Blogroll

BANNER 728X90

Sunday, 30 December 2018

Kuskurena Page 6 - ISMAIL SANI



❣🤦🏻‍♂ _*KUSKURENA*_❣🤦🏻‍♀
 
```{The story is Interesting! Attractive! Impressive! to cut a long story the story is a fascinating story the readers will entertain and enjoy it.}  ```


❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
***************************************
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣



               _*BY*_

 ©, _*RAMLERT Y SALIS*_
          _*(NAZRA /FIRRAM )*_ 
           ~08164530838~✍🏻


_Tue, Des 17, 2018._

_*Page  6......*_



A tsorace ta mik'e zaune, tana k'ara bin mutumin da kallo shi ba saurayiba ammah km shiba magidanci ba, a hankalin ya dinga matsowa inda take har sai data jingina da bango.



Jikin izzatu rawa ya fr yi duk da air conditioning dake d'akin ammah zufa takeyi, kamota yayi ya cillata kan kado sai alokacin ta gane nufinsa, kuka ta saki me k'arfi tana cewa ;
Dan Allah kayi hakuri, menayi ma?dan Allah karka cutar dani.

Stood ya samu ya zauna dake gefen gadon, sannan yace, mlm izzatu kwantar da hankalinki babu abinda zan miki bazan miki abinda kike tunani ba ammah fa idan kinji km kinyi abinda zan ce miki, da fari nidai nazone badan namiki fyad'e ba kamar yadda kike tsammani, akwai wani aki danazo yi ammah saikin bani had'in kai zai tafi dai_dai idan km kika k'i to wallahi zammiki abinda kikayi tsammani ammah idan kikayi zamu rabu lpy. Da fari ina wayarki ?
Jin yace bazai yi mt komai ba yasa izzatu ta d'an rage tsoronsa, a hankalin ta jawo jakarta ta ciro wayar ta mik'amasa.
Number sa yasa a wayar izzatu sai ya k'ira layinsa nan da nan kuwa wayarsa ta fr ringing  d'aga k'iran yayi tana ta tafiya zuwa kamar mintuna biyar sai ya kashe sannan sai ya cillah mata wayarta.
Izzatu batasan me yayi ba dan hk bata duba ba, ta d'auka number ta kawai ya d'auka, zuciyarta cike da tsoro addua takeyi Allah ya kawo safraz cikin gaggawa.


Mik'ewa tsaye yayi ya cire kayan jikinsa ya bari dg shi sai gajeran wando da singlet, izzatu takuma firgita sosai kuka takeyi sosai.

Tsawa ya daka mata yace; ke nace miki babu abinda zanmiki zaki dena wannan kukan ko kuwa sai na koyamiki hankalin, sai ya fr nufowa inda take.
 Hannun tasa ta toshe bakinta sabida ta kasa tsayar da kukannata, sai yaja da baya yace, karki k'ara idan km……sai ya girgiza kai.


Tsayawa yayi yana k'aremata kallo, sai ya d'aga gira yace, maganar gaskiya naji tausayinki wannan ranarkice ra farinciki ammah kuma……sai yy shuru.
yace, inason yanxu ki shiga toilet kiyi wanka.
A  tsorace izzatu ta d'ago idonta ta kallesa tana zare ido.
izzatu tace, bawan Allah kaji tausayina yau itace ranata ta farko a gidan mijina dan Allah karka 6atamin rayuwa.
yace, mlm izzatu na rantse miki da Allah babu abinda zanmiki idan har kikayi dukkan abinda zan sakaki ai ba'awasa da Allah, Allah bazan miki abinda kike tsammaniba, yana gm fad'in hk ya matsa kusa da ita ya janye mayafinta jikinta sai rawa yake tsoro cike da ranta.

Izzatu kuka yazo mata ammah sai maidashi takeyi banda karkarwa babu abinda jikinta yakeyi, d'an kwalin kanta yaja shima ya ciresa, kallonta yayi yace saura aikinki.

kallonsa takeyi tana d'aga kai, yace ko bazakiyi ?
da sauri ta girgiza kai, yace, cire zaninki ai nasan akwai siket aciki, izzatu da sauri ta dira akan gadon tayi hanyar toilet dan ta shiga ta sa key.
  Shikuma cikin hanzari ya cafko ta, tsinka mata mari yayi yace, naga abin naki wasa ne bazakiyi abinda nasakiba ko ?har sai mijinki yazo ya samemo mu ko?da kokawa ya cire dukkan kayan dake jikin izzatu duk karfinta sai daya kare wajen kwace kanta ammah ta kasa toilet ya jata ya kaita ya tufeta daga ita sai pant ne a jikinta.

Izzatu tuni ta sare duk tunaninta fyad'e zai mata, ilahirin jikinta duk ya mutu bata da wani k'arfi kukan ma ya kasa zuwa mt.

Shima bakin gadon ya samu ya zauna yana maida numfashi, Ana hk yaji shigowar mota harabar gidan ta window ya lek'a ya hango safraz ya nufo part d'in.

 Da sauri ya tashi shima ya shige toilet d'in, alokacin izzatu ta d'aura towel ajikinta, ruwa ya shashshada ajikinsa tamkar wanda ya fito dg wanka hakama izzatu ya  fincike towel d'in dg jikinta ya watsa mt ruwa dg sama har k'asa sannan ya maida mt towel d'in ba musu ta k'ar6a ta d'aura dan zuwa lokacin ta dena tsoro abin mamaki kuma yake bata meye nufinsa shine abinda bata ganeba.
Yanajin safraz ya shigo d'akin ya bud'e k'ofar yacewa izzatu ta fita.

Safraz da saurinsa ya shigo d'akin yana cewa, slm my sweet sorry for keep waiting. turus yayi ganin kayan izzatu a tsakiyar d'akin ga kuma kayan maza jens da t-shirt bai kawo komai a ransaba yace, my izzat kina ina are you in toilet ?hanyar toilet d'in ya nufa a dai_dai bakin toilet d'in yace mine na dawo kiyi hakuri kinji in shigo dear ?
Izzatu sai alokacin ta gane me mutumin nan yake nufi wato sharri yazo dan ya kulla mata ji tayi hajijiya ta kwasheta ta tafi luuuuuuu zata fad'i da sauri yasa hannayensa ya tarota a dai_dai lokacin safraz ya bud'e toilet d'in.

Tsayawa safraz yayi sororo yana binsu da kallo, idan ba mafarki yakeyi ba kamar izzatunsa yake kallo a jikin wani ?da sauri ya murza idanuwansa da gani yake tamkar ba gaskiya yake gani ba, shikuwa mutumin shima da sauri ya saki izzatu itama cikin hanzari ta dafa bango dan tafiya tayi zata fad'i.

 Cikin d'aga murya safraz yace, Izzatu waye wannan ?wayeshi ?wayeshi nace miki har kukayi wanka tare?ya k'arasa maganar yana d'aga murya sosai.

zuwa lokacin izzatu tama rasa me zata fad'a danta kare kanta agurin safraz hawayene kawai suka fr bin idonta, dukkan su suna tsaye sai kallon kallo sukeyi.


Safraz dukan k'ofar toilet d'in yayi ya k'arasa shigowa, kafad'unta ya rik'e duka biyu yana girgizawa yana cewa;wayeshi nacemiki izzatu ?meye had'inki dashi me kukayi izzatu ?lokaci d'aya fuskar safraz ta canza idanuwansa suka juya daga fari zuwa jajazur, izzatu kuwa kuka ta fashe dashi me ban tausayi, shikuwa mutumin ko ajikinsa sema ya tsaya yana kallonsu babu alamun zai gudu ma.

Ran safraz ya kai matukar 6aci zuciyarsa tana k'una yana rayawa a ransa "wato abinda yake zargi shine ya faru kenan shiyasa ta kasa bashi amsa"

tas! tas! kakeji, safraz ne ya kwashe mutumin da maruka guda biyu, muryar safraz a shak'e ya kalli mutumin sama da k'asa yace, me ya kawo cikin gidana?meye had'inka da matata ta sunna ?kai waye ?safraz ya dungule hannu zai naushi mutum sai mutumin ya rik'e hannun safraz da sauri yace, kai malam dakata ! , meyasa zakaga laifina dan ka ganni a gidanka gidanka d'in banza, nafi k'arfin inbi matarka sai dai ta bini, ko zanzo gidanka mezaisa nazo a ranar daren farkonka kai da ita, ita ta k'irana tacemin nazo ka fita nacemata bazanzo ba sabida maybe ba nisa kayiba karkazo ka tarar damu sai tacemin mahaifiyar kace bata da lafiya da alamun idan katafi zaka dad'e kar na damu nazo kawai koda ka kamamu ita bata shakkar a ganni tare da ita dan tayi imanin babu namijin da zaiyi mata abinda nakeyi mata.
Kirjin safraz ne yake fad'uwa duf ! duf !, da sauri ya kalli izzatu hawaye na bin fuskarshi yace, Dan Allah izzatu kicemin bakuyi sex ba, dan Allah karki cemin kunyi, Itama shi take kallo kuka yaci k'arfinta tana tsananin mamakin tarkon da mutumin ya d'anamata bame k'aryata shi.
  Muryan mutum sukaji yace, izzatu wallahi nayi nadamar amsa k'iranki, kin k'asak'antar dani a gaban mijinki, da lokacin da muka kammala kin barni na tafi da baizo ya samemu ba ammah kikace sai munyi wanka tare. Ya k'arasa maganar yana jan tsaki.

Izzatu tace,Wallahi k'arya yakeyi, wallahi ban sanshi ba ban ta6a ganinsa ba sai yau, besty karka yarda dashi sharri yakeso yamin,

 Mutumin yace, au hk zakice izzatu ?idan namiki k'arya ai shi ba makawo bane ya ganmu tare kina nufin ni kwartone?wayarki ma ai shedace domin da ita kika k'irani.
 Safraz da k'yar ya dafa bango ya fito daga toilet d'in idonsa yana gani dishi_dishi yana isowa tsakiyar d'akin ya fad'i yanajan numfashi da k'yar hakan ya bawa mutumin damar fitowa ya fice abinsa.

 Itama izzatu fitowa tayi hawaye nabin fuskarta, ganin safraz a tsakiyar d'akin a kwance yasa  ta k'arasa idan yake hankalinta ya tashi ganin da k'yar yake jan numfashi, hannu tasa ta rik'esa tana cewa, besty kar abin ka gani yayi tasiri a ranka dan Allah wallahi tallahi sharrine nima ban sanshi ba wallahi.

Hankad'eta gefe yayi sai da towel d'in jikinta ya kunce da sauri ya kawar da idansa itama cikin hanzari ta maida ta d'aura.

  A hankali ya mik'e tsaye ya bar d'akin, kan kujera yasamu a falo ya zauna, tunani kala_kala suna zuwa masa ransa.

Izzatu kayanta ta d'auka tasa zuwa lokacin hawaye ya k'afe a  idonta zaman dirshan tayi a k'asa tarasa me yakeyi mata dad'i tunanin ta d'aya " laifin metayiwa wanda ya aikata mata hk, aikoshi akayi ko kuwa dan kasan yayi" a hankalin take takawa har zuwa ta fito falon.




Ma'u me aiki tana zaune a d'akin da aka basu ita da Abu a gefen part d'in izzatu a ranta tana cewa" Anya kuwa Allah zai yafema na kuwa?muzo danmu lalata rayuwar auren bayin Allan nan hk kawai sabida za'a bamu kud'i, yaune fa darensu na farko ammah nasan Abu tuni ya gama lalata musu wannan daren, tabbas yarinyar abin a tausayamata ne a ina zatasa ranta ?yanzu kuma idan aka kama Abu yazamuyi ?"  tana cikin wannan tunanin taji an banko k'ofa da k'arfi.
Abu ce ta shigo da sauri tasawa k'ofar ki sannan tazo kusa da ma'u ta zauna tana sauk'e ajiyar zuciya.
zuwa can sam'u tace, ya ake ciki?
Abu tace, komai ya tafi dai_dai sai dai fa angon yana cikin matsala sosai dan yanxuma ya fad'i kamar sumamme hakanne yabani damar fitowa.

Ma'u tace, to muk'ira hajiya mu fad'amata ammah kar muce mt akwai wata matsa domin gaskiya ni inajin tsoron abin da kaje yazo.

Abu tace, ke wannan fa bawani abin tsoro bane miliyan d'ayafa za'a bamu cas a hannu gobe, dan mu kashe auren yarinya nan ni a ganina babu wani shiga hakkinta da mukayi dan 'yar gidan masu hannu da shuni ce kota bar nan gidan cikin daula zata cigaba da rayuwarta agidansu,  kinga kayan da aka zuba mata kuwa yadda kikasan ba a duniya kikeba idan kika shiga d'akinta,   mukuwa talauci yayi mana katutu kamar ya kashemu abincin damukeyi ma yanxu ba'a wani cinikin kirki.

Ma'u tace, hmmm hkne ammah wallahi inajin tausayinta sosai adaren farko aka mt wannan sharri me girma hk .
Abu tace, matsala dake ai kenan, idan kinsan bazaki iya wannan aikin ba tun wuru ki fad'a kar sai tafiya tayi nisa kisa agane mu mazane ba mataba.

ma'u tace, hb yama za'ayi hk ta faru zan kiyaye dukkan hanyar daza tasa a fahimci mu mazane ba mt karki ji komai.

Abu ce ta ciro 'yar k'aramar wayarta me k'iran nokia, number momy adama tak'ira wanda alokacin 11:37 na dare ammah nan da nan aka d'aga.

momy tace, saminu ya sai?
Abu tace, hajiya komai ya tafi yadda kikace.
momy tace, yauwa hk nakeson ji daga gareku, muma yanxu hk ab sallamemu dg asibitin muna gida.

Abu tace, hajiya babu wani abu wanda za'ayiyanxu ?

momy tace, babu komai, yanxu kawai zamu jira zuwa gobe ne muga mai zai biyo baya, duk abinda za'ayi zan fad'amuku sannan inason ku kiyaye sosai kar a fahimci ku suwaye.

Abu tace, indai wannan ne hajiya karki samu damuwa angama, daga nan suka kashe wayar.


_Saminu da k'aninsa Ado 'yan daudune da suke aikin dafa abincin siyarwa a kasuwa, ko acikin 'yan daudun da suke aikin dafa abinci a kasuwarsu saminu yayi k'aurin suna kowa yasanshi idan a harkar fitsane a kalla zai kai shekaru 31, Ado kuma k'aninsane me bin umarninsa duk abinda yasashi, saminu shine yake amsa sunan Abu shikuma Ado shine ma'u._







Har izzatu ta iso inda safraz yake baisan ta zoba, yana kan kujera a zaune yayi nisa a tunani ga kuma hawaye yana bin kumatunsa.
   Safraz izzatu ta fad'a, d'agowa yayi ya kalleta sai alokacin yasan tazo gurin.
 Tacigaba da cewa,  Dan Allah ka fahimci ne safraz, karkamin mummunan zato dan Allah, wallahi ni ba fasik'a bace bazan ta6a iya aikata abinda kake tunani ba nasan kayi bincike akaina kafin ka nemi aurena kasamu sheda me kyau akaina da iyayena, wallahi ban ta6a sanin wani d'a miji arayuwata ba ban ta6a zubda mutuncina ba wannan abun daya faru makircine da sharri akeson a k'ullamin bansan menayiwa wanda ya aikatamin hk ba dan Allah safraz kamin kyakykyawan fahimta. Ta k'arasa maganar tana fashewa da kuka me ban tausayi.

 Har cikin zuciyarsa yaji tausayinta bayanson zubar hawayenta kokad'an yanaji tamkar yayi hauka sabida tsananin sonta da yakeyi,  kukan datakeyi yanzuma ji yakeyi kamar ana sukar kirjinsa da mashi, ammah taya zai yarda da abinda tace bayan abinda ya gani da idonsa.

Ya isa!safraz ya fad'a yana kallon izzatu.
Yacigaba da cewa, kidena kukan nan hk ya isa come over.
 ya fad'a yana mik'a mata hannunsa.

A hankalin ta taso ta matso inda yake, hannu daya mik'o mata bata da za6i itama ta mik'a masa nata bisa mamakinta taji ya jawo jikinsa.

Rungumeta yayi sosai ajikinsa kamar zai maida ita ciki, A hankali yake sauk'e ajiyar zuciya, sun dad'e a hk zuwa can safraz ya fara cewa;
 Hakik'a izzatu ina matuk'ar  k'aunarki a raina yadda nakeji babu abinda nakeso kamarki a duk duniya baki d'aya kece mace ta farko dana fara so a zuciyana nasha fad'amiki ban ta6a soyayyah ba izzatu, nayi rayuwa a k'asa shen turawa ammah ammah hakan baisa na ta6a aikata zina ba duk wani burina yana kanki izzatu dukkan tanadina nakine my dear but why do that to me?meyasa kikamin hk ?koda kin kasance kina aikata hk kafin aurenmu meyasa baki hakura ba  alokacin da mukaza ma'aurata muyi rayuwa me kyau ki nemi yafiyar ubangiji akan wanda kika aikata a baya, Ammah izzatu naji bak'in ciki sosai duk tunanin ban ta6a tunanin you can do that ba but why izzatu ?kuka yakeyi sosai izzatu dake kan kirjinsa rungume tanajin zubar hawayensa akan fuskarta, D'agowa tayi itama hawaye sun cika idonta hannun tasa tana goge masa hawayen dake zuba a fuskarsa shima hannu yasa yana gogemata hawayen dake zuba a fuskarta.

 Izzatu tace, Ka yarda dani dear wallahi ban aikata ba gaskiya nake fad'ama.

Safraz ya kwantar da kansa akan bayan kujeran sannan yace, idan sharri yazo yamiki ya akayi yasan nafita bana nan bawanda zaiyi tunanin zan fita inbarki a dai_dai wannan lokacin idan ba fad'a akayiba taya yasan mamice bata da lpy ?izzatu na kasa yarda dake gaskiya.
Izzatu tace, wallahi bansan ya akayi ya saniba ammah bani bace na aikata hk dear believe me pls what am telling you is true.
Dukkansu sukayi shuru ba wanda ya k'ara cewa komai.

 Safraz ne ya fara zame jikinsa daga jikin izzatu ya tashi sai da yayi tafiya kamar taku biyar sannan ya juyo ya kelleta yace sai da safe.
  Wani d'aki dake kusa da d'akin izzatu ya bud'e ya shiga yasa key ya rufe, bed ya fad'a ya fara kukan zuci wanda yafi na fuska ciwo.

Ko da izzatu tazo ta murd'a kofar taji yasa key har zata wuce d'akinta kuma sai ta fasa ta durkushe a wajen taba ta kuka marar saiti a wajen ta kwanta a kan tile yadda taga rana hk taga dare sai zuwa can kusa da asuba bacci 6arawo ya saceta.

Shima safraz hk yake a 6angarensa be rintsa ba sai dayaji ankusa tayar da salla a masallaci sannan ya shiga toilet yayi alwala.
 Yabud'e k'ofar dan fita masallacin kenan yaganta kwance a bakin k'ofar tayi fillo da d'an kwalinta gashin kanta ya rufe fuskarta bacci takeyi tana sauk'ar da ajiyar zuciya alamu tayi kuka har ta gaji.

 kwalla yaji tana neman zubowa a idonsa da sauri ya danne, hannayensa yass ta d'auke ya nufi d'akinta, har kan gado ya kaita sannan ya janyo bedshit ya lullu6eta  dashi ya fice.

 Ko daya dawo dg masallacin ya lek'a yaga bata tashiba sai ya wuce d'akinsa.


  I zzatu farkawa tayi ta ganta a d'akinta batayi mamakiba tasan safraz ne ya kawota, bayan tayi sallah akan sallar bacci yakuma kwasheta Sai k'arfe 8 ta tashi.

Jitayi gidan ya d'au kashin turare me dad'i, toilet ta shiga tayi wanka ta shirya cikin bak'ar doguwar riga me dogon hannu d'an kwalin rigar ta yafa a kanta ta fito falo, ga mamakinta sai taga an gyara ko ina tsab_tsab sai ganshin turare ke tashi a falon,  tana cikin mamaki ma'u ta shigo falon d'auke da kayan abinci Abu tana biye mata baya itama da kaya a hannunta.

 Deining table suka wuce suka jere kayan, sannan suka nufo inda izzatu take tsaye. dukkansu suka zube k'asa.
Ma'u tace, hajiya ina kwana?
Izzatu ta amsa da lpy tana murmushin yak'e.

Abu ba ta gyara murya tamkar mace tace, Batka da safiya hajiya dafatan ku tashi lpy?

Izzatu ta kalleta tace, lpy qlau. suna had'a ido da Abu gaban izzatu ya yanke ya fad'i tas!hk kawai idanuwan matar yayi mata kama da mutumin daya shigomata jiya ammah kasancewar Abu tasa jambaki sasu goda harda eyeshadow yasa kamar ta so ta 6ace.

Ma'u tace, mu masu aikine da aka d'aiko jiya nasan Alhaji ya sanar miki d'akinmu yana dg wajen lambu bayan wannan part d'in, mungama komai ko akwai abinda za'ayi miki ?

Izzatu tayi murmushi tace, Ayyah sannunku babu komai ku huta hk kunsha aiki.

Ma'u ta kuma cewa, idan kinban izini zanje in gyara miki d'akinki.

Izzatu tace, A'a ku ht hk babu komai zan gyara zuwa anjima.

Abu tace, a'a hajiya yana dg cikin aikin da hajiya wato mahaifiyar mijinki tace mudinga yi d'akin mijinki ne kawai bamu da hakkin gyarawa ki barmu muyi kar musaki wahala ranki ya dad'e.

murmushi izzatu takumayi tace, to shikenan kuyi ammah ai bawani aiki bane me wuya da kun barshi.

Ma'u tace, ai tace kar mu barki ki d'au koda tsinke inda muna nan.

Izzatu tace , Allah sarki nagode ya sunaku?

ma'u tace ni sunan ma'u itakuma wannan yayatace sunanta Abbu.

Izzatu tace, Ayyah sannunku da k'ok'ari nagode.


Abu tace, mune da godiya hajiya, sannan Abu ta kalli ma'u tace kije ke ki gyara d'akin ni zanje in gyara kitchen inyi wanke_wanke.

Izzatu data gaji da jira safraz bai fito ba dan hk itama ta koma d'akinta aikuwa tas ta ganshi sai k'anshi dake tashi a d'akin har toilet duk anwanke tsab.  Kayan mutumin nan ta gani ma'u ta ninke ta d'ora mata a kan gado sai taji hawaye na zuba a idonta aranta tace 'wato  ma'u tayi zaton ko kayan mijina ne'  window ta zuge ta watsasu ta baya.



Tsawon sati d'aya Haka izzatu da safraz suka ciga da rayuwa alokacin amarci ammah su yazama lokacin kunci da damuwa domin babu abinda yake had'asu sai gaisuwa wani lokacin ma ko izzatu ta gaishesa baya amsawa, sai dai duk randa ta wuni bata fito faloba hankalinsa zai tashi sai yaje yaga abinda yake faruwa abinci ma wani lokacin idan yaga bataje deining taciba har d'akinta yake zuwa ya kawo mata shidai kawai sam bayan ta masa mgn sabida ya kasa manta abinda yagani a daren farkon su.

 Satinsu biyu da yin aure iyayen izzatu zukazo yimata sallama domin zasu tafi k'asar America wani aiki ya tasowa babanta itama mahaiyarta zata bisa, Izzatu rayi kuka kamar ranta zai fita har ummi wato mahaifiyarta taso ta gane akwai matsala a zamantakewa aurenta da safraz, sun rabu dukkansu suna jimami domin izzatu ita d'ayace 'ya agurinsu.


Alokacin da sukayi wata d'aya cif da aure izzatu duk tabi ta rame ta kod'e kamar wacce bata da jini ajikinta, Babu abinda ya canza tsakaninta da safraz kullum idan ya fita office tun safe sai yamma yake dawowa, tayi masa zancen komarta makaranta tunda ashekarar k'arshe take zata kammla degree d'inta  ammah yace bai yarda ba zata dinga had'uwa da mutumin dazo masa gidane dan hk ta hakura da karatun ba yadda ta iya hk ta hakura kullum cikin zubda hawaye takeyi, wani lokacin mami tana zuwa ta dubata tana janta jiki sosai hkm shahida da sakina suna zuwa mata lokaci zuwa lokaci.

Ba wanda yasan halin da suke ciki jafar abokin safraz daya fahimci akwai abinda yake damun safraz daya tambayesa yak'i fad'amasa idan ya takura sai yace masa kawai bayanson ya bar izzatu agida ita d'ayane abinne yake damunsa,


Momy kuwa har ta gaji da zura ido taga me safraz zaiyi ammah shuru, ammah tabbas ta fahimci basa zaune qlau shida izzatu domin fuskar izzatu cike take da damuwa duk sanda taje gidan, mami kuwa duk ta d'auka ko izzatu ta fara laulayi ne shiyasa bata tambayarta meke damunta.


Yau ya kasance watan izzatu d'aya harda sati d'aya dayin aure, tana zaune a a falon safraz yayi sallama ya shigo ya dawo dg office.

Izzatu tace, sannu da zuwa.

safraz bai kalli inda takeba yace, yauwa sannu.

Taje tasa hannu dan ta kar6i jakar hannunsa ammah yace ta barshi. d'akinsa ya wuce ya shiga.


Yayi kamar mintuna talatin da shiga izzatu ta tashi ta shiga d'akin itama, wannan shine karo na farkon data ta6a shiga d'akin safraz duk sanda tazo shiga akulle take samu kota buga baya bud'ewa.


A dai_dai lokacin data shigo safraz ya fito dg wanka d'aure da towel, da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa.





~Sunnu_sannu kwana nesa muje zuwa page 7 yau da gobe batabar komai ba~👌🏻



0 comments:

Post a Comment