Thursday, 29 November 2018
Home »
Canjin Rayuwa Complete
» CANJIN RAYUWA Kashi Na 1 (Shafi 21-25) - ISMAIL SANI
CANJIN RAYUWA Kashi Na 1 (Shafi 21-25) - ISMAIL SANI
CANJIN RAYUWA
[Kashi na 1]
(Shafi 21-25) Tare da - Halima K. Mashi
Post By ISMAIL SANI
Kuma tana son ya zama na karshe, takaicinta ma talaka ne shi, ba wani isashshe ba. daf da zai fita daga cikin gidan,abdulkarim ya yi masa sallama,ya tsaya suka gaisa ta hanyar yin musabaha. ya ce,ai ina ta sallama baka ji ba,ya ce, na ga fuskar ka ba walwala ko yaran ne suka hada maka zafi?malam lsmail ya ce,ko kusa ai yaran gidan nan basu da matsala sam, sai dai wata bakuwa da hajiya ta ce a koya mata karatu,amma ba yar ta bace ko?abdulkarim ya sake matsowa kusa da shi,ya ce,ba dai MIMI ba?
lsmil ya ce,kamar haka naji an kira ta,gaskiya saboda ita zan iya daina zuwa gidan nan in har zata dinga zuwa karatu. Abdulkarim ya ce,kai mata nuna maka halinta kenan,don allah kayi hakuri zan fada ma hajiya, kuma ina zaton ma gobe zata tafi,lsmail ya ce, shikenan ba damuwa. Suka yi sallama ya fita, abdulkarim ya nufi ciki kai tsaye zuwa falon hajiya, duk suna falon,MIMI kuma tana kujerar dining,ranta cinkushe,ya kalli hajiya,ke ki ka tura MIMI tayi karatu gurin lsmail,ta ce tayi masa rashin kunya ko? abdulkarim ya ce,ta yi masa kenan tunda ya ce, matsawar zata dinga zuwa gurinsa daukar karatu to kuwa zai daina koyar da yaran gidan nan.
Hajiya cikin fushi mai tsanani ta rufe MIMI da fada,ta ce,in kika sake na samu labarin kin yi sanadiyar koran malamin nan sai kin sha mamakin abinda zan yi miki,sai kin yi zaton ban sanki bama,sam bare ki tuna cewa nice na haife ki.don malamin nan ya fi min ke amfani,MIMI ta sa kuka,hajiya ta ci gaba,tunda na lura karatun ne baki so,to sai kin yishi,bari alhaji ya dawo nan zai barki sai nayi maganin abinda ke damun ki a cikin kanki. MIMI ta fada daki tana kuka. hajiya ta kira layin malam tana bashi hakuri a kan abinda MIMI tayi masa,yace babu komai ai yarinya ce. Washegari misalin shadaya da rabi alhaji ya dawo.ya iso cike tam,ya ce,a ba MIMI wayanta, amma ba a bata ba.sai dai yadda ya samu hajiya rai bace kamar ma har kuka tayi,sai kuma ya juya da tambayar shi kanta yana son jin abinda ya same ta ciki, Damuwa mai tsanani irin wanda bai taba gani a fuskarta ba,ta ce,ko kaji bazaka magance mun abinda ke damuna baya tausasa murya haba sauda yaya zaki ce haka?daga lokacin da muka zama maaurata shekara talatin da bakwai zuwa yanzu kin taba samun kanki cikin matsala ban taimaka miki ba?ta dube shi,karon na san bazaka…ya daga mata hannu dole ta dakata ya ce.amsa min kawai.
Ta ce,ban ce baka taimakamin ba alhaji,amma karon na san zai yi wuya, ya kama hannunta. matsalar kudi ce?ta ce,aa ni da yar gwal dinka ce MIMI,ta kalli fuskarsa yayi dan murmushi,ki ce abun me sauki ne,me ya faru?ta ce,ina son dai ka bar ta a nan saboda sam bata san komai kan addininta na musulunci ba. sallah har da kuka tayi,saboda allah a ce kamar MIMI shekararta nawa? amma bata yin sallah,malamin yaran nan lsmalil don ance taje ya koya mata karatu kurum, ta je tayi masa rashin mutumci. sannan ta toge tana jiran ka dawo ta ce ka kore shi.to bazan yarda ba,ita kanta ma dole ta zauna ya koya mata karatu,don baza ta koma bata yi tazama cikin jahilci, yayi shiru yana nazari. ya san dai komai za a yi bazai bar MIMI a gidan nan ba. ta ce,ai dama na san zai yi wuya ka bar MIMI nan,to ina son tunatar da kai iyaye abin tambaya ne game da kiwon da aka ba suna ‘ya’ya a ranar gobe kiyama, ta mike ta fita abinta.
Ya fito falo.hussaina tana yin home work ya ce,ke ce da MIMI ta same ni a daki na.itama cikin kuka wiwi ta cewa dady,don allah ka kori malamin nan wallahi na tsane shi.tunda nake ba a taba yi mini abinda yayi min ba.ina son in nuna mi shi talaka ba komai bane a guri na.alhaji ya ce,uwata yi shiru ki daina kuka.zauna,ta zauna a kan kujera shi kuma yana bakin gado ya ce,MIMI ina son kibar batun koran yaron nan,domin mahaifiyarki mata zo min da zancen.ta bukaci in barki a nan ki kare hutun ki,domin ta lura baki cika son ibada c,kuma nima tunda baki son yin sallah bazan amince ba, domin abin yayi yawa kenan MIMI.don gaskiya mahaifiyarki tana da hujjar cewa in barki, MIMI ta rude,dad don allah kar ka bar ni,ka san fa ba sa so na.
Ya ce,suna sonki na sani MIMI,in kin dan zauna zaku shaku ni ma ba a son raina zan barki ba.ta soma kuka wiwi tana fadin dady kawai ka ce ka daina so na,please dady kar ka barni ba zan zauna ba.ya dafa ta,shikenan naji ki yi shiru zan tafi dake,amma kin san dole sai ta bata rai ko?ta ce,dad in mun tafi zata huce,ya ce aa dole mu sunkuyar da kai mu tafi da yardar ta.ta yi shiru tana tunani,ya katse tada cewa, dole mu samu wani malami wanda zai dinga koya miki karatu,don ni maba zan so a ce ‘ya ta mai kyau kamarki,bata san komai a cikin addininta ba take wata dabara ta fado wa MIMI ta ce,dady me zai sa bazaka daukar min wannan malamin ba? ya kalle ta,ke kika ce kin tsane shi zaki ce a daukar miki shi?ta kirkiro murmushi,dady naga yanda hajiya ke son karatun shi ne.sai naga in shine zata fi saurin yarda in tafi.yayi ‘yar dariya me wayo kawai,to zan shawarce ta,amma zaki yi karatun ko?don na sanki duk abinda kika ce kin tsana,tabbas kina nufin abinda kika fada,ta ce,zan yi dady. ya girgiza kafadarta cikin jinjinawa ‘ya ta.kira min mahaifiyarkin in lallaba ta ta amince ina so ki bata hakuri a bisa laifukan da take tuhumarki, ta ce,to dady zan bata,sannan ta fita. ta sami hajiya tana jera kayanta na sawa a cikin wadirof.bayan sallamar da ta yi hajiya ta amsa ta kasa cewa komai,ita kuwa hajiya dama bata waiwayoba kuma bata fasa abinda take yiba. ta dai san MIMI ce,bayan shudewar mintunan da basu kai uku ba,sai MIMI ta soma magana cikin in’ina ta ce,emm,da mazan ce ne hajiya don allah kiyi hakuri in sha allahu ba zan sake ba.kuma zan rika yin sallah ta a kan lokaci.hajiya ta ajiye kayan dake hannunta ta dauko zata saka a cikin durowar ta zauna a bakin gado.da hannu ta kira MIMI alamun tazo,ta ce,zauna kusa dani,MIMI ta zauna.
hajiya ta tausasa murya ta kalli MIMI ta ce,ina son ki sani ba ina nuna miki kuskuren ki don wani abu bane,face don rayuwarki,
Tayi kyau,ba ina cewa ki yi sallah don ni ba ne,aa don kanki ne kiyi don allah.malamai suna fada mana cewa sallah ita ce abu ta farko da za a fara binciken aikin bawa in ya mutu.in tayi kyau ana sa ran sauran ayyukan sa zasu yi kyau.sallah ita ce abinda ta raba tsakanin musulmi da kafiri. lta ce ta raba mutum da dadda,sallah ba abin wasa ba ce,ki kiyaye.ki zubar da duk dabiun banza nan da kikeyi na yahudawa da nasara,wanda kike zaton na wayewa ne,to ina son ki sani ba wayewa ba ce,duk wata wayewa ta duniya da lahira addininmu na musulunci yazo da shi wancan kuwa da kika ka dauka bata ne,mu hausawa da mu ke da alada mai kyau wadda bata ci karo da addini ba.ina me yi miki nasiha da ki daina irin shigar ta kafirai,ki kama suturar ki ta aladarki da addininki,ki dauka ke da kowa duk daya ne,ba don allah yafi sonki ba ne ya sa ki ka fito a guri mahaifinki mai tarin arziki,ki muamakanci kowa kamar yadda addininki ya zana.
Kan MIMI kasa,kwarai ta kosa ta gama wadannan zantukan da ita sam bata ma fahimtar hajiyar.yaya ma allah yaba ta ubanta, hajiya ta ce,kar ta yi gadara?tayi dai murmushi a ranta ta ce,tab wannan ma kuskure ne,ta daga ta kalli hajiyar,dad ya ce,ki je. hajiya ta mike tsaye tare da dafa kafadar MIMI naji dadi da kika gane kuskurenki.kuma in kin canza zan nuna miki kauna irin ta ‘ya da mahaifiya, murmushi MIMI tayi,wanda ita kadai ta san maanar shi, hajiyar ta fita tare da cewa karasa jera min kayan nan cikin word durop tana fita MIMI tayi dariya irin wadda ta fi yi idan taga mugunta,a fili ta ce,ka ji hajiya wai da talaka da mai kudi wai duk daya ne,ta ina suka hadu?ai bambamcin ma a bayyane yake.ai talaka wahalalle ne bayin mu ne,ita hajiya dai kawai bata waye ba ne,take irin maganar.
shi kuma wawa sakaran malamin allah yasa ya yarda ya bini zuwa abuja, sai na taka shi,na ja shi,na tozarta shi,sai ya gane ya taba MIMI.lta kuwa hajiya da dadin rai ta fita dakin,na ta a zaton ta ‘yarta ta soma hawa hanya, Tunda har ta soma ba da hakuri,abinda bata taba yi ba a tsawon rayuwarta.watau tayi laifi ta bayar da hakur,gani ta ke yi ta kaskanta. da sallama hajiya ta shiga dakin yana zaune kan kujera,yana duba jaridar leadership.ta zauna a hannun kujerar ga ni alhaji. ya kalle ta,kin san dai tafiya zan yiki ka koma dakin kika share ni ko?ya ci gaba,ni gaskiya wannan zuwa ba samu wa maraba sosai ba kamar baya.ta yi yar dariya,sai dana ce,kar kazo da MIMI,ai amma ka ki,duk ita ce ta yi ta dama min lissafi.ya ce,to naji shikenan,ai tunda nima nayi mata fada wasa da sallah,ta daina in sha allahu, don haka ma nike so ki taimaka kiba mu aron malamin nan na yaranki tunda naji kina yabon shi gurin kwazo da jaruntar koyar da yara,in ya so sai ki samo masu wani.
hajiya ta ce,tabdi,ai ba zai yiwu ba,sai dai in a samo maku wani,ya ce.saboda me?bafa da koyarwan gidan nan kadai ya dogara ba.malami ne a makarantaru,ina zaton akwai gidajen da yake koyarwa.ka bar ta kawai ta karasa hutu a nan,na san kafin ta koma nan da wata biyu ta samu abinda ta samu.ya kama hannunta ina son ki kira shi fiye da abinda yake samu.ta ce,in har ya amince kana ganin zata yi karatun a can? Ya dan matse hannunta, kar ki damu sauda zata yi,ta ce,shikenan zan kira shi,sai dai ban so ba zai bar yara na,ni dai suna karatu sosai a gurin shi. hajiya sauda ta kira malam lsmail ta ce masa don allah in yana da lokaci yazo maigida yana son ganin shi.ko yarinyar nan ce ta kai karar shi,kuma yasan halin masu kudin nan da jarabar son yaran tsiya. ta katse mishi tunani da cewa,kar ka damu alheri ne,bari ma dai in fada maka,a takaice so yake ya dauke ka zuwa abuja saboda yarinyar nan,ka dinga koya mata karatu da kannen ta na can.don allah zan roke ka kar ka ce aa, saboda nasan zai biya ka da kyau. kuma nima zaka taimake ni.ya ce,hajiya gaskiya yarinyar nan da kyar in zata bayar da hadin kai a kan karatu,ga ayyuka na a nan.ta ce,ka dai zo din a yi magana a zaune ko?
(Zan ci gaba)…
#IP
0 comments:
Post a Comment