Blogroll

BANNER 728X90

Friday, 30 November 2018

CANJIN RAYUWA Kashi Na 1 (Shafi 31-35) - ISMAIL SANI


CANJIN RAYUWA
[Kashi na 1]
(Shafi 31-35) Tare da - Halima K. Mashi
Post By ISMAIL SANI

Yaushe kuma za a kai ka abujan? saboda ku soma karatun da wuri.lsmail ya gyara zama,hajiya batun albashi dai ni ba zan iya cewa ga shi ba,ta ce yauwa ni ma bana son ka ce ma shi kaza ne. Don alhaji in mutum yana son ya ce moriyar shi to ya biyo shi ta haka,zan fada mishi cewa ka ce duk abinda ya ga yayi,na san zai nemi shawarata.ni kuma na san abinda zan ce masa labarinka daka bamu a jiya na tausaya maka, kuma na tabbatar kana bukatar taimako,yanzu ka yi magana da malamin naku?ya ce,eh?gobe zan je gidajen da nake koyarwa in sanar da su.ko zuwa jibi sai mu tafi abuja din.ta ce shikenan lsmail sai ka zo jibin,ya ce to na gode, hajiya ta ce ba komai.           sun yi sallama hajiya tana ji a zuciyarta lsmail tamkar danta.washegari kamar yadda ya alkawarta ya sanar da duk wanda ya kamata cewa,gobe zai yi tafiya zuwa abuja,ya sanar dasu zainaba kadai ta rage masa ya je su yi sallama.

Da yamma laasar ya shirya zuwa gurin mahamud don ya raka shi zuwa gurin abar son sa,su yi sallama.yana isa lslamiyyar da suke koyarwa ya samu mahamud ya fito daga ajin da yake.bayan sun gaisa lsmail ya ce mu je ka raka ni gidan su zainab in duba ta da jiki,daga nan in yi sallama da ita.ko ta zo lslamiyya?mahamud ya bata fuska,gaskiya lsmail ka je kawai.ka ga ba a ma ta shi ba.ya ce amma ka fito ajin ai,wai me yasa ne ko yaushe idan na ce muje gidan su zainab sai ka be min aa?yau dai dolenka mu je,kuma gurin ka zanbar amanar ta. 

mahamud ya ce,mu je dai, amma ba ruwa na da wata batun amana. Suka jera a hanya ya kalli mahamud,ban san me yasa kuke jin haushin yarinyar nan ba.haka yaya amina kullun sai ta yi min korafi. mahamud ya ce,ai ban boye maka dalilin ba.yarinyar tana da karancin tarbiya,sannan ‘yar mace ce.ga shi uwar ta dora dogon buri a kanta. lsmail ya ce in fadi maka ni ba wata matsala ba ce a guri na.ni dai ina sonta don allah ita ma tana so na. ln ta zo hannu na ba sai yadda na yi da ita ba? mahamud ya ce,haka kake fada.
Mahamud ya ce, haka kake fada.suna isa kofar gidan suka aiki wani yaro ya kira ta.ya fito ya ce an aike ta,lsmail ya ce jikin yayi sauki kenan,ya kalli yaron,je ka ce nesa ne ta je,ko kusa ne mu jira ta?yaron ya koma,lsmail ya kalli mahamud,in nesa ne sai mu tafi mu dawo da daddare.mahamud ya ce ka dawo dai ni kan bazan zo ba.yaro ya iso tare da cewa da nisa,suna juyawa da niyyar tafiya. Sai ga ta dauke da tire goro,ta tsaya cikin daburcewa irin ta marasa gaskiya. sam ba ta tsammaci zuwan su ba.don bai cika zuwa da yamma ba. ran mahamud ya yi matukar baci.duk da irin yarjejeniyar da muka yi?da ma karya ne lafiyarki lau,ki ka dain zuwa lslamiyya? zainab cikin in-ina ta ce, dama gidan wata tsohuwa kadai na kai, amma bana zuwa talla. ya ce,karya kike yi,in mutum daya zaki kaima wa,ya ya baki sa a leda ba?sai ki dora tire a kai,bayan kuma na fada miki babu abinda nafi tsana irin in ganki da wannan tiren a kai.

kuma na fada na sake fada,bana son talla.kun dora min dari uku kullum, na yarda,kuma ina baku,shine zaki munafunce ni?ta sassauta murya ta ce,ka yi hakuri,ya ce,ke malama ba wani hakuri jeki yi min sallama da innarki,don bazan tafi in bar baya da kura ba.ta nufi ciki tsaki mahamud yayi,ya ce kalli irin gidan daza ka nemi aure. a ce uwar daza tayi wa yayanka tarbiya?wai kyan take birge ka ko me? lsmail ya ce,don ALLAH mahamud ka bar ni in ji da abu daya.kalli wulakancin, sama da wata takwas duk sati biyu sai naba su dubu biyu da dari daya ko dari uku.ko da ba zan ci ba, ba zan sha ba,sai na basu kudin nan.don kawai ta daina talla,ashe suna nan suna yaudara ta ne. Mahamud ya be duk kai ka so,yaran mata gasu nan a fadin garin katsina masu tarbiyya da ilimi,ka kau da kai a gurin su,na san dai ka san cewa,in ba nema wa ‘ya’ya uwa ta gari.lsmail ya ce,baza ka gane ba,ina yiwa yarinyar wani mugun so ne,ba zan iya rabuwa da ita ba.mahamud ya daga kafadunsa guda biyu tare da fadin ruwan ka.
Daidai lokacin zainab ta sake fitowa ta ce, shigo daga soro,nan suka tsugunguna.lta ma innar ta tsuguna.suka gaishe ta,lsmail ya soma magana cikin fushi,inna nazo ne nayi wa zainab sallam zan tafi abuja.sai kuma na ganta da tiren goro,bayan na san mun jima da wuce maganar talla.eh.nina ce ta zaga da goro tunda tun shekaranjiya ya kamata ka aiko da kudin amma shiru. lsmail ya sake shakar takaici,ciki sauri ya ce,amma inna ko na sati biyu na tara ina badawa ko? ya ci gaba gaskiya bai kamata a saba mun kaida ba.inna in na bar gari sai yaya kenan,bai da be fa a saba mun alkawari ba. lnna ta dago ta dube shi, aikin gwamnati ka samu a can abujan?ya dube ta,ya sunkuyar da kai ya ce,aa koyarwa ce.ta ja tsaki ta ce,ana nan dai.ta mike ya ce,inna zan bata kudin ta kawo,ni dai roko na kada ta dinga daukar tallar nan. ina hijaban dana dinka mata ne,yau na ganta da gyale? Ta daga masa hannu,dakata kai lsmail,ba fa ka bada sadakin zainab bane daza kayi ta sa mani dokoki iri-iri a kan ‘yata,kuma bazan gaji da fada maka cewa ba zan bayar da ‘yata inda zata sha wuya ba,kamar yadda ni na sha wahalar talaucin ubansu.’yata tana da kyau, baza maida ta baya ba. lsmail ya mike shi dama mahamud tuni ya kai waje. ranshi ful takaici,zuciyarsa tana tafasa. Zainab dake cikin gida kusa da soro ta leko cikin damuwa ta ce,innarmu don ALLAH ki daina wannan zancen,wai ke kullum in zaki yi magana sai kin sako babanmu?lsmail yasa hannu cikin aljihu,zainab zo in baki sako,innar ta koma cikin gida.zainab ta kalle shi,malama don allah kayi hakuri,ya ce,zainab ni dai rokon da zan miki,don ALLAH ki rike min amana. Ya sake yin kasa da murya,kin dai san ina sonki ko?ta kalle shi da manyan idanunta na sani malam.to ki kula min da kanki,yasa hannu cikin aljihu ya ciro dubu uku,ki cire kudin sati, sai ki rike saura.in na dawo zan saya miki waya saboda mu rinka gaisawa, zan turo iyayena.ta ce,to nima zan fi son ka turo din,don allah kayi kokari ka dan yi kudi ko.

Da ba masu yawa bane,saboda innarmu ta daina yi maka haka. Ya ce,kar ki damu shi arziki na allah ne yana bayar da shi ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so.muna rokon shi ya bamu na halas,ta ce amin.yawwa a gidanku wace ce fatu? ya ce,me ya faru? ya tattara hankalinsa gurinta,sun hadu ne a gidan wani biki can kofar marusa,shine take cewa innarmu wai kar ta yadda ka aure ni,wai wuya zan sha baka da komai,sai dan daki daya daka gada a zaure.baka da aiki, sai kalallahu,kala rasulu. lsmail ya lunshe ido na dan lokaci, ya bude tare da furzar da huci mai zafi.ya ce,zainab don ALLAH ki toshe kunnuwanki,wadannan abubuwan duk kafin in mallake ki ne.da zarar kin zama mata ta,dole kowa ya zura mana ido.ta ce to shikenan amma wace ce fatu din?ya ce,matar wa na ce,kar ya dame ki,ni zan tafi ta ce to shikenan. sai yaushe? ya ce,sai dai na zo, don sai naje naga yanayin gurin,har ya kai bakin kofa ta ce,malam don allah kar ka manta ka samo kudin. bai iya cewa komai ba.ta shiga cikin gida shi kuma ya je ya samu mahamud suka wuce.mahamud ya kasa yin shiru,suna tafe ya ce, lsmail don ALLAH dubi irin wulakancin,don ALLAH ka yi zuciya ka bar mata yarinyar ta. lsmail ya ce,hmm ka san na sha yunkurin yin haka,amma sai in samu kaina cikin tashin hankali,ban san lokacin da na soma son ta ba.ka yi hakuri mahamud ban ki batunka ba,abin ya wuce duk yanda kake tunani.kai dai ka gode ma ALLAH tun da baka da matsala da iyayen rabia. mahamud ya ce,ko da ina da matsala da su bazan dauki haka ba,sai in bar su da yarsu. kaima ina mamakin duk zuciyar da kake da ita,ya dafa mahamud kar kaji komai,ka sa ni cikin adduarka. mahamud ya ce,ka binciki asalinsu?lsmail ya ce, yaya amina ce ta binciko,ranar take gayamin wai ubansu bakano ne.dan wani kauye wai shi kurje keya.ita kuma uwar ‘yar ruma ce,can wajen safana.ya auro ta lokacin yana da abin hannunsa.’ya’yansu shida maza uku mata uku,maza ne manya mata kuwa zainb ce babba,tunda arzikinsa ya karye sai buga-buga sai ta raina shi.
Sai ta raina shi, ‘ya’yan ma suka raina shi,sai abinda ta ce.ta dauki dogon buri ta dora a zainab,don kuwa ta ga yarinyar tana da kyau,ita sam ba za ta ba talaka ba.         sannan yaran babu tarbiya babu karatu sai talla.maza kuwa daga kwandasto sai kwasan bola,sai karamin su mai sayar da rake.ka ji bayanin da yaya amina ta yi min. mahamud ya ce,tabdijan kuma ka ji ka gani?lsmail ya ce,to yaya zan yi?ba ni da zabin da ya wuce aurenta.buri na shine in ta zama tawa zan tsaya mata ta yi karatu duka biyu.mahamud ya ce,ALLAH ya taimake ka. bayan sallar lsha suka yi sallama da mahamud kan cewa sai gobe in sun hadu, kafin lsmail din ya tafi gida, gidan yaya amina ya nufa, a tsakar gida ya same su ita da yara suna cin abinci. nan yaran suka shiga yi masa sannu da zuwa.ya ciro naira dari ya ba sadam babban,je ka sayo maku biskit,ya ruga da gudu yana murna,yaya amina ta ce,ba ka gajiya ne?haba dai.ta ce aisha dauko ma kawunku tabarma.bayan sun gaisa sai yake sanar da ita batun tafiyarsa abuja.ta ce, gaskiya na yi murna.ALLAH ya sa alheri ne ya kira ka abujan.lsmail ya ce,amin yaya ina son in na dawo in tura gidan su zainab.yaya ta ce,umm!kai dai kana son wannan zainb din yayi dan murmushi,ku taya ni da addua ALLAH ya sa haka shine mafi alhari.ta ce.umm to amin,sun jima suna hira sannan suka yi bankwana ya tafi.yana shiga gida ya kunna wayarsa ya shiga soro su ya ciro makulli dakin ya bude.ya dubi makunnin wutar ya kunna haske ya wadace dakin ya shiga.ya dauki buta ya fita zuwa cikin gida don zagawa ban daki.a tsakiyar gidan matan yayyin sa ne da ‘ya’yansu suke ta hira,ya yi sallama suka amsa yayi masu sannunku ya wuce.don shi dama tsakaninsu bai wuce haka ba,sai da ya fito bandakin sannan ya nufi dakin inna,ya yi sallama tana ta gyangyadi.sallamar shi ce ta tashe ta,ya shiga ya gaida ta,ta amsa tare da cewa kananan?ya ce eh na shigo da safe ki na bandaki. ta ce,haka dai ka ce,indai nina haife ka ai don ina bandaki ka jira ni.yayi dan murmushi,

Zuwa yanzun ya saba da halin inna.ya daina jin haushin maganganun da take fada masa marasa dadi.dama zan sanar da ke ne gobe in ALLAH ya kaimu  zan tafi abuja.ta ce habuja?kai ko me zaka yi a habuja?ya ce,koyarwa na samu a wani gida zan dinga koyar da yaran gidan    ta tashi tsaye,can kuma ka kutsa,lallai ba shakka,ya mike,ya jima da sanin inna zai yi wuya tayi masa adduar ALLAH ya sa alheri. ya fito yasa takalmi tare da daukar butarsa. Tun kafin ya bar tsakar gida yana jinta tana cewa kunji mutan gidan nan,samail ya samu koyarwa a habuja,ya fadawa mazajenku?fatu ce ta soma magana,lallai ba shakka,ya fadawa mazajenmu su a su wa?ke ma don kar a ce dai bai fada bane,kala bai ce ba ya wuce dakinsa. Da safe sai da ya shirya tsaf,sannan yayi wa yayyansa maza sallama,su kam sun yi masa ALLAH ya sa a dace.gidan su mahamud ya nufa.yayi sallama da malam aminu mahaifin mahamud sannan suka nufi gidan hajiya sauda.mahamud ya goya shi a mashin,kuma sun yi shawara a kan mahamud zai ci gaba da koyar da su hussaina.
A waya ya kira hajiya ya fadi mata ya iso,ta sa ya shigo,kar ya damu ai shima tamkar shi dan gida ne.suka shigo falon baki nan ta same su,ya gabatar mata da mahamud,bayan sun gaisa ta kuma kara rokonsa a kan ya tsaya mata sosai a kan MIMI,duk lokacin data yi yunkuri ko barazanar koran shi,to ya kira ta.ta ce nasan aiki ne na baka mai wahala,amma kamar jihadi ne,ya ce,na yi miki alkawarin zan tsaya a kanta kamar kanwa ta,zan jure saboda ALLAH da kuma halaccin da ki kai mun.ya’u direba ne zai kai shi,sai da motar ta tashi sannan mahamud ya buga mashin cikin kewa.suna tafe suna labari shi da ya’u cewa yayi,gaskiya ina yi maka jajena kan wannan aiki,gara in yi aikin kwasar kashi don na tsani wulakanci,lsmail ya ce,hmm ni fa gani nake kamar wata kaddar tasa zan je koyar da yarinyar nan. Wata zuciya kuma tana fada mini ALLAH zai taimake ka.ina tunawa ni NAMIJI ne,sai inga to wai meye ne abin tsoro.

(Zan ci gaba)…


#IP


0 comments:

Post a Comment