Sunday, 29 September 2019
Home »
Kuskurena Complete
» Kuskurena Page 15 - ISMAIL SANI
Kuskurena Page 15 - ISMAIL SANI
[❣🤦🏻♂ _*KUSKURENA*_❣🤦🏻♀
{The story is Interesting! Attractive! Impressive! to cut a long story short the story is a fascinating story the readers will entertain and enjoy it.}
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
**************************************
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
*BY*
_*©, RAMLERT Y SALIS*_
~08037862213✍🏻~
*No part of this book maybe an object of privacy✖*
_Wedn , Sept 25 , 2019._
_*Page 15......*_
Doctor Mahmud ne atsaye akan Izzatu dake kwance a gado, wasu nurses biyu a tsaye a bayanshi, Sai daya gm gwaje gwajensa sannan yajuyo ya kalli nurses din yace, she has demised, da sauri nurses din suka karaso bakin gadon, Dayar ce tasa hannu ta rufe mata ido sannan taja blanket ta rufeta dashi.
Dakin da ake ajiye dead body suka kai Izzatu akasakata acikin bayan suncire mata dukkan kayan dake jikinta sun doshe hanci da hunnenta da audiga sun samata wata powder, wani dogon akwati aka sakata aciki kamar durowa Sannan suka lullubeta dawani kyalle suka tura akwatin suka rufe,
Doctor Mahmud yana office dinsa a zaune jafar da safraz suka shigo jiki a sanyaye, bayan sun zauna jafar ya kalli Muhmud yace, Doctor sannu da aiki, dg yanayin fuskar jafar doctor Mahmud yasan mutuwar ta jikinsace sosai danshi Sam baisan safraz ba yana dai jin sunanshi agurin jafar amma baisan shi a fuska ba muhmud shima cikin kulawa da nuna alhini yace, Lpy jafar yakuma Karin hakuri?
Wani irin bugawa kirjin jafar yayi dammmm! Duk dayaga a yanayin daka fita da Izzatu amma bai gama fidda rai ta rasuba sai dayaji abinda abokinsa Mahmud yace anan ya tabbatar da rasu, Safraz kuwa da darkarewa yayi ya kasa motsawa a inda yake a zaune sai yaji kamar ba dai dai kunansa yaji masa ba kasa wani yunkuri yayi idanuwansa suka kafe kama bakinsa yakasa furta komai, doctor muhmud ne ya mike tsaye yacewa jafar, let's go. Mikewa jafar yayi yabi bayansa amma har sukaje dai dai kofar fita Safraz bai biyosuba, Safraz kataso abinda jafar yafada kenan yajuya yabi bayan doctor, Da kyar yamike tsaye ya fara dakawa a hankali yanajin kamar zai fadi kasa har yakusa isosu, Sun danyi tpy kadan suka iso kofar wani daki da security guda biyu a tsaye a kofar kowanne dauke da bindiga, dakin suka shiga akwai mutane ma aikata su biyar kowa yana harkar gabansa wani daki suka kuma shiga again, duk Safraz yana bayansu yana binsu Sannan doctor Mahmud yasa key ya bude wata kofa ya shiga jafar nabisa Safraz nabiye masa baya, Dakin duhu sosai muhmud yayi nufi wani waje ya dau wata babbar fitila ya kuna, Dakin dauke yake dogayen akwatuna nasa gawa Wanda zasukai guda talatin, numbers din dake jikin akwatunan ya fara dubawa gar tazo 15 a hankali ya jawo kamar ya bude durowa, juyowa yayi ya kalli inda su jafar da Safraz suke tsaye yace, Bismillah! da murya kasa kasa hannun Safraz jafar ya kama suka karasa gurin sai dasuka karaso Sannan doctor Mahmud yasa hannunsa ya yaye kyallen da aka rufeta dashi yabude iya fuskarta, Idon safraz ne ya kai kan Izzatu dake kwance idanuwanta a rufe an toshe hancinta da kunenta da auduga,
Izzatuuuuuuuuu! Safraz ya fada da karfi kuma cikin razine, luuuuu yatafi da baya zai fadi jafar yayi saurin taroshe ya fada jikinsa ya suma.
Da sauri doctor Mahmud ya maida akwatin ya rufe yayo kansa suka kamashi suka fita a dakin, Da sauri sauran ma aikatan sukayo kansu ganin sun kamo Safraz a hannu gadon da ake Dora gawa idan a fita da ita akai suka dora Safraz sukayi emergency dashi cikin sauri.
Sai da doctor Mahmud yabashi kulawa ta musamman sannan ya auna Bp Sa jininsa ya hau sosai Allurar bacci yayimasa sannan suka koma office dinsa shida jafar, Ajiyar zuciya doctor Mahmud yayi Sannan yace, Ai bansan yar,uwarsa bace sosai hk dabai kamata yamushiga dashi ba Allah sarki, Kallonsa jafar yayi yace matarsa ce , kamar bayason yin mgn. Allah sarki Allah yaji kanta da Rahama waye ya aikata mt hk!? Cewar doctor Mahmud, jafar Rasa abinda zaice masa yayi sai ya fara kame-kame um ah nima dai bansaniba, Doctor Mahmud gazing din jafar yayi Sannan yace, you are laying jafar look ! Kafadamin gaskiya Dan karmusamu matsala da Jami,an tsaron asibitin nan karban gwatan zai iya bamu matsala ta inda baka tunani tunda bata da file a asibitin nan kuma anan tayi jinyaba tell me the truth, ya karasa mgnr yana cire glasses din dake idonsa, Badan jafar yasoba ya fada masa cewa sun samu yar matsalane a tsakaninsu Safraz yy zuciya ya daketa shine tsautsayi ya kawo ajali, Arazane doctor Mahmud yake kallon jafar Sannan yace, Wlh if nasani bazan tabashiba Dana rabu dashi dg suman ya zarce shima ta mutu ranshi a bace ya fadi hk, Wato saboda abokinka ne shine zaka goya mai baya a rufe zancen ko to badani ammah jafar kabani mamaki wlh zaka iya goyawa zalunci baya kenan? ya watsa masa wani kallo me kama da harara, A nitse jafar yace, No doctor try to understand me pls bawai abinda kk tunanina abisa *kuskure* ne, da masifa doctor Mahmud yace, Wane laifine zatayi masa hk har data cancanci dukan mutuwa? Ni sai yanxu nagane *KUSKURENA* dana karbi gwatar a asibitina duk tunanina accident ne wlh ina dubata naga kisan hannune sabida shaqar dayayi mata fatar wuyanta duk sai daya salube wannan za,a kira kuskure??? Ya karasa mgnr yana buga teburin dake gabanshi, innalillahi wa inna,ilaijirraju,,un shine kawai abinda jafar yake maimaitawa tare da dafe kansa bawanda yakuma cewa komai zuwa can jafar ya dago yace, shine Safraz Best friend dina danake baka blr kaji nacema wlh to wallahi summa tallahi ba da ganganci hk ta faruba ko cinnaka bantaba tunanin Safraz zai kasheba abun yazo da tsautsayine wlh Safraz is a moral person he cares about everyone around him moreover he is a very religion ni kai na ina cikin damuwa over, the reason why I decided to seek your assistant because Dan gidan Alh Hashim Muhammad ne his father is famous nasan kasanshi shiyasa nake son rufe mgn not because of Safraz is my friend you know?
Kai doctor Mahmud ya daga masa sannan ya yace, Any way kasanar da iyayen yarinyar shima Safraz din ya samu hawan jini kuma yakamata yaga neurosurgeon (likitan kwakwalwa) saboda da alamun indai kamilin mutum ne as you said lpy qlau bazai akaita hk ba yafadi hk yana mikewa tsaye hanyar fita waje yy yana cewa komai tayi masa inhar yaji bazai jureba sai ya saketa shot and simple ya kara fadin hk yana fita a office din.
Jafar ya Dade a zaune a office din shi daya Sannan ya tashi ya fita ya nufi gidan su Safraz.
Mami zaune a falo ita sa momy Adama sai gudanar da harkoki akeyi a shirya wancan a kulla wancan wannan shu Shiga wadancan su fita dukdan bikin Safraz da karima, Can dakin Shahida karima ce ita da babbar aminyarta fauza wacce suke karatu tare a England fauza dake sun samu hutun 2weeks yasa fauza ta biyo karima Dan susha shagalin bikinta, Dariya suke suna shewa karima tagama bata dukkan labarin abunuwan dasuka kitsawa Izzatu fauza ce tace, Ai wlh kina enter kiyo out da ita, ita din wa? Karki raga mata ina fadamiki kawata sai kin tsaya da kafarki ita din banza I'm telling you zakiyi nasara, dariya karima tayi tace hehehe ke! Rabu da bakin halina idan ya motsa zanyi maganinta jina nakeyi dai dai da ita ai ita ganin kyantanam takeyi tafi kowa Ammana nikuma... Sai tayi shuru ganin sakina tashigo dakin food is Read shine kawai abinda sakina ta fadamusu tajuya ta fice , kallo suka bita dashi fauza tace yanaga tana frown fin face karima tace, himmm hk take da wannan bakin halin nata tare suka mike suka falon dukkan su suna deining table suma suka karasa suka zauna.
Bayan sun kammala suna zaune dukkansu a falon Jafar yashigo da sallama, cikin fara,a mami ta tare shi gaisawa sukayi na Dan wani lokaci mami ta kalli inda Shahida take tace, Shahida kawowa yayanki drink mana, ahhh mami tabari nagode dama zuwani sai kuma yayi shuru yarasa ta inda zai fara
~Sannu sannu kwane nesa muje zuwa page 16 yau da gobe bata bar komai ba~
0 comments:
Post a Comment