NA
RAMLERT y
salis
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝
DA SUNAN ALLAH ……...YA ALLAH MUNA
ROKONKA ABINDA ANNABI S A W YAROKRKA,MUNA NEMAN TSARINKA DAGA ABINDA ANNABI S A
W YANEMI TSARINKA DA SHI.
Wannan page mallakane gareki khadija
nanancy my bloody
page 34
Kuka takeyi sosai ranta namata
kuna,tace ummi karkina fadin zaki tafi kibarni inazanje ummi ?wanake dashi inbakeba takarasa maganar tana share hawayen fuskarta .
Allah yana tare dake afifah tabbas
BAYAN WUYA SAI DADI,dan hk koda na mutu Allah ne zai baki mafita.
Abin dana iya tunawa
arayuwata kafin na hadu da wannan mantuwar shine:
Mahaifina babban dan kasuwa ne mutum
ne mai tarin dukiya,yana kasuwancinsa da gaskiya da rikon amana wannan shiyasa
kullum kasuwancinsa yake kara habaka,afifah Nakasa tuna koda sunan mutum daya a
gidanmu sai dai dukkan su ina ganinsu a idona,Babana yana odar kaya daga
kashashen waje abinda yashafi kayan mata,jakunkuna da takalma kayan mata dai
sosai atampopi har da yadukan,maxa da takalma turaruka,agogo,sarkoki har dana
kwal,afifah duk wani,nau'in material zaki sameshi a manya manyan shagunan
babana,dukiyar da mahaifina yake da ita tafi karfin in iya lissafawa.
mahaifina su 5ne awajen
iyayensu,babana shine babba sai kannansa maza3sai kanwarsa,su hudu
Maza sai autarsu mace,
babansu ma'aikacin gwanatine kakana
kenan ammah na mance wane aiki yakeyi,mutumne mai rufin asiri wacce ta haifi
babana ita ma'aikaciyar gwanatice.
lokacin da mahaifina ya gama karatu
alokacin yafara kasuwancin,dan dama shi yakaranta .
babana yatabayin aure kafin
mahaiyata,matar ta mutu a hanyarta tazuwa kasarsu dama acan suka hadu,ta haifi
danta namiji,afifah banso,na mance sunan babban yayana ba wanda muka hada uba
dashi domin duk cikin yayyena wanda muke uwa daya bawan
Da yanunamin so irin sa.
babana yayi aure na2bayan mutuwar
daya matar data rasu,mahaifiyata ya aura.
ammah kinsan me afifah ?family meeting sukayi akan wata rigima da'akayi,dangin,matar da
mahaifina ya aura wacce ta mutu danginta sun dage sai anbasu dan data
haifa,shikuma babana ya dage bazai dau dansa ya kai har wata kasaba,ammah
yayimusu alkhairi duk sanda kasuwancinsa yakawoshi zaizo musu dashi,ammah kiki
yarda ba yadda ba'ayi da mahaifina ba ammah shima fir yaki basu.To dasukayi
taron family Kakarmu tace "daga rana irin ta yau andena auren bare a
zuri'arsu"wasu daga cikinsu basu yardaba ammah ta kafe bayanda suka iya da
ita,domin ko cinkin yan uwanta itace babba wacce ta haifi mahaifina kenan,kuma
iyayensu sun mutu ita ta zama uwa ga kanenta.ita da mijin tama yan uwane
kakaninmu kenan,kuma yawanci family auren zumunci sukayi tun kafin tasa dokar.
Da mahaifina da mahaifiyata yayan wa
da kanine,me bin mahaifina shine ya auri kanwar mahaifiyata hama sauran
kanensa duk auren gida suka yi.mu 7 ne agurin mahaifimu yayyena 5
maza,sai ni da kaninah,babban yayanmu yan'uwansa sun matsa dole babanmu ya
hakura ya bar musushi,munyi shakuwa sosai dashi saboda nikadaice mace
cikinsu,lokacin da zai tafi nakusa gama primary,kuka sosai nayi dan ganin zai
koma can da zama sai da'akamin wayo mukaje tare nayi kwana uku sannan nadawo
akan cewa da anyi,hutu zan koma nibasan wayo akamin ba.Lokaci na tafiya komai
nacanxa wa,dukiyar mahaifina sai ha6aka takeyi,kullum gidanmu cike yake da
jama'a
Yake musamman ranar juma'a,bawanda
zaizo acemasa babu.
Gata tako ina nake samu baga
yayyenaba kadai,har iyayena da kakaninna da sauran yan uwa,hakan yasamo asaline
sbd iyayena nikadaice yarsu mace,yayunama nikadaice kanwarsu mace musamman
babban yayana duk da ba zaune yake akasarba ammah ina samun kulawarsa,ko da
yaushe muna hira awaya,duk abinda ya shigo nayayi sai ya siya ya aikomin.
dan har kakarsa cewa tayi wai suna
son abarmusuni,ammah hakan ba mai yiwuwa bane nikuma lokacin sbd Yaranta banki
na tsallake dukkan yan'uwana nakoma gurin yayanaba na barmusu kasar.
yanda kikaganki hk afifah
tonima lokacin danake budurwa dukkan kamaninmu daya dake,sai dai kyawuna yafi
naki bayyana sbd irin hutu da kulawar danake samu,afifah ko yar shugaban kasa
baxata nunamin hutu ko wani abun more rayuwa ba.
babban yayana farine sol
kamarni,domin mamarshi balarabiyyace,duk inda mukaje tare sai azata shine kawai
muke uwa daya uba daya dashi,kasancewar mufararene sukuma sauran duk babanmu
Sukayo,shikuma babanmu bazakace masa fari sol ba ammah fatine,
family dinmu fulani ne afifah
da farare sol dawanda farinsu bai fito sosai ba,da mahaifiyata nake kama.
yayyen mahaifina kowa soyake
yaga yafaran amin,komai sukasamu ni,hakan yasamo asaline sbd ko wanw yaro a
family babanake daukar nauyin karatunsa ko wace kasa yake son xuwa, mazan su da
matansu,hk kuma duk yarinyar daza'a aurar da ita to duk kudin da
mahaifinta kedashi babana baya barinsa yamata komai,shine yakeyi.
Yana taimakon "yan'uwansa
sosai wasu yana sasu abakin,kasuwancinsa wasu kuma yana,nema musu aikin
gwanati.
kasancewata yarsa macr tal,yasa
kowa keson farantamin dan sunsan yadda yake sona.
hk muka cigaba da rayuwa cikin
farinciki da yan'uwa da iyayena da babban yayana dabaya kasar,
a family mu ba'a barin mace
tayi wani karatu mai zurfi akeyimata aure,wata iya secondary,wata kuma sai
tafata jami'a,da miji yaxo inhar kingama secondary za'a aurar dake,ammah sai
dai inshima dan'uwane wani
Lokacin ma hadaki da wani za'ayi
inhar yayimiki kema kinyimasa to sai amuku aure,ammah ba'a taba yimuku dole
inbakwason juna,wasu da kansu zasu kulla soyayyah ba'asanibama har sai in
lokacin auren yayi su fada.
afifah family dinmu
abun,burgewane,akwai akwai ma'aikata daban daban ,yan kasuwa
,malamai,dasauransu ,
Kuma sau daya a shekara ake
bikin aure a family din,sai kiga an hada mutum goma ko kasa da haka,muna da
yawa a family din.
Ashekarar daza'ayiwa yayuna
aure akayi wani taro a family
"cewa zamu,gina family HAUSE
wanda kowa zai koma ciki da zama"a lokacin nayi matukar farinciki ammah
sai nake ganin kamar baxsi yiwuba sbd muna dayawa.
Wanibabban fili na gwanati
babana yasiya duk da haka sai daya kara da siyan wasu filaye da gine ginan dake
kusa da filin,sannan yasamu babban fili sosai.
Gudummawa kowa yafara kawowa
dame karamin karfi dame babban karfi,ammah sai babana yace "shi bazai
karbi kudin kowaba,zai gina gidan kuma baxai banbanta ba .
Mahaifiyarsace ta hana shi
Kakata kenan,cewa "yakar6i gudummawa ga duk wanda yakawo saboda ya rage
wani abun"sannan ya karba.
komai dakikasani daga waje
akayoodarsa wanda za'ayi aikin gidan, daga kofofi,winduna,get,kayan
bandaki,fankoki,Ac,duk dai wani abun da'ake bukata a aikin gida wanda za'asa da
wanda za'asa in an gama.
Dan ban manta ba company da'
akasiya agurinsu sune suka dau nauyin kawo kayan kasarnan dan kayan dayawa
sosai.
Damukaje ganin gidan lokacin
da'aka gama ginawa,nayi mamaki sosai afifah wane irin
Kudine hk da babana duk danasan kowa
yabada nasa taimakon ammah yakashe kudi sosai,part part ne agidan kowane part
da,number dinsa,kowane part akwai decoration na flower a gabansa da bayansa.
kasan gidan kuma kwaltane
kwance,kofar kowane part akwai wajen ajiye motoci,akwai wani katon lambu agidan
sai wajen wasan yara da wajen kiwo dan dama babana yana kiwo sosai.
Gidan yayi kyau sosai ankashe
kudi ba kadan ba,
Alokacin daza'ayi bikin ina JSS one
murnayi sosai domin yayuna zasuyi aure,babbanYayana shine kawai bazai zauna
agidan ba ammah yar kanin babanmu zai aura,sai dai yatafi da ita duk sanda
zasuzo suna da part dinsu dazasu zauna ciki,sbd yan'uwan,mahaifiyarsa baxasu
yarda ya dawo gurin muba sunce"mahaifiyarsa ita dayace 'yarsu to shima shi
dayane jikansu"hk abun yake dama ga wasu kasashen daga da daya sai biyu
insunyi yawa uku.
Agidan mu akwai mutum 4 maza wanda
za'a aurar,ni da kaninane muka rage,Gidan kanin babanmu akwai mutun 3 mata 2
namiji daya,daya kanin babanmu mutum 4 shima mata uku namiji daya,sai kanwar
babanmu ita kuma 'yarta mace daya.
MATA 6 MAZA
6 haka akafara hidimar biki ta kowane 6angare,
Anfara biki cikin farinciki da
annushuwa,ana gobe za'a bude family hause yayana sukazo da yan'uwansa
akan cewa bayan angama biki zasu koma can suma suyi nasu bayan an kai musu amarya
da yan kai amarya.
Hakama kanwar babanmu itama
taxo da 'yarta wacce itace zata auri yayana wan Da nake bi,itakuma sai sai
iyayenta sukoma babu ita domin mune,dangin miji.
Ranar da'aka bude family hause
kowa yayi farinciki mara misaltuwa,dan kowa ka gani aranar cikin farinciki
yake,an bawa kowa key din,part dinsa har da angwaye,dangin su yayana dasukazo
bikin suke ta mamaki "wai wannan family dayane sukan abun ya burge
su,ganin har da jikinsu shima yana da nashi part din "
Babana ne yayi wani jawabi
kafin taron yatashi cewa "kowa yasa aransa agidansa yake zaune shi ba aro
yabasuba Kyautane har abada" Itama kakata cewa tayi "ko bayan ranta
bata yarda danta ko dan kannenta ba ko jikokinta su fita daga gidan da nufin
canxa gurin zama ammah 'yayan jikokinta suna da zabi insuna son zama
gidan inma basa so duk zasu iya domin wata rana yawan zai iya yin yawa
"Afifah nida mahaifinkine muka fara karya wannan dokar,danmu kasar muka
bari ba gidan ba.
sai datayi kuka mai isarta
daga ita har afifah bamai rarrashin wani,sannan tacigaba da cewa "haka aka
gama bikin kowa na murna
Bayan bikin wasu daga cikin yan'uwa
wanda sukariga sukayi aure ba'auren gidaba sune suka koma gidajensu da
wanda ba yan garinba da wanda ba 'yan kasarba.
Acigaba da rayuwa a family
hause cikin zumunci,kullum ina part din amare musamman wacce ta auri yayana
wanda nake bi,saura sati biyu hutun makaranta yakare BABANA yamin biza
zuwa can inda babban yayana yake domin dama ba'aje dani bikin su nacan ba.
Nakarasa hutuna acan badan son
raina na dawoba.
Akwana atashi na kammala karatuna na
Secondary,alokacin abubuwa da dama
sun faru a family hause wasu sun mutu wasu sun haihu,babana shekarar tazo
masada farinciki har da mahaifiyata domin sun samu jikoki har 5,baban yayana
matarsa ta haihu 'yan biyu mace da namiji sauran yayuna kuma duk maza suka
haifa.
alokacin samari sunmin cahh
dana family dana waje wanda ba yan'uwaba ,sanin dokar family yasa bana
bata lokacin kuka su.
Afifah in kina son ganin 'yargata ta
karshe alokacin inkika sameni kin samu,bani dawata matsala arayuwata Babana ya
tsayemin komai kaf family ba yarinyar dazata nunamin kyau,ko kudi,ko hawa mota
me tsada.
motor na uku ne daya tazuwa
school akwai wanda shine yake driving dina hk shine yake daukoni,daya ta yawonace
nida kaina nake driving kaina,daya kuma itace nake kwasar yara ranar daba
school nariga yawo dasu zuwa gidan wasanni,duk da muna da wajen wasan yara
agida.
Afifah ina da yan aiki su uku
suma,mekula da dakina da toilet dayimin wanki,dame girkina da kula da lokacin
cin abincina domin
Ina da wasa da cin abinci,dame kula
da laphia ta duk inda zani tana tare dami,ko makaranta ko unguwa saboda tasab
inda zani,da namiji ne yake kula sa shige da fice na ammah babana yace baiyarda
da alakata da namiji ba.
Mahaifina mutun ne mai addini
sosai,mahaifiyata tana sa kirki sosai.
Koyaushe part dinmu baya rabuwa
da matan manya,saboda tana kawomusu gwalagwalai,jakunkuna irin na manyan mata
masu tsada da takalma,sarkane,har agogon gwal.
Matan gwana wani lokacin sukanzo
har gidan Musamman intayi sabuwar oda,bata kai kayanta wani guri duk matsayin
ka sai dai kazo gida kasiya ko ka aiko,inkuna dawata alakane sosai zatasa
akaimaka,dan akwai sanda rasa driver na yakaiwa,matar gwana wata sarka da
agogon gwal to kasancewar suna da kudi sosai yasa tace muje tare,hk mukaje tare
zuwana gidan gwanati na farko afifah falon gidan yayi kyau sosai ammah babu
wani abu dazai nunawa namu falon,anan muka,hadu da danta har mukayi
musayan number ammah abun bai yiwuba domin da gwamna ya Tuntu6i babana dazancen
babana bai boyemasa komai na dokar family muba.
Ina aji 2 a jami'a
babanki ya dawo daga karatu muka dara soyayyah sosai,
wacce sai yanxu nake dana sanin
yinta,munsaku a matsala munsa iyayen mu a damuwa munsa kammu anadama,munyanke
farinciki kowa munyi sanadiyyar maidaku marayu munguji iyayenmu mun nuna musu
munfison yayanmu akansu.
kaicona !afifah kiyafeni tabbas inkikaji karshen labarin zali tsaneni,du da gata
da iyayena suka nunamin nagujesu saboda miji kuma
Saboda yarana,
mezancewa ubangiji na inna mutu
bannemi gafarar iyayena da sauran yaranaba?munyi babban
kuskure mun bijire maganar iyayen mu saboda son zuciyarmu akarshe munyi niyar
dawowa garesu ammah Allah ya saukar mana da jarrabawa wacce tayi sanadiyyar
mutuwar babban yarona dakuma ...daku...ma .. Sai ta kasa karasawa kuka kawai
takeyi. Itakuma afifah tama kasa zubda hawaye a fuskarta saboda wani tunani
datakeyi "wai shin ummi da babana mesukayiwa mahaifansu datake ikiratin
zantsaneta inaji"?
ummi ki karasamin dan Allah waye kuma
ya mutu bayan yayana?afifah ta fada tana durkusa gwuiwarta
a kasa.
NIMA TAMBAYAR DAZANYIWA UMMI
KENAN KUMA ME SUKAYIWA,IYAYEN SU HK?MEYE DALILIN GUJEWA IYAYENNASU?MEYESA BATA KOMA MUSUBA TO YANXU TAKE RYW CIKIN WHL BAYAN YAR GATACE
GABA DA BAYA ?
MUJE ZUWA y salis (Ramlert )✍🏻
0 comments:
Post a Comment