BUDURWAR KAUYE Page 1-5
.
Written by Faty mmn Faty
.
Bismillahirrahmanirrahim, ina godia ga Allah daya bani ikon fara rubuta wannan littafi, sannan wannan qagaggen labarine banyishi dan wata ko wani ba, Allahu yasa mudace, Ameen
.
"Alhaji Abubakar Muhammad da Alhaji Usman Sanusi, aminan junane qud da qud wanda hakan yasa suka zama tamkar yan uwa na jini "
" Alhaji Abubakar haifaffen garin Dambam ne ta jihar bauchi, wanda yakasance d'a na uku ga sarki Muhammad bin Abdurrahman wato sarkin dambam"
"Alhaji Usman Sanusi shikuma d'ane ga malam Sanusi mai almajirai wanda ya kasancewa malamin sarkine a fada kuma limamin babban masallacin garin dambam"
Tun tasowansu suke abota mai qarfi, tare suke Komai kusan ba wadda bai san da zaman abotarsu ba"
"kasancewar gidansu ba nisa atsakani, tare suke cin abinci hatta bacci basa raba makwanci sabida Alhaji Abubakar bai dauki kansa da wani abuba haka zasuje gidansu Alhaji Usman suci abinci hatta kwana sunayi tare acan"
"tare sukayi primary da secondary school dinsu, bayan sun qare ne daganan suka rabu amma rabuwa na wajen zama"
"Alhaji Usman shi baicigaba da karatu ba daganan ya fara kasuwanci, yana kuma noma, yayinda Alhaji Abubakar kuma yasamu fita waje qasar india karatu inda yasamu gurbin karatu a jami'ar new delhi yana karatun likitanci"
"Ranan da zasu rabu sai da sukayi kuka kamar wasu yara qanana, haka Alhaji Usman yayi ta zaman kadaici wadda daqyar ya saba da hakan"
"acan new delhi ma haka Alhaji Abubakar da qyar yasaba da kewan gida had'i da rashin aminnsa, ya fiskanci karatunsa sosai, lokacin da yayi shekara 1 anan ne yazo gida, yana arba da aminnsa sai kukan murna, ranan kwana sukayi suna hirar yaushe gamo "
" hutunsa na qarewa ya koma daganan bai sake zuwaba sai bayan Shekara guda da haka2 har ya kammala karatunsa, lokacin daya dawo gida yasanar da mahaifinsa cewar yazo ne amma zaikoma dan yasamu aiki acan sannan kuma yana da shaawar zama nawani lokaci acan, mahaifinsa baiqi ba amma yasanar masa sai dai ya tafi da iyali dan bazai je can ya auro wata qabila ba ya kuma amince da hakan "
" yana fitowa gida wajen aminnsa ya nufa sai dai abin farin ciki ya tarar amininsa yayi aure watanni hud'u da suka wuce "
" nan suka sha hira inda ya kawo masa alheri sosai kamar yadda yasaba dik lokacin daya zo , ya kuma sanar masa batun komawarsa hadda abinda mahaifinsa ya fad'a, ya taya shi murna kwarai "
" Alhaji Abubakar ya nisa yace kasan meye aminina? Aa sai kafad'a ya amsa masa, yace wlh nibansan ta ina zan fara neman matar bama kuma na tabbata mai martaba bazai lamunce mun tafiyar nan batare da dana cika umarninsaba, Alhaji Usman yace inaga abinda zaifi kawai kabasu zabi nasan bazasu maka zaben tumun dare dare ba, nan yayi naam da shawarar aminnsa"
"nan suka shiga cikin gida wajen matar aminnsa, suka gaisa ya kuma yaba da hankalin ta sosai inda yayi addu'a Allah ya bashi mata mai natsuwa kamar matar aminnsa "
" lokacinda Alhaji Abubakar yajewa mahaifinsa da zancen ya basu zabin matar dazai aura sunyi farin ciki nan take mai martaba yayi shawari da uwargidansa nan suka tsaida zance akan zaa hada shi da saudah yar kanin mai martaba "
Cikin qanqanin lokaci aka tsaida maganar aure, saura sati daya sutafi aka d'aura aure, cikin kwana uku aka gama shagalin biki, ana gobe zasu tafi suna sallama da amininsa sai Alhaji Usman yace shikenan yanzu inkatafi da iyalinka xumuncinmu ya qare kenan dan bawanda yasan sanda zaka sake zuwa kuma "
"yace haba dai ai zumuncin mu har 'ya'yanmu sai sunyi, nidai kamun alqawarin idan Allah yasa da namiji ka haifa to motarsa acikin yara nane idan kuma nine nafara haifan da namiji to matarsa tana acikin 'ya'yanka, na amince aminina Allah yasadamu da alkhairi, nan suka rungume juna da qyar suka rabu "
*INDIA*
" tinda Alhaji Abubakar yatafo da matarsa saudah new delhi, bai sake waiwayan gida ba, afannin aikinsa kuwa yasamu ci gaba sabida kwazonsa, har kwatance suke da shi a asibitinsu sabida kwarewar sa akan aikinsa"
"zamansa da saudah zamane na amana ahankali suka fara son junansu, cikin qanqanin lokaci Alhaji Abubakar ya kamu da son saudah fiye da tunani sabida saudah wayayyar mace ce, nan itama ta sami wata college ta ci gaba da karatunta "
" Bayan shekara 1,saudah ta haifi yarta mace kyakyakyawa kamarta daya da mamanta, suka mata suna da *MABARUKHA*, sai da mabarukha ta shekara tukun suka shirya zuwa gida nigeria "
*NIGERIA*
" afannin hajar matar Alhaji Usman kuwa, har yau Allah bai basu haihuwa amma hakan bai d'aga hankalinsu ba dan sunyi tawakalli da Allah shine mai badawa da hanawa "
" watarana Alhaji Usman yadawo kasuwa da yamma suna zaune shida hajar atsakan gida suna hira, kwatsam sukaji sallama, wazasu gani Alhaji Abubakar d matarsa harda yarsu "
" sunyi murna sosai da ganinsu, nan yake cewa tin jiya da dare muka iso, dasafe kuma nasan katafi kasuwa shiyasa nace mubari sai dayamma sai mushigo, nan sukasha hiransu, hajar tana riqe da mabarukha kamar subarmata ita dan yarinyar tashiga ranta "
" watansu 1 suka koma new delhi, tinda suka tafi basu sake zuwa ba sai bayan shekara uku nanma suka zo da yarsu mai watanni 9,takwarar mahaifiyar Alhaji Abubakar Maryam suna karanta niima, awannan zuwan ne da yayi ne ya biya masu hajji shida amininsa "
" inda suka tsananta addu'a aka'aba akan Allah ya cika masu burinsu, na alqawarin da suka d'aukanma junansu"
"Bayan sun dawo ne Alhaji Abubakar suka koma Bayan shekara 1 abin mamaki sai saudah tasamu ciki, dik da planning dasuke, haka suka reni cikin har yakai haihuwa, saudah ta haifi da namiji kyakykyawan gaske kamarsu 1 da babansa, suka saka masa suna *Muhammad Alameen* takwaran mai martaba, amma sabida babban suna gareshi yasa suka masa alkunya da *Papa* wato baba sunbi harshen india "
" papa nada watanni shida suka zo nigeria, kowa yayi farin cikin qaruwan da rana suka samu, awannan zuwan ne yasaima amininsa gida mai, sunje ganin gidanne Alhaji Abubakar yace ma amininsa, kaga lamarin ubangiji ko sabida haka kada ka fidda rai Allah y rubuta matar papa daga cikin yaranka ne shiyasa Allah bai baku haihuwa ba har yanzun "
" Alhaji Usman yace Allahu yashaa, inanan kullum ina addua Allah yabani haihuwa, Alhaji Abubakar yace insha Allah, Allah zai baka, bayan sati biyu suka koma india "
.
"Kwanaki sun wuce, watanni sun shud'e, shekaru sunja, Allahu maji roqon bawansa "
" Kwatsam ba zato, ba tsammani Allah ya azurta hajar da samun ciki, murna farin ciki ba kalan da basu yiba, hatta wani nasu ma ya taya su murna matiqa "
" cikin ikon Allah suka raini cikin lfy har tasauqa lfy, ta haifi yarinya mace, kyau kam kamar ita tayi kanta, dik wadda ya kalleta sai yace masha Allah, ranan suna taci sunan mahaifiyar Alhaji Usman wato Fateema suna kiranta da Fauziyyah, tindaganan kuma basu sake samin haihuwaba "
" haka suka ci gaba da rainon Fauziyyah cikin so da kulawa, Fauziyyah ta taso cikin gata sai dai son dasuke mata bai hana su tarbiyantar da ita ba "
" Fauziyyah tana da shekara 4 aka sakata a makarantar allo sai dai me, albasa batai halin ruwa ba, dan Fauziyyah bata dakko halin mahaifinta na haquri ba baran mahaifiyarta dako yatsa kasa mata abaki haka zaka cireshi "
" wasa, barna, tsokala dik ta had'a abin baa cewa Komai, idan taje makaranta wanda tafishi tadakeshi, wanda ya fita kuma ta tsokaleshi malam har gaji da kawo masa qarar ta da ake, gashi dududu shekarar ta 4"
"Fauziyyah nada shekara 6 aka sanya ta a makarantar primary, nan danan kowa yasanta a makarantar dan Fauziyyah akwai ilmi gata yarinya qarama , uwa uba kuma tsokalalta su suka saka kowa yasanta "
" tin abin bai damin mama harya fara daminta, wata rana Alhaji Usman ya dawo daga kasuwa da yamma suna zaune, sai yana hajar tayi shiru kamar mai tunanin wani abu"
"dubanta yayi cikin kulawa yace, mmn Fauziyyah yadai kikayi shiru haka? Nisawa tayi tace hmm wlh Alhaji alamarin Fauziyyah yanzu yafara bani tsoro, cikin sauri yace namefa? Fahimtar dani, tace wlh ba hali Fauziyyah ta fita baa kawomun qarar taba, kona hanata fita haka zata fakeni ta fice, tin ina ganin yarintane har abin yafara wuce tinanina "
" murmushi yayi yace haba hajar, dik ma shekarun mama na nawa suke, shekarnta shida da d'oriya nefa, kuma kowa da kalan yarintarsa, zata bari bari ta qara girma kiga dik zata bari, tace toh Allah yasa mudace amma Fauziyyah ga barnan ganganci datakemun ban isa na aje abina afili ba saita tab'a"
"dariya yayi yace to kinga yarintar kenan, tace hakane Allah yasa mudace, yace amin, kinsan ni yanzu ba abinda ke damina kamar rashin jin labarin aminina yau kimanin shekara 7 kenan rabonsa da gida abinda bai tab'a yiba kenan, tace gaskiya kam Allah yasa suna cikin halin lfy, yace dan lfy kam lfy suke sai dai kawai bai samu daman zuwaba neba, tace toh Allah yasadamu da alheri, ya amsa da amin "
*INDIA*
“Wata kyakykyawar mace nagano zaune awani qayataccen falo, idanunta sanye da siririn farin glass tana duba wata doguwar takarda"
"lokaci 1 tad'ago kanta sakamakon bud'e qofar dataji anyi, wani qayataccen murmushi tafara lokaci guda, kallon qofar nayi dan naga metakema wannan murmushi mai tsadan "
" wani matashin saurayi wadda akalla shekarunsa bazasu fice 16 ba, amma kyau kam iya kyau Allah ya bashi daganinsa zaka fahimci d'an kwalisane, kuma d'an gata lura da irin kayan jikinsa da wayoyin dake hannunsa "
" shima da murmushi afiskansa wanda yaqara qawatar da fiskartasa, ya nufo inda take, zagayowa yayi ta bayan kujerar datake zaune, rungumeta yayi ta baya ya d'aura kansa akan dokin wuyanta, da cool voice nasa yace hello momcy, kesi hoo? (yaya kike), tace am fine my son aur tum ? (kaifa), yace me too momcy, lekin (sai dai) am tied wlh, momcy tace oh papa aikin me kayi har kagaji, cikin shagwab'a yace haba momcy deko (duba) naje wajen salman, daganan mukaje shan ice cream fa dik kice bangajiba, shafo lallausan gashin kansa tayi, da sigan rarrashi tace eyyerh sowwie jawo kamre (kaje d'aki) kahuta ko"
"miqewa yayi ya wuce harya kai bakin qofa ya juyo yana cewa, kahahe daddy momcy? (ina daddy momcy), ya fita kasan gobe jirgin karfe 10am zamu wuce "
" oh momcy bazaa barnaganan zuwa nijer dinnan ba, yafad'a rai b'ace, tace haba papa ba mungama maganar nan ba just 1month nefa zamuyi mudawo sabida karatunka n pls ka haqura, wucewa yayi bai sake kulata ba sai ma qananun surutai dayake akan bai son zuwa nigeria "
" d'akinsa ya wuce, yana shiga ya fad'a kan tangamemen gadonsa rai b'ace, afili ya furta why daddy why kskeson zuwa nijer, always baka da magana sai na nijer wani dogon tsaki yaja ya furzar da wani iska mai zafi daga vakinsa, miqewa yayi kamar an tsunkuleshi ya nufi bathroom, shower ya sakarma kansa sosai, ya kai 30mins kafin y fito "
" wasu shirt da 3quater nashan iska yasaka, sannan ya bud'e wata drower, wasu drugs naga ya d'ebo ya watsa abakinsa ya bisu da ruwa sannan yabi lfyr gado, nan da nan bacci yai gaba dashi "
" papa kenan dan gatan daddy da momcy, yataso cikin so da qauna d kuma kula ta mahaifa, papa tin yana qarami haka yataso da ra'ayi idan baiso abuba aka sakashi to tabbas abin ba zaiyi kyauta"
"tin tasowarsa haka yake komai nasa unique ne, dan baison qazanta, baison hayaniya haka baison rayuwar area shiyasa ya tsani zuwa nigeria, acewarsa mutanen can sunfaye hayaniya "
" yanzun yagama secendary school nasa, zai tafi universty amma idan kaga irin shagalinsa dayake sha wane wani wanda ya kammala jami'a"
"tin yanayi ab'oye har ya zamana baya b'oyewa, tsiyarsa yake tsulawa, shaye2 kuwa baacewa Komai, su momcy kullum adduarsu Allah ya shiryeshi"
"amma dik abinda yake baya wasa da sallah, haka karatunsa kullum d gread mai kyau ya fitowa, shidai matsalar 1 baison zuwa nigeria dik sanda zaa zo sai yaji damuwa tamasa yawa papa kenan dan daddy da momcy"
"Washegari suka tafo amma basu iso ba sai wata Washegari, nan gida gida ya rud'e da murnan zuwansu, da daddare ana cike afalon mai martaba anata hira amma banda papa, mai martaba yana lura dashi, azuciyarsa yace tabbas wannan dik acikin jikokina da takwarorina babu wanda ya gadoni ya kuma cika jinin sarauta kamar Aminu, da hannu ya nuna masa alamun yazo kusa dashi, ba musu ya je wajensa kuma papa ya sake dashi har suna hira yana ta murmushi "
" Washegari da yamma daddy, momcy, didi (adda) mabarukha, didi niima da papa, suka tafi gidan Alhaji Usman, suna isowa qofar gidan kowa ya fito amma banda papa"
"daddy yace muje mana kazauna anan, b'ata rai yayi sannan yace main hoon nah daddy(ni ina nan daddy) daddy yace oh Alamin don't say that mana umm, ohyah lets go "
Haka dai ransa baiso ba yafito, dik sun shige shine na bayan shiga aiko yasa qafarsa zai shiga yaji anbige ta baya anwuce shi da gudu"
"bayanta kawai yagani kamar walqiya ta wuce ciki bai idah tinanin mai ya koro ta gudu haka har tana bigeshiba yaga wata yarinya tana cewa wlh zaki fito sai naci ubanki badai inkika daka kika gudu ba, toh bazanma kai qararkiba baran abani haquri, shegiya kawai tana kaiwa nan ta juya ta wuce"
"papa dai ya gama quluwa jiyake tamkar ya juya, haka yaqarasa ciki, nan ya tarar da su daddy sai murnan labarin dasuka samu na fauziyyah suke, Alhaji Usman yace baku ko zaunaba wannan shashashar tashigo da hauka, daddy yace ai nikam bazan iya zamaba "
" ikon Allah, sai haka yake maimatawa, momcy ce ta jawo fauziyyah jikinta tace zonan 'yata, nan suka zauna aka shiga hirar bayan rabuwa, mama ce tace da fauziyyah baki iya gaisuwa bane kina rakubewa dan kinyi saa ban dakekiba"
"daddy ne yace haba dai amata ahankali mana, zonan matar Alamin, daram gaban papa ya fad' I, dasauri y d'ago kansa yana kallon daddy sai yaji Abba yana cewa aiko zaisha fama dawannan rigimar "
" ransa ya gama baci, nawa yake da zaa masa zance aure, aurenma da wata qaramar yarinya, qazama, yar qauye, burinsa bai fice su tafiba kozai samu amsar tambayansa awajen daddy "
" basu suka tafi ba sai kusan sallan magriba, aiko suna shiga mota yace daddy wai wane Alamin ne mijin wannan jaririyar? "
" daddy yayi dariyansu na manya yace momyn yara kinji danki da wani zance, tace inajinsa daddy papa sai kai daddy nikam rigima zai tsayar mun"
"daddy yace dana fiso muyi maganar anatse, amma tunda katambaya nan ya bashi labarin alqawarin dake tsakaninsa da amininsa"
"papa yace ammadai baniba dan auri wannan qaramar yarinyar, yar qauye villager haba god fobid, daddy yace aifa kaima karatu zaka fara, kafin kagama Itakuma ai tazama budurwa "
" papa yace never mai zanyi da *BUDURWAR* *QAUYE*, kuma ma nifa mata basa gabana kawai ka warware wannan alqawarin cos I can't marry that villager girl that's all"
.
"Daddy yace kawai abar maganan nan sai lokacinta yayi, n all I want u to know, I can't break that promise, yeh hai vadha (this is a promise) "
" papa yace kyiu Daddy kyiu? (meyasa, meyasa)
Daddy yace mubar maganan nan ko, ya isah haka, ya fadi hakane dan yasan yanzu sai yatayar masu da rikici "
" niima ce tace bross kadafa ta girma kazo kana rigima, afusace ya juyo, momcy Allah kimata magana "
" su mabarukha sai dariya suke masa, momcy tace mabarukha bass(ya isa), rabu dasu kaji, har suka zo gida baisake maganaba, kallo 1 zaka fahimci ransa ab'ace ne"
"tin daga ranan bawanda yasake tada maganar fauziyyah, amma aqasan zuciyarsa wani tsana yakeji gameda da ita baran idan ya tuna yadda ta bugeshi ta wuce da gudu, afili ya furta pagal(mahaukaciya) "
" watansu 1 suka koma akan sai After six months dasu dawo bikin mabarukha dan sun dai dai ta da dan yayan daddy, harma an masu baiko "
" bayan sun koma da 1month papa ya fara zuwa skull, inda yake karantan medicine, acan sake samun wasu friends, inda iskancinsa yafi nada "
*6 months later*
Suka shirya tahowa bakin mabarukha, wannan zuwan papa yana doki sabida bikin sis nasa"
"satinsu biyu da zuwa akayi biki nagani nafada, aka kai amarya gidan mijinta acan abuja inda yake aiki "
" daganan suka koma, bayan shekara biyu Daddy ya yanke shawarin dawowa nigeria da zama, haka suka shirya suka taho inda sukabar papa acan sabida karatunsa"
"kowa yayi farin cikin dawowansu, inda yace amma agarin bauchi zai zauna, bata lokaci ya sai fili a unguwar gida dubu ya hau gini hadda ginin asibitinsa"
"watanninsu shida a dambam suka koma bauchi, inda yanzu zumuncinsa da amininsa yaqara qarfi dan yana yawan zuwa dambam shima kuma yana ziyartarsa "
" afannin papa kuwa, tinda su daddy suka bar india baizo nijer ba, dan baya cikin kad'aici, ya had'u da wani friend nasa d'an bauchi shima karatu yakaishi can, tare suke sheqe ayarsu, tun papa bai iya shan giyaba yanzun yazama expert, shiyasa yake manta zuwa gida ma, watarana suna waya da daddy yake cema daddy shifa idan yaqare karatunsa bazai dawo ba, daddy yace bai aminceba ganin ran daddy ya baci sosai yasa ya haqura "
*After 4years*
"kyawawan motoci qiran zamani suka tsaya a qofar wani tangamemen gate inda mai gadi ya bud'e masu suka shige ciki"
"motar dake gaba daddy da momcy ne suka fito fiskansu dauke da murmushi, dayar motan kuma wani kyakykyawan saurayi na gano tabaya, dogone sosai qirjinsa yana da fadi, ina zagayowa naga papa ne dan nayi zaton hakan"
"papa ne yagama zama cikakken saurayi, daga yanayinsa kawai zaka fahimci hutu atare dashi, kyansa yadad'a fitowa, Daddy suka qaraso ya rugumeta Daddy yana cewa I missed u Daddy, Daddy yace muma munyi missing naka sosai son"
"sake Daddy yayi ya rungume momcy, momcy nayi qewarki dayawa, nima haka papa amma yanzun ai kadawo Komai ya wuce, yes momcy barin sake nisa dakuba "
" har side nasa suka rakashi, Daddy yace son kayi, momcy tace kana tayyar ho (ga abinci yayi gamu) ko bazakaci girkin momcy ba? Waw momcy thanks nafayi missing girkin kifa "
" ok saika fito suka fice, halliru mai wanki ne ya shigo, yana jaye da jakan kayansa, dasauri yace hey what ar u doing here yana nuna sa da hannu, shiru yayi alamun bai fahimce shiba, tsaki yaja cikin tsawa yace mekake mun adaki "
" adiririce yace hajiya ce tace na kawo maka kayanka, sai kawuce falo kashigo mun har daki so kada kasake, next time dik abinda kazo dashi katsaya daga qofar falo kayi knorcking samje (kagane)
Ayi Haquri yallabai bazaa sakeba, kana iya tafiya yace dashi, qarema dakin kallo yake, dan yanayin dakin yamasa"
"wanka yayi ya shirya tsaf, afalo yasami su Daddy suka wuce dinning, bayan sun gama cin abuncin suna hira papa yace momcy awani unguwa didi niima takene, tana federal lowcost tacema gobe data zo, ok bamatsala barina dan huta "
Da yamma lis ya fito shikin wasu black troser da red shirt mai dogon hannu, hannunsa riqe da wayoyi, momcy tace ina zuwa haka, momcy inason fita akwai abinda dan sayo, to kaida bakasan gariba sai dai driver ya kaika"
"Bayan magriba yana zaune adakinsa layin TJ ya kira yana dayawa yace ya akayine man, dariya yayi taya kasan nine, TJ yace inafa tajiran call naka so ina ganin baqon layi nasan kaine, ok to ya kasamu mutan gida, lfy lau sai dai ina missing abarfa
Papa yace ina ai sai da nafita na nemo ta, TJ yace shege mutumina ainan dad yakasa ya tsare haka na haqura, amma gobe zan shigo, ok sai naganka"
Ranan haka papa yayi tatil abinsa, nan yahau bacci kamar ba gobe, momcy tashigo yanayin data gashi ya bata tsoro dan gefensa kwalabaine na syrup da giya ga wasu drugs agefe, Daddy ta kira yazo ya gani takaici yahanashi magana kawai ya juya ya fita "
" dasafe momcy ta tuhumeshi akan abinda tagani, yace haba momcy mene aciki kawai fa ina dan wartsake gajiya, ganin yaqi sauraran ta yasa tace Allah ya shiryeka "
" satin papa 1 da dawowa Daddy yace ya shirya suje dambam weekend, ana gobe dasu tafine suna zaune a afalon Daddy, Daddy yace Alamin mene zaka kaiwa fauziyyah tsaraba? "
" fauziyyah ya maimaita sunan kafin yace, konhe fauziyyah (waye fauziyyah) dan shi harga Allah yama manta da labarinta "
Daddy yace tumare dulhan (amaryarka), dulhan, dulhan ya maimaita sunan, momcy tace yar gidan uncle Usman mana papa kake kamar kamanta ta"
"nan take ya tuno aiko ya bone fiska, yace pls Daddy kabar maganan nan nibani da abinda dan bata, yana fadin haka yayi hanyar waje, Daddy yana kiransa ko ya juyo ya fice abinsa"
"Daddy yace hajiya kihada mata kayan kwalliya, kuma dole yakai rabudashi, momcy tace ai papa rigimace dashi, badamuwa zaa hada"
"ranan da sukaje dambam Daddy yabawa papa kayan kwalliya da momcy ta hada yace yaje yagaida mama ya kuma bawa fauziyyah, inba hakaba ransa dai baci, haka ya karba bada san ransa ba ya tafi "
" atsakar gida yasami mama tana tsefe ma fauziyyah kanta sai kuka take wai zafi, da faraa mama ta karbeshi suka gaisa, mama tace bazaki gaida yayankibane "
" fiska shabe2 da kuka ta dago, aiko kallo daya ya mata ya kau da kansa, ina yini tafada tana goge hawayen fiskanta, lfy kawai yace, miqewa yayi yace mama zan tafi ana jirana awaje, ajiye ledn hannunsa yayi yace agaida abba gobe zanzo bagaidashi"
"mama tace angode Allah yasa ka, madalla agaidasu hajiyn, y amsa da dayaji"
"yana tafe a mota yana saqa da warwara, dan gaskiya zanje nasami Daddy ya ma warwara wannan alqawarin, haba wata qazamar yarinyan, toh shi inma aure zaiyi yayi me da ita, wlh bazai yiyuba sam dasake "
.
“Yana isowa gida falon Daddy ya nufa amma ganinsa da baqi yasa ya juya, room nasa ya wuce rai b'ace, zuciyarsa kamar tafashe haka yakeji
Syrup ya d'akko ya balle murfin yakai bakinsa, sai daya shanye tass sannan ya ajiye, ahankali yafara jin b'acin ran yana raguwa dan tafara tafiya dashi duniyar sama "
" yana nan kwance shiba bacci ba haka ba idonsa biyu ba, har akayi sallan magriba bai tashiba
Daddy ne ya shigo, Matsowa daf dashi yayi yaja yatsun qafarsa ya kira sunansa Alamin, jin bai amsaba yasa ya tunanin ko bacci yake
Alamin yasake kiransa, sai anan ya motsa tare da fad'in uhumm
Daddy yace au kana jina dama ka yi shiru har akayi sallah baka fitoba
Naji ai zanyi, to is better katashi kasan lokacin magriba dawure yake qurewa, da kyar ya miqe zaune dan dik jikinsa ciwo yake masa
Daddy ya juya zaifita ya ga kwarbar Syrup a jife, hannu yasa ya d'ago, rai b'ace ya dubi papa, yace yeh sab kyahe? (mene ne wannan) yana nuna masa Kwalban
Shiru yayi baice komaiba saima b'ata fiska da yayi
Daddy yace yanzun Alamin abinda kake kana kyautama kanka kenan, ka dubi irin abinda kake sha kamar baka san illansaba
Haba Daddy dawanne danji ne da irin kashemun rayuwa da kuke qoqarinyi ko kuma da wadannann sarautan naka
Wanne irin kashe maka rayuwa kuma?
Ah waccar qazamiyan yarinyan da na kusa haifata ma dakuke wani cewa wai ita zan aura, to wlh ni dana auri wannan yarinyan gara na mutu ba aure dan ni mata basa gabana
Daddy yace kashe rayuwa ya fice wanda kake ma kanka, ka sha wannan kasha wancan kamar ba Dr ba, ko so kake kace bakasan illansaba, toh wlh kashiga hankalinsa da wannan shaye2n naka, inba haka ba ranka zai mummunan baci kodan kaga na zura maka idanu ina kallonka shiyasa kullum kake qoqarin zubarmun da mutunci
Daddy nifa banfa nemi dogon maganaba kawai kasan abinyi, inkuma ka matsa wlh sai kunji dama baku somaba dan bata yanda zan fara rayuwa da wannan jsririyar
To idan naqifa sai yaya ko zagina zakayi tinda ka girma
No, nifa gaskiyace kawai fa I can't marry that villager atow
Toh tinda ka girma har ka iya sa insa dani zangani nida kai waya haifi wani, ka kuma bud'e kunnenka da kyau kaji wlh kaji na rantse aure babu fashi, saanka 1 fauziyyah har yanzu yarinyace da acikin satinnan zaa daura auren inyaso idan aka kawo ta ka ratayeta, kuma ko Bayan raina banyafe makaba matuqar baka auri fauziyyah ba shashasha yana fad'in haka ya juya ya fita ransa a b'ace
Daddy yana fita papa ya kira momcy awaya, aiko tana dagawa ya fashe da kuka
Momcy hankali tashe tace papa lfy mene yafaru? Da kyar yayi shiru yafada mata yadda sukayi da Daddy
Rarrashinsa tayi tace kayi Haquri zuwa kudawo ba gobe daku dawoba, yace eh
Toh kaje kabawa Daddy Haquri inyaso idan kundawo dansan abinyi tunda baka so aiba dole
Yawwa momcy pls help me out, kada kadamu son ammafa kaje kabasa Haquri
Gaskiya nifa momcy bawani Haquri dazan basa kawai rabu dashi, ganin zai tsiyar mata rikici yasa tace shikenan sai kundawo din
Washegarin dawowarsu momcy tasamu Daddy akan maganar fauziyyah, nan yamata ba Daddy yace kuma kada tasake sa bakinta aciki tinda goyon bayan danta take
******
Watanni papa uku da dawowa Daddy yace toh papa ya shirya next week zai fara fita office
Ransa dai bai soba haka ya amince
Watan papa biyu da fara fita aiki amma har ansanshi acikin asibitin dan kwarewansa akan aikisa dik wata lalura indai yashafi harkan qashi, da ikon Allah bata gagararsa
Hakan yasa kowa Dr Alamin, sai dai miskilanci yasa bai kula kowa, cleaners kuwa basa barin ya kamasu da laifi dan yanzun yaci mutuncin mutum baqaramin aikinsa bane
Ahakanma yanzun sai ya gadama yake fita aikin, acewarsa baison stress, Daddy dai ya zuba masa idanu tsakaninsu sai adduar shiriya
.
Haka rayuwa take tafiya, inda kullum alamarin papa qarauwa yake, tun su momcy suna damuwa har sun dawo yimasa addu'a kawai
Afannin aikinsa da kyar Daddy ya shawo kansa ya amince yana fita kullum, gashi teaching hospital ma sun nemeshi yazo ya masu aiki
Yacema Daddy shifa barai iyaba, aiki dai masa yawa, Daddy yace masa ai hakan ba laifi bane inkuma bazaiyiba shiya sani
Ganin ran Daddy ya baci yasa ya amince
Kafin wani lokaci, kamar wasa sunan Dr Alamin yabazu
Sannan hanyar shigan kudi ya qaru masa, sai iskancinsa ya fi nada
Wani gida flat mai kyau sosai yasaya a sokoto road, wanda ko su Daddy basu san yasayaba
inya taso daga wajen aiki can yake wucewa ya sha shagalinsa
Amma dik abinda zaiyi da mace sai dai ya romancing d'inta ya barta dan baqaramun kyankyami yake da ba
Sau da dama TJ kan ce masa anya kuwa Ameen kana da lfy
Yace me kagani, haba abokina dik irin lokacin da kake b'atawa da mace amma baka iya....
Dariya kawai yayi yace umm kawai banson qazanta da jaqwali shiyasa tinda mutum baisan suwane suka.......
TJ ya jinjina ma abokinsa yace tab wlh nikam sai naci kudina tsaf dana bari
Papa yace kadafa watarana kaci wahala
TJ yace ina nimahaukacine da zanyi ba condom
Papa yace kabi dai ahankali
Yanzu gidama bai komawa sai 12 wani tym har 1pm, idan yadawo da wuri kuma to irin 11pm ne
Yanzun hankalinsa akwance yake ganin lokaci yana tafiya bai kuma jin Daddy ya sake maganar waccar *BUDURWAR QAUYE* ba
Inda shikuma har yau baiga macen data burgesa amatsayin matar aureba
************
*Bayan wasu Shekaru*
Yan makarantar secondary ne sun taso amakaranta misalin 12:30pm
Wata kyakykyawar yarinya, yar matashiyar budurwa wadda shekarunta bazasu fice 15 ba
Tana da dogon fiska mai dauke da dara2n idanuwa, dogon hanci had'i da d'an mitsi2n bakinta, Allah ya mata yalwar gashin gira
Fara ce tass wadda idan kaganta zaka fahimci ba algus acikin farin ta
Fauziyyah Usman, daga bayanta wata ta kwala mata kira
Juyawa tayi ba tare da ta amsa ba, ganin mai kiranta yasa ta gyara tsayuwarta dan jiran isowarta
Tana isowa tace, ashe kinfito inatakan dubaki bangankiba sai Aisha salman tacemun kintafi
Fauziyyah tace wlh saurinake yau suna zamuje da mama
Kai Fauziyyah ba kya girma bikin suna kuma
Tsaki tayi gami d juya manyan idanuwanta amasifance tace eh d'in, ni kina b'atamun lokaci mene yasa kika tsaidani
Sanin halin Fauziyyah na fad'a yasa tace haba qawata ba nufina kiyi fushiba amma Allah ya baki haquri, dama note d'in Basic science nakeso ki aramun
Tabd'ijam, kinajifa abinda uncle bala ya fad'a d'azu, kada kowa yayi wasa da note d'insa saura mana term 1 daga wannan mu fara JSSCE
Kuma dik sai antambayemu abinda aka mana tin daga first term
Marairaice murya tayi haba qawata gobefa zan dawo maki dashi
Toh indai kinyi alqawari shikenan, barin nabaki
Yawwa nagode
Bud'e jakarta tayi ta lalimo mata, gashi ta miqa mata saura kuma kibari qannenki su shafamin miya
Uwar masifa ta fad'a aranta, amma afili sai tace haba dai yadda kika bani haka zandawo maki da kayanki
Sallama sukayi kowa ya wuce, tanashan kwana taji horn d'in mota abayanta
Juyawa tayi ganin wadda ke cikin motar yasa ta murmushi da yaqawata fiskanta
Parking yayi ya fito, dogon saurayi choculate colour, kyakykyawa dashi
Da murmushi ya qaraso wajenta, shine kika tafi abinki ko beauty na, abinda ya fad'a kenan
Sunkuyar da kanta qasa tayi, kayi haquri uncle yasir sauri nake kada mama ta tafi ta barni
Yar mama kenan kinfa girma yanzun kam, kibar mama take zuwa unguwa ita kad'anta
Shagwab'e fiska tayi, bikin sunafa damuje a can gongola
Toh shikenan kada na tsaidaki amma amshi wannan nagaji da rashin jin muryarki ko yaushe
Duban tsaleliyar wayar daya miqo mata tayi, shiru tayi bata amsa ba
Amshi mana beauty yace da ita
Gaskiya ina tsoron mama tamun fad'a
Haba my fauzee pls ki amsa kinji inyaso kada kibari mama ta gani
Amsa tayi tace nagode
Aa nine da godia
Ahuta gajiya ko baby na saina kiraki
Toh amsa sannan ta wuce
Juyawa yayi ya koma mota, wanda yasan koda yamata tayin zai maida ta gida bayadda datayiba
*Wanene Yasir?*
Yasir Mukhtar shine ainahin sunansa, asalinsa haifaffen garin Gombe ne, shine d'an fari a gidansu, iyayensa suna zaune a unguwar Buba Shango, kuma balaifi suna da hali
Bautar qasa ya kaishi dambam, inda aka turashi makarantar su Fauziyyah, shine malaminsu na Mathematics
Tin lokacin da yaga Fauziyyah yaji yana tsananin sonta, kuma da aure yake sonta
Da kyar ya shawo kan Fauziyyah har takarbi tayin soyauyarsa, inda yanzu suke tsananin son junansu
Kuma Fauziyyah ta amince masa da zarar sungama JSSCE shima dai dai da gama service d'insa zai turo magabatansa maganar aure
Inyaso taci gaba agidansa, dan jiyake bazai iya haqura har ta qare secondary ba, wannan kenan
.
Tana shigowa gida, sallama tayi tana mai cire hijabin wuyanta
Daga cikin d'aki mama ta amsa mata
Wurgar da hijab da d'ankwalinta tayi atsakar d'aki, jakarma firo tayi da ita sannan tayi super kan gado tana cewa wash Allah na
Mama ta miqe tana tsintar kayan data watsar tana fad'a
Aifa kindawo kenan, Komai haka zaki watsar mun kamar haka kikaga nakeyi
Haba mama zafifa na d'ebo wlh nagaji
Bawani nan dama haka kike kullum, aiko a ruwan sama kika dawo haka zaki hejjefar da kayanki
To mama nabari shikenan
Aikam daya fi maki, inkuma haka zaki keyi ad'akin mijinki to kinada aiki ja
Wuwwurga qafafu tafara haba mama nikuma nawa ma nake, kullum kice gidan mijina
Sai kiyi kuma mama tace tana fita waje
Yanda tabarta haka tasameta akwance, toh kitashi kici abinci gashinnan, kishirya mutafi inkuma bazaki ba toh kada kibata mun lokaci
Tashi tayi zaune ta bude plate din, lafiyayyar shinkafa da miya da maccaroni, yaji naman rago
Nan tafara ci hankali kwance dan mama badai iya girki ba
Nan da nan taci ta shirya suka tafi gidan suna
Gafda magriba suka dawo, basu jimaba Abba yadawo
Bayan sallan ishai, suka hadu sukaci abincin dare atare kamar yadda suka saba ko yaushe
Fauziyyah ta miqe tamasu saida safe, ta wuce d'akinta, sai data kulle qofarta tayi adduan kwanciya sannan ta jawo wayar da yasir ya bata
Nan ta kunna aiko ba tafi 2mins sai call ya shigo
Assalamu alaikum ta fada lokacin data daga wayar
Lumshe idanunsa yayi, yace waalaikumussalam beauty na
Dftn ka yini lfy
Lfy lau my baby n u
Tace umm nima haka lfy lau
That's good, dayaushe kuka dawo?
Umm tin kafin sallan magriba
Ayyah ina ta trying wayarki bai shigaba sai yanzun
Umm yanzun na kunna dftn habiby baiyi fushi ba
Haba dai waneni, nifa yanzun burina bai fice kuyi JSSCE nanba, su dad suzo kodan sami natsuwa
Kai uncle yasir yan....
Katseta yayi nifa banson uncle dinnan, gaskiya
Dariya tayi toh habiby naji barin sakeba
Yawwa ko kefa, nan suka sha hiransu sosai na masoya daga bisani sukayi sallama akan sai sun hadu gobe a school
Rayuwa tana tafiya ma Fauziyyah da yasir yadda suke so, ana haka suka fara exams na second term, kuma idan anyi hutu yasir zai tafi gombe shima
Ranan da suka gama exams, aranan yasir ya tafi amma da kyar suka rabu da Fauziyyah, tasha kuka kam shima ba qaramun daure zuciyarsa yayi ba
Bayan tafiyan yasir Fauziyyah tayi kewarsa shima haka amma saukin suna waya
Ana gobe hutunsu zai qare yasir ya dawo, Allah Allah yake gari ya waye yaga abin qaunarsa
Haka Fauziyyah itama dokin wayewar gari take dan yanzun ta tabbatar yasir yazama wani bangare na rayuwarta
Wanda batajin akwai abinda zai iya rabasu (toh fa lalle akwai chakwakiya inji Mmn Faty)
*********
Daddy ne zaune da Abba wanda ya kawo masa ziyara
Suna harabar gidan Daddy sai hira suke kasancewar saturday ne
Papa ne ya fito cikin shiga ta alfarma kamar kada ya yaushe, rigace navy blue da ash troser, yasha wasu bufolino shoes, gashin kansa sai kyalli yake alamun yasha gyara kuma ankashe kudi
Qarasowa yayi wajensu, da faraa yagaida Abba, Abba ya amsa cikin sakin fiska
Miqewa yayi Daddy barinje wajen TJ
Toh saika dawo yace dashi, wajen motarsa ya nufa wadda tasha wanki sai kyalli take
Mai gadi na ganin haka dasauri ya bude qofa gudun yin laifi
Sai daya fice sannan Abba ya dubi Daddy yace Alhaji inaga lokaci yayi Da zamuyi Wa yaranna aure, badan mamana ba aa sabida Alamin, bazaiyiwu muna kallonsa har fice munzalin aure ba gaskiya sabida wani dalili nadaban
Daddy yayi shiru yana sauraronsa, sai daya qare sannan Daddy yaja dogon numfashi yace
Gaskiyane Alhaji amma tin bayauba nakeson muyi maganar nan sai dai bansan ta inda zan somo makaba, nayi shiru ne danaga Fauziyyah ma yanzun take kan karatunta
Abba yace ai karatu bazai hana aureba, tinda yanzun nan da watanni uku masu zuwa zasu zana jarabarsu ta JSSCE to ya isa haka agidana, sai kuma ta ci gaba agidan mijinta, kuma ko Alamin yace bai aminta da ci gaba ba to balaifi matarsace, baranma shima ai yasan dadin karatun
Daddy cikin damuwa yace aiko da idan hakan ya faru danafi kowa farin ciki, sai dai hakan bazaiyiwu ba
Abba yace bazai yiwuba kuma, yana kallon Daddy dan yamasa qarin bayani
Daddy yace kwarai sabida Fauziyyah bata dace da miji irin papa ba, aurensu bawani abu sai tauye mata rayuwa da zaiyi, tana yarinya qarama
Cikin rashin fahimta Abba yace kafahimtar dani Alhaji
Daddy yace Alamin yacanza daga Alamin d'in daka sani, Alamin yadauko wasu halaye nadaban yamaidasu abokan rayuwarsa nan ya zayyanema Abba halin papa tas sannan yace kaga fitan da yayi yanzun toh shida yadawo sai 12am ko 1am
Shiyasa nace maka sam Fauziyyah bata dace dashiba, sai yaje can ya nemo abokiyar shashancinsa ya aura
Abba kuwa zufa kawai ke tsatstsafo masa ta ko ina
Nisawa yayi sannan yace tabbas wannan alamarine babba kuma abin dubawa.....
.
Amma wannan bazai hana komaiba, Fauziyyah matar Alamin ce
Muyi fatan Allah ubangiji yasa sanadin auren yazama shiriyarsa kuma muci gaba da addua Allahu ya shiryeshi
Wani dadi Daddy yaji, rungume amininsa yayi yace nagode nagode Allah ya bar zumunci
Abba yace da Fauziyyah da Alamin dik 1 sike awajena, kamar yadda barin kyamaci Fauziyyah ba haka barin kyamaci Alamin ba
Daddy yace babu abinda zan cemaka kagama mun Komai arayuwa
Abba yace bakomai inaga kawai nan da watanni 4 masu zuwa sai ayi bikin ko kuwa
Daddy yace dik yadda ka tsara hakan zaayi, Allah ya kaimu ya nuna mana
Abba ya amsa da amin, Inyaso sai yazo su fahimci juna kafin lokacin biki
Daddy yace insha Allah next week zaizo Allah yasa Fauziyyah ta amince
Abba yace ai Fauziyyah bazataqi dan uwantaba sabida dan bawani saurayima take dashiba dan nahana babu wani wanda ke zuwa wajenta fatanmu Allah ya daidaita su
Washegari da safe Abba ya koma
Bayan tafiyar Abba Daddy yasamu momcy yamata bayanin yadda sukayi da Abba
Momcy taji farin ciki sosai, nan taji wani sabon son Fauziyyah har cikin zuciyarta
*********
Abba da mama suna zaune Bayan sun tattauna maganar biki, sai dai sam bai fada mata halayen papa ba
Mama tayi naam da hukuncin da suka yanke
Abba yace ta kira masa Fauziyyah
Tare suka shigo dakin Abba, durqusawa tayi gani Abba
Zauna da kyau mamana, gyara zamanta tayi
Fatima Abba ya kira sunanta
Dam zuciyarta ya buga dan Abba bai taba kiran sunanta haka direct ba sai yau
Naam ta amsa asanyaye
Abinda yasa na kiraki munyanke shawarin hada ki aure da dan uwanki Alamin dan gidan baffanki na bauchi
Dasauri ta dago kanta, dan jin maganar tayi kamar amafarki
Sannan ba shawarinki nake nemaba umarni nabaki, ina fata zaki amince masa dan kitayani cika alqawarin dana dauka shekara da shekaru
Kuma ina fatan yau kin fahimci dalilin dayasa, na haneki tsayawa da samari sabida gudun fadawa soyayyar wani bayan akwai mijin da muka tanada maki
Daga kanta kawai ta iyayi dan intace zatayi magana to tabbas kukane zai kubce mata
Abba yace Allah ya maki albarka, tashi kije
Tana fitowa da gudu ta nufi dakin ta, tana shiga ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya, dan bata taba tunanin haka zai kasance ba arayuwarta, fatanta Allahu yasa mafarki take kozata farka taga hakan bai faruba
*********
Ranan friday da daddare, Daddy da momcy da papa suna zaune afalon Daddy
Papa yace Daddy gani
Daddy ya gyara zama da kyau sannan ya dubi papa fiska ba walwala
Alamin inason ka bude kunnenka da kyau, kuma kasaurari abinda zan fada maka umarni ne ba shawaraba dafatan kanajina
Papa yayi shiru yace eh inaji
Daddy yace good, so abinda nake so dakai gobe idan Allah ya kaimu kaje dambam gidan baffanku Usman kasami yarsa Fauziyyah ku daidaita dan aurenku nan da watanni 4 masu zuwane
Dftn kufahimci magana ta kuma banson musu ko excuse dan aure babu fashi
Papa dake zaune sai daya miqe dan jin maganar yayi kamar saukan guduma atsakar kansa
Idanunsa nan take suka kada sukayi jajur, no no Daddy shine abinda yake fada yana girgiza kansa
Daddy yace ai nagama magana kuma zamu bata dakai matuqar ka tsallake maganata that's all
Juyawa yayi yana kallon momcy ko zata sa baki
Amma sai yaji tace ga wannan ka kaima Fauziyyah kuma koda wasa kada kace nina bata, kabata amatsayin tsarabarka
Karba yayi ya fice kawai
Dakinsa ya wuce kansa kawai ya dafe dan yarasa mafita
Washegari ba wanda yayi ma sallama ya wuce abinsa dan dik haushinsu yakeji
Bayan azahar ya isa, sai daya huta kafin ya sake wanka, shiryawa yayi cikin farar shirt mai layin baqi da black jins
Baqaqen bufalinos ya saka aqafarsa kallo daya zaka masa kagane akwai naira a hannunsa
Wayoyinsa ya dauka ya fice, danwareriyar motarsa ya shiga itama baqa sannan ya nufi gidan Abba
Fauziyyah ta fito daga wanka kenan tana kwalliya dan zataje gidansu Amina Ibrahim qawarta
Sai taji mama tana gaisawa da mutum, daga yanayin maganar ta fahimci baqon da Abba taji yace zaizone ya iso
Dogon tsaki taja yanzun dik saurina ya tashi a banza kenan, naso na fice kafin yazo ta fada afili
Mama ce ta shigo tace Fauziyyah ga Alamin yazo yana waje sai ki bude masa falon abbanki
Naji shine abinda tace
Takai 15mins kafin ta fito nanma sai da mama ta sake mata magana
Papa yagama quluwa kamarshi ace wata banza har ta ajiyeshi, duba time yayi nan da 5mins idan bata fito ba to zaiyi tafiyarsa
Sai gata ta fito, fiskanta fayau ba kwalliya tana sanye da atampa riga da zani, da farar hijab
Wani wawan tsuka yaja Dan gaba daya haushi ta bashi, ji qirjinta kamar na sauro to ma yaci me da ita
Ganin yayi shiru yasa tazargi kallonta yake ta cikin glass din idonsa
Kallo 1 tamasa ta kauda kanta, ina yini tace dashi
Qalau yar Qauye, Zaro ido tayi
Yace meye kike Zaro ido qaryane, dubeki wai Budurwar Qauye ko
Toh kisani nafarko banson raini dan nasan halinki ne
Sannan wannan auren hadin iyayenmune kada kiyi tinanin inasonki kozan soki, so kitsaya amatsayinki
Kada nakuma zuwa ki bata mun lokaci
Yana fadin haka ya bude mota, wani bag mai kyau ya miqo mata gashi inji momcy
Bata riqe ba yasake, jakar tafadi aqasa
Ko kulawa baiba ya wuce ya shiga mota yayi tafiyarsa
Fauziyyah kuwa rasa ma mai zatayi tayi, lalle wannan inna bashshi abinda zai mun kare bazaiciba
Amma zan gwada masa nafishi qin wannan auren
Sunkuyawa tayi ta dauki jakar tayi cikin gida da tunani kala2 aranta........
Please can i know the admin of this website, iwant ask him some question if is around send me his email or phone number in mustaphaalkasim8@gmail.com
ReplyDelete