Blogroll

BANNER 728X90

Monday, 17 December 2018

Kuskurena Page 4 - ISMAIL SANI


❣🤦🏻‍♂ _*KUSKURENA*_❣🤦🏻‍♀
 
```{The story is Interesting! Attractive! Impressive! to cut a long story the story is a fascinating story the readers will entertain and enjoy it.}  ```


❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
***************************************
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣



               _*BY*_

 ©, _*RAMLERT Y SALIS*_
          _*(NAZRA /FIRRAM )*_
           ~08164530838~✍🏻



_LONG TIME ...sorry for late posting i think one week kenan banyi post ba i am very busy that's why but now, insha Allah i cameback posting on time_


_Mon, Des 17, 2018._

_*Page  4......*_


 Hajiya maryam tace, Aunty adama shi yaga yarinyar yace yanaso kinsan mahaifinsa besan da zacen ba shi kanshi safraz kwanaki dana fara yimasa zancen yaje ya nemi karima cemin yayi shifa bayason ayimasa tallar mace yafison idan ya ganta da idonsa intayi masa to, ammah Aunty bawai bawai naki karima da auren safraz bane bugu da k'ari naga karima ta fita waje karatu shiyasa da safraz yazomin da zacen yaga wata yarinya ban hanashi domin maybe alokacin yake buk'atar auren.

Cikin 6acin rai momy adama tace, Au yanzu kariman ce anyi masa talla?yarinyar da maxa ke tururuwar zuwa wajenta ammah na hana nace ni d'ana zan bawa domin zumunci ya k'ara dank'o ammah ni safraz yayiwa hk ? wallahi tallahi indai safraz yak'i amince da za6ina to kuwa zumuncinmu yana daf da rushewa ko ke maryam na isa na fad'amiki kiji balle d'anki ko kin manta ni wace agareki ?
Hajiya maryam cikin raunanniyar murya tace, Aunty adama dan Allah karkice hk yara bazasu ta6a sawa zumuncinmu ya rushe karki manta mu biyune fa tak iyayen mu suka haifa bamu da kowa sai Allah yanxu me zaisa wani k'aramin dalili ya rabamu, In dai nice na haifi safraz to wallahi insha Allah sai ya auri karima ammah inason kimin afuwa kar a rusa wannan zancen neman auren nasa kiyi hakuri yayi auren bayan karima ta kammala karatun ta sai ayi musu aure alokacin.

Wani murmushi momy adama tayi tace, Hb ai sai yanxu naji mgn ammah nasan karima batason kishiya sai dai tayi hakuri, taya zanyi na d'auki 'yata d'aya na bawa bare ammah idan safraz ne ko na mutu bani da wata matsala nasan zai rik'eta amana sabida 'yar'uwarsace.

Hajiya maryam tace hk Aunty nima bani da burin daya wuce ng zumuncinmu ya d'ore har abada.

Daga nan suka cigaba da hirarsu, ammah zuciyar hajiya maryam a cunkushe take tunani takeyi kala_kala tasan,cewa karima sam ba irin matan da safraz ke so bane bugu da k'ari bata da wata tarbiya, wannan tunanin shike damu hajiya maryam.
******************************************


A 6angaren iyayen  izzatu kuwa sunata shirye_shiryen biki, bikin 'ya d'aya tilo awajensu komai na bikin na musamman ne har zuwa kayan da suka yiwa d'iyar tasu oder wajece masu kyau da tsada.

 A yau takasance ana saura sati d'aya biki,  safraz ne zaune shida hajiya maryam.
Safraz yace, mami meyasa zakimin hk ? ni bana santa bai dace na aureta ba mami ya aza'ayi ace bayan aurena da wata biyu kuma ace sai na k'ara yin wani auren, me zancewa izzatu ?auren soyayyah zamuyi da ita fa mami banyi mata adalci ba da munyu aure wata biyu na k'ara aure zansata a zargin mutane dole mutane zasu tsammanin wata matsalace da ita shiyasa zan k'ara aure , mami ki taimakeni kujanye wannan zancen bazan iya yiwa izzatu kishiya ba.

Mami itama da ranta yake k'una tace, safraz nice na haifeka na isa na saka abu kuma kayi wallahi nima ba'a son raina,hk zata kasance ba, umarni momynku ta bani kuma wallahi safraz baxan iya tsallake umarninta ba koda zan 6atawa kowa ita zan faranta mata sabida tamin halacci a rayuwa wanda ko da uwata tana da rai iya abinda zatamin kenan, naji kuma na yarda baka son karima ammah kayi hakuri ka sharemin hawayen dan Allah ba danni ba, ta k'arasa maganar tana matse kwallar dg idonta.

 Da sauri safraz yasa hannunsa yana wiping d'in tears dg checks d'inta, shima duk hawaye ya cika idonsa yana cewa, hb mami meyasa zaki 6ata hawayenki mami duk abinda zaisaki farinciki a duniya zanyisa kinji, nothing is more  painful to me then tears in your checks my mom, mami in kince na hakuri da izzatu ma zan hakuri sai na auri karima, insha Allah zanyi dukkan abinda kika ce.

Mami murmushin k'arfin hali tayi sannan tace, thank you so much my son, your are my pride i love you so much because you love me too, Allah ya maka albarka safraz ya yayima jagoranci, bance ka hakura da izzatu ba innayi hk ban damu da farincikinka ba Allah ya bk ikon rik'esu su biyu ameen.

 Koda safraz ya koma d'akinsa komai dagule masa yayi izzatu kawai yakeji taya zai sanar da ita, besan sa'adda hawaye suka dinga bin idanuwansa ba duniya yaji duka tayimasa zafi, wani tunanine yazomasa, fita yayi ya nufi gidansu izzatu.


Yayi sa'a kuwa ya tadda baban izzatu a gida, bayan sun gaisa baban izzatu da kansa ya isar da safraz zuwa falon bak'i.
Safraz yace, Abbu ina so muyi wt mgn ne dama.

Abbu dayake niyar fita dg d'akin sai ya dawo ya zauna.

Abbu yace, safraz ina sauraronka, Dm tun daga wannan bakin naka nasan akwai mgn, ya k'arasa maganar yana dariya.

Anan safraz ta kwashe duk yadda dukayi da mami ya fad'awa Abbu dukda yadda yake matuk'ar  jin kunyarsa.

Dogon numfashi Abbu yaja sannan yace, hak'ik'a safraz ka cika d'a km ka burgeni matuk'a, ka k'ara shiga raina na k'ara yin farinciki sosai sabida nasan wa nabawa auren 'ya ta, umarnin iyaye abune me girma da km nauyin gaske ba kowa yake iya binsa ba, Ina maka addua Allah ya tayaka rik'onsu duka biyu, ina k'ara yima nisiha akan bin iyaye, sannan kuma karka fad'awa izzatu wannan mgn ko mahaifiyarta ka bari sai bayan biki domin mata akwai 'yan zuga zasu iya lalata lamarin.
Safraz yy farinciki sosai hk ya tafi yana yabawa da hali irin na mahaifin izzatu, sai alokacin hankalinsa ya kwanta sannan har zuwa time d'in yanajin a ransa bazai iya zaman aure da karima ba sai dai kawai bayason mami ta shiga damuwa.






Karima dake can k'asar England tana,karatu sam bata da labarin safraz zaiyi aure tunanin ya k'are akan da ta kammala karatu ita zai aure kamar ance ta d'auki wayarta tayi connect d'in data ta duba twitter daga nan tayi facebook sai ta koma whatsAp kuma Hankalin karima ne ya tashi alokacin ta ta fara karanta wanu posting cewa _SAFRAZ HASHIM MUHD_ d'a ga Minister ilimi na jahar kano zaiyi aure ranar sunday wanda alokacin ya rage kwana biyune kacal,  hankalinta ne ta tashi sosai ganin ko tantama babu safraz d'intane saima dataga hotunan safraz da izzatu dasuka biyo bayan sak'on alokacin numfashinta ya fr sama_sama kamar zai d'auke, cilli tayi da wayar ta fr farfasa abubuwan dake d'akin hardasu bedshit duk tabi ta yayyaga alokacin dai ta zama tamkar mahaukaciya sai data gaji dan kanta sannan ta fad'i gefe guda tana maida numpashi daga nan ta fashe da dukaka mai ban tausayi , wayan ta d'auko ta har had'a sannan ta fara neman number mahaifiyarta wato momy adama.


~Sunnu_sannu kwana nesa muje zuwa page 5 yau da gobe batabar komaiba~👌🏻


0 comments:

Post a Comment