Blogroll

BANNER 728X90

Tuesday, 16 April 2019

Kuskurena Page 12 - ISMAIL SANI


❣🤦🏻‍♂ _*KUSKURENA*_❣🤦🏻‍♀
 
{The story is Interesting! Attractive! Impressive! to cut a long story the story is a fascinating story the readers will entertain and enjoy it.} 


❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
**************************************
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣



               *BY*

 _*©, RAMLERT Y SALIS*_
         
             ~08164530838✍🏻~






*No part of this book maybe an object of privacy✖*


_Tues , April 16  , 2019._

_*Page  12......*_



Kamar walk'iya sakina tayi saurin fitowa dg toilet tayo falon, ganin Izzatu na k'ok'arin kai cup d'in lemo bakinta yasa ta arta dawani bala'in gudu tanufi Izzatu.
 Cikin zafin nama sakina tasa hannu ta buge kopin wanda tuni izzatu hartasa sashi bakan    bakinta tana k'ok'arin kur6ar lemon, Tas ! Kakeji k'aran fad'uwar kopin nan ya tarwatse a wajen lemon kuwa yad'an zubarwa izzatu a jikinta.
Sakina kirjinta ta dafe tana maida numfaahi domin hankalinta ya gama tashi, da izzatu tasha da tasan komai yariga yadagule amma sai ta godewa Allah da hkn bai faruba tana maida numfashi ta d'ago ta kalli Izzatu.
 Izzatu kuwa ta tsaya sororo tana kallon abun mamaki, sakina tace, Aunty menace miki d'azu , karki kuma cin duk abunda yafito a hannun wad'annan masu aikin, kiyi tunani sosai akan abunda yafaru dake dole wasuke ne suka shirya kuma wanda sukeda kusanci dakene So ki sallamisu kawai dan kar wani abu yakuma faruwa.  Sakina aranta tace"Bani da damar tona asirin mahaifiyata dana fad'amiki gaskiya aunty amma zan baki kariya iya iyawata kafin Allah ya tona musu asiri dan Allahba azzalumi bane".
Izzatu tana dariya tace, Sakina kin bani dariya wlh sai kace wanda zasu samin kuba acikin abinci, Karki wani damu su sukemin girki koyaushe, abundaya faru kuma yariga yawuce ai dukda cewar wanda yavkullamin sharrin ba hk yasoba so yayi ya raba aurenmu nida safraz amma kinga ikon Allah komai yayi dai_dai, Kizo muci abincin nan kawai babu wani abu dazai faru.

Sakina takalli izzatu tace, hne Aunty amma kije d'aki tun d'azu uncle yanata k'ran wayanki dakika fita, inkin dawo sai muci abinci.

Izzatu tayi hanyar d'akin da sauritana dingisa k'afa.
Tana tafiya sakina ta tashi da sauri ta tattara duk abincin tayi waje dazu duk ta juye a kwandon shara lemukan kuwa suma duk ta zubar, sannan taje kitchen ta wanke kwanukan sosai, Inda cup d'in ya fashe ta share ta goge wajen sannan ta koma kitchen ta fara shirya musu abincin rana julop d'in taliya tayi da kifi da lemon kwakwa, Har tazo deining ta jere kayan Izzatu bata dawo falon ba.


Itakuwa uzzatu koda tashiga d'aga ta duba wayar bataga misscalled d'in safraz kamar yadda sakina ta fad'amataba sai tayi tunanin ko sakina ta taga tacemasa bata kusane kawai sai taje toilet tacire rigan jikinta daya 6aci ta watse ruwa,  Bayan tagama shiryawa cikin riga da sikita na atamfa kanta ko d'an kwali babu tayi hanyar falo sai kuma ta tuna, dawowa tayi ta d'au wayanta tayi dialing number safraz wanda tayi saving da suna _MY RIGHT CHOICE_ kan gado ta fad'a suka fara wayarsu wanda babu komai acikinta sai kalmomin k'auna dasuke fad'awa juna da bayyanawa juna yadda sukayi missing junansu.

  Sakina data kammala komai sai tayo d'akin dan taga meyasa izzatu ta dad'e hk, Rungume da fulo ta ganta kan gado tana wani lumshe ido.
  Sakina tace, Aunty nagaji da jira nidai zaje inci abincina nafa jin yunwa, har sakina tayi hanyar fita dg d'akin izzatu ta dakatar da ita.

  Tacan 6angarenne safraz yaji abunda sakina  take cewa shiyasa yacewa izzatu taje taci abinci,  Izzatu ta wani shagwa6e murya tace, My sweet kaima inason kayi lunch yanzu kaji.
Safraz  yace, to my queen kici abinci sosai ki kulamin da kanki, tace, tom realityna tayi mai kiss sannan ta kashe wayan.




A6angaren su Abu masu aiki kuwa, mamaki ya damesu musamman Abu domin ma'u dama tacire hannunta aciki dama shirin tafiya takeyi tabar gidan sai gashi tun kafin ta tafi izzatu tazo ta sallamesu.

Kai tsaye gidan momy su Abu suka tafi Afalo suka sameta a zaune tana kallo, Tayi mamakin ganinsu amma sai tayi tunanin ko aikin datasasune yayi kyau sukazo sanar mata, cikin fara'a ta k'ar6esu suka gaisa.

Tunkafin momy tace komai Abu ta kwashe komai ta fad'a mata, Nan momy tacika da matuk'ar mamaki har tanayin zufa.

   Momy fuska babu annuri ta kalli Su Abu tace, Kun tabbata bata gane wani abuba? Abu tace, wlh hajiya babu wani Abu damuka bari ta fahimta Abincin safema mumuka dafa kuma dashi suka karya, to da ranannan ne dai kawai tazo ta sallamu tace badan munyi mata komaiba hk kawai.

 Momy ta girgiza kai tace , lallai wannan yarinyar tawuce tunanina kodai bokantane yak'irata ya fad'amata kar taci? Hmmm ! Naga ikon Allah, kun tabbata safraz bazai dawo da ranaba kar muje ya dawo yaci abincin musha uku?

 Abu tace, Ah ! hajiya ai sam baya dawowa da rana, Abincinma d'an dai_dai iya cinta muka dafa dan ka taci tarage wani yaci.

Momy tace, To yayi , Allah yasa taci matsiyaciya kawai idan ma bataciba saina 6ullomata   ta wata hanyar, Kutashi kuje Abunku sai na nemeku.

  Nan suka mata sallama suka tafi.
Suna kan hanya ma'u ta kalli Abbu tace, Sai dai ta nemeki wlh dg yau babuni babu lamarinku.

   Abu tace, hmmm kaji dashi kai kad'ai.

 Dama idan baku mantaba, Su Abu mazane na mataba, Kasan cewarsu 'yan daudu shiyasa zaiyi wahala kaganesu idan sukayi shigar mataa
Wata rayuwace me cike da d'umbin soyayyah da kulawa  tashiga tsakanin safraz da izzatu, kullum cikin farantawa juna suke, Koda izzatu ta fad'wa safraz ta sallami masu aiki baice komaiba saima murna da yayi domin yana ganin hkn zaifi yimasa dad'i ya sake shida matarsa.



Momy kuwa tazuba ido taga wani abu yabiyo baya amma shuru har tsawon kwana 3 hkne ya tabbatar mata cewa izzatu bataci abincin da'akasa poison d'inba ba k'aramin 6aci ranta yayiba, Sakina kuwa kwata kwata tadena zama suyi hira ita da momy kullum tana d'akinta hk kawai sai tadinga jin haushin momy tanajin zafi da rad'ad'in abinda taso aikatawa hkm karima idan ta k'ira bata d'agawa ko tayi mata mgn ta social media bata reply.
Akwana atashi ya rage saura kwana 3 kacal d'aurin auren Safraz da Karima, Duk izzatu tashiga damuwa amma duk da hk safraz yafita shiga damuwa kullum cikin rarrashinta yake sam bayason damuwarta da da yadda zaiyi afasa auren da yayi domin shima bayaso ko kad'an tsawon sati 1 kenan baya zuwu office yana manne da izzatu kullum cikin rarrashinta yakeyi har ta manta da duk wata damuwa idan kaga yadda sukeyin rayuwa abun abun sha'awa.
Safraz ne a tsaye gaban madubi daga gani daga wanka yafito yana shiryawa, itakuma izzatu tana kan gado ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tanata danne dannan waya.

Safraz yace, Baby har yanzu bakiga wayana ba kou? To kodai a waje na 'yarne.
Izzatu ta ajiye wayan hannunta ta kalleshi tace, a'a bayan fitankama daka dawo da wayar a hannunka sai dai ko wani wajen ta fad'a gashikuma a silent take ko ank'ira baza aji ringing ba matsalan.

Safraz yace wallahi kuwa tana silent sai dai kicigaba da dubamin kafin nadawo, Amma kibani aron wayanki idan na fita dole zanyi amfani da waya, My love kidubamin nawa pls kafin nadawo dan nasan anata k'irana.
Har bakin motansa ta rakashi ya shiga yaja yatafi sannan ta dawo ciki , Abun mamaki tana shigowa falon ta hangi wayartasa a k'asan deining table murmushi tayi tace, ko na k'irashine ya dawo ya d'auka har zata k'arashi sai kuma kawai ta fasa.


Kai tsaye safraz gidansu ya nufa, a falo ya tarar da maminsa da momy sunata hidimar biki hk kawai yaji ransa yayi masa bak'i sam shi mantawa yakeyima wai jibi za'a d'aura masa aure da wata karima.

Bayan sun gaisane mami ta kalleshi cikin kulawa tace, Ina k'ranka a waya tun safe amma baka d'agawa meyasa?

Safraz yace, Wlh mami wayan nawane muka nemeta muka rasa a falo yanzuma sai wayan izzatu na d'auko dazan fito domin har yanzu ba'a gantaba.

Mami tace, hb ni nasan dama akwai dalili kaje wajen Abbannakune ?

Safraz yace, Yana nema nane? Bari naje 6angarensa.

Mami tace,  yanzu kam yafita sai dai zuwa gobe da safe.

Tunda suka afara magana momy taji cewa wayar izzatuce a hannun safraz taji wani dad'i a ranta dan tayi wani tunani tasamu damar kulla wani sharrin a yanxu.

A dai_dai lokacin karima tashigo tana wani rangwad'a da karairaya ganin safraz a falon, Abunka da mara kunya ganin momynta da mami bai hanaba sai tazo kusa dashi ta zauna.

Big bro barka da fitowa, Karima ta fad'a tana wani wawwara ido ita bata yaddaba tana fari da ido.

Wani haushinta ne ya kama safraz kamar yatashi ya bar wajen amma ganin akwai iyayensu awajen sai kawai ya daure yace, Yauwa karima  sauk'an yaushe ?

Nan takuma narkewa jin yana tambayan yaushe ta dawo tunaninta ai duk acikin damuwa da lamarintane yasashi yayi tambayar, Cikin kinibibi ta shagwa6e murya tace, Am d'azu da safe na iso lokacin da na sauk'a a Nigeria inata k'ranka kazo airport ka d'aukoni amma kak'i kayi receiving call d"ina why dear ?

Safraz da tuni haushinta yacikashi yace, Okay my phone got lose since morning, Wannan ma wayan my choice d'inace not mine yayi nuni dawayan dake hannunsa.

Wani irin haushi taji dataji yacewa Izzatu my choice wato magana yakeson fad'a mata kenan, tace hmm aiko ba yauba inna k'iraka baka d'agawa kuma kai baka k'irana why?

Safraz daya fara gakiya da maganganunta sai yayi k'asa_k'asa da murya ta yadda su mami bazasujiba yace, Wannan kuma bani da lokacinkine you know? Ya d'aga mata kira.
Takaici ne ya kama karima tun kafin takuma cewa komai safraz ya mik'e ya fice dg falon.

Mami ma ta tashi ta shiga d'akinta zata d'auko wani Abu, yarage falon dg karima sai momynta.

K'asa_k'asa momy ta fara cewa karima, ai bazama zakiyiba Tunda wayarta tana hannunshi kitashi kishiga ciki ki rubuta text message na Sharri iri_iri amatsayin kwartontane yaturo mata baisan cewa wayar tana hannun mijintaba  kidinga tura masa Sai momy tazo kusa da karima ta fara rad'a mata maganganu a kunne.





~Sannu_sannu kwana nesa muje zuwa page 13 yau da gobe batabar komaiba👌🏻~


0 comments:

Post a Comment