NA Benazir Ummar (NWA) (BASED ON A TRUE LIFE STORY) .
sAI NI KUMA ABDULLAHI YAHAYA SAAD DANA KAWO MUKU NACE cewa muyi saurare lafiya
(wannan labarin gaskiya ne, yafaru, sai dai nacanja gari, suna dakuma wasu abubuwan, I just hope it should be useful) .
Wawan birki naja, gabana ya tsinke ya fad'i, numfashina na kokarin daukewa, tunanina ya tsaya cak, na sa hannu na murza idanuna don tabbatar da cewa ba bacci nakeyi ba, bakuma mafarki nakeyi ba, na kuma tabbata ba gamo nayi ba, toh ko dai gamon ne? A tarihin rayuwata nasan India da kyau, nasan larabawa da kyau nakuma san jinsin Fulani da shuwa harma hausawan kasanmu da kyau, sai dai a film ko labari, tadi ko wasa, bantaba ganin halittar 'Da namijin dake gabana ba, nayi ayatul qursiyu natofa ajikina, gashi dai bai matsamin akan hanyan ba balle nasa ran wucewa, da alamu ya bugu iya buguwa, ya sha wani Abu. "innalilahi wainnailaihi rajiun" na ambata wa kaina a lokacin Dana kara hada ido na danashi, dogo ne , fari ne ,saidai ba fari can ba akwai alamun dishewa a alamarinsa, yana da dogon hanci, gashin kansa ta kwanta luf tamkar na bahaushen balarabe, idanunsa manya ne,, saidai Wanda bature kekira da sexy eyes, a lumshe suke tamkar yanajin bacci gasu farare sol, innalilahi wainna ilaihi rajiun shinaci gaba da ambata dasauri najuya akalar motar dan barin gurin, zuciyata takasa amincemin cewa mutum ne ba aljanniba, . ina tafiya ina waigawa don tabbatar dacewa baya biyoni Nashiga uku ni Nadra nayi gamo da katar!!!!! Dasauri na nufi gida, maigadi yabude min gate nashige, tsantsan rikidewa mantawa nayi ban rufe kofar ba balle nacire key din, dakina na nufa kai tsaye, Allah ya taimakeni mammy( mahaifiyata) batanan narufo kofan nafada kan gadon, . na lumshe ido ina tunanin halittan da nayi, nidai banyi gamo ba, mutum ne zahirin gaskiya, ahaka bacci ta kwasheni ban farka ba sai magrib, na dauro alwala nayi sallah,na mike na fito falo inda naga mammy na shirya dinning abinci abamama(mahaifina, yadda natashi naga yayuna nakiranshi), "ke kuma wani sabon salo kika samu na bacci dayamma!, .
ko dai jikinne?" " a'a mammy, wlh nadawo gun tela ne, daga kwanciya ashe bacci ya kwashen," "toh ai saiki zo ki nutsu kisha ruwa, kullum ke zakiyi azumi amma kina mantawa , bayan nace miki manzon Allah SAW ya umurcemu da mu gaggauta shan ruwa, mu jinkirta suhur, amma banda ke, ki kiyayeni fa" "oops, mammy naci dabino a daki AI" na nufi hanyar kitchen don maganan gaskiya na manta azumi nakeyi, tsantsan damuwan Dana Shiga yau, kuma kasanchewar yau baayi rana ba, nidai na nufi talatu ta hada mini kayan shan ruwa nazauna zanci, ikon Allah saikuma nagagara CI, tunanin bawan Allah yadamen, yakamata na koma gun ko zansameshi, toh amma ko ma shi giyan wake baza'a barni nafita ba, tuni dabara yafado min, namike na leka falo abamama nacin abinci, na zauna gefensa ina murmushi, shima murmushin yakeyi "lafiya auta?, ko jikin ne? " . "ae daddy ciwon kai ne shine nakeso ko zanfita na leka chemist" "subhanallah, ya za'ayi kije ke kadai?, ina kamal ? kirashi yazo yakaiki, shi ko wani dai a samarin gidan nan!" nayi murmushi nace "toh" jikina na bari naleka daki nadauko mayafi na da mukullin mota na, Nazo nawuce, fannin samarin gidanmu na nufa, su rai shida narinka buga musu dakuna, Wanda dama dakuna shida ne a bq din, kowa da nasa, yaya kamal bayanan donhaka na buga na ya amir, yana shirin fita asham , . "ya amir abamama yace ka rakani asibiti" ya kallen ta gefen ido batare da yayi magana ba yana kokarin rufe dakin nasa , na maraice kaman zanyi kuka, bai amsa ba nabi sawunsa, daman ban sa araina zai kulani ba, miskilancinshi daban ne, nidai inzai fita dani shikenan, motar sa yanufa nabi bayansa kaman agwagwa da yayanta, "wani asibiti?" "reemee" dama a gida nayi analysing cewa daga gidanmu wani asibiti zanbi Wanda dole nabi wannan hanyar naganshi? .
Nagano remee ne kawai, aikuwa muna yanko kwanar fita daga layin , hasken wutan titin ta haskoshi yana zaune sanye da jallabiya, gabana ta tsinke ta fadi, ba shiri nace "yaa amir ka tsaya" yaja birki tare da juyowa alamun tambaya, ban kulashi ba nabude kofan motan, dasauri na nufeshi, bashiri ya amir yabiyoni kaman na zauce, ina zuwa nasa hannu nataba shi, ya Allahu, mutum ne, ba aljanni ba, dagowa yayi yakallen idonsa tayi jaa hasken wutan ya haskashi sosai, gabana bata bar fadiba, cikin sassanyar murya mai zaki wanda kunnena yajiyomin yace "lafiya?"jinayi an janyoni da karfi aka wurgani mota "ya amir ka tsaya mudaukeshi, ba mahaukaci bane , .
wallahi mutum ne, ba aljanni bane" Ba tare da ya saurari kalamuna ba ya jefani motar, wani bakin ciki naji ya gulleni a rai hawaye ya soma ruwa a idanuwata ina kallonsa har muka wuce, yaa Amir in banda jan tsaki babu abinda yakeyi nasan ranshi ya baci anma nashi kadan ne akan nawa, da zai auna bakin ciki na da nashi da zai san cewa shi wasan yara yakeyi, rai a bace nace kaina ke ciwo akaban magani muka biya kudi muka fito, a hanyan komawa haka nayita lekawa ki zan ganshi. .
YA WANNAN FA? MU CIGABA KO MU TSAYA ANAN MU CHANZA WANI?
=== CIWON IDANUNA 2 === .
A hanyan komawa haka nayita lekawa ki zan ganshi, aikuwa yana kwance akan wata kujera kamar wani sarki muna shiga gida mammy tana falo zaune dasu yaa kamal duk sunyi jigum suna jiranmu ganina yasa tamike da hanzarinta "zo auta na, meya faru? sun baki magani? kan yadena ciwo?" . na lumshe ido jim yadda ta kamo kaina " toh mammy kin rike kan" dasauri ta sake tana tofa min addua, mikewa nayi na nufi daki ba tare da na kula yayuna dake cikin falon ba, tabbas sunsan ina cikin damuwa don a yanda nake da gagara da kansu suke korata daga falon amma yau ni ce a nutse hakan ya daga hankalin mammy batasan ciwon so bane ya damen Allah sarki ni, sallahn ishai nayi nayi nafila sannan nabi lafiyan gado sai dai bacci ya kaurace wa idona, tunani da fargaba ya damen , dafarkon ina tunanin waye bawan Allahn nan nabiyu ina tunanin ya akayi yake sheme a wajen? ko dai maraya ne? bai da yan uwa ne? meya sameshi? oh ni Nadra a kunnena aka kira asuba, dakyar na mike nayi nakoma kan gadon nan bacci barawo ya saceni. . Ban farka ba sai karfe sha biyu na rana, mummy na zaune a gefeta ta tsura min ido dasauri na mike nace " mummy nace miki kidena bude ni da extra key, narufe kofan fa" " ke yar nan, saboda tsautsayi ne kinsa hankalina yatashi daga kwanciya kin kwanta kaman gawa dole na saki a gaba ina gadi" dariya tabani sai dai na daure nace " wanka zanyi natafi lalle da saloon kinga jibi sallah" " tashi to! ko kefa yanzu nasan auta ta tawarke anma kwanciyan ki bana son shi ko kadan" tana fada ta mike tanufi toilet ta kunna min heater sannan tafara ciro towel nayi murmushi sannan nace " ayya mammy dai, banma gaysheki ba, ina kwana? ina abamama?" "lafiya lao, ya jikin naki?
. yaje aiki anma zai dawo dawuri yasan baki da lafiya ai" "da yayi zamansa na warke nikam" na nufi toilet na rufo kofan, ruwan da ya danyi zafi nashiga na kunna ina wanka a hankali ina tunani har na fito mammy tafice dasauri na shafa mai dama nayi alwala na , nayi sallah nasaka abaya baki da bakar jaka sai snickers baki kasancewar inada haske sosai yasa nayi kyau fuska na farau farau na fice mukullin motata na dauka nayiwa mammy sallama sannan na fice, yau banci saa ba domin kuwa banga bawan Allahn nan ba nadamu matuka sai dai naji dadin rashin ganinsa a wajen, toh ko dai sai dare yake zuwa? anma ranan da yamma na ganshi, tunani dai barkatai araina nawuce saloon sannan naje gidan lalle ban gama lalle ba sai karfe shida na yamma dasauri nafito don tafiya gida, dai dai gun na tsaya banganshi ba , toh ai yana azumi, anma ranan a buge yake kuma ana azumi, Allah ya kyauta, da tunani na nufi gida har ankira sallah domin masallacin gidanmu har an idar nasamu nashige ciki, naci karo da rikakkun samarin gidanmu wai sun shigo shan ruwa, .
bakinciki kaman ya kasheni ganin dukkansu sunkai aure anma sunbar mammy da musu abun shan ruwa, ganin sun baje a falon abamama na kan dinning yasa na murtuke fuska sannan nace " mu dai mungaji da ciyar da manya, kowa ya fito da mata ayi aure abar min uwa ta huta" yaa usman ne yasamin kafa sai gani Dim akasa, " wayyo Allah mammy zasu kasheni" dasauri ta nufi kaina " Usman ka kiyayeni, bana son bakin mugunta, karya tayi? yara kunanan dirka dirka kunki aure, duk mata zan nema muku" bai ce komi ba sai harara dana ke kwasa, yaa amir kam daman ba mai magana bane, su yaa kamal kuma yunwa ta debe shi baya magana sai yayi nak, mikewa nayi na dauki tray dina da aka zuba min nawa kason na nufi kan dinning gun abamama , . muna ci muna tadi har muka gama, nan muka dawo falo ana tadin sallah, yaa kamal yace " zanyi hawan daushe fa, tunda abamama bai son hawa zan shiga ayari kawai , tawagan sarki kawai zamu duru mu shiga, da fatan zaki zo kallon hawa? don naga bakya son zuwa?" " me zanje yi in banda shan rana inyi baki kirin nasamu ruwan gida ya karben nayi haske" " aikuwa sai kinje" haka dai muka yita tadi da yayuna har goma tayi kowannensu yamike ya nufi fanninsa, ina dokin sallah gashi saura kwana biyu ne! . Yau take washegarin sallah, sannan kuma hawan daushe a garin bauchi, tun karfe tara na safe dana mike na fada bandaki wanka nayi nazo gaban madubi nafara kwaliyya, .
sai dana tabbatar nayi kyau na kalli kaina sosai ajikin madubin sannan na yi murmushi na bude wardrobe dina nadauko kayan da zansa, super wax ce peach nd green colour yasha lafiyayyen dinki dana saka aka yimin a abuja, na saka sannann na kara dauko gyaleta na yafa ta agefe, na jefa wayata da powder cikin jaka da turare kwaya daya sannan na fito ina murmushi, yaa Amir na jirana mutafi kallon hawan daushe dama su yaa kamal sun dade da tafiya kasancewar shi zaiyi hawa, mammy na falon abamama nafito muka wuce, yaa amir ke jan motar har muka isa state low cost inda zanhadu da yan ajinmu domin dadin kallon, duk da cewa ni yaa kamal nafito kalla. . #ays
=== CIWON IDANUNA 3 === .
Anfara kallo rimi rimi abu yayi kyau ayi dariya ayi kallo nida kawata amma ty munata dariyan wani daya ke rawan shoki na ga tawagan gaba sunzo wucewa, ban lura da sunan tawagan ba , sai dai na hangoshi gabana ya tsinke ya fadi, na kara zura ido tabbas shine! rabon da na ganshi tun ran jajibar dana ganshi a hanyan komawa gida daga kasuwa , innalilahi wainna ilaihi rajiun gabana sai bugawa takeyi, yasha farin rawani da farin kaya duk da fuskansa arufe take bai hanani ganesa ba, dasauri rike da coke din hannuna na isa gabansa na mika masa, duk da yana kallon sama bai hanashi sauko da fuskarsa muka hada ido ya lumshe idonsa sannan ya karba, "nagode" cikin sassanyar muryarsa ya fada agefeta wata sai daga masa hannu takeyi " Yaa Aliyuu! Yaa Aliyuu!! Yaa Aliyu!!!" na kalleta ina murmushi ko ba komi nasan sunansa , drinks din hannunta takoma dasu don ya riga yakarba na hannuna, ko yayi tunanin muna tare ne oho 'ALIYU HAIDAR' nafada acikin raina, sannan naja numfashi na juya na koma na ci gaba da daga masa hannu, zuciyata tayi wani sanyi, naji sanyi araina, haka na rinka fara'a har su yaa kamal suka wuce, cikin jin dadi nazauna inajiran yaa amir saiga wannan yarinyan dasauri na rike gyalenta tajuyo tana murmushi nace mata " inbazaki damu ba don Allah tambaya nakeyi?" ta gyra tsayuwarta tana kurban ruwa daga goran hannunta sannan ta gyada kai alamun tana jina "Yaa Aliyu danaji kince yayanki ne?" "ohh!! hamma Aliyu? yes, same mum same dad" naja numfashi sannan nace " don Allah numbanshi zaki bani " batare data ce komi ba ta kirgo min numban nikuwa na saka awayata, numban ba wahala sauki gareshi don harna rike, special number ne, sannan tace Aliyu hameed sunan,godiya na mata sannan na wuce, kuma sai data sanar min cewa yayanta ne na lura cewa suna kama asalin kama sukeyi , murna kaman me ahaka muka isa gida da gudu naje na rungumi mammy, ina dariya ita kanta tasha mamaki domin tayi sati bata ga farin cikina irinna lokacin ba , daki na nufa nayi adding numban a whatsapp, dpnshi hotonshi ne dasauri naje nayi saving nasa a wallpaper na, sai juyi na keyi, yau zanyi baccin dadi,Allah na gode maka Allah. na saka hannu na danna layin yayi ringing har ya gama baa dauka ba, dasauri na kara dannawa wannan karon ya dauka cikin sassanyar murya yace "hello" jikina yana bari nace "hy ina wuni" sai kuma yayi shiru zan kara magana ya kashe wayan, nakara kira kawai naji switch off, innalilahi wainna ilaihi rajiun
. Nakara kira naji akashe, sai kawai hawaye yabi idanuna nayi ragon azanci dana karbi numbern kanwar, oh Allah ni ga samu ga rashi, haka na zauna inata kiran numban bai shiga ba, akalla nakai awa biyar ranan walwala ta kadan ne na tsaya tunanin rayuwata ma tukunna, nasan mai karatu ya matsu yaji wacece ni!, ga tarihina kadan kuji, Sunana Nadrah Ahmed ni ce ya mace agun iyayena, inada yayu maza kwaya shida, yaa kamal first born, sai yaa Amir, yaa Usman, yaa Anas, Yaa faisal, sai yaa ahmed kafin ni, ni kadai ce mace kuma yar gata, a gidanmu anhada manyan maaikata domin kuwa yaa kamal lawyer ne, yaa Amir banker, yaa usman quantity surveyor, yaa Ahmed da yaa faisal na medical school suna medicine, yaa anas kuma yatafi maritime sai ni danake karanta architecture a atbu, Abamama yana bala'in son yaransa, duk abunda muke bukata yana mana, tunda natashi izuwa yau bantaba rashin wani abu ba ko acikin kawayena nafita zarra, nadawo abun kwatance, shekaruna ashirin cif a duniya sannan kuma ni banda tarukucen kawaye kawata kwaya daya ce Ammaty, itama don iyayenmu abokai ne munsan juna, inada gagara da neman tsokana fara'a dakuma son mutane, sai dai bana shiga mutane, Allah yaban ilmi da wayo sosai, inada farin jini sosai agun samari tun daga yara zuwa magidanta sai dai duk cikinsu babu wanda raina ke biyawa, asalima ni bantaba soyayya ba bansan so ba bankuma san dadin so ba sai yanzu danake shan azabanta, nake son hauka domin kuwa so ne yafita acikin addini, ni kaina nasan yayi yawa anma yazanyi da raina? iyayena basa kaunar fushi ta domin anhaifeni da ciwon zuciya lallabina sukeyi duk abunda nakeso anamin haka zalika yayuna, acikin yayuna nafi shakuwa da yaa kamal nakan manta inada mahaifi domin duk wani nauyi yadaukemin, ba yabon kai ba samarin gidanmu duk flowers ne maana sunada kyau domin gidanmu duk farare ne babu baki a gidanmu gamu da manyan idanuwa da gashi basai nakara bayani ba mai karatu zaigane cewa yan mata ba karamin safa da marwa sukeyi a gidanmu ba anma samarin gidanmu sun rufe ido babu niyyar aure akansu, tunda babu wanda bai kai aure acikinsu ba, ya Ahmed ma da nake binsa ma shekaranshi ashirin da shida. Iyayena asalinsu yan gombe ne Abamama kuma shuwa ne , mammy yar gombe sai su Abamama suka koma zama a gombe sanadin zamansu kenan, Labarina kenan kadan ne anma nasan nayi bayani dakowa zaigane. .
ZA MU CIGABA INSHA ALLAHU DA SAFE. Allah Ya tashemu Lafiya
==== CIWON IDANUNA 4==== .
Wayan haidar na kashe har dare, ban hakura ba domin sai kira nakeyi baya shiga, karfe goma dai dai nakira wayan naji akunne, nan naja numfashi domin kuwa ji nayi kaman zan sauke aikin hajji, bai dauka ba harta tsinke hakan yasa na kara kira, wannan karon yana daukawa yayi sallama "salamu alaikum" dasauri na amsa masa "waalaikumsalam" sai kuma nayi shiru, ina tunanin me zance, can dabara ta fadomin nayi gyran murya sannan nace " ina wuni yaa haidar" sai yayi jum kafin yace "lafiya" alamun bai gane waye ba' " na kira ne na gaysheka dama " "nagode" yana fadan haka ya katse wayan, na zurawa wayan ido kaman zai bani amsan tambayoyin dake cikin raina, nayi jum can dai na ajiye wayan nasa caji naficr falo, yau ba kowa don hatta mammy tana fannin abamama donhaka na kunna tv nayi kallo duk da ban fahimci kalilan ba , zuciyata tayi tunanin shi wanda ayanzu yazame min alada, na dauko cake ina ci saikuma wani dabara ya fadomin nayi murmushi na kashe tvn na koma daki don yin bacci wanda rabi tunanin haidar ne. ******* karfe sha daya nashirya tsaf na fito bayan sallama da su mammy zanje gidansu ammaty, ahanya na tsaya ko zan ganshi anma ban ganshi ba donhaka nawuce abuna, yau dai nasa araina insha Allah saina ganshi, .
ko sha biyun dare zankai a gidansu ammaty sai najira yafito naganshi , gate din gidan abude wanda baisa nayi mamaki ba domin gidansu ammaty haka yake cika duk sallah, gidansu babban gida ne sosai kuma gidan sarauta, nayi parking agefe sannan na haura sama fanninta, arufe ne donhaka nawuce na hajiyanta saidai kuma wasu yanmata nagani a zaune suna gaida hajiyan, na tsugunna na gaida ta har na mike naga ta gefen, tabbas idan brain dina yana aiki wannan itace tabani numban Aliyu jiya tace min yayanta ne uwa daya uba daya bansan lokacin dana fara murmushi ba muka gaisa, itama murmushin tamin duk da nasan bata ganeni ba. Na zauna agefenta sannan na rage muryata nace "kinganeni?" ta kara kallona sosai sannan ta girgiza kai " jiya a filin hawa muna tsaye tare" "ohh oh ke na bawa numban hamma Aliyu ko?" na daga kai sannan tace " kin kirashi ko? don naga jiya wayanshi tawuni a kashe " na yi murmushi sannan na girgiza kai " bani bane nake nema, wata kawata ke so daman" " ayya! Allah yasa ya kulata" "banganeba" " arayuwa idan kika cireni ni kanwarsa damuke uwa daya uba daya hamma bai tsayawa da wata mace kuyi maganan da tafi na minti goma" ji nayi gabana ta tsinke ta fadi " anya kuwa? . wannan kawar tawa tanada kyau fa sosai" "hmm ko itace aljanna kuwa, muna nam dake duk randa muka kara haduwa zaki bani labari" na girgiza kaina ina tausayin kaina sai dai naji dadi cewa baya kula kowa, ko ba komi kishi na zai kwanta, mikewa nayi nafice don naga dakin sai cika akeyina koma fannin Ammaty saikuma naga kofan abude, da gudu ta rungumeni tana dariya " bebz na zata baza kizo bane ai" "who born me!" na riko ta dasauri muka zauna akan gado sannan nace " akwai wasu dana gani a dakin hajiya yanmata guda uku kinsan su? " " su Amrah kenan, yaran gidan tofi , Hameed tofi, kwaya daya kenan sai sauran daga fadan sarki me ya faru?"nayi gyran murya sannan nace " shi Hameed tofi yaransa akwai maza?" "bebz yhne kam? ko kinga flower hamma Aliyu ne?" "ya akayi kika san shi nake nufi?" " haba mana shi kadai ne dan gidan Hameed tofi daga shi sai Amrah" " shine baki taba ban labari ba?" " noo nadrahh karki cemin kinfars sonshi? you better stop! karma kiyi garaje, wallahi wannan flowern daga nesa zaki ganshi ki hakura dashi baya kula mata afterol me zakiyi da me shaye shaye?? shi ya kawo kanwarshin ai, yanzu haka yana kasa" hankali na atashe na ruko ta " Ammaty don girman Allah don darajan manzon Allah, kitaimaka min, tunda nake dake for the past fifiteen years baki taba ji nace ina son wani ba, kitaimaka min wallahi zan iya rasa raina idan ban mallakeshi ba, kiyi hakuri kimin hanya, na ajiye duk wani girman kai na ya mace ko alfahari na ya mace , kitaimaka kimin hanya" . ina fada hawaye na Zubo min a fuska abunda yayi matukar bata mamaki don ganin yadda take kallona bakinta a bude, ta rike hannuna sannan tace " nasan Hamma Aliyu, yana da kyau wanda ni kaina na yi crushing dinshi harna hakura, kintuna lokacin da muke school nace miki naga yayan wata family friend dinmu inasonshi? nayi ta damunki? ki kayita zagina? shinefa! bani kadai ba duk wata mace da zata so hamma baya sonta wallahi wulakan ta ki zaiyi, kinsan mai shaye shaye bawai ya mallaki hankalin mutunta ki bane, kije kidaure ki hakura, ahankali zaki manta dashi" na kalleta na share hawayen idona " wallahi bazan iyaba, Ammaty zuciyata na ciwo, nakai sati ina muradinsa, ko kallonsa ne nayi ban da damuwa, wallahi zan jure duk wani wulakanci, ko da kullum zaina dukana ne zan jura Ammaty duk abunda yayi wallahi kara sonshi nakeyi, jarabawa ce wallahi daga Allah" kuka nakeyi sosai Ammaty kuwa baki a sake tace " lallai nadrah kinyi nisa bakyajin kira, ko ince son hauka yakamaki. .
Ina kallonta ta mike sannan ta leka ta window, sai kuma ta juyo sannan tace "muje" jiki na bari na bi ta muka sauka kasa, yana cikin mota yasaka kafansa daya ta waje daya ta ciki, yasauke kujeran motan kida na tashi a hankali, Ammaty tayi sallama ya amsa ba yabo ba fallasa hakan ya gwadamin cewa halittanshi ce rashin murmushi amma duk da haka nikam yamin kyau, na gagara dauke idona akansa duk da Ammaty yake kalla kaman baisan akwai halittar mutum a gefensa ba, tace "Amrah nake nema, tazo tanan?" ya girgiza kai alamun a a sannan yaci gaba da danna wayar hannunsa, yatsunsa na bi da kallo, nan na lumshe ido tare da dogon istigifari, hannu na taja muka bar wajen ganin banda niyyan motsawa, har mun shigo ciki ta tsaya tareda cewa " kin dai ga kalam wulakancinsa daga nesa, ki kama kannki kifita alamarinsa, it is not meant to be" nayi murmushi sannan nace " wallahi yakara burgeni, naji na kara sonshi" hannu tasa ta makeni akai tuni na haura sama ina dariya, munci karo da Amrah tana hanyan dakin Ammaty, nan muka tsaya da ita tana gaisawa da Ammaty "Daga ina kuke?" "Munje gaida Hamma" sai ta juyo ta kallen sannan tace " har yanzu bata farfado bane? .
" Ammaty tayi murmushi sannan tace "dolenta ai yanzu kam" ido nasa musu, suka tafa sannan suka cigaba da magana, alamun sunsan juna suna kuma tare. Amrah taja hannuna muka shiga cikin dakin Ammaty, na zauna ina kallonta domin mugun kama suke da yayan nata, "ina so ne ki sanarmin kina sonsa kokuma a'a crushing kikeyi bayan kwana biyu zaki gaji dashi?", jiki na bari nace " wallahi ina sonshi, don Allah' damuwa ta muhadu dashi zan jure duk wani wulakanci don in faranta masa" dahaka ta ce " Hamma nada wuyan shaani, akwai yanmata kala kala masu kai mara hari amma Hamma baya kulasu, asalima shi yake wulakantasu, bantaba jin wanda ta jureshi na wata hudu ajere ba, ni kaina da zansami wanda hamma zai kula ko ya sota wlh da na ji dadi, Hajiya kanta ta damu , sai dai nasan kema zaki gaji, amma ni zanyi kokari na hadaku zanna zuwa gidanku da shi kekuma saikiyi sauran, Allah yabaki saa" na ja numfashi ko kadan banyi dar ba balle tsoro nace " na yarda nikuwa zan baki mamaki" murmushi tayi alamun taji anma bata yarda ba, muka mike muka rakota kasa, sauran suntafi shikuwa yana jiranta, har bakin kofan motan mukaje tayi sallama, akaro na farko naga yayi murmushi, tareda fitowa, tace "Hamma ga kawata ku gaysa sunanta Nadrah" ya kallen a fizge idanuwansa kaman yana jin bacci a lumshe farare zubin madara manya dara dara, sannan yayi murmushi " sannunki" sai da ta juyo ta kallen alamun mamaki wanda nima da Ammaty shi mukeyi.
=== CIWON IDANUNA 5 === .
Bansan lokacin dana mai da murmushin ba, saikuma yakara dacewa "kinzo kina neman Amrah aina kika samota?" wani kunya naji da muka gane gaba daya ba wa ni yake wa murmushin ba, da Ammaty yakeyi, ta ce " a sama, ashe tana can tana jirana itama" ya gyda kai ba tare da ya kallen ba yashiga motarsa, wani murmushin takaici nayi amma a zuciyata nace ' ko dukana zakayi ka bazan daina bibiyanka ba' Amrah ta jawo ni gefe sannan tace " kinga ke kikace zaki iya, kar wannan karamin abun ya bata miki rai, akwai abunda yafishi anan gaba" nayi yake da hakorana sannan na gyada kai anan tashige suka tafi ni da Ammaty kuma muka koma sama, duk jikinta yayi sanyi taga dai baza ta iya shiru ba tace " yanzu dagaske kikeyi zaki iya?" . " zan iya mana, sa kai yafi bauta ciwo" ta lumshe ido tamike kan gado batare da tace komi ba nima sainaji kawai natafi gida, tafara bani haushi akan meyasa zata hanani sonshi, duk da nasan Ammaty da fadan gaskiya komim dacinta Amma bazan iyaba donhaka na dau jakata na ce " bye bye zan wuce gida" bata ko kulani ba hakan ya tabbatar min ranta ya baci donhaka na fice na wuce gida. Abamama na falo yana karanta jarida dasauri na nufi kanshi na zauna agefensa, jingina kai na nayi da gefen kujeran na lumshe ido, Aliyu kawai nake hange, murmushin da yayi dakuma maganarsa duk ta tsaya min akai, jinayi Abamama yace " lafiya ko jikinne?" " a'a kawai dai inajin jiri ne" " zan hanaki tuki to, kar watarana kije kisami matsala duk inda zakije ki kira yayunki su kaiki, meye sukeyi da bazasu iya kaiki ba?" " Abamama makaranta fa, kayi hakuri bazaa sani matsala ba insha Allah" bai ce komi ba amma nasan bai gamsu ba, Yadda Allah yabani miskilan yayu ta ina zanfara yawo dasu ayadda nake yawo a atbu kaman gidan baba na? yaa kamal ne kawai yake da surutu da shiga jama'a toh shikuma kullum yana office tunda babban barrister ne, yaa faisal , yaaa anas da yaa ahmed kuma zasu koma makaranta acikin satin nan don haka yaa Amir ne da yaa usman sukayi saura, Yaa Amir in ya tafi bank tun bakwai na safe sai shida na yamma yake dawowa, Yaa usman ne kadai zance nakan ganshi a gida inya gudo office to shikuma son jiki da son baccinsa bazai sa ya yarda yayi yawo dani ba, nikuma na tsani driver yayi yawo dani duk sai inajin wani iri gwara dai Abamama yataimaka kar ya kwace motannan, banda lafiya sosai shiyasa iyayena ke lallaba ta, komi kankanta damuwata suna kokarin kawar da shi.
******
Yau zamu koma makaranta don haka dawuri na shirya zan wuce hanyan Aliyu ko zan ganshi amma ban ganshi ba, kusan sati biyu kenan da nake duba hanyan tunda naganshi sau biyu ban kara ganinshi ba, to ko wucewa yakeyi agun? yakamata ma nayi binciken waye shi da duk abunda ya shafeshi, nasan cewa Ammaty ba zata bani amsa ba donhaka dasauri na dauki wayata ina hanyan atbu nakira suleimanu, suleimanu dan ajinmu ne a makaranta muna dan mutunci dashi kuma cikakken dan bauchi ne donhaka na ce mishi " kasan Hameed tofi?" " kai Nadrah waye a bauchi bai sanshi ba?" nayi mamakin kalamunsa tunda ni bansanshiba sai da na fara son dansa donhaka sai nace " waye shi?" Share . Babban dan kasuwa mana, Sannan yana siyasa kadan, ga kuma sarauta!" " yayansa nawa? ko baka saniba?" " na sani mana, abokin babana ne" " yauwa gani a gate din school, kana ina nazo na sameka?" " ina cafteria sai kinzo" da rawan jiki na kashe wayan na fara sauri, ko ba komi zan samu labarin Aliyu yau, ina isa na ganshi a kofan gun na kashe motan na sauka sannan na isa gunshi , yana murumshi nikuwa ina cikin zulumi " Nadrah ko dai kin fara son Aliyu ne?" .
a tsorace na kallesa " me yasa kamin wannan tambayan?" " saboda yau kece ta goma sha uku a cikin makarantan nan dakika min tambayan waye hameed tofi, kuma duk akan Aliyu ake bincike" "hmm, yanzu dai bani amsa ta" " toh barin fada miki kamar yadda na fada wa sauran, gidansa yana new gra, sannan matarsa daya yaransa biyu, Amrah da Aliyu, Aliyu dan shekara talatin amma inkin ganshi zakice Dan shekara ashirin da biyu ne yana da karamin ruwa, kanwar sa Amrah shekaranta ashirin da daya, sannan Aliyu , likitan aikin zuciya ne , wato Cardiac surgeon, sannan tun yana shekara sha shida babansa yakaisa california, inda yaje Stanford University School , anan yayi medical school dinsu har yazama cikakken likita shekara biyu da suka wuce yadawo nigeria, yafara aiki a nigeria a national hospital abuja, can california ba yadda basuyi dashi yafara aiki dasu ba saboda yana da ilmi sosai, yaje kasashe daban daban inda suka turashi yayi aikin zuciyan amma yaki ya musu aiki, dawowansa nigeria atake national hospital suka daukeshi kuma yaje, daga shekara biyu zuwa yanzu yayi aiki yakai guda sittin da hudu babu failure aciki, yanzu haka yazama hot cake, toh anan shikuma ya samu saran gudowa bauchi ko wani sati zaki ganshi yazo, ko sallah hatta azumi gaba daya anan yakeyi, tunda kika tambaya waye shi nasan cewa kin taba ganinshi, . kin ga kyaunshi, toh saidai yana da matsala daya, yana shaye shaye, wasu dunce asiri yan gun aikinsa suka masa, wasu kuma sunce tsabar tension din aiki yafara tunda fara aikinsa yafarayi baiyi a yarinta ba, nutsattsen mutum ne, sai dai arayuwansa babu halittar dake masa saukin wulakantawa kamar mace, zai daraja sauro fiye da ke, kinga dai na gayamiki komi akanshi amma zanrufe magana ta dacewa kiyi hakuri ki taimaka karki fara sonshi wallahi zaki wahala, kina da mutuncinki da kyaunki kar ya wulakantaki" wani harara na sakar masa sannan nace " nayi maka kama da wacce zata hakura? ko kuma wacce zaa wulakanta? shiru yayi sannan ya cigaba " kanwarsa da uwarsa kadai ke cin daraja a idonsa, yana da ilmin addini daidai gwargwado sannan ko zaki mutu bazaki ganshi da aboki ba, shi kadai ke rayuwansa" " yanzu dai kace yana zuwa bauchi ko wani sati?" " ae, sosai ma, inkinji ana DR. Haidar Tofi toh shine" nayi ajiyan zuciya na koma mota, OH NI NADRA YA ZANYI? ku ban shawara
0 comments:
Post a Comment