Blogroll

BANNER 728X90

Thursday, 6 December 2018

Kuskurena Page 3 - ISMAIL SANI


❣🤦🏻‍♂ _*KUSKURENA*_❣🤦🏻‍♀
 
```{The story is Interesting! Attractive! Impressive! to cut a long story the story is a fascinating story the readers will entertain and enjoy it.}  ```


❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
***************************************
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣



               _*BY*_

 ©, _*RAMLERT Y SALIS*_
          _*(NAZRA /FIRRAM )*_
           ~08164530838~✍🏻


_Thu , Des 6 ,2018._

_*Page  3......*_




Wani  shocked jikina yayi na ware ido ina kallo izzatu wacce itama ni take kallo, na razana da jin abinda ta fad'a taya hkn zata faru bayan yadda safraz ke nuna son izzatu a gaban kowa.

Izzatu tace, kamar yadda kika sani munyi graduated on 2008, na fr university on 2009  ina shekaran k'arshe befi saura two month na kammala degree ba muka had'u da safraz , Aranar naje _B U K_old side, naje domin wani program da za'a gabatar a ranar domin ni a _B U K_ new side, nake attending lecture department d'inmu na Islamic studies a _B U K_new side yake idan kinga na shiga old side to ko zanje wani program da za'a gabatar a can, to aranar ma hkne domin najene wani program _GLOBAL MONEY WEEK_ wato satin kud'i na duniya, a ranar Allah yayi had'uwata da safraz.


Byan an kammala program ina cikin,tafiya tun kafin na fito dg _B U K_ sai mota ta talalace nayi duk iya k'ok'arina motan yak'i tashi ga yamma tana k'arayi ga babu me gyaran mota akusa da waje mutane kad'an kad'anne ma suke wucewa ta gurin, Ina cikin tunanin yadda zanyi sai ga wata mota tazo ta wuce har tayi nisa sai kuma ta dawo da by, Jafar ne ya bud'e motan ya fito ya iso inda nake yana murmushi, sallama yamin na amsa sannan yace,  Can i help you ng kamar your car has broke down,

Nace, hkne zan samu me gyara kuwa a nan ciki?

jafar yace, bazaki samu me gyara ba sai dai idan kin ft waje but you will suffer before you get, if there's no problem kuzo mu rage miki hanya idan yaso gobe sai kizo da me gyaran sabida yanxu dare yayi i am sure ba wanda zai ta6a miki motanki ko?ya k'arasa maganar yana d'aga mata giransa.
 Hk akayi izzatu motan su jafar ta shiga ta bar tata monta a nan, koda ta shiga safraz ta gani a zaune a matuk'in driver sai da suka fita get sannan jafar ya juyo ya kalli izzatu yace, hajiya wace unguwa ce ?
Izzatu tace, a'a babu komai ku sauk'eni  a nan tunda kunkawoni main road zan samu abin hawa sai na k'arasa.
jafar yace, no madam baxa'ayi hk ba kibarmu mu k'arasa ladanmu ki taimaka wane unguwa?

izzatu tace, kar na shiga lokacinku maybe you have something important to do.

jafar yace, karki ji komai inane?
izzatu tace, sharad'a pes 1, nagode sosai.

jafar yace, okay mune da godiya.
 Tun lokacin da izzatu ta fara mgn safraz ya tsinci kansa a wani yanayi na jin dad'in muryanta hakan yasa ya d'aga ido ya kalleta ta glass itama a dai_dai lokacin ta kalli glass gaban mutar caraf suka had'a ido, safraz ya sakar mt murmushi itama ta maida masa da martini sai kuma gabanta ya shiga fad'uwa duf!duf magar gaskiya tsabar kyawun safraz sai daya firgita izzatu shikuwa har da gyara glass d'in sosai ta yadda zai dinga kallonta da kyau, izzatu kuwa sunkuyar da kanta ty k'asa domin ta gane kallonta yake tayi. 6angaren jafar kuwa duk yaga abinda safraz yakeyi dariya taso ta kwace masa awani 6angaren km murna yakeyi dan yaga alamun yarinyar zata samu shiga agurinsafraz dan yafi kowa farinciki idan hk ta faru domin babbar burinsa shine yaga safraz yasamu yarinyar da tayi masa  yayi aure domin yammata sudena kawo masa hari ga safraz kuma baya kula yammata ammah yau dayaga sun wuce izzatu yaga safraz harda juyawa ya kalleta shiyasa yace masa su d'anyi baya.
A dai_dai k'ofar gida suka sauk'e izzatu, tayi musu godiya ta shifa gida.

Haushine ya cika jafar ganin,har sukayi sallama da izzatu safraz baiyi mt mgn ba balle ya k'ar6i number ta. hk suka tafi hanya jafar yana tayiwa safraz masifa shikuwa safraz kallon jafar yayi yana marairaice fuska yace, Ay kasan ni bansan ya akeyiba shiyasa na d'auka zakace mt wani abune shiyasa, jafar da haushi ya isheshi sai yayiwa safraz babza kamar be jisaba.
Abu kamar wasa safraz kwance kan gado ammah sam yakasa bacci, daya rufe ido izzatu yake gani hk kawai sai maganganunta su dinga dawo masa  _kar na shiga lokacinku maybe you have something important to do_. A daren dai bai samu bacci ba hk ya kwana yana tinaninta,  koda yagari ya waye suna breakfast  cokali kawai yake juyawa a flat ba abinda yake ci, ba wanda ya fahimci halin dayake ciki sai mahaifiyar bayan kowa ya kammala Abbansu yayi sallama dasu ya fita, ya rage daga safraz sai maminsu da k'annansa shahida da shahida.
Mami tace, twins maza a tafi school karku zama late comers.

A tare suka mik'e, shahid ne yace,  mami and big bro sai mun dawo.

mami tace, yauwa yaran kirki adawo lpy Allah ya taimaka.
safraz yace, pls try to study hard banda wasa sannan ku kulamin da kanku sosai and don't forget the azkar.

shahida tace, big bro shahid is too much play with his friends by karatu yanxu.

safraz yace, lah! shahid kaifa d'an albarkane gaka yaron kirki why too much playing ?

shahid ya 6ata fuska sannan yace, big bro yarinyar nan fa joking takeyima.

shahida ta kwashe da dariya sannan tayi waje shima shahid yabi bayanta already driver yana jiransu a parking lot.


Mami ta kalli safraz tace, safraz what's happening ne ng yau duk baka da walwala?
safraz yace, mami nothing gajiya ce kawsi.
mami tace, hym ay ba hk kakeyiba ko gajiyar ce to ma wai me kayi da zaka gaji ?
safraz yace, weather ce kawai mami ammah normal nake.

mami tace, baza dai kawai ka fad'amin ba if don't share your problem with me whom you share with ?i am your mother your worries  is my wworries
 Or telling me your worries will not help matters ?

safraz yayi saurin kallon mami yace, nop mami ba hk bene .
mami tace, to menene.
safraz ya tattara nutsuwarsa ya kalli mami sannan yace, dama jiyane ... ya kwashe duk yadda had'uwarsu da izzatu ya kasance ya fad'wa mami sannan yacigaba da cewa, mami shine fa too much thinking about her since yesterday i don't know ?
dariya mami ta dingayi sannan ta kalli safraz tace, wallahi safraz kacika d'an fari  yanxu baxaka iya yiwa budurwa mgn ba?
safraz sosa k'eya yayi yace, yace mami to me zance.
Dariya ta kuma yi sannan tace,  to ni yanxu koyama zanyi ko ya?
safraz yace, ehmana mami.
Mami tace to tunda kaga gidansu yanxu abinda za'ayi shine kaje kayi wanka ka sanya manyan kaya ba wai court ba, kaje gidansu idan kaje bawai ita zaka k'iranaba  a'a da mahaifinta zakayi sallama idan kuka gaisa sai kace masa kaxone idan baiyiwa 'yarsa mijin ba kanason ya baka izini ka fara zuwa gurinta, to anan zai iya yiwuwa ba ita d'aya bace 'yarsa budurwa idan yace wacce sai ka kwatanta masa ita, daga nan sai kaji me me zai cema idan ba'ayi mt mijinba to shikenan, daga baya  sai ka fr binciken halayenta dama nagarta gidansu ammah idan anyimata to sai kayi hakuri domin haramne neman aure acikin neman aure. Idan kasamu ganin yarinyar bawai ka tsaya kana yimata wannan murmushinaka ba, idan kun gaisa sai kacemata dama tun dana gankine jiya sai naga kin burgeni Allah yasa kema hkne agurinki, sai kayi shuru kaji me zata ce idan kuma tayi murmushi kawai to kaima ka burgeta, sai ka fad'amata kai manufarka akanta itace aure bawai asha soyayyah ba. To my son sauran aykin saika k'arasa inamaka fatan nasara kuma na haneka da k'arya, sannan ka kiyaye kayi tsabtatacciyar soyayyah banda romantic kaji tsoron Allah watarana kaima ubane km baxaka so ayiwa taka 'yar ba to saika kiyaye domin Annabi yace abinda kayi shi za'aymaka.

Safraz da murnansa yace, mami nagode this my mom da sauri ya matsa inda take yayi mata kiss a check d'inta duk farinciki ya cikashi ya rasa me zaiyiwa mami ya burgeta, sai kuma ya tashi kamar wanda aka tsikara da Allura ya nufi 6angarensa d'insa.

Sai daya shirya tsaf sannan ya fito a falon yakuma samun mami ammah duk sai yaji kunya ta kama sa, safraz yace, mami na tafi need your prayer.
mami tace, my son wish all the best !

mami bayansa tabi da kallo tana,murmushi, itama ta tsincin kanta acikin farinciki tana son taga safraz yayi aure sabida yana buk'tar kulawar mace ayanxu.
 Kamar yadda mami ta fad'awa safraz hk yayi,  mahaifin izzatu yayi matuk'ar  farinciki km ya k'ar6esa hannu biyu domin izzatu ita kad'ai ya haifa baya barin kowa zuwa wajenta sai akan safraz yaji ya aminta dashi bai 6ata lokaci ba ya bashi izinin zuwa wajenta har cikin gidan yashiga ya gaida mahaifiyarta dukkansu sun amshesa da mutunci.

 Mahaifin izzatu prof, Abdullah Abubakar professor ne, d'an salin jahar kano ne matarsa d'aya itace hajiya Rukayya, wato mahaifiyar izzatu, 'yarsu d'aya itace izzatu mahaifinta yana da ra'ayin 'yarsa tayi karatu akan yasa ko samari izzatu bata kulawa sai abin yaxama abin munafurci a unguwa ammah duk da hk hakan bai dami izzatu ba da iyayenta sunajin zagi iri_iri  ammah sun toshe kunansu.

  Prof Abdullahi, mutumne kamili kuma salihi bashi da abokin fad'a  ammah mutane sun samishi ido, itama hajiya rukayya bata da shige_shige irin na mata hk ma izzatu dan ko k'awa bata shi a unguwar sai dai a shchool ammah suna zaune da mak'otansu lpy, izzatu yarinya ce me nagarta sai dai akwai sa idon mutane a kanata.
Safraz da izzatu soyayyah ce ta shiga tsakaninsu me tsananin k'arfi, zakayi tunanin sun dad'e a tare jafar kusan yafi safraz son kasancewarsa da izzatu.
Ba'a d'au wani lokaci ba aka saka ranar aurensu, sai alokacin 'yan'uwa da abokan arziki suka san,da zancen.
 Safraz d'ane ga Alhaji Hashim Muhammad,  Alhaji hashim babban kusane a gwamnati ya rik'e matakai iri_iri  wanda a yanxu yana d'aua dg cikin masu nemsn takarar gwammna a kano, Mahaifiyarsa safraz  Hajiya maryam muktar babbar mace ce mai ilimi da dattko, safraz shine d'ansu na farko sai twins shahid da shahida,
Hajiya maryam tana da yayarta wacce itace ta rik'eta tun rasuwar iyayensu kuma su biyu kawai suka haifa sunanta momy Adama suna matuk'ar kama da hajiya maryam daka gansu kaga asalin fulani kyawawan asali.
momy adama tana da 'yaranta mata guda biyu karima itace babban sai sailuba.

*************************************


Momy Adama ce zaune a falon hajiya maryam dagani ranta a 6ace yake ta had'e girar sama da k'asa,
Hajiya maryam ta kalleta tace, Aunty adama nima sai da akayi komai mahaifinsa yake sanarmin sunsa ranar auren safraz wata biyu wallahi bansaniba.

Maryam tunda d'ankinne ai dole kice hk kin nunamin bani da iko akan 'ya'yanki, tun yaushe nake cemiki karima tana son safraz km na hanata kula ko wanne saurayi idan ta dawo sai su dai_daita kansu ammah kawai sai inji kwatsam wai safraz yana neman wata a can.



~Sannu_sannu kwana nesa muje zuwa page 4 yau da gobe batabar komai ba~👌🏻


0 comments:

Post a Comment