Blogroll

BANNER 728X90

Wednesday, 9 January 2019

Kuskurena Page 7 - ISMAIL SANI


❣🤦🏻‍♂ _*KUSKURENA*_❣🤦🏻‍♀
 
```{The story is Interesting! Attractive! Impressive! to cut a long story the story is a fascinating story the readers will entertain and enjoy it.}  ```


❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
***************************************
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣



               _*BY*_

 ©, _*RAMLERT Y SALIS*_
          _*(NAZRA /FIRRAM )*_ 
           ~08164530838~✍🏻


_Wed , Jan 9  , 2019._

_*Page  7......*_



Kanta a sunkuye kunya ta kamata, "Da tasan zata shigo ta sameshi hk da bata shigoba" sai taji kamar ta koma da baya.

  Shima safraz mamaki yakeyi ganin izzatu a d'akinsa  ammah duk da hk yaji dad'in biyoshi da tayi dan sau da dama yana son zuwa d'akinta ammah sai ya kasa musamman idan ya tuna ganinta da yayi da wani najimin ammah ko kad'an har yanzu baiji zai iya hakura da izzatu saboda abinda ta aikata masa ba saima matsanancin sonta da kullum yake k'ara shiga zuciyarsa awani 6angaren kuma yana feeling d'inta kamar ya mutu ya rasa taya zai tinkareta bayan tayi mu'amala da wani bashiba idan ya tuna bazai sameta a budurwa saiji duk duniya tayi masa zafi.

A hankali ya zauna a gefen gadon yana binta da kallo har zuwa lokacin kanta yana k'asa a sunkuye. wani 6arin na zuciyarsa yana cemasa" anya bana cutar da izzatu ?laifin da tayimin ya kai na k'aurace mata hk inason izzatu a raina kamar ny hauka ammah daren aurenmu na farko na kama izzatu da k'warto a gida meyasa baxanyi hakuri na rungumi matata muyu rayuwar farinciki ba sai dai na kasa mantawa da abinda idanuwana suka gani"

Katse tunaninsa yayi da cewa, Izzatu !
A sanyaye ta d'ago kanta tace, na'am.
 Sai ya rasa me zaice mata kawai sai yace, kina buk'atar wani abune ?

Izzatu tace, a'a um um inason muyi mgn ne dama ammah bari naje falo kafin ka gama.
 Tana gm fad'in hk tayi sauri ta juya zata fita.
K'irjinsa ne ya fara dukan uku_uku a ransa yana tunanin  "maganar me izzatu zata fad'amasa kodai zatace ta gaji da zama da shine hk'? hk kawai yaji ya damu kuma yaji zaman da sukeyi kamar lefinsa ne bata da wani laifi.

 Cikin hanzari ya bita ya rok'o hannunta alokacin har ta murd'a hannun k'ofar zata fita.
 Muryansa a k'asa_k'asa yace, muje ki tayani saka kaya mana Reality dm ko bakizoba yau zanzo gurinki in baki……
 Sai kuma yayi shuru ya kasa k'arasawa.
Izzatu kuwa har cikin ranta taji dad'in abinda yace ammah tana cike da kunyarsa ji takeyi kamar tayi hugging d'insa ko zata rage kewar dad'ad'an kalamansa da tayi tun kafin suyi aure.
Kasa yimasa musu tayi hannunta yaja har gaban sif d'in kayansa sannan ya kalleta yace,  za6amin kayan da zansa reality.
Sai data gama k'arewa sif d'in kallo sannan ta d'auko wata bak'ar T_shirt da breeches wato k'aramin wandon daya wuce gwuiwa kad'an shima bak'i.
  Kallonta yayi yay murmushi yace, Nice colour reality, muje ki gyaramin gashin kaina ki shafamin mai sannan kisamin k……
 Sai yayi shuru bai k'arasaba yana kallonta ta gefen ido.

Mamakine ya cika ran izzatu sosai gani takeyi kamar ba safraz bane a gabanta yake wannan maganar, ga kunyarsa da takeji musamman idan ta tuna abinda ya faro a first night d'insu.

gefen gadon ya zauna bayan ya kwaso mata abubuwan da zatayi masa amfani dasu.

mayukan ta d'auka tana dubawa tana karanta batare data tambayesa ba.

A hankalin take shafa masa mai ajikinsa tamkar wacce bata jini ajikinta, shikuwa safraz rufe idonsa yayi sun masa nauyi sam ya kasa bud'ewa har ta gama, sannan ta fara gyara gashin kansa dake kwance tamkar na jinjiri tana shafa masa mai d'aya bayan d'aya.

Na gama izzatu ta fad'a sai alokacin ya bud'e idonsa dasuka sauya dg fari zuwa ja, da ido ya nuna mata kayan,

Ringar ta d'auka ta fr k'ok'arin saka masa har ta gama sannan ta d'au wandon ta rik'e a hannunta kawai ta rasa yaya zatayi, zuwa can safraz yaji shuru sai ya bud'e idonsa yana kallonta, yanayinta daya gani ne yasa ya gane kunya takeji sai yasa hannu ya kar6a yasa da kanshi.

Mik'ewa tsaye yayi sannanya rik'e hannunta yace, zo muje in rakaki d'aki kiyi wanka ko zakaiyi a nan ?ya d'afa mt girarsa.

Murya k'asa_k'asa tace, Ban dad'e dayin wanka ba.

Safraz yace, Okay muje falo sai ki fad'amin maganar.

tare suka jera har zuwa babban falon, daf da daf suka zauna.

 Zuciyar safraz tana cike da tsoron jin abinda izzatu zata fad'amasa  sai zulumi yakeyi, tsoronsa d'aya kar ta furta abinda yake zargi.

Dan ya shashantar da maganar sai ya kalleta yace, madam nifa yunwa nakeji zo muje muci abicci sai muyi maganar dg baya kou?

Bata masa musuba ta tashi ta bishi tajin dad'in  yadda suke a tare yau, tanaji a ranta "koma kawai ta fasa yimasa zancen da zata yimasa ammah wata zuciyar tana cewa a'a kiyimasa kikasani kou ya koma kamar da d'in" da hk suka isa deining itace tayi saved d'insa bata zubawa kantaba, Abinda yakuma faranta ranta a baki safraz yadinga bata har ya tabbatar ta k'oshi.

Bayan sun kammala safraz ya kalleta ammah duk da hk yanajin fargaba a ransa shi yanajin a ransa "zai manta da komai kamar ba'ayiba ya nunawa matarsa irin sonta dayakeyi" safraz yace, Reality ina saurarenki.

Izzatu da fuskarta ta nuna alamun damuwa tace, Dama inason in bk hakuri ne akan abinda ya faru, zaman da mukeyi ni dai hkn yana damuna kayi hakuri dan Allah.

Sai alokacin safraz yayi ajiyar zuciya daya tabbatar ba abinda yake tsammani zt fad'aba, yace, izzatu koni naso na danne namanta dashi  ammah na kasa babu abinda yafi 6atamin rai da kikak'i yarda kin aikata kikace sharri ne, ammah yanxu kinyarda ?

Kwallace ta cika idanuwanta zuciyarta na bugawa da k'arfi tanajin rad'ad'i me zafi a ranta "Allah ya isa tsanina da duk wanda ya kullamin wannan sharrin, ya Allah ka bani mafita" izzatu ta fad'a a ranta.

Safraz yace, izzatu ina saurarenki ni wallahi idan kika fad'amin gaskiya babu wanda zan fad'awa idan kinajin tsoron ko zan fad'a i will keep your secret.

Wani 6arin na zuciyar izzatu yace mt" gara ki amince kinyi laifin akan ku ringa irin wannan zaman tunda yace bawanda zai fad'awa"

 A hankalin ta d'aga idonta da suke cike da kwalla tace, am!kayi hakuri na yarda, sai ta fashe da kuka me ban tausayi.

A firgice ya d'aga idonsa ya kalleta nan da nan yaji  jikinsa ya d'au rawa kanshi yana juyawa.

Itama kuka yaci k'arfinta atake taji kuma nadama tazo mata tafara dana sanin amsa laifin da batayiba.


_IZZATU DA TAKE BANI LABARIN HAWAYE NABIN IDONTA TA KALLENI TACE, RAMLERT AMSA LAIFIN DA BANYIBA WANNAN SHINE BABBAN *KUSKURENA* NAYI DANASANI MARA AMFANI.TACIGABA DA BANI LABARIN KAMAR HK……_





Idonsa sunyi jajajir fuskarshi a d'aure yace, meye amfanin hkn da kika aikata?dama kin kasance kinayi meyasa da kikayi aure bazaki hakura ba?izzatu ko dm bakya sonane?

Batace masa komaiba tacigaba da kuka tana takaicin amsa laifin da tayi.

Sai kuma taji zuciyarta ta dake kwata_kwata rayuwar auren ta fita a ranta.


Muryanta  a dake tace, safraz bani da banki da zancema komai ammah dan Allah inason ka sauwak'emin na koma gaban iyayena hkn zaifi.

A afirgice ya kalleta ransa yayi matuk'ar 6aci cikin 6acin rai yace,  harni zaki kalla kice na sauwak'e miki ?ke da yin laifi ammah ni da kika yiwa laifin bance zan sauwak'e miki ba sai ke?dama kinsan bakya sona why zaki yarda ki aureni ko kina nufin kin aureni ne dan ki dinga kawomin kwartayanki gidana ?Impossible wallahi, Kinason in sakeki kou?kibari zanyi tunani idan na,yankw hukunci zakigani *fasik'a* kawai. Yaja tsaki tare da buga table dake gabansa.

Hawaye nabin fiskarta tace, safraz nice fasik'a?karka k'ara cemin fasik'a niba fasik'a bace. Cikin sanyin murya ta fad'a tana kallonsa ido cikin ido.


A harxuk'e yace, nafad'a fasik'a kuma mazinaciya idan banda fasik'acin kafin kiyi aure kina aikata zina bayan kinyi aure mezaisa kiyi?wallahi izzatu kin cuceni idan badan darajar mahaifinki ba dana hakura dake idan yaso ciwon sanki ya kasheni ammah ina duba halin da iyayenki zasu shiga idan suka sani 'yarsu dy tilo abinda takeyi, kin bani kunya sun d'au son duniya sun d'oramiki ammah kinci amarsu tir dame hali irin naki izzatu.

Yana gm fad'an hk ya tashi ya bar gurin ya wuce d'akinsa.


Kasan tile izzatu ta zube tana kuka me d'aga hankali da ban tausayi, ta dad'e tana kuka har kanta ya fr ciwo dan kar masu aiki su shigo kwashe kayan dasukaci abinci su ganta yasa ta tashi da k'yar tawuce d'akinta.

Safraz yana shiga d'akinsa ya fad'a gado shima kuka yayi sosai har ya gode Allah, sai da kukan nashi ya lafa sannan ya tashi zaune, sai kuma alokacin ya fr danasanin abinda yayi mata tausayinta ya kamashi kamar yaje ya bt hakuri sai km yaji bazai iyaba.
 Izzatu meyasa zakimin hk?inasonki kamar na mutu why do that to me?dm bakicemin kinyarda ba dama kinkuma cemin sharri akayi miki, Yazanyi da raina Allah hk kaso ka ganni, hk safraz yadinga sambatu shi kad'e har bacci ya fr d'aukarsa.

Karima ce dg can england rik'e da waya a hannunta tana magana:

haba momy ni wallahi na gaji da gafara sa banga k'ahoba yanzu fa harsunyi wata d'aya dayin aure ammah shuru babu wani labari.

momy tace, nima dai abun ya d'auremin kai sosai ammah da masu aikin sun sanarmin kamar basa zaman lafiya dan tun safe yake fita by dawowa sai yamma kinga babu wani zaman lpy a tsaninsu ni a tunanima yarinyar nan ba hk ta barsaba ta asircesa ammah idan banda hk ya kamata da k'warto ammah har yanxu suna tare.

karima tace, momy yanxu to yaya za'ayi?saura baifi wata dy ba na kammala karatuna yanzu hk saura 5 days musamu hutu na 3 weeks sannan mu dawi muyi final exam. yanxu zanzo nayi hutu ns 3 weeks a nigeria inason kafin na dawo ayi waje da ita gaskiya.

Momy tace, ki kwantar da hankalinki koda bata ft ba idan kika shiga zan fad'amiki yadda zakiyi ki fidda ita,  nizanfi so idanma kinzo hutun kawai a d'aura auren idan yaso sai ki koma kiyi exam d'inki idan kin dawo saiki tare kou?


karima tace, Wow!wallahi hkne momy shiyasa nakesonki sosai fa!momy sai naxo kawai.

A dai_dai lokacin sakina tashigo falon momy hkne yasa momy ta kashe wayar dan kar taji mesuke cewa.


sakina ta kalli momy tace, momy nasa da aunty kuke waya kou?wai momu haryanxu baku hakura da zancen safraz bane?ni dai har kullum ina k'ara fad"a muku  kuji tsoron Allah. yanxu idan akayiwa big bro dole ya auri aunty kina tinanin za'ayi zaman lpy kuwa?wallahi matarsa me mutunci bata da fitina ammah aunty fa masifa tayi mt yawa zata dinga kawo rigima iri_iri.


Momy cikin tsawa tace, ke!zancimiki wallahi sakarya kawai sha_shar banza, karna k'arajin wannan zancen a bakinki kona 6atamiki rai wallahi.

Sakina tace, Allah ya baki hakuri momy ban fad'a danna 6atamiki raiba.

Momy taja tsaki sannan tace, tafi can kibani waje sai iya ladabi kamar gaske, nawa kika samu ciromin ?

Momy bank d'in da layi saosai shiyasa na dad'e ammah abin yaban mamaki sosai me akayi da million d'aya momy ?yaushe aka cire?

momy tace, babu ruwanki bani sakona.

Kud'in ta mik'amata sannan tace, yauwa momy yau na had'u da kawu a banki yace na gaisheku, yana tacemin sailuba!sailuba ammah sam bangane da ni yakeba sai da wasu sukamin mgn.

momy tace, hym!muna amsawa.

sakina takuma cewa, yauwa momy meyass akadena k'irana da sailuba aka kuma sakina?

Momy tace, Dangin ubankune da wannan kinibibin da tsohon cikinki babanku yarasu bayan na haife sukace wai asamiki sunan 'yar autarsu sailuba nikuma naga bsbu wanda yamin rainon cikinki balle rainon goyo shiyasa nake k'iranki da sunan da na za6a bawai za6insuba.

Sakina tayi murmushi tace, kai momy ai da kin barsu da ba'a rabamin sunaba.

momy tace to uwata. tare da harararna, ni tashi ki d'aukomin jakana driver ya kaini gidansu shahida.









***
**
*

Karima dake zaune ita da wata k'awarta aminiyarta fauzan, alokacin da karima ta gm waya sai fauzan ta kalleta tace,

wai ya ake cikine ?
karima ta kwashe duk sharrin da suka lak'anawa izzatu ta fad'awa fauzan, sannan ta k'ara da ceea, ammah kinsan me?haryanxu bai saketa ba tanan a gidan munafuka.

fauzan tayi dariya tayi shewa tace, lallai ke wawuya ce waya fad'amiki hk ta barshi ai tini ta gm dashi da asiri, idan zakice zaki jira sai ta ft sannan zaki shiga to ai kin tabka babban *KUSKUREN* ai kawai malama tunda har kinsamu za'asashi ya aure dole to ki shiga kawai inyaso k'yasan yadda zakiyi dh baya ammah idan kika tsaya kallon ruwa to kwad'o zai miki k'afa.

Karima tace, hkne fa kou?sis


**************************





Rayuwar izzatu abin tausayi komai yakuma jagulewa babu abinda yake had'ata da safraz


Momy tace, Dangin ubankune da wannan kinibibin da tsohon cikinki babanku yarasu bayan na haife sukace wai asamiki sunan 'yar autarsu sailuba nikuma naga bsbu wanda yamin rainon cikinki balle rainon goyo shiyasa nake k'iranki da sunan da na za6a bawai za6insuba.

Sakina tayi murmushi tace, kai momy ai da kin barsu da ba'a rabamin sunaba.

momy tace to uwata. tare da harararna, ni tashi ki d'aukomin jakana driver ya kaini gidansu shahida.









***
**
*

Karima dake zaune ita da wata k'awarta aminiyarta fauzan, alokacin da karima ta gm waya sai fauzan ta kalleta tace,

wai ya ake cikine ?
karima ta kwashe duk sharrin da suka lak'anawa izzatu ta fad'awa fauzan, sannan ta k'ara da ceea, ammah kinsan me?haryanxu bai saketa ba tanan a gidan munafuka.

fauzan tayi dariya tayi shewa tace, lallai ke wawuya ce waya fad'amiki hk ta barshi ai tini ta gm dashi da asiri, idan zakice zaki jira sai ta ft sannan zaki shiga to ai kin tabka babban *KUSKUREN* ai kawai malama tunda har kinsamu za'asashi ya aure dole to ki shiga kawai inyaso k'yasan yadda zakiyi dh baya ammah idan kika tsaya kallon ruwa to kwad'o zai miki k'afa.

Karima tace, hkne fa kou?sis

fauzan tace, ni na d'auka ke wayis ace dod'isce mtsss


Hk suka dinga hirarrakinsu du akan izzatu.






**************************





Rayuwar izzatu abin tausayi komai yakuma jagulewa babu abinda yake had'ata da safraz ko giftawarsa ma yanxu tadena gani sai dai wani lokacin taji motsacinsa hk sukeciki har tsawon sati d'aya, kusan kullum sai tayi waya da iyayenta ammah bata bari sun fahimci tana wt matsalaba, sakina da shahida suna zuea mata sosai sun shak'u da ita sosai wani lokacin harda shahid, yanxu harta saba da rayuwarta a hk ta rage damuwa wani lokacin tayi kallo ko cht hkm k'awayenta suna kawo mt ziyara duk da ba wasu k'awayene da itaba dg sumayyah, Aisha sai firdausee k'awayenta ne na university.





Izzatu tana zaune a falo tana kallon tashar TV ta Arew24 sai jin sallamar mami tayi, zuwa tayi ta tarota cikin farinciki da jin dad'i,



Bayan sun gaisa ta kawowa mami kayan motsa baki, sun dad'e suna hira  sannan mami ta kalli izzatu tace,

izzatu nazone inason muyi wata magana.


Dub!k'irjin izzatu ya buga, "kar dai safraz ya fad'awa maminsa abinda ya faru"? izzatu ta fad'a a rabta.



~Sunnu_sannu kwana nesa muje zuwa page 8 yau da gobe batabar komai ba~👌🏻


0 comments:

Post a Comment