Blogroll

BANNER 728X90

Tuesday, 8 October 2019

Kuskurena Page 17 - ISMAIL SANI




❣🤦🏻‍♂ _*KUSKURENA*_❣🤦🏻‍♀
 
{The story is Interesting! Attractive! Impressive! to cut a long story short the story is a fascinating story the readers will entertain and enjoy it.} 


❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
**************************************
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣



               *BY*

 _*©, RAMLERT Y SALIS*_
         
             ~08037862213✍🏻~






*No part of this book maybe an object of privacy✖*


_Tuesd  , October 8 , 2019._

_*Page  17......*_



Ranace ta bakinciki da zubda hawaye, domin both site dukkansu yadda sukaga dare hk  sukaga rana kowa yana juyayin abun azuciyarsa, kowa hankalinsa ya karkata Neman dalilin dayasa Safraz aikata hk  saka  da warwara kowa yakeyi a zuciyarsa summan mutane uku mami, Hajiya Rukayya sai kuma sakina.

Mami tunaninta yaki tsayawa  a waje daya tayi kuka har idanuwanta sudena zubda hawaye headache mai karfi da fever suka rufeta, ta kure iya tunaninta tana son dalilin sanin  meyasa Safraz ya kashe matarsa, tunaninta yafi  karkata akan Karin auren da zaiyi ko shine ya haddasa matsalar wannan shine abinda tunaninta yafi  bata, " ko Izzatu tayi masa wani abune daya fusa  tashi yayi zuciya domin tasan  Dan nata  akwai matukar hakuri amma fushinsa bashi da kyau,   inhar sadin Karin auren nan ne hk  ta faru to tabbas nayi danasani nice sila Keenan? Tunda Nina tilasta shi badasan ranshi ba" sake-saken da mami tadinga yi kenan domin ta Dorawa kanta  alhakin salwantar ran Izzatu da sanya  danta  cikin wani hali, Nan sabo kuka yazomata tayi tayi har asuba.


Itama Hajiya Rukayya tunaninta bai wuce akan Karin auren da Safraz zaiyi ne hk  ta faru, tayi kuka kamar ranta  zai fita tun  Prof yana rarrashinta har yafara yimata fada, hk  suka kasance suma  har asuba.


Sakina  tashiga matsanancin damuwa domin duk tunaninta ya sauka  akan mahaifiyarta da yayarta sune  abun zargi a zuciyarta duk dataji ance  Safraz ne amma zuciyarta tana bata wani mummunan abu suka sake kulla mata adaren ranar sakina tayi kuka Wanda bata taba  yin irinsaba hk  take ta saka  da warwara har gari ya waye.


Safraz daya tsinci kansa arayuwar dako  a mafarki bai taba  tunanin ba wato police station dakin da aka sakashi Dan karamine ko kafarka bazaka iya mikewaba, black T-shirt a jikinsa me karamin hannu hakan yasa sauro suka samu daman cizonsa hannayensa har fuskarsa wani hawari dakin yakeyi hakan yasa baibi ta kan cizon da sauron sukeyi masa ba ya hau  vomiting kamar zai amayar da hanjin cikinsa, Abunka da Dan Hutu tuni yafita a hayyacinsa ya galabaita tamkar Wanda yayi one month bashi da lpy,  sai spiting yakeyi kamar mai ciki duk inda sauro yayi biting dinsa daya itching sai wajen ya kumbura, su biyarne a adan  karamin dakin sauran hudun sunyi barcinsu a tattakure sai snoring sukeyi very soundly, Snoring dinsu yabi ya cika masa kunne yadda yaga rana hk  yaga dare a rakube a zaune yana wiping tears in his eyes.


Fauza ce  zaune a gefen gado tayi tagumi tana kallon karima dake kwance on bed tana baccinta hankalinta kwance, Mami da fargabane suka cika mata zuciya ganin abinda kawartata ta aikata har yayi sanadin salwantar rai, A hankali ta sauke sight tana Dana sanin biyota gidansu datayi  anya bazata shirya  gobe  tawuce gombe ba domin a gidansu babu Wanda yasan tazo Nigeria, dama karima ce  ta dauki  duk wani responsibility data akan ana gama bikin su koma bawanda yasan tazo, duk son duniyanta sai take ganin bazata iya aikata abinda karima da mahaifiyarta suke kullawaba da hk  taja blanket itama ta kwanta.


Shima Jafar haka take a bangarensa matarsa tana zaune gefensa tana tayashi jimami mutuwar izzatu tayi matukar girgizata Dan dan zaman dasukayi na two months sun saba sosai sun zama cloth friends, ta zubda hawayen rashin izzatu sosai Sam lbrn da mijinta ya bata bata yadda dashi ba tafi dangantashi da sharri bata ji  cewa izzatu zata  iya aikata abinda ake ganin ta aikataba, kaf tunanin ya kare wajen gano shin waye me shiryawa izzatu wannan tuggun? Sam hankalinta kuwa kwallarta tunaninta sun kasa koda hasaso mata wani ko wata da hk  bacci ya dauketa, shikuwa jafar kwannan zaune yayi jimami gami  da tausayin abokinsa ya cika masa zuciya tawani bangaren kuma Haushi da tsanar doctor muhmud sun cika shi.



Tun  sassafe suka nufi hospital din, Alhaji Hashim sai daya riga  Prof isa asibitin, Suna zaune acikin office din doctor Mahmud, Babu Wanda yacewa wani qala shikuma doctor Mahmud yanata rubuce -rubucan yadda zasu karbi dead body na izzatu batare da wani problem ba.
 Alhaji Hashim ne ya kalli Prof yace, Alhaji Abdullahi!! Prof dagowa yayi ya kallesa batare daya amsaba. Alhaji Hashim yacigaba yacewa, Dan Allah kayi hakuri ni yanxu nasan babu Wani Abu dazan fada maka Wanda zai sanyaya zuciyarka amma Dan Allah ina  me baka hakuri Dan Allah, Nine zan shige gaba ganin anyankewa safraz hukuncin daya dace dashi muddi ba,a kashesaba to zansa ayimasa daurin  rai da rai, wlh ban taba tunanin safraz zai aikata hk  ba nasan yarone me nagarta  bansan me yajashiba ya aikata hk  wallahi kasancewar Sa Dana bazai sa  inkasa hukuntasaba inhar nayi hukuncin da baiyimaba ka daukaka kara a kowacce kotu a duniyar nan wallahi zan tayaka.

 Ajiyar zuciya Prof yayi Sannan yace, kadena mgn kamar dani da Kai bamu zama dayaba, kamar izzatu da safraz ba dayane a wajenaba kana mgn ne kamar nafison izzatu akan safraz to wallahi kayi *Kuskure* Alhaji izzatu tariga ta tafi kuma nasan idan an bincika akwai kwakwkwaran dalilin dayasa har yakai hannu ya daketa Allah takawo ajali safraz yazama sanadi Amma ba Dan yaso  hakaba shima safraz bazai aikata hk  da ganganba *KUSKURENE* izzatu ta tafi muyi mata zaton Alkhairi a yanxu nafi jin halin da Safraz yake ciki  banso abun yaje gurin hukuma ba abinda nafi damuwa insani  menene ya hadasu har ta Kai ga hk  na tabbata Safraz is a moral person he have good behavior kamar yadda na tabba izzatu ma hk  take.
  Allah sarki!!! Shine abinda Alhaji Hashim ya fada a zuciyarsa, Babu mai iya yin abinda Prof yayi sai  Adali kuma jurumin mutum Wanda addini da tauhidi suka gm ratsa zuciyarsa.

A dai dai lokacin jafar yashigo da sallama, duk suka amsa  masa Sannan suka gaisa.
An dau kamar awa  biyu da rabi  Sannan doctor yace subi bayansa a dai dai dakin ajiye gawa suka dakata shikuma ya Shiga.

 Kamar mintuna 22 hk suna tsaye suna jiran fitowa  gowar dan har an kawo motar da za,a sakata a ciki Sukaga doctor Mahmud ya fito da gudu wasu ma,aikata biyu na tura gado dauke da mutum a kwance a Kai an lullubesa, da gudu suke tura gadon iyakarfisu kamar zasu tashi sama shima doctor Mahmud yana binsu da gudu, duk inda suka wuce sai jama,a subisu  da kallo har suka isa emergency.


 Dakin da aka kwantar da Safraz nan suka Shiga suka rufo kafar cikin hanzari suka dorata akan gado har zuwa lokacin tanatayin  hiccup wato shakuwa da sauri daya dg  cikin nurses din ta juya  tafita  a dakin doctor Mahmud nan ya hau  Danna chest dinta in a haste, danna kirjinta yake da sauri da sauri har yanayin zufa ya dau kamar mintuna 5 yana dannawa Sannan nurse din ta dawo dakin dauke dawasu abubu gida 2 kamar dutsen guga sai dai basu kai dutsen guga girma ba da sauri doctor Mahmud ya karba cikin hanzari ya Dan tattaba jikin abubuwan alam ya kuna  Sannan ya rike daya a left hand din shi daya kuma a right. A saman kirjinta ya Dora wani irin firgita tayi ta zabura, yakuma  dorawa takuma  zabura kamar zata  mike zaune, Ana uku yana dorawa ta bude idonta tare da jan numfashi. _Alhamdulillah_ Doctor Mahmud ya fada tare da mikawa nurses abinda ke hannunsa,  tana kwance idonta a lumshe yazo saitin kunnanta yace _Izzatu_ kamar yadda yaji Safraz ya fada sa'ada ya suma, idanuwanta ta kuma budewa tar ta kallesa alamu taji  kiran   dayayi mata.

 Baya doctor Mahmud yaja  ya fada kan kujera ya zauna yana saukar da Ajiyar zuciya yace, _Alhamdulillah saura kadan  mu tabka babban *Kuskure* Allah mun godema daka  tashi wannan baiwarta taka damun aikata kisa cikin *Kuskure*_



_*I'm sorry fans for my Daley, kumin uziri ina  intensely busy gakuma   yanayin typing kuyi hakuri da wannan, nasan cewa  ~Sannu sannu kwane  nesa  muje zuwa page 18 yau da gobe  bata bar komai ba~*_


0 comments:

Post a Comment