Tuesday, 4 December 2018
Home »
Kuskurena Complete
» Kuskurena Page 1 - ISMAIL SANI
Kuskurena Page 1 - ISMAIL SANI
❣🤦🏻♂ _*KUSKURENA*_❣🤦🏻♀
```{The story is Interesting! Attractive! Impressive! to cut a long story the story is a fascinating story the readers will entertain and enjoy it.} ```
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
***************************************
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
_*BY*_
©, _*RAMLERT Y SALIS*_
_*(FIRRAM /NAZRA)*_
~08164530838✍🏻~
_Mon , Dec 3 , 2018._
_*Page 1......*_
_HALL_ d'in cike yake damk'am da da mutane, ko ina ka kalla al'umma ne zazzaune da alamun ba'a fara gabatar da occasion d'inba.
_Nima a dai_dai lokacin nasamu isowa k'ofar babban d'akin taron, agogon dake hannuna na duba 7:25 am, hakan ya tabbatarmin saura 5 minutes afara gabatar da occasion d'in, wani security ne ya dakatar dani dacewa "madam can i see your get pass " ? Ina k'ok'arin manna siririn glasses a ido na d'ago na kalli security nace " I don't have a get pass but i am from *Muslim Sisters Organization of nigeria (m.s.o)* na k'arasa fad'ar haka ina me nunamasa wata sheda dake manne ajikin mayafin danayi roling kaina dashi , cikin kulawa securityn yace" you highly welcome madam please your name before you enter and your phone number and email address if available" ? okay RAMLERT Y SALIS is my name my no is 081…… , thank you ya fad'a sannan na doshi k'ofar shiga hall d'in kafin na k'arasa k'ofar ta bud'e ina shiga ta koma ta rufe_
Babban d'akin tarone ya tsaru iya tsaruwa hall d'in babbane na gaban kwatance, wannan shine karona na farko dana ta6a halartar _Transcorp Hilton Hotel_ duk iya tunanina baza'a samu wajen taro me kyau da tsari haka a nigeria ba ammah dana tuna _Transcorp Hilton_ shine babban hotel a duk nigeria sai na dena mamaki but the place is interesting is nice place.
Kowa ka gani acikin hall d'in yayi shiga irin ta Alfarma wayancin mutanan danake kallo sunsa too expensive clothes hakan ya tabbatarmin _the occasion is noble and significant_, mutanen dake d'akin taron sun had'a da manya_manya 'yan siyasa matansu da maza ma aikatan gidan radio da TV ga manyan 'yan jaridu da sauran manyan mutane , waje nasamu na zauna banfi mintuna 2 da zama ba sautin speaker ya fara tashi.
_AYANZU NE NIKUMA MARUBUCIYARKI ZAN FARA KAWO MUKU RAHOTO, HAR IZUWA K'ARSHEN LITTAFINA NA *KUSKURENA* ASHA KARATU LPY_
Matashi ne baxai wuce shekaru 35 ba sanye yake cikin black court, daganinsa kaga wanda ya gama jika acikin hutu a hankali yake magana cikin speaker d'in.
"Assalamu Alaikum Warahamatullahi Wabarakatuhu, muna k'ara godewa Allah da ni'imarsa har ya kawomu wannan rana me tarin daraja da tarihi, Aminci ya k'ara tabbata ga Annabi (s a w)da dukkan iyalansa da sahabbansa da dukkan wanda ya bada gaskiya da ranar lahira ameen, godiya ta musamman game girma _Governor_ da muk'arrabansa , 'yan majalissu da mutananu, Abonka aiki da sauran al'ummar dasukaxo dan tayamu murna".
Sai yayi shuru na d'an wani lokaci sannan ya d'ora dacewa"At the first place _JAFAR MUHD_ is my name I am the best friend of groom _SAFRAZ HASHIM MUHD_, We are waiting for our groom and his bride along side with his _first lady_ keep waiting please.
Rufe bakinsa keda wuya, hayaniya ta d'an fara shigowa hall d'in daga wata k'ofa dake can watakusurwa a hall d'in hakan ya tabbatar ango yasamu isowa tare da amarya da kuma first lady kamar yadda jafar ya fad'a.
Baka ganin komai sai haske cemara dake ta haskawa nanfa masu video suka fara aikinsu da masu hotuna da 'yan jaridu da sauransu.
Su uku suka jero sun sashi a tsakiya, daka ganshi zaka tabbatar shine angon kallo d'aya zaka masa kace balarabe ne haduwa kam ya gama ya k'are kamar shi yayi kansa dan kyau _SAFRAZ_ yana da tsayi ammah ba can sosai ba ba siriri bane kuma bashi da jiki fari ne tas yana da manyan danuwa da dogon hanci da k'aramin baki, sajensa ya kwanta a fuskarsa tamkar gashin jararin da aka haifa yau se jajayen la6ensa dasuma dace da fuskarsa, let stop describing , nasan me karatu you already visualize, to see him in your eyes mind.
Amarya ce a gefensa na hagu tayi shiga cikin tsadaddun kaya sai walkiya takeyi, siririyace tana da tsaya medium, chocolate colour ce sai dai daganin fatanta ta gaki da hutu da jin dad'i, tana da doguwar fuska da matsakaicin hanci da baki medium eyes fuskarta tasha kwalliya, Sai wacce ke gefensa na dama da alamun matarsa ce domin yana sak'ale da hannunta kallo d'aya zaka mata kaga tayima masifar kyau, kwarjini, da burgewa, mace ce ajin farko ko mace 'yar 'uwarta idan ta kalleta sai ta k'ara balle kuma ace namiji , komai nata idan ka kalla zai burgeka farace ammah ba fari irin tas ba dan mijin ta ya fita fari , ba siririya bace kuma bata da k'iba tana da dara_daran idanuwa da dogon hanci bakinta d'an dai_dai le6enta bak'ine sai gashi daya kwanta a gaban goshinta tanada diri sosai.
Inda aka tanada dan zaman ango da amarya nansuka nufa, ammah sai dai kujeru guda buyune awajen na alfarma ganin hk yasa _IZZATU_ ta fara kwace hannunta dg hannun mijin nata dan tasan kujeru biyun data gani nashine shida amaryarsa babu ita a lissafin, shima safraz ya gane abinda matar tasa izzatu take nufi ammah sai yayi kamar be fahimta ba yakuma rik'e hannunta sosai ta yadda bazata iya kwacewa ba.
Sam ranta baiso ta karasa wurin zaman ba ammah hk ta bisu suka isa ga mazaunin nasu, Amarya _KARIMA_ inda aka tanada dan ita tasamu ta zauna zuciyata a cunkushe ranta sai tafasa yakeyi ganin yadda safraz yake wani mannewa matarsa kuma wai agurin shagalin bikinta bata k'ara jin 6acin raiba sai data ga safraz yana tayiwa izzatu magiya dan Allah ta zauna itakuma izzatu ganin yadda ya marairaice mt kuma gashi people duk su suke kallo sai ta zauna ammah ba dan ranta yasoba tana zama kuwa shima ya zauna karima jitayi kamar tasa hannu aka tayi ihu ganin sun zauna a kujera d'aya wanda ango kawai aka tanadarwa.
Ina !anan hall d'in ya d'auka wasu na dariya da shewa wasu kuwa ransu a 6ace suna ganin abinda angon yayi bai daceba.
Jafar da yake shine minister of the occasion yana dg inda yake yana kallonsu ko kad'an abokinnasa bai bashi aushinba saima burgesa da yayi, sai da hall d'in ya lafa sannan jafar ya fara mgn kamar hk" Alhamdulillahi kamar yadda muka riga muka gani ango da amarya sun iso tare da first lady ayanxu ne km zamu fr gabatar da wannan taro namu God willing, so, batare da 6ata lokaci our first presenter itace hajiya km malama izzatu wato first lady uwargida awajen ango, idan me girma uwargida ga ango ta shirya muna sauraronta"
Cikin mamaki izzatu take sauraron abinda jafar yake cewa, safraz ta kalla sannan tace" Besty why do that to me ?ni mezance idan na tashi ?hb besty nasan wannan plan d'in duk naka ne u have nothing to say ni gaskiya" ta karasa maganar kamar zatayi kwalla, murmushi safraz yayi sannan yace" hb reality don't say that pls kina da abinda fad'amana sosai i am your one and only pa inason kije ki tabbatarwa jama'an dake hall d'innan bawai mijinki ya k'ara aure bane dan by sonki ke har yanxu sabuwace a gurinsa sauran mt suyi koyi dake my queen " ya k'arasa mgnr yana d'anyin dariya izzatu dataji ya fr irin wad'annan zancen nasa sai ta galla ms harara ta mik'e a hankali ta fara tafiya, karima da tn jin duk abinda suke cewa ta ta6e baki duk haushi ya isheta.
Taku takeyi cikin nutsuwa fuskarta d'auke da fara'a kowa ya maida hankalinsa kanta wasu na mamaki ganin yadda fuskarta ta nuna kamar tana cikin farinciki sosai batayi kama da wacce akeyi kishiya ba.
Tana isa wajen jafar ya bata abin mgn shima yasamu waje ya zauna, sai data dai_dai ta tsayuwarta sannan ta fr mgn kamar hk-
‘Alhamdulillahi ala kulli halin, I am Izzatu Abubakar the wife of safraz hashim muhd groom of today, okay before i begin let me greet you like am suppose to do so may peace be upon you, Ina yiwa dukkan bak'inmu barka da zuwa muna godiya sosai da sosai dan zuwa tayamu murna a wannan rana me,matukar daraja ’ sai tayi shuru na d'an wani lokaci sannan tacigaba da cewa-
" 'Y ar fad'akarwar da zanyi zuwa ga amarya zanyi, 1 _Kiji tsoron Allah a zamanta kewarku Allah zai sanya miki mafita a dukkan lamuranki._!
2 _Aure ibadane kisani cewa zaki iya ji ko ganin abinda rai baya so, don hk kiyi hakuri sai ki sami aljannarki cikin sauki.!_
3 _Hak'uri da juriya, rayuwar aure bata wata d'aya bace ko shekara d'aya ko goma ba, rayuwace ta har abada sai da hakuri da juriya.!_
4 _Miji shugabane a gareki, dan hk duk abinda yake buk'ata akowane lokaci dole ki aikatashi muddin ba sa6on Allah bane._!
5 _Nisantar abinda miji yake k'i, dukkan abinda mijinki bayaso ki nisanceshi domin yawan sa6awa miji zai jawo miki tsana._!
6 _Yin abinda miji yakeso, ki kula da da dukkan abinda mijinki yakeso, ki aikatashi koda zaki wahala wajen aikatawa domin wannan shi zaisa mijinki ya k'ara sonki da k'aunarki, kuma ki sani aljannarki tn k'ark'ashin duga_dugan mijinki, ma'ana yin biyayya agaresa zai shigar dake aljannah.!_
7 _Yin taka tsan_tsan da shawarwarin k'awaye, ki kula da dukkan shawara da ko wacce k'awa zt baki, ki za6i mace mai ilimi kuma ma'abociya addini a matsayin abokiyar shawararki.!_
8 _Rik'e sirrinki, kada ki dinga yadda wani yana sanin sirrinki tsakaninki da mijinki koda kuwa 'yan'uwankine.!_
9 _Kyautata zamantakewaki da 'yan'uwan mijinki kiyi iya k'ok'arinki dan ganin kin kyautatawa iyayensa, yayyensa k'anansa, da sauran danginsa.!_
10 _Gaskiya da rik'on amana , kiyiwa zamantakewarki ado da yin gaskiyaduk abinda zakiyi kiyi gaskiya km ki rik'e amanar mijinki.!_"
_HALL_ d'inne ya d'au tafi wasu kuma suna kabbara, izzatu ta burge mt da sama a wajen harma da mazan gurin shikuma safraz sai murmushi yakeyi ganin yadda jama'a ke jinjinawa matarsa amarya karima kuwa jikinta yayi sanyi sosai ganin babu wanda yata6a yimata nasiha ta gaskiya km me ratsa jiki irin izzatu wai kuma kishiyartace sai taji ta burgeta sosai ammah sai wani 6arin na zuciyarta ya ce mt ay kawai izzatu ty hkne dan kawai ta burge mutane ayi zaton ko dan Allah tayi.
Sai da hall d'in ya d'an saurara sannan izzatu tacigaba dacewa -
" Yake amarya ki bud'e kunnanki sosai ki jini ki kiyaye wad'annan Abubuwan da zan fadamiki su yanxu guda goma domin suna daga cikin _SUNNONIN AURE_ Idan har kika kiyaye su zaki zm 'yar auta agurin mijinki‘’
_NA D'AYA_……...
~Sannu _sannu kwana nesa muje zuwa page na 2 yau da gobe bata bar komai ba~👌🏻
0 comments:
Post a Comment