❣🤦🏻♂ _*KUSKURENA*_❣🤦🏻♀
```{The story is Interesting! Attractive! Impressive! to cut a long story the story is a fascinating story the readers will entertain and enjoy it.} ```
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
***************************************
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
_*BY*_
©, _*RAMLERT Y SALIS*_
_*(NAZRA /FIRRAM )*_
~08164530838~✍🏻
_Tue, Des 25, 2018._
_*Page 5......*_
Ringing biyu tayi aka d'aga, karima fashewa tayi da kuka sai kuma taji magana kamar ba momy ba.
Aunty what wrong with you ?cewar sakina lokacin data d'aga wayar taji karima na kuka.
Karima jin k'anwarta sakina ce ta d'aga wayar yasa ta dakatar da kukan nata, cikin tsawa tace, why received the calling if i need talk to you i will call your phone not momy's phone.
Sakina tace, hb Aunty what i did it's a something bad?
Karima takuma hasala sannan tace, kinga stop disturbing me where is momy?is she around ?
Sakina tace, hym mutum kullum cikin fad'a sai kace barkono, momynsu dake gefe a zaune sakina ta mik'awa wayar.
Momy tarik'e wayan tana cewa;sakina ke dawa kike mgn ne ?
fuskar sakina a d'aure tace, momy kinsan baxai wuce wannan 'yar girman kan ba mutum yayi nesa ma ammah hali yana nan jiya i'yau.
Karima da duk tanajin abinda sukeyi ranta yakuma 6aci, sai alokacin momy ta kara wayan a kunenta tace, Hello mutanan england yau kuma an tunamu da sassafe hk ?
daga can 6angaren karima tace, momy 6an taba tunanin za'ayimin hk ba, sai kuma ta fashe da kuka.
Momy hankalinta yaso ya fara tashi jin kukan karima domin ta d'au dukkan soyayyar duniya nan ta d'ora akan 'ya'yanta biyu tak karima da sakina bata k'aunar dukkan abinda zai ta6a su musamman ma karima. A duk tinaninta karima na kukane sabida abinda sukayi da sakina yanxu domin sam batason tasan safraz zai yi aure dan akwai tashin hankali sosai shiyasa bata fada mata ba har sai ta dawo.
Momy cikin rarrashi tace, hb karima me ya had'aki da 'yar'uwar taki har zai saki kuka hk so kike ta rainaki kou ?
Cikin hasala bawani ladabi karima tace, wai wayace miki ni wannan banzar ce damuwata, ashe momy baki damu da farincikina ba kamar yadda kike fad'a ke da bakinki kikace safraz bashi da matar data wuceni ammah momy why zaki 6oyemin safraz zaiyi aure ?sai Dai ingani a magazine da social media, ta k'arasa maganar tana kuka.
Shuru momy tayi domin tayi matukar kad'uwa da mamaki, ko sa'ilin taso ta boyewa karima tace k'aryane to ammah sai ta tuna cewa tace a jarida ta gani da social media ba damar ta k'aryata, yazama dole ta fad'a mt gaskiya.
Karima ta kuma cewa, momy kikayi shuru ko kina nufin kema kice baki saniba ne ?
Momy tace, kai!karima kinsan banason damuwarki wannan ba abin tashin hankali bane, kinsan bana mgn biyu kamar kin auri safraz kin gama kisa wannan a ranki da zaki bar wannan maganar ki bari sai kin dawo tukunna kwata_kwata kwana nawa ya rage miki ne naga.
karima tace, ni ban gane me kike nufi ba pa momy, safraz zaiyi aure acikin satinan ammah kina maganan kamar na auresa na gama, kina nufin zai hakura da auren ne ko kuwa nice zan zauna da kishiya!?
Momy ta kuma kada murya tace, matsalana dake bakya cin ribar zance, Anan momy ta kwashe duk yadda sukayi da k'anwarta wato hajiya maryam mahaifiya ga safraz ta fad'awa karima.
Wata irin k'ara karima ta saki wanda yasa momyn ma ta firgita tare da cewa, momy!ni ! ni ! ni ! ni za'ayiwa kishiya ?momy kinsa me kike fad'a kuwa ?safraz ya aureni a ta biyu, wallahi Impossible wallahi yau nasan bakya sona har zaki amince 'yarki ta zauna da kishiya this is play child momy and i sure you hate me momy.
momy tace, hb sha lelena baki tsaya kinji k'arshen zancen ba ai listen to me pls zaki gane gatan da zammiki.
karima tace, na gama fahimtanki momy you have nothing to tell me stop deceiving me the game is over, kibarni ni zan sharewa kaina hawaye wallahi gobe zan dira a 9geria sai nayi me yiwuwa dan lalata lamarin auren nan. Bata jira me momy zatace ba ta katse wayan.
Momy ta dinga k'iranta ammah tak'i d'agawa duk tashiga damuwa ta rasa inda zatasa kanta. Sakina dake zaune a gefe ranta itama a 6ace jin yadda karima ke yiwa mahaifiyar tasu mgn babu ladabi.
Sakina tace, momy wannan abinda kikewa aunty wallahi ba gata ba ki duba fa kiga bata jin shakkar fad'amiki ko wacce irin mgn ammah momy a hk kike binta kina rarrashinta, safraz sam wallahi bai dace ya auri mara tarbiya irin aunty ba kuma wallahi momy baya sonta kune dai kuka dage zakusa mami tayi masa dole kuma dan ansan shid'in mai tarbiya ne ammah ai ba'ayiwa namiji auren dole ko aunty tayi nasarar aurensa wallahi zata gane tayi babban _*KUSKURE*_ , momy karki manta damu da safraz duk d'ayane awajen ni ni tabbata bazaki ta6a yadda mu auri wanda bama so ba ammah to meyasa shi akeson ayimasa dole sai ya aureta momy kamar fa talla ne aunty takeyi da kanta ta bari yaxo yace yana sonta ammah karta kai kanta garesa.
Momy ta gallawa sakina wata harara tace zaki rufemin baki ko kuwa sai na sa6amiki, sannan ta mik'a mata wayar tace, a6i nan zoki rubutamin text in tura mata ko hankalinta zai kwanta.
Sakina tace, momy dan Allah karkisani acikin wannan lamarin momy ki rubuta text d'in da hannunki dan Allah ko ki k'ara k'iranta ki fad'amata ni dai gaskiya bani acikin wannan lamarin.
Momy ta 6ata rai tace, okay ban isa nasaki abu kiyi ba kou?ko kuma kin raina ni ne bansaniba idan na isa da ke sai kin rubuta ke baki damu da damuwar 'yar'uwarki bane kou?
Dole sakina ta kar6i wayan ta rubuta dukkan abinda momy ta umarce ta rubuta.
A can d'aya 6angaren karima data gama shiryawa da nufin ta nufi airport dan ta shirya yadda zata tafi nigeria gobe, text ne ya shigo wayanta sai tayi kamar bazata duba ba sai kuma ta bud'e ganin text d'in dg momy ne yasa ta koma da baya ta zauna akan wata 'yar k'aramar
Sakina tace, momy dan Allah karkisani acikin wannan lamarin momy ki rubuta text d'in da hannunki dan Allah ko ki k'ara k'iranta ki fad'amata ni dai gaskiya bani acikin wannan lamarin.
Momy ta 6ata rai tace, okay ban isa nasaki abu kiyi ba kou?ko kuma kin raina ni ne bansaniba idan na isa da ke sai kin rubuta ke baki damu da damuwar 'yar'uwarki bane kou?
Dole sakina ta kar6i wayan ta rubuta dukkan abinda momy ta umarce ta rubuta.
A can d'aya 6angaren karima data gama shiryawa da nufin ta nufi airport dan ta shirya yadda zata tafi nigeria gobe, text ne ya shigo wayanta sai tayi kamar bazata duba ba sai kuma ta bud'e ganin text d'in dg momy ne yasa ta koma da baya ta zauna akan wata 'yar k'aramar kujera dake gefen bed ta fara karanta wa;
_My daughter come down pls, karki dami kanki akan wani k'aramin dalili ni na d'au alwashin cika miki burinki ko ta halin k'ak'a, Ba boka ba malam safraz zai aureki ina bin a sannu ammah ke kinfi son ayi gaggawa no karima ku nutsu ki fahimci abinda zan fad'amiki, mu rabu da safraz yayi aurensa ammah kinsan me?tun dg first night d'insa shida amaryarsa zamu fara kula kiyaye a tsakaninsu zamu rabasu da kwanciyar hankali shi da kansa zai saketa tun kafin su cika watanni biyu da aure ke kuma nan da wata biyu kina dawowa zaki shiga gidan koda be saketa ba kekuma kina shiga zakiyi waje da ita, ammah idan kikace sai munyi yadda zai hana yayi aurensa to zai tsaneki ne a ransa muda muke neman soyayyah dole ta k'asa zamu dinga bi, makirci kisisina tare da kissa duka zaki koya karki kuskura wani ya gane kina bak'in ciki da auren ki kirashi ma a waya ki tayasa murna karki na nuna komai a fuska ki danne kawai idan kin samu dama ma kizo bikin ko kwana uku ne saikiyi ki koma_
Karima tana gama karantawa sai taji ranta ya d'anyi sanyi, sai alokacin ta gane me momy take nufi tabbas yanxu hankalinsa yana kan wata bazai saurarenta ba duk abinda zatayi, murmushi tayi sannan ta tafi laluben number safraz.
_*BAYAN KWANA BIYU*_
*****************
*************
**********
********
*****
**
*
Taro yayi taro, jama'a iya jama'a bikine daya tara manyan mutane, naira tayi kuka an zubar da ita tamkar ba'a so kamar ba'asan zafin nemanta ba _SAFRAZ HASHIM MUHD, TARE DA AMARYARSA IZZATU ABDULLAHI ABUBAKAR_
Kowanne 6angaren sun nuna bajintarsu, kowa cikin farinciki yake musamman ango safraz momy adama ta zage tana ta hidima tamkar babu komai a ranta hakama karima ranar d'aurin aurw da sassafe ta diro nigeria sun gama kulla komai ita da mahaifiyarta sam basu bari sakina ta san abinda suke kullawa ba, mami taji dad'in yadda yayarta momy tayi hidima sosai a bikin abin ya bata mamaki ganin karima itama ta sake babu wata damuwa a ranta.
Zuwa can da yamma mami da momy suna zaune a d'aki su biyu suna hira,
momy tace, gaskiya na yaba da hankalin yarinyar da safraz ya za6a Allah ya basu zaman lpy.
mami tace, ameen aunty adama iyayenta suna da dattko sosai sun samu yabo sosai awajen jama'a.
momy tace, hk ake so ai, yanxu inason in k'ira sakina da karima da shahida suzo su fara shirya musu kalolin abincin da za'a kai musu gobe da safe wanda zasuyi breakfast dashi ko ya kika ce?
Mami tace, duk yadda kikayi aunty yayi dai_dai.
momy waya ta d'auka tak'ra karima, hello karima kina ina inason yanxu keda shahida da sakina kuzo ku sameni a d'akin maminku maza.
karima tace, momy ai mu tuni munyi nisa wallahi yanxu hk muna gidan amarya kuma baxamu taho ba sai an kawota momy, mezamu yi miki momy ?
momy tace, hb karima ku taho mana ba sai ku koma ba dg baya, inason kuzo ku fr shiya abinda ango da amarya zasuyi breakfast dashi gobene.
karima ta marairaice murya kamar zatayi kuka tace, hb momy ki bari sai mun dawo idan banga amarya yauba gobe around 10 fa zan tafi, momy ai yanxu ma andena kai abinci dg gida kawai masu aiki zaku nema musu kamar guda biyu hk, gidan fa da nisa momy har yaushe akayi girki da safe aka kai musu koda anyi da sassafe momy kuma fisabilillah da sassafe sai aje a tashesu koda basu tashiba wannan tsarin baiyiba momy ga store d'insu acike da kayan abinci kicewa mami tasa yanxu aje anemo me aiki kawai dan ko me gadi babu a gidan. Tana gama fadin hk ta katse wayan batajira momy ta k'ara cewa komaiba.
Dayake wayan yana speaker mami tana jin duk abinda karima tace, sai taji abun yayi mata dad'i kuma karima ta burgeta duk da tana son safraz hakan bai hana ta fad'i gaskiya ba, mami taji dad'i sosai.
_Abinda mami bata saniba hakan duk yana cikin mak'ircinsu da suka shirya_
hk akayi kuwa mami ta amince da abinda karima ta fad'a, nan take momy ta k'ira wata k'awarta tace, a turo mata masu aiki guda biyu.
Momy dama tuni tasan suwa za'a turomata wasu 'yan daudune guda biyu dukkan sunyu shigar mata ba wanda zai kallesu yace mazane ba mataba sun sa kaya tsaf_tsaf daka gansu zaka rantse matane har maganarsu sunyi cikon ko ina ajikinsu kamar mata.
Momy ta kallesu tacewa mami sunyi ko?mami tace ba wata matsala ng suna da tsafta sosai harda kwalliyarsu abinsu sunyi.
momy ta kallesu tace ya sunanku?
Ta farkon tace, ni sunana Abu itakuma wannan k'anwata ce sunanta ma'u.
momy tace to yayi, yarona ne yayi aure yau shiyasa nakeson 'yan aiki.
Abu tace, Allah ya sanya alkhairi ajiya, insha Allah zamuyi aiki da gaskiya zasuji dad'in aikinmu.
mami tace, to nawane za ana biyanku duk wata ?
Abu tace, girki, wanke_wanke, da gyaran gida da share_share da aike da sauran d'awainiya harma da wankin matar gida da yara ana biyanmu dubu talatin duk wata, ammah idan baza'a bamu wajen kwanaba ana biyanmu dubu ishirin duk wata, muba agari mukeba hayan dak'i muke kamawa duk wata dubu goma shiyasa muke cire dubu goma ya zama ishirin idan za'a bamu wajen kwana a gidan.
Mami ta kalli momy tace ya kika gani?momy tace to dole dama amasu wajen zama tunda safraz yana fita aiki itama matar tana karatu kou?mami tace, hkne wannan to yanxu za'a baku wajen kwana sannan za'a dinga biyanku dubu talatin d'in insha Allah.
A dai_dai lokacin safraz ya shigo d'akin nan mami tayi masa bayani shima kuwa yaji dad'in zancen sosai take yasa driver ya kai su Abu gidansa aka nuna musu wani d'aki daga gefen part d'in izzatu nan ne d'akinsu tun zuwansu karima ta hangosu sai wani farinciki takeyi wato shirinsu ya tafi dai_dai ba wanda zai gane mazane ba mt ba.
An kawo amarya kowa ya watse, 'yan aiki suna 6angarensu, amarya da ango suma suna part d'insu,
safraz ya kalli izzatu datake lullube cikin mayafi yace, Izzatu tun da nake a duniya banta6a jin farinciki irin yauba.
Izzatu ta kuma rufe fuskanta da mayafin tana murmushi, hira suka dinga yi a tsakaninsu sannan suka gabatar da sallah raka'a biyu da addu'o'i da suka zo a sannu.
A gidan mami kuwa 'yan biki duk sun watse saura kad'an wanda 'yan'uwa ne na nesa, mami ta kalli shahida dake saka kaya a sif tace, shahida kaina wani irin ciwo yakemin nemiomin maganin ciwon kai ga hajijiya da nake ji.
shahida tace, Ayya! mami sannu ko dai tarone yasa kikejin gajiya hk ?
mami tace a'a shahida wannan ya wuce hayaniyan taro sosai nakejin ciwon kan.
shahida fita tayi dan ta d'auko mata maganin.
Momy kuwa tana falo ta idar da sallah tana jiran result d'insu ya fito, wato tun lokacin da jama'a suka fara watsewa momy tasa aka kawo musu abinci tasa mami a gaba tace ta zauna su ci abinci domin taga alamun sam bata ci wani abin kirki tun safe, mami ta zauna sukaci karima ta kawo musu lemo ammah saida lemon da mami tasha sun riga sun zuba maganin bacci over aciki yadda zai iya fitar da mutum acikin hayyacinsa wannan shi yasa mami ta farajin alamu.
Shahida tana kawo wa mami maganin ciwon kan sai ta samu mami rana ta juyi akan gado sai k'iran wayyo Allah takeyi duk tabi ta fita hayyacinta.
Nan da nan shahida ta fara kukan neman taimako, da sauri momy ta shiga d'akin tana farinciki maganin ya fr aiki momy itama taso ta firgita ganin yadda mami takeyi ammah sai ta kalli shahida tace maza d'au waya ki k'ira safraz, dayake shahida yarinyace bata wuce shekaru 12 ba batayi tunanin bai dace a k'ira safraz ba nan da nan ta k'irashi.
Safraz yana zaune kusa da izzatu yanata magiya akan ta bud'e baki yasa mata naman daya yago tak'i, sai ga ringing ya shigo wayansa ya d'au wayan da niyar yayi rejectint call d'in sannan ya kashe wayan kawai sai yaga number mami ne da sauri ya d'aga sai yaji muryan shahida tana cewa;
Big bro mami zata mutu sai kuka takeyi tana cewa wayyo Allah, sai ta fashe da kuka.
safraz mik'ewa tsaye yayi zumbur ya yar da naman da yake hannunsa, cikin firgita yace, shahida meya sameta ?shahida tace, bro i don't know but she said she have a headache right now.
Safraz cikin rud'ani yace, ina zuwa. shahida ta kashe wayan momy datake k'ok'arin d'aga mami tacewa shahida me yace?shahida tace yanazuwa yanzu.
Alokacin shahida da karima suka shigo d'akin dayake namiji yafi mace hankalin nan da nan shahid ya k'ira Abbansu ya sanar masa shima Abban baya gida yace masa su k'ira driver ya kaita hospital gashinan zuwa ammah kar a fad'awa safraz.
Shahid yace Aunty karima ku kamata mu kaita mota Abba yace driver ya kaimu hospital, momy tayi saurin cewa kai ajira safraz yazo mana shahid yace, momy Abba yace kar a fad'amasa.
Dan kar su shahid da shahida su gane yasa momy tasa suka kama mami har zuwa mota a harabar gidan sakina ta gansu hankalinta ya tashi sosai ganin halin da mami take ciki ita tayi drivering ta kaisu har hospital d'in momy bataso hk ba taso sai safraz yazo tukunna su kaita hospital d'in tare, ammah sai ta tuna yace yana zuwa sai ta d'an ji dad'i hakama 6angaren karima sai tunani takeyi ya za'ayi safraz yazo batan tuni momy tasa shahida ta fad'a masa ba.
Safraz cikin gaggawa ya bar gidan da yayi kamar ta tafi tare da izzatun kuma sai ya tuna bai daceba hk yasa ya tafi ya barta badan ransa yaso ba, koda yazo gd aka sheda masa sun tafi asibiti sai ya k'ira number mami, momy ce ta d'aga ta fad'amasa hospital d'in da suke, ba 6ata lokaci ya isa asibitin, lokacin daya isa har likita ya dubata ya mata wata allura, likitan ya sheda musu karsu wani damu nan da mintuna ishirin zata farka kuma zata dawo normal abinda yasa hakan ya faru da ita maybe tasha wani magani ne over ammah babu wata matsala.
D'akin suka shiga dukkansu suka zazzauna mami itakuma tana bacci, safraz ne yaje bakin gadon ya dafa goshinta da yake ta zufa duk sai yaga idonta ya zurma ciki lokaci d'aya.
Bayan mutuna 12 Abba ya iso shima, nan suka fad'a masa abinda likitan yace, Abba yayi_yayi safraz ya koma gida ammah safraz yaki wai sao ya jira ta farka.
ba'a dad'e ba mami ta farka ware ido tayi tana kallonsu one by one, dukkan su suka hau murna.
murya a dashe tace, meyake faruwa naga ango a nan a ina ka bar 'yar mutane?
Safraz yace, wallahi mami na tsorata sosai ammah wane magani kikasha me k'arfi hk?
mami tace, ciwon kaine naji me tsanani ban ma sha ko wanne magani ba.
momy tace, to likita yace kin sha wani maganine da yawa.
mami tace, Allah yanxu garau nake jina km ba wani magani dana sha.
Abba ya kalleta yace, ko dai kinsha batare da kinsaniba sabida tsananin ciwon kan ?
mami tayi dariya tace, sai kace wata 'yar kwaya zansha abu ban saniba
Abba ya kalli safraz yace, kai wuce ka koma gida, nace kar a fad'amaka ammah sai kazo kou?maza tafi muma yanxu zamu tafi.
Safraz yayimusu sallama ya tafi, yana driverint ammah Allah_Allah yake ya isa ga izzatunsa.
Momy ta fita ta kira Abu me aiki ta sanar mata ga safraz nan yanxu zai dawo.
Izzatu tana zaune bakin gado ta kwantar da kanta a kan gadon taji shigowar mutum da sauri ta d'aga kanta dan tunanin safraz ne ya dawo ammah kawai sai ta ga wani mutum tsaye a kanta.
~Sunnu_sannu kwana nesa muje zuwa page 6 yau da gobe batabar komai ba~👌🏻
0 comments:
Post a Comment