta ina kokarin murmushi yaa kamal yace " sunanta ummi aisha" anan na gane me yake nufi wato dai budurwarsa kenan, a dai dai lokacin wani tari ya zo min a kirji ba shiri na yi shi wanda sai da nayi nadama domin kuwa ji nayi tamkar kirjina zai fado haka naci gaba da tarinnan kaman zan mutu a gigice yaa kamal yafita don kiran likita hajiyati kuwa duk ta rude haka zalika ummi aisha idonta duk ya ciko da hawaye, anan kawai sai ga tarin jini , na rike a hannuna ina kallo hankalina yayi balain tashi domin mammy na tuna itama haka tayi wannan tarin sannan ta rasu, duk da bansan sauran labarin ba, Abamaama boye min yakeyi ba yaso na sani, Dr.Hisham ne ya shigo a guje idonsa tayi jajur nan nurse ta biyo bayanshi, alokacin tarin ya tsaya, sai bari da jikina yakeyi wani allura yamin sannan ya kwantar dani fuskarshi kaman zaiyi kuka cikin takaici yace " don girman Allah hajiya ku taimaka yarinyannan ta daina tunanin da takeyi , ba karamin illa yake kara mata ba, ciwonta bai kai haka tsanani ba magani tana sha zai sauka don ma gadon shi tayi amma yanzu ta janyo wa kanta wani babban cuta daban fisabililah"
=== CIWON IDANUNA 10 === .
A yadda yake maganan cikin tsananin damuwa yasa ita kanta hajiyati tana damuwa daukan wayanta tayi ta fara kiran Abamama yana dauka tace yayi sauri yazo,
cikin minti ashirin sai gashi aikuwa tana kuka tace dr.Hisham ya masa bayani shikuwa dama kaman jira yakeyi ya zauna nan yace masa " Baba zan yi magana ne ba a matsayin likitan Nadrah ba zanyi magana ne a matsayin abokinta sannan kuma mai sonta" Abamama ya zaro ido don yanayin da Hisham yake magana dole jikin mutum yayi sanyi anan ya cigaba da cewa " Baba Nadrah tana da damuwa bansan ko ka sani ba, Amma akwai likitan mu anan likitan zuciya ne, Nadrah tana sonshi sosai amma baba baya sonta, son da take mishi yasa yanzu gaba daya ta dawo haka, wani zai dauka ko rasuwan mammy ne amma acikin dari kashi saba'in saboda shi ne, idan batayi hankali ba zata iya rasa ranta, kaga tsantsan nuna kaunar da take masa gudunta yake yi, nayi iya kokarina in janye hankalinta akanshi amma na kasa" dukka dakin kowa tsit yayi Abamama ya kallen amma na rasa gane kallon meye daya , gyran murya yayi sannan yace " wato Hisham na gode sosai da wannan labarin da ka bani, nayi sake sosai akan y'ata tun rasuwar mahaifiyata, Amma naji dadin wannan bayani insha Allah zan dau mataki da gaggawa" yana gama fada ya fice yabar dakin, ya kamal kuwa kaina ya iso alokacin sakon harara nake turawa Hisham shi kuwa ko ajikinsa ya fice yabarni irin wato na ci kaina kawai, yaa kamal yayi murmushi sannan yace " me ya hanaki fada mun tuntuni?" juya kaina nayi domin shi kanshi ya sani da ace fada masa nayi in bai makeni ba toh zansha mari cikin biyu za'ayi daya, ummi aisha kuwa jugum tayi tana ganin ikon Allah. Tun ranan Abamama bai dawo cikin asibitin ba, haka zalika ban hada ido da Haidar ba, hajiyati kadai ke jinyata sai yayuna idan sun zo, duk na jime na dawo abun tausayi, Ammati kullum tana cikin yimin test a makaranta, sati na na biyu Abamama ya shigo da Visa a hannunsa ga kuma epassport wanda ina tsammani nawa yayi renewing don tayi expire , jiki a sanyaye na zauna ina kokarin gaisheshi nan ya katseni " na saka kamal ya hada kayanki dukka zamu hadu a airport, ki wuce dubai kije gun Ammi(kanwar Mammy da take zama acan) , skul nan zanmiki differing ko kuma na nema miki transfer idan zai yiwu" tun da ya fara kallonsa nakeyi har ya idda yana gamawa nace "Abamama ba zanje ba". wani kallon mamaki yamin daga shi har hajiyati domin yadda na fada da confidence dina babu tsoro aikuwa ya gyra tsayuwa sannan yace " Nadrah idan zaki mutu anan sai an dauki gawanki ankai can don haka ki tashi ki zo ki wuce na karba miki ticket ki wuce abuja jirginku zai tashi karfe biyun dare. . Tashi nayi na mike na riko kafarsa ina kuka "Abamama kayi hakuri bazanje ba " ko kulani baiyiba, ya fice yana goge gefen idonsa alamun share hawaye a fuskarsa,kowa sai da ya tausaya min kukan da nakeyi agun, Yaa kamal ne yasa nurse din ta min wanka na shirya tsaf asibitin suka sallamen mukayi sallama da hajiyati da kuka, airport muka nufa cikin minti arbain da biyar muka isa abuja, muka yi zaman awa biyar, awannan zaman dr.Hisham yakirani mukayi sallama, muryarsa duk ta dishe alamun yana cikin bakin ciki, ni dai ko ajikina tunanina duk shine Aliyu, na kira numbanshi bai dauka ba don haka nakira Amrah nace mata zanyi tafiya amma zandawo don Allah ta gaishemin da yaa Aliyu tayi dariya kafin ta amsamin. Anan ma take sanar dani cewan yana abuja, rokonta nayi ta turo min address dinshi yana zaune a maitama har dadu house number nayi murmushi sannan na kashe wayan.
Anan muka shiga ethopian airline nan ma muka tsaya a addis baba wanda ke birnini ethopia, mukayi awa uku kafin muka wuce dubai duk wannan lokacin yaa kamal bai tanka min ba kaman kishiyoyi waya san meyake damunsa, oho nidai ina kissa yadda zan gudu,daga airport dinsu muka zauna jiran Motan gidan Ammi da zai zo yakaimu sharjah inda suke da zama, Yaa kamal yaje nemo mana coffee duk kayanmu na ajiye anan na mike sadaf sadaf na bar kayan agun sannan na koma cikin airport din na tambayi yaushe zansamu jirign zuwa nigeria a daren mutumin ya kallen yace nan da awa biyu, na ce to inaso na biya, yayi dariya sannan yace "ai bazai yiwu ba" duk cikin harshen turanci muke magana, a gigice nace masa " me yasa?" ya kallen yace " wannan fa international airport ne ba state zakije ba" duk da haka ban yarda ba nace " toh duba ko akwai wanda sukayi cancelling flight dinsu" yayi murmushi ganin yadda na rikice kuma nake juyawa in kalli bayana in kalleshi,nan ma yace babu, wayata na ciro na kunna dama mtn dina ne akai, tuni na kunna wifi dina a gigice na hau whatsapp ganin asiri na zai tonu yasa na shiga ladies tsaf tsaf babu kazanta daga masu shiga sai masu gyra makeup dinsu da masu gulma wasu turanci wasu larabci dama ladies ya gaji haka, na hau whatsapp dina sannan na ga iby, iby kuma abokina ne sosai anan natuna yana zama a dubai, a gigice na mishi magana, na ce masa gani a kasarsu amma inason komawa, tambayata yayi da wani layi nake amfani nace masa da wanda nake whatsapp kawai ganin wayansa nayi , na dauka ya tambayeni me ya faru, nan na masa bayanin komi dama asali yasan Aliyu don haka kawai da na masa bayani yace ina ina? na sanar masa da gani a airport , nan ya bani hakuri yace na nemi hotel na kwana yana da mutane a embassy zai roka ko za'asami mai zuwa gobe, nan ma nafara kuka don Alah yagani bazan iya kai gobe ba, haka nan dai nafito ina share hawayena rike da wayata a hannu sai jakata, aikuwa ganin yaa kamal nayi agabana, idonsa tayi jajur alamun yana cikin tashin hankali yace " daga ina kike?" cikin rikicewa dan zufa har ya ketomin nasan kalan ubana da zanci, nace " toilet naje" bai ce komi ba yayi gaba nayi bayansa ina waige kamar barauniya, nikam na shiga uku idan ban koma ba, ya zanyi da hamma Aliyu , mota muka shiga muka wuce sharjah cikin minti arbain muka isa gidan Ammi, buga kofan mukayi aka bude numfashina ne ya tsaya cak ganin wanda idona ke nunamin.
0 comments:
Post a Comment