Blogroll

BANNER 728X90

Wednesday, 17 January 2018

NI A.Y.S NAKE SO Page 31-35

NI AYS NAKE SO Page 31-35
.
WRITEN BY Princess Eshat Aysm
.
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
.
Su Hajara suna ganin Momi sukayo waje da gudu, suka zo suka ruk'unk'ume Aisha, dak'yar Abbah yajanyeta suka shiga, ?akin Ammi yakaita, Ammi tana ganinta farinciki ya kamata, kowa murna sunajin ranar kamar daren sallah, Abbah waje ya koma don yayi tsammanin da Faruq suka taho, hango Abdul yayi jingine ajikin motar ya har?e hannayensa a k'irji, shi kanshi bazai iya misalta halinda yake ciki ba, jinshi yake kamar yana yawo a sararin samaniya, dayake darene kuma Abdul ?in ya k'ara girma sosai, shiyasa Abbah bai ganeshi ba, hasken lantarkin dake haska wajen shi yada?a taimakawa wajen ?oye kamanninsa, hanu Abbah ya mik'a masa suka gaisa a mutunce, tambayarsa yayi tare suke ko, Abdul yace "Nine Doctorn Aisha, akwai bayani ne shiyasa muka taho tare".
Abbah ya fa?a?a fara'arsa yace "atohh tohh mushiga daga ciki".
Cikin takunsa yabi Abbah abaya.
?akin bak'i yakaishi sannan yasa aka ha?a masa kayan abinci, har Ammi saida tazo suka gaisa, tayi masa godiya sosai, murmushi kawai yabita dashi, mutanen sunyi masa.
Da wuri Momi ta koma gida tace da safe zata dawo, tunda 'yarta tadawo babu zama, godiya sosai Abbah yayi mata.
Ranar Aisha saida suka raba dare suna hira da Ammi, Hajarama a ?akin ta kwana, kusan k'arfe 2 nadare ta zabura ta tashi zata fita, Ammi ta ce "ke lafiyarki kuwa, ina zakije muna cikin magana".
?an sunkuyar dakai tayi kamar zatayi kuka tace "zan duba Dr ne".
Zaro ido Ammi tayi tace "kin kalli lokaci kuwa, me zaki masa idan kin dubashi".
Shiru tayi babu amsa, Ammi ta ce "dawo ki kwanta kiyi barci".
zun?ura baki tayi tace "Ammi to ki rakani, dubashi kawai zanyi ko yayi bacci".
Da mamaki Ammi tace "idan baiyi ba kumafa".
abu kamar wasa tasa wa Ammi rigima ita dole sai taje ta dubashi, jikinta yana bata idonshi 2, tun Ammi tana masifa harta fara lalla?ata amma k'arshe tafashe mata da kuka, Hajara data fara bacci tace "Ammi don Allah ki rakata taje, kinsanta da naci, yanzu saita hanamu bacci, ajiyan zuciya Ammi ta sauk'e ta ce "muje to".
zuciyar fal mamaki, daga nesa da ?akin Ammi ta tsaya ta ce "ki lek'a ta window kizo yanzunnan, "to".
kawai tace tayi gaba.
.
Kamar daga sama yaganta tana tahowa, lokacin yana tsaye jikin k'ofa don bazai iya bacci ba, burinsa gari ya yawe yatabbatar da ba mafarki yakeyi ba, da sauri ya fito shima suka ci karo a bakin k'ofar, ba k'aramin razana tayi ba, tayi baya da gudu zata koma ya fizgota, saura ka?an ta fa?a jikinsa, Murmushi yasakar mata ya ce "me kike nema"?
itama murmushin tayi ta ce "nazo duba ajiyata, nasan ya kasa bacci".
hancinta yaja ya ce "taya za'ayi yayi bacci bayan yashiga haske da duhu a tare, Esha, nan gidanku kuma mahaifinki ne ba mafarki nakeyi ba"?
kallon mamaki tayi masa ta ce "eh".
janyo ta yayi zai rungumeta tayi saurin ja da baya, numfashi yafara sauk'ewa har yakasa magana, juyawa tayi bayanta, ganin Ammi tana tsaye ta ce "kayi bacci don Allah, Ammi tana jirana".
batajira me zaice ba tayi gaba, da kallo yabita cike da tsananin so fiyeda ko yaushe, kamar yasace ta ya gudu haka yakeji, dayake darene duk abuda suka fa?a a kunnen Ammi, bin Aisha tayi da kallo har suka shiga ?aki, harta kwanta Ammi tace "tashi Aisha".
ba musu ta tashi ta zauna, Ammi ta ce "anya wannan doctorn ne kuwa, menene alak'arku dashi da bazaki iya bacci ba sai kin dubashi, ni nakaraya da wannan jinyar gaskiya, dama k'attin mazane ke gadinki...
rufe bakin Ammi tayi ta ce "tun tasowata bansaba ?oye miki komai ba Ammi, kada kizargi komai, wannan sunanshi Abdul, kuma shine AYS ?ina Ammi".
Ammi ta kama baki ta ce "a ina kika ha?u dashi, ke haukar taki tanananma ashe, sunan Ays har yanzu bai bar bakinki ba ohh ni Amina na banu".
Murmushi Aisha tayi ta ce "Ammi ni?inne ban warke ba, wlh Ammi dagaske nake miki, kuma banma nuna mishi na ganeshi ba".
Ganin Ammi tak'i yadda yasa ta kwashe labarin shi ta fa?a mata, harda rayuwarsu acan, sosai abun al'ajabin ya ta?a Ammi, ta ce "wannan wani ikon Allah ne babbah, shiyasa idan anga yaro ya mak'ale wa abu kamata yayi aduba abun, yanzu gashi auren naki baije ko ina ba, kuma wancan ?in da ake gudu hanunshi kika fa?a, da wannan nakeso ki gane komai a rubuce yake, Allah yayi Faruq ba mijinki bane, don ya fa?a mana iya zamanku tare bai ?aura miki iddah ba, kuma bincike ya nuna asiri akayi masa don a rabaku, wannan dalilin yasa ana ?aura auren sa da Sadiya, banaso ko na misk'ala zarratin ki nuna damuwarki akan haka tunda asalima ba sonshi kikeyi ba, Allah yayi muku albarka gaba ?aya yasa hakan yazamto alkairi a rayuwarku".
jiki a sanyaye Aisha ta ce "Ameen Ammi, amma waye yayi asirin to"?
ka?a kai ammi tayi tace "baruwanki da sanin wannan, shiyasa kullum nake nusar daku ku rik'e addua, babu abunda yakaishi a duniya, kana naka mutane suna shiga rayuwarka ta inda bakayi tsammani ba, yanzune ma zama bai kamaki ba, duk inda aka samu tsantsan so sai ansamu tsantsan k'iyayya daga gefe, Allah yada?a karemun ku aduk inda kuke".
Kwantar da kanta tayi ajikin Ammi tace Ammi, gani nake kamar baniba, wai harda hauka nayifa Ammi".
"ba hauka kikayi ba, kin?an samu matsala ne, kuma bagashi yazamomiki alkairiba, dama hakane ai, idan ancutar dakai sai kaga Allah ya musanya maka yazamo alkairi agareka matuk'ar ka rik'e addua".
basu runtsa ba har aka k'ira asuba sukayi Sallah suka shiga kitchen, farinciki takeji, rayuwar gidansu yafi mata na no'ina da?i, donma babu Sadiya.
.
Zuwa yanzu cikin Unaisa harya fara fitowa, kullum cikin hijabi take, tazan duk ranarda aka gane saidai wata ba ita ba, duk k'ok'arinta cikin yak'i zubewa, Malam kuwa ya?au son duniya ya ?aurawa cikin amma bai ta?a nuna mata haka, kullum lalla?ata yakeyi akan cikin yayi kusan zubewa, aduk lokacinda yaga daman hutawarsa da ita saiya mur?a kanbunsa da kanta take zuwa, wani lokacin har kwanaki takeyi agidanshi yana abu ?aya, sai ta dawo taci kukanta babu me rarrashinta, tayi danasani yafi a irga, ita yanzu Faruq ?inma bashi gabanta, wannan k'addararren cikin yafi komai k'ona mata rai, wannan shine biyu babu.
Allah yasa mudace
.
sukayi sai kunun gya?a wanda babu shinkafa aciki, Ammi sai farinciki takeyi ganin inda Aisha tak'ara kyau, wanke kwanikan da suka ?ata sukeyi, Hajara tace "Aunty yanzu keda wa kuka zauna acan, ko duk marasa lafiyar a ?aki ?aya kuke kamar na TH"?
kallon Ammi Aisha tayi kafin tace "kowa da nashi ?akin, idan macece sukan ha?ata mace wacce zata rik'a kula da ita, namiji kuma akan ha?ashi da ?an uwanshi namiji, asibitin badai tsaruwaba kam, da wata aka ha?ani sunanta Lidia, tanada kirki sosai, da zan taho saida tayi kuka".
Ajiyar zuciya Hajara ta sauk'e ta ce "jiya kamar mafarki nakeyi naji kinacewa wannan bak'on Ays ne".
Ammi ta ce "to sarkin gulma, zakiyi sauri ki gamane ko kuwa".
"haba Ammi, rabona da Aunty fa na manta, don nasan matsalarta shine gulma"?
Tashi Ammi tayi tace "zan gyara ?aki kuyi sauri ku kaiwa bak'on abinci".
Da murmushi suka rakata Hajara tana cewa "to" Ammi.
matsowa kusa da Aisha tayi ta ce "Aunty dagaske Ays ne, bayanin danaji kinayi wa Ammi ba mafarki bane".
Murmushi Aisha tayi, ta mur?a kunnenta ta ce "bazaki canzaba Hajara, dagaskene ba mafarki bane".
Tsalle Hajara tayi sannan ta fara taka rawa, sai juyi takeyi tana cewa "Allah mai iko ga Ays a gidanmu".
Abbah ta hango tayi saurin saita nutsuwarta, da mamaki a fuskarsa ya k'araso wajen, da sauri Aisha ta rungumeshi tana cemasa ina kwana Abbah, murmushi yayi me ?auke da farinciki yace "kin tashi lapiya Mamana".
gya?a mishi kai tayi, ya ce "kunje kun gaida bak'on"?
Hajara tayi caraf ta ce "yanzu zamuje".
.
Abbah ya ce "inafata dai lafiyarki law, naga kina rawa".
dariya dukansu sukayi, Jafar ne yazo da gudu ya rungume Aisha yana tambaya yaushe ta dawo, su Al'amin da Abdu ma sai murna sukeyi, cikin Farinciki suka gama komai suka juye a inda zasu juye, wanka suka shiga suna gamawa ta ?au riga da wandonta tasaka sannan tasa afterdrees asaman ta yafa ?ankwalin, trey ta ?auka ta jera komai akai tacewa Hajara biyoni da abincinnan mukai mishi.
kallo suka samu yanayi amma idonshi a lumshe da alamar baima san me akeyi a tv n ba, Sallamarsu ne yasa ya?an ?ago, zuba mata ido yayi kamar bai ta?a ganinta ba, yanda yakeji a zuciyarsa har gani yake gaba ?aya ta canza, Hajara sai mamakin irin kallon takeyi, har k'asa ta tsuguna ta gaisheshi sannan tajuya ta fita, ?an nesa dashi Aisha ta zauna ta ce masa "ina kwana bak'o"?
murmushi yayi ya ?an susa kanshi ya ce "nine bak'on, zanramane, meyasa baki zo tunda asuba naganki ba"?
waro ido tayi ta ce "kaima fa?a kakeyi".
murmusawa yayi ya ce "tun barinki nan na matsu gari ya waye, kumafa duk zumu?innan ganinki kawai nakeson yi, inaso zan tafi zaria da wurine, akwai muhimmin abunda zai kaini, da nasake kwana anan".
"uhm".
kawai tace tana murmushi, langa?ar dakai yayi yace "yunwa nakeji".
da hanzari ta mik'e ta zuzzuba mishi, jin k'amshin kunun saida yawunshi ya tsink'e, rabonshi da ganin kunu harya manta, ajiyewa tayi agabanshi ta ce "gashi".
?ata rai yayi ya ce "me zanyi wai, kice dai kinaso na tafi da yunwa kawai".
zuba mishi ido tati ta ce "bakacin irin wannan ne".
kamo hanunta yayi, zata k'wace ya damk'e da k'arfi, ya ce "abaki zaki bani, ance bak'onka annabinka".
harara ta watsa masa ta ce "kaifa kacika fitina, yaushe zan iya baka abinci kana kato dakai".
dariyane ya kufce masa yace "haka kika ce ko, to na k'oshi".
yafa?a tare da yin kalan tausayi, zun?ura baki tayi tana guna guni tafara bashi, ba kunya yayita ci, har wanda ta zuba ya k'are, ta ?auko Sami buns ?in tafara bashi, ka?an yaci sannan tafara bashi kunun gya?ar, saida yaji cikinshi yana neman fashewa yace mata ya k'oshi, ta ?ata rai tace "Allah sai ka shanye kunun".
haka tayi ta ?ura mishi, harda k'wallanshi ita kuma tana ta k'yalk'yale dariya, k'ak'arin amai taji yafara tayi saurin ajiyewa tafara bubbuga bayanshi, lumshe ido yayi yanajin masifeffen sonta inda yafara tasowa, ?an janyeta yayi gefe yace "zanyi wanka".
ta?e baki tayi tace "gacan bayi saika fa?amun".
da gudu tabar ?akin tana dariya, ganin irin kallon da yake mata, shikuma mamaki yakeyi wai yau shine tare da Esha a gidansu, tana fita ya runtse ido yanajin inda numfashin shi ya fara harbawa, ko yaya ya fara tunanin ta sai yaji bugun zuciya, dak'yar ya mik'e yayi wankan ya shirya ya?au wayarshi da ?an jakarsa ya fita, da Jafar sukaci karo ya ce "zo abokina".
da sauri Jafar yazo ya ce "wajen Abbah zanje yakaini makaranta, kuma yau Abba zai sayamin keke nayi na?aya a makaranta, malaminmu fa baya dukana yace inada k'okari, ranarma...
Abdu dage gefe yaja tsaki yace "fa?i ba'a tambayeka ba, harma ka iya k'arya, yaushe kayi na ?aya".
Murmushi Abdul yayi ya ce "Abokina baya k'arya, menene sunanshi".
yace JAFAR MUHAMMAD".
.
yajuya kan Abdu yace kaifa, yace "sunana ABDU".
shafa kanshi yayi yace ashe inada takwara, abokina kaini wajen Ammi mu gaisa, "Ammi tana falon Abbah saidai nakaika wajen".
murmushi yayi ya ce "muje ka kaini".
a mutunce suka gaisa da Ammi sannan suka gaisa da Abah, kallo ?aya Ammi tayi masa ta gamsu da kamalarsa, yayi mata 100%.
kanshi na sunkuye yacewa Abbah "ni zan wuce".
da fara'a Abbah yace kaci abinci kuwa".
murmushi yayi ya ce "naci Abbah".
.
godiya Abbah yayi masa sosai sannan ya ?auko ku?i masu tarin yawa ya bashi amma fir yak'i kar?a, haka suka barshi, yana fitowa yaja hanun Abdu da Jafar ya ce "Abbah baishirya ba muje nakaika makarantar, da murna jafar yabishi, saida suka ?au hanya yacewa Abdu ata ina kasuwa yake"?.
kwatance yayi ta masa har suka isa, keke yasaima jafar da wasu tarkace sannan ya jibgawa su Abdu siyayya kamar ba ku?i yake kashewa ba, makarata suka ajiye Jafar wanda yacika da murna da son Abdul aranshi, sannan yakai Abdul gida, suna gama fito da kayan ya mik'a masa wani letter yace kabaiwa Auntyn ka, daganan yaja motarsa yabara wuta da k'arfi ya?au hanyar zaria.
Shiru Abbah yayi yana kallon Ammi can yace Amina nifa gani nake kamar nasan yaronnan amma nakasa tuna a ina naganshi".
Ajiyar zuciya Ammi tayi ta ce "dama inaso na tambayeka, ranarda aka ?aura auren Aisha kamar kace yaronnan Ays yazo harya suma muku".
Kafin yabada amsa Abdu yashigo da gudu yana murna, Abbah yaci "ungo naka, menene haka kuma"?
Shiya mantama lettern hanunshi ya mik'awa Abbah ya ce "muje kagani Abbah, wannan bak'onne ya tafi damu kasuwa harda keke yasaiwa Jafar".
Baki bu?e Abbah ya ce "to muje nagani".
Momi tace "kayi shirin sai su shigo dashi kasan su damaida k'arami babbah".
Shikam fita yayi a ?akin, Abbah ya warware takaddan da Abdu ya bashi yafara karantawa.
_SAK'ONE GAREKI MASOYIYA TA, NARASA TAYAYA ZANYI NA FAHIMTAR DAKE, AMMA DAI INASO KI SANI, LOKACINDA NARASAKI A FARKO NASHA WAHALA, YA ZAMTO BANA GANE KOWA DA KOMAI, KINSHIGA RAINA KIN ZAMTO TAMKAR FITILA A RAYUWATA, BANASO NASAKE RASAKI AISHA, KECE KAD'AI MAGANI NA, NATAFI ZARIA ZAN TURO IYAYENA AYI MAGANAR AURENMU, BAZAN SAKE YADDA SONKI YA ZAMTO CUTA A ZUCIYATA BA, BAZAN SAKE KUKAN RASHINKI BA AISHA TA_
*Abdullahi AYS, Nasan bazaki ta?a manta sunanba, sai na dawo Eshat*
ware ido Abbah yayi da ya gama karantawa, cillawa Momi takaddar yayi ya ce "ikon Allah, me nake gani haka"?
Murmushi Ammi tayi ta ce "atoh, kaga na huta da bayani, sai kasan nayi".
murmushi Abbah yayi ya ce "ai yanzu kome yace zan masa, balle irin soyayyar dayakeyi wa 'yata nima naji inasonshi".
Dariya kawai Ammi takeyi tana jinjina lamari na Allah.
.
Lokacinda sak'on ya isa wajen Aisha tayi murna sosai ha?e da mamakin kodai ya gane itace.
Saboda tsaban gudun dayakeyi da wuri ya isa Zariya, lokacin aka shiga Sallar isha, tun daga tsayuwar motar tasa aka fara ihu AYS yazo, bai saurari kowa kamar yadda ya saba ba ya wuce wajen ummansa, da farinciki ta tare shi, ?an rungumota yayi ya mata pick a goshi ya wuce masallaci.
A can suka ha?u da Abbahn shi, sun juma suna gaisawa kafin suka taho gida, Raliya tafi kowa murnar ganinshi, Umma ta ha?a musu abinci Tuwon gero miyar ku?ewa tasha manshanu, irin abincin da yafi so kenan amma baya samu tun komawarsa Abuja.
"Abdul ka shammace mu tahowa babu sanarwa".
Baban yafa?a yana kai loma, Abdul ya susa kai yace "zuwana yanzu akwai dalili ne".
Kallon Umman nashi yayi kafin yace Umma albishir".
Kallonshi tayi ta ce "goro fari".
Yayi k'asa da murya yace "Na ha?u da Aisha...
Shiru yayi ganin duk sun tsareshi da ido, Umma ta ce "wai kai kanada lafiya kuwa, wace kuma bayan wa'inda sukayi Aure".
Kai ya?an sake sosawa yana murmushi ya ce "Auren ta ya k'are".
Kama baki Umma tayi ta ce "kana nufin bazawara zaka aura, kabar wannan maganar, na?au kasamo abun arzikine har kake wani ?a?atu".
Murmushi Baban nashi yayi ya ce
"mata dangin kuruciya, menene a auren bazawara, shekaru nawa muna fama dashi yanzu yazo da wannan maganar bazaki yimasa fatan alkairi ba".
Ajiyan zuciya ta sauk'e kafin tace "Allah yasanya alkairi".
Murmushi yayi ya ce "ameen".
Shi kam Abdul cin tuwonshi yakeyi don yasan mahaifinshi bashida matsala, itama Umman tanason shi bazata iya hanashi ba, farincikin dayake ciki ma bazai bari yagane abunda ake fa?a na aibu ba.
K'asa k'asa suka fara magana da Abbahn shi, ganin batajin me suke fa?a yasa ta mik'e ta tattara kwanukan tayi gaba abunta.
"a'a Baba don Allah kuje gobe kada na rasata".
"to naji, amma kasani matuk'ar aka samu matsala bazan kuma tura kowa ba, gaggawa ai aikin she?anne".
Murmushi yayi yace "idan kun nace bawani matsalar da za'a samu, wannan fa ba gaggawa bane, tsawon shekaru...
Fitowar Raliya ce tasa yayi shiru yana washe mata baki.
Zun?ura baki tayi ta ce "ko nemana bakayi ba".
Waro ido yayi ya ce "ba yanzu kika bar kusa dani ba".
Murmushi tayi ta ce "na?au ?oki yasa baka gane...
Binta yayi da gudu ta shige ?aki tana masa dariya, murmushi kawai Baban nashi yayi ganin walwalan ?anshi ya dawo.
Washegari tunda akayi Sallar Asuba ya tisa Baban da zancen tafiya, dole ba yanda ya iya yak'ira wansa da abokinsa yashaida musu zasuje neman aure wa Abdul a garin Bauchi, cikin k'ank'anin lokaci suka tafi cike da Farinciki, don dama kowa ya matsu yayi auren, da address ?in daya basu sukayi
Amfani, sun samu kyakkyawan tar?a, basu ?ata lokaciba suka shaida abunda ya kawosu, Abbah shima ya nuna musu yayi Farinciki da haka, cikin lokaci ka?an suka shirya komai, a take suka bada sadaki.
5 na yamma suka ?au hanyar komawa Zaria.
Tun tafiyarsu Abbah Ays yake cike da Farinciki, cikin hanzari yayi wanka ya tafi wajen abokin shi SAFWAN, Umma ta ce "lallai yau kadawo asalin Abdul ?inka harda ziyara, rabonka da zuwa wajen wani tun lokacin da kazama likitannan".
Shidai murmushi kawai yayi y tafi, a hankali yake tuk'i shi ka?ai yanata murmushi, duk motsinshi Aisha yake yagani, fargabar sa ?aya kada mahaifinta ya kwafsa, yayi murmushi a ranshi ya ce "wannan karan ko anhanani ita saina sace ta ne".
dai dai lokacin ya iso ma'aikatan su Safwan, kai tsaye office ?inshi ya wuce, yana tsaka da aiki yaji knckn, ganin Abdul ne mamaki ya kamashi, lokaci guda ya mik'e ya taro shi, "wa nake gani kamar bokan turai, ba'a ganinka kwata2 saika manta damu haka akeyi, ?azu su Nabil suke tambayarka ai".
nuna masa sit yayi kafin yaci gaba da surutun, Abdul yayi dariya ya ce "kaima ka kasa canzawa, magana kamar mace".
Safwan yayi dariya ya ce "kaima bazaka canza ba".
Su duka sukayi dariya, Safwan ya ce "kasan nayi aure ko, watanni hu?u kenan".
da mamaki Abdul ya ce "Aure kuma Safwan, shine ko labari babu, ko Raliya bata fa?a munba kuwa".
"to tayaya zakasani kaida baka zuwa, ko kazo baka neman mutane".
Abdul ya shafa suman kanshi ya ce "kasan aikin namu ba sauk'i, bamuda wani lokaci, yanzuma daliline ya kawoni, Aure nazo Abbah ya nemarmun".
Safwan ya ware ido cike da mamaki ya ce "Aure? ka hak'ura ka manta da aljanar taka da ta hanaka aurenne"?
Murmushi Abdul yayi ya ce "Ai bazan iya hak'ura ba, ita zan aura".
wani tsalle Safwan yayi kamar yaro ya ce "wai dagaske kakei, babu wanda baisan irin halinda kashiga lokacin da karasata ba, amma abokina garin yaya kuma zaka aure ta".
labari yabashi Safwan ya cika da mamakin ikon Allah, tsaban murnar daya tayashi haka ya jingine aiyu kanshi yaja Abdul suka
tafi wajen sauran abokanansu.
Sai dare su Abbah suka dawo, lokacin yana ?akin Ummah suna hira jefi2, duk hankalinshi yana kan lokaci.
Sallamar Abbah yaji ya tashi da sauri ya zauna, Ummah ta ce "ohh ni nata?a ganin irin wannan al'amarin kuwa, Allah ya kyauta".
Abbah da yake k'ok'arin shigowa yace "ameen".
Cikin susa kai Abdul ya?an zame yamasa sannu da dawowa, ko zama  baiyi ba yace "Abbah andace kuwa".
Harara Jmma ta watsa masa tace "ai kabar mun miji ya huta kafin ko".
Murmushi yayi ya ce "Umma yafa riga ya tsufa, ki?arshi yabani amsa saina baku waje".
Baki ta ta?e ta ce "neman aurenne yasa kamaida ni kakanka ko".
Abbah yace "je kayi baccinka angama komai, har sadakin mun basuk.
Ai bai san lokacinda ya rungume Abbah ba yana mishi godiya.
Kwanciya yayi amma babu alamar jin bacci a tare dashi, haushi ne ya kamashi da ya tuna Aisha bata da waya, wani dogon tsuka yayi yana zun?ura baki, k'iran Mansur ne ya shigo wayarsa, yana ?agawa yace "shege haka akeyi bazaka k'irani ba, yanzu kana ina, Bauchi ko Zaria"?
Ta?e baki yayi kafin yace "shine saika zageni don ka k'irani, to ka kashe saina k'ira".
Dariya Mansur yayi ya ce "kana kan tsininka kenan, me yake k'asa ne, kasanfa bana iya jure aiki sosai yakamata kadawo".
Dariya Abdul yayi ya ce "idan ka ganni to an?aura Aurena da Eshat, yau ?innan Abbah yakai Sadaki".
mamaki yakama Mansur "abdul bakada dama, har anzo wajen kenan, kace dai nafara shirin tahowa".
"gaskiya kafara shiri don yau zan ha?a komai akai kayan aure asa mana rana, zan rok'esu kada yafi kwana goma".
sunyi ta tsara inda zasu gudanar da bikin kafin sukayi Sallama yana cike da murna.
.
.
.
"Ammi wai gaskiyane iyayen Abdul sunzo gidannan"?
Aisha ta tambaya suna karyawa, Sallamar Sadiya ne ya katsesu, da gudu
Suka rungume juna, gaishe da Ammi ta farayi sannan tagaida Aisha, Hajara dake can gefe tana game da wayar Ammi ta gaisheta, Aisha sai binta da kallo takeyi, tayi wani masifar kyau kamar ancanzata, ita kanta Ammi ta yaba da irin murjewar da tayi, Aisha ta ce "Sadiya wai kinganki kuwa, kodai ba'a k'asarnan kuka zauna ba".
Sunkuyar dakai tayi tana dariya, ita kunyar Aishar takeji har cikin ranta, Aisha tayi dariya ta ce "ikon Allah, yau kuma kunyata kikeji kenan....
Faruq ne yashiga Falon Ammi da Sallamar sa, bayan sun gaisa Aisha tace "sannunku 'yan k'annena".
Har Ammi saida tayi dariya, Faruq kunya kamar ya nitse, murmusawa kawai yakeyi, Aisha taci gaba dacewa "kunga na huta da zuwa yi muku fa?a a matsayina na babba, tunda gaku a gabana, da farko kaga kai namijine, yakamata kazamto me hak'uri dakai zuciya nesa, sannan zato yana jawo mummunan zunubi, duk abunda zata maka kayi hanzarin fa?a mata koda fa?ane hakan zaisa ku fahimci juna sosai, ?aukar maganar mutane akan matarka duk ba naka bane, kazamto namiji dai dayasan fari da bak'i".
"ke kuma kece mace, a k'ark'ashinsa kike, shine shugabanki har gaban *ABADAN*_SAFIYYA HUGUMA_.
idan kikayi biyayya kika rik'e mahaifiyarsa tamkar taki zakiji da?in rayuwarki, ki zamto me kauda kai kedai naki biyayya kawai, yi nayi bari na bari, Aljannarki tana k'ark'ashin k'afarshi, ki kuyi hak'uri ba komai zaiyi miki ki ?ata raiba, Allah yayi muku albarka".
Dariyar Abbah ne yasasu juyawa dukansu, Ammi ma murmushi fal ranta, Faruq kam mamaki yasashi sake baki yana kallonta ko k'yaftawa bayayi, shikam har gobe baisan ranarda zata daina burgeshi ba, gashi yanaji yanagani tazama Auntynsa, wani huci ya furzar sannan yayi murmushi ya ce "mungode Aunty".
wani irin k'ara Sadiya ta saki jin cikinta yana mur?awa, da sauri Faruq yarik'ota du ya gama ru?ewa yana tambayarta lafiya, kafin tayi magana ta kece da amai ajikinsa, saida tagama ya rungumeta sosai yana shafa bayanta, shi yamanta da mutanen da suke kanta ma, kowa ya ru?e yana tinanin lafiya kuwa, Aisha ne ta ?ago ta a hankali tace mata sannu, sannan ta ?ago tafin hannunta ta ?an matsa sannan ta zuba ma hanun ido, can tace "Congratilation k'anina Faruq, matarka tana ?auke da juna biyu".
sai a sannan suka tuna abunda ta karanta, Abbah ya k'arasa shigowa, Hajara ta taso suka rufu suna murna.
.
.
Ranar wuni sukayi suna murnar ganin juna ga murnar cikin da Sadiya tasamu, sai yanzu Aisha ta tuna mafarkinda takeyi a baya, koda yaushe idan ta biyo faruq zatasa shi a rami Sadiya ce da wasu yara suke tareshi, wannan ya nuna shine uban 'ya'yanta, a hankali ta share hawayen da ya sauk'o mata batasan na menene ba.
Kallon Sadiya tayi ta ce "bani wayar hannunki na gani".
Da sauri ta mik'a mata, tashi tayi tsam ta nufi ?aki, jakarta ta ?auko ta fito da wani card, numbobin jiki ta jera kamar zata k'ira ta fasa, text ta tura.
_Ni takace har abada, farinciki na fatan ka isa gida lafiya._
Ko minti ?aya batayi da turawa ba ya k'ira, jin sallamar ta yayi har tsakiyan kanshi, wani lumshe ido yayi kafin yace "wayar waye kika samu"?
Shiru tayi na?an dak'ik'u sannan ta ce "yaya su Ummana"?
Ta?e baki yayi ya ce "Umma tana gaisheki, amma fa sai kinbani amsata".
murmushi tayi me?an sauti tace "wayar Sadiya ce".
Dariya yayi dagaji najin da?ine, "naji da?i, bannaso naji kince wayar wani ne".
Murmushi tayi tana jinjina kishi irin nashi, mezai kaita kar?ar wayar wani kuma oho.
"kinyi shiru Aisha, kuma baki tayani farinciki Sadakina yana kanki ba, kuma baki cemun komai akan lettern dana baki ranarda zan tafi ba".
ajiyar zauciya ta sauke ta ce "Ina taya mijina murnar fara jin k'amshin angonci, tuzuron da ya girma ba aure...
Wani lumshe ido yayi yakasa bu?ewa, "Aisha ina tausaya miki ranar da nakamaki, ?an yaro dani kice tuzuru".
Dariya ta k'yalk'yale dashi ta ce "wani tausayi kuma, ko kamanta ni naji komai".
runtse ido yayi ya ce "Aisha kidaina tunamun kinyi aure plx banason ji, baki da damuwa akan haka ko"?
Murmushi tayi ta ce "banida wani damuwa sai tsantsan shauk'i, damuwar me zanyi ina tare da abunda yake sakani  nisha?i, nasan zanyi alfahari da kai a gidan aure na".
cikin sanyin murya ya ce "Aisha, wani irin so kike mun, kinajin zuciyanki yana bugawa idan muna ta?i"?
sassanyar ajiyan zuciya tayi takasa magana, kiran sunanta yasakeyi da wani irin murya dayasa tsikan jikinta tashi, ta lumshe ido ta ce "yaushe zan ganka, kazo gobe".
murmushi yayi Yace "Angama Uwargida".
Zun?ura baki tayi kamar yana ganin ta ta ce "kana nufin zakamun amarya ne"?
dariya yayi ya ce "ehmana ko kina nufin zan zauna dake ke ka?aine"?
kuka tasakar masa datasa yagama ru?ewa, "wallahi wasa nake miki, ni ke ka?aice Uwargida kuma amaryata, har Abada zanrik'e ki, Dake ka?ai zanyi alfahari har k'arshen rayuwata".
tsagaita kukan tayi tana sauraronshi, sai lumshe ido takeyi.
saida ya tabbatar ta fara dariya sukayi sallama, ?agowa tayi taga Sadiya tsaye akanta fuskarta cike da mamaki.
"Aunty wai wa kika samune".
murmushi tayi ta ce Ays mana".
?an zaro ido tayi tace "wai dama lavarin da Ammi tabani gaskiyane".
kamo hanunta tayi ta zauna kusa da ita ta ce "gaskiya ne Sadiya, ina alfahari da haka".
da haka tayi ta shan cikin Sadiya ko zata gane tana cikin matsala amma babu alamar haka, da?i taji sosai.
wunin ranar haka sukayi suna tsokanarta, motsi ka?an sai suce *NI AYS NAKESO*
Saida Ammi ta ?ata rai suka daina.
Sai dare Faruq yazo ya?auki Sadiya, kamar kada ta tafi.
Washe gari kuwa da rana tana kwance a ?aki kamar me bacci taji hayaniya, lek'a window tayi tana tunanin wasu irin bak'i sukayi haka, waro ido tayi ganin ana shigo da akwatina, da sauri ta koma ta kwanta tana dariya, watau da gaske duk abunda Ays yafa?a mata ba k'arya bane, dariya tashiga yi tana murna, burinta ya kusa cika a rayuwa.
.
.
.
.
"malam katayani ganin cikin Unaisa dayake ta girma, anya laulayin da tayi bana ciki bane"?.
Shiru yayi zuciyarshi na tafarfasa, dama ya da?e yana ayyana hakan kuma abokanshi sun fa?a mishi, wani k'aton katako ya ?auko ya nufi kanta, wani ihu ta kurma tana Baba kayimun rai wallahi ba iskanci nayi nasamu ba, ko kallonta baiyu ba ya hau jibgarta, ihu take tana cewa "Mama ki ceceni".
?an share hawaye maman tayi tace "meyasa haka Unaisa, an ta?a samun ciki ba'ayi komaiba ne"?
Dak'yar take magana saboda ra?a?in duka, dak'yar uban ya saketa, a wahalce ta ce "don Allah Baba katausayamun, Kareema ce takaini wajen wani wai don na auri Faruq, shine yamun cikin".
Wani shak'a da uban yayi matane yasa tayi shiru, janta yayi har waje yace "idan kika kuskura kika shigomun gida ALLAH YA ISAH".
.
Wasa wasa nesa yanata matsowa kusa, ankawo kayan lefe daya zarce tunanin mutane, kowa yagani sai yayi san barka, ita kanta Aysha saida ta razana da kayan, an tsayar da ranar Aure Sati biyu.
farincikin da mutanen biyu suke ciki baya misaltuwa, tako wani fanni shirye shiryen biki akeyi, gaba ?aya garin Zaria ko ina kataka sai ansanar dakai maganar Auren *AYS* da *ESHAT.*
Ranar TALATA ta kasance saura kwana uku a ?aura Aure, wani yadine a jikin shi me ?an karen shek'i kalar maroon, fuskanshi yayi sayau saboda ?an ramar dayayi, agogo yake ?aurawa a hannunshi k'irar Fugh, Ummanshi tana zaune daga gefe, "Abdul kana nufin tun yau zaku tafi Auren"?
Murmushi yayi me cike da annuri ya ce "Umma ba mun gama maganaba, akwai abubuwan daza'ayi a can kuma kinga dole angawaye suna can".
Ya fa?a yana kanne ido, murmushi tayi ta ce "sai yaushe kuma kudawo".
Suman kanshi ya baza yana dariya ha?e da sunkuyawa, ta?e baki Umma tayi ta ce "uhh ni 'yasu".
Murmushi yayi ya ce "Nifa daga yau bazaki ganni ba sai tare da matata".
Salati tayi "zama zakaje kayi a gidan sarakan ko me"?
"a'a tare fa da abokaina zamu tafi, kinga sunata jirana Umma, kimun addua".
Addua tafara kwarara masa kamar ba gobe, cike da farinciki ya tafi wajenda abokansa suke jiranshi, duk wani abunda zasu buk'ata sun tafi dashi, sun kai su 8 kai kace ?aura auren zasuje.
sai dare suka isa garin Bauchi, kai tsaye Hotel suka kama ?akuna uku, saida suka gama komai suka ci abinci suka zauna huta gajiya.
Abdul daya gaji lik'is ya kwanta tare da lumshe ido, Aisha kawai yakeson gani ko hankalinshi zai kwanta, juyi yaketa yi FAISAL ya ce "mutumin wai duk gajiyane"?
Iska ya furzar ya ce "Aisha nakeson gani, amma banajin zan iya tuk'i nagaji".
Shiru Faisal yayi kafin ya ce "muje na kaika mana".
Zuba mishi ido yayi kamar bazai tashi ba, "muje to, ganinta kawai zanyi mudawo bacci nakeji sosai".
Shidai Faisal baice komaiba ya ?au key yafita, Safwan ne kawai ya iya cemusu a dawo lafiya duk da baisan ina zasu je ba.
A hankali yakejan motar, Abdul idonshi yana lumshe, ji yake kamar ma anyi auren daya ganshi a Bauchi.
Dayake bikin akeyi gidan cike da mutane, bakace dare yayi bama, hatta k'ofar gidan 'yanmata ne suketa shawagi, har?e hannayenshi yayi ya ce "Faisal bazan iya shiga cikin mutanennan ba, mu koma kawai".
Harararsa Faisal yayi ya ce "kafa rainamun hankali Abdul, infito a gajiye kace bazakaje ba, dole ciki zaka shigane"?
Tsaki yaja ya ci gaba da cewa "kajirani infito da ita".
shidai binshi yayi da kallo harya fita a motar, sannan ya sauk'e ajiyan zuciya, wata farar yarinya yagani bazata wuce 14 ba, da sauri ya isa gabanta ganin zata shiga gidan, Murmushi yayi mata ya ce "?an tsaya ki taimaka mun, Amarya nake ki k'iramun".
Da sauri ta kalleshi tace "Aunty Aishar"?
Gya?a mata kai yayi alamar Eh".
"to ince mata waye".
murmushi yayi ya ce "kice mata mijinta ke magana".
Zaro ido tayi ta ce "kaine Ays ?in".
Bai bata amsa ba ta runtuma da gudu tayi ciki tana cewa Aunty Ays yazo".
wata tsohuwa ce tace "kunfara shiririrantan naku ko".
rantsuwa ta shigayi tana cewa wlh shine.
Aisha tana ?aki ana shafa mata dilke saida gabanta ya fa?i.
Yana tsaye a jikin Motar Faisal yana masa dariya wai ashe har yara sun san Aisha da Ays, gu?a suka fara ji tun daga soron gidan, basuyi mamaki ba sai ganin tsofin da suka fito suna gu?a sun nufosu, yarinyar da Faisal ya tura tana gaba, da sauri Abdul ya bu?e mota zai shiga Faisal ya fizgoshi, "ina zakaje ka barni bacin kai akewa gu?a".
Muryar tsuhowar sukaji tana cewa "ina Ays ?in namu a cikinku".
Dariya Faisal yayi yanuna Abdul, aikuwa suka rufu akanshi suna fesa mishi turare, tsawon mintina kafin tsohuwar ta ce "tunda kaza?i tsohuwa kabarni ai saika zo ka ganta don bata futa".
shidai don sun ja shine kawai amma da gudu zaiyi, shikam Faisal dariya yayi tayi don yasan mutumin nashi baya son hargowa.
Tunda suka shiga dashi gidan ya runtume da ihu, ?akin Ammi suka Fara kaishi suka gaisa a mutunce, sai a sannan ya?an samu sa'ida kamar kada ya fita, jin tsohuwar ta sake jan hanunshi saida yaji kamar ya kurma ihu, suna barin ?akin Ammi tafito ta ce "kada wani ya sake cika mata kunne".
Sai a lokacin kowa ya nutsu, ita Ammi ta ?auka waje kaka tayi da Ays shiyasa bata sauraresu ba ta koma ciki, itakam kaka kai tsaye ?akin da akeyiwa Aisha Dilke ta turashi, "kuna gaisawa ka fito don dani za'ayi aurennan".
Murmushi kawai yayi ya ka?a kai ganin tabar wajen, a ranshi yace "ita kuma wacece oho".
mur?a k'ofar ?akin yayi a hankali kamar me tsoron ganin wani abu, ganin falon wayam yasa ya nufi ?akin, angama shafa mata kenan ana murza mata na fuskarta ya shiga, K'amshinsa kawai taji k'irjinta ya fara dukan uku uku, kaddai shigowa yayi... Bata ankare tunanin ba taji me diken tana cewa ka?an jira a wanke mata, wani ihu Aisha tafasa dayasa me dilken tayi waje da gudu, tasowa tayi idonta a rufe tana cewa "waye ya shigo Bagana"?.
Jin tayi karo da mutum yasa tasake fasa ihu, rungumota jikinsa yayi a hankali ya ce "ihun me kikeyi, kada kibari haukarki ta dawo sai an?aura mana aure fa".
Dukanshi ta shiga yi tana cewa "yafita".
binta kawai yakeyi da kallo, towel ne kawai a jikinta k'arami shima, tunani ya farayi "to menene ake shafa mata haka".
jin tanata dukanshi yasa ya rik'e hanun ya ce "Aisha, kidaina fa kada ya shiga miki ido, muje na wanke miki".
wani tsalle ta buga tana neman hanyar guduwa, dariya yayi ya ce "menene wannan ake shafa miki".
me dilken ne ta?an lek'o ta ce "ciwon ya lafa ne"?
Haushine ya kama Aisha ta ce "haba bagana, ni kizo ki wankemun".
Saketa Abdul yayi yana dariya acan k'asan zuciyarsa, neman waje yayi ya zauna yana binta da kallo kamar maye, Bagana ta kamata tace muje na wanke miki.
fuskar ta fara wanke mata, Aisha ta ?ago da sauri ta ce "don Allah meyasa kuka bar mutuminnan ya shigo".
Bagana tayi k'asa da murya ta ce "Allah yasoki kin ta?a Aure da kinsha fitina daga ganinshi".
waro ido Aisha tayi tace "wani irin fitina Bagana".
harararta tayi ta ce "kinfini sani tunda ke ba budurwa bace".
shiru Aisha tayi tana tunanin me take nufi.
yana zaune idonshi yana kan toilet ?in da suka shiga, santala santalan cinyoyin ta yake gani a idonshi, har wani lumshe ido yakeyi, bai ta?a jin fellings irin nayauba tunda yake a rayuwarshi, kasala ne yasauk'a mishi, shi sam ya manta da wani Faisal, yananan zaune Bagana ta fito daga bayin ta fita, kamar ya tashi ya shiga bayin haka yakeji, ko minti ?aya batayi ba tadawo tauke da dogon riga da hijabi, bayin ta shige takaiwa Aisha,
Rigar kawai ta zura tasaka hijabin, ta dubi Bagana ta ce "kunyar ganinshi nakeyi".
Bagana ta ta?e baki tace "kefa kinfiye iya shege, wani irin kunya kuma".
Kallo ta bita dashi kamin ta ce "a hakafa yaganni ko kaya babu".
Ta fa?a kamar zatayi kuka, Bagana tace "ke ko felek'en zaurawan baki iyaba kuma hardasu jin kunya, yau aka fara ganinki".
Shiru Aisha tayi kafin tayi narai narai da ido ta ce "nifa auren danayi ko k'afata bana tsammanin ya ta?a gani balle yaganni a haka".
Kama baki Bagana tayi ta ce "dagaske kikeyi".
"Allah dagaskene Bagana".
Jinjina kai tayi ta ce "gara da kika fa?amun, zan san abunda zanyi akai".
Kafin tayi magana tajata tace "yana jiranki".
saida suka fito yaga bala'in canzawar da tayi, fuskarta har wani k'yalk'yali yakeyi, a hankali ta nemi waje a gefenshi ta zauna ta juya fuska, Bagana ta wucesu tayi tafiyarta, murmushi yayi ganin yanda ta juya fuska, "Bakiyi murnar ganina ba kenan".
Ya fa?a yana lek'a fuskarta, ?oye fuskar tayi a hijabi ta ce "shine zaka shigo ka ganni".
"menene idan naganki, gobe saura 2 fa".
Dukda baya ganinta saida ta dara, ta kuma kasa magana.
A hankali ya ce "ganinki nazoyi amma kinata ?oye fuska, a gajiye nake".
Sai lokacin ta ?ago ta ce "yaya hanya".
Murmushi yayi ya ce "ni zan tafi, gobe kada ku ?ata mana lokaci, nasan kinga komai a jikin katin, ina fata ku?in da naturo zai isa".
Kai ta ?aga masa, yaja hancin ya ce "magana zakiyi".
"eh".
tace masa tana murmushi, zuba mata ido, kamar me ra?a ya ce "har yanzu gani nake kamar mafarki nakeyi Aisha".
Murmushi kawai tayi masa, "to kifa?amun menene aka shafa miki".
hancinshi ta ?an ja tace "kafiye gulma".
baisan lokacin da yayi dariya ba.
Da sauri ya mik'e ya ce "muje ku gaisa da Faisal, yana waje".
zun?uro baki tayi ta ce "ni katafi kawai".
kallon mitsitsin bakinta yayi, wani yawu ya ha?iye yace "wasu tsofi ?azu sun samun ciwon kai".
dariya tayi ta ce Kaka ce da 'kannanta da k'awayenta, kullum basuda ta?i saina lissafin ranar zuwanka, tunda Abbah ya basu labarinka suka samu suna me da?i".
wani murmushi yayi, "Abbah dakanshi"?
murmushin ta me tsumashi ta watsa masa dayasa kanshi ya fara kuncewa, rungumota yayi da sauri yana sauk'e numfashi, duk yadda taso ta k'wace haka ta kasa, saida yagama numfashinsa ya sake ta, pickn goshin ta yayi sannan yayi mata a kumatu.
ganin idonta a lumshe yasa yayi murmushi ya ce "na tafi, ki kula dakanki, inason k'amshinnan"
Murmushi tayi masa kafin ya fic
Tunda suka ?au hanya Faisal yake kallonshi, yana mamakin irin k'amshin da yake tashi a jikinshi me shegen k'amshi da da?i, ga wani ta?are ta?are da ya mammane ajikin sa, shidai kasa hak'ura yayi ya ce "Abdul menene ke k'amshi a jikinka ne, kaga yanda ka ?ata kayanka kuwa".
lumshe ido yayi yana murmushi, tunowa dayayi dilkan jikin Aisha ne ya?atashi, girgiza kai kawai Faisal yayi.
.
*MASU TAMBAYATA KO AYS MIJINANE, "AYS BA MIJINA BANE, BUT TSAWON SHEKARU 5 MUNA TARE, BAMU TAB'A HAD'UWA BA, A TAK'AICEMA SHINE MUTUM NA FARKO DANA FARA SO A RAYUWATA".*
_ba kuma baizo bane kawai ha?uwar ne ta gagara._
MASU NEMAN CONTACT NASHI DON ALLAH KUYI HAK'URI

0 comments:

Post a Comment