Sunday, 29 September 2019
Home »
Kuskurena Complete
» Kuskurena Page 16 - ISMAIL SANI
Kuskurena Page 16 - ISMAIL SANI
❣🤦🏻♂ _*KUSKURENA*_❣🤦🏻♀
{The story is Interesting! Attractive! Impressive! to cut a long story short the story is a fascinating story the readers will entertain and enjoy it.}
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
**************************************
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
*BY*
_*©, RAMLERT Y SALIS*_
~08037862213✍🏻~
*No part of this book maybe an object of privacy✖*
_Sun , Sept 29 , 2019._
_*Page 16......*_
Kallonsa mami tayi ta gano dumbin damuwa tattare a fuskarsa har zuwa lokacin kansa na sunkuye ya kasa dagowa su hada ido, sakina da Shahida suna harkokin gabansu amma Anty Adama, Fauza, da karima hankalinsu ya kan mami da jafar.
Cikin tausasa lafazi mami tace, jafar ko akwai wata matsalane? naga kamar kanason yin mgn amma ka kasa fell Free I'm listening you ta fadi hk tana cire siririn glasses din dake idonta, Daurewa jafar yayi ya daugo ya kalli mami face to face har suna hada ido sai kuma ya dauke idonsa ya kalli gefe, ya fara mgn yanacewa, Mani Allah yayiwa Izzatu rasuwa yanzunan safraz yana hospital a kwance ba lafiya, ya fada a takaice.
Duppppp Falon yayi tsit tamkar babu wani Abun mai rai acikinsa, Duk cikinsu babu Wanda baiji abinda jafar yafadaba amma dukkansu kokonto sukeyi anya kunansu ya jiye musu dai dai kuwa.
Sakina ce tayi Saurin zabura ta mike tsaye ta nufo inda jafar yake tana cewa, innalillahi wa,inna ilaihirraji,un ta karasowa ta zube akan gwuiwowinta tace, Yaya jafar mekace? Anty Izzatu kace?? Lokacin idanuwanta na zubda kwalla, daga mata kai yayi alamun eh shima yana kokarin goge kwallar dake dg idonsa, wani kuka tasaki me ban tausayi tana kifa kanta akan kujerar da jafar yake zaune, Mami tuni ta nemi ganinta ta rasa sai data laluba inda tasa glasses dinta ta dauka tasaka Sannan ta fara gani dashi-dashi kallon jafar tayi tace, ja far Iz za tu na ta ra su kace?? Hawaye nabin fuskarta, kuka takeyi sosai tamkar ranta zai fita, Shahida fadawa tayi kan kujera itama tasaki wani kuka da karfi, Aunty Adama wani yanayi ta shiga Wanda tarasa gane na farincikine ko tsoro amma sai zufa takeyi, Sakina kuwa indan banda dukan uku-uku babu abinda kirjinta yakeyi tsoro yabi ya mamayeta jitakeyi kamar za'agane abunda sukayi, fauza ma hk ne anata bangaren tsoro ya cikata sosai.
A dai dai lokacin Abbansu safraz yashigo falon yana rike da hannun Shahid, turus yayi ganin yanayin
Mutanan dk parlour wasu na kuka wasu sunyi jugum jugum, Idonsa ne ya kai kan jafar dake zaune kan shi a sunkuye takawa yayi yakai izuwa tsakiyan falon izuwa lokacin shima fargaba tab cike da zuciyarsa domin ganin yadda mami take kuka.
A lokacin Anty Adama tasa hannu tawani mutsitstsika idonta zata kakalo kukan karya ta fara cewa, Innalillahi Kai duniya ina zaki damu ayyah Izzatu yarinyar arziki diyar albarka kwana ya kare sai ta fashe da kuka ta kalli inda Alhaji Hashim yake tsaye tacigaba dacewa, Ayyah Alhaji yanxu nan mummunan lbr ya riskemu Allah yayiwa Izzatu rasuwa tacigaba da yin kuka kamar gaske, Alhj Hashim inda mami take ya kalla cikin rudani yace, Ah ni ah ban ganeba wacce Izzatu kuke nufi? Caraf Anty Adama takuma cewa, Alhj wacce Izzatu ce damu idan ba matar safraz ba, wayyo mutuwa gamu manya meyasa bazaki daukemuba kibar matasa su muri rayuwa suma Ayyah rayuwa Izzatu Allah yamiki Rahama Allah yasa can yafimiki nan Allah ya yafe miki yarinyar arziki duksan da naje gidanta ta tareni tamkar mahaifiyarta ta karramani har inajin dadi karima tasamu abokiyar zama ta gari Ashe Ashe zamuyi babban rashi tacigaba da garzan kukanta Abu kamar gaske.
Alhj Hashim shima dabaya yaja yasamu kusa da jafar ya zauna, yanata mai maita innalillahi wa,inna ilaihirraji,un sai da aka dau tsawon kamar mintuna goma bawanda yacewa wani qala sunata sharar hawaye, zuwa can Alhj Hashim ya dubi mami yace, ya isa hk mami you have to stop crying the best she needs now is prayer, ya fadi hk yana goge kwallar dake idonsa da handkerchief din dake hannunsa.
Sakina ya kallah da Shahida yace, kudena kuka ya isa hk pray for her, shima Shahid sai goge nass hawaye yake yacigaba dacewa, Indeed we belong to Allah, and indeed to him we will return. Killi nafsin za'iqatul maut, may Almighty Allah rest her soul, May Allah forgive her jafar dake gefensa yace, Amen.
Murya a dashe mami ta kalli jafar tace, jafar what happened to her? Nasan lafiyanta qlau da safen nan Dan bayan da Safraz ya bar nan munyi waya da ita banji wani alamun rashin lpy a tattare da itaba hkm Safraz har ya bar nan baicemin tana rashin lpy ko wani abuba.
Sai da jafar yaji fafuwar gaba amma cikin dakiya ya kalli mami yace, nima bansan meya sametaba mami, caraf Anty Adama tace, shi ajali inyayi kira koba ciwo dole aje.
Alhj Hashim yayi ajiyar zuciya Sannan yace, Allah ya Mata Rahama wlh na Dade banji mutuwar data girgizaniba irin wannan jiyapa muka gama waya da mahaifinta yake cemin yau zasu sauka a Nigeria nake cemasa indai Dan Daurin Auren Safraz ne wlh yabari andauke masa Sam yaki yadda wai yaza ayi daurin aure babu waliyin ango hk mukayi sallama akan yau zasu iso, yanxu wannan zasuzo su tarar nashiga rudani ya karasa mgnr yana yana sauke wata ajiyar zuciyar, Sannan ya kalli jafar yace, ina Safraz? A sanyaye jafar yace, yana can hospital din shima ba lpy.
Karfe 4:00pm dai dai suka sauka a Airport dukkansu fuskokinsu dauke da fara'a musabbin farincikin nasa bai wuce ayau zasuga 'yarsu daya wato Izzatu, Suna fitowa ta Arrival yazo ya taresu ya karbi wani Dan keke dasuka Dora jakunkunasu akai suna turawa karasa tura keken yayi har inda motarsa take Sannan yasa jakunkunan a boot, murmushi dauke a fuskarsa yace, Yaya sannunku da hanya Prof Abdullahi yana murmushi ya kalli kanin nasa yace, Hanya Alhamdulillah Abbas ya muka sameku? Wlh lpy qlau Yaya Abbas ya fada, Hajiya Rukayya ta kalli Abbas tace, naga duk ka kara tsufa Dan wata2 nan da ban gankaba ta karasa mgnr tana dariya, Abbas yace, Ah bawani Anty kawai kedai kice kin saba ganin fararen fata a America yanxu kuma kinga baki, dukkansu suka kwashe da dariya Sannan suka shiga motar suka nufi gida.
Abangaren Safraz kuwa shikadaine kwance a side room, Dakin dan medium ne hk dauke da gado guda daya sai fridge a kusurwar gadon ta dama sai Dan dogon drawer a bangaren hagu sai AC dake saitin gadon dayake kwance Sannan toilet dake kallon kofar fita, (wannan daki shi akecewa side room a hospital masu kudine ke kama irin wannan dakin kuma bako a wanne hospital akesamu side room ba sai babban asibiti).
A hankali ya bude eyes dinsa yunkuri yayi zai mike zaune amma yaji kansa yayi masa nauyi tamkar an Dora masa wani Abu akai, Dukda zanyi air conditioning dake dakin hakan bai hana Safraz yin zufaba sai panting yakeyi kamar Wanda yayi gudu, da kyar yasamu tashi zaune Sannan yasa hannu ya cire Karin ruwan dake daya hannunsa, yunkuri Yayi ya sauka a kan gadon yaji bazai iyaba komawa yayi ya jingina da gadon yana maida numfashi.
Suna zaune a parlour bayan sun Dan huta sunci abinci hjy Rukayya ta kalli Prof tace, Sai kiran number Izzatu nakeyi amma ba,a dagawa, Sighting yayi Sannan yace, maybe bata kusa da wayan ne basuna cikin bikiba ko kin manta, Frowning face dinta tayi Sannan tace, Me zai kaita bikin kishiyarta kaima da son mgn takarasa mgnr tana kuma dialing number din Izzatu, prof ya kalleta yace, kinga matsalarku Ku mata ai yadan ja gutun tsaki yasa hannu ya dau wayarsa dake ringing ganin surukinsa ne ke kiransa yasa yayi murmushi yayi accepting din call din, Assalamu Alaikum Prof ya fada.
Daga can Alhj Hashim ya amsa sallamar tare dacewa ina fata kun sauka lafiya.
Prof yace, Lpy Alhamdulillah Alhj yanxu nake shirin in kiraka inshedama munsauka.
Alhj Hashim yace, Masha Allah barka da isowa.
Prof yace, Yauwa barka dai ya shirin taro kuma?
Alhj Hashim yace, Taro gashinan anata shiri, sai kuma yayi shuru na Dan wani lokacin yarasa me zai cemasa zuwa can yace, gamu ma a asibiti Safraz babu lafiya.
Subhanallah !!! Meyasa mesa? Cewar professor Abdullahii.
Ahj Hashim yace, gashinan dai muma zuwanmu kenan asibitin.
Wanne hospital ne? Prof ya tambsya.
JK hospital ne, Alhj Hashim yabashu amsa.
Ganin isowa in sha Allah prof ya fada a takaice, Sannan sukayi sallama.
Hjy Rukayya taji dukkan abinda sukace kasancewar wayar a fee take, Shiyasa naketa kiran Izzatu bata daukaba Ashe Allah ya bashi lpy, prof yace Amen shirya muje Mu dubashi tashi tayi tashiga bedroom bata dadeba ta fito suka fice.
Safraz yana nan zaune Abbansu da jafar mami momy dama sakina Shahid da Shahida suka shigo dakin, Tunda daya kallesu bai kara dagowa Yakuma kallon kowa acikinsuba yanayin yadda yaga fiskokinsu yasan sunsan da lbrn mutuwar izzatu, Sunsan Nina kashe Izzatu? Shine tambayar da yayiwa kansa. Abbansu ne ya kaste masa tunani dacewa sannu Safraz kayi hakuri Allah yayi mata Rahama, wani sabon kukane yaji yazo masa mamima hawaye take zubarwa tana Kallon yadda dannata yafita a hayyacinsa kowa jayayi ya tsaya jugum jugum.
Ba'a dau wani lokaci ba Prof suka iso hospital din shida matarsa, dakin da Safraz yake suka nema aka Kai su da sallama suka Shiga, Aunty Adam ce ta amsa yanayin dasukaga mutanan dakinne yasa suka dauka ko Safraz yana shan jikine sosai, koda sukayi masa yaji bai amsaba sai wani fashewa dayayi da kuka, Prof ne yace haba Safraz Kai fa jarumine cuta ai ba mutuwa bace be patient my son sannu kaji wish you quick recovery itama Hajiya Rukayya cewa tayi, sannu Safraz Allah yasa kaffarane meyake damunka? Shuru yy Mata baice komai ba hkn bai dametaba tunaninta jikinnasane yasa bazai
Iya mgn ba, kallon mami tayi tace, Hb Hajiya meyasa zakina yin hawaye hk zakina karyar mai da zuciya ai Ayi hakuri Allah zai bashi lpy.
Hajiya Rukayya kasa hakuri tayi ganin bataga Izzatunta ba yasa ta Dan numfasa tace, izzatu batana nan kenan nakikkira wayanta bata daukaba nayi tunanin ko zamu sameta dan batasan yau zamu dawoba ban fada mataba Dan nayi mata bazata, Ganin babu Wanda yace Mata uffan yasa tace, Niko kodai akwai wani Abu daya faru bayan rashin lpyr Safraz ne? Ta karasa mgnr tana sauke idonta akan Safraz da idanuwansa a rufe amma tears sunta rolling in his checks.
Dai dai lokacin Doctor Mahmud ya shigo, Har gaban Ahj Hashim yazo ya tsugunna Dan dama sunsan juna sosai yace, Ina wuni Alhaji ya hakuri kuma? Sai dayayi kamar bazai amsaba domin yarasa tayaya zai tinkarisu ya fada musu rasuwar yarsu, a sanyaye yace lpy doctor hakuri Alhamdulillah. Doctor Mahmud yakuma cewa, Allah yy mata Rahama Allah yasa ta huta. Alhaji ya amsa da Amen.
Doctor inda Safraz yake yanufa danya cire masa ruwan daya daura masa.
Prof ne ya kalli Alhaji Hashim yace, wacece ta rasu? Itama Hajiya Rukayya a matukar firgice tace wacce ta rasu? ........
Iz za tuuuu..... Jafar ya fada Mauryarsa na rawa dasauri suka kallesa Hajiya Rukayya ta Mike tsaye a razane shima Prof mikewa yayi, Allah yayiwa Izzatu rayuwa a yau dinnan sai dai hakuri Alhaji Hashim ya fada yana sunkuyar da Kai kasa.
Innalillahi wa, inna,ilaihirraji,un shine abinda Prof ya fada yana cire hular dake kansa hawaye ya cika idonsa amma bai bari sun gangaroba yayi sauren sharesu, Itama Hajiya Rukayya bakinta na rawa tace, inn..lillahi.. Bata karasa ba kuka ya kubce mata me tsananin gaske.
The terrible day !!! The day of sorrow!!! Bad moment !!! The most Painful day in their life, they missed their only daughter izzatu they are very sad.
Cikin dakiya da dauriya Prof ya goge idanuwansa ya kalli Safraz dayake ta garzar kuka yace, ya isa hk Safraz you should stop crying, I pity you I know how much you love my daughter izzatu but Allah loves her More then us, our prayers she needs now pls wipe your eyes. Yajuya ya kalli Hajiya Rukayya ma yace, Rukayya ban yadda ki kara zubar mata da hawaye ba nothing is more painful to me then tears in your checks stop crying this an Oder from me.
Sai a lokacin doctor Mahmud ya gane sune iyayen marigayiyar take yaji wani tausayinsu ya saukar masa a zuciya ksllonsu yake cike da tausayi Dan ko kadan baya tausayin Safraz saima haushinsa da yakeji.
Doctor Mahmud ne ya katse shurun dakowa yayi dacewa, Sai gobe za,a karbi gawan ko? Alhaji Hashim yace, eh doctor in Allah ya kaimu yanxu yamma tayi, Doctor meyake damunta Wanda yayi leading to death in haste hk? Take jafar yashiga wani yanayi na rudani Safraz kuwa tuni ya gama saddakarwa kawai shima akashesa.
Shuru doctor Mahmud yayi, Ahj Hashim yakuma cewa, doctor menene ya dameta jafar yace, bai saniba Safraz kuma nasan bazai iya cemana komai ba wannan mutuwa ta farat daya dukda in lokaci yayi Dole ko babu ciwo dole za,a mutu, dukkansu shuru sukayi suna saurarensa.
Doctor Mahmud ya nisa yace jafar kuyi hakuri I can't hid the truth, marigayiyar batayi jinya a hannunmu ba ko lokacin da aka kawota tariga ta rasu ko tun acan gida ko akan hanya, Dana takura jafar yafadamin menene yasameta Danna ciwon dake jikinta tamkar ba accident bane dukane yacemin sun samu sabani da mijinnatane har ya daketa wannan shine sanadin rasuwarta.
Tun kafin doctor ya gama fada Safraz ya sauko dg kan gadon ya durkusa akan gwuiwowunsa yana zubda hawaye wani bayan wani.
Kowa da abunda bakinsa yake furtawa na dg addua mamice ta rushe da wani irin kuka Hajiya Rukayya kuwa idonta kafewa yayi hawaye suka kasa fitama kawai kallon Safraz take zuciyar ta na bugawa, Prof kasa motsawa yayi kamar an shukasa awajen hk ya tsaya sai kafafunsa dasuka dau rawa, sakina Shahida Shahid razanace ta bayyana a fuskokinsu har Anty Adama sai data razana.
Alhaji Hashim ne ya tako yazo Gavan Safraz ya tsaya yana Kallonsa sai daya Dade tana yimasa wani irin kallo Sannan ya daukesa da wani gigitaccen mari ya hau dukansa baji ba gani yana kuka yana cewa, let kill you too I'm regretting get you as my son, Ashe ban saniba kai mahaukacine, are you in youth sane Safraz zaka kashe yar mutane? Da kyar Prof ya janye Alhaji Hashim dg kan Safraz duk kuwa ya fasa masa baki da hanci jinine kawai ke fita fuskarsa tayi jajawur.
Afusace Alhaji Hashim yayi waje yabar dakin, Cikin abinda baifi mintuna 10 ya dawo da police uku a bayansa, inda Safraz yake ya nuna musu sukayi kansa suka samasa ankwa a hannayensa, malam tashi daya dg cikin police din ya daka masa tsawa, da kyar ya iya mikewa tsaya hajijiya na kwasarshi, Abbah !! Safraz ya fada yana kallon mahaifinsa yacigaba dacewa, I know I'm guilty but I beg you for the sake of Allah do me a favor Inason in halacci zana izar matata ya karasa fadar haka yana daga hannunsa alamun yana roko, cikin tsawa Alhaji Hashim yace kufita dashi, Prof zai mgn shima ya dakatar dashi, suka fice da Safraz Wanda da kyar yake iya takawa yana tafiya yana tangadi kamar zai fadi.
~Sannu sannu kwane nesa muje zuwa page 17 yau da gobe bata bar komai ba~
0 comments:
Post a Comment