Blogroll

BANNER 728X90

Thursday, 29 November 2018

CANJIN RAYUWA Kashi Na 1 (Shafi 26-30) - ISMAIL SANI


CANJIN RAYUWA
[Kashi na 1]
(Shafi 26-30) Tare da - Halima K. Mashi
Post By ISMAIL SANI

Ya ce,to shikenan in na yi wanka yanzu zan taho. sai da ya bita gidan su mahamuda abokin shi,ya isa yayi sallama mahamud ya amsa tare da cewa,dan halak!sauri nake in zo gidanku yanzu,ashe kana tafe,ya ce,lafiya dai zaka zo?mahamuda ya ce,lafiya lau,takardun nan ne na manta,wanda headmaster ya baka kayi makin na dalibai.  ya ce,shaf! na manta,ko dana zo gida fa ban tuna ba.suka fito tare ya ce,in bazaka fita ba mahamud mashin dinka zan ara,zan je gidan bashir masari.mahamud ya ce,to ka sauke ni bakin kasuwa? ya ce,to ka san me zai kaini?ya ce,aa lsmail ya ce, hajiya ce ta kira ni, wai tana son in koma abuja in koyar da wannan mara kunyar da nake baka labari jiya.wai tasan zan sami kudi.
Mahamud ya ce, kawai kaje,kar ka manta da tarin bukatun ka wadanda kudi kawai suke so.lsmail ya ce,ina sane, matsalar kawai bana jin zan dauki rainin yarinyar ko da suna taka kudi.mahamud ya ce,ka dai je kaji in abin zai yiwu,amma dari bisa dari na baka goyon baya. A falon baki abdulkarim yayi wa lsmail jagora,ya shiga ya sanar da hajiya cewa ga malamin yaran nan tare da alhaji.suka jera zuwa falon bakin ya gaida su cikin mutumci da sanin ya kamata,hajiya ce ta gabatar ma malam lsmail bukatar,yayi shiru.alhaji ya ce,kar ka damu nasa kana koyarwa a gurare dabam-dabam ba da gidan na kadai ka dogara ba.ina son ka hada abinda kake samu a kowane wata ka fada min.in har zaka amince ni kuma zan ninka maka kudi abu daya dai da zan roke ka shine ka tabbatar yarinyar nan ta iya karatu. hajiya ta ce,ka dinga yi mata nasiha ka tsoratar da ita.alhaji ya daga mata hannu,wata irin tsoratarwa kuma?karatu dai ta ce, shikenan karatu ai ya hada komai.
lsmail dai yan jinsu kanshi a sunkuye lissafi yake tsakanin amincewa ko akasinta,can alhaji ya katse mishi tunani da cewa, me ka ce?ya dago ya dube shi da nufin cewa aa,sai mutuncin hajiya da kwarji ninsu ya hana shi fadin haka,sai ya bige da cewa,a bani lokaci domin sai na sanar da gidajen dani ke koyar da ‘yayansu.
Na rubuta takardan barin aiki a lslamiyyar dani ke koyarwa. alhaji ya ce,yanzu dai a takaice ka yarda kenan?lsmail ya ce,na yarda,sai dai in fara watan gobe.alhaji ya ce, shikenan,nawa kake samu duk wata?hajiya ta ce,ai sai ya je yayi lissafi ko malam lsmail?ya ce,eh! haka ne.alhaji ya ce,kana da mata ne?ya girgiza kai tare da cewa aa,ina dai nema.alhaji ya ce,to shikenan,hajiya gaki nan, za ji komai gare ki.amma kafin haka zan so in san wanene lsmail? ya dago ya kalli alhaji,hajiya ta ce,wannan kaidar shi ce in dai zai dauki mutum aiki a karkashin sa,sai ya san wani abu daga tarihinsa,ko da kadan ne.
lsmail ya ce,haka ne. lsmail bin abdulrahaman shine suna da aka fi kira na.mahaifina malam abdulrahaman ya rasu tun ina jss2,haifaffen nan katsina ne,dan kauyen ‘yargoje.amma shi yayi gidansa a nan kofar soro.hakanan mahaifiyata ta rasu wata shida bayan rasuwar mahaifina,mu biyu ne ‘ya’yanta.kasancewar tana da ciwon sikila tana shan wahala a guri haihuwa ta hakura tun daga kaina,sai aka tsaida mata,ciwon shine yayi sanadiyyar mutuwarta. kafin haka dama bata jin dadin zama da abokiyar zamanta lnna,wacce ita ce uwargida. lrin mata nan ne masu kishin tsiya,yaranta goma sha daya,kuma duk su ne manya damu,bakwai duk maza ne,sai mata hudu,kuma duk suna raye,daga cikin yaran nata, manya guda uku suna zaune a gidan yanzu haka da matansu da ‘ya’yansu. dama an raba mana gado, ni na samu daki a soro,ita kuma yata dake aure a kofar soro sai aka bata wani dan fili karami dake jikin dakina ta kofar gida.       lsmail ya dago ya kalli su hajiya,ku yi hakuri ina fada maku ba.nima ban san dalilin da zuciyata amince in sanar daku abinda bana son ina tunawa bama.hajiya ta ce, kar ka damu ci gaba.tunda na rasa iyayena haka na taso bana jin dadin kowa a gidamu,tun daga yayyina har ya zuwa mahaifiyarsu, babu mai biya min kudin makaranta. yaya amina kuwa,ita ma ba mai karfi take aure ba ga yara tana dasu har biyar.don tsakani na da ita akwai tazara ta,
Don tsakani na da ita akwai tazara ta gurin haihuwa,mijinta ne ya kai ni wajen koyon gyaran TV,da yake ina son karatu sosai,sai na mayar da hankali har na iya,da dan abinda nake samu na biya kudin makaranta.                 lslamiyya kuwa akwai mahaifin abokina malam aminu shine malaminmu na lslamiyya,shi ya dauki nauyi karatu na lslamiyyata.da ya lura ina son karatu lokacin dana kammala sakandire di nada saukar alkur’ani.
Haka kuma mahaifin mahamud shi ya tsaya min na samu shiga mutawassid wato js1 na lslamiyya tare da dansa mahamud.koda yake ya ce min makarantar tana da tsada,ta yaran masu hali ce,ya roki mai makarantar ya rage masa biyu bisa biyar na kudin. Amma fa akwai karatu,malaman kwararu ne,makarantar reshen ta yana madina.sukan bayar da tallafi ga dalibai guda uku da suka zama zakaru a matakin difloma,don yin karatun digiri a jamiar madina.wannan yasa na zage dantsen karatu bana wasa ba.duk da karancin shekaru na malam aminu shine ya sake yimin hanyar koyarwa a wani gida,saboda in dinga samun na siyan littatafai.hakanan ina koyarwa a lslamiyyar shi wanda muka yi sauka. Da wannan ne nake tallafe da rayuwata.har na kammala shekaru shida na sanawiyya,lokacin ne na samu koyarwa a nan gidan, wanda malam lsa mai makarantar mu yayi min tayi,ya ce min yaran a makarantar sa suke karatu, ‘ya’yan bashir masari ne,in zan koyar dasu.ban yin gardama ba,don ina son ci gaba da difilomata a nan makarantaarmu eh-mukhtar,yau wata biyu da kammala difiloma,ta kuma nayi nasarar zuwa na uku a ajinmu,sai dai kash makarantar daza muje a madina mutum biyu ta bukata,don haka bana ciki.sai dai ko wani lokaci zasu iya neman na uku,ina burin in karanta larabci ko kuma tafsir. amma a yanzu ina da haddar sittin,ina da haddar hadisai da dama.na san tauhidi da fikihu daidai gwargwado. Malamai da dama suna jinjina ma kwakwalwata. malam aminu mahaifin mahamuda yana yin tafsiri da azumi a babban masallacin unguwarmu,sau da yawa nine,
Malam aminu mahaifin mahamud yana yin tafsiri da azumi a babban masallacin unguwarmu,sau da yawa nine nake ja masa baki. kuma zuwa yanzu shekara ta ashirin da bakwai.              ya kalli su hajiya wadanda suka yi shiru suma saurare. ya ce,shine tarihin lsmail bin abdulrahaman. alhaji ya ce, shikenan zaka iya tafiya duk yadda kuka yi zanji gurin hajiya.kuwa tausayin lsmail ya cika ta,ta ce,zan iya tambayarka? ya ce,eh zaki iya.ta ce a fannin boko fa,daga sakandire ka tsaya? ya ce,eh,amma yanzu na zana jamb domin karanta zama ban samu wancan damar ba.hajiya ta ce, ALLAH ya taimaka ya bayar da saa,zan baka ‘yar shawara ka dinga ziyartan malamai don neman karin ilimi,ya ce,ina zuwa hajiya, duk asubahi ina daukar karatu.ta ce,ALLAH ya taimaka Alhaji ya ciro kudi daga aljuhunsa ya mika masa,ga shi ka hau mota.ya ce,ba komai alhaji da mashin nazo ka barshi,hajiya ta ce,ka amsa sai ka sha mai. sai na ganka,ka sanar dasu. ya amsa tare da yin godiya suka yi sallam.lsmail ya buga mashin kai tsaye gidan su mahamud ya nufa don ya kai masa mashin dinsa.kuma ya gana da mahaifin mahamud,su kuma sake tataunawa a kan batun tafiyarsa abuja.cikin saa yana tsayawa mahamud yana fitowa cikin faraa,suka nufi juna lsmail ya ce,sai ka ce dama kana jiran isowa ta?mahamud ya ce,wai inna ke son alayyahu,duk ga yaran sun tafi islamiyya,suka yi musabaha tare da gaisawa,lsmail ya ce,to hau muje a mashin mana muje mu amso mata,sai da suka je suka dawo suka zauna a dakalin kofar gidan.
lsmail ya kalli mahamud,ka san cewa na kasa samun natsuwa da batun zuwa abujan nan?ga shi naje da nufin ince aa ba zanyi ba, amma ban san kadarar data sana amsa ba.duk sai suka yi min kwarjini na kasa kin amincewa. mahamud ya ce,in ka ce haka ka ban mamaki,kai dana sani dakakke mara tsoro,naga ko a nan a lslamiyya da muke koyarwa duk yaran masu da shi din ne,amma shakkar ka sauke yi lsmail ya ce,baza ka gane ba,ita fa yarinyar ina zaton irin Tabararrun nan ne ko da ban sani ba dai,amma na ga alamar kamar uban bai so a takura mata,ga ta da alamun ta tsani talaka bata dauke shi wani abu ba,ni kuma duk sun san hali na,bana son raini.shi yasa bana raina mutane,dalili kenan dana keta tunanin ya ya koyarwar tamu zata kasance? mahamud ya ce, shawarata a nan kawai ka aje duk wani waswasi kai dai ka amshi kudinka ka cika burinka. ka tuna da karatun da muke son yi,kai ko yau jamiar madina suka kira kaza ka bukaci kudi.ga yarinyar nan daka dauki son duniya ka dora mata, zainaba,kar ka manta da abinda mahaifiyarta ta ce,sadakin ‘yarta dubu dari, akwatin ‘yarta me shida ne,lsmail ya ce,da na tuna abubuwan nike jin cewa ya kamata in jajirce in je,yanzu dai malam nake son gani in nemi shawararsa. da ya amince zan kara samun kwarin gwiwa.haka kuwa yana unguwar har aka yi lshai, lokacin ne lsmail ya samu magana da malam,yayi masa bayanin komai,malam ya bashi goyon baya tare da karfafa masa gwiwa, cikin farin ciki ya nufi gidasu     dakinsa da ke soro ya bude ya shiga ya kunna wuta haske ya gauraye dakin,ya zauna bakin katifarsa ya cire hularsa da agogo tare kuma da wayarsa ya dora a teburin da ke gefen katifar mai dauke da tarin littafai,ya ciro kudin da alhaji ya ba shi,da ma ya ba mahamud dari biyar daga ciki.ya dauko wani littafi wanda a cikinsa ya ke ajiyar kudi ya dora su a kan kudin da yake ciki,ya mayar da su ya rufe,ya mayar dashi a mazauninsa.ya dan kwanta rigin-gine gurin zainaba yake son zuwa don zuciyarsa ta matsu da son ganinta,amma yana jin jikinsa ya gaji.wayarsa ta soma ruri,yana daukowa ya ga hajiya ce. Ya daga tare da sallama ta amsa ya gaida ta.ta ce, ka yi hakuri na kira ka cikin dare.ya ce,ba komai hajiya. ni mana so in kira ki,sai naga bari dai in bari sai da safe.ta ce daman na kira kane in sanar da kai cewa alhaji sun tafi dazun da mimi,ina son don mu karkare maganar ina son in sanar da shi.ka fada min albashinka,yaushe kuma za a kai,
(Zan ci gaba)..

IP


0 comments:

Post a Comment