BAYAN WUYA SAI……
NA
RAMLERT y
salis
KAINUWA WRITERS
ASSOCIATION 🤝
DA SUNAN ALLAH ……...YA ALLAH KANUNA
MANA GASKIYA ,GASKIYA CE KABAMU IKON BINTA .KANUNA MANA KARYA,KARYA CE KABAMU
IKON GUJEMATA.
Wannan page nakane
ya mustynah!sadaukar wace agareka
page 56
Soyayyahce ta shiga tsakaninmu mai
karfi,muna son juna sosai afifah mahaifinki dan kanin babanane,tun lokacin
damuka hadu dashi bayan dawowarsa daga karatu,nadena kula kowane saurayi a
family domin nasa a raina shine zai zama mijina.
Akwai wani dan kanin
babana shine likitan family dinmu,duk wani rashin lafiya daza'yi ko wata
matsala data shafi lafiya shi ake sawa saboda babban likita ne,ninasan akwai
mutunci a tsakaninmu ammah bansan yana sonaba,kuma akwai shakuwa sosai
atsakaninmu.amma banTaba sanin yana sonaba sai da babanki ya dawo muka fara
soyayyah, har manya sukashiga tsakani,yanemi soyayyahta alokacin danikuma
babanki nake so hakuri nabashi ammah yaki hakura wai ai tunkagin nasan babanki
shinafara sani kuma nasan yana sona,sosai abun yaso yaxamamin matsala dan akwai
mutunci sosai a tsakaninmu banason muyi rabuwar rashin kyautawa.ammah fir yaki
saurarata waishi dole sai najanye daga kula mahaifinki shibayaso,kuma shi
auranmu nankusa yakeso bazai iya jira har sai shekara ta
Zagayoba sannan ayiba,
nashiga damuwa sosai
akan,lamarin dannarasa taya zan rabu dashi batare da ansamu matsala a
zumuncinmu ba,Ana hk su babana suka kirani akan zancen mahaifinki,ban6ata mudu
lokaci ba na amsa cewa ina sonsa.babana yayi farinciki sosai hakama baban
mahaifinki har aka yimana baiko bansan waye ya sanar dasu muna soyayyah ba.
Watarana da yamma ina zaune a
falo a part dinmu,sai ga dan kanin babanmu yashigo a birkice wato likitan
family din,gabana yazo ya tsaya Yana huci,inna kulama kamar hawayene afuskar
shi da yatsansa yanuna ni yana cewa "nizaki yaudara menayi miki meyesa
zakimin haka kinsan yadda nake sonki basai nafadamiki ba,ammah wai naji anyi
baikonku jiya da wannan banza.tsawon wane lokaci muke tare dake ammah baifi
wata daya da dawowarsa ba zaki zabe shi akaina mena miki haka"?jikina rawa ya fara nayi zaton dukana zaiyi sai kuma yatsugunna yarike
kafata yana kuka yanacewa"ki taimakeni karki barni dan Allah kicemusu
kinfasa wlh bazan iya rayuwa babu keba,nasan nayi kuskuren kin fadamiki
ammah nayi tunanin kinsanine kin fahimci inda na dosa,bawanda yasan da irin son
danake miki sai mahaifiyata kiyi hakuri karki barni"
Afifah nashiga rudani alokacin
sosai nafarko naji tausayinsa sosai sai naji konajenye ammah dana tuna irin son
danakewa babanki sai naji bazan iyaba yin abinda yaceba,na dai samu na
rarrasheshi tsawon kwana biyu. Kullum muna wasan yar buyadaga karshe mukayi
wata haduwa a school bansan yana binaba har na isa,fadamasa
Gaskiya nayi sosai mukayi rigima muka
rabu kancewa "bazai bari na auri kowaba inbashi ba sai dai muyita zama
haka dagani har shi"ni dai kawai najishine ammah gani nake bai isaba,haka
suka kulla gaba da babanki ko gaisawa basayi.
Ana saura sati daya bikinmu
nida mahaifinki,duk wanda za'a aurar a shekarar muka hadu a babban falon babana
yayimana nasiha,sannan yace dukkan mu za'amana gwajin jini dan a tabbatar kowa
na lafiya kuma asan matsayin jinin kowa kamar yadda akasaba.
Dahaka aka fara gwaJi har akazo kanmu
nida babanki likitan damun hada ido sai yayi murmushin mugunta niduk ban kawo
komai araina ba,Afifah ashe akwai abinda yake shiryawa,wannan mutumin shine
silar shiga matsalarmu domin shine ya hadamu da iyayen mu.
Daya gwada jininmu sai yace
wasu babanmu ai akwai matsala,"cewa in mukayi aure dani da babanki jininmu
zai bada sikila wato zamuna haifar yara masu cutar sikila"dafari bamu
dauki abun dawata matsalaba sai damukaji irin illar sikila.
sosai iyayen mu sukayi bakinci
Suka cemasa meye to mafita sai yace"Ai bawata mafita gaskiya sai dai
muhakura inkuma bamu hakura ba to zamuna samun yara marasa lafiya"kowa ya
girgiza da zancen sa shima sai yanuna kamar abun bai masa dadiba.
Haka aka tashi daga taron kowa
jikinsa a sanyaye,nikam har da kuka, nida babanki aka kiramu bayan munje
su babanmu suka cemana to su dai da ana haifar yara ba lafiya kuma abun zaiyi
yawa tunda munsan auren family akeyi gara mu hakura da juna,sai kowa a canza
masa abokin zama.
Tashin hankali mukashiga sosai,mun
rokesu akan su barmu amma sam sukaki haka har aka tashi daga taron.
Acikin kwana uku na zabge
sosai nayi rama duk nazama wata iri,bani da aiki sai kuka narasa ina zansa
raina,hakama babanki kullum yana cikin damuwa.
shawara babanki yazomin da ita
kancewa "shifa bai yarda da abun da likita ya fadaba akan gwajin jininmu
yafadane dan yana son yasameni"sai daya fada sannan nima nayarda hakan zai
iya kasancewar.
Asibiti muka tafi mukaje gurin
wani babban likita Yasake yimana gwaji anan ya tabbatar mana bamu dawata
matsala ajininmu zamu iya yin aure.
mamaki mukayi sosai dajin
abinda yafadamana,Anan muka tabbatar abinda likita yafadawa su baba karyane
yayine dan a rabamu da babanki.
Da murna muka koma gida muka nunawa
su babanmu ammah sai sukace karya mukeyi zuwa mukayi akayimana result din karya
dan su amince mana kuma ma ai likita bazai mana karyaba.
ina kuka ina musu rantsuwa
ammah basu sauraremu ba,kowa kin yarda yayi da zancen.
likita nasamu
Narinka rokonsa akan yayi hakuri
yafadawa su babanmu gaskiya ammah sai cewa yayi "aishi yafadamin baxai iya
kallon na auri wani bashiba"
Bawanda bamuje gurinsa yarokesu
suyardaba ammah abun yaki yiwuwa,kullum saina kira babban yayana ina masa kuka
har garashi shiyana rarrashina sosai yamin nasiha akan nayi yadda sukace.
Babana sosai ya tausayamin ganin
yadda nakoma,haka zai zauna yana rarrashina yanatamin nasiha inyi hakuri inyi
yadda suka umarceni saboda gujewa shiga matsala kar azo asamu yara Marasa
lafiya,kuma in yace zai barni na aureshi yan'uwansa zasuga kamar yayi son kai
saboda ni 'yarsace ya gwammace akawo musu matsala cikin family,duk dacewa shine
babban su ammah suma sunada hakkin yake hukunci akan yaransa,kuma bantaba neman
abu agurin sa narasa ba to shima yau yanason nayi masa wannan alfarmar nanemi
abu yabarni na auri wanda nake so ammah bai barniba na daure nayimasa wannan
alfarmar"wannan itace maganar da mahaifina yake fadamin duk sanda naje
masa ina kuka.
mahaifiyata Itama tana bani
baki sosai,itama tashiga damuwa ganin yadda nakoma.kowa bani baki yakeyi gara
nahakura akan nasa yaran dazan haifa a matsala.
Dahaka na hakura,inaji
inagani karyace aka mana, ammah nasamu mahaifina nace masa duk mijin dazasu
canjamin karsubani likita,ya tambayeni meyesa bance masa sharrine gwajin dayayi
manaba,kawai cemasa nayi ba komai.
Alkawari yamin akaro na biyu zai bani
duk wanda nake inhar ba irin waccan matsalar,amince masa nayi yabani duk wanda
yakeso ammah banda Likita domin zan iya zama da kowa banda wanda yayi silar
rabani da babanki.
wani daban,aka bani wanda zan
aura,shina mahaifinki aka basa wacce zai aura.alokacin har nafi mahaifinki
dauriya domin sai da aka kwantar dashi a asibiti yana rashin lafiya sosai,
Ana gobe za'a fara
biki,kwanwar su babanmu ta ido da duk yan'uwa wanda ba a kasar sukeba.har
babban yayana da matarsa.
Da kwanwarsu babanmu taje
asibiti duba babanki sosai hankalinta ya tashi ganin yadda yake,nima danaje
dubashi asume aka
Dawo dani,hakan yakara tayar da
hankalinta.
Su babanmu tasamu tace tazo da shawara
"ita a ganinta su barmu mu auri JUNA tunda kowannenmu na cikin
damuwa"basu yarda da zancen taba, sai datasa wani sharadi nacewa"duk
dan dazan haifa bazan shayar dashi nono ba aranar dana huihu za'a dauke yaron
har sai ya girma,tunda bai sha nonoba ba'abunda zai sameshi"duk da haka
basu amince mataba,sai data tsugunna akan gwuiwowinta har hawaye nazuba
afuskar tace"tun tasowata nake karkashin umarninku amatsayinkuNa
yayuna,ina da wanda nake so ammah kukace nima auren gida zakuyimin ba yadda
na'iya haka nabi umarninku dan kawai inmuku biyayya ba dan banason
saurayinba,ko bayan aurena duk abinda kukace haka nakeyi dai dai da rana daya
bantaba sa6awa umarninkuba har zuwa yau danake durkushe a gabanku.ashe nima
kenan baxan iya kawo shawara ku daukaba bazan iya yankewa yayanku hukunci ba
kenan.ko bayan ranku dolene na rungumesu domin nima tamkar yaran cikinane,yadda
suke nunawa junansu soyayyah koda an aurar
Dasu ga wasu daban,bakwa tsoron
sukasa rabuwa da juna kowannensu da aure kansa ammah suna bibiyar juna,in har
aka rabata da dan dazata haifa bai sha nonontaba ba'abinda zai samu yaronta
tunda dama duk wani abu ta nono yara suke sha,da wannan nake neman
afuwarku ku duba sannan ku yanke hukunci .
Anan suka yanke hukunci akan
shawararta cewa sun amince da sharadin aranar dana haihu zasu dauke dan
ko 'yar su kaimata dan inhar zasu bar dan a kasar nan zami iya zuwa.
wasu sunyi murna wasu kuma ba
Suyiba,dan suna ganin araba uwa da
danta data haifa aranar bakaramin damuwa bane.
Dani da babanki farinciki muka
shiga,sosai mara misaltuwa,wasu na gargadina kar nasake nayarda ace daga na
haihu za'dauke dan gara na auri wani daban,Nikuma jinsu kawai nakeyi dan gani
nake gara hakan sosai da'arabamu,shima babanki haka yace gara haka sau dubu da
a rabamu.
Afifah biki akayi wanda ba'ata6a irin
saba a family,mu shida aka aurar mata uku maza uku.babanki shine auta
agun iyayensa nikuma nikadaice mace Dan haka akayi 6arin naira sosai,afifah
inkinga gidana acikin family hause zakiyi mamaki domin ankashe kudi sosai wanda
hankali da tunani bazasu iya daukaba.
Daga kayan danasa ranar kamu zuwa
ranar party,ranar budan,kai har ran daurin aure,afifah kudinsu baxai dauki
hankaliba mahaifiyata da babban yayana sune da wannan aikin, abunda zan iya
tunawa iya sarkokin danayi amfani dasu abikin zasu kai millions arba'in,takalma
da jakunkuna sun kai millions saba'in,haka wasu agoguna da mahaifiyata tasiye
Su da dadewa bansa nita ajiyewa ba suma sunkai millions biyar.komai nawa danasa
abikin makudan kudine suka siyesu,har abin yafara zama surutu a family sai
da'akaje gidanama akafara surutu masu mamaki nayi masu gulma haka,afifah dakin
ganni alokacin zaki dauka wata sarauniyarce zata gasar kyau,ranar daza'akaini
babana yamin nasiha da mahaifiyata da yayunama nayi kuka sosai duk da acikin
gidanne naji radadin rabuwa dasu.
Alokacin da akakaini part din
kakarki tawajen uba,wata abaya tadauko wacce Akayimata ado da gwal wacce ta,kai
millions dari har dawani abu ta nadamin da kanta,kowa mamaki yayi sosai wasu na
guda cewa tayi kowama ya dena mamaki dan da a lefe zatasa ammah saitaga gara
sai nazo dan haka yanzu nazama autarta tunda nazama matar auta,haka take cewa
babanki.
Rayuwa mukayi da
babanki cikin kwanciyar hankali ga dumbin soyayyar damukewa juna,kyau nakara
sosai nayi giba.babana sosai yakejin dadi duk sanda naje gaisheshi hakama
mahaifiyata take koyamin business irin nata.
Hakama surukata tana kula dani sosai
inada masu yimin komai tamkar diyar sarki.
Rayiwatamin dadi soyayyah muke
da mijina sosai,ana haka har nasamu ciki ananma na fara samun wata kulawa ta
musamman ammah damun tuna za'a dauke abunda zan haifa abin sai yafara damunmu.
Aranar dana haihu na haifu
yarana yan biyu duka maza,kowa yayi farinciki babanki yayi kuka har dana murna,
kowa na murna aranar.
aranarne kanwarsu babanmu ta
sauka a kasar,sai kuma nashiga damuwa ganin da gaske za'adauke minYarana kuka
nayi sosai sanda za'atafi dasu hakama babanki.kakarkice take ta rarrashina
ammah gani nake duk abanza ace na haihu yarana badu dan dani nono naba kuma a
daukesu.
kullum ina cikin damuwa har nagama
wankan jego asatin dana gama babanki yamana biza muka tafi ganin yaranmu.
sun danyi wayo,dukkan du da
babanki suke kama sai dai babban farine sol karamin kuma ruwan tarwatsane inaji
ina gani na baro yarana muka dawo gida.
tun muna damuwa har
mukadaine,mahaifiyata nabani hakuri sosai haka Ma surukata.mun koma rayuwar mu
kamar da kamar ban haihuba,cikin so da kauna.
Ana haka nakuma samun ciki na
haifi 'yata mace mai kyau itama kamat babanku ruwan tarwatsane fatar ta.
afifah haka itama aka rabani da
ita hakan yadame mu sosai nida babanki har zuwa mukayi muka samu likita muka
rokeshi akan yaje ya fadamusu gaskiya ammah ko saurararmu baiyi ba.
Bayan shekara biyu sai na kuma
samun ciki,dana fadawa babanki sai yace kar infadawa kowadanshi yagaji bazai
iya kara bari arabamu da dan
Dazan kuma haifaba.
Aiki ya nema a saudia kuma
akayi sa'a yasamu kuma zasu bashi gida da motar hawa.fadamin yayi
cewa"zamu gudu mubar mudu kasar bazai kara bada dansaba,bazamu dawoba har
sai abinda zan haifa ya girma sunga bawata cuta dayasamu daya sha
nonona".nima sosai nayi farinciki da shawararsa,kuma ba wanda zamu fadawa
inda muke.
Wannan shine babban kuskuren damuka
aikata,sai tasaki kuka mai ban tausayi ta rungume afifah tana kuka tana cewa"kece
muka haifa afifah damuka gudu saudia"
Aranar dazamu tafi sai damukaje gidan
kowa da kowa muna musu sallama bayate dasusaniba,
Nayi kuka sosai dan zanbar
iyayena da 'yan'uwana babankine yaita bani baki har nadena.
abinda yasa nakasa manta saudia saboda
nasan canne ake aikin haji,inna tuna wannan sai ingane saudia muka gudu.12:00pm
jirginmu zai tashi aranar,kuma aranar ne kanwarsu babanmu taxo wai ta kawo 'yan
biyu wai ta yaye kanwarsune tafara cin abinci,'yan biyu kuma alokacin suna
tafiya ko inaabin sha'awa kamar yaran turawa.
Ba abinda muka dauka sai
bizanmu da wani abun hotuna bikinmu wanda babban yayana yamin,abun security
akesamasa bamai budewa sai wanda yasan sunan da'aka saka kums sunnan,babban
yayana nasa akan abun mai kama da karamar tibi,afifah abun yana gida yanzu haka
sai dai bawanda zai tunamin sunan yayana da yabude kinga hotunan family mu baki
daya.
lokacin dazamu tafi goman dare tawuce
'yan biyu suna part dimu alokacin karamin ne yake kuka sai babanki yasa aka
maidashi gurin mai renonsa dan yana da
Kiwiya sosai,
babban kuma yana hannun babanki har
muka fito harabar gidan,mahaifinki yace bazaima maida sshiba dashi zamu
tafi.kin yarda nayi nace bai kamata arabashi da dan'uwansaba,haka muka fito
dashi har muka isa airport ina kuka.
Damuka isa babanki ya kira gida
a waya yafadamusu sudena neman yaron yana gurinmu,dukace masa ina mukaje bamu
kwana agida ba,cemusu yayi munbar kasar har saina haihu zamu dawo.fada sukayi
masa sosai kuma akancewa mudawo aranar,ammah mukacire layin wayarma mu
Ashe kusan wayarmu ta
karshe kenan,munzalinci kanmu mun manta rayuwar mu ba'a hannun mu takeba.
karamar yarkoyo
RAMLERT y salis ✍🏻 inajin dadin addu'oinku da encouraging dinku ALLAH yabar zumuncin
KAUNA masoya.
0 comments:
Post a Comment