❣🤦🏻♂ _*KUSKURENA*_❣🤦🏻♀
```{The story is Interesting! Attractive! Impressive! to cut a long story the story is a fascinating story the readers will entertain and enjoy it.} ```
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
***************************************
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
_*BY*_
©, _*RAMLERT Y SALIS*_
_*(NAZRA /FIRRAM )*_
~08164530838~✍🏻
_Wed , Jan 16 , 2019._
_*Page 8......*_
A tsorace izzatu ta d'ago ta kalli mami, alamun tashin hankalin suka bayyana a fuskarta.
Mami tace, inason ki nutsu izzatu dan abinda zan fad'amiki ba lallai yamiki dad'i ba.
Jitayi kamar falon yana juyawa zuciyarta sai harbawa takeyi "wato abinda take zargi ya tabbata mami tasan zancen kenan" izzatu take sak'awa a ranta.
Mami takuma cewa, Izzatu nasan kina da ilimi kuma da hankali, ki k'ar6i abun da zan fad'amiki a matsayin k'addararki karki tashi hankalinki, kinga a yau kuke da wata d'aya harda sati biyu keda safraz dayin aure, safraz zai k'ara aure nan da sati biyu masu zuwa izzatu kiyi hakuri badan baya sanki ba sai dan hk Allah ya k'ddara.
A firgice izzatu ta ware manyan idanuwanta tana kallon mami, nan da nan kuwa hawaye ya suka fara rolling into her checks. muryanta na rawa tace, ma mi wal lahi nafad'amasa ba……
Sai mami tayi cuting d'inta da cewa, pls izzatu wipe your eyes wallahi safraz shi da kanshi bayason k'ara auren da bayadda zaiyi ne shiyasa. nasan kinaso ki cemin kin fad'a masa bakyason kishiya kou?kiyi hakuri ki saurareni zaki fahimta insha Allah.
Sai alokacin izzatu ta fahimci ba abinda take tunanin mami zata fad'amataba, Amma hankalinta ya kasa kwanciya sabida zancen safraz zai k'ara aure.
Mami ta kalleta tace, Nice da kaina na bashi umarnin sai ya k'ara aure ammah ba wai shine yace zai k'ara da kanshi ba, kuma nima banyi hk danna k'untata mikiba izzatu, wallahi nima umarni ne na yayata bayadda na iya dashi nasan kinsan momynsu sakina yayata mu kad'ai ne awajen iyayenmu izzatu, akwai yayar sakina sunanta karima itace 'yar aunty adama ta farko yarinyar tanason safraz tun kafin ta tafi karatu england to hkn ne yasa aunty adama tazomin da zancen tun kafin aurenku keda safraz ba yadda na iya nima na tuntu6i,safraz da zancen ammah ya nunamin shi bayaso ban k'ara yi masa zancen ba har lokacin daya had'u dake kuka fara soyayyah alokacin da zancen aurenku ya bayyana sai aunty adama ta nunamin 6acin ranta sosai akan dole safraz ya auri 'yarta sakina tanason mu k'ulla zumuncin, hakuri na dinga bata akan cewa ta barshi ya aureki idan yaso dg baya sai ya auri karima tunda anriga da anyi maganar aurensa da ke kuma shiya ganki yce yanaso, akan hk muka bar zancen izzatu ni nasan safraz bayason karima ko kad'an ammah bayadda zanyi auty adama ta fahimceni shiyasa nabi umarnin ammah nima badan nasoba sabida itace tazamamin uwa alokacin da muka rasa iyayenmu.
Nasani cewa na cutar da safraz nayi masa dole kema nashiga rayuwarki wasu ma zasuyi tsammanin wani mummunan abine yasa mijinki k'ara aure tun baki dad'e agidansa ba, ko ajiya dana,k'ira safraz nace,masa ya fad'amiki cewa yayimin wallahi shi bazai iyaba sabida zai tayar miki da hankalin kuka ya dingayimin sosai wai bayason abinda zai sa ki damuwa kuma zakiyi tunanin yaudararki kawai yayi ya aureki, nima nashiga damuwa sosai ganin halin daya shiga, anan na sanar masa dama niyafi dace nazo na fad'amiki ammah na masa alk'awarin indai hankalinki ya tashi kuma baki amince ba to zan janye umarnin danayi masa na auren karima dan ku zauna lpy, izzatu ina rok'onki dan Allah ki bani goyon baya akan zancen nan, nasani inhar na baki labarin irin halaccin da aunty adama tamin a baya to kema zakiga cewa bai dace na juyawa buk'atarta ba.
Tabbas aunty adama tayi matuk'ar k'ok'ari akaina, Iyayenmu bawasu masu k'arfi bane talakawa ne, Muna rayuwa cikin rufin asiri akaha har akayiwa aunty adama aure ya rage saura ni kaid'e alokacin ina da shekaru12, Awata damuna da akayi a can baya watarana akayi ruwa mai k'arki da dare fi sai d'akin da ummanmu da babanmu suke kwance ya rushe akansu wannan shine sanadin rasuwarsu.
Bayan anyi arba'in d'insu aunty adama ta sanar da dangin mahaifanmu cewa tanason ta d'aukeni na koma zama a wajenta hk akayi ba wanda ya hanata mijinta ma ya amince.
A gabanta na cigaba da rayuwa tana 'yan sana'o'in hannun dasu take biyamin kud'in makaranta har na gama primary na shiga secondary, Muna cikin rayuwa ahaka sai Allah yayiwa mijinta rasuwa.
A hk muka koma gidan yayan babanmu shima dai bashi da wani k'arfi kusanma aunty adamace take ciyar mu ni da ita domin matansa basa bamu abinci ko yaushe ga wulakanci da rashin mutunci kala_kala, aunty adama ta kuma yin wani auren ammah wanda ta aura yana da mata guda biyu itace ta uku, bata dad'e dayin aureba namma ta d'aukeni na koma gabanta da zama domin tasan irin zaman gidan yayan babanmu, to muna cikin hk har naje secondary aji hud'u ammah sai dai yaran mijinta sun takuramin sosai agola suke cemin, 'yar talakawa wai su nufinsu ni amakarantar gomnati nake sukuma amakaranta kud'i suke, wani lokacin sumin duka sosai, idan aunty adama tayi mgn mijinta yace shifa baxa'a takura yaransaba su da gidan ubansu, kullum cikin matsalan muku da aunty adama ta gaji sai ta fara ramamin duk yarinyar data dakeni, shima mijin idan matansa suka fad'a masa sai yazo ya daki aunty adama hk zamu zauna,muyi kuka a d'aki har mu gaji, A na hk watarana badawo daga makaranta ina shigowa suka fr tsokana ta dasukaga namu shuru sai duka a nan sukamin duka sosai dukkansu 'yammata kamarni 15 years, a ranarma aunty adama ta ramamin, dana fita zanje kanti na siyo aunty adama fulawa domin tanayin fanken siyarwa da safe duk dan inyi karatu, sai suka bini hanya sukamin dukan tsiya nayi wujiga_wujiga har kaina ya fashe abinka da farar fata tuni fatata tayi rud'u_rud'u, a hanya na fad'i sai kawoni gida akayi.
Ko wanne asibiti aka kaini sai suk'i k'ar6ata wai dole sai da 'yan sanda saboda ciwokan dake jikina, aka muka dinga wayo asibiti zuwa asibiti a k'arshe dole sai da Aunty adama taje police station ta d'au d'an sanda sannan aka dubani.
Bayan angama komai anrubuta min magani an sallameni, Sai 'yan sandan suka tambayeni wayamin hk, Na fad'amusu , sukace ai dole sai sun kaiwa mahaifin yaran dasuka dakeni sammaci, A nan aunty adama tace dasu a'a ai 'yan'uwane ta yafe zatayiba masa mgn da kanta, 'yan sanda sukak'i dole hk suka bimu har gida.
Alokacin da muka iso gida shima mijin aunty adama a dai_dai lokacin yana gida, ba yadda aunty adama batayiba ammah sai da suka tafi dashi, wajen k'arfe 10 na dare sai gashi ya dawo nan ya dingawa aunty adama masifa wai ta d'ebo masa 'yansanda akan k'anwarta wai dole sai dai ta za6i d'aya ko dai ta maidani gida ko kuma ya saketa, da safe yakuma shigowa d'akinta ya tambayeta tace masa ita sai baxata iya maidani gidaba inhar yaga bazai iya zama da ita tare daniba to shikenan ya sauwak'e mata.
Hk muka koma gidan kawu da zama yau da dad'i gobe babu dad'i, Duk wanda ya fito neman auren aunty adama sai tace masa inya amince zata d'auke ammah duk yawancinsu saisu k'i, dg k'arshe tace bazatayi aureba har sai na kammala karatuna nayi aure sai itama tayi.
Ita ta ringa d'aukan nauyin karatuna da sana'o'in hannu da takeyi har naje 2 hundred level a university, Anan ne na had'u da Abbansu safraz alokacin shikuma lecturer a university d'in, Ya taimakamin sosai ina karatu mun fr soyayyah har naje 4 hundred level ina cikin watan k'arshe a school aka sa ranar aurenmu dashi, shi kuma alokacin ya k'aro karatu ya tashi dg lecturer duwa Dr.
Akawana Atashi babu wuya na kammala karatuna na fita da first class, University dana gama karatu acikinta su suka d'aukeni aiki, Anan rayuwa ta kuma canzs mana,muka fr mantawa da wahalhalun rayuwa domin na fara d'aukan albashi every my month ga Dr hashim shima yana min kyaututtuka sosai, Ahk har lokacin bikinmu yayi aunty adama tayi bajinta sosai da sosai domin tamin kayan d'aki da kayan kitchen masi tsada da kyau da sauran kayayyaki dukda shima Dr hashim yabani kud'i masu yawa, hk akayi biki aka kaini gidana.
Nayi haihuwa ta farko safraz kenan, sai bayan shekaru biyar bayan na haifi safraz sannan aunty adama tayi aure, albashina biyu muke rabawa ni da ita duk wata, safraz yana sa wajen shekaru 13 sannan aunty adama ta haifi karima, bayan 2years takuma haihuwar sakina tunkafin a haifi sakina mijin aunty adama ya rasu da wata biyar nima na kuma haihuar shahid da shahida.
A lokacin Abban su safraz ya fara siyasa lokacin kud'i suna shigomin sosai hakan yasa na ginawa aunty adama babban gida ta dawo ciki ita da yaranta biyu, karima na kammala secondary na d'au nauyinta ta tafi england karatu duk dan inason aunty adama tayi alfahari dani kamar yadda naji dad'in kulawar da tayi akaina,
Mami ta kalli izzatu tace, izzatu wannan shine labarina wanda akwai abubuwa da dama wanda na tak'aicesu kyautatawar da tayimin ina yarinya izzatu wannan yasa bazan iya kallon idonta nace a'a ba, mutum ce me zafi wani lokacin shiyasa nakeson inbita a sannu dan wallahi mutane da yawa sun d'auka itace ta haifeni, pls do me a favor, kowa da irin k'addararsa mu kinga munyi rayuwar wahala a baya ammah yanxu kinga _*BAYAN WUYA SAI DAD'I*_(my fomer book).
Nasan kwanciyar hankalinki shine samun nutsuwar safraz, keda safraz ba banbanci awajena a yanxu izzatu.
Sai izzatu taji kwarin gwuiwa sosai a ranta jin labarin mami datayi, sai tasa a ranta itama wannan itace k'addararta , sai taji a ranta tabbas tayi babban _*KUSKURE*_ zaman da sukeyi da safraz ba ruwan wani da wani kamata yayi ta gyara _*KUSKUREN*_ ta tunkafin wata taxo ta k'ace mata miji wanda tana da tabbacin yana masifar sonta.
Da kwarin gwuiwan izzatu ya d'ago ta kalli mami tace, mami kinfi k'arfin ki nemi alfarma koki rok'eni, umarnin kawai zaki bani kuma dole nabi domin uwace ke wajena, mami namiki alk'warin zaman py dani da karima da safraz insha Allah. Ke uwace ta gari kuma wacce za'ayi alfahari da ita domin kina k'ok'arin rama alkhairi da alkhairi tsakaninki da momynsu sakina tabbas ta cancanci kiyimata fiye da hk ma, bayan nanma karima koda bayan babu momy kece me za6a mata miji, ina alfahari da wannan had'in mami Allah ya tabbatar da alkhairi.
Mami taji dad'i sosai aranta da kalaman izzatu tana murmushi tace, izzatu naji dad'i sosai gaskiya Allah ya miki albarka kinji Allah ya baku zaman lpy, nayi farinciki sosai izzatu Allah ya miki albarka.
Sun dad'e tare sai yamma mami tabar gidan, shikuwa safraz sam hankalinsa kasa kwanciya yayi a wunin ranar ga ayyuka masu mahimmanci a office ammah ya kasayi tunaninsa d'aya idan izzatu yaji zancen nan mezai faru, koda ya taso dg office gidan mami ya nufa domin sanin halin da izzatu ta kasance lokacin sa mami ta fad'a mata.
A main falo ya tarar dasu dukkan su har Abbansu, dasuka gaisa Abbansu ya kalli shahid da shahida yace, twins give me a space. Tare suka bar falon sannan Abba yayi gyaran murya ya kalli safraz yace, Am safraz naji dukkanin zance dg bakin mahaifiyarka but am not satisfy i need explanation i am listening to you.
Safraz da bashida za6i daya wuce ya kare mahaifiyarsa ya d'ago yace, Hkne Abba there's relationship between karima and i since before she want england to study, but i think she don't marry me if she cameback this why i get marriage with izzatu but i still love her i want to marry her that all.
Abba yace, hym!i understood but is too early to get marriage again now, because you only spented one month and something with izzatu's married now you have to stop like one year or so.
Safraz har ransa yaji dad'in abinda Abbansa ya fad'a ammah sai ya tuna mami sai ya kalli Abba yace, Abba izzatu is a easy going lady she already understand my point and accepted, but karima is expecting i am try to deceive her pls Abba allow me to marry her now they will leave peacefully insha Allah.
Abba yace, shikenan is allright i can't reject your request safraz you have a chance to marry more then two wavies, But try to do justice between them don't be a selfish man, may Allah assist you.
Safraz yace, Amen Abba.
besamu damat tambayar mami ba saboda Abbansu yana gurin hk ya tafi.
Safraz yana zuwa bakin k'ofar falon zai shiga yaji wani k'amshi ya doki hancinsa, Labulene ya fara yimasa sallama da wani daddad'an k'amshi, da sallama ya shiga ammah sai ya tsaya turusa ya kasa gaba ko baya, Izzatu ya gani ta fito dg kitchen d'in dake falon d'auke da kayan abinci a hannunta, sanye take da mini skirt bekai gwuiwaryaba sai 'yar wata top itama bata rufe cibiyartaba me k'aramin hannu ga gashin kanta ya sauk'o kan kafad'unta sai shek'i yakeyi, fuskarta d'auke da simple makeup.
Deining taje ta ajiye kayan da yake hannunta ta taho da gudunta tana cewa:
Oyoyo reality, tana isowa ta rungumesa so tight sannan she kiss him in his rehead and check.
~Sunnu_sannu kwana nesa muje zuwa page 9 yau da gobe batabar komai ba~👌🏻
0 comments:
Post a Comment